Complete Hausa Novels

Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Tantiriya_A_Gidan_Yari_Part_3_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 13 of 20

PAGE NAKI NE
Hajjafatty

Haneef ya riga su Mero Isa kauyen ma,suna zuwa suka ga motarsa acan har an yiwa gawa sutura za a tafi kaita da shi aka tafi kaita,Khadija tana ta sharbar kuka biyu ga na mutuwa ga na abinda ya faru da ita,gidansu a cike da Yan uwa da abokan arziki,Khadija ta shiga ciki ana ta bata hakuri ana mata ta'aziyya ko amsawa bata yi gado ta samu ta kwanta tana ta kuka.
Jummai kuwa sai sambatu take yi Allah yasa mun rabu da Sani lafiya,tunda muke dama shi Sani baya fada baya fada dani sam ,ko Abu yaga nayi ba daidai ba sai dai ya nema min shiriya wajen Allah,masifa ta same mu rana tsaka,mutuwa me Yankan kauna,ta rasa Ina zata je sai gidanmu ta rushe da kuka,ana bata hakuri mutane suna cewa sai hakuri,haka Allah yaso,Maza suka dawo daga janaza ai kuwa sai ga Haneef ya shugo har ciki yayi gaisuwa,yace Ina Khadija? Akace zazzabi take baza ta iya fitowa ba,yace to ayi mata ta'aziyya duk da haka sai da Jummai tace shine Wanda Khadija zata aura ai take fadawa mutane,badan ya so ba haka ya juya ya fita kasa tafiya yayi ya zauna wajen makoki abinsa.
Sai wurin dare ya tafi ransa a bace zuciyarsa kamar ta fashe sabo da bacin rai da bakin cikin abinda ya aikata.

Khadija haka zuwa dare ta lallaba tayi wanka tare da tsarkake jikinta tana kuka tayi sallolinta tana ta addua tare da neman yafiyar Allah, shine ma ta samu sassauci ranar a haka ta kwana,washe gari Haneef duk yanda zai ga Khadija abin yaki ta boye kanta a daki,har aka yi Sadakar Uku bai ganta ba kullum sai yaje Kuma,su kuwa Yan gari Jummai kawai ake zagi ana yi mata Allah ya Kara,suna cewa yanzu maga Inda zata sa kanta,zamu ga ya zata yi,abinci ma sai ya gagare ta,Wanda basu San shi Allah ba haka yake ba.
Bai sake zuwa ba sai da aka yi Sadakar Bakwai,Yana shugowa gidan ya ga Khadija,wani Sanyi yaji a ransa,tana gyara wake duk ta rame,tana Jin muryarsa ta fashe da kuka ta mike ta fada daki tana rusa kuka,Jummai tace lafiya Yar Nan kamar Kinga maye zai lashe miki kurwa,wannan kuka naki Mero na rasa dalilinsa,ko ni da nake Matar ubanki nayi hakuri nayi tawakali amma ke kinki bafa zai dawo ba,Munnir ma ya hakura,Haneef ya durkusa a kasa,Jummai tace tashi Dan Allah ga tabarma yaron kirki,ta karkade Masa tabarma ya zauna.

Da ladabi ya gaishe ta tare da Kara yi mata ta'aziyya,tace an gode fa da hidima ga kayan abinci suna tafe ga kudi Allah ya Kara budi,yace ba komai,Jummai tace shiga dakin nata tana ciki zafin mutuwa ne watakil taji maganarka kai.
Haneef tashi yayi ya shiga dakin Mero ba komai a ciki sai ledar tsakar daki me kyau sai Yar katifarta karama sai kayanta a Ghana must go a gefe,tsaf tsaf an goge.
Haneef ya sameta a kwance tana ganinsa tace ka tafi wlh bana kaunar ganinka na tsaneka,mazinaci fasiki,Idonsa ya runtse sabo da zafin Kalmar da yake ji tana fada Masa,na tsaneka wlh bana sonka bazan aure ka ba macuci,Jummai tana Jin komai amma Bata San dalilin da yasa Khadija take cin mutuncin Wanda zata aura haka ba.

