Trending Hausa Novels

Auren Huce Haushi Book 1 Complete Hausa Novels By Maman Fatima

Reading file: AUREN HUCE HAUSHI BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN FATIMA.txt

Chapter 31 of 34

Page 41.

📖🖋️

________Wani irin barci me nauyi yayi awon gaba da zahra, sai da Sameer ya shigo yace Rukayya ta duba Masa Zahra oga ya Kira yace Masa da matsala.
Dakin Rukayya ta shiga ganin Zahrar tana barci ga wayar Ya Sameer a gefen ta, daukar wayar tayi tana dubawa a airplane mode taga wayar 'yar dariya tayi tana fadin "good yarinya kinsan kanki kenan ai Ina bayanki ki tsaya tsayin daka akan wannan mijin naki idanun Mata a kansa suke kinyi dai-dai wallahi".
Wayar ta cire daga flight mode din tayi waje da sauri tana fadin "gashi ya Sameer wallahi barci takeyi" .
Wayar ya Karba Yana dubawa gashi Nan a kunne take haka datar itama ba wani matsala.
Tsaki yayi kadan Yana fadin "duk nema suke su dagulamin lissafi wallahi har na rasa Yanda zanyi" .
Rukayya najinsa tayi Shiru haushinsa takeji tun buyagin da ya yi Mata dazu,waje ya juya ya fita Yana kokarin Kiran waya.
Hajiyar makwarari ce ta fito daga daki da manyan tabarmin roba a hannu tana fadin "zo Nan Rakiya ki shimfida su cikin baranda kafin mutane su Fara taruwa".
Zuburo Baki tayi "Allah ki daina fada min sunan nan ni sunana Rukayya haka a ringa batawa mutum suna".
Ta taso tana karbar tabarmin.
"Gidanku, nace Rakiya ba sunan ki bane, Kizo ki shiga kurmin ki karbo min masoro gurin Alhajin Baba nayi na hadawa yarinyar Nan magani na Bata tun yau ta Fara amfani dashi ba'a bori da sanyin jiki".
Saida ta Gama shimfidar ta shiga gurin Hajiyar cikin falonta suna duba kayan da za'a bawa masu kawo kefen robar da aka zuba chicken pepper ta bude tana fadin "bari na dauki Daya naji kamshin yayi min Dadi".
"Ki rufe wannan gashi can a kitchen a waje ki diba harda snacks din duka, Amma ki Fara karbo Mata sakon a kasuwar tukunna kuje da sadiya ta rakaki ku shiga a dai daita tunda ba nisa ga cunkoson cikin kasuwa Kuma kinsan Sameer baze Baki motarsa ba, wadda mukazo da ita Kuma Aliyu yayi nasa gurin da ita".
Basu dauki minti talatin ba suka dawo da sakon har lokacin Zahra barci take sai da jama'a sun Fara taruwa a gidan duk dangi need sai dai-daikun Yan uwan mahaifar mujahidar.
A blender hajiyar taba mommy ta nika Mata masoron ta juyo mata shi a cikin robar da Hajiyar ta bada a zuba a ciki.
Lokacin da mommy ta kawo Mata Hajiyar da kanta ta nufi dakin mujahidar tana fadin "Ina matar Mahmudun take?.
Barcinta take sadidan Dan tabata Hajiyar tayi tana fadin. "Tashi 'yar nan ga maganin lalurar ki da izinin Allah".
Tashi zahrar tayi tana bin Hajiyar da kallo lokacin data aje robar kusa da ita.
"Bude ki gani sai nayi Miki bayanin yanda za'ayi dashi".
Batayi musu ba ta bude robar taga garin masoron.
"Kina jina? Abinda za'ayi dashi ki ringa diba Kashi Daya bisa hudu na karamin cokalin shayi kina zubawa a ruwab zafi tafasashshe cikin kofin ok ki barshi yayi minti ashirin a ciki sai ki tace ki Shanye ruwan,haka Zaki ringa yi har ya Kare in Sha Allah ze narke yabi jinin al'adarki ya fice, ki rabu da wannan shirmen komai ace za'a yanka mutum kamar kabewa"
'yar dariya Zahra tayi tana fadin in Sha Allah zanyi na gode madallah Allah ya saka da Alkhairi".
