Auren Huce Haushi Book 1 Complete Hausa Novels By Maman Fatima
Reading file: AUREN HUCE HAUSHI BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN FATIMA.txt
Chapter 7 of 34
PAGE NINEđź”·(9)
____Akwatuna ne na garari masu tsadedden kyau har set biyu aka shigo dasu, sai wasu irin manyan jakunkuna guda uku, guda Zilai ta dinga gud tana fadin "wani kaya sai amale wane jaki. Allah ya Kara daukaki Fatima ya Dora ki akan makiyanki lallai girma sai dan girma kaga wadda ta gaji arziki gaba da baya"
Inna maimuna ce ta jimko kudi ta dankawa zilai tana fadin "na fanshi jikata tunda kin koma roko".
Dariya tayi tana fadin "wallahi Inna Dana iya kirarin da yafi wannan da nayi Mata. Uwar dakina murucin kan dutse ce Bata fito ba Saida ta shirya, yakuwar akan kabarice bakin cikin 'yan taushe, bikin cikinka sauro yau ga xanzaro a bene" .
Ta Kara kwarara wata gudar.
Da sauri Mama ma tazo ta dankawa zilai kudi tana fadin yau ai ranar farin ciki ce maza bude Mana muga karamar Arziki"
Tunda aka Fara shigo da kayan Zahra tayi dakinsu tabar su Sajidar anan.Hameeda da zilai ne suke fama bude kayan suna santinsu komai na ciki Mai kyau ne ba karya duk wadda ta hado kayan 'yar gayu ce ta gani kasheni komai na ciki classic ne.
Saida suka bude kowa ne akwatin duka Sha biyun.
Ba abinda Inna maimuna ke maimatawa sai Masha Allah,Allah ya kade fitina yasa gurin zamane Allah ya hada arzikinsau.
Duk bidirin da ake Salma na tsaye Bata taba ko tsinke a ciki ba sai cika take tana batsewa Kamar anyi Mata dole sai ta zaune a gurin.
Su Sajida da Mujiba da Hameeda ne suka shigar da kayan falon Ammah.
Sai da suka jerasu sannan Hameeda ta nufi dakin Mama su Kuma su Mujiba suka nufi gurin Zahra.
Wata uwar harara Salma da dokawa Hameeda tafin tayi dogon tsaki tana fadin "Allah wadaran naka ya lalace yanzu ke ko kishin Kai Baki dashi Kika bige gurin jidar kayan kanwar bayanki kina wani washe Baki ke game kirki". Baki Hameedar ta murguda Mata tayi gaba tana cewa "Ina ruwanki Aunty Salma danke bakya ra'ayinta dole Nima sai nabi naki ra'ayi kowa yayi ta kansa kawai ni bana ara na yafa abinda Babu ruwana ba.
Mama ce ta fito daga bed room dinta fuskarta a hade da waya a hannunta kallon Hameedar tayi "to rasa kunya b'eran tanka Dan ta fada Miki gaskiya Zaki kare Mata tana din rashin mutunci cewa nake koni Dana tsuguna na haifeki ban Isa kizo inda nake ba Saida Kika dangana da gurin kanwar uwarki".
Baki Hameedar ta zumbura tayi gaba tana magana kasa -kasa.
"Ai Daman za'a rina tunda Naga kin biyo Mama daki, wallahi mutum ya kiyayi gulma da munafurci in dai yansla son yaga ci gaba a rayuwarsa"
Tana Gama fada ta shige uwar daki.
A waya Ammqh ta Kira Aunty Hasana ta fada Mata an kawo lefen Zahra.
Lokacin da tazo taga kayan ta kadu da gasken gaske, Amma dai Bata furta komai ba kada Ammah taga Kamar Bata son auren ne ko wani Abu.
Sai bayan sallar magariba Mujiba tayiwa su Ammah sallama Sajida ta rakata ita Haidar din Aunty Hasana.
Tun Zahra na tsammanin ganin Hameeda har ta hakura saboda dare ya fara so sai Dan Sajida har tayi barci, sai tayi Kamar ta kirata a waya saita fasa, da taga zaman yayi yawa sai ta dauko alqur'ani ta Fara karatu har Saida daya ta gota sannan tayi addu'a ta shafa.
Kwantawa tayi rigingine tana tariyo rayuwartan ta baya komai ya ringa dawo Mata Kamar lokacin yake faruwa
************_
_
TUSHEN LABARIN
AZARE KATAGUM L.G.A
BAUCHI STATE
UNGUWAR FAMFON SHANU.
Yarinya ce 'yar kimanin sheKara goma Sha biyu haka, kyakykyawar gaske fara irin farin Nan Mai hade da Kamar golden yellow , idanunta dara-dara farare tas sai gashin kanta bakirkirin har gadon bayanta hancinta irin dogon Nan ne har baka bakinta Dan karami Mai dauke da 'yan jaja-jaja pink-pink din lebe, bazaka kirata doguwa sosai ba irin tsaka tsakiyar nan, jikin lublub Kamar Mai rayuwa a kasanshen sanyi komai nata Mai kyau ne Wanda idan ka kalleta saika Kara kallonta Dan Allah s.w.a yayi Mata sura Mai kyau na a gani a Kara kalla. Da sallama ta shigo cikin gida tana fadar "wash Allah Ammah wallahi na gaji wadannan littatafan sunyi nauyi da yawa inaga sai dai na kwafo time table kullum na ringa zuwa da Wanda zamuyi amfani dasu kawai". Ta fada tana kokarin Ciro jikar daga bayanta, dariya Ammah tayi tana fadin "ke dai anyi raguwa wallahi zahra ke Sam bakya da juriya jakar da Zaki Goya zuwa mota ma neman gagararki tajeyi".
Kwantawa tayi saman kujera tana fadin "Allah da nauyi dauki fa kiji".
Sulaiman ne ya shigo shima da tasa jakar a kafada Yana dariya.
"Kai Kuma dariyar me kake?"
Ammah ta tambaye shi.
Zahra ya nuna Yana cigaba da dariya. Baki ta zumbura tana dira kafa tana fadar "Allaha Ammah ki rabani da Ya sulaiman Kinga tundazu yake min dariya Kuma nace ya tayani daukar jikar ya Kiya".
"Wai Kai meye haka kazo kana ta dariya Kamar wani sabon kamu".
Jakarsa ya jefa kusa data Zahra kafin ya zauna Yana ba Ammah labari.
"Wato Ammah muna hanyar dawowa ne man motar ya Kare tunanin Malam Bala harya kawo mu gida man Bai Kare ba saboda yace ya biya gidan man yaga da layi idan yace zebi layin zamu Dade muna jiransa shine kawai ya taho, to muna zuwa wurin gidan sarki kawai man motar Nan ya Kare shine fa muka tako a kafa, ita Kuma gwanar iya son jiki ta wani shagwabe mini Wai na daukar Mata jaka na hada da tawa Kamar wani jaki, shine Dan tsabar rainin hankali Wai to na dauka zata karbi kudin gurin Abba ta biyani Kamar wani Dan dako".
Tsaki Ammah tayi tana hararar Sulaiman din "wannan shine abin dariyar Kuma wallahi kayi girman kwabo da meye amfanin hada babba da yaron ba saboda taimakon ba".
"A'a Ammah duka da wata biyar fa na girme mata, to Ina wani girma sa'anni muke ba gashi ajinmu daya ba da dai su Ya Sadiq ne su Aunty Janah, kuma fa duk su Hameeda kowa fa ya dauko tasa sai itace tafi kowa son jika za'a daukar Mata wa zata yiwa karatun ba kanta ba".
Ya fada Yana cire safarsa.
Fita Ammah tayi, ita Kuma Zahra ta shige bedroom din Ammah ba Wanda ya Kara bi takan sulaiman.wanka ta shiga tayi kafin taci abinci saboda Bata son ta makara a islamiyya Sam Bata son abinda ze taba lafiyar jikinta tunda a makarantar bokon suke sallar Azahar.
Lokacin data fito tana sanye da uniform din islamiyya da Jakarta tana kokarin shiga dakin Mama ta biya Hameeda ne taga Hameedar da wani Kaya a wata leda babba ta fito tana zumburar Baki.
"Ya Naga Baki shirya ba ko bazaki makarantar ba? Kinga fa yau zamu bada hadda".
Mama ce ta fito daga dakin tana hararar Zahra "to uwar kinibibi bazatan ba ki Kama hanya ki wuce, ko zata ai bazaku tafi tare ba ana gqninki waye ze kalleta na nuna Miki bana son kina shige Mata amman kin kasa ganewa, Haba yarinya sai kwawa"
Duk wanna maganar da Mama takeyi a hankali take fada Banda Zahrar da Hameedar ba Mai jin abinda take fada duk da Ammah na kofar kitchen dinsu Wanda yake kusa da bangaren na Mama.