Haneef yace Dan Allah ki daina daga Murya,wlh banyi Dan na cutar da ke ba,bani da lafiya ne lokacin da kika zo Ina kan gwiwa,duk zaman da muke yi Ina tare da matsananciyar sha'awa wacce har ta Kai ga ta zuba min lalura a jikina magani ma Likita ya bani amma na Sha banji sauki ba,Ina Baki check kika rungumeni daga lokacin na kasa control bazan iya control ba a lokacin,kiyi hakuri ki yafe min,banyi da niyyar hakan ba,karki manta na San mace tunda nayi aure na taba sex ba sau Daya ba,kamata bazan iya hakurin zama haka ba mace ba,kin San irin macen dana aura,nayi nayi Mama ta bari a daura mana aure cikin gaggawa amma taki yarda shine har Hakan ta faru,Kuma nayi niyyar ana kawo kudin a daura amma mahaifinki ya fara rashin lafiya,kaddara ce Allah ya gani bada hayyacina nayi ba Kuma bada so na ba,Khadija tana kuka tace ai dama komai sai ace kaddara ce bazan yafe ba Kuma bana sonka ka fita ka bani waje,kallonta yayi tace ka fita nace bana kaunar ganinka,kiyi hakuri ...ka fita bana son Jin komai,Haneef ya fita kawai ba yanda zaiyi da ita,Jummai tana kallo ya fice kamar zaiyi kuka,dakin Mero ta shiga ta sameta tace ke kuwa Meke faruwa haka da ke Khadija? Mero tana kuka ta kwashe labarin kawai ya fadawa Innarsu,Jummai kirji ta dafe tace Yau na shiga uku ni Jummai Dan iskan yaro hanci kamar sillen kara,ta tabbata Munnir kambun baka ne da shi abinda ya fada ya faru,Wayyo Ina zan saka kaina ga Mutuwar miji gashi an lalata min yarinya, Jummai tace da me zan ji a rayuwa ni kuwa Jummai,kawai a haka rami a binne ni na huta,Mero tana kuka tace ai duk laifinki ne da son kudi da kin barni a gida ko zamu hadu da shi sai dai yazo gidan iyayena ya same ni gashi yanzu ta karfi ya lalatani waye zai aure ni a haka?

Jummai tace shine Haneef din,tunda haka ta faru ai kuwa shi zai aure ki wlh dole,Mero tace bana sonsa bazan aure shi ba,gwara kawai na kama siyar da abincin siyarwa in nemi na kaina,Jummai tace wlh Baki isa ba Khadija ko mutuwa zakiyi sai kin aure shi,Allah ya kawo mana hutu da gata kice baza ki aure shi ba,to ribar me kika ci? Ya lalata ki sannan arzikin baza mu ci ba? Yanzu Ina check din da ya Baki na million uku da Rabin? Na mayarsa Masa da abinsa,Jummai hannu ta daura a Kai tace kin cuce mu,to me kika yi kenan? An lalataki yaci banza,gashi auren ma kince baza ki aure shi ba to ki gaya min ribar da kika samu,Mero tace ai mutunci yafi kudi,Mutunci ya kare tuni Mero tunda ya samu Jikin ki ai aikin gama ya gama tuni yayi wasa ya cinye kwallo,Manchester da Arsenal ai sai buga wasa,Sabo da haka wlh sai na karbi million uku da rabi Kuma aure sai kin aure shi,Mero tace ni Kuma wlh bazan zauna ba,gwara ma ki kyale ni ko na tonawa kaina asiri a gari nace yarki an lalata ta,Jummai ta bude Baki taji tsoro tace Inshaallah ma zaki sakko ki hakura ku rufawa juna asiri,yanzu kiyi shuru da bakinki ko Munnir kar yaji zancen nan Dan Allah bare ya fita gari aji.
Dole na gyaraki sosai ya gama dake.