"Allahumma Amin. Allah ya Baki lafiya,ayi ta hakuri irin mijinki Mata Ido rufe suke nemansu sai kin kauda Kai zakiçi ribar zaman aurenki. Amma kada ki kuskura ki yarda a nuna Miki San iyawa akan mijinki, ki kula da sukarki Bata da damuwa ko kalilan ki girmama Masa danginsa da kakarsa jiya ya wannan suna gidan Nan sunzo ganin Mai sunan mijinki na wurin Sameeru, Ni cewa nake can wurinku zasu sauka ma sai naji Sameeru na maganar su fito zasu koma a jiyan kinsan sha'anin tafiyar iska, ba wani nisa ke gareta ba".
Ita dai Zahra Jin Hajiyar take Dan ba komai ta fashimta ba.
Rukayya ce ta shigo da Abinci dasu snacks a babban tray tana fadin " Ai tunda naji shiru Hajiya Baki fito ba nasan kin hanata barci kawai wallahi ke idan Kika so Abu ba sauki saina Allah idan kinyi hakuri zata tashi ki bata".
"Ke tafi can waya fada Miki ana bori da sanyin jiki Baki San hadarin wannan abun bane baya barin haihuwa fa ba dole a tari abun ba tunda wuri, wannan yarinya tubarakallah haka ai ba'aso a samu abinda ze kawo Mata cikas a zaman aurenta ba, ni tunda na ganta ta kwanta min har maganin tsarin jiki Zan karbo mata a Sanka, nan babban gida".
Baki Rukayya ta rike tana kakabin Abun "Ikon Allah to ke Hajiya fada Miki tayi tana son na tsarin jikin? Da kike faman fadin Zaki karbo Mata".
Kafin Hajiyar ta Kara magana Zahra ta rigata.
"Haba Aunty Rukayya Ina laifin Hajiya kuwa tunda na sako Qafa gidan Nan Bata huta ba hidimata takeyi".
"Eh haka ne kam tunda har kasuwar kurmi ta aikeni, da girnana da komai nace bazanj ba tace nayi mata kiwa dan rabon da naje cikin kurmi tun Ina secondary Dan ma ban manta shogon ba"
Ficewa Hajiyar tana fadin kyaji dashi idan Kaya ne".
Tashi zahrar tayi tana fadin Bari na dawo, ta fice daga dakin.
Toilet ta shiga ta Kara gyara Kanta, lokacin data fito dai dai lokacin masu kawo lefen suka karaso suma Nan da nan gudan ya dauki jama'a Dan makota ma Wanda suka makara suka ringa shigowa.
Ganin gidan ya kacame da jama'a yasa Zahra tayi amfani da wannan damar ta nufi hanyar soron gidan, a soron ta tsaya ta Ciro wani face mask da yake cikin jakar ta da eyeglasses dinta ta saka ta fice daga gidan.
Ba Bata lokaci tana fita Dan sahu Yana kawo Kai, ta dafe shi ta shige, tana fadin "Janbulo zaka Kaini".
"Hajiya sai dai drop gaskiya Dan hanyar ta baude ni rimi na nufa".
"Muje Zan baka kudin drop din".
Ta fada tana Dan leken gefenta kamar narar gaskiya, hankalinta be kwanta ba sai da taga sunyi nisa da unguwar, ajiyar zuciya ta sauke tana "na barka da Dr Sai ku cinye kanku haka kawai za'a sabautani saboda Kai,Wanda har yanzu bansan daga wace bahiyar ka bullo ba, ayi min sakiyar da Babu ruwa a cuceni a cuci rayuwata shi yasa na taho da hirina idan tayi ruwa rijiya idan batayi ba ta Zama Masai"
Kafin su karasa layin su Ssjida tacewa Mai adaidaita din ya taya gurin me P. O.S zata ciri kudi.
Har kiofar gate din gidan ya kaita 10k ta bashi, cikin mamaki ya dubeta "Hajiya kudin sunyi over dari bakwai ne kudin, Hala ke bakuwa ce?"
Gaga tayi Tana fadin na sani kaje kawai nagode Allah ya tsare".
"Na gode Allah ya rufa asiri ya kara Miki daukaka".
Tana tafiya tana fadin. "Allahumma Amin".
Ta shige gidan shi Kuma ya juya Kan mashin dinsa ya wuce Yana Fadin "Bari na koma na sallami gidan sai na Kara fitowa".

