Complete Hausa Novels

Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Tantiriya_A_Gidan_Yari_Part_3_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 4 of 20

PAGE NAKU NE
Binta Abba
~Teemah

Hey lovelies

Ke matar aure ce kuma kina neman business din dazakiyi daga gida da kuma baya bukatan jari?

Kai dan makaranta ne kuma kana neman inda zaka ringa samun kudin kashewa?

Ko a'a ke kinada business dinki Amma kina neman wani side hustle haka da zai Kara Miki extra source of income?

Ko kinada business idea da kikeson kifara Amma Babu jarin farawa?

Toh duk ku tarkato wannan training din, dan ga solution nan nasamo muku, kawai ki danna wannan link din Dan Samun damar shiga group din

https://wa.link/49vn47

Jauro ya Kalli Abba Dolo yace bazan biye maka ba,ni ba Kubra bace itace ya zama dole ta dinga biye Maka Banda ni, Abba yace an dora ka a keken bera,ka Sha amarcinka Jauro ni ba wani Abu nace Maka ba,ya maganar zuwan naku Abuja? Jauro yace so nake sai na koma wajen Habiba itama nayi mata kwana biyun ta sai muje kasan mata sai tace sai da kwananta ya zagayo na takalo unguwa,Abba yace ba tace ta baka sati ba,Jauro yace Kai sai na zauna nayi satin? karya take gwada ni tayi,baka San tsiyar mata ba tunda baka taba yin mata biyu ba?

Abba yace to ka koma kace ka fada baza ka iya har sati ba tare da ita ba,itama ka zuga mata karya tunda yanzu dama Kai munafukin mata ne,ban gane munafukin mata ba,Abba yace to Nan kazo kace Maman Annoor ba wata kamarta,can ka koma kace ba kamar Habiba ai ka zama Dan iska kawai a gari,ni bazan iya Kara aure ba sabo da dole na Fadi gaskiya,idan naji Amarya ta kwace ni zan fadawa Yar Inna gaskiya nace ni can yafi dadi,idan Yar Inna ce ta kwace ni sai na fadawa Amarya kaga zaman aure bazai yuwu da haka ba ni Kuma dole sai na fada shi yasa gwara na hakura ,suje da kyawunsu da komai zan karasa da na Kubra.
Jauro yayi dariya yace dama mata biyu ai sai mu gwarazan Maza.

Bayan sati daya Abba da shi za Azo Abuja yace ko Dan yazo yaga gidan auren yarsa ai yazo,Jauro,Annoor,Iman sai Haidar,Jauro duk ya biya kudin jirgi harda Maman Iman Rahma,Abba me 'ya tuni ya fadawa Naila zasu zo da baki,tare da Yar aiki da su Mufee suka shirya girke girke,Spark yau fasa fita yayi,tace baza ka fita bane yau? Yace Ina zanje surukaina zasu zo ai dole na zauna,Naila sai da suka gama komai suka gyara gidan sannan su Mufee suka tafi gida,Naila yanzu har kannen miji ake sawa aiki.

Spark driver ya tura aka dakko su har gida,Abba yau yaga gidan 'yarsa,yace Allah ya Kara zaunar da ku lafiya baza ki fita daga gidan Nan ba Naila, Aljannar duniya, da nasan abin ya Kai haka ai kullum tsaiwar dare zan dinga yi karki fito daga gidan nan,Iman tana kusa da Annoor dinta,ita da Babar tata sai kallon kallo sabo da rashin shakuwa,Suna shiga Sanyi da kamshi ya dake su,Naila ta musu sannu da zuwa suka zauna,Abba yace Naila ki rage cin dadin nan kar kiba ta miki yawa ki jawa kanki ya dinga hango Yan shawalwalai,dariya suka yi,Naila tace Abba ni Ina naga wata kiba a haka,gaisawa suka yi da juna sannan ta haura sama ta kira Spark tace sunzo wai nayi kiba Inji Abba? Spark yace to kina ta cin kudina kin hanani Tara abin duniya ba dole ba,dariya Naila tayi ta jawo hannunsa ya mike suka fita,Jauro yace Ashe masu gidan ana Nan Kai sai kace Amarya,Spark ya iso ya gaisar da su da ladabi ya mikawa Annoor hannu suka gaisa,Iman tana makale a Jikin mijinta tayi shuru.

