Trending Hausa Novels

Auren Huce Haushi Book 1 Complete Hausa Novels By Maman Fatima

Reading file: AUREN HUCE HAUSHI BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN FATIMA.txt

Chapter 2 of 34

Page three đź”·
📖🖋️

.............. Tunda Mahmud ya fito daga gurin Baba Malam yake nazarin yanda zai bullowa lamarin, baya son ko kadan a Sami kurkure, guri ya Sami nesa da makarantar kasancewar Alhamis ce Yara basa karatun safe sai ya zamana yawancin su suna dakunan su.
Waya ya Ciro daga aljihun wandonsa yayi dialing din number Bata jima tana ringing ba kada daga magana ya Fara "kana jina Sameer sakon Dana turo maka kada a samu kuskure kayi kokarin ganin komai yayi yanda ya kamata fa".
Dan Jim yayi alamun ana fad'a Masa wani abu
"Ok to shi kenan take care".
Ya kashe wayar.
__

Nama ne da kayan miya ake ta shigo dasu cikin gidan da manyan kuloli sabbi Hajiya mama ce a kofar kitchen din na tsakar gida tana bada umarnin abinda za'ayi, yaran dake shigo da kayan ta kalla "wannan fa daga Ina?".
Magaji ne ya Bata amsa kafin yaron data tambaya ya fad'a Mata "tare muke Mama na abincin bakin Abba ne".
"Ikon Allah Naga ai an kawo wasu da sassafe dazu gasu nan har an kusa Gama aikinsu".
"Eh to shi dai yace a kawo wadannan ma".
Magajin ya fad'a Yana shiga dakin Amma.
"Kai dawa Kuma kake tafiya kana magana"
Cewar Inna maimuna.
Kusa da ita ya zauna Yana fadin "nida Hajiya mama ne kayan miya ne da Naman rago Dana kaji Abba ya Kara badawa aka kawo shine take magana ko yayi yawa kame?"
Dan murmushi Amma tayi "Abban Nan naku baya son a zauna lafiya wallahi magaji kamar zai aurar da Yara uku sai irin wannan shidima yake haka".
Kai magajin ya jinjina "Amma kenan kin manta yanda Abba keson Zahra ai kawai kowa ya zuba Ido ana auren uwar masu gida tab ai kowa sai yasan anayi Yasin, ki Bari kawai Ammah Nan zan kawo nama a ajiye min".
Ya fad'a Yana dariya ya nufi kofar fita saboda sallamar wasu Mata da yaji a kofar dakin.

___

Daki Mahmud ya koma ya samu Habib a tsaye a tsakar dakin da alama daga wanka ya fito, saida ya Gama wayar sannan ya kalli Mahmud.
"Wai ina kaje ne? Naga fitowarka daga gurin Baba Malam kafin na saka caji na nemeka na rasa, Bilya ne ya kirani Wai mu sameshi a hayin Banki shi Yana can yaje da masu aiki su duba yanda za'ayi gyaran"
Dan Dafe Kai Mahmud yayi ya Dan fesar da numfashi.
"Ikon Allah Wai Daman kamar jira kuke ace za'ayi min auren Nan kowa sai rawar jiki yake yi, daga fad'a shine har ya want kwashi jiki da masu aiki ya tafi tun garin Bai Gama watstsakewa ba".

"Naka wasa ne Alaji, aini yanzu haka mun Gama magana dasu Bashir sunce mun gasu Nan zuwa har suna cewa shegen zurfin ciki ne da Kai baka fad'a musu ba jiya ko kunya kakeji irin ta Mata".
Ya karasa maganar Yana dariya.
Har ya nufi gurin mirror ya tsaya "kaji na manta ba Salis yace na tura Masa cikakken sunan da ze saka a IV da zeyi a waya ya turawa friends na kusa".
"Ok ba matsala ka tura Masa kawai da sunan aika Sani ba saina maimaita make ba".

Misalin karfe Sha daya na safe wata bakar Hilux sabuwa kar ta dira a kofar gidan Malam Bukar.
Lokacin yaran sun firfito suna sugogin su masu wanki nayi masu wasa nayi Amma idan ba fada maka akayi bazaka taba cewa yaran Almajirai bane kowa cikin tsabta Kuma a lokacin anyi hutun makarantar book shi yasa basayi tunda suma tsarin makarantar gwamnati suke bi.
Mutane biyu be suka fito daga motar da sauri 'yan samarin dake kusa taso da sauri suna fadin barkan ki da zuwa kasancewar sun saba dasu sosai sune wadanda suke kawo musu tallafi daga organization din.
Da sauri suka bude musu falon saukar bakin Malam kafin wani ya shiga ya fadawa Malam din.

