Trending Hausa Novels

Auren Huce Haushi Book 1 Complete Hausa Novels By Maman Fatima

Reading file: AUREN HUCE HAUSHI BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN FATIMA.txt

Chapter 4 of 34

Page five
📖🖋️
_______ Shiru dakin ya dauka har zawan lokacin da Aunty Hasana ta idar da sallar.
Dan juyowa tayi kadan tana fadin "wa'alaikumus Salam warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu, sannunku da zuwa Bismillah ga kujeru nan ku zauna".
"To mun gode Aunty" Sameer ya fada.
Cikin ladabi da mutuntawa suka gaishe ta tare da tambayar Mai jikin, ta amsa musu da sauki, sai kuma dakin ya Kara daukar shuru Zahra dai tunda ta rufe ido Bata Kara gigin budewa ba, ita ji take duk ya cika dakin ita tun ganinta na farko dashi a duniya ya birkita Mata lissafi, Kuma saboda Allah meya kawo shi gurinta asibiti duk da tasan mutumin Ya Abdul Hakeem ne Amma sai taga kamar ba sai yayi Masa Kara ba, ko Kuma yazo wata sagbar ne asibitni ya Sami labarin shine ya shigo ya dubata.
Magaji ne ya shigo dakin da sallama sai Kuma ya Dan tsaya baiyi tunanin ganinsa ba Sam da fara'a ya karaso Yana fadin "Ashe Kuna Nan ai tare muke da Ya Abdul Hakeem ma".
"Ok" abinda Mahmud ya fad'a kenan
Shi Kuma Magajin ya karasa gurin Auntyn Yana gaishe ta.
Abdul Hakeem ne ya shigo Yana rike da wayarsa a hannu da sauri ya karasa gurinsu Mahmud din Yana fadin "A'a angon ne da kansa" Yana Mika masa hannu.
Saroro Aunty Hasana tayi ita wace iri ce kawai dai taga sun shigo sun gaisa wallahi Sam Bata kawo ba ita da akace Mata Alamajirin Baba malam ne ai ta dauka irin wannan gaddawan ne, yo ta Ina wadannan sukayi wani Kama da kolaye ai ita zallar ilimi ta gano da wayewa a tattare dasu.
Hanyar wajen ta nufa tana janye da hannun magaji duk sai taji kunya ta kamata Ashe sukanta ne.
Ita kuwa Mai gayya Mai aikin ai tana jin an ambaci ango ta bude idonta girjinta Yana wata irin dokawa "ango a nan to waye a tsakaninsu da suka shigo tare?
Abdul Hakeem ne ya kalli gurin gadon Yana fadi.
"Masha Allah! Ashe kin tashi, ya jikin?"
Ya fad'a Yana karasawa jikin garon Sameer ma Dan matsawa yayi Yana dubata Kai kawai ta gyada musu, tana kallon Ya Abdul Hakeem din, kallo irin na neman Karin bayani.
Yi yayi kamar Bai Gane ba ya juya yana yiwa Sameer magana suka fita.
Har suka fice Bai dago ba Yana ta faman tab'a waya sai da ya Mula Dan kan shi sannan ya tashi ya tunkari gadon.
"Ya jikin?"
Ya fad'a Kai tsaye, Bai Kuma jira ta amsa ba Dan ko kwakwkwaran motsi ta kasa sai tunanin da yake Mata Kai komo.
"Badai wannan bane ake nufin an daura min auren dashi Amman da Naga ta kaina".
Shine ya katse tunaninta.
"Ki kwantar da hankalinki ki daina saka damuwa a ranki da kannan shekarunki, ki kuma dagawa Ammah Ă­ nata hankalin, idan nine bakya so ba damuwa Nima kusan hakan take. Amma kada mu watsawa iyayen mu kasa a ido Mana tun yanzu gara ki nutsu ki kwantar da hankalinki daga baya sai a duba Mai yuwuwa tunda nasan bazaki so Zama da almajiri marar karatun boko mai zurfi, ga karqncin wayewa ga rashin madafa ta yau da kullum, Nima kasada ce tasa na yarda da tayin da akayi min tunda Naga nema ake a tozarta min da iyayen a kunyata su a idon duniya aci mutuncin su".
Ita da'i ko motsin kirki ta kasa da gaske gani take duk ya cika dakin, ga wani fitinan kamshinsa duk ya cika Mata hanci.

A bazato taji ya Dan shafi gefen fuskarta idan ba kunnenta ne suka jiyo Mata ba da'i dai ba sai taji kamar yace "my previous" a hankali sannan ya Mike Yana fadin "Bari a kawo maganin ki saimu wuce gida tunda doctor yace zamu iya wucewa, Amman yace ki rage yawan tunani Yana haddasa cututtuka".

Har dakin Amma Abdul Hakeem ya raka Zahra lokacin duk yawancin bakin sun tafi sai 'yan uwan Amma na Mubi Dana Jimeta sai Kuma Aunty Hasana da take dakon dawowar su, ai tunda magaji ya Kara Kora Mata bayani akan Mahmud ta tafi daga asibitin tunda Mai dungurungum din yazo ita bataga ta Zama ba.
Saida ta matsawa Zahrar tayi wanka Tasha tea da magungunan ta kwanta sannan tayi haramar wucewa gida.

