Trending Hausa Novels

Auren Huce Haushi Book 1 Complete Hausa Novels By Maman Fatima

Reading file: AUREN HUCE HAUSHI BOOK COMPLETE DOCUMENT BY MAMAN FATIMA.txt

Chapter 23 of 34

Page 34

AssalamuAlaikum warahamatullahita'ala wabarakatuhu.
'yan uwa muna barar addu'oin ku bisa rashin abokiyar aiki da mukayi ECCD co-ordinator ta KIRIKASAMMA LOCAL GOVERNMENT JIGAWA STATE muna rokon Allah s.w.a ya jikaanta yayi Mata Rahama yasa Aljanna makomarta tare da Iyayen mu da sauran Al'ummar musulmi Baki daya ya Raya abinda ta Bari ya Albarkaci bayanta.

______ Misalin karfe uku da rabi jirgin sun Mahmud ya sauka a DUBAI INTERNATIONAL AIRPORT (DXB) cikin amincin Allah, yana cikin kusan rukunin mutanen karshe a fitowa, yana sanye da suit ash colour na kamfanin Armani hannunsa sanye da ogogo Rolex, baya tare da komai sai jakar laptop dinsa a hankali yake gangarowa cikin takunsa na cikakken namiji me ji da lafiya da karfi, direct gurin da taxin airport suke ya nufa, baya bukatar asan yazo garin so yake ya tantance wata jimurda da aka hada, taxin ya shiga saida sukayi balance a titi sannan ya fadawa direban ya kaishi JW moritte marquis hotel cikin harshen larabci,sunyi tafiya mai tsayi kafin su karaso hotel din, bashi da matsalar kama daki dan tun yana china yayi booking din dakin ta online, katin dakin kawai ya karba ya koma waje yin 'yan uzurirrika daga baya ya nufi ciki, wanka ya fara kafin yayi order abinci, sai da ya gama komai sannan ya kwanta dan yayi matukar gajiya, yaso kwarai ya kira 'yar gidansa amma yana son su tattauna sosai, sai yanzu yake jin haushin wani ra'ayin nasa badan haka da suna tare da ita suna hutawarsu, yanzu kadaicin rashinta da be dameshi ba, wlh da beyi alkawari ba da visa zesa ayi mata ta sameshi a nan saboda hotel din yayi masa, yana daga cikin lattest hotels na duniya be taba sauka a wani hotel ba a dubai sai BURJ AL ARAB JUMAEIRAH dakinsa parmanent ne duk mai hulda dashi a dubai nan suka sani, duk da yana da gidaje a kasar shi be fiye son yakai abokanin bussiness dinsa gida ba. Wannan shigar ta sirri ce shi yasa ya canza sheka baya son asan ya shigo kasar mamaya sake son yakai wasu gurare, yanda har ya gama abinda yake yabar kasar wani be sani ba duk da abune mawuyaci hakan ta faru.
Barcinsa yasha sosai dan har akayi sallar magariba be sani ba, lokacin daya tashi ana gab da kiran sallar insha'i, a gurguje yayi wanka ya zura sabuwar jallabiyar daya saya cikin kayansa a kasar, a cikin dakin yayi sallar magariba ya fito yabi lifter zuwa masallaci,koda suka idar da sallah be dawo daki ba a nan harabar hotel din ya Zauna da gaske yanayin gurin ya burge shi sosai, coffee yayi order ba'a jima ba wata matashiyar balarabiyar yarinya ta kawo masa coffeen sai yaga kamar 'yar gidansa, nan da nan yaji duk rintsi ita yake muradin gani number dinta ya lalubo ya kira duk ba baya son kira direct yafi son ta Whatsapp.
Suna zaune a parlour ita da zilai tana Shan mutuniyar tata farm fresh, Kira ya shigo a wayarta dake kusa da ita, tayi mamakin ganin code din Dubai har sai da ta kusa katsewa sannan ta dauka, batayi magana ba Shima baice komai ba, ganin shirun yayi yawa yasa zilan Fadin "naji kinyi shiru koba Kira bane".
Karamin tsaki Zahra tayi "wlh na daga amma naji shiru inaga ko wrong number ne dan code din na Dubai ne ni kuwa waye ze kirani daga Dubai da dai Aunty Nawwara Bata saudiyya da saina dauka ko sunje ne da mijinta tunda business man ne, Bari na kashe wata kilama ba'asan an Kira ba"..