Ba jimawa Malam din ya fito suka gaisa a mutunce, sannan suka gabarwa da kayan abincin da suka kawo sannan suka gabatar Masa da bukatar daukar Mahmud zuwa wani taron karawa juna Sani na makarantun tsangaya Wanda za'ayi a kano, tunda shine Wanda suka dauka aiki a Nan tsangayar yake wakiltar su kuma gobe juma'a za'ayi taron na Rana daya ne kawai.
Dan Jim malam din yayi kafin yace " Ikon Allah malam Sameeru ga koshi ga kwanan yunwa WALLAHI shi Mahmudan dai baze Sami damar halartar taron nan naku ba, domin a goben in Sha Allah za'a daura Masa Aure".
Cikin wani irin madaukakin mamaki Sameer dake kusa da Malam din Kuma jagaban tafiyar ya kalli Malam Yana cewa.
"Aure! Kuma Malam?".
Kai ya jinjina Masa alamar tabbatarwa, "yanzu haka suna can gidan da ze zauna ana dudduba gyaran da za'a Masa duk da gidan Bai jima da kammaluwa ba kasan kullum abin duniya sabuntashi akeyi".
Kai ya jinjina ya hadiye wani yawu da kyar shifa duk ya shiga rudu meye hakan Wai Kuma.

Fara'ar dole Sameer ya kirkiro Yana kallon Malam yana fadar "Masha Allah Abu yayi Dadi to ai mu wannan lamarin namu ne munzo a dai dai kenan tunda Abu ne na ma'aikacin mu koma kunya zatayi Masa malam kada kuyi komai yanzu zanyi waya za'ayi duk abinda ya kamata tun daga abinda ango ze saka har abinda za'aci duk Yana karkashin kularmu tunda mu yakewa aiki, Kuma zamu zauna sai an daura auren damu in Sha Allah. Maganar taron Kuma sai dai a daga zuwa wani lokacin Dan bamaso wani yayi missing gaskiya".
Tunda Sameer ya Fara Kora bayani malam ke jinjina Kai saida yake Aya sannan ya Sami zarafin magana.
"To malam sameeru anyi haka abin fa da yawa kids bakuzo da Shirin wannan abun ba kunzo Kuma kuyi ya kuyi makarbiya ai da wahala abun".
Dariya Sameer din yayi Yana fadar "malam ba abunda ze gagara kungiyoyin masu karfi ne, yanzu ma ga wannan saboda biyan sadaki".
Ya aje Masa cheque na Banki suka Mike Yana fadar "Bari na Nemo shi a waya sai muje muji meye shirye-shiryen nasu, a huta lfy".
Suka kad'a suka fita.

_____
Kyakykyawan guri ne Aunty Hasana ta kama inda za'ayi mother's day din gurin ya kayatu ba karya kudi dai an kashe su gurin Kama event center din, anyi taron Mata 'yan gayu kamar ba gobe amarya tasha kyau kamar a dauke ba boye.
Ga wani slow music da mc din ya saka na wakar Amarya da ango kowa ka gani cikin nishadi yake sabanin Amarya da Yayarta Banda ta Riga ta gayyato mutane harda wadanda sukayo Mata tafiyayya sukazo da ba abinda ze saka tayi wannan taron to Amma mutum Bai Tara Sani ga Allah ba.
An raba kayayyaki na alfarma na bikin, sai magariba taron ya tashi, zuwa yanzu 'yan Qananan maganganu sun Fara fita a tsakanin kawayen Zahra tunda har zuwa lokacin ba wani duriyar Ango ko wani nasa, sai Dan kus-kus ake abinda yafi bada mamaki bai wuce ganin anata faman programs ba normal.

Su Mahmud Basu samu kansu ban sai bayan sallar insha'i lokacin suka zauna Dan wuni guda suna ta faman sunturi daga can zuwa can abin dai ba sauki dan su sameer suna zuwa gidan suka babbago aikin da sai anyi sati ba'a Gama ba Dan sunce tsarin gidan gaba daya za'a sake, basunda ta cewa tunda oganninsu ne sai godiya suka dunga zubawa harda su Bashir.
Gurin karfe goma malam ya Kira Mahmud a waya yace yazo cikin gida ya same shi.
Saida ya leka falon iya Abu suka gaisa tana faman jansa tana ita ce ta karfen Dan haka ita zata koma sabon gidan a kawo Amarya nan.
Da haka ya karasa turakar malam Yana zaune a falo Yana sauraren wa'azi a TV, yayi sallama Malam din ya bashi izinin shiga, Nan kasa ya zauna Yana gaishe da malam din.Wasu manyan ledoji malam din ya nunawa Mahmd Yana fadin.

"Dauko wadan can kayan ka duba daya Wanda nasa a kawo maka ne biyun Kuma wadannan masu kungiyar ne ta taimakon tsangayu suka kawo ga lemuka can da ruwan roba sun kawo yafi catoon dari sunce kada ayi abinci ma duk za'a kawo, har na rasa da wane bakin zan gode musu, sai dai Ina rokon Ubangiji s.w.w yafi mu yabawa, naji su Habibu ma sun ce sun dauko aiki Mai yawa a wancan gidan ko?"
"Eh wallahi munyi-munyi su Bari suka Kiya Wai haka aikin Qungiyar yake in dai kana musu aiki idan wani Abu ya sameka Mai Dadi ko marar dadi su zasu tsaya maka".
"Alhaji yace min kun shiga dazu bayan sallar magariba har da bakin kunyi Masa godiya, kun kyauta haka ake so".