Sai wurin karfe Tara sannan Hajiya mama ta shigo dakin tana fadin "wallahi daga idar da sallar ta barci ya dakeni sai Dana tashi zilai Mai wanke wanke take fad'a min an dawo da Zahra har sun shigo sun duba ta".
"Wallahi kuwa ai jiki da sauki yanzu Tasha magani ta kwanta"
"To Allah ya Kara lfy, Wai Hajiya wanene mijin yarinyar Nan ne naji ana fadar Wai cikin Almajiran baba Malam ne, shine nace haba yaushe Alhaji zeyi wannan danyen aikin ya rasa bazai bawa aure Sai a cikin Almajirai".
Inna maimuna ce tace "ai mu Hajiya ko waye Alhaji Jafar ya aurawa Fatima wallahi mun karba da hannu biyu mun gode tunda mun San har abada Babu cutarwa a tsakanin Asama'u da dashi da ita Fatiman da abinda ya Haifa bamu taba ganin banbanci ba, Dan haka mun karba da kyakykyawan niyyarsa Allah ta tabbatar Mana da Alkhairi".
Gaba daya suka amas "Amin"
Hajiya mamar ta Dan jima a dakin kafin ta koma dakinta.
Bayan Zahra tayi sallar Asuba ta gama Azkar dinta komawa tayi ta kwanta har lokacin kanta Yana Mata ciwo kadan kadan, sai gurin takwas da rabi Inna maimuna ta tasheta tana fad'a Mata tayi maza ta kimtsa Abbansu Yana nemanta.
A gurguje tayi wankan ta fito lokacin an kawo Mata kunun gyada da fanke, kunun gyadar kawai tadan Sha kadan ta shafa lotion dinta ta saka doguwar rigar atamfa ko dankwalin Bata daura ba ta fito cikin takunta na nutsuwa Wanda da yawa mutane ke gani a matsayin yanga da jiji da Kai.
A tsakar gidan suka rinka gaisawa da tsirarun yan uwansu na Mubi da sauran ma'aikatan gidan Mata.
Da sallama a bakinta ta shiga falon Abban nasu, tayi mamakin ganin kusan duk 'ya'yan Abban suna Nan sai su Ammah da Inna maimuna da kanwar Abban Maman lafia.

"Zo nan kusa dani Uwata".
Abban ya fad'a Yana murmushi, itama murmushin tayi ta karasa kusa dashi ta zauna nata fadar "Abbana Ina kwana?".
"Lafiya kalau Alhamdulillahi Uwata".
Sannan ta juya tana gaishe da jama'ar gurin.
Said Kuma dakin yayi shiru.
Abban ne yacewa Imam "Mai sunan Malam ayi Mana addu'a".
Ya jima Yana addu'a sanan aka shafa. Sannan Abban ya Dora da cewa.
"Alhamdulillahi ala kulli halin, dole ne mu godewa Allah s.w.a a cikin kowane Hali mutum ya Samu kansa, kowa yasan yanda lamarin Auren Uwata ya ringa kasancewa a baya abune ba Mai dadin maimaitawa ba, to wannan karon ma tarihine yaso maimaita kansa Amma na yanzu sai yafi sauran tada hankali ni Kuma Naga a wannan gab'ar bazan Kara bada wata kafa ba wadda za'a dunga walagigi da rayuwar yarinya karama ba kamar Uwata. Sunanta Ya kira Fatima dago ki kalleni, cikin girmamawa ta dago kanta kamar yanda yayi Mata umarni. Hannunsa yasa ya nuna kansa yace kina ganin zan iya zaluntar k?" Da sauri ta girgiza Kai hawaye na zubo mata.
Yace "To Fatima na daura Miki aure da bakon yaron Nan Mahmud na wajen Aminina Malam Bukar". Duk da taji haka daga bakinsa a jiya Amma Bai hanata kara shiga rudu ba saboda wannan taji daga bakin da bazeyi Mata karya ba, Nan da Nan ialahirin jikinta ya shiga rawa wallahi ita a jiyan jinsa kawai take gani take kamar almara ce kawai.
Muryar Abbansu ce ta Kara katse Mata tunani "kiyi hakuri Uwata kowa da irin jarabawar da ubangji yake Masa ki dauka taki jarabawar kenan, ki yadda da kaddararki sai Ubangiji ya jibinci lamarinki wannan ba hadin kowa bane hadin Allah ne, kiyiwan mininmi biyayya in Sha Allah zakici ribar rayuwa, ki cire yaron Nan Musbahu daga zuciyarki ki rungumi abinda Allah ya baki. Allah yayi Miki albarka yanda Kika yi min biyayya Allah ya Baki 'ya'ya Wanda zasuyi Miki biyayya kema, Allah ya albarkaci aurenku ya tsone idon makiya da mahassada".

Hajiya mama ce ta fasa Kuka tana fadin "Haba Alhaji wannan wane irin danyan hukunci ne? ya zaka dauki 'yar marainyar Allah ka baiwa Wanda ba'asan asalinsa ba, ai duniya saita zage ka Dan Allah ka janye maganar Nan da wannan ba gara kaba salmaun gidan Hajiya Dago ba tunda ya jima Yana son yarinyar Nan Amma ka Hana shi"
Kowa a falon kallonta yake ba Wanda ya tofa sai danta Hamza yace "haba mama menene haka kikeyi Dan Allah kiyi shiru da wannan maganar salmanun me Allah ya sauwake me za'a da wannan zuri'ar".
Hannu Abban ya dagawa Hamza Yana fadin "ya Isa haka tunda ka Bata amsa basai nace komai ba, Amman ki rubuta ki aje in Sha Allah sai wannan auren ya Zama abin kwatance Kuma abin alfahari duk Wanda ze zageni ya Dade Bai zageni ba, Kuma duk Mai ganin zalunci ne yasa na aurawa Fatima Mahmud na barshi da Allah wallahil Azeem ban taba kallon Uwata a matsayin 'yar wani ba kullum Ina Mata kallon 'yata malak malak a makaranta ne kawai ban saka Mata sunana ba shima nayi haka ne Dan tasan nata mahaifin ta rinka Yi musu addu'a".
Addu'a Abban yasa Imama yayi yaba kowa izinin tafiya Amma yace Ammah ta tsaya ita da Hajiya mamar da Inna maimuna da Maman lafia.