Daki Mama ta nunawa Hameeda ta koma yayin da Zahra ta nufi Ammah tana fadin "Ammah na tafi"
"To Allah ya bada sa'a a maida hankali ki biyawa Mujiba ki tafi".
"To" ta amsa ta nufi waje da sauri.
Saida dama Ammah tana ankare da Mama Sam Bata son Zahra na mu'amala da Hameeda kwata-kwata sai Kuma Allah ya hada wata irin kauna tsakanin yaran salma ce Sam basa jituwa da Zahra da ita wata sakarai ce da zahra ko ruwa Mai dadi Salma bazata Bari Tasha a gidan ba, motsi ba motsi ba sai ta Fara fadin ai dai Nan ba gidanki bane ke 'yar riko ce.
Lokacin da Ammah taji maganar a bakin yarinyar tayi mamaki sosai Dan a lokacin wayonta Bai Kai ta iya banbance tsakanin Dan gida na ruko.
Da Ammah ta tsareta ta fada Mata wayace Zahra ba 'yar gidan bace sai tace " Mama ce ta fada tace min na duba Mana Naga ko kalar jiki mu ba iri daya bace mu daina tafiya ma da ita, Wai ta fimu kyau idan muna binta idan muka girma baza'a sure mu ba".
Kan Salma Ammah ta dafa tana fadin "itama 'yar uwarku ce kuyi zumunci da ita kinji" kai ta gyada alamar to.
Abin ya jima Yana baiwa Ammah mamaki Bata zaci haka a gurin mamar ba, tunda a zahiri ba komai a tsakaninsu sai mutunta juna duk da tasan sha'anin kishi ta ciki na ciki ne ta baka na baka.
Sai kusan magariba su zahra suka shigo hannunsu na sarkafe da juna ita da Hameedar, daga gurin Aiken ta wuce makarantar Amma Tasha bulalar makara.
Bayan sun Gama cin abincin dare ne suna hira a dakin Ammah Hameeda ta shigo ta gaishe da Ammah ta zauna sukaci gaba da hira lokacin Ammar tana dakin Abbansu ta Kai Masa abinci.
Lokacin data shigo dakin ya kacame sunata musu akan wani aiki da akayi musu yau a makaranta su matan suna ga yanda za'ayi shi Kuma Sulaiman Yana fadar ga yanda za'ayi, Ammar ce ta zauna tana fadin su kawo ta gani maths ne, Kuma duk hanyar da akabi za'a kaiga samun amsar Dan haka tace kowa yayi nasa yanda ya fashimta.
Har ta shiga bedroom dinta ta fito tana fadin "Na manta Abbanku yace na fada muku ranar Saturday zakiyi jarabawar share fagen shiga karamar secondary school ta kwamnatin tarayya, yace kuyi karatu duk Wanda baici ba baze saimasa ba Saida yaci gaba a makarantar da yake".
Murna suka farayi da gudu Hameeda ta nufi dakinsu Dan ta fadawa Mama.
******Alhaji Jafar Mai yadi haifaffan garin Azare ne ta jihar Bauch a unguwar fanfon shanu, su hudu ne iyayensu suka Haifa uku maza sai autarsu daya mace amman su biyu suka rayu biyu tun suna Yara suka rasu, sun taso shi da kanwarsa Amina a hannun Babarsu Hajiya Fatima wadda ake kiranta da Nanna, kasancewar Babansu Malam Ibrahim Wanda ake Masa laqabi khalilu Allah yayi masa rasuwa tun Yana aji day na babbar sakandire Amina Kuma tana aji shida na primary.
Sun Sha wahala kasancewar mahaifan su ba Mai karfi bane Bai bar musu wani Abu Mai yawa ba daga gidan da suke cikin sai konaki biyu, tunda Jafar ya Gama babbar sakandire yake zaune a gida saidai dinkin hula da aikin hannu na riguna kusan dashi yake rike Nanna da Amina said Kuma 'yan kulle-kullen kayan Miya daaya kafawa Nanna jarinsu.
A hankali Jafar yana Tara kudinsa lokacin daya da yaga kudin sun danyi auki ya nemi Shawarar Nanna akan yana son ya Fara sayar da Yadiddika na maza, tayi murna sosai ta dinga saka Masa albarka.
Cikin ikon Allah ya Fara kasuwar da kafar dama Nan da Nan abun ya Fara bunkasa da taimakon wani uban gida da Allah ya hada jininsu yake bashi Kaya akan farashi Mai sauki har takai ga Fara tura shi aba Yana sawo Masa Kaya a hankali ya bashi aron kudi masu Dan yawa yace shima ya hada da nasa jarin ya sawo nasa kayan zeyi Masa kokarin shago kafin ya dawo.
Nan da Nan al'amura suka kankama ba'a rufe shekara ba arzikinsau ya Fara habaka da taimakon Ubangidansa ya samu Yara masu amana ya zuba a shagon shi Kuma ya shiga cuku- cukun nema admission Nan University ta Bauchi cikin ikon Allah ya samu course din da ya nema Agricultural science.
Cikin ikon Allah karatu ya kankama, yayin da a gefe ga kasuwanci Yana ta habaka. Lokacin Yana shiga level 300 lokaci Amina ta kammala secondary dinta manema sukayi Mata chaaaa, Amma an kada an raya ta fitar da gwani ta Kiya Wai duk Bata sonsu.
Haha aka tattara aka kyaleta Jafar yaso ya nemar Mata gurbin karatun N.C.E Amma Nanna tayi tsalle ta dire ba za'a wannan aiki da ita ba, haka suka zauna har kusan shekara Amina ita ba karatun ba ba auren ba.
Wata ranar juma'a lokacin su Jafar sunzo hutun karshen first semester na level 400, Nanna ta aiki Amina kasuwa gurin Jafar ta karbo Mata wasu kudi uzurinsu ya taso Mata na gaggawa.
Lokacin da taje baya shogon nasa Yana shagon Ubangidansa Alhaji Dauda, can ta nufa tunda tasan shagon nasa.
Suna ciki Hira da bakon Alhaji Dauda kawai ya hango Amina ta nufo shagon tana gaishe da Alhajin daya fita a lokacin, kafin ta karaso har taso ya nufo ta Yana fadin"lafiya Amina? Daga Ina kike?"
Dariya tayi kyawawan hakoranta jerarru farare tas suka bayyana tana fadin "kai Yaya ba komai fa Nanna ce ta Aiko ni".
Fita sukayi ta fada Masa sakon sukaje shago ya Bata ai Bari ta hau abin Hawa ba ya dauketa a mashin dinsa suka tafi gida.
Da dare Yana zaune a inda suke Hira yaga motar Alhaji Dauda ta tsaya a kofar gidansu da sauri ya tashi ya nufi inda yayi parking sai yaga harda bakon Alhajin Zakariyya suke tare, sun gaisa sosai kafin Alhaji Daudan ya fada Masa Amininsa Kuma Dan uwansa ne yaga Amina Yana so shine nace yazo muji da zafi -zafi akan bugi karfe.
Jafar yaji Dadi sosai zaifi kowa murna idan hakan ta kasance Dan ya yaba sosai da hankalinsa sosai.
Cikin gidan Jafar ya shiga ba jimawa ya fito Yana musu iso ciki sun gaisa da Nanna Alhaji Dauda ne yayiwa Nanna bayanin koma itama irin amsar Jafar ta fada idan tana so ba matsala ba inda aure baya Kai mace Nasarawa batayi nisa ba.
Cikin ikon Allah kuwa Amina taji Alhaji Zakariyya ya kwanta mata a rai Kuma zata iya aurensa duk da fada Mata Yana da Mata harda Yara biyu.
A cikin wata biyu akayi bikin Amina da Alhaji zakariyyan, Jafar yayi Mata komai da uba yake aka kaita can Nasarawa state cikin garin Akwanga.
Wannan kenan.
Haka Jafar yaci gaba da karatunsa har ya Gama ya dawo gida Yana jiran shiga camp.
Lokacin da saki post na tafiya service sunan Jafar ya Fado a cikin masu zuwa Jos yayi murna sosai ko banza Yana jiyo kamshin gida tunda suna makotan jahohi.
Bayan gama zaman camp wata makarantar 'yan Mata jeka ka dawo aka Kai Jafar, Baiyi wata biyu ba Allah ya hada shi da wata yarinya Rabi'a yaji yarinyar ta kwanta Masa tana Kuma da irin Qualities din da yake fatan Samu a gurin matarsa.