***********

Bayan tafiyar masu kawo lefen an baje anata kallon kayan arzikin da suka kawo Masha Allah kayansu sunyi kyau sosai Dan akwatuna set hudu suka kawo da manyan jakunkuna uku har da adudu biyu.
Saida komai ya lafa sannan hankalin Rukayya ya dawo jikinta ta shiga neman zahra, abin mamaki ba zahra ba alamarta Abu kamar Wasa ya Zama gaske Nan da Nan tashin hankali ya wanzu a gidan Dan mantawa akayi da murnar wani lefe Nan da Nan Rukayya ta Fara share hawaye.
Mommy ce ta Farayi Mata fada "Haba Rukayya menene haka Zahra Karamar yarinya ce ku shiga makota Mana ko taron jama'a ne bataso ta shiga can ta zauna ba kince toilet tace Miki zata shiga ba? Kafin ta fito Kuma bakin sun shigo?"
"Eh haka ne Amma Naga fitowarta harta tsaya a can daga Nan mutane sukayi yawa ban sake ganinta ba".
"Ke Zubaida maza ku shiga gidajen kusa ku duba ko can ta shiga ku kirawota".
"To mommy". Ta fada sukayi waje su uku.
Hajiyar makwarari kuwa cewa take "Ina yarinyar nan ta shiga ko masu kawo kayan tabi suka tafi".
Wani kallo Rukayya tayi Mata "kaji Hajiya da wani zance kamar wata 'yar baby ce zahrar da zatabi wasu mutane".
"Ungo Nan".
Abu kamar Wasa karamar magana tana neman Zama babba, duk kukkuken babu it's Babu dalilinta komai Kama da Zahra Babu.
Mommy da Kanta ta Kira Sameer tace duk inda yake yazo yanzu tana son ganinsa.
Daman ba nusa yayi ba Yana tare da abokansa na unguwar Dan a hannun Hajiyar ya girma harya Gama secondary school dinsa.
A tsakar gida ya samu su mommy anyi cirko-cirko.
"Gani mommy lafiya na ganku haka?".
Hajiya ce ta Fara fadar "Ina fa lafiya ba'aga matar Mahmudu ba har makota anbi baku ko alamarta".
Mommy ya kalla. "Kamar ya ba'a ganta ba? To Ina ta shiga?"
"Allahu A'alam, da farko abin ban dauke shi haka ba sai yanzu da naga da gaske ne yasa nace Bari na Kira ka".
"Ok, Bari naje Nan Ina zuwa"
Ya juya ya fice da sauri, cikin tashin hankali me ze fadawa Mijinta Ina ta tafi?.
Tambayar mutanen kusa masu sana'a a kofar gidan ya rinka yi, har ya juya sai wani Mai sayar da Mai yace yaga fitowarta da face mask da glass a Ido ta hau a dai- daita sahu sunyi hanyar nan ya nuna hanyar gidan shatema.
Dafe Kai yayi cikin tashin hankali, "wannan wace irin masifa ce haka kawai an tadawa yarinya hankali har ta yanke Shawarar tayi tafiyar ta, to tana Ina? Ina ta tafi? Ba wani ta sani a garin Nan ba ga Babu waya a hannunta, Saida ya fada masa ya fito Mata a mutum sak a wuce wannan wasan yaran ya kaita inda ya Dace a duba Masa ita amma ya gano ya yiwa Haseena waya ta a duba Masa ita yasan karshen film din ba Mai kyau bane"
Jiki ba kwari ya koma ciki..

***** ***** *****

Hankalin Zahra be kwanta ba so sai Saida ta ganta a cikin falon gidan su Sajida, Mai aikinsu ta bude Mata parlourn tana fadin "A'a marhabin maraba da Amarya sannu da zuwa".
Ta fada tana murmushi, tare suka shigo ciki.
"Yauwa Mama Hauwa sannu da gida, ya naji gidan naku Shiru ko su Mamar basa nan ne?"
"Wallahi sunje Rimin sumaila duba kanin Baffa bashi da lafiya,a nan ya kwanta a Asibitin Murtala to shine sukaje su Kara duba shi da jikin".
"Allah sarki ko kawu Musa?"
"Shine Ashe kin sanshi".
Eh nasan shi Mana, har a gidansa mun kwana lokacin da mukaje da sajida. Allah ya bashi lafiya yasa kaffara ne"..
"Allahumma Amin, Bari na bude Miki dakin mutuniyar ki shiga na kawo Miki abinci can, inaga sai dare zasu dawo tunda suka Kai har wannan lokacin".
Wanka ta shiga ta Dade a toilet din kafin ta fito tana tsane jikinta da towel, lotion ta shafa ta dauko Rigar material marar nauyi ta saka a cikin kayan sajida.
Jallop din kuskus aka kawo Mata wadda Tasha kayan lambu da pepper soup na kayan ciki da kunun aya Mai sanyi da ruwa.
Abincin taci ta koshi ta dora da kayan sanyi tayi hamdala ga Allah ta kishingida jinta take fresh idan Allah ya kaimu safiya ta karawa motarta Mai, ganinta a araha yasa ake garata kamar kwallo.AUREN HUCE HAUSHI.

MAMAN FATEEMAH

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.