Aunty Hasana ce ta kamo hannun Zahra zuwa dakin Ammah tana kuka, yarinyar tausayi take Bata kamar yanda Abban ya fad'a ana walagigi da rayuwar ta.
Cikin bed room din Ammah suka wuce, bayan sun zauna ne Auntyn ta riko hannun Zahrar "kiyi hakuri kinji Allah Yana sane da halin da kike ciki, Dan Allah kad'a ki watsawa Abba kasa a Ido ki bijirewa auren nan wallahi irin wanna auren Yana albarka fiye da tunanin".
Wasu sabbin hawayen ta goge. Cikin shashhshekar kuka tace "wallahi Aunty nifa tsironsa nakeji idan muka hada Ido wani Abu nake gani a idonsa".
Sororo Auntyn tayi kafin tace "ban Gane ba tsoronss kamar Yaya, Daman kinsansa ne runtuni?.
Kai ta gyada Mata alamar Eh.
"Allah ya kyauta" kawai Auntyn tace.
"Ko meme ma dai wannan tsakaninku ne kin gyarota can".
Ta Mike tana fadin "Bari na koma gida sai zuwa an jima zamu shigo da Sajida da Amatu itama Bata tafi ba jiyan.

********Tun bayan suka dawo daga sallar Asuba Mahmud yake ta faman aiki a cikin laptop dinsa, Yana kallon Sameer Yana kwasar barcin gajiya. Bai gama aikin ba sai kusan karfe takwas na safe, kai tsaye toilet ya nufa ya jima a ciki kafin ya fito daure da towel a kugunsa karami Kuma a hannunsa ya goge sumar kansa me baka sidik Mai laushi Saida ya shirts cikin wani farin yadi filtex marara nauyi ya feda turarensa Alburaq sannan yaje gefen bedside ya dauki wayarsa ya kunna.
Abinci ya bukata a kawo musu, yana Gama wayar Kira ya shigo sunan Habib ya gani, ya daga da sallama daga cen Habib Fara fadar.
"Habe Dan Allah dukka tadawa Baba malam hankali baka kwana a gida ba abinda baka Saba ba Koda wasa duk dare zaka dawo Amma jiya daga Bari kaje ka dawo shi kenan kayi layar zana Kuma ka Kama ka kulle waya".
Dariya yayi Yana cewa "kana tunanin Kona bi dare nayi Gudun auren dole ko?"
Shima Habib din dariyar yayi.
"Ka Gudun Mana idan ka Isa mai wannan tsaleliyar Ina zaya ya barta koka gudu ka dawo da kafarka, kawai da malam ne ya matsa yaji kana ina".
"Ok shi kenan Bari na kira shi Dan hankalinsa ya kwanta Ina Nan tare da Oga Sameer shine ya rikeni nayi Masa wani aiki".
Yana kashe wayar ya nufi sofa ya zauna yana janyo stool din da aka Dora abincin.
"Oh ni Sameer yaushe na rikeka? ka rikeni dai ka Hanani tafiya ka barni da kame kame ga madam can tana fama da kanta ba mataimaki gaskiya yau in Sha Allah sai kano".
Ya fad'a yana nufar toilet shima.
Can hayin bankin suka Fara zuwa gurin masu aikin gidan Masha Allah aikin yayi nisa kamar ba jiya aka Fara ba Sam an canzawa gidan fasali kamar bashi ba, duk abinda ake bukata Sameer ya danka shi a hannun Binya.
Sannan suka nufi cikin gari.
Wani mall suka shiga Mahmud ya jido kayan fruits dasu kayan tea sai chocolates dasu farm fresh yogurt da fresh milk. Leda uku aka cika manya Saida suka dauki hanya Sameer ya kalli Mahmud yana fadin "wadannan kayan fa yallabai na waye".
"Dubiya zamu saika Bata tunda ni dai kowa yasan bani da kudin sayansu.

💋❤️ AUREN HUCE HAUSHI 💋❤️

đź”· Page sixđź”·

P📖🖋️

________Sun jima a gurin Baba Malam Yana yiwa Sameer godiyar dawainiyar da yasha akan wannan lamarin, sannan yayiwa Baba Malam din sallama akan zai wuce sai hutu ya Kare zasuzo da mutanen su suna son su kawo wasu ayyukan da za'ayi.
Har gurin mota Malam dasu Habib sukayi Masa rakiya, Baba malam Yana fadin "Bari muyi addu'a".
Nan yaja doguwar addu'a akan Allah ya tsare hanya, har Sameer ya shiga mota ya fito ya nufi Malam Wanda har ya Fara tafiya, sai Kuma yaja ya tsaya Yana jiran karasowar Sameer din.
Dan risinawa yayi Yana fadin "ko za'a samu Wanda ze rakani na Kara dubo jikin wannan yarinyar?"
Wani kallon kasan ido Mahmud ya bashi dashi "Wai yarinya".
"To! To! Masha Allah ai sai kuje da Mahmud din da Habibu kuga jikin, ai wannan tunani ne Mai kyau.Nima na shiga da safe gurin Alhajin naji yata kwana".
Har cikin harabar gidan Sameer ya shiga da motar, Abdul Hakeem Habib ya Kira kafin su shigo ma ya fito Nan Harabar gidan Yana jiransu.
Shi yayi musu jagora zuwa falon Abban, yayi murna sosai da ganinsu sun gaisa sosai sun masa godiya sosai da karamcin da yayi musu, yaji dadi sosai Dan har ya ringa tsokanar Sameer Yana fadar "wato tunda kazo gabatar da aikinku ban sake ganin kafarka ba a gidan Nan sai yau dana baku Mata ko? Dan na lura baka da aminin daya wuce Mahmud a garin nan. Masha Allah, Malam ya fada min duk Fadi tashin ku akan lamarin Allah ya saka da Alkhairi yabar zumunci".
Suka Amma da "Amin ya Rabbi".
Mahmud Alhajin ya kalla Yana fadin "kayi hakuri fa Mahmud munyi maka nauyin kuka".
Kai ya gairgiza Yana fadin "ko daya wallahi ba komai nagode, Allah ya saka da Alkhairi ya Kara lafiya Nisan kwana Mai albarka"
"Allahumma Amin. Allah yayi Albarka, ya baku zaman lafiya ya baku zuru'a Mai Albarka, sai ayi ta hakuri da lamarin Mata fa. Abdul Hakeem ku shiga ciki su gaisa da Iyayen nasu".

