Auren Huce Haushi Book 1 Complete Hausa Novels By Maman Fatima
Reading file: AUREN HUCE HAUSHI BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN FATIMA.txt
Chapter 32 of 34
Page 42.
_______Abu kamar Wasa har kusan karfe taran dare ba zahra ba labarinta, iya Rahane mommy ta Kira tana tambayarta kosu Rukayya sun dawo? Dan bazata fada ba direct tace ana neman zahrar hakan dabara ce ta tambaya a fakaice.
Amsar data Bata ita ta Kara tadawa kowa hankali cewa tayi "Basu dawo ba tun fitar safe da sukayi ga zulai ma duk ta shiga damuwa tace tun yamma Ammarta ke Kiran wayar zilan tace wayar zahara'un Bata shiga".
"Yanzu ya za'ayi kenan?"
Rukayya ta tambaya.
"Ni damuwa ta Daya kada ta fada mugun hannu Dan ma dai ba lallai ansan matar waye ba Amma yau abin tsoro ce kiransa zanyi kawai na fada Masa halin da ake ciki ko yasan wasu 'yan uwansu a nan kanon, tunda barin Kashi a ciki baya maganin yunwa gara ya fada kawai asan Yanda za'ayi tun guri be kure ba.
Number dinsa yayi ta try Amma amsar Daya ce a rufe take.
Da kyar ya mayar dasu mommy gida har Rukayya a gidansu ta sauka, to ta koma tacewa baiwar Allah da sukazo tare zahrar ta Bata ko me?"
Duk wani lissafi ya gama suncewa Sameer, duk wannan Abu be tashi faruwa ba Saida sukazo gidan kakarsa, ita kanta Hajiyar makwararin tashi Dan kukanta tana mitar yarinyar Nan Bata kyauta Mata ba ta rasa a inda zatayi irin wannan shegantakar sai a gidanta.
Jiki ba kwari Sameer ya shiga gidansa, sau Daya Fateeha ta kalleshi ta dauke Kai ta cika fam da fushi tun safe Daya fice Bata Kara sakashi a idanunta ba, ta kirawo shi ya Kai sau biyar sai dai yace Mata gashi Nan Amma bezo ba sai yanzu wurin Sha dayan dare.
A kusa da ita ya zauna ta kauda Kai, hannu yasa ya dauki yaron a Kan cinyarta, yasa hannu Daya ya tallabota ta hada da babyn ya rungumesu, Jin ajiyar zuciyar da yake saukewa a jajjere yasa Fateeha ta gane da matsala.
"Wai menene?"
Ta fada cikin damuwa.
"Bari kawai wlh hankalina a tashe yake, tun bayan Azzahar Zahra ta fice daga gidan Hajiyar makwarari bamu San inda ta nufa ba, duk inda muke tunanin zataje munje Bata nan".
Itama mantawa tayi da fushin da takeyi dashi ta Fara sallallami "Yanzu Ina ta tafi? Kadafa wani Abu ya sameta kasan mutane yanzu gaskiyar su kadan ce".
Dafe kansa da yake Sara Masa yayi "Bana tunanin haka gaskiya da Kanta ta fita ta tafi kawai dai an Bata Mata Rai ne ban Kuma yi tunanin abin yayi Mata zafi haka ba da bazan barta a gidan Hajiyar ba, amfani tayi da masu kawo lefen mujahida ana can gurin karbar lefe ita Kuma ta fice daga gidan Dan akwai Wanda ya fada min Yanda ta fito nasan da niyya ta fice abunta".
Zuru Fateeha tayi tana sauraren mijinta.
"Ka Kira ka fada masa?"
Kai ya girgiza Yana fadin na kasa samunsa nafi one hour Ina nemansa ban same shi ba".
*** *** *** ***
Karfe Tara su Umman sajida suka shigo gidan lokacin Zahra na parlour suna hira da Mama Hauwa, turus Maman tayi ganin zahra ko rantsuwa tayi Babu kaffara, wannan ba zuwan arziki bane amma sai ta share tana fadin "wa nake gani haka?"
Dariya Zahra tayi tana fadin "Umman mu sannunku da hanya".
"Yauwa sannu,aike za'a yiwa sannu kin sha doguwar tafiya".
Shiru zahrar tayi batace komai ba, kannen Sajidar ne suka Fara gaisheta suna fadin "Aunty kin rigamu zuwa munata cewa idan Ya Abba ze Kai Miki sakonki da Baffan Rimi ya bada a Kai Miki zamu bishi sai gashi Kuma kinzo"
Karamar kanwarsu ta janyo tana fadin "ai zakuje ko mutuniyar tunda anyi min Alkawarin zuwan".