Haneef kuwa ya rasa Inda zai saka kansa,ko wayarta ya kira sai dai ta kashe,idan ya tura mata text shuru,Hakan ya Kara tashin hankalinsa ya rasa Inda zai saka kansa.
Jummai kuwa yarta take gyarawa sosai ta dole take wa Mero duren magani,kudin da suka samu na sadaka da su Mero ta fara siyar da wake da shinkafa da Miya harda salat a kauyen kusa da Inda mutane suke taruwa,harda kafa katon table da bench dinta na zama,abincin ta zubo a manyan coolers Almajirai su kawo mata wajen tazo ta siyar da abinta,bata shiga safgar kowa ranta a bace yake.

Washe gari da sassafe Mero ta rage tunani tana kwance ta koma bacci wani Zakaran gidan su ya hanata bacci da cara,a cikin bacin rai take da takaici,fitowa tayi ta cafke Zakaran tare da zaro Masa Ido ta nuna shi da hannu tare da yi Masa dakuwa zagi ambola tace uwarka nace,shege Dan iska ka dameni,wlh duk ranar da Ina bacci ka dameni da cara sai naci ubanka,ko Dan kaga kwai aka yi aka sameka zaka yiwa mutane wulakanci ta make kansa tace duk ranar da ka Kara sai naci ubanka matsiyaci,ta wullo shi waje tana cewa Allah yasa barayi su Kama ka,Jummai tace ba Ameen ba inshaallah sai Sallah zan yanka shi..
Akuyar Munnir ce tayi kuka meeee ....Mero tace kan Babarki munafuka uwarki za ayi miki ba an Baki abinci ba,ke a akuyoyin ma baki da kyau kumatu kuful kuful duk tayani Muni shegen Ido duk kwantsa,in Baki wasa ba sai na kaiki kasuwa gobe ta ja tsaki ta koma bedroom.

Sai 2:30 Mero ta fita Inda take sana'arta tana cikin zubawa wani abinci a plate zai siya Haneef ya motarsa baka katuwa ta gangaro a hankali,Yana bayan mota ya hango Khadija cikin Maza tana zuba abinci,kishi ya kamashi Wanda bai taba Jin irinsa ba,sai da ya dandana Mero ma ya fara wani mahaukacin kishinta baya kauna wani ya kalleta.
Yanzu Kuma bashi da bakin magana,driver yayiwa magana da ya tsaya,bayan sun tsaya ya fito ya Sha glass ga wani danyen yafi a jikinsa fari ba karamin kyau yayi ba,gaba daya kallo ya Koma kansa,ya tako a hankali Inda Khadija take hankalinsa duk a tashe,ko kunyar uban kowa bai ji ba yace Dan Allah kiyi hakuri, Bai kamata a shafe duka alkhairan mutum ba,ki tausaya min,Khadija ta kalle shi kawai ta ja tsaki taci gaba da zuba abincinta kamar bada ita yake ba,mutane suna jinsu,idan ba so kike na fadawa duniya ba Dan Allah kiyi magana,ba tare da ta kalle shi ba ta furta ka fa takura min kaje wajen wata mana dole ne ana so dole ne ta ja ta juya taci gaba da cinikinta.
Idonsa ya lumshe zuciyarsa tana suya ya juya ya shiga mota abinsa sabo da Yan kauyen sai kallonsa suke yi,Yana shiga mota ya runtse idonsa tare da zuba tagumi hawaye suka zubo Masa na takaici,Driver ya sa suka juya kawai.
Yana komawa gida ya samu Mamansa tazo ta neme shi a waya taji shuru,Yana shiga Parlo ya ganta,Mama tace Kai me ya sameka Subhannallah naga ka rame Haneef baka da lafiya ne,ko magana baiyi ba ya wuce ya haura sama abinsa ai duk sune suka ja Masa.