Wannan shine shigar Mahmud na biyu gidan, na farko lokacin da magaji yayi accident da mashin suka shigo shida Abdul Hakeem da Hamza ya duba shi a dakin Ammah, dan ma lokacin ba kowa a gidan sunje gaisuwar mutuwa.
Directly dakin Hajiya Mama Abdul ya nufa dasu, Zilai Mai musu wanke wanke ce tayi zuruf ta shiga dakin Ammah.
Tana fadin "Ammah Ina Jin fa ga mijin Zahara'u Nan sun shiga dakin Mama shida Abdul Hakeem da wasu inaga abokansa ne".
Ta juya ta fita.
Gyalen Inna maimuna Ammar ta dauka dake kusa da ita ta yafa a jikinta.
Da sallama Abdul Hakeem din ya shigo Yana fadin Bismillah ku shigo Mana, a nan kan carpet a kasa suka zauna suna gaishe dasu Ammar tare da tambayar Mai jikin.
Abdul Hakeem ne yace " Inna mijin Zahra ne da ubangidansa suka shigo duba ta shi yau ze wuce shine yace a rako shi ya Kara dubata da jikin nata".

"Kai Masha Allah an gode madallah Allah ya saka da Alkhairi ya maida ka gida lafiya". Inna maimuna ta fada sannan ta kara da cewa "to waye angon nawa Dan nice ta karfe ita wannan Farafarar ba wani abun azo a gani zata iya ba ni kuwa ko banza na tuka maka tuwon dawa da man shanu ko ba haka ba?" Ta tambaye shi tana kallonsu.
Duk dariya sukayi Amma shi gogan Dan murmushi yayi kadan Yana basarwa.
Abdul Hakeem ne ya nuna Mahmud Yana cewa.
"Ga angon naki nan nagama kamar kunyarki yakeji"
"A'a! Masha Allah tubarakallah Mai gidan nawa wanke hannu daka taba ne, kaga dago ka kalleni ni Kaka ce kada kaji wata kunya ta".
Kara sadda Kai yayi shifa duk jinsa yake wani iri Wai shine a zaune a dakin surukai Ashe da gaske ana jin kunyar shi wallahi da ji yake kawai fada ake ba wani nauyin da akeji Saida ya same shi yanzu yake gaskata hakan.
A kaikaice Ammah ta kalleshi "Masha Allah" ta fada a zuciyar ta, ita bataga wata makusa ba a tare dashi Kuma idan ba idon tane yake Mata gizo ba sai taga duk cikin Wanda zasu auri Zahrar a baya bataga Mai nagarat wannan yaron ba.
Albarka da nasiha dai ya Sha ta gurin Inna maimuna.
A haka suka fito daga dakin har suka fito compound din Abdul Hakeem Bai fito ba sai duba agogo Sameer keyi Yana mita.
"Nifa bana son nayi Rana a tafiyar Nan gaskiya, Naga alamar kuma neman kuke kusa nayi yamma ma".
Kafin Mahmud ya bashi amsa Abdul Hakeem din ya fito da sauri da key a hannunsa Yana fadin "kuyi hakuri key din ne ba'a gani ba da wuri ku karaso ciki kafin Zahrar ta fito ku gaisa".
Mahmud ne yace "Kai haba da an kyaketa ta huta ita da Bata da lafiyar kirki".
Karamin falo ne da kujeru masu kyau sosai da kayan kallon alama an tana deshi ne saboda Yara Mata na gidan da Kuma dai dai kun Baki.
Bayan fitar Abdul Hakeem, Sameer ya kalli Mahmud.
"Dan Allah my man yaushe idonka ya koyi kunya? Naga sai wani sadda Kai kake, nifa lamarinka ya Fara bani tsoro na rasa wace alkibla ka kalla kazo garin mutane ka Mike kafa kana wata irin rayuwa a takure nace zan dauki mataki ka aje min sharadi, da kasan bazan it's tsallakewa ba, yanzu Kuma Rana tsaka a tarko aure Kai kadai kamar marar gata sai walagigi kake alhalin kana da madafa".
Tsaki yayi " kana da matsala wallahi ko me zance fada maka bazaka Gane ba, amma idan lokaci yayi zaka fashinmta,yanzu duk bayanin da zanyi maka ba fashinmta zakayi ba, kawai mu bar maganar kawaai"
Kanshin turaren ne ya alamta musu zuwanta. sallama tayi cikin siririyar muryarta.
Sameer ne ya amsa Mata sallamar a zahiri Dan shi Dan gogan a saman lebensa ta amsa sallamar. Sameer din ne ya Dan Mike Yana fadar.
"Masha Allah jiki yayi sauki kam, "Bismillah". Yana nuna Mata kujerar gefen Mahmud. Kai ta dangirgiza Masa tana dan murmushi kasa kasa.
A Nan kan carpet ta zauna daga gefe tana gaishe da su a jimlace.
"Lafiya kalau"
Sameer ya amsa Yana fadin "ya jikin naki?"
"Alhamdulillahi" ta amsa masa.
Sai Kuma duk sukayi shiru, ganin lokaci Yana qurewa Sameer ya Mike tare da kallon Zahra Yana fadin " To madam bako zeyi halinsa Allah ya bada zaman lafiya. Amma fa sai kina hakuri da halinsa gaskiya ba kirki ya cika ba Ina son idan na dawo Naga canji na zahiri a tare dashi, sunan Sameer Sa'ad koko, zeyi miki cikakken bayanin koni waye a gurinsa Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a mai..albarka Allah yasa next year by now muna bkin suna"
Da sauri Mahmud ya kalli Sameer a zuciyarsa Yana fadin "Allah ya shiryeka Sam baka girma".

