Complete Hausa Novels

Aisha Saddiqah Book 4 Complete Hausa Novel

Reading file: Aisha_Saddiqah_Book_4_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 4 of 17

Daga haka suka fice. Suka bar Taiwo a durkushe a wurin.
Taiwo sai kuka ta ke tana tsine wa wadanda suka kawo Siddiqah duniya.
Ba su jima da fita ba, Taiwo ta mike ta koma gidanta, nan ta hau hada kayanta.
Bari kawai ta hakura da aikin asibiti daga yau, ta koma wajen mijinta dindindin. Za ta wuce gidanta na Lagos, daga can ta yi shirin wucewa UK. Ba ta jin nan kusa za ta zo Ilorin balle gidan iyayenta a Lagos, tunda sun sallame ta a kan Siddiqah.
Ba wani biko da za ta je wa Kehinde, tunda shima yace bata da haske yanzu a idonsa. Yo da aurensa da wannan yarinyar ai gara mata zamansa yadda yake shi kadai a baya, da Dawakansa da soyayarsa da da kulawarsa gareta.

“Shin me ke damun Murjanatu-Taiwo exactly?”
Tambayar da iyayenta ke yi wa zukatansu kenan a ranar har suka koma Lagos, Kuma a washegarin ranar da suka koma suka ji labarin Taiwo ta baro Ilorin itama zuwa Lagos, kuma wai tayi resigning daga aikinta na asibiti, ba tareda ta yi shawara da kowa nata ba, sannan bata yiwa kowa sallama daga masarauta ba ta baro Ilorin.
Su dai sun san daidai gwargwado sun bata tarbiyya daya da Kehinde, sun mata nuni da sanin darajar kowanne dan adam, hali ne kawai, wato halayen dan Adam mabanbanta na halitta da dabi'a wanda bai da alaka da tarbiyyar da ta samu daga garesu.
Ko bahaushe kan ce hali zanen dutse ne. In ka shekara ba ka ga mutum ba tambaye shi wani abun daban amma banda halinsa. Tun tana yarinya suka fuskanci tana da nakasu a halayya da dabi’a.
Nenne a zuciyarta sai ta koma addu’a tunda nasiha da tunasarwa bazasu yi ba, ta soma addu’a tana rokawa Taiwo gyaruwar hali da saukin kai da halin tawali’u, da daukar duniya da sauki.
Don haka Taiwo ko kai amare gidajensu ba ta je ba, ta wuce gidanta na Lagos ta bar Hakeem a Ilorin.