Mama ta bishi sama kafin ta shiga ya sawa dakinsa key ,Mama mamaki ya kamata,Danta me biyayya bai taba yi mata haka ba,tace Haneef wai lafiya,kukansa taji kawai a ciki,tace na shiga uku ni Yar nan,ko akan Khadija ne? Wlh idan a kanta ne na yarda ka aure ta,na yarda Dan Allah kayi hakuri ka bude kofar,Haneef yaki budewa tana cewa Haneef nice fa na haifeka bani da kowa sai Kai Haneef,Haneef ya tashi ya bude sabo da darajar iyaye,hannayensa ta rike tace meke faruwa ne? Gefen bed suka zauna Yana hawaye sosai ya bata labarin abinda ya faru,yace kune kuka bata min rayuwa,kune Sila ai, Salati Mama ta dinga ja,tace me yasa baka fada min ba? Kince ko mene bazan aure ta ba,nayi nayi dake ya kike so nayi,akan Ihsan din da Bata damu dani ba,yanzu Khadijan taki hakura? Yace ae taki hakura naje naje har na gaji da zuwa tace baza ta aure ni ba,wlh idan bata aure ni ba sai na zama Dan iska cikakken,sai na koma goggen kati,ai kune kuka jawo min,Mana tace Inshaallah zata hakura kaji,yanzu kayi hakuri ka daina zuwa tukun sai ta huce Inshaallah zata hakura,yace to ai ni idan ban ganta ba bana Jin dadi sannan yanzu sana'a take yi a cikin Maza a samu a hanata kawai wlh.
Mama tace ka daga kafa kayi hakuri shine dai dai Haneef,ka daure kaji,yace to zan gwada,Mama da kanta tayi girki yaci tana lallaba shi da kanta ta bashi a baki.

Mero shuru taga Haneef ya daina zuwa,yau tana dakinta ta dawo daga sana'a tayi wanka ta kwanta tana hutawa,in banda tunanin Haneef ba abinda take faman yi sai tunanin Haneef,a fili tace aikin banza to kar yazo mana in bai zo ba sai me,na zauna Ina batawa kaina lokaci a banza ta ja tsaki tare da furta Ina ruwana da shi mtsswwww ta ja tsuka ta Mari kumatunta tare da furta ke dai Mero Tinkiya ce balama haba.

Jummai tana kallon Yarta kullum a tunani take,tace Khadija kina son bawan Allah ki hakura ki aure shi,nasan Nima ban kyauta ba banyi aiki da hankali ba wlh Sam,yanzu tunda Sani ya rasu nake Jin Ina ma na dawo da rayuwa baya na gyara Halayena,Munnir Yana jinsu yace in an fada muku gaskiya ai bakwa ji sai da ta baci,duk uwar da ta sa son abin duniya a ranta wai yarta itace jarinta to tana da wahala,dama an haifi yara ne su zama jarin iyaye?,ace yarinya itace zata kawo kudi Kuma ke Inna Allah bai hana ba,Baffa Yana da rufin asiri kina sana'a amma kika yarda Yar da kika Haifa a cikinki itace jarinki,yanzu wa gari ya waya? Ina fada muku gaskiya baku ji,ai nasan boye min kuke yi amma naji komai Kuna zancen,an lalata Khadija,wannan izina ce abinda ya dace tuntuni ace anyi mata kenan dama ko Kya gane gaskiya Inna,Allah ya kiyaye ma ba da ciki kika ganta ba,yanzu ya rage naku ko ku gyara ko karku gyara,amma mace kamar Khadija a aikatau ai gwara tayi aure.

Jummai shuru tayi,Munnir yace sai kiyi hakuri kaddara ta riga fata ki rufawa kanki asiri ki aure shi,domin wallahi wani ya aureki in ya gane zaki Sha gori da wulakanci,wa zaki samu ma kamar sa,gwara ma ki hakura kawai ku rufawa juna asiri.
Khadija da Jummai shuru suka yi kowa da abinda yake tunani a ransa,suna ganin Munnir yaro amma ya fisu hangen nesa,Jummai tana Jin wani irin daci a ranta marar misali da irin abubuwan da take aikatawa, yayin da Maman Haneef ta zauna tana kula da danta sosai tana kwantar Masa da hankali.