A hankali tace " Mun gode kwarai Allah ya tsare ya kiyaye hanya".
"Amin" ya amsa Yana kallon Mahmud.
"Ni zan wuce saina sake shigowa ayi kokarin ganin aikin Nan ya kammalu".
Ya fada Yana nufar kofar fita.
Sai lokacin Mahmud din yayi magana "pls ka jirani minti biyar Dan Allah".

"Idan ya wuce haka Kam...."

Ya fice ba tare daya karasa fada ba.

Tunda Sameer din ya fita take wasa da karamin zoben da yake hannunta. Bata dagon kalle shi ba shi Kuma Bai tofa tasa ba amman idonsa Yana kanta, Kare Mata kallo yake Yana fadar "Masha Allah tabarakakkahu ahasanil kaliqin".
Tsam ya taso daga inda yake ya sauko kasa inda take zaune.
"Ya jikin naki?".
Ta tsinkayi maganarsa kusa da ita daf Sam bataga lokacin daya taso ba.
Cikin daburcewa saboda kusancin nasu yayi matukar yawa ji tayi kamar ma iskar gurin ta tsaya sai munfashinsa take shaqa kawai.
A mamakance taga yasa hannunsa ya dago fuskarta suka hada Ido hudu dashi. Da sauri ta runtse idanunta zuciyarta na wata irin bugawa.
"Bude idon Kona Baki mamaki".
Marmar ta Fara da idon tana budewa a hankali Amma taki kallon nasa idon.
"Ya jikin?".
Ya Kara maiamaitawa, a hankali ta bude bakinta tace "da sauki"
Gamshin Lister mint ne ya daki fuskarsa. Banda Yana daf da ita ba yanda za'ayi yaji abinda ta fada.
"Allah ya Kara lafiya".
"Ameen"
Ta fada.
Hannunsa ya cire daga fuskarta yana Dan furzar da iska daga bikinsa ya Mike tsaye, a hankali ta sauke wani numfashi.
A bazata taji yace "bani wayarki"
Ba musu ta Mika masa, aljihu taga ya saka Yana fadin "ki shiga gida ki kwanta kiyi barci sosai kada ki yawaita hayaniya ki samu hutu sosai, zan tambayi magaji idan bakya hutawa yanda ya kamata ni Ina da inda zan kaiki ki samu isolation, tashi muje ki shiga gida ana jirana".
Saida ta shige ciki kafin ya juya ya nufi gurin da Sameer da Abdul Hakeem suke suna Hira.

Lokacin data shiga dakin ta Samu Aunty Hasana dasu sajida sunzo har da yaran duka.
Da guda ta karasa cikin suka rungume juna da Sajida Nan da Nan sai hawaye itama sajidar kukan ta fara.
Ammah ce tace "Naga abinda ya isheni meye haka zaku tasa mutane a gaba Kuna kuka, to kukan maganin me ze muku aikin Gama ai ya Riga ya Gama Saida hakuri da addu'a kawai".
Uwar dakin Ammah suka shige.
Magaji ne yayi sallama ya shigo da manyan ledoji guda biyu niqi-niqi da kaya Auntyn Hasan na tambayar"daga Ina?"
Ya fice da sauran Yana fadin "ina zuwa Aunty"
Wata ledar ya shigo da ita Yana fadar"kayan dubiya ne aka kawo Mata" ledar daya kawo daga karshen ya bude rafar 'yan dari bibiyu hura biyu ya dauko daga saman kayan, Aunty Hasana ya
Mikawa yana fadar "gashi nan inji abokin mijinta Wanda suka shigo dashi dazu".
Godiya su Inna maimuna sukayi tayi kamar Yana nan a gurin suna ta Saka albarka.

********* Bayan tafiyar Sameer can gurin aikin gidan suka wuce, ba karamin mamaki Habib yayi ba har ya kasa hakuri ya tambayi Bilyaminu lokacin Mahmud Yana ciki. "Dan Allah wane irin kudi gayen Nan ya bada haka Nan da Nan gidan ya juye ya Zama kamar daukowa akayi daga wata kasar".
"Wallahi Nima bazance ga abinda ake kashewa ba, iya kudin aiki Dana abinci kawai suke a hannuna, bakaga wash bakin fuska ba su biyu?'
"Eh nagansu"
Habib ya fada. "To ai tun jiya sukazo da komai na aikin bakaga Nata'ala ba shima lebura ya koma kaga ai da malam shi yasa a Kira saboda 'yan gyare gyaren amman da masu iyawar sukazo shima yaronsu ya koma".
Ya fada Yana dariya.
"Wallahi Bilya sai a kyaleka Kai kowama sai ka tab'a".
"Gaskiyar kenan ni wallahi burgeni ma yayi tunda baiyi zuciya ba ya tafi, ko banza nasan Yana lure da koma Dan gyaran nasa aikin".