Zuwa lokacin gama service dinsu har magana tayi karfi inda iyaye suka shiga.
Wani gida Jafar ya saya kusa da gidansu ya gyara' ba'a dauki lokaci ba akayi bikinsa da Rabi'a suka tare a gidansu. Duk wata kulawarsa da soyayya ya tattara ya baiwa Rabi'a ba abinda ta nema ta rasa sai abinda baza'a rasa ba. Rabi'a irin matan Nan ne masu kissa kafin wani lokaci ta kanainaye zuciyar Nanna.
Kwanci tashi ba wahala a gurin Allah aurensu ya shekara Amma kalubaken da suka Fara fuskanta na Rashn zaman ciki a jikin Rabi'a kusan barinta uku. Ana haka Jafar ya samu aiki da ma'aikatar gona ta jihar Bauchi BARDA.
Cikin kankanin lokaci kofofin wadata suka budewa Jafar kafin shekara biyu ya gina gida Mai kyau sunje makka shida Nanna.
Nan da Nan likafa tayi gaba Amma dai matsalar su na Nan ta rashin haihuwa.
Yayin da abin ma ya Fara damun Nanna har ta gaji tayi Masa magana akan ko maganin hausa za'a fata nemawa Rabi'a ne.
Amma sai ya nuna Mata ayi hakuri tunda tana ganin consultant na Gynicology a gani idan ba wani cigaba sai ayi na hausan.
A Kuma ciki shekarar ne Alhaji Jafar ya koma Abuja da aiki inda arzikinsa ya Kara bunkasa gashi Allah yayi shi Mai sakakken hannu bashi da rowa ko kadan, in dai Yana gari to kofar gidansa Cike take da jama'a, sai Suma mutane suna tausaya Masa akan rashin haihuwa ga dukiyar dai Kama hankadota ake Amma ba magaji.
Ana haka Allah ya kawo ibtila'in ambaliyar ruwa a Adamawa state yankin MUBI.
Lokacin da gwamnati tarayya zata tura masu zuwa jaje sai sunan Alhaji Jafar ya shigo cikin tawagar vice president.
Sun jajje guraren da b'arnar ta afku anyi rubuce rubuce sosai da Alkawarin ka na gwamnatin tarayya sanan an bada kayan agaji ga wadanda iftila'in ya shafa a hanyarsu ta komawa ne Alhaji Jafar suna tattaunawa da Ardon filanin Yana Karayi Masa bayanin abinda ya faru.
Suka jiyo maganar mace daga bayansu lokacin ayarin sun danyi nisa dasu, da sauri Ardon ya juya Yama fadin "ho! 'yar nema Saida Kika biyoni Nan ko ma'u?"
Dariya tayi tana kare fuskarta da wani littafin Mai Dan fadi dake hannunta cikin shiga take ta Kamala Riga da siket na lace brown sai takalman ta da jaka da mayafinta farare.
Har kasa ta tsuguna tana gaishe da Baffan nata kafin ta Dan kalli gurin da Alhaji Jafar yake ta gaishe shi.
Baffan nata ta mikawa littafin hannunta tana fadar "Baffa ga project din nawa komai ya kammala".
Baki sake Alhaji Jafar ke kallonsu wannan 'yar yarinyar har ta Gama karatu ake nufi ko me"
💋❤
💋❤️️
AUREN HUCE HAUSHIN
💋❤️
💋❤️
đź”·PEGE TENđź”·
Story
&
Written
By
MAMAN FATIMAH
******Jujjuya littafin project din Ardo yayi, sai Kuma ya mikawa Alhaji Jafar Yana fadin "Duba ka gani Yallabai ni tunda ba ganewa zanyi ba,naji Dadi da Allah yasa aka Gama wannan karatun ba domin na saka auduga na toshe kunnuwa naba da ba'ayi karatun Nan ba, tunda Wanda yaso auren nata yace in dai zatayi karatun Nan shi ya fasa, shi Kuma Dan uwanta na wajen kanena yace karatu Babu gashi tunda tana ganewa Kuma tana so, kaga yanzu duk gurin nan namu ita me yiwa mutane Allura".
Kallonta Alhaji Jafar ya karayi,sannan ya kalli Ardon Yana fadin.
"Yaushe ta Fara karatun ne na ganta karama amma har ta hada diploma?"
Gyara tsayuwa Ardon yayi Yana fadin "wallahi am tun tana aji hudu na furamare Dan uwanta ta kaita aji daya na sakandire tunda yayi wani zuwa suka zauna da kannen nasa yaga tana da kokari shine yace Mata idan ta Gama makarantar tana son taci gaba da karatu, shine tace Masa tana son ta Zama malamar asibiti, to tunda sukayi haka ya kudurci aniyar tsayawa akan karatunta shi yasa da akayi Mata chaaaa akan maganar aure yace Bai Hana ayi maganar aure ba. Amma ya Dora sharadin saidai idan mijin ze barta tayi karatu abinda ya gagara kenan aka fasa Amma duk yan uwanta anyi musu".
"Masha Allah. Allah ya Sanya Albarka, haka ake so a rinka barin Yara Mata suna karatu barin ma na bangaren lafiyar da malaman makaranta, yanzu ba cewa kayi ita ke yiwa mutane allura ba da sauran abubuwa? To da batayi karatun ba da basai an tafi wai gurin an nema ba? Ba komai in Sha Allah zatayi auren ta Kamar kowa".
Ardo ya amsa da "Allahumma Amin".
Ma'un Alhajin ya kalla "Asma'u kin amince na tafi da project din naki na duba a hankali in yasa said dawo Miki dashi".
Kai ta gyada alamar Eh.
Sunyi sallama da Ardo tawagarsu suka wuce zuwa Yola inda zasu bi jirgi zuwa Abuja.
Wannan shine silar haduwar Alhaji Jafar da Ammah, ya koma maida project da Kuma kafa gwanatinsa cikin ikon Allah suka yarjewa juna.
Lokacin da magana tayi karfi Rabi'a taso tada hankalinta saida Nanna ta taushe ta da kalamai masu kwantar da hankali.
Cikin kankanin lokaci akayi bikinsu. Amarya ta tare cikin ikon Allah zaman Rabi'a da Asma'u ya kasance Zama Mai tsabta.
Wata uku da auren Asma'u ciki ya bullo duk masoyin Alhaji Jafar ya Taya shi murna sosai a lokacin ne Alhaji Jafar ya biyawa Rabi'a makka kusan abinda ya kwantar Mata da hankali kenan Dan ya fada Mata idan take tayi addu'a sosai akan matsalar ta.
A haka rayuwa ta dunga gurguwa har cikin ya Isa haihuwa Ardo dasu Inna maimuna sun so Ma'un to koma gida zaman haihuwa Amma Nanna ta Hana tace meye amfanin ta ita in dai sai Asma'u ta koma gida.
Cikin ikon Allah a wani dare nakuda ta tasowa Asma'u lokacin Alhajin Yana nan, Nan da Nan suka nufi asibiti wurin karfe biyu da rabi Amma kafin hudu Allah ya dauketa lafiya ta haifi takwaye mace da namiji.
Murna gurin wannan iyalin ba magana ranar suna yaran aka bar musu sunan su sai dai su Hassan da Hasana aka daka musu.
Kullum yaran suna tsakanin Rabi'a da Asma'u suka rainon 'ya'yansu. Lokacin da aka yayesu a lokacin Allah ya baiwa Rabi'a ciki itama ba'ayi wata biyu ba Asma'u ma ta Fara laulayi, cikin ikon Allah cikin Rabi'a ya zauna kusan lokaci daya suka haihu Rabi'a haifi Hamza yayin da Asma'u ta haifi Abdul Hakeem.
Bayan haihwar Hamza Rabi'a Bata Kara haihuwa ba Saida Asma'u tayi maza biyu sanan Rabi'a ta haifi mace Murjanatu, bayan Murjanatu Rabi'a ta Kara haihuwar Salma sai auta Hameeda ita Kuma Asma'u ta haifi Sulaiman sai auta Musaddiq, zuwa lokacin sunansu ya bace yayin da ake gadawa Hajiya Rabi'a Mama wasu na waje suce Hajiya Mama, Hajiya Asma'u Kuma Ammah.
WACECE FATIMAH ZAHRA?
'ya daya tilo ga kanin Ammah shaqiqi Muhammad Sani. Mahaifiyar Zahra Najwa Balarabiyar Jordan ce sun hadu da Muhammad Sani ne lokacin da yaje karatu kasar da farko mutunci suke da Najwa sai daga baya ya juye ya Zama soyayya har Allah ya nufesu da aure da taimakon wani malaminsu Dan kano Dan kusan ta bagarensa su Ardo wanda suke Kira Baffa ya Sani ya Kuma amince da Malam Muhammad Kabir ya Zama waliyyin Muhammad Sani a can.
