Aisha Saddiqah Book 4 Complete Hausa Novel
Reading file: Aisha_Saddiqah_Book_4_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 12 of 17
I reserved the day for you only, as I reserved myself for 43 years waiting for the day. Please Baby, ki bani dukkan go ahead da juriyar ki da zan bukata, kinji?"
Kunya kamar ta kashe Aisha. Prince ya cigaba da kashe Aisha da kalamai masu dadi yana gaya mata irin tanadin soyayyar da yayi mata daga ranar data dawo, har zuwa karshen rayuwar su.
Ashe dai Ishaq da take ji a ranta akan yana gaya mata kalamai da suke zauna mata a rai bai iya komai ba. Ga inda kalaman fatar baki kadai ke neman narkar da zuciyarta a take. Har hakan ya saka mata (nervousness) akan zuwan ranar tarewarta dinnan da Prince ke ta maimaitawa, ba tareda Prince ya san ya saka mata nervousness din ba.
A daren yau Hammah ya gaya mata maganganu masu matukar nauyi. A ciki ya gaya mata cewa throughout the 43 years of his life he had never had a sex with anyone. Waiting for her…. his dream wife.
As a hopeless romantic, ya jira zuwan true love dinsa tsayin wannan lokacin, and today, he thank the Exalted Lord Almighty for bringing her to his life.
(Duk da Haseenah ta so ta saka Prince ya kauce hanya Kehinde bai taba yin abinda ya wuce kissing na shan minti da ita ba. Wanda a yau, wancan abinda ya dan gitta a tsakaninsu ma regretting dinsa yake yi, yana kara istigfari).
Ya yarda ba wata soyayya ta kwanciyar hankali da sakewa da jin dadi mara misaltuwa kamar ta auren Sunnah.
Da sanyin muryar Prince dake kasheta da dadadan kalamai cikin kunnenta Aisha tayi barci akan wayar, sai ji yayi numfashin ta ya canza a hankali mai nuna tayi barci ta bar shi da wayarsa, batareda ta san lokacin da barcin ya sace ta ba. Shine dai yaga wayar na cigaba da reading kuma bai kara jinta ba. Dole ya kyaleta ya kwanta shima. Amma kam yau Prince yayi wahalallen barci na azaba wanda ko zamanin samartakarsa dana tashen balagarsa baiyi irinsa ba.
Firdaus ta taba gayawa Nenne a cikin gorin da Maman Kiki tayi wa Aisha harda na 'Lefe'. Ashe Nenne bata manta wannan ba abin yana tsaye a ranta.
Don haka tun ranar da suka koma Lagos ta kira Hamma Abdulrasheed suka gaisa.
Nenne tace "Hammansu akan zancen lefen Aisha ne, na maka aure da dukkan hidimarsa amma lefe na al'adar Hausa Fulani na tuna ba’ayi ba na bar maka kayi da kanka. Zaka fi sanin irin dawainiyar dake cikin aure da wahalar sa".
Prince yayi murmushi yace "Nenne kenan, ai da kin fada tuntuni da tuni an yi. Yanzunma bata baci ‘better late than never’. Nawa zan bayar?" Nenne tace "da yawa. Don sawa zanyi a hada komai cikin kwana uku kafin Aisha ta baro Gombe ta dora hannunta akan lefen nan" shi ya san Aisha sarai bata wani damu da abin duniya ba balle wani lefe, kuma ita a wurinta maganganun Taiwo sun dade da wucewa bata kara waiwayarsu, amma yasan Nennensa sarai tunda ta rike shi a ranta to fa sai anyi. Hamma yace,
"to Nenne bakomai, ayi amfani da 'Black Card' dina dana baki ajiya kafin na taho, ba limit a cikinsa. In ce ko shikenan?"
Nenne tayi murmushi bata yi magana ba. Prince ya sake cewa "in ma kin karar da abinda ke ciki Nenne dana iso zan bada ‘dollar card’ dina a karasa, ince ko hakan yayi miki? Ayi lefe lafiya".
Yana sauka a Lagos kuwa gidansu ya zarce. Yace "Nenne yaya an gama lefen?"
Tace "an kusa dai". Har ya fita zai tafi gidansa ya dawo. Ya baima Nenne dollar card dinsa yace "in case wancan ya kare" Nenne na dariya a ranta tace Hammansu da Dade dinsa ‘are real Yoruba Demons’ akan son matansu basu da na biyu.