*****A bedroom din ammah Zahra ce da Sajida suke tattaunawa akan abinda ya faru,sunyi iya nasu hasashen amma sun kasa gano bakin zare Sajida ce tace "nifa Zahra Ina hasashen wani Abu akan lamarin ki"
"Kamar me kenan?"
Dan Jim tayi kafin tace "Anya ba asiri ake yiwa duk wani Wanda yazo da niyyar aurenki ba? Ki tsaya kiyi nazarin abun Mana ko mafarkan da kike yi duk lokacin da maganar aurenki ta taso abin dubawa ne"
Dan murmushi Zahrar tayi "kin jiki kema bestie wane irin asiri Kuma,ana zaune lafiya to waye har ze bata lokacinsa da kudinsa gurin yi min wani Abu kawai daga Allah ne kinsan kowa da yanda Allah make jarabtarsa ni tawace tazo a haka".
"Eh na yarda daga Allah ne bana inkari Amma akwai sanadi, inaga gobe ma zan wuce duk da nacewa Umma sai Wednesday Amma na fasa wallahi Rimi zanje gurin Baban Umma na fada Masa ai kinsan shi farin sani Kuma zeyi duk abinda ya kamata tunda ke wani lokacin kanki ba Maths".
Kwarkwar tayi da ido Dan Allah Saji kada ki tafi ki Bari a Gama komai saiki tafin".
Wani kallo tayiwa Zahra "tafiya dole na tafi Amma zan dawo kwana kusa in Sha Allah, kinsan Zama da Baffa yasa Ina Gane wasu abubuwan tunda Yana fadw min ire -iren abubuwan da suka shafi sihiri Kinga yace min duk wani ciwon da yake da lokaci misali ace kullun sai dare mutun yake kasa barci kinsan da matsala, ko ace mace duk ranar girkinta Bata da lafiya ko duk ranar girkinta tana zubar da jini amma idan ta Gama aikin shike nan sai ya dauke babu, ko kamar taki matsalar sai an saka Miki ranar aure sai ana gaf da biki abun yake lalacewa, Kika sani ko Abban naku ma ya Fara irin wannan tunanin ne yasa ya yanke wanna hukuncin cikin sirri ki tsaya kiyi tunani Mana"
Sosai magungunan Sajida sun sakata a tunanin da Bata tabayi ba.
Sauke zazzafan numfashi tayi tana fadin "Allah ya kyauta ni duk kin sakani a tunani wallahi"
Haba "Bestie ai kinsan ruwa baya tsami a banza me ake nema a gurin mace Allah Bai Baki ba Amma sai an Yi abu kama-kama ya lalace zance da muka Dade munayj da Aunty Hasana kenan jiya Kuma ta bain go ahead na naje na faduwa Baffan rimin, tace ma zata fadawa Ammah, ma".
Kiran da Aunty Hasana tayi wa Sajida ne ya katse musu tattaunawar, ta tashi ta fita.

Washe gari duk bakin Ammah suka tafi, Inna maimuna kadai suka Bari sai Amarya taje dakinta zata koma gida.
Part din da bakin suka zauna Ammah tasa su Zilai suka gyara sosai tunda Daman nasu Zahra ne, kafin yamma gurin yayi tas kamar ba'ayi wata dabdala a cikinsa ba.
Bayan sallar insha'i zahra da Sajida suka koma part din.
Suna zaune a kan gado Autan Ammah musaddiq ya shigo dakin da sallama hannunsa rike da leda fara Mai kyau ya mikowa Zahra yana fadin "gashi Aunty inji wannan na gidan Baba Malam din yace a kawo Miki Kuma yana duba ki, Kinga Nima ya bani".
Ya Mika nata 1 k din dake hannunsa.".
"To angode madallah".
Ledar Sajida ta dauka ta bude waya ta gani sabuwa kar a ciki.
"Wow gaskiya ba karya ke! Irin wannan babbar harka haka, Dan Allah Yi min bayani naji yace wannan na gidan Baba malam din waye ko angon namu ne da ake Raina mana ya Fara tsula Mana abun arziki haka?".
Baki ta Zahra ta zunbura.
"Nace Masa Ina bukatar sabuwar waya ne da zai kawo min, ni wallahi a mayar Masa".
Ta fada tana kokarin amsar ledar faga hannun sajidar.
"Ke tsaya da Allah yi min bayani yanda zan gane, Ina taking wayar naji kina wata magana".

"Tana gurinsa tun safe ya karba ni bansan abinda zeyi da ita ba, ya dai ce na bashi kawai ni kuma na bashin shine Kuma maimakon ya bani tawa shine ya Aiko min da wannan".

Musaddiq Sajida ta kalla 'kai auta maza kaje kace tace ta gode Allah ya Kara nudi"
Sai da ya fita sannna ta juyo gurin Zahra. "Amman wallahi kin bani mamaki Allah ya tarfawa garinki nono ki nemi ki Bata rawarki da tsalle to kici gaba har ki nuna b'araka a gaban 'yan uba, Koda wasa kara ki Kara ba'a yiwa miji haka ko bakaso Abu baka nunawa a gabansa, kika san da Yaya yayi sawo Miki danya faranta Miki Rai Amma Zaki wani kwasale shi kice a mayar Masa kina son tun yanzu ki kashe Masa Gwiwa ko".
💋❤️ AUREN HUCE HAUSHI💋❤️

JINJINA TA MUSAMMAN GA MALAMAN MAKARANTA ALLAH YAYI JAGORA YA QARA BASIRA DA JURIYAR SAUKEN NAUYIN DA AKA DORA MUKU NA AMANAR YARA QANANA👫👫👫👫👍👍👍✍️
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
This page is deducted to you Families of late Alhaji Isah Musa Bakin kasuwa kazaure jigawa state.
đź”·PAGE SEVENđź”·