Lokacin da Muhammad Sani ya Gama karatu ya zauna a can yayi aiki kusan shekara biyu daga baya ya tattaro nasu ya nasu suka dawo Nigeria, lokacin Najwa nada cikin Zahra wata bakwai a lokacin Kuma Ammah na goyon Sulaiman Mama na goyon Hameeda.
A Jimeta Muhammad Sani ya sayi gida saidai suje Mubi kawai suga iyayensa,ba dadewa Najwa ta haifi 'yarta Zahra wadda taci sunan mutum biyu mahaifiyar Najwa da Mahaifiyar su Ammah.
Haihuwar Zahra ba dadewa Muhammad sani ya Sami aiki a Abuja karkashi minstary of internal affairs da taimakon Alhaji Jafar.
Zahra nada wata biyar wani cikin ya bullo a jikin Najwa Mai wata irin masifar laulayi, Wanda ya tilasta Ammah ta dauke Zahra daga bakin nono.
Lokacin da komai da dai dai ta a gurin aikin nasa ya dauki Najwa suka koma Abuja.
Saida watan haihuwarta ya Kama ya kaita Mubi shi Kuma ya koma Abuja.
Lokacin data haihuwa iyayenta sunzo Nigeria da kanwarta Nawwara a Karon na biyu Mahaifiyar ta taso tafiya da Zahra Ammah ta dunga magiyar abar Mata ita harda kukanta.
Lokacin da suka Gama wanka Muhammad sani yazo ya tafi dasu tafiyar da har abada Basu dawo ba a hanya sukayi hadari sun bar Jos Basu karasa Abuja ba.
Yan uwa da iyaye sun shiga cikin tashin hankali marar misaltuwa Ammah tayi Kika Kamar ba gobe,ta rasa Dan uwanta shakiki, ba karamin Kai ruwa Rana akayi ba kafin Ummee kakar Zahra ta hakura ta barwa Ammah Zahrar.
Tunda daga lokacin Ammah ke baiwa Zahra wata irin kulawa ta musamman sai Kuma shima Mai gidan ya kwallafa ransa akan soyayyar yarinyar abinda ya haddasa tsana Mai tsanani tsakanin Mama da zahra inda ita mamar ke ganin Kamar nema ne yasa Alhaji ke kaunar Zahra, tana ganin idan Dan tana 'ya mace ne karama ai itama tana da nata kananan 'ya'yan mata Amma baya nuna kulawa akasu Kamar Zahra ko Dan tafisu kyaune tunda Babu inda ta baro uwarta.
Wannan kenan.
Ranar da za'ayi jarabawar share fagen shiga karamar secondary ta gwamnatin tarayya tun sassafe zu Zahra suka shirya ita da Sulaiman da Hameeda da Salma duk da Salma ta girmesu Amma yawan yi Mata repeating yasa suka taddo ta.
Har sun shiga mota Bala direba na niyyar shiga Zahra ta bude ta fito da sauri ta nufi cikin gida Sulaiman Yana kiranta tayi banza dashi ta shige da gudu ta karasa dakin Ammah tana fadin "Ammah na manta kayana da Ya Hassan ya kawo min har zamu tafi na tuna".
Daga toilet Ammar ta fito ta nufi bedside locker ta janyo ta mikowa Zahra ledar tare da fadar "Maza kada ku makara mana".
Kai Zahra ta gyada kafin tace "Ammah ki kara yi Mana addu'a Dan Allah Ina son naci jarabawar saboda Abbana yace idan naci makarantar zemin kyautar wani Abu"
"To naji maza Allah ya bada sa'a"
A kofa suka hadu da Sulaiman ya biyo ta tana fadin "Na rantsa da Allah zamu tafi mu barki ba Dan Abba ya fito ba da wallahi sai dai ki fito kiga bama gidan".
Kafin ya saki labulen ya juya Zahra ta Kai kofar da zata kaika compound din gidan.
Masha Allah anyi jarabawa an Gama sai jiran sakamako.
A haka sukaci Baga da zuwa makaranta har suka Zama common enterence a matakin jaha.
Lokacin da suka dawo zaman gida lokacin ne Alhaji Jafar da kansa ya yiwa Zahra passport da visa Saida ya Gama komai sannan ya fadawa su Ammah da Mama. Godiya Ammah ta shiga jerawa Mai gidan nasu,yayin da Mama tayi shiru Kamar bazatayi magana ba sai Kuma tace "yanzu Yallabai da kanka zaka rakata ai da Koda Hasana ko Hassan ka hadasu zasu kaita ko Kuma a fadawa cen kakanninta su turo a tafi da ita ai cacar kudin Kamar yayi yawa".
Daga Ammah har Alhaji Jafar din kallon Mamar suke ita dai Ammah shiru tayi yayin da Alhajin yace.
Saboda ban San darajar 'ya'ya ba zan hada Yara a tafiyar uwa duniya daga Nan har Jordan na kwanta a gida hanakli kwance ko?"
Kai ta gaigice tare da fadin "gani makudan kudi za'a kashe".
Wani kallo yayi Mata "kada ki kawo b'araka Rabi'a duk yaran dake gabana daya na daukesu yada zan yiwa abinda na Haifa haka zan yiwa marainiyar Allah. Da Kuma kike maganar cacar kudi idan zan jera shekara Ina Kai zahra Jordan kullum ba abinda ze girgaiza a cikin abinda na mallaka".
Ku tashi kuje.
Lokacin da zasu tafi anyi Mata tsara sosai Dan Nanna ma kilishi tasa aka yi Mai yawa na tsaraba.
Har kano su Ammah da yara sukayi musu rakiya.
Lokacin da sukaje Jordan din ba karamar murna kakanninta zukayi ba Dan Babu zato suka gansu, sun Kuma Kara yabawa da cika Alkawarin Alhaji Jafar Dan da kansa yayi musu Alkawarin ze kawo musu Zahra Dan ko a waya Bai fada musu zuwansu ba,sai address dai daya taba tambaya can wani lokaci.
A ranar Zahra taga zallar soyayya a gurin dangin Najwa Dan gidan cika yayi da 'yan uwa aka dasa sabon kukan rashin Najwar da kyar Abbie da Abbanta suka dinga Basu hakuri Dan ma Alhaji Jafar ba larabcin yakeji sosai ba saidai Wanda suke Jin turanci suka ringa magana dasu.
Lokacin da Alhaji Jafar din ze tafi masukin daya Kama a hotel Abbie hanawa yayi duk yanda yaso zillewa kin yarda yayi dole ya amince aka sauke shi a wani part dake kusa da nasa Ummee din, Dan ba karya dukiya dai Kam akwaita Dan shi kanshi Alhajin yayi mamakin yanda ya riskesu Bai taba kawo haka suke ba lallai yasan hadin Allah ne kawai da suka bawa Muhammad sani auren 'yarsu Dan tazarar Mai nisa ce a tsakanin su.
Kwanan Alhaji Jafar bakwai ya wuce Umara yayin da Ummee tayi Masa Alkawarin zasu hadu a Saudiyyar tunda zata kawo Zahrar Nan gurin iyayenta da 'yan uwa su ganta a cikin garin Madinatul Munawwara.
Satinsa daya da zuwa Suma su Zahrar sukazo Saudiyyar ita da Ummeen da Aunty Nawwara.
A Nan ma Saudiyyar Zahra taga gata iya gata Dan kowa Nan Nan yake da ita, Dan kanwar Ummee Hanifa sosai ta kafe sai dai a bar Mata Zahra ta tafi da ita Istanbul inda take aure Wai Bata yarda da zaman Nigeria ba.
Ankai ruwa Rana da ita kafin ta hakura Dan da gaske Alhaji Jafar ya bude Mata aiki Dan cewa yayi idan irin haka za'a ringa yi bazai Kara bawo musu ita ba saidai duk Mai son ganinta taje ya ganota Kamar yanda Ummee keyi, hakuri aka ringa bashi.
Saida aka Kai Zahra makka suyi kayi umara sannan suka fara Shirin baro kasar.l Sayyaya dai Zahra ta shata Dan wasu kayan sai a awon cargo akayo musu su.
Sarkar gwal da warwaro zobe kuwa kirar Saudiyya da Dubai zuwa kirar Bahrain sun Kai kala goma duk dai dai size din ta sai na Ammah biyu na Hasana ma biyu shi kanshi Alhajin anyone mass goma Sha Tara ta Arziki.