Spark Yana Office Yana meeting Naila ta addabe shi da kira,ya zaci wani mummunan Abu ne ya faru,ya dauki Excuse ya daga wayarsa yace family issue ne,Yana dagawa Naila tace Baby Yana son Ganinka ka dawo gida wlh,Murmushi yayi yace yaushe ya fada? tunda ka fita yake cewa Daddy ya dawo gida Kuma a siyo kifi ya kare kasan in baici kifi ba ulcer ce zata kamashi,yace ai zan dawo meeting fa nake yi,mu Ina ruwan mu da Meeting dinka in zaka dawo kawai ka dawo muma ai meeting din sai ayi damu,kudin da zan samu fa a barshi? Naila tace wlh in baka dawo ba sai nazo yanzu,yace zanzo kwantar da hankalinki Babyna,tace to sai ka dawo,Kuma yau kazanta nake ji ba Wanda zai Sa nayi wanka a gidan nan,yace ai normal dama turawa ma basa wanka kullum mune sarakan tsafta sai mu dinga wanka kullum ai watarana sai mu huta,tace we love you,ke da wa? Baby mana,I love you too Baby girl ya kashe wayar,Suna jinsa su mamaki suka yi bai tashi ba a gabansu yayi kalamansa ko kunya bai jiba,kowa idan zaiyi waya da mace fita yake amma Banda Spark ko a gaban uban waye maganarsa yake.

Fuskewa yayi suka ci gaba,abinda Naila tace ya sa an Kai mata amma bai koma gida ba sai da ya tashi gaba daya,yasan akwai rigima Yana zuwa ya iske ta yanda ya fita ya barta kuwa bata yi wankan ba,yace Beb ba sannu da zuwa? Ashe Baki wankan ba? tace kazanta nake so yau haka zan kwana,tashi to muje gidan Arham,Arham Kuma? Ae mana sun tare ai,dubiya zamu je mu gano Jikin,Naila tace to amma Allah ni yau bana son wanka kazanta nake so ala dole zanyi,sai inyi miki ma sorry muje,ya lallabata da wayo suka yi wankan,ana wanka tana harararsa yace me nayi Kuma? Sai kallon cikina kake yi ka juya bayanka duk nayi Muni,sai bayan sun fito suka shirya sannan suka fita,an Kai Masa abinci Office shi yasa bai nema ba yanzu.