_______Mika tayi tana salatin ma'aiki s a.w.w sannan ta Zoro kafafunta kasa, tunda ta farka tasan tabbas karfe biyu tayi na sulsulin dare har ya zamar Mata jiki. Dubanta ta kai inda Sajida ke kwance barcinta take sadidan cikin kwanciya hankali, sai taji Ina ma ita ce haka, wasu hawayen ne suka ciko idanunta a hankali tace "Ya Rabbi ga baiwarka Mai rauna ka jibinci lamarina dan Isar Manzon Allah s a.w.w. kada ka barni da iyawata ka iya min da iyawarka kada ka Bari makiya su yi min dariya ka bani rinjaye ka dorani akan duk Wanda yake son Hawa kaina".
Ta Mike tsam ta nufi toilet din cikin dakin sai Kuma ta fito saboda shaf ta manta kafin su kwanta taga famfon ya dauke Kuma da alama ba'a kunna layinsu na tanki ba. Cikin rashin tsoro ta bude kofar ta fita zuwa bayan part din Mama don ta kunno ruwan, gurin ta dosa gadan gadan sai Kuma tayi turus, magana take jiyowa daga wurin da sauri ta koma baya dan bata San abinda zata gani ba. Tana tsuma ita fa duk da Bata da tsoro amma tana tsoron ganin abinda yafi karfin idonta ko Kuma wani mugun abun.
Dole tayi hakurin yin sallar a koma ta kwanta tana ta sake-sake har kusan Asuba, ba Kuma taji motsin wani na tada hankali ba.
Saida Sajida ta tashe ta lokacin har an Fara sallah a masallacin gidan nasu.
A gurguje tayo alwala da alama Sajida ce ta shigo da ruwan.
Bayan sunyi sallah zaman Azkar sukayi har lokacin da gari yayi shahhh alamar wayewa, sannan suka koma suka kwanta. Dukkan su ba barci suke ba, Zahra ce ta danyi tsaki kadan ta tashi zaune.
Kallonta Sajida tayi.
"Yaya Bestie akwai damuwa ne?"
Dan juyowa zahrar tayi tana kallon sajidar tana Kara wani tsakin "nifa wallahi na fada Miki tsoron mutumin nan nakeji tun ranar Dana Fara ganinsa a gidan Baba malam nake Jin wata irin shakkarsa. Dan Allah a haka zamu rayu bana ko son kallon idanunsa? Kinsan wani tarin abin haushin jiya fa hannu yasa ya dago fuskata Wai dole saina bude idona na kalle shi ko Kuma ya bani mamaki, Kuma fa ranar Nan a asibiti har wani shafar min fuska yayi Yana fadar nayi hakuri da wannan hadin shima ba so yake ba, kawai yayi biyaya ne tunda baze iya yiwa su Abba musu ba, amma ni Ina iya fada musu bana so".
Baki Sajida ta rufe tana kunshe dariyar ta. Kai ta shiga girgizawa tana fadar Babbar magana ki fadawa su Abba bakyaso! Wato ke ga marar ta ido ko? Shima har yasan kimarsu da baze iya yin musu dasu ba saike ce marar kunya Zaki Fadi Baki so, ki rabu dashi kwaai abinda nake so dake yanzu ki koyi dakewa a gaban nasa sannan ki daina tsoron idanun nasa, Wai tsaya fada min menene a cikin idon nasa da yake firgitaki duk girmanki da wayonki da wayewar ki?"
Wani shagwabe fuska tayi kamar Mai Shirin fasa kuka.
"Bazaki gabe ba, ni kaina bansan ya zanyi ba saboda shi fa na daina zuwa gidan Baba malam tunda lokacin kullum Yana tare da shi kuma sai yayi ta kallona yana tsareni da wadannan idunuwan nasa kamar Mai jin barci".
Yanzu dariya sosai Sajida keyi harda kwalla tana fadar Babbar magana tab kice abin asali ya Samo shi ai kaya ne suka tsinke Masa a gidin kaba kece dai kike bulayi"
"Kamar yaya?"
"A'a bazakiji mutuwar sarki a bakina ba ai tunda an hada anyi Mai walahar...".
Sautin kiran waya ya dakatar da shegantakar da sajidar ke mata.
Wayar da aka kawo Mata jiya ce ta dauki kida, Sajida ce ta Mika hannu ta dauka M.M DANGE ta gani Yana yawo akan screen din.
Zahra ta mikawa tana fadar oga ne da alama a Sha soyayya lfy. Tayi waje tana fadin Bari naje nayiwa Ammah shara.
Bata daga Kiran ba har Saida ya kusa katsewa kana ta daga tasa a kunnenta. Daga can taji Yana fadar "Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu".
A zuciyar ta a amsa Dan da gaske in dai zata ganshi ko taji maganarsa kasa samun nutsuwa take.
Sake maimaita sallamar yayi, da kyar ta amsa masa tare da fadar " Ina kwana?"
Shiru taji ba'a amsa ba kamar ma an sauka daga layin, amma ga mamakinta tana dubawa sai taga Yana nan, itama shirun tayi kudin sunata tafiya saita saka handsfree ta aje wayar kusa da daga gefe tana kallon ikon Allah.
Saida ya mula Dan kansa "yace ya jikin naki I hope kin shan maganinki?"
"Eh" ta fada a takaice.
"Fine"yace shima a takaicen.
Ita mamaki ma yake Bata har wani turanci yake jefawa a magana kamar gaske.
"Sai an jima ta fada tana kokarin katse Kiran.
"Kada ki kuskurs ki kashe min Kira" ya fada in serious tongue.
Shiru tayi tana mamakinsa sai wata izza yake Mata kamar wani abin azo a gani.
Muryarshi ta tsinkaya Yana fadin ki bude data na turo Miki sako idan da abinda kike bukatar ayi ko a Kara sai ki fada min, take care".
Kit ya kashe kiran.
"Kutt!" Ta fada "amman gayen nan yama Raina ni wlh Wai kada na kashe Masa waya"
Kwafa tayi "zakaga na kiraka ganin idon ka" ta Jafar da wayar tana mita.
Taso yin barci Amma ta kasa dole ta hakura, wayar ta Kara daukowa tana kare Mata kallo.
Number din Hameeda ta Fara sakawa tunda taga sabon layi ne ya dauke natan, ga mamakinta sai taga sunan Hameedar ya bayyana ba bata lokaci ta kira.
Tana ta ringing kamar baza'a dauka ba sai Kuma ta daga da sallama ai tana jin muryar Zahra ta Fara mita "yanzu Dan Allah kin kyauta tun jiya nake neman layinki Amma shiru na Kira Mama nace ta Baki tace min bakya Jin Dadi kina barci, wallahi Kinga yanda hankalina ya tashi kuwa ki Bari lokacin da Sajida ta fada min halin da ake ciki wallahi daba final muke ba Allah da barinta zanyi c/o na taho gida har fada mukayi da Salma Wai ai sai inje na baiwa Mushahun hakuri ya dawo ya aure maganganu dai gasu nan ki Bari kawai ai jibi zamu Gama in Sha Allah komai dare a gida zan kwana".
"Allah ya yarda ki Bari kawai wallahi Ina cikin yanayi akwai damuwa Dan Allah kizo ko naji sauki abubuwan".
Ta fada tana share hawaye, sukayi sallma Dan it ma Hameedar kukan take.
Wai ita Mushahu ya yiwa haka, duk wadanda suka fasa aurenta Bata taba Jin Wanda ya Bata Mata Rai ya Kuma tsaya Mata kamar wannan ba ai ko wace irin matsala ce ita ya kamata ya Fara fadawa ba ya yanke mu'amala da ita ba a lokacin da take matukar bukatarsa ya manta shakuwar dake tsakanin su da alkawarirrikan da suka yiwa juna.