Ranar da zasu dawo Zahra Tasha kuka haka kakarta Ummee,har jidda sukayo musu rakiya Basu suka tafi ba sai da jirgin su Zahra ya tashi a sararin subahanahu wata'ala.
Saukar safe sukayi anan suka samu Bala direban Alhaji Dan Bai fadawa kowa sun taho ba sai Balan kawai, sau da yawa idan ya fada gashi Nan a hanya hankalin Nanna baya kwanciya har sai ya iso.
Lokacin da suka shigo harabar gidan suna tsayawa Zahra to garzaya cikin gida tana fadin "Ammah!!! mun dawo".
Da gudu Hameeda ta fito daga part dinsu, rungume juna sukayi suna ta tsallen murna Sai jikin zahra Hameedar ke shafawa gani take kamar canza Mata Zahrar akayi.
Da sauri Ammah ta fito tana "fadin wa nake gani ne haka Kamar bakin saudiyya zuwa ba notice?"
Alhajin ne ya Bata amsa.
"Surprised din ki mukayi ko Zahra na?.
Kai ta gyada masa.
Kayansu ne su Bala da Mai gadi suka Fara shigowa dasu kafin Alhajin ya nufi part dinsa na cikin gidan yayin da Ammah ta rufa Masa baya.
Har yayi wanka ya shirya Mama Bata shigo ba, har ya tambayar Ammah yayi Ina Rabi'a ? Tace Masa tana ciki watakila ko barci take.
Kusan kwana su Zahra sukayi tana baiwa Hameeda labarin abinda ta gani da inda sukaje a Jordan da saudiyya, wurin karfe biyu Ammah ta tashi zatayi nafila ta jiyo su suna Hira a dayan bed room dinta lokacin wuri biyu da rabi na dare, leko tace su kwanta basu san dare yayi sosai ba.
Washe gari an baje tsarabar Zahra an baiwa kowa dai dai gwargwado.
Amman tsarabar Hameeda daban take Dan har sarka Saida ta baiwa Hameedar.
Basifi sati biyu da dawowa ba jarabarsu ta fito ta Federal inda Zahra ta samu F.G.G.C KAZAURE yayin da Sulaiman ya samu F.G.C DAURA, Hameeda F.G.C AZARE. Salma ce kawai bata samu ba a cikinsu.
Sunyi murna Kuma sunyi bakin cikin rashin samun makaranta daya duk an watsa su Abban Kuma da ya Hassan sunce kowa ya tafi inda ya samu, ita Hameeda Bata da damuwa tana gida, su Kuma duka 'ya'yan Ammah duk sun fita waje danma hanyarsu daya sai an aje Zahra a karasa da Sulaiman.
Ranar da zasu tafi sun Sha kuka haka suka dauko hanya malam Bala da Ya Hassan ne suka kaisu.
Lokacin da aka Kai Zahra an tashi daga aji, wasu Yara House master dinsu ya kira da wata prefect yasa su Kai Zahra room din 'yan j.s one.
A cikin yaran da suka Taya Zahra daukar kayane wata yarinya tace Mata "sister kizo ki zauna a kwana ta tunda ni daya ce saman gadona ba kowa".
Kai kawai zahra ta gyada Mata tana ta sauke ajiyar zuciya.
Ita ta taimkawa Zahra ta shirya komai a locker dinta, Saida ta Bari zahra ta HUCE daga kukan da tsaha sannan tace Mata "ni sunana Sajida Musa ni 'yar kano ce unguwar Gwammaja kefa ya sunanki?".
Nan Zahra ta fada Mata komai nata tun daga Nan suke tare har suka Zama aminai komai nasu ya Zama daya banbanci su kawai Sajida na A Zahra na C.
Haka sukaci gaba da rayuwa a makarantar gasu Kuma Yara masu kwazo barin zahra ga kyau ga ilimi Nan da Nan tayi suna a makarantar kafin hutu tayi popular sosai a makarantar, idan kace 'yar larabawa kowa ya santa ba Kuma Dan Babu irin jiinsin nata ba A'a farin jini ne daga Allah.
Lokacin da akayi hutu Zahra ba karamar murna tayi ba Kuma cikin ikon Allah da wuri malam Bala yazo lokacin har ya dauko Sulaiman.
Bayan Azahar kadan suka shiga Azare sunyi murna sosai da ganin mutanen gida Dan Sulaiman har da kuka, Nan su Hameeda suka saka gaba suna tsokana.
Haka suka cigaba da karatunsu cikin amincin Allah, lokacin da sukazo hutun third term ne akayi auren Aunty Hasana aka kaita Jos, Ya Hassan Kuma Daman Yana karatunsa a Rasha.
Kowa inda yake yacigaba da karatunsa Salmace Allah ya taikata ta samu shiga FGC AZAREN itama a ss1.
A haka aka dunga juyawa har suka Gama secondary School dinsu suka dawo gida.
Dawowarsu ba dadewa Allah ya yiwa Nanna rasuwa rashin daya taba Abbansu sosai.
Dan ya Dade Yana fama da damuwa tunda a rayuwa da ita ya tashi baisan dadin uba namiji ba itace komai nasa.
Ganin abin nasa Yana neman yayi yawa yasa Abokinsa bakon malamin daya sauka Nan daura gidan Nanna da almajiransa dududu Bai zaifi sa'an Alhajin ba malam Bubar ya dukufa yi Masa addu'a tare da saka Yara kanana suna Masa addu'a, cikin ikon Allah sai komai ya daidaita.
Ranar wata laraba zahra ta shirya zata raka Hameeda duba Qawarta meenal gidan Dan majalissarsu Mai wakiltar su majalissar Jaha, wani material ta saka Mai ruwan sararin samaniya yayi matukar karbar jikinta haka dinki ma ya Dace da material din, simple makeup tayi ta saka turarenta Amber oud new edition na kamfanin Al haramaini.
Tunda ta fito Mama ke Mata wani irin kallo Wanda har saida ta rinqa Jin ta takura kafin Hameedar ta fito.
A kasa suka taka suna Hira har sulaje gidan,sun Dan jima suna Hira da marara lafiyar kasancewar breast lump ne aka cire Mata ba wani serious case bane.
Lokacin da zasu tafi suka Kara komawa gurin mamanta sukayi Mata sallama suna zaune ne da a falonta kafin meenal din tayi Mata magana ta fito. Wani handsome guy ne ya shigo falon da sallama ya Dan jefa car key dinsa sama, kana ganinsa kasan hutu ya Kama jikinsa.
Ciki ya shigo lokacin da Suke amsa masa sallamarsa kujera two seaters ya zauna a Kai wadda ke facing dinsu Hameedar.
Gaishe shi sukayi su Duke ya amsa Yana cewa "Hameeda daman kina Nan na Dade ban ganki ba gaskiya Ina ga tun kafin na tafi Colombia fa".
Dan rausayar da Kai tayi tana fadar "wallahi Kam Ya Sahal an jima Kam kune dai bakwa ganuwa Kuna uwa duniya kunyi shiru Kum barmu da zafin Kasarmu".
Ta fada tana dariya.
Dai dai lokacin mommyn su meenal din ta fito kallon Sahal tayi tana fadar Kai Kuma haka mukayi da Kai?"
Kaisa ya Dan Sosa da key din hannunsa Yana fadi "Iam so sorry Mom kada ki damu yanzu zanje na kawo Miki in Sha Allah."
Ya fada Yana mikewa da nufin tafiya Meenal tayi tsagal tana fadin "Dan Allah Ya Sahal ka tafi dasu tunda cikin garin kayi.
Suka yiwa mommy sallama da godiya suka fito da leda Mai Dan girma a hannun Meenal wadda mommyn ta Basu.
Har kofar gida ya kawosu suna tsayawa ya kalli Hameeda Yana fadar "Dan Allah ki bani aron sister din take Mana Kona ten minutes ne Mana".
Dan murmushi tayi tana fadar.
"Ka Fara yiwa Abban mu magana dai haka Naga anayi"
Ita dai Zahra ciki ta wuce Dan Kamar a kan.kaya take duk ya takura Mata da wani irin kallo har a cikin mota ma saita mirror yayi sitinta tunda Hameeda ce ta zauna a seat din gaba tana Masa Hira Amman gaba daya hankalinsa yana kan Zahra.
Ita dai zahra Bata San yanda suka Kare ba taga dai Lokacin da Hameedar ta shigo ta wuce dakin su.
Bayan kwana biyu da zuwa gidansu Meenal da yamma su zahra sun tafi islamiyya ne baki sukazo gurin Alhaji Jafar, ya sansu farin sani daya kanin Dan majalissar su ne dayan Kuma kanin Babansu.