Lokacin Mahmud ya koma dakinsu Habib baya Nan gurin da yake aje makullin lifan dinsa ya duba ya kuwa you sa'a yana nan, lodojin ya zube a kan gado ya dauki makullin ya rufe dakin ya hau mashin din yayi gaba.
Bai dawo ba sai kusan Sha biyu da rabi har lokacin kuma Habib baya dakin yasan suna can suna kujuba kujuba.

Yauma Zahra taso kwana a dakin Aunty Hasana saboda tana bukatar kadaicewa Amma Sajida ta matsa Mata da mita Saida suka tafi Amma fa zuciyarta Bata da nutsuwa gashi tana ankare da Aunty Hasana tun jiya da dare a taje can gida cikin gari Bata da nutsuwa ko alama Amma tana ta kokarin ta basar sai dai ko Yaya mutum ya shiga damuwa indai kayi Masa farin Sani zaka fahimta, ita Abu mafi Bata mamaki yanda aketa kwaramniyar bikin ba wani canji sai dai abunda baza'a rasa ba duk da Daman ba wata muguwar bidi'a ba ta had'a, walima ce kawai Bata Sami ba saboda tace ita malam Tijjani Ahmad zeyi Mata Kuma bayanan yana Umara.
Tunda tayi sallah ta kasa tashi daga gurin tana kallon su Sajida sunata sabgarsu, Amma ita da wata irin faduwar gaba ta tashi ta rasa nutsuwarta kwata kwata da kyar ta tsahi sauko kasa gurin Aunty Hasana a fall ta sameta tana hadawa Abbansu Haidar break fast.
Gurin dining din ta karasa tana gaishe shi sannan gaida Auntyn.
Dakin Auntyn ta shiga kwanciya tayi tana ta faman sakawa da kwancewa zuwa yanzu dai tasan tabbas da matsala sai dai yanda ba Wanda ya fad'a Mata shi yasa itama ta zubawa sarautar Allah Ido taga iya karshen film din tasan ko menene yau dai za'a yita ta Kare tunda yau ne deadline duk wata kunbiya kunbiya za'a zazzageta.

Tun karfe goma Mai yiwa Amarya make up tazo Amma kememe Zahra tace ita bataso a kyaleta aka dunga yiwa kawayenta, ganin guri ze kure ne Sajida take ta fadawa Aunty Hasana Saida tazo sannan akayi Mata light makeup Amma fa duk da hakan tayi karshen kyau, farin material ne ta sakata Mai touching din sky blue sai aka daura Mata head shima sky blue din takalman da pos din duk sky blue din ne.
Wani san sanyan kyau tayi na ban mamaki, komai na Zahra Mai kyau lallai zaharar ce Dan duk cikin kawayen Bata da mahad'i.

A babban masallacin juma'a za'a daura auren Masha Allah, ango ya fito Shar abokansa sai mamakinsa suke Basu taba sanin kyawunsa da cikar haibarsa ya Kai haka ba sai daya fito sun Sha mamakin kwarai har wasu suka Fara kokonto a kansa, Yana kallon yanda idanun sukayi Masa caa.
Dan dakakkiyar getzener ta saka ga takalman da agogo ga hula, Sam bazaka taba cewa Wai alamajirin malam bane ba, ga wani irin kamshin tunda ta tumkaro taron abokanensa kamshin ya hade gurin.
Daga gefe sameer ne da abokinsa Naraddeen suna tsaye lokacin da Mahmud ya fito Sameer ya kalli Naraddeen din yace "wallahi wannan guy kwallon Dan duniya ne na rasa Gane kan alkiblar daya kalla Wai aure zai daura shi kadai kamar marara gata, ni so nake Naga karshen wannan wasan kwaikwayon nasa.
Daga inda yake tsaye ya kafe Sameer da Ido ko Bai fad'a ba yasan me yake nufi tun jiya yake tuhumarsa aka zuwa da abokinsa da yayi duk da ya nuna Masa wannan ba wata matsala bace Amma har yanzu Yana hukunta shida idanunsa.

Masha Allah dubban mutane ne suka shaida daurin Auren FATIMAH ZAHRA AHMAD SANI da Angonta MAHMUD MUHAMMAD DANGE akan sadaki dubu dari uku lakadan ba ajalan ba.

Daurin aure daya bawa dubun mutane mamaki bare wadanda sukazo daga bangaren Mushahu sunyi mamaki kwarai sunan Amarya dai shine Amma ba mijin daya gayyato su bane yayin da yan unguwa ya Zama abin kasawa a faifai ana yawo dashi, da yawa na ganin beken Alhaji Jafar na aurawa bakon da ba'asan asalinsa ba yarinya kamar Zahra yayin da wasu ke fadar ai Dan ba 'yarsa bace shi yasa yayin wannan danyan aikin.
.......
💋❤️AUREN HUCE HAUSHI 💋❤️

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.