Kwantawa tayi tana tunanin baya a haka wani wahalallan barci yayi gaba da ita.

**********Tun Yana tsammanin ganin ta bude data ta duba sakon har ya cire Rai da hakan.
Lambar Abdul Hakeem ya Kira sun jima suna waya kafin suyi sallama.
Laptop dinsa ya janyo yaci gaba da aiyukansa sai kusan azzahar ya Gama. toilet din cikin dakin ya shiga ya dauro alwala,a masallacin hotel din Yaya sallah lokacin daya fito Kiran Habib ya shigo Masa "Wai Dan Allah kana Ina ne tun dazu muke nemanka kazo masu aikin hada furniture's din Nan ne suka Gama da cabinet din kitchen".
"Ok gani Nan inaga kada kayi nisa zuwa an jima su Aunty zasuzo suga gurin"
Ya fada.
Yana nufar gurin da ya saba aje lifan din Habib.
Wayar Ammah Abdul Hakeem ya Kira ya fada Mata Mahmud yace a turo a gano gidan an Gama gyaran, dakin Mama Ammah ta shiga ta fada Mata sannan Kira Aunty Hasana ta fada Mata kafin ta wuce gurin Alhajin ta fada Masa tunda shiya dawo daga gidan gonar sai su Abdul Hakeem ya baro suna yiwa shanu Allura da Basu magunguna.
Wurin karfe biyar Aunty Hasana ta debesu a mota harda Sajida suka nufi Hayin bankin cikin jagorancin Habib, lokacin Inna Bata Nan taje MIYA gurin wata aminiyar ta da sukayi aikin Haji shekara daya.

Duk cikinsu ba wadda Bata kadu da ganin gidan ba domin ba karaya an narka mahaukatan kudi a gidan bazaka tab'a cewa renovation akayi Masa ba, bedroom's ne guda uku biyu suna kallon juna dayan Kuma daga gefe da alama yafi sauran girma Kuma shi kadai ne a rufe, sun zagaya ko Ina sai santin gidan Sajida tace tana ta daukar video, falon kadai abin kallo ne duk da ba komai a cikinsa sai fitilu da aka kunna sai Kuma AC da aka ware.
Hajiya mama ce ta kasa hakuri ta leka ta Kira Habib Nan falon ya shigo Yana fadin "gani Mama"
Yana Dan rankwafawa.
Aunty Hasana mama ta kalla "Hasana Dan Allah ki tayani tambayar yaron Nan tunda shi namu ne na gida baze cucemu ba, Wai wannan yaron sana'ar me yake daya iya Kama hayar wannan uban gidan"?"
Kara risinawa yayi Yana fadar "ba haya ya Kama ba Baba malam ne ya bashi kyauta, sai Kuma kungiyar yake yiwa aiki suka kawo masu aiki suka yiwa gidan 'yan gyare -gyare harda kayan daki ma suka zuba masa, Bismillah Bari na bude muku ku gani yanzu ba dadewa zuka Gama hadawa da kitchen din suka tafi".
Dakin ya bude musu ba Hajiya mama da take ta kwana biyu ba, ko Aunty Hasana da Sajida Saida suka Zama 'yan kauye Dan tunda suke Basu taba ganin irin wanna gadon a zahiri ba, ita kanta aunty Hasana lamarin Yana neman ya gagari tunaninta fa ance Almajirin Baba malam to Amma idan aka saka mizanin hankali abin yafi karfin yanda aka fada to wane irin NGO's ne da suke irin wannan aikin akan daidaikun ma'aikatan su haka?" Gaskiya abin akwai abin dubawa.
Lokacin da suka fito harabar gidan ne wata Hilux ta shigo da kaya a bayan motar mutane uku ne a motar bakar fata biyu fari daya Kamar balarabe Kamar kwara.
Kameme Hajiya mama ta hanasu tafiya sai da aka sauke kayan ta gani abinda da suka Gane irin katuwar plasima din Nan Mai cin Rabin bangon Nan ne kawai amman sauran tarkacen Basu Gane komai ba, haka suka kada suka tafi mama nata mitar "A'a da sake Alhaji ya titsiya yaron Nan saiya nuna Iyayen shi kafin a Kai Masa yarinyar Nan haka kawai aje ayi kitso da kwarkawata mutanen yanzu ba abin yarda bane sai kaga mutum har mutum Amman a Baki malam a ciki Kuma Fir'auna".
Maganar data Basu Aunty dariya kenan.

💋❤️
💋❤️
💋❤️
AUREN HUCE HAUSHI

💋❤️
💋❤️
💋❤️

STORY
AND
. WRITTEN
BY
MAMAN FATIMAH

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.