Abba yace ya Banga kayan ciye ciye bane ni bana so a sani gaba da magana ko lemo babu gwara a ajiye min abinci a tafi a bani waje,Naila ta mike ta dinga jera musu abin ci da Sha,Abba ya Kalli Spark yace Allah ya Baki Naila Lada ashe haka kike Shan wahala a gidan miji Yana kallo bazai tayaki ba,dama samun miji irinmu a zamanin nan ai sai an tona,Uwarki ta fiki dace Naila data sameni,da nine bazan zira mata Ido ta dinga aiki haka ba,Jauro yace ai yanzu babu irinmu a kasar Nan sai dai ko a Larabawa, Su Annoor suna ta dariya,Maman Iman tace ku don Allah baza kuyi shuru ba agaban yaran ku,Jauro yace a'a bama shuru mu bakinmu kalau yake fes kullum ga brush ga aswaki ta ya za muyi shuru,Spark shi dai dariya yake kawai dan abin na su Abba Dolo sai Ido.
Ba ruwansu suka bude abinci sai da suka zaba,Naila tace ko a Kai Dining? Abba yace a'a muna da me ciwon baya Jauro kawo mana abin zama mu a kasa zamu zauna.

Naila taje ta kawo musu suka baje a kasa,Iman ta zubawa Annoor su suna kujera,Abba yace ku a sama zaki ci? Annoor yace ya za ayi ta zauna a kasa Iman a'a,Jauro yace Kai yaro munga Habiba ma yanzu ta hakura zama take,Nan wai Kai gyara kake taya matarka? Kayi ka gama,Haidar tunda aka zo aka gaisa baiyi magana ba sai lokacin yace ni ba me zuba min wato ko naci ko na barshi

Naila har ta yunkura zata mike kiri kiri Spark ya jawo rigarta ana kallo ya fuske yace zauna,Haidar yace Allah sarki ai shike nan ya zuba abinsa,Annoor Yana ta Masa dariya yace wlh Kuma matata baza ta zuba Maka ko ruwa ba,Abba yace shi yasa naki zuwa da Yar Inna suka kwashe da dariya,Haidar yace ni me zance matarka tayi min Abba ai uwata ce,Abba yace ake kaunar mahaukaciya ma bare tsohuwa da hankalinta,har abada baza ka samu irin Yar Inna ba,ga Maman Iman kaji tarihinta dai to bare dattijuwa irin Yar Inna a kanta sai ka wulakanta budurwa,Spark Yana ta dariyar Abba da son Yar Inna.

Sai da suka koshi suka huta sannan mazan suka tafi masallaci Naila ta Kai su Iman bedroom suka yi sallah suka kwanta suna hutawa,Maman Iman bacci tayi Iman ta fito ta samu Naila suna gyara palon da me aiki,ta taya su suka yi wanke wanke suka gyara ko Ina har kitchen,Iman tace Dan Allah Naila kice na kwana a nan gidan kar a tafi dani hotel,Naila tace sabo da me? Iman tace to mijina baida hakuri bazai bari na huta ba na gaji wlh duk ya kashe min kugu,Naila tayi dariya tace zaki Saba ne,ni dai Dan Allah kice zan kwana a nan,Naila tace to shike nan zan gwada,harda bawa Iman Yan tsumi na gyaran jiki ta Sha abinta ta bata wasu ta sa a jaka.

Jauro bayan sun dawo daga sallah yace Maman Haidar ta turo min address din gidan su Haidar,Naila tace ni Ina ganin kamar haidar da wani wlh na rasa gidan waye Kuma,sai naga kamar Yana da kanne kamar babu na rasa Inda nasan me kamar sa,Abba yace ai ga address zamu je har gidan,Spark ya karbi Address din ya duba yace a'a to wannan ai gidan su Rafeeq kanina ne,Jauro yace mutumin fa bai taba haihuwa ba,Ae shine fa sunansa Aliyu Shima sunansu Daya da mijin Mummy amma shi ba a kiransa da Aliyu Sunan garinsu ake fada Masa.

Yace bari na kira Rafeeq muje gidan kawai ,Rafeeq ya kira suna tare da Ikhram dinsa ya gaji da halinta ya kaita asibiti cikinta ma yafi na Chika kwanaki a duniya,Spark ya fada Masa dai a gurguje,yace to ku sameni a gidan ai kuwa mijin Mama Yana gida yau,suka tafi Rafeeq ma ya tafi da Ikhram can,Spark suka tafi gaba daya,suna zuwa Suka shiga har Palo, Maman Rafeeq Hannun bibiyu ta tarbe su,Jauro yace wajen me gidan muka zo,tace ai kuwa Yana Nan ta mike taje ta fada Masa ta dawo tace yanzu zai fito,ta kawo musu ruwa da lemo.

Fitowa yayi cikin shiga ta alfarma Yana tafiya ta manyan masu kudi yanda ya Saba,har ya bude baki zaiyi masifa me ya kawo Maza har palon matarsa baza a jira shi a waje ba sai suka yi Ido biyu da Maman Iman,Baki ya bude mamaki ya kama shi,yace Rahma me zan gani kece? Rahma ta mike tsaye tace nice nan Sudan,Spark yace dama na fada muku da Sudan aka sanshi amma sunansa Aliyu.