Yayi mamakin ganinsu Saida suka gaisa ne suka bijiro da abinda ya kawo su na yiwa yaron gurin Dan uwansu Sahal kidiba yaga yarinyar gurinsa Yana so. Shine mahaifansa ya turosu ya gabatar da maganar Yana neman izininsa na Fara zuwa gurinta Shira.
Alhajin yaji Dadi sosai na yanda suka zo suka memi izininsa duk da Daman sharadinsa kenan, ya Kuma nemi Jin wacece daga cikin yaran suka gada Masa zahra ce, nan ya amince musu da addu'ar Allah ya hada kawunan su.
Tun daga lokacin Sahal ya Fara zuwa gurin Zahra cikin ikon Allah tayi na'am dashi Basu Dade sosai ba sukayi wata irin shakuwa ta ban mamaki duk Wanda ya kwana ya tashi a unguwar yasan irin soyayyar da sahal yakewa zahra kusan Kullum da yamma Yana nan makale da ita, a haka har manya suka shiga maganar aka tsaida lokaci wata shida inda zasu tafi Colombia inda yake hada masters dinsa ita kuma zata Fara nata degree din.
Anyi lefe na garari Wanda ya dauki Baki fiye da tunanin Mai tunani, an kashe kudi Kamar ba'a San zafinsu ba.
Lokacin da bikin ya rage baifi saura wata biyu ba sai lamarin ya Fara canzawa kwata -kwata Sahal ya rage zuwa gurin Zahra haka ma sai a kwana a wuni Bai kirata ba, duk wani zazzari da yake na bikin su events din da yake ta faman damun zahra da maganar duk ya daina Kai tafi-tafi sai ayi kwana uku hudu har sati Bai kirata ba, da farkon abin tana kiransa taji ko lafiya a yanayin yanda yake amsa Mata wayar saita hakura da Kiran nasa, tun Ammah na zuba ido har ta samu Zahra a wani dare ta tsareta da tambayar ko wani Abu ya hadata da Sahal ne? Ta Bata tabbacin ba abinda ya hadasu sai dai ta fada Mata yanda suka ringa yi dashi a kwanaki idan ta Kira shi.
Addu'a Ammah ta Bata tace ta ringa yi itama zataci gaba da yi, Mata sannan ta umarceta da kada ta Kara kiransa a wayar ta zuba ido kawai.
Duk abinda Ammah take na shirye-shiryen Baki Bata fasa ba, tayi waya mutanan Jordan ma sunce suna Nan tafe Amma a daure a turo Zahra Kamar saura wata data bikin.
Ba'afi sati daya da waya da kakanninta na uwa ba sakon kayan dakinta ya sauka Nigeria daga Istanbul kayan da suka gigita Mama Dan ba kayan Wasa bane set din gado har hudu kujeru set uku bayan electronics kuwa wasu har ba'a San amfaninsu ba sai dai idan an duba manual din.
Alhaji Jafar yayi fada Kamar ya Ari Baki lokacin daya Kira Abbie akan danme zasuyi Masa haka toshi meye amfaninsa da bazasu Bari yayi Mata kayan dakin ba.
Hakuri Abbien ya shiga bashi akan su basuyi Dan su Bata Masa raiba, sunga abinda ya kamata suyiwa diyar Najwa kenan.
Ammah da Mama Alhaji Jafar ya Kira ya fada musu tunda an Riga an yiwa zahra kayan dakin da duk abinda ya kamata to ga fifty million Nan ya baiwa Zahra idan komai ya nutsa saita Fara business na abinda take son sayarwa sannan ya Bata shanu biyar.
Kuka Ammah ta saka saboda Dadi ta rasa bakin da zatayi Masa godiya, yanda take dawainya da wannan marainiyar Allah Bai taba gajiyawa ba.
Mama ce ta Ari bakinta tana ta yiwa Abban godiya da saka Albarka sai faman dariya tace bakinta yaki rufuwa, tun Ammah na ganin dariyar farin ciki ce har ta Fara wani tunani na daban, Nan da Nan ta Kori shaidan akan abinda zuciya ke sawwala Mata.
Lokaci na Kara tafiya daukewar ma'amala na Kara yawaita a tsakanin Sahal da zahra, yanzu ta Kai kwata-kwata sun daina waya dashi, ana saura kwana talatin da hudu a Fara biki Wanda yayi daidai da saura kwana uku zahra da Hameeda da Abdul Hakeem su tafi Istanbul. Dan direct gurin kanwar Ummeen Hanifa zasu tafi daga baya su Ummeen sun samesu a can, idan an Gama komai su rankato Nigeria Dan da gaske Ummee ta shiryawa bikin sosai.
Washe gari, tunda gari ya waje Mama ke Kai kawo tsakar gida duk da ba aikinta bane ba Kuma halayyarta bane hakan. Yayin da a bangaren Ammah ta rasa me yake Mata Dadi duk kasala ta baibayeta jinta take Kamar ma zazzabi na neman rufata...

✨AUREN HUCE HAUSHIN ✨️
💋❤️
💋❤️
STORY
&
WRITTEN
BY
MAMAN FATIMAH.
🔷✨PAGE ELEVEN✨🔷 (11)
________Misalin Sha biyu da rabi na Rana kawar Mama kuma Aminiyar Asabe tazo gidan macece wayayya Mai kisisina Bata fiye zuwa gidan sosai ba sai lokaci lokaci, ta Dan jima a dakin Ammah suna hira har tana tsokanar zahra da Amaryar gobe ana dariya.
Part din Mama ta shiga suka kule a master bedroom dinta.
Batafi awa daya da zuwa ba, wasu Mata suka shigo gidan lokacin Ammah tana bangaren Abba.
Zilai Mai aik cei ta leko tana fadin "uwar dakina anyi baki kuwa ko Ammah zaki yiwa magana Naga bakin nata be"
Mayafi karami ta Dora a saman gashinta da tayi parking dinsa har wajen kugunta Yana reto Baki sidik dashi jikin Nan nata Kamar ka taba jini fito.
Lekowa tayi tana musu sannu da zuwa tare da gaishe su tana fadar "ku shigo daga ciki Bari na Kira Ammar".
Ta fada tana zura silifar a kafarta.
Daya daga cikin su ukun ne ta tabe Baki ta kauda Kai tana fadar "kirawo ta tazo ba sai mun shiga ba tunda ba Zama mukazo ba"
Ita dai Zahra gaba tayi yayin da su Zilai masu aiki suka zuba musu idanu suna kallon kallo ya junansu Dan daga Jin lafazinsu sun San ba abin Arziki ne ya kawosu ba.
Kafin Ammah ta fito daga bangaren Abba sahura Daya Mai aikinta ta leka ta fadawa Mama anyi baki. Da ita da Asaben suka fito Asaben na fadin "lale barhabin kushigo Mana kun tsaya daga wajen"
Wata ce daga cikinsu Bata farkon da tayi maganar ba tace "A"a Hajiya ba Zama mukazo ba munzo ne mu karbi kayan lefen da muka kawo na Sahal yace baya yi akai kasuwa".
Lafazin da Ya yiwa Ammah sallama kenan lokacin data fito Zahra na biye da ita.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un"
Abinda Ammah ta fada kenan a zuciyar ta Nan da Nan wani jibi ya taso Mata.
Salatin Mama da Asabe ne ya fito da Alhajin daga part dinsa yayin da su Zilai sukayi cirko-cirko duk wuta ta dauke musu Dan maganar tasu ba karamin razani tasa a zukatansu ba.
A hankali ya karaso kusa da Ammah Yana tambayar meke faruwa ne kafin tayi magana Mama tayi tsagal tana fadin "wane irin cin mutunci ne Alhaji ba laifi tsaye bana zaune zasuzo suce a Basu lefensu Wai auren amfasa".
Ta karasa fada tana fashewa da kuka tana maganganu, ita kuwa Ammah ba abinda take sai ambaton Allah yayin da Zahra ta nemi gefen inda aka shuka filawoyi ya zauna Dan ji tayi Nan da Nan jiri Yana nema kayar da ita, itama bakinta ba abinda yake sai ambaton Allah.
Kallo Daya Alhaji Jafar yayiwa Baki ya kawar da kansa Dan da alama da rashin mutunci suka shigo gidan. Gyaran murya yayi kafin yace "Masha Allah munji sakonku Amma Dan Allah ku koma kuce musu zuwa anjima inshallah Allahu za'a dawo da duk wani Abu daya kasance nasu ne har sadakin da suka kawo Allah yasa hakan yafi Alkhairi".
Yana Gama fadar haka ya juya dakinsa ya barsu a Nan a teaye, Dan dukkansu ba karamin kwarjini yayi musu ba.