Suna zuwa suka iske Mayu Misam da Rafeeq a gidan,Arham ne ya fito shi a dole me gida ya Sha wanka cikin gezna Yana bulbula kamshi,tun kafin yayi magana Misam yake dariya,ya basar kuwa harda cewa ga parlo na ku dawo can,sai kace wani me gidan kirki cewar spark,bayan sun koma cikin parlon iya su Maza su hudu Naila tana wajen Basma,Misam yace yaro an girma Kuma,Arham ya share zancen yace ya aiki,mun barshi a Office dubiya muka zo a fada mana halin da Amarya take,Arham yace tana nan ranga ranga,Spark yace wai Kai namiji ko?Arham sosai ma kuwa Kai ai nasan ko kirji baka iya tabawa ba, you no sabi handle booby,Misam ya fara dariya harda buga kafa ance Spark boobs Bai iya sarrafa shi ba,Rafeeq yace Amma baka da kunya Arham babban Yaya guda Spark,Kai da kake maganar kasan scissors? Misam yace ni fa? ai Kai Dan bariki ne ba a ja daku jikan Zeenatu kasan komai,kasan clockwise and Anti clockwise?ya Kalli Rafeeq,Rafeeq yace Ina zan sani sai irinku Yan zamani,zaku zo ku dameni ya Amarya ya Amarya ba abinda ban sani ba na iya komai,a jiin mace Kun San Reginal zone?kuzo na dinga koya muku darasi,Spark tagumi yayi kawai Yana kallon Arham,yace in banda ku yayin ma gaku Nan ne dai me zai kawo ku gidan kaninku yau,jiya an kawo Amarya yau kuzo daga Jin nayi abin bajinta,sai kace mata zaku koyi tsegumi,sai kuje ta bude muku kuga dinkin ai,Spark yace shike nan tunda haka kace da matan mu Dan uwarka ma zamuyi a Nan Dan Munji ka tare munzo ganin gida tunda haka kace baza sake zuwa ba,Ni na zo kuje ai kamata yayi ku bari na kawo muku ita gida ta gaida manyan yayye amma sai kuzo Kuma ni da nake so ta kasa hada Ido daku sabo da kunya,Spark yace a'a ta kalleni wlh ni ko bani da riga ba ruwana zata iya kallona bare Ido,dariya Arham yayi yace ai shike nan tunda baza ka karbi girman ba,yace na barwa Misam,Misam yace yi can da shi ku bawa Rafeeq,Rafeeq yace ni ko yanzu ta saki layi binta zanyi muyi zancen a barwa Khalil girmansa,Spark yace girma ai sai Papa su ya kama da Mummy na,Kai kaga Mummy na Kai mata ziyara ta dinga shagwaba,Allah sarki Baseeru Kusa ta tuna tayi zaton shine cewar Misam, Spark yace Inda kasan ta macen kwaduwa Ina da uwa a wajen nan,Mummy Bariki a jikinta yake,Rafeeq suna dariya,ta fashe min da kuka my son ana fari nace ahhhh...Misam yace Kai duk haka suke wlh har Mima har yanzu wai Papa Yana Jin dadin shagwabarta bai daina jiba,Rafeeq yace Kai Misam bama son sharri yace to haka na gani da idona na fuske kamar ban gani ba,Arham hankalinsa Yana kan Amarya shi Kam,yace wai kuwa in aka yi dinki suna yin sati basu warke ba? Tambayi masu jego cewar Misam,wayarsa ya dakko yace bari nayi searching a Google ya fara rubutawa da turanci yace Yan midwifery Kuna Ina kuzo ga ranar ku,akan haka sai na tafi asibiti nayi tambaya.

Naila kuwa tana wajen Basma wacce ta dan zauna tare da jingina da Jikin bed,Naila tace Amarya an Sha Mai,Basma kamar zata yi kuka tace Allah bazan sake yarda ba kamar an tambayeta,taci gaba da cewa Dan kawai yace kar na fada ne ba kyau amma wlh da sai duniya taji abinda yayi min,dama ai ba sirri ne dani ba,bana barin zance a ciki ni,yanzu Yar maganar nan ta sirrin aure da aka hanani fada a kanta sai nayi muguwar rama sabo da zata dinga cina a rai,Naila tayi dariya tace ai Basma babu me tausaya miki ko kadan irin rashin kunyar da kuka yi.
Ai na zaci mutumin kirki ne ashe ashe ba haka bane.
Sun dade a haka suna Hira kafin Spark yace ta fito su tafi.

Suna watsewa Maman Rafeeq ta zauna a dakin Basma ta kafa ta tsare,Arham yace nifa wlh ban San zance ba,gwara ki tafi kawai ko na tube a gabanki wlh ai uwata ce ke in kin kalla ma na danki ne,idan Kuma so kike to kema zan iya Dake,Mama tace na shiga uku na lalace Arham ni din kanwar uwarka,to ki canja daki Tabesting zanyi ko nayi a gabanki,Mama tace ba Inda zani karamin marar kunya,a gefen Basma ya zauna Yana kallonta Yana shafa gashinta yace Babyna Yaya? Kirjinta ya taba da hannu biyu ya rike ya sun daina ciwon? Mama mikewa tayi a gigice yace bude muga ciwo in Dan lashe miki....kafin ya rufe baki Mama ta tsinci kanta a waje tuni,dariya yayi Gani yanda ta bar dakin yace da ki zauna mana Kiga yanda akewa Nippi Nippi.

Ayi hakuri Ina wajen sauka

AsmaBaffa
[3/4, 8:35 PM] AsmaBaffa: 🏫TANTIRIYA🏫
A GIDAN YARI

BOOK 3
~TAIMAKO~

66-70

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.