Complete Hausa Novels

Matar Yaro Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Matar_Yaro_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 23 of 24

Page (44/45)

"Baki ta tunxuro gaba tana
kun kuni kayan jikin ta tacire shiga toilet. Domin ta watsa ruwa" Da ido AUNTY JIDDAH" tabita tana mamakin hali irinna UMMU" yarin'ya sai taurin kai" tunani kala? AUNTY JIDDAH" keyi. UMMU da tafito daga toilet tana tsane gashin kanta ta dubi" Aunty jiddah sannan tace Aunty tunanin mekikeyi haka?" Babu komai ta bata amsa A'gajerance" tare da tashi ta fita daga dakin bata jima ba saigata da kaskon tiraran wuta" ta ajiye wasu turarur ruka taxuba acikin gar"washin ta dubi UMMU da haryanxu' take tsane gashin kanta. Tace kixo ki tsuguna anan.

Ido tawaro ganin Uban garwashin dake cin kaskon sannan tace AUNTY" Ai wannan saiya konani. Wata uwar harara AUNTY" JIDDAH"ta dallah mata kana tace Idanma kasheki xatayi saide ta kasheki karewar konewa" tana kuka tana komai ta tsu guna gaban kaskon bata barta ta tashi ba harseda tiraran ya dena hayaki"Aranar saida tai mata Kusan Ukku sannan ta kyaleta" Amma fa dik inda ta gitta saikaji tashin kamahi na tashi" na innah niha"

Xaune suke a'farlo sunyi jigum jigum ko wanne da abinda yake sakawa aranshi"Jamila ce ta dago ta dubi yanda UBAIDA" tarame ta lalace sai kasusuwa" tadena cin abinci" kwata? in kuwa kaga UBAIDA" takai abinci bakinta to jitayi xata gan gara" ita kanta JAMILA"daureya wa kawai take Amma abin ya Isheta" tarasa inaxata sa kanta" tsoranta daya kar UBAIDA" ta kamu da wata cutar sanadin soyayyar wan can banxan yaron da ba kaunarshi take"kawai dan UBAIDA" ta dage shi takeso shiyasa ta boye ki yayyar da takemai.

Xama ta gyara sannan tace UBAIDA kidenasa damuwa da yawa aranki ina jin tsoro karki janyo kanki wani ciwon kinga ai xance yabaci tunda ba kida lpy bare munemi wata hanyar" dan haka kidena damuwa ki dinga cin abinci kafin muga abin hali yayi" dik da nasan da A kwai wahala Amma kidaure" kinji ta karashe maganar da sigar lallshi.

Kallan ta UBAIDA tayi tace yanxu mama kina nufin narasa YUSIF kenan? Waiyoo Allah nashiga uku na. Ni UBAIDA" A gigice JAMILA" ta rukota tana lallashin ta tare da yimata Alkawarin Auran YUSIF kota halinkaka"da ira iran wa innan kalaman JAMILA ta shawo kan yar ta ta harta ci abinci" Amma dik da haka bata saki jikinta ba kamar dah.

"Yau juma a kuma yaune ranar kamu" tinda safe Aunty jiddah take kula da UMMU"musamman wajan gyran jiki da kwalliya" misalin karfe {{5:00}} dai dai na yamma yan uwa da abokan arxiki sun cika gidan kowa kagani fuskar sa dauke da Annuri"ban garan amarya kuwa Sai fama ake da ita kan ta tshi ta shirya ita kadai akejira. Tana jinsu Amma tai mirsisi sai sharar hawaye takeyi da suka gaji da lallashin ta sai suka sanar da mommy abinda yake faruwa" Ran mommy inyayi dubu yabaci"

hardakin mommy tashiga tacewa mutanan dake dakin su dan basu guri xasuyi magana.saida kowa yafita mommy tamai da fuskar ta tashanu ta dubi UMMU da kanta ke kasa"sai shashshekar kuka take. Saida tayi taku biyu sannan ta fara magana Da cewa UMMU idan harnina haifeki na shayar dake na goyaki abayana to ina mai baki UMAR NI da dik abinda ya shafeni komeyeshi karki sake kallansa ama tsayin kunada dan gantaka karki kuma shiga Cikin xuriyata kije na.

Bata karasa abinda takeson fade ba UMMU tayi kukan kura ta dire agaban mommy tare da dur kusawa a gabanta" tace dan allah mommy karki furta wannan kalma agareni karkiyimin furicin da xai tarwa tsa rayuwata gaba daya" narokeki da kiji kaina kiya femin saita kuma fashe da kuka mai tsuma xuciya tare da kan kame kafafun mommy.

Mommy na karkimin haka dan allah. Momey dake tsaye.saitaji tasayin yar ta ta" ya kamata Tabbas ranta yabaci sosai Amma ba kamata ta yake hukunci cikin fishi ba allah sarki tsakanin da da mahaifi sai allah" wani tausayin tane ya kuma ma mayeta"

Dur kusawa tayi ta kamo ta tareda lallashin ta itama UMMU hakuri ta bawa tare da cewa baxata kuma ba "Ba karamin dadi mommy taji ba fita mommy tayi tasanar da AUNTY JIDDAH" su shiga tare dameyi mata kwalliya" kan sushiga harta xura kayan da aka ware mata na kamu" ke kwalli ma tashiga nata aikin. Kan kaceme saiga UMMU ta koma kamar wata bala rabiya dan kyau ga kanshi ta ko inata tashi yake" daurewa kawai Ummu take dan babu yanda xatayi gashi taceawa mommy baxata kuma ba. Wannan dalili shi yahana UMMU yin kuka ta kuma yi al kawarin baxata kuma xubda hawaye ba harseta bar gidan.

Suna karasawa far fajiyar gidan aka dauki guda dama anan xa ayi kamun babu bata lokaci a'kafara kamu kamar dai yanda kowa yasani bayan angama akashiga yin nasiha da yanda xaki kula da mijin ki. Karfe shida da rabi aka gama kamu kowa ya kama gabansa. Da dare yayi UMMU ta kasa bacci Sabida tunanin barin gida tasan gobe iwar haka anfara haramar kaita gidan YUSIF ama tsayin matar sa" waiyoo allah na ni UMMU"yaxanyi da wannan auran da aka kaka bamin? Tayiwa kanta tamabayar da bata dame vata amsa" sai wajejan Asbah baci yayi awan gaba da ita.

Sai kusan ba kwai ta farka tayi mika tare da jero addu Oi da salatin annabi Muhammad (S A W) wata matashiyar budurwa da kexaune a gefan gadon ta kalla. Nawwara Yaushe kuka xo? Wacca aka kira da NAWWARA ta dago fukarta dauke da murmushi tace yau da safennan jirginmu ya sauka" na tambayi mommy kina ina tacemin kina nan dana shigo kuma sai naga kina barci shiyasa banta sheki ba" Sabida nasan kingaji dayawa Amar yar ya'yanmu YUSIF" takarashe maganar tare da sakin dariyar shakiyanci

"Wata uwar harara UMMU ta aikamata da ita tace xakifara ko kedama gaki da shegen surutu da tsokana ko yar dariya ta kumayi sannan tace allah ya huci gimbiyar Yusif" ta fada tare da kashemata ido daya" kwafa UMMU tayi tai shigewarta toilet dan tasan halin NAWWARA" da tsokanar ba i, inta biyemata saita sata kuka, ba karamin aikinta bane.

Share fisabilillah
Mmn hibbat ce...

MATAR YARO

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.