Kafin ta dauke wayar daga kunnen ta taji yayi magana cikin husky voice kada ki kashe min waya, ki bude data zamuyi magana". kit ya kashe Kiran wayar tabi da kallo a zuciyar ta tana Fadin "ikon Allah shine Kuma a Dubai ya illahiy, to Wai wannan Dan talikin waye shi lamarin fa Yana neman Zama abin tsoro fa, yace Yana yiwa kungiyoyin waje aiki ita Kuma a gefe guda wani Abu yake yi irin na Mai bada umarni Kuma bataga yanayi gaban kowa ba sai ita, kamar Ranar da taji yana Kiran zayyan da umarnin daya Bashi akan lallai ya sameshi da safe Kuma Bai karya Umarnin ba"
Wayar ta kalla tana mikiwa zuwa bedroom dinta Saida ta shiga ta duba data idan Babu ta saka tunda Sam Bata taba saka data ba tunda ta Fara amfani da wayar datar data gani tayi bala'in Bata mamaki 4.5 BT ta gani sub din shekara daya ne.
Cikin sofa ta zauna Tana juya wayar Bata bude datar ba, wani Kiran ne ya sake shigowa still dai nashi ne, dagawa tayi tana fadin Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu".
"Wa'alaiki Salam warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu, meya hanaki bude datar danace a bude?"
Shiru tayi ta kasa magana,.
"Wai ko sai nayi ramuwar sayen bakin da banyi bane ake min jan aji irin haka. Dan Allah kimin magana kona samu nutsuwa wlh ji nakeyi Kamar na gudo tun ba'a gama ba duk kin mamaye ko Ina na kasa komai sai tunanin ki, Ni danasanin zuwan ma nakeyi gashi sun rarraba mu wasu suna London mu kuma suka kawo mu hadaddiyar daular larabawa, shine nace Bari na kira na fada Miki Koda abinda kike bukata na taho Miki dashi tunda da kudinki a gurina"
"Kudina kuma? Name nene kuma yaushe na baka".
"Bake Kika bani ba ke aka bawa na manta na Baki Sai a Nan na tuna danaga Kaya irin naku na 'yan Mata".
Ya fada Yana dariya.
"Wai 'yan Mata".
Ta fada tana Dan turo Baki irin bataji dadin Nan ba.
"Au ashefa an wuce wannan stage din ko?"
Ya fada da alamun zolaya.
"Wato kinki bude data sai kin cinye min 'yan canjin da aka saka Mana kinsan dai ni ba iya saka Kati zanyi a kasar Nan ba, pls Dan Allah ki bude datar na ganki kona samu nutsuwa nayi aikin daya kawoni, naso ace kina gefena a wannan gurin Kinga dakina kuwa? da Hali gareni anan zamuyi honey moon irin Wanda naji su Habib suna fada idan ana hira ko Zaki biya ki taho ki sameni?"
Ido ta ware kamar Yana kallonta.
"Na biyoka nayi maka menene?"
"Kiyi min abinda mace take yiwa mijinta ai kin gane?".
"Ya Salam haba Ya Mahmud menene haka kaifa yayana ne".
Wata dariya ce ta kubce Masa "A yaushe na zama Yayanki? Ki gyara zancen niba Yayanki bane, haka kawai ki haramta min abinda Allah ya halasta min idan Zaki Ware ki Dan ina dawowa labarin ze canza salo gara mu fuskanci juna ki tausaya min Kinga Sameer fa ya Zama Daddy madam dinsa ta haihu sunyi min takwara,ai gara muma mu zage dantse ko?"
Dokin haihuwar da aka fada Mata ita ta Hana ta gane inda nasa zancen ya dosa, cikin nuna farin ciki tace "Dan Allah da gaske yaushe Fateehar ta haihu? Masha Allah! Allah ya Raya kace mu sai Kano ko Yaya?".
"Allah bakinki ya kiyayi fada min yayan Nan tsabar kinibibi kawai yau Kika tashi dashi Wai wani Yaya kamar a kauye, kibar 'yan garinmu su Fadi Amma Banda ke wato Ni da yake ba Dan bokon kirki bane ba baza'ace min sweetie ba ko irin su my love ko Dear, saboda almajirin soro ne ni ko?"
"A'a wlh ni ban fada ba, kawai dai Naga abokin Ya Abdul Hakeem ne kai ai kaima yayan ne".
"To anki wayon, Kuma da kike cewa Zaki Kano ganin yaro keda wa zakuje kuma waye ze kaiki Kuma kice Mata wacece ke".