Nenne da Taiwo suka hada lefe na gani na fada ranar Friday Taiwo ta taho da lefen Gombe.
Sai Nani Oummana tasa wata Aunty dinsu da matar Uncle Abdulmajeed da tazo a lokacin tareda Taiwo suka kawo lefen gidansu Aisha da daddare.
Sai ga Taiwo har dakin Aisha yau, tana cike da 'guilt' mai yawa, Don gani take hatta lefen nan sabida ita aka yi shi. Ta kara jin nadama mai yawa. Sai ta bige da yiwa Aisha hirar Kiki, ta gaya mata Kiki na tafe sati biyu masu zuwa, kuma da tazo za'a saka ranar aurenta da Tosin.
Nenne kuwa taji dadi da akayi hakan, ko ba komai anyi drawing attention dinsu zuwa ga abinda yake cikon al'adar aure ga Hausa/ Fulani.
Taiwo ta sanar da Haj. Zainab sakon Nenne na cewa ita zata wuce Lagos da Aisha idan ta gama jamb dinta ranar asabar, to lahadi sai su tafi.
Haj. Zainab dai basu gaya mata zasu kawo lefe ba, don haka duk a dame take da rashin shirya musu komai bisa al'ada su kuma Nenne sun yi haka ne don kada su tasheta tsaye inji Nenne, duk da haka sai ta aika Sunusi ya kira Baba Furaira ta karbi lefen. Suka bada tukuici na kudi Inji Baba Barau. Aka rabu cike da farinciki da godiya ga juna.
Don haka Umman Aisha ta dukufa da yiwa Aisha gyaran da tuntuni take son yi mata cikin kwana biyun daya rage musu. Tasa an yiwa Aisha halawa da Dilka mai kunshi kuma tazo har guda ta rangada mata irin black and red henna dinnan. A gefe kwararriyar mai kitso tayi nata aikin, kitso yiri-yiri ta yiwa Aisha kamar da allura ta tsaga shi irin na 'yan Maiduguri.
Sai ga Aisha ta fito tas a cikakkiyar amaryarta tana sheki da sparkling. Abubuwa ne da tun wancan lokacin Haj Zainab taso tayi mata bata samu dama ba sai yanzu. Don haka Aisha ba karamin gyaran amarci ta samu ba, ta fito tayi das da ita.
Washegari Asabar Malam Yunus da kansa ya kai Aisha yin Jamb a location din da zata zana, Jamb dinda Aisha ta kallafawa rai yau Allah yayi an zana ta. Tun 7:30 suka fita karfe 8 suka shiga kuma kafin 10 Aisha ta gama. Abbanta ya jirata har ta kammala ya dawo da ita gida.
A daren Aisha suke sallama dasu Umma. Sun raba dare suna hira, Nenne ma ta bugo taji yaya Shirin tahowar tasu ta gaya mata ta gama shiryawa, sallama suke itada Umma. Aunty Taiwo tace sai 11 zasu zo su dauketa su zarce airport.
Hakan kuwa akayi. Malam Buhari da Taiwo a kofar gidan su Siddiqah 11 na safe tayi musu. Aunty Taiwo ta shigo suka gaisa da Umman Aisha, sukayi sallama, Sunusi ya kai kayan Aisha mota, ta rungume Umma, ta sake rungumeta. Har ta fita soro ta dawo ta sake rungume Umma ido fal kwallah. Umma dariya da dauriya duka, tace.
"Petel dina, zanyi kewarki! Allah ya tsare yayi albarka mai yawa".
**** **** ****
Su Aisha sun sauka Lagos da tsakar rana, nan suka tadda tarbar Nenne ta alfarma. Ga abinci (Yoruba traditional food) da fresh juice din kankana da apple Nenne ta shirya musu. Ga yoghurt da ta yiwa Aisha na musamman. Aisha na bude warmers din taga Ewedu ta hau dariyar farin ciki, tasan tayi kewar kalolin abincin Hamma har mafarkinsu take amma ashe Nenne ta fita sanin su take marmarin ci. Nenne kamar tasan me takewa dariyar, tace “shiyasa nayi miki su ai, na san rabonki da Yoruba food tun barinki Lagos”.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.