Ammah part dinta ta nufa duk kwakwar mutum baze taba Gane Yanayin da take ciki ba.Dan Allah yayi Mata wata irin zuciya Mai iya danne bacin Rai da wuya ka Gane fushinta tana da hadiye fushi sosai, dakin suka bita suna Bata magana Mama sai sharbe take tana Dan Allah wannan wane irin cin zarafi ne da tazarce ace saida komai ya kankama sannan za'a bullo da wannan cin zatafin dan a wulakanta yarinya har a ringa yi Mata wani gani -gani aga Kamar wani Abu tayi yasa aka fasa".
Sai lokacin Ammah tayi magana tana fadin "ba komai Mama Daman can haka Allah ya nufa ba mijinta bane Kuma maganar mutane su ringa ganin Kamar wani Abu marar kyau ne yasa aka fasa na barsu da Allah yayi Mani maganin komai, ba komai haka Allah ya nufa rubutaccen Al'amarine baya goguwa".
Tana Gama fadar haka ta wuce bedroom dinta sun jima a falon suna tattaunawa kafin su koma dakin mamar su Zilai kuma suka nufi in da Zahra tace zaune suka dinga Bata magana duk da Bata want rude ba a nitsenta take.
Duk wannan kwamacalar da akayi su Hameeda da Salma basa Nan sunje Aiken Mama.
Tunda Alhaji Jafar ya koma daki ya kasa zaune ya kasa tsaye Bai taba zaton karamar magana daga gida irin Honorable ba Amma ya hanasu kayan ne Dan ya tabbatar da daga Ina maganar take shin da sanin uban yaron da waliyayansa ko Babu Dan yanda sukayi komai cikin girma da mutunci ya kamata ko baza'ayi auren ba to a rabu cikin mutunta juna.
Su malam Bukar da Yayan Alhajin Wanda suke 'yan maza Alhajin ya Samu da maganar basuyi kasa a Gwiwa ba zuka nufi gurin waliyyan Sahal sai dai maganar haka take Dan sun tsame ma hannunsu daga lamarin tunda iyayensa Basu da lissafi, Wai yaron ne yace musu shi baze iya auren Zahrar ba yanzu ba wadda ya tsana kamarta duk duniya".
Lokacin da suka dawowa da Alhajin wannan labarin ransa yayi matukar baci, a ranar aka maida duk wani Abu da yake mallakinsu ne.
Sai dare Abban ya Samu kebewa da Ammah in da ya ringa tausarta da kalamai masu Dadi har ta Samu ta Samu nutsuwa Amma fa kasa kwana tayi a dakin nasa.
Lokacin data dawo daki Zahra Bata tafi nasu bangaren ba tana dakin Amma a kan gadon tayi rigingine idanuta a rife hawaye na zurarowa daga gefen idon wani Abu yake Mata yukuki a zuciyar ta.
Har Ammah ta bude kofa zahra Bata sani ba saida ta zauna a kiss da ita taji shashhshekar kukanta kasa -kasa.
"Tashi zaune magana zamuyi".
Daga sama taji maganar Sam bata San Ammar ta shigo ba.
Ba musu ta tashi zaunen tana koge fuskarta da tayi wajir.
"Meye dalilin da Sahal ya fasa Aurenki ko ya sanki 'ya mace ne".
Cikin tashin hankali marar misaltuwa Zahra ta dago ta kalli Ammah kafin ta fasa kukan da take dannewa tana na zuci. Kai ta shiga girgizawa tana wani irin numfashi nKamar wadda zata shide.
Kafin Allah ya batan ikon bude bakinta ta magantu. "Wallahi Ammah ban taba abinda kike tuhumata ba Koda wasa wallahi zan rantse Miki da Alur'an a bani zanyi Alwala in ratse, idan na taba Zina Ammah Allah ya haramtamin shiga Aljannarsa ranar Alkiyama"
Ta fada tana wani irin kuka Mai taba zuciyar Mai sauraro.
"Shitttt.....kada na Kara Jin wata magana makaranciyar wannan daga bakin ki. Ba zarginki nakeyi ba na kasa samun nutusawa ne tun lokacin da sabbin halayensa suka Fara fitowa, nake cikin zulumi da taraddadi saboda sanin yanda rayuwa ta Zama abinda ta zama, ba komai kansa yayiwa ke kuma Allah yayi Miki Albarka ya bakin Wanda yafi Sahal".
Bata iya amsawa a fill ba sai a zuciyar ta.
Tun bayan faruwar lamarin Zahra ke cikin damuwa Dan ma Haneeda tana tausarta da kalamai na kwantar da hankali. Ammah ta Kira su Ummee ta fada musu komai sun so kwarai zahrar taje Amma Alhaji Jafar yayi uwa yayi makarb'iya akan suzuzo idan hankali ya kwanta, da haka suka bar zancen.
A Dan tsakanain ne Aunty Hasana tazo, sun Sha jajantawa sosai da Ammah itama sai da ta tsare zahra da tambayoyi kala kala, daga karshe ta Kare da nasiha Mai tsoratarwa sosai.
Lokacin da zata koma Jos ta nemi zata tafi da Zahra Abban bai Hana ba Yana ganin idan tayi nisa da garin zatafi Samun kwanciyar hankali.
Zamanta a Jos Mai Dadi ne Dan daga baya ma fafutukar nemar Mata admission mijin Aunty Hasanar ya Fara ba'a samu wadda ake so ba, sai diploma ya nemar Mata a wata private school ta Fara computer science.
Hankalinta ya kwanta sosai ta cire soyayya daga zuciyar ta Sam taqi ba kowa fuska akan soyayya duk da yanda ake kawo Mata Rida.
Ranar wata litinin sun Gama lectures dinsu na safe suna zaune da wata course mate dinta 'yar kabilar Tiv suna wani Assignment jininsu ya hadu da jannifer sosai Dan har gidan Aunty Hasana tana zuwa idan zasuyi wani aikin.
Bayan sun Gama ne suka nufe caf'e na cikin makarantar a cire musu hard copy din aikin suka tarar da cinkoson mutane dole tasa suka fito waje ayi musu.
Har sun Gama sun fito suna niyyar tsallaka titi ne wata mota Mai azabar kyau ta tsaya dai dai inda suke tsaye. A hankali na ciki ya sauke tinted glass din motar, wani guy ne da gani hutu ya ratsa shi sosai, murmushi yayi musu idonsa na kan zahra
Yana fadin "sannunki"
Jannifer ce to amsa masa Dan tana Jin hausa Kamar jakar kano.
"Yauwa sannunka" ta fada.
Kofar ya bude ya fito Yana sanye da kananun Kaya,fari tas dashi kamar irin ruwa biyu din Nan half cast Dan sumarsa a nannade take kamar irin ta buzaye din Nan.
Cikin kwarewa da yadda da Kai kalli jannifer Yana fadar "Naga kawarki ne inso da fatan zakiyi min campaign".
Dariya tayi tana kallon Zahra wadda tayi kicin kicin da fuska Kamar zatace wayyo Allah.
"Gaskiya na tafi tunda Baki da aikin Yi ke saiki zauna".
Zahra ta fada tana nufar titi ganin an Sami space din tsallawa.
Jannifer da Dan jima dashi kafin ta shigo cikin makarantar, Koda ta shigo Bata yi Mata maganar komai ba har suka Gama lacture dinsu suka tashi. Direban su Aunty Hasana ya dauke su ya ajiye jannifer a hanya kasancewar su zahra sun gaba dasu Amma hanyarsu daya sau da Daman sukan tafi tare ranar da jannifer Bata zuwa shagonsu.
Ranar Saturday misalin hudu da rabi haka su zahra da yaran Aunty suna compound din gidan tana Dora Yara kan lilo marry go round suna Wasa kusan duk weekend a Nan suke hutawa da yamma tunda islamiyyar safe suke zuwa a weekend.
Mai gadi ne ya nufo gurin da suke Yana fadin Zahara'u ki fadawa yallabai Yana da bako a waje".
Auntyn ta fadawa Abban su Faruq Yana da bako inji Mai gadi.
Lokacin daya fito yayi mamakin da baiga bakon ba ya nufi gate Yana tambayar Mai gadi, shine yace "ni ne na hana ya shigo tunda yace bakasan da zuwansa ba bilhasal ma yace baka sanshi ba"
Kofar Mai gadin ya bude masa ya nufi gurin da motar take yayin da shi kuma na cikin ya fito. Da gaske baisan yaron ba, hannu ya bashi sukayi musahiha sai Kuma sukayi shiru Ya Aliyun ne mijin Aunty Hasanar yace Masa "ko kaine maisallama Dani?".