"Address zata turo min Mana, Kuma maganar kaiwa sai Malam Bala direba kaimu nida mujiba wuni daya dai, Kuma nace Mata matar yaron mijinta ce ko ba haka ba?
"Yayi Kam Amma saina dawo ki rakani muje tare anfi saurin ganeki ga kafarki ga tawa, kice na sawo Miki kayan baby na zuwa barka kenan? ko kema a hado Miki kayan naki babyn? tunda da karfina Zan dawo wata kilan ni double shoot ma zanyi tunda Nima Dan biyu ne Ina da twins sister Aishat".
"Twins sister da gaske?"
"Kin taba ganin nayi Miki karya? wlh mu biyu Ammin mu ta haifa first born dinta, mun B'ata ne da ita shiyasa bakisanta ba. Amma nan gaba zaki santa ne Amma fa Zaki Sha surutu Dan sister Aishat parrot ce".
"Amman laifin me tayi maka da zafi haka? Mu namu twins din basa doguwar batawa gaskiya gashi kaima Ammin irin na Ammah tayi mace da namiji".
"Ki Bari kawai labarin da tsawo sai na dawo ai nace Zaki San duk labarina kaf ba abinda Zan boye Miki tunda kin sarkafo min zuciya tun kina free matured dinki Kika Hana duniyata zaman lfy,da farko na dauki irin mutum ya burge ka ne Ashe diban Karan mahaukaciya Kikayi da gudan tsokar kirjina".
Dariya maganarsa ta bata.
"Au dariya ma kike min ko? bayani zakiyi da yarenki, yanda nayi ta fama da garari saina fanshe kayana tas idan Zaki shirya ki shirya".
Cuno Baki tayi kamar tana gabansa ta Fara turza kafa tana fadin "Ni yaushe kaga Ina maka dariya kawai dai... ni banyi maka dariya ba kaifa yayana ne koka manta my big bro....." Ta wani ja cikin salon da ita kanta Bata San tayi ba.
"Ya salam" ya fada a hankali Dan yanda tayi magana har cikin bargonsa.
"Kinaso ki karya min budget ko?"
Ya jefa Mata tambayar.
"Wane irin budget Zan karya maka kana Nan Ina Nan".
"Idan kina min irin haka ai sai kisa na saki layin Dana hau na tattaro ya nawa ya nawa ko komo gida ko ba'a gama ba".

"To me nayi daga magana tom shike Nan sai anjima".
"Wlh Kika kashe min Kira sai kinzo Dubai ko a kafa ne kuma saina yi Miki abinda bazaki manta ba Dan tarihi me kyau Zan kafa Miki ki kashe ki gani, muna hira kina bani nutsuwa Zaki gudu nida ake yashewa Yan canjina Baki tausaya min ba shine Zaki tsere ki barni da Mata masu farauta ta ko? Yanzu haka guda uku tun dazu suke shawagi a gabana suna tunanin irin nasu ne Dan hannu".
Gyara Zama Zahra tayi kirjinta ba dukan tara tara bama uku uku ba.
"Mata kace ko me?"
"Eh Mata Mana bake kina min rowar ganin halalina ba to gashi Nan free sai Wanda yayi maka ka zabi son ranka, ba nace ki bude data na kalli kayana ba Amma kika Kiya Kinga kuwa yanzu saina duba na darje na zaba ta rage min dare, koya kikace my previous?"
Ya Dana Mata kiss ta cikin wayar ya kashe abarsa.
Yana fadin gobe ma idan bace ki bude datar ki qiya, saina kowa Miki kishina ba gaske kafin na kaiki Ina zakiyi da hujja Amma ki shiga yanzu ai Africa ce da sauran gyara.

AUREN HUCE HAUSHI

MAMAN FATEEMAH

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.