Rahma ta dafa Iman tace ga Yarka,Maman Rafeeq da Rafeeq suka zaro ido waje,Jauro yace ga Danka Kuma bakin Dan iska tambadadden dattijo,Abba yace a'a Jauro yaransa suna ji kana zagar musu Uba ba dadi,Haidar yace mene amfaninsa ni wlh a Kara Masa wani,a wajen Aliyu Sudan ya durkushe yayi zaman dirshan a kasa ya Dora hannaye a Kai Yana kuka,yace Rahma ki yafe min na cutar dake son ki ne ya sa na aikata miki haka,har lokacin kina halin ciwon hauka Ina ta bibiyar Inda kike har na ganki a kango na da nake ginawa daga nan zuciyata ta kasa hakuri Dake har naci gaba da amfani dake,dalilin sonki na kasa kula da matata ta aure Ina zaluntarta,farko da na fara bataki Baki samu ciki ba sai dai lokacin da kike halin ciwo na hauka tabbas wlh wannan 'yata ce,Jauro yace Kai rufe mana baki algungumi ko kunya baka ji duk mutanen unguwa sun San kaine ka aikata tunda ana ganinka kana fita da ita,Kai rashin Imaninka yayi yawa mace tana ciwon hauka,Rahma ce tayi magana tace sharrin shedan ne laifin kaka ne data Hana shi ni,ni nasan Yana so na,duk ita ce ta jawo min,Aliyu Sudan yace kwarai kuwa.

Abba yace to shi Kuma Haidar din fa? Jauro yace ai kasan matar da tazo aiki gidanka Yar wanke wanke da shara Binta,kayi mata ciki kuka koreta Kai da matarka,Jauro ya nuna Maman Rafeeq, kece da laifinki wai ku son miji son aure kar asiri ya tonu Kuna kallo mazajenku suna aikata fasadi sai ku Goya musu baya ku kare zancen to yanzu gashi ke ba take yake ba Kuma gashi ya tara yara har biyu ba yaran sunna ba,ke Kuma Allah bai baki naki ba,mutane baza su hakura da jarabawar Allah ba,Kun cuci yara kawai.

Maman Rafeeq tana ta rusa kuka mijinta yayi abin kunya bayan itace ta Kori uwar Haidar tace ta yiwa mijinta sharri,Aliyu Sudan yace yanzu Ina Binta take? Haidar yace tuni ta koma Fatima tana England ta samu hadadde tana aure" jiranka zata yi?,ka daina ce mata Binta" Fatima ce yanzu,Kuma ko tana Nan baza ta aure ka ba,me za ayi da miji irinka,shi yasa kullum na dinga tsallaka katanga kullum son Bariki nake ashe gado nayi ni nasan da dalili,Allah ya kiyaye Yan tabe tabe nayi banyi babban ba adduar Kawu tana bina,Aliyu Sudan yace Nima tawa zata bika,Haidar yace a'a'a ko kayi baza ta karbu ba,irin wannan laifi naka munana Ina zaka sa min albarka ta bini Kai kanka inaga sai da aka sallamaka ka gudo daga Sudan din, nidai kawai ka cuceni,cuta ka gama damu Allah ya yafe Maka,bamu muka yi laifi ba da sauki,takaicin ma da banyi aure ba" da nayi aure ne ma da sauki to ban aure ba wace zata ji Dan shege ta aura,Spark yace Kai in da kudinka ko Yankan Kai kake mata yanzu aureka zasu yi,ni da nake da kanne na baka daya a ciki ko Mufee ko Haly wawarka zasu yi.

Annoor Yana jinsu takaici ma ya hanashi magana,yace mudai kawai an cuce mu,yanzu Haidar Kai ubanku Daya da Iman kenan? Yace to ya zaka yi na zama surukin ka,shi yasa muke kama ma,Annoor ya Kalli Haidar ya Kalli Iman yace Kai ya Akai ban kula ba sai yau Kuma Kuna yanayi fa,Haidar yace sa wasa yaro,Haidar ya Kalli babansa yace to yanzu Kai Baba zamu ce ko me kasan bamu da gadonka sai a bamu rabonmu tun a duniya,in kana so mu ce Maka Baba wlh in baka so to kaje da kudinka ni dai ba sake Ganina zaka yi ba dama can Ina da Ubana daban me zanzo nayi Maka,uwar tawa da ka koreta Gombe garinsu,Aliyu Sudan yayi mukus kunya ta isheshi.