"Eh nine"sai Kuma ya danyi shiru.
Ya Aliyun ne yace "my friend pls talk feel free with me".
Nan yayi Masa bayanin yaga Zahra ne Yana sonta shine ya biyota gida, ya fada masa sunansa MUNEEB mahaifansa Kuma Alhaji Salman Mai fata. Kallonsa ya Aliyu ya karayi yayi mamakin yanda d'a Kamar na Alhaji Salman Mai fata yake da irin wannan tarbiyya ganin yanda mahaifansa yake da mahaukanta kudi Kuma yasan 'ya'yansa sosai Amma da yawansu gata yasa sun lalace basa ganin kan mutane da gashi.
Ya Aliyun yaji dadi sosai ya Kuma bashi damar zuwa gurin Zahrar sannan ya Dan fada Masa wacece Zahrar a gurinsa.
Lokacin da ya Aliyun ya koma bayani ya yiwa Aunty Hasana na abinda ya faru itama ta bada goyon baya tasan ko yanzu Zahra tayi gaba Allah ya Bata Wanda yafi Sahal Dan ba karya ba hadi a tafiyar.
Da dare Aunty ta Samu zahra da maganar da farko tuburewa tayi akan ita Bata so saida Aunty ta fito Mata ta bayan gida sannan ta fashimci abinda Auntyn take son ta Gane.
Washe gari Aunty har da ita aka hadawa MUNEEB abin tarba, Zahra ta Dade tana mamakin yanda akayi yasan gidan su Amma data Zama very curious sai ta gano duk yanda akayi jannifer ce ta bashi address dinta. Yau ma da yamma yazo, falon Ya Aliyu aka bude Masa yayin da Mai aikin Aunty shema'u ta Kai Masa abin tarba.
Wata straight gown ta saka ta atamfa glitter Mai ruwan peach colour sai madaidaici gyale kalar lemon green irin touching din jikin atamfar sai takalmi shima lemon green din plat Mai kyau. Bata daura dankwalin kayan ba. Ta fesa turenta Amber oud gold, tun kafin ta karaso kamshin ta ya fada Masa zuwanta, kofar ya zubawa idanu ai lokacin data shigo da sallama Saida ya Dan samu shock na wucin gadi Ashe ranar ba inishin Zahrar ya gani ba yanzu ne yaga zahirinta, a kasa ta zauna kan carpet tana gaishe shi kanta Yana kallon kasa. Nan ya gabatar Mata da kansa da abinda ya kawo na son aurenta, bai matsa Mata na lallai sai yaji ra'ayinta a sannan ba shima bai jima ba ya tafi, bayan ta shigo ne Mai gadi yayi knocking a kofar falon shema'u ta bude manyan ledoji ne ya Mika Mata guda biyu yace a bawa Zahara'u inji bakonta.
Tun daga lokacin Koda yaushe Muneeb yana hanyar gurin Zahra,r tun tana dari dari dashi har ta sake, shi mutum ne Mai saurin shiga Rai Yana da wasu Qualities da zasusa asoshi.
Kafin su rufe wata biyu sunyi wata irin shakuwa ta ban mamaki duk Wanda ya kwana ya tashi a family din Mubeen yasan da zaman Zahra haka itama nata sun San Muneeb Dan har Azare yaje ya gaishe su da ashirin bama sha tarabta Arziki ba,har Saida Abban su yayi Masa fada sosai akan kada ya Kara musu haka in dai Yana son su Shirya.
Sun daf da Gama diploma dinsu Iyayen Muneeb sukayi maganar aure, ba Bata lokaci aka saka Rana ba'a wani ja lokaci ba Mai tsawo ba, abu kama-kama shima Kamar na baya abun ya shashence ba wani cikakken dalili haka Nan Rana tsaka Muneeb yace ya fasa akayi juyin duniyar Nan yace shifa aure ba dai da Zahra ba komai za'ayi, dole aka hakura Dan shi cewa yayi har kayan ya bar Mata saidai abinda iyayenta Basu amince ba kenan.
Fadin halin da zahra da su Ammah suka shiga bazai misaltu ba, Dan hankalinsu yanzu yafi tashi fiye da wancan lokacin.
Ammah taso kwarai zahrar ta koma Azare Amman Maman Ya Aliyu ta roki Alfarmar zata Kai zahra gurin masu Islamic chemist a gani ko namijin Aljani ne ya aureta.
Ammah ba tayi musu ba sai godiya tayi sosai, sunje harda Aunty Hasana anyiwa Zahra tambayoyi ba alamar Aljani a jikinta sai dai sun fada musu da alamar sihiri a tare da ita Amma ba sosai ba, Nan suka bada magunguna Hajiyar ta biya suka dawo gida.
Jannifer ma tayi bakin cikin abinda ya faru taso Zahra ta Bata dama taje garinsu ayi mata wani Abu akan idan ma wani ne yake lalata lamarin auren zega abinda ze same shi. Nunawa tayi Bata so ita haka Allah ya tsara Mata wannan qaddarorin Kuma ba makawa sai sun sameta.
A haka har suka Gama diploma dinsu kafin Aunty Hasana ta mayar da Zahra Azare.
Haha rayuwa taci gaba da gudana, duk wani buri akan aure Zahra ta cire shi Bata kula kowa duk iya nacin mutum Bai isheta kallo ba, wani lokacin har fada suke da Hameeda akan rashin kula samari sai dai sau da yawa tana Mata uzuri akan irin yanda fasuwar aure take walagigi da ita.
Zama ya Mika lokacin har anyi wurin wata Tara da fasa aurenta da Muneeb. Wani yammaci suna zaune a bayan part din Ammah ita da Hameeda da Mujiba data shigo musu yawan yamma suna hira Kiran ya Abdul Hakeem ya shigo wayar Hameeda Yana tambayar suna ina ne ya shigo Bai gansu ba.
Inda suke ta fada Masa suna niyyar tashi ya zagayo bayan, a tare suka gaishe dashi ya amsa Yana gaisuwar tasu yana fadin "Congratulations"
"For what Yaya?" cewar Zahra.
Irin Brown din envelope din Nan babba ya Mika Mata Admissions letters ne guda biyu a ciki na Salma da Hameeda duk sun Sami gurbin karata a federal University Dutse jigawa state (F.U.D).
Cikin murna ta rungume Hameeda tana fadin "congratulations sister".
Kafin ta sake ta tana Mika Mata takardun, ai tana arba da wannan abin Arziki ta Diba a guje tana fadin"thank you Yaya Allah ya saka maka da Alkhairi".
Bayan ta wuce ne zahra ma ta Kara Masa godiya sosai.
Kujerar da Hameeda ta tashi ya janyo ya zauna alamun dake nuna magana Mai mahimmanci zeyi da ita.
Ganin haka yasa Mujiba tashi tana fadin "Yaya sai anjima".
"Dawo ki zauna ba Zama zanyi ba.magana zan fada Mata kawai"
A takure ta koma ta zauna.
Kan Zahra ya maida kallonsa "kina jina?" Kai ta gyada Masa alamar eh.
"Good" ya fada.
"Ina ga Nan da one month ko three weeks kema Zaki wuce Zuwa Turkey daga can Kuma idan komai ya daidaita Zaki wuce syprus inda Zaki hada a degree dinki, idan kin tuna Kamar two months da suka wuce ai na karbi komai naki to Mama Hanifa ce ta bukata a tura Mata a she makarantar zata nemar Miki taso a Samu a Nan turkey din to ba'a samu ba, ita kuma Bata son a Kara Bata lokaci, shine ta yiwa danta magana tunda a can yake aiki da ofishin jakadancin turkiyya na kasar Kuma ma Nan ne kawai Mama Hanifar ke ganin yafi kusa da istanbul din".
Ba Zahra kawai ba hatta Mujiba tayi murna kwarai da gaske gatan da za'a yiwa Zahra kenan a irin wannan lokacin na a rabata da kasar gaba daya Kota Samu peace of mind.
Godiya ta ringa yiwa ya Abdul Hakeem din harda 'yan hawayenta na Dadi.
Gashi Ammah Bata Nan taje Jimeta gurin biki, taso tana Nan ta kwanta a jikinta suyi sharing din farin cikin. Har ya Abdul Hakeem din ya kai kwanar da ze fita ya juyo Yana fadin "don't talk to anyone, keep silent pls, nasan Mujiba Bata da problem shi yasa na fada a gabanta".
Yasa Kai ya wuce.
Kallon junan su sukayi suna son banbance maganar Ya Abdul Hakeem.
💋❤️
AUREN HUCE HAUSHI
💋❤️
MAMAN FATIMAH
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.