"Eh zamuzo Aunty zahra".
Nusaiba ta fada suna Zama kusa da zahrar, yayin da Maman su ta wuce bedroom dinta tana cike da tunani barkatai a zuciyar ta.
Tana shiga jakar hannunta ta zuge ta Ciro wayar ta, Ammah ta Kira Dan bazata Zama uwar banza ba da alama gudowa yarinyar Nan tayi.
Lokacin da Kiran ya shigowa Ammah tana duba wasu kaya da Hajiya kaltume ta Aiko Mata dasu ne.
Ganin Umman sajida ne yasa ta aje kayan ta dauki wayar tare da sallama.
"Wa'alaiki Salam warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu".
"Hajiya ya gida ya wajen Amare? Ina ta son na Kira mu gaisa Allah Bai nufa ba sai yau, itama zahrar mun kwana biyu bamu gaisa ba".
"Wallahi kowa lafiya, Amare Kuma suna nan kusa daku Bata jin dadi ne mijin ya matsa suzo Nan Kano a dubata ni tun safe da muka gaisa da wayar zilai ban Kara samunta ba, na Kirawo zilan ma tace min har yanzu Basu dawo ba duk ta tada hankalin ta, nace ita da ba ita kadai ta fita ba tare suke da amininsa da kanwarsa, Kinga duk inda suke ai suna tare".
Shiru Maman tayi kenan hasashenta ya kusa Zama gaskiya Kenan.
"Hajiya ga zahrar a gidan nan,yanzu muka dawo daga Rimi Sai na tarar da ita Ina ganinta nasan ba lafiya ba Ashe garin sukazo ta kawo min ziyara".
Jim Ammah tayi tana jinjina lamarin.
"Anya kuwa ki dai saka Mata Ido zuwa safe kome ke nan sai ki fada min idan anzo daukarta to da sanin mijin tazo idan Kuma tace zata tafi ki hanata ki fada min na gode kwarai Allah yayi Mana jagora ya Raya Mana zuri'a".
"Allahumma Amin". Sukayi sallama.
Zuciyar Ammah sai bugawa takeyi a hankali ta furta "meke Nan Kuma? Ni Asma'u Allah ka taimaki 'yar marainiyar Allah, matsaloli daga an toshe wannan sai waccen ta bulle Allah yayi Mana maganin wannan matsaloli yanzu kuma ko menene damuwar datasa ta tsallake tabar inda suke gashi ta Kama wayar ta rufe Dan ma kada a San inda take,ai kuwa zamu gauraya bazan dauki shashanci ba".
Ta hada duk kayan ta zuba a ledar da aka kawosu ta fice daga dakin ta nufi dakin Abban Yara tunda ita keda girki.
Saida Umman sajida tayi wanka tayi sallah sannan ta fito har lokacin suna falon da yaran direct dining ta nufa taci abinci sannan ta dawo falon.
Gaisheta zahra ta Karayi tana tambayar ya Mai jikin,
Dasu Baffa.
Sun dauki lokaci suna hira kafin Ummar tace "Wai daga Ina kikazo ne daga can Azaren ne ko Kuma kinzo nan garin ne?"
Shiru zahrar tayi kafin tace "ganin likita nazo akan wannan ciwon marar da bakeyi duk wata".
"Ikon Allah kuma ke kadai Kika taho ganin likitan kamar marar gata".
"A'a bani kadai nazo ba tare da Aunty Zilai Mai aikin Ammah mukazo tana can a Nasarawa G.R.A".
"Ok, to mryasa baku taho tare ba Nan din".
Shiru tayi Bata ce komai ba, ganin da Yara yasa itama ummar tabar zancen.
Kafin kowa ya tashi Zahra ta tashi tana fadin "Umma Bari naje ba kwanta barci nakeji"
"To Allah ya tashemu lafiya.
Basu Dade ba Suma suka shige daki Daman duk sun gaji.
Lokacin da Ammah ta shiga dakin Abban samun Mama tayi kane -kane tana ta zuba zance da kudi a hannunta masu Dan yawa da gani a gurin Abban ta Karba, cikin alamun rashin gaskiya mamar ta Fara fadin. "Aina leka parlourn ki naji Shiru nayi zaton kina Nan wallahi Ashe Baki shigo ba"
Fuska ba annuri Ammah tace. "Eh ban shigo ba idan kin gama na dawo ta juya har Takai kofar ficewa Abban yayi gyaran murya Yana fadin "dawo ki zauna Ina Kuma Zaki ita ta tashi ta tafi tunda ta gama abinda ya kawo ta"
Jiki ba kwari Mama ta tashi tana fadin "ai Kam na Gama Allah ya tashemu lafiya nagode Allah ya Kara arziki".