Rafeeq yace abin kunya ya bar gidan su Spark ya dawo gidanmu,'Ya'ya biyu rigis ba aure aka same su,sai nayi wata ban zo gidan Nan ba,dama Nima ba kaunata yake ba tunda aka kawo ni riko ka tsaneni,kwana a gidansa bana yi sabo da ba shi ya haife ni ba,matarsa duk kyan gidan Nan abinci wahala yake mata,badan ni ba da yanzu ta canja kamanni,dama shi yasa ake so mutum ya shuka Alkhairi in kaki Kuma duk sanda Allah ya Kamaka to wlh shike nan Kuma,yanzu gashi iya wannan ya isheka,ba duka ba zagi asirinka ya tonu a idon duniya,ga hakkin yaranka,hakkin matan daka zalunta,hakkin matarka ta sunna gani ni kaina Dan riko hakkina kadai sai yasa asirinka ya tonu,yanzu ni uwata zaka sakar min mu ware tunda ba sonta kake ba dama ga Rahma ta dawo ka aureta ka sakar min uwa wlh.

Spark yace wlh kuwa ka saketa kawai kanwar uwar mu a saketa mu tafi da abar mu,Rahma tace in aka saketa Nima bazan aure shi ba Dan Allah kuyi hakuri zai gyara halinsa sai mu zauna lafiya mu hada kanmu,Maman Rafeeq takaici ya kamata tace wato ita wannan kawai ma tunaninta aurensa zata yi ta shugo gidan sabo da so,ni na hakura da Kai Aliyu Sudan ka Aiko min da takarda ta sai na koma gidan Rafeeq,Rafeeq yace gidan Mima zaki zauna gidana bazai zaunu ba,gidana ba gidan zama bane Mama, mu kin San ba a rabamu da Uhum hum,daki ta shiga Aliyu ya bita Yana Bata hakuri ta fito da akwatinta.
Spark yace ni Ashraf na kashe auren kanwar babata yau mutafi gida kina da gata muje ku hadu ku uku a gidan Mima kwana Nan uwata zata tafi babban gida,Haidar yace ku tafi da ita wlh kar ta zauna karku yarda sai ya bata Jan kati uku.

Abba yace Dan Allah ku zauna,Kai Ashraf ku tsaya,suka tsaya Shima Aliyu Sudan din ya zauna ya nutsu Yana kwalla,Abba yace duk wannan abin babu abinda zai gyara ayi hakuri a tattara a yafi juna babu abinda ya Kai hakuri riba,Kai tunda kasan baka son matarka na mene zaka takura mata ka barta ta samu Wanda ke sonta,ka auri wacce kake so kaima shine zaman lafiya,da ka auri wacce kake so duk baza ta kaika ga aikata wannan cikin shegen ba,yace Nima iyaye ne suka hada,Maman Rafeeq tace Nima na tsane shi ba sonshi nake ba sabo da abinda yake min bana kaunarsa" kawai ya sake ni ya auri wacce yake so final

Jauro da Abba suka zauna suna ta sasanci Abu yaki yuwuwa,Maman Rafeeq tace ita tana jiran takarda,Ikhram tana ta kallon Haidar tasan tarihinsa yayi kama da Wanda akace sun hadu ta bangaren uwa,magana tayi tace Haidar Dan Allah a Gombe su waye danginka? Jauro ya karbe zancen ya bata labarin dangin tace to wlh shine cousin dina da babata da babarsa uwarsu Daya ubansu daya ita babata ta rasu a prison,ka kira Mamanka kaji,Haidar yace Kai karfa a dinga gayyato min Yan uwan da ba nawa ba sabo da ni Dan gaba da fatiha ne kowa sai yace Dan uwana nane,ya kira Mamansa tace Haidar kunje kuwa? Yace ae an gama komai zan Baki labari ga wata Ikhram wai yarki ce Yar gidan Sarah wai wacce ta rasu a prison,Maman Haidar harda kuka tana Allahu Akbar Allahu Akbar bani ita 'yata ce,Rafeeq yace to fa Yan uwantaka ta tafi tayi naso harda Ikhy dita.

Sun Dade suna waya da Ikhram,Jauro ya mike yace ku tashi mu tafi sauran bayani ya rage gareka Sudan in ka yanke hukunci ka tuntube mu,suka mike suka fice ya biyo su ya karbi number waya kunyar duniya ta ishe shi,Abba yace ba Sudan ba ko Makkah ne Kai ba ruwan mu.

Gidan Mima suka dunguma,Mima Taga sabuwar masifa Kuma again kanwarta itama wata ta afka wani hali,Mima tana Jin komai ta dinga salati tana sallalami,Mummy tace ni gwara ma na bar garin Nan na huta da wannan masifa,Arham yace saura kis ai jibi za a fara zama,tace zanci ubanka wlh,suna zaune Mufee ta fito cikin atamfa fitted gown ta zuba kyau gasu da kyau dama,Haly ta fito suka gaishe su Mