Trending Hausa Novels

Auren Huce Haushi Book 1 Complete Hausa Novels By Maman Fatima

Reading file: AUREN HUCE HAUSHI BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN FATIMA.txt

Chapter 26 of 34

Page 36

______Zahra tana Gama fadawa Asaben abinda ke cikinta ta juya musu baya, ko banza bazata kwana da fushin zuciya ba, dan tasan idan ba ita tayi magana ba Babu abinda Ammah zata ce Dan sau da yawa idan irin haka ta faru ko kallon Mama batayi sai dai ta bawa banza ajiyarta.
Daga Asaben har Mama ba Wanda ya Kara magana,haka Ammar ma da Zilai ba Wanda ko tari ya kuncewa, Auta kuwa wayar mamar ya dauka yaci gaba da sha'aninsa.
Shiru dakin ya dauka kamar mutuwa ta ratsa, sallamar Abdul Hakeem da Abba ta katse shirun cikin nuna tsantsar duniyanci Mama ta tashi da sauri tana fadin "Abba har kun karaso sannu da Zuwa" tana gyara Masa kujerar kusa da gadon.
Sai da ya zauna sannan ya amsa gaisuwar dasu Zilai da Asabe ke Masa suna jajanta masa, suka gaisa da Abdul Hakeem sannan suka fice daga dakin.
Mama ce ta Fara gaishe da Abban kafin Ammah ma ta gaishe shi, sannan Abdul Hakeem ya gaisu dasu Ammar Yana tambayar Mai jikin.
Zahar ce ta juyo tana fadin. "Abbana sannu da Zuwa, ina yini?".
"Yauwa uwata lafiya kalau Alhamdulillahi jiki yayi kyau".
"Eh Abba Daman Kai nake jira kazo kayi musu magana su sallameni mu tafi Nina warke na gaji da Asibitin tunda sunyi min hoton da gwajin da safe mun dawo mu karba bana son kwanan gurin Nan".
Ta fada tana hade rai.
"Eh Nima abinda ya taso ni Kenan maganar tafiyar taku gidan ne Dan yanzu haka daga office din doctor din muke sun bamu referral Zuwa Aminu Kano kamar yanda mijinki ya bukata yace da safe zaku tafi kiga gynecology doctor ayi bincke tunda ance kin jima kina fama da matsalar".
Kafin Ammah tayi magana Mama ta rigata.
"Wane irin Kano Kuma ana zaune lafiya, Wai ciwon har ya Kai haka ne idan Asibitin ake son canzawa aje Bauchi Mana Amma har kano akan ciwon mara kawai".
Dan murmushi Ammah tayi Bata ce komai ba.
Abban ne yace. "Yanzu kina nufin na Kira shi nace masa abinda ya fada baze yuwu ba Kenan ko Kuma Yaya kike son ayi?".
Shiru tayi Bata ce komai ba. Ammah ya kalla "kinyi Shiru ko kema hakan ne nufinki".
Kai ta girgaiza tana fadin "A'a tunda ga yanda ya fada ai shike da iko da matarsa ita da waye zasu tafi kanon?".
"Yace Sameer ne zezo sai zilai ta rakata haka dai ya fada min yanzu da Daren nan"
" To Allah ya kaimu yanzu tafiya zamuyi ke Nan?".
"Eh haka ne, ku kuje Abdul Hakeem ya mayar daku gida kafin ya dawo ruwan ya Kare sai na raka uwata gida" ya fada Yana murmushi.
Sororo Mama tayi Jin Abba da kansa ze maida su Zahra gida.
Badai ta tofa ba Amma a ranta taji ba dadi. Tun kafin Ammah ta dauko hand bag dinta Mama ta fice daga dakin.

******
MAHMUD
Bayan sun gama waya dasu Abba, Sameer ya Kira harta katse ba'a dauka ba sake Kiran yayi tana Fara ringing ta dauka.
"Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu".
Ya fada Yana Zama kusa da Fateeha tana shayar da jaririn su.
Daga can Mahmud ya amsa sallamar ya Dora da fadin "gobe in Allah ya kaimu ka shiga Azare ka taho da madam zataga doctor a Nan kanon na Kira doctor Haseena za'a kawo patient dina".
"Doctor Haseena fa! ita zata duba maka madam din?".
"Eh Mana ko da matsala ne?".
"A'a gani nayi kada taga anyi Mata cin fuska".
"Ba wani damuwa kawai,do what I said".
"Ok. In Sha Allah".
"Kada ka kaisu gidanka a kaisu gidan dake Nan DAWAKI ROAD su zauna har su Gama abinda zasuyi su koma".
"Kana ganin Bai musu girma ba kuwa? dana karkasara aka kaisu yafi kusa da Asibitin ma akan na Nasarawa GRA".
"A Nan nake son ta zauna kake maganar girma har wani babban gida ne ka barta ta saba da Zama a irinsu tun yanzu Kai dai kasan kuma abinda zaka fada Mata, a Kai musu duk abinda ya kamata sai dai na fada ba kayi komai kawai, ka fadawa momi ta Basu house maid daya su hadu da tata sai su ringa aikin tare, kayan sakawa dai nasan ba matsala ka Kira Rukayya ta duba abinda ya kamata sai taje ta sawo, ka Bata card din master bedroom na kasa ta sauka a nan.
"Shike Nan za'ayi yanda kace, amma baka tunanin taga wata shaida data danganceka a gidan?"
"Gaskiya bana tunanin akwai wata alama dake alamtani da gidan".
"Anyway, Allah ya kaimu goben, takwaranka na gaisheka".
"Oh sorry a shafa kansa sai nazo ganinsa, kaina ne ya dauki zafi".
Dan murmushi Sameer ya kashe Kiran Yana kallon Fateeha dake Masa kallon Karin bayani.
"Oga ne, Kinga yanda ya shiga damuwa kuwa nifa Banga abinda oga ya damu dashi ba irin yarinyar Nan idan Kika cire Iyayensa to ba na biyunta, ai ban Gama sarewa da lamarin sa ba saida ya nemi guri ya zauna a dakin kofar gida na almajirai duk da gurin bashi da wani aibu". Baki bude Fateeha ta bi Sameer da kallo "dakin Almajirai fa tace shi ogan da kansa? Tab lamarin Azimun ne, Allah ya bamu ko Rabin yanda tayi sa'ar sace zuciyar jarimi kamarsa Wanda Mata ko kallo basu isheshi ba".
Lakuce Mata kumatu yayi Yana fadin.
"Waya fada miki ba'a Miki so irin Wanda ake mata?" 'yar dariya tayi kawai tasan zance ne inji 'yan magana

*******

Lokacin da Ya Abdul Hakeem ya dawo ruwan ya qare har an cire Mata.
Cikin marairaita Zahra ta kalli Abban da Ya Abdul Hakeem.
"Dan Allah Abba ka tafi Dani gida wlh jiya nasha wahala gashi ba kowa a kusa dani kada na mutu Ni kadai a daki".
Saita saka Masa kuka.
Baki Ya Abdul Hakeem ya bude alamar mamaki.
"Ke! Amma wallahi wannan dai abun kunya ne ki wani kama kuka, kin manta yanzu ba da bane kema fa soon Zaki Zama uwa".
"Ungo Abdul uwata kake fadawa haka a gabana? Fita ka Kirawo zulaihatu ta tattara musu magungunan Nan sai mu tafi can din"..

Dariya yayi ya fice Yana mamakin Abba yanda yake nunawa Zahra soyayya fiye da kowa.
Ba zato ba tsammani Amma taga zilai ta shigo da Kaya a hannu Zahra na biye da ita.
"A'a ku kuma ya haka Naga Abba yace ze rakaki gida sai Kuma gaku a nan?"
Maganar Abban Ammah taji a bakin kofar parloun.
"Ni nace ta taho gida tunda batajin dadi Kuma gida su kadai, gashi Mai gidan nata yace goben zasu wuce kanon gara su kwana a Nan kawai tunda ke dai ba can zaki bita ba gara su tafi a gaban ki".
"Ok, ai ban sani ba nayi tunanin ko gaban kanta tayi nasanta da kulafucin gida ganin ta samu dama zata iya fakewa da haka ta taho kaima Abba kasan halinta"..
D'an Bata fuska tayi "Kai Ammah Dan Allah fa....."
"Kinga uwarta wuce ki kwanta ki huta Keda Baki da lafiya gida dai ai na danki ne, ba Mai hanaki shigowa Zan Kira shi Mahmud din na fada masa ".
"To Abba na gode".
Ta fada tana shigewa cikin Zilai ta bita da ledar magungunan ta.

Abban Bai jima ba ya fice saboda ya baro mutane masu son ganinsa da yawa a kofa.
A bakin kofar bedroom din Ammah suka had'u da zilai tana kokarin fitowa.
"Ku kuma sai koyo gudun hijira bakwa tsoron maganar mutane masu jiran k'iris su karawa miya gishiri?".
"Kayya Ammah idan za'a biyewa maganar mutane ai ko ruwa ruwa ka shiga sunce ka tada k'ura, Kuma ma waye ya ganta Kuma gobe da safe zamu wuce Kano idan Allah ya dawo damu ta wuce dakinta".

Zahra na shiga ta fada toilet Dan babu abinda take bukata sama da wanka du ji take jikinta na warin Asaibi.
Ta jima tana zubawa kanta ruwa kafin ta fito, sabuwar rigar barci ta dauko cikin kayan Ammah ta saka, ta dauko zumbuelen hijabin Ammah ta Fara sallah.
Ammah ce ta shigo dakin lokacin Zahra ta Idar da sallah Tana addu'a, sai da ta shafa sannan ta juyo tana fadin.
"Sannu da dawowa Ammah".
"A'a ke za'a yiwa sannu, ya jikin naki?".
"Da sauki sosai nifa da Abba ze fada Masa bama sai munje wani Kano ba, na warke tunda Daman na Saba duk wata inayi wannan ne kawai ya matsa min sosai".
"Kamar Yaya Abba ya fada Masa shi wa za'a fadawa?".
Ammah ta fada tana kallon zahrar, Baki ta turo tana fadin. "kema Ammah kin sani fa kowa nake nufi".
Dan murmushi tayi kawai.
"Ki Kira ki fada Masa bazakije ba Mana sai Abba ne ze Miki tafinta, tunda yace ga yanda yake so ai haka Zaki hakura kuje a duba ki tunda Naga alama Nan din be kwanta Masa ba, Kuma dazu naji kina maidawa Asabe har da Mama magana tona Hana kada na k'ara Jin makamanciyar magana irinta daga bakinki, ki bar mutum da halinsa kedai ki Zama me kauda Kai kawai ki Kuma rike Addu'a takobin mumuni ce kuma hassada ga Mai rabo taki ce".
"Kiyi hakuri Ammah in Sha Allah bazan Kara tankawa kowa ba,gani nayi basuji kunyar maganar a gabanki ba shi yasa na rama Nima".
Knockig da Sallamar Abdul Hakeem ce ta dakatar da abinda Ammah zata fada. Ammah ce ta amsa sallamar ta bashi uzinin shigowa.
Sannu da dare ya Kara yiwa Ammah sannan ya mikawa Zahra wayarsa dake Hannunsa da alama vedio call yakeyi, Yana fadar "gashi Mahmud zeyi magana dake".
A d'an kaikaice ta kalli gafen da Ammah take kafin ta Mika hannu ta karbi wayar.
Tana karba Ya Abdul Hakeem ya juya, Ammah tabi bayansa tana Masa maganar danyar Madarar da akace ya Aiko da ita da yamma lokacin tana Asibiti.
Saida Zahra ta tabbatar sun fice gaba daya daga dakin sannan ta dubi
Screen din wayar fuskarsa ta gani Yana kallon ta sai taga yayi wani zuru-zuru kamar Wanda yayi ciwo sai hancinsa ya Kara fitowa zuwat dashi hakensa ma ya qaru.
"A hankalin tayi masa sallama tana fadin "Ya M baka da lafiya ne Naga ka rame?".
Bushashshen lebensa ya da tura cikin Bakinsa ya lumshe idanunsa tun lokacin da aka fada Masa Bata da lafiya bai samu peace of mind ba sai yanzu daya ganta. Dan ita ke ciwon Amma shi keda zulumin da ramar Dan tun daga lokacin zuwa yanzu daya ganta Baya Jin yaci wani Abu na kirki a cikinsa.
A hankali ya bude idonsa ya Dora akan tata fuskar dake kallonsa, wani yarrrr taji da suka hada idon.
Cikin tsantsar kasala da jigata ya bude Bakinsa a hankali yace.
"My previous hankalina ya tashi, wallahi gani nakeyi kamar Zan rasaki, ya jikin naki? Kuma tun yaushe ciwon ya kamaki Baki fada min ba? sai Zayyan ne yayi min text Wai an wuce dake Asibiti, kinsan kuwa yanda hankalina ya tashi? Daman kina yin irin hakan ne ko yanzu ya Fara Miki?".
Dan walainiya tayi da idanunta tana fadin " Naji fa sauki Daman inayi kawai wannan ne yayi min tsanani sosai, amman tunda akayi min allurai da drip na warke, kaga ai ba sai munje Asibtin Malam din ba ko?". Wani kallon Baki da lissafi yayi Mata, shi Yana can ya kasa tsugun da ransa ita Kuma tana fada masa wani shirme.
"Zuwa can ba fashi, kuma da izininwa Kika taho gida jinya kin tambayeni Zaki zo gida?" Narai narai tayi da Ido abinda ke tsuma shi kenan yaji Yana neman sakin layi.
"Kai Yaya wallahi na fada maka Zanzo gurin Ammah Kuma ka amince kace nazo koka manta Ranar da zaka tafi?" Ta fada a shagwabe tana zubawa Masa sexy eyes dinta da suka Kara wani hasken wahala data Sha.
"Kawai dai kin min wayo tunda kin fini sanin takan duniya kin fini ilimin boko me zurfi shine zakiyi min education, haka ake cewa ko?".
Shiru tayi Masa.
"Kiyi magana Mana nifa bana son Shiru sai Naga kamar jikin ne"
"Nifa na fada maka na warke sai wani jikon Kuma".
Zaro Ido yayi Yana Mata kallon mamaki.
"Sai wani jikon kamar Yaya? Kenan har kina tunanin Zaki qara fuskantar wani ciwon bayan wannan?".
Kai ta gyada Masa alamar Eh.
"Pls talk ki bude Baki kiyi min bayani as how kike expecting Zaki Kara irin wannan ciwon?".
Sai da ta kauda kanta ta daina kallonsa sannan tace Masa.
"Nifa each and every month sai nayi wannan ciwon".
Ta fada tana Kara juyar da kai.
Cikin damuwa yace. "Pls juyo muyi magana Ina son sanin yanda ciwon yake ne Zan fadawa wani doctor Kinga ai saina San komai kafin na fada Masa yanayin ciwon"
Cikin Jin kunya da nauyinsa tace. "Nifa idan zanyi period ne nake yin ciwon cikin Baya sauki sai anyi min doclofenic injection yake denawa".
"Ok, to idan period din yazo Kuma shike nan baya Kara ciwon?".
Kai ta gyada masa. "Ki cire hijabin Naga yanda Kika rame tunda Nima daba ciwon nayi ba na rame lokaci daya dubi yanda nayi Rama? a lokaci aiki ma zanyi amma na kasa tabuka komai".
Rufe bakinta tayi cikin mamaki tace.
"Dan Allah ka daina haka ka manta a dakin Ammah fa nake idan ta shigo fa ta ganni a yanda nake me kake son na fada Mata?".
"To ya za'ayi Kenan Ranar data ganki da ciki Kuma a jikinki tunda kina kunyar taga muna video call ba hijabi kamar Wanda ta aikata alfasha Allah idan na dawo dole asan abinyi na Fara gajiya gaskiya sai ragaita nake kamar marayan da bashi da uwa, alhalin Allah ya Gama min sutura, koba haka ba?".
Shiru tayi Kamar ruwa ya cinyeta idan ta biye masa kunya ze Bata tunda taga alama Yana neman fitsare idanunsa.
Jin tayi Shiru yasa Shima ya bar zancen ya koma Kan batun tafiyar su Asibiti.
"Goben idan Allah ya kaimu magaji ya kaiki ki dauko wayarki tunda tana gida ki dauko Yan abun bukata tunda sai kun Gama komai kafin ku dawo wata Kila zaku dauki lokaci ba'a Gama gwaje-gwajen da zasuyi Miki ba, itama wannan Matar ta dauki abinda ya Kanata nata saiki fada Mata".
Sun Dade suna wayar har Ammah ta wuce part din Abba Basu Gama ba, sai kusan Sha daya ya hakura sukayi sallama.
Da safe tunda wuri Ammah ta saka magaji yakai Zilai gidan ta karkashe kayan electronics, ta cire duk abinda ake ganin ze iya lalacewa ta Mika gidan maman junior bisa Umarnin Ammah.
Karfe bakwai da rabi Mai kyau su zilan sun koma gidan Ammah da kayan Zahra a jaka set biyar da sauran tarkace na bukatar yau da Kullum.
Sam Mama Bata da labarin kwanan zahrar a gidan Sai da zilai ta shigo da Kaya a hannu magaji Kuma karamar luggage a hannunsa da sauri ta aje bowl din dake hannunta ta nufo Zilai tana fadin "lafiya kuwa daga Ina haka zilai?"
Gaishe ta zilan tayi tana fadin "munje mun daukowa Zahra kayan sawarta tunda Bata koma gidan ba Nan muka kwana daga asibitin gida mukayo". Ikon Allah wallahi ban sani ba, Babu Wanda ya fada min tun daren, Bari na shiga Naga jikin nata".
Suka nufi part din Ammah.

✨✨✨

AUREN HUCE HAUSHI

✨✨✨

MAMAN FATEEMAH.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.