Ta nufi inda Ammah ke tsaye tana fadin "mu kwana lafiya ki tayani yiwa Abban yara godiyar abin arzikin Daya bawa Najjahi na kudin registration".
"Masha Allah! An gode Allah ya bada sa'a".
Ta fada fuskar ta Babu walwala ko alama, da gaske ta kule Abun Yana so ya Zama rainin hankali tayi noticing dinta duk ranar girkinta sai ta dunga Karakaina a part din Abban Amma idan tasan wata ai Bata San wata ba.
Dawowa tayi ta zauna kusa dashi "meya Bata Miki Rai ne Kika juya Zaki bar dakin?"
"Ba komai".
Ta Bashi amsar in short.
Haka Nan yabar zancen badan ya gamsu da abinda ya fada ba.
"Neman izinika na shigo zanje Kano gobe in Sha Allah"..
Saida ya Kare Mata kallo tsab sannan yace. "me akeyi a kanon da zakije?"
Kai ta girgiza ba komai zanje barka ne na yaron nan Sameer ranar da yazo daukar su Zahra yake fadawa magaji anyi Masa haihuwa an samu takwaran mijin Zahra".
"Kai Masha Allah, ai ban sani ba da nayi Masa barka ranar da yazo".
Tashi tayi zata fice Abban ya mayar da ita "Wai me yake faruwa ne Naga ranki a bace tun shigowar ki".
"Ba komai zanje na dawo ne yanzu in Sha Allah".
Ta Mike ta nufi kifar ficewa, haka Nan yayi Shiru badan ya yarda da ba yasan da abinda yake damunta taqi fada Masa ne kawai".
Ammah na shiga part dinta ta Kirawo Abdul Hakeem, lokacin Yana kofar masallaci tare da Habib.
A parlour ya samu Ammar ta zuba tagumi.
Saida yayi sallama biyu sannan taji.
"Wa'alaika Salam".
Ta fada tana kallon Abdul Hakeem din, kusa da ita ya zauna Yana fadin "lafiya kuwa Ammah Ina sallama bakya jina?"
Ajiyar zuciya ta sauke tana fadin "yanzu ba dadewa Umman Sajida ta kirani waiga zahra taje Mata zata kwana a can Kuma ita kadai ba tare da zilai ba, na Kira zilan tace min tun fitar safe Basu dawo ba har dazun, ka Kira Sameer kaji shin yasan da tafiyar ko Kuma wani Abu ya faru tayi musu yqji nasan halin kayana zatayi abinda yafi haka ma in dai zahra ce, Dan haka ka kwana da Shirin Kano sakko zamuyi ko Abban KU ban fada Masa wannan maganar ba ina tsoron ta fito duk da nasan ba lallai ta fito din ba amma sha'anin mace da miji sai Allah"
"Allah ya rufa asiri".
Abdul Hakeem ya fada Yana Kiran Sameer duk da lokacin ya ja Sha Daya ta gota.
Ringing Daya saneer ya daga kafin Abdul Hakeem ya Fara magana Sameer ya rigashi Dan ko sallama Babu ya Fara fadin "Abdul Hakeem zahrar tazo Nan ne?.
"Easy my man! Tana Nan Kanon a Janbulu gidansu Sajida, yanzu Umman su sajidar ta Kira Ammah ta fada Mata saboda hankalin ta be kwanta da ganin zahrar ba duka yaushe akayi Abu da zata wani zo yawon ziyara tasan da wata a kasa, shine ta Kira zilai ta fada Mata tun fitar safe baku dawo ba".
Ajiyar zuciya ya sauke, sai Yanzu ya samu nutsuwa dan Yanzu suka gama wayar da mommy akan ko akwai wani cigaba? Yace Mata Babu Kuma tun lokacin da abun ya faru yake ta kokarin ya Sami Mahmud Abun ya faskara.
"Na gode kwarai Abdul wallahi muna nan hankalin mu a tashe tun bayan Azzahar muke Abu Daya, Dan Allah kayi min godiya gurin Ammah, kace Kuma tayi hakuri ba sai tazo ba Dan Allah ga mommy ta Isa tayi komai ka fada Mata laifi akayi mata amma in Sha Allah hakan baze Kara faruwa ba wannan ma tsautsayi ne".
Kai kawai Ammar ta gyadawa Abdul Hakeem ya gane me take nufi tunda handsfree ya saka wayar".
"To ba damuwa tace ayi maka godiya da kwaramniya"
"Ba komai yiwa Kaine ka turo min da address din gidan Yanzu na gode".
Sukayi sallama ta kashe Kiran Yana Maida hankalinsa a Kan Ammah.
"Ammah lokaci yayi daya kamata a zauna da Mahmud asan who's he? Aure ba Abun Wasa bane asan asalinsa Kinga muna tare sosai wallahi be taba fada min asalinsa ba kawai dai nasan he's educated fiye da tunanin mu badai ya nunwa ne kawai anyway kome Kenan dai kiyi abinda ya kamata kawai".
*** **** ***
Suna Gama waya Sameer ya lalubo Number Rukayya tana dauka yace ki fadawa mommy gani Nan zamuje mu taho da Zahra tana janbulo gidansu friend dinta".
Bai jira tayi abinda zata fada ba ya katse Kiran ya saka jallabiya ya dauki key din motar yayi waje.
A kofar parlour ya tarar da Rukayya da Mommy.
Fitowa yayi yana fadawa mommy Yanda sukayi da Abdul Hakeem da Ammah.
"Dan Allah ki zauna mommy muje da ya Sameer kawai ana ganin mu dake za'a San ba lafiya ba Kinga ai itama zato takeyi kawai muce Mata ya Mahmud ne ya dawo yace muzo mu taho da ita tinda da saura lokaci".
"To shigo mu tafi tsari mistress".
Saida suka dauki titin rijiyar zakin sannan Sameer ya mikawa Rukayya wayar da address din da aka turo Yana fadin " duba ki gani ko kinsan laying kune masu yawo lungu da sako na garin nan".
Dubawa tayi tana fadin " Nasan gurin layin gidan su saliha sani Musa ne tare mukayi Excel da ita".
Cikin ikon Allah suna tsayawa a kofar gate din motar ya Abba ta shigo shida Abie dinsu sun dawo daga kwangwalam bodar NIGER inda sukaje gaisuwar mahaifar amininsa data rasu jiya, sun biya ta kazaure gurin wani abokin aikinsa daya kwanta a Asibiti Shima a Nan sukayi dare.
Ganin mota a kofar gidan yasa Abie yace Abba ya tsaya yaje yaji ko lafiya Yana fita Mai gadi ma ya fito Yana ganin Abba ya karasa gurin da sauri, fitowa Sameer yayi ya tarbesu Yana Mika musu hannu sukayi musabaha Yana fadin "Ayi hakuri munzo cikin dare ba sanarwa,Daman munzo mu tafi da zahra ne tun Rana tazo Bata Fadi zata kwana ba sai Yanzu mijinta ya dawo gashi ba waya a hannunta, ganin da sauran daren yasa muka biyo samunta".
,"Ok. Ba damuwa muma Yanzu shigowar kenan munje unguwa tare muke da Abie".
"To mu karasa Mana na gaishe shi ya juya yabi bayansu suka nufi gurin Abie din, Rukayya gani tayi kamar akwai rashin kyautawa ace tana kallo aje a gaishe da babban mutum tana zaune sai kawai ta fito ta rufa musu baya.
Cikin girmamawa Sameer ya gaishe da Abie din sai Jin muryar Rukayya sukayi daga baya tana gaishe da Abie din, hankalin Ya Abba biyu ya kasu ga wata murya data fizgeshi lokaci Daya ga Kuma bayanin da yake yiwa Abie.
""Ba wani Abu Bari a Kirawo Umman tasu saita fada Mata ta fito wannan ai shashanci ne ya za'a bar yarinya ta nemi gurin kwana da mijinta da komai".
Sameer ne ya Dan shafa Kai.
"Ayi hakuri Abie mijin ne baya Nan sai yanzu ba dadewa ya shigo kasar".
Mazaunin direba Abban ya koma suka nufi ciki tunda Daman Mai gadi ya bude gate Yana jiran su shigo.
A waya Abie ya Kira Umma har lokacin idanunta biyu da wuya tayi barci matukar tasan mijinta baya Nan da sauri ta dauki wayar tana Masa sannu da zuwa.
"Yauwa ya amsa a takaice Yana fadin. "ki taso bakuwar da kikayi a gidan mijinta ya dawo gasu Nan a gate". Ya kashe Yana nufar part dinsa.
Shiru tayi waye ya fada masa da bakuwar a gidan jiki ba kwari ta nufi dakin sajida, barci ta Samu tanayi sadidan kamar Nan duniya Bata da damuwa Kota sisi dakin ta shigo tazo bakin gadon ta tsaya tana Kiran sunan ta a hankali, tana fadin "tashi ki kimtsa ki fito ga Mai gidanki can zaku tafi gida". Idanun tadan zaro tana fadin "wallahi bazani ba Umma kice musu bana nan
sai hawaye"..
AUREN HUCE HAUSHI.
MAMAN FATEEMAH.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.