*** *** ***
An wuce kai amare Lagos Prince ya samu ya sulale ya wuce Gombe.
Don ya gama yarda daga Nenne har Dade babu mai saka hannu ya lallashi Siddiqa ta dawo. Balle su je masa biko har gaban iyayenta. Ga shi ta ajiye masa wayarsa barin ma ya samu damar communicating da ita.
Ya sauka a Gombe yamma lis, kuma dama tun kafin ya taso ya gaya wa Malam Buhari direban Nani Oummana tasowarsa, don haka yana sauka ya tarar da shi yana jiransa. Malam Buhari akwai wannan kokarin ga iyalin Oummana sabida yadda suma suke kyautata masa. Yasa baya gajiya da hidimar zirga-zirgarsu a duk lokacin da suka bukata.
Prince na da gida wani madaidaicin gida flat a mahaifar Nennensa wato Gombe daya dade da saya tuntuni a GRA. Ba zai manta ba, Nani Oummana ce silar sayen gidan da yayi, a wani zuwa da yayi shekarun baya. Domin ta ce in yana so ya faranta mata dole ya sayi gida wanda iyalinsa za su ke sauka a Gombe, bazata yarda ta barwa Akannis shi bakidayansa ba, dole sai sun raba shi gida biyu an baiwa kowanne bangare hakkinsa, ko don ‘ya’yansa in sun taso su basu nasu muhimmancin na dangin Uwa domin kuwa lokacin da suka bada auren Nenne Sappa ga Akannis, sun ce, ‘ya’yanta dole su zo Arewa.
A wurin Uncle Abdulmajid ya sayi gidan da jimawa, kasancewar likita Abdulmajid din kafin komawarsa Morocco yana taba sana’ar ginin gidaje yana sayarwa tsakanin Gombe da Bauchi.
Duk da haka Malam Buhari bai wuce dashu gidannasa ba, ya wuce da shi kai tsaye fadar Gombe bisa umarninsa, yayiwa maigadin gidan a waya da yaron gidan yace a yi masa gyara yana iya zuwa yau ko gobe. Kai tsaye wajen Oummana ya sauka.
A sassan Uwar gari Hajiya Ummana, Prince ne zaune a gefen damanta, tanata zuba mishi hira cikin fulatanci. Sannan tana kokarin saka mishi abinci da fura, wadda ta ji kindirmo ga kananan kankara an zuba a ciki, amma Prince duk sonsa da fura, wadda yake yiwa shan gani kasheni idan ya zo Gombe, yau ko rabin kofi bai sha ba.
Nani ta ce, “Ai na san da zuwan nata, Nennenka ta gaya min komai. In shaAllahu za’a gyara komai”.
Prince ya ji dadi sosai, iyayensa da kakanninsa ba dai sanin yakamata ba da halin dattaku, duk abin da ya kamata su yi don saya wa ‘ya’yansu mutunci sun sani, bai san inda Taiwo ta debo bakin hali na rashin sanin darajar Dan Adam ba. Shi abin da ke daure masa kai da lamarin Taiwo, ta so Haseenah ma da bata da kowa, bata da nasaba, amma wai duk da haka ta kasa son Aisha. Aishar da saidai a nuna mata gadon mulki da sarauta kawai.
Ya nisa a hankali yana cewa cikin ransa, “Murjanatu baki kyauta min ba. Saida kika ga na samu sabon hope, wanda ya farfado dani daga suma na, na fada a wata korama da zaqinta yafi na zuma, gardinta yafi na madara, wadda ban taba fadawa ba a tsayin rayuwata, sannan ne zaki kore min wannan farin cikin dana nema na rasa (for over a decade), bisa wasu hujjojinki akan Aisha marasa ma’ana marasa makama. Aisha ki yafe mu!”.
Nani Oummana da yake ta san hakikanin matsalar da ta kawo Aisha Gombe. Nenne ta yi mata cikakken bayani a waya. Amma Oummana ta so ta tambayi Nenne me ya sa ta taho ita kadai? Ta tuna ana tsaka da bikinsu Fatima ne.
Ita ma ciwon kafa ne ya hana ta zuwa Ilorin, amma duk haularta da na Uban kasa wato yayan Nenne Sarki Ahmadu Jalloh ‘ya’ya da jikoki sun tafi suna can don yiwa Nenne kara. Da su aka yi komai, don haka Prince Malam Buhari ya sa a gaba ya yi masa jagora zuwa Jeka da fari.
Zuwan Prince na farko kenan gidan iyayen Aisha tun auren su.
Yana daga cikin mota mai duhun gilassai (tinted) yana nazarin gidan su Aisha da Malam Buhari ya yi parking a kofar gidan. Gidan karami ne, ko kuwa madaidaici, ya sha farin fenti mai santsi, sannan harabar gidan a share take tas. Soron gidan tsaf-tsaf da shi, tsafta ta zauna masa, ba dai gida ne na talakkawa can ba, don ko a layin gidansu Aisha ya fi kowanne fita da haske, kuma fentin da aka yi bai shekara ba, lokacin aurenta aka yi shi watanni tara kenan.
Buhari ya bude masa kofa ya fito, Prince yana sanye da yadin filtex sky blue, ya lankwasa hularsu ta yarbawa a kansa.
A fuskarsa yau ya dora farin glass, wanda ya dora a saman dogon hancinsa, Kamshin turarensa na ‘Baccarat’ tun daga soron farko sai da ya kai tsakar gidansuAisha. Malam Buhari ne ya zagaya ya bude masa kofa ya fito ya yi ta rafka sallama don bai ga yaron da zai aika ba. Wani matashin yaro ne ya fito daga gidan, wato Sunusi yaron da ke ma Umma aike. Buhari ya ce masa, “Ko Malam na gida?”
Sunusi ya ce, “Eh Malam na nan”. Yace “to don Allah ka gaya masa Abdulrasheed ne yazo daga Lagos”, Sunusi yace “toh, bari in gaya masa”.
Sunusi ya gayawa Malam Yunus zuwan bakon nasa. Malam Yunus ya dubi Umma itama ta dubeshi sai yace Sunusi ya shigo dashi.
Prince ya shigo ya tsugunna ya fara gaishesu, Umma da Malam Yunus suka karbi Prince hannu bibbiyu, fuskarsu ba yabo ba fallasa, Malam ya tambayeshi ya hanya da gajiyar biki da yadda ya baro su Nenne. Malam Yunus na cewa a ransa Prince baiwa Aisha laifin komai ba kuma ba shi ya zageta ba. ya gaya masa Aisha tana gidan Yaya Barau don shine waliyyinta daman, yace babu komai amman dai ka je ka samu Baba Barau magana tana hannunsa. In don ta ni ne ma Abdulrasheed nasan har yanzu akwai kuruciya a tare da Taiwo mace duk shekarunta ai baka rabata da halin yara. Kuma iyayenka su sun san su waye mu, ba don haka ba da bazasu matsa wajen nema maka auren Aisha ba.
Amman dai ina baka shawarar kaje ka samu Yaya Barau. Zan sa a raka ka yanzu”.
Prince yaji dadi sosai ya kara yabawa da dattakun iyayen Aisha. Ya sunkuya yana kara baiwa Ummanta hakuri, Umma tace “aibabu komai, banda rigimar Aisha ma in nice bazan kula ba”. nan Abdulrasheed yace “a’ah Umma, gara da tayiwa Taiwo haka, ni kaina bansan yaushe Taiwo ta zama mai wannan baudadden halin ba sai yanzu, kuma wallahi na mata iyaka da iyali na, koda wasa abinda ya faru bazai kara faruwa ba in sha Allah. Iyaye ai na kowa ne, wannan ba tarbiyyar da aka bamu bane, don Allah kuma ina kara bada hakuri”.
Malam Yunus yaji dadi sosai a ransa, ya tabbatar ya kuma kara yarda bai aurawa Aisha mijin banza ba tunda gashinan hakikanin gaskiyarsa yake basu hakuri, yake kuma Allah wadai da halin ‘yar uwarsa wanda shi kansa Malam Yunusya san tabbas wulakanci ba halinsu bane. Amma still he is so proud da Aisha ta nuna musu iyayenta ba abin wasa bane don haka bazata dau wulakanci ba.
Sannan kuma ya ga girma da soyayyar Aishaa idon YarimaAbdulrasheed wanda yasa ya kara jin dadi, amma duk da haka yace bazai shiga maganarsu da Baba Barau ba. gara yaje Baba Barau ya kara wana shi amma zancen kashe aure yanzu babu shi in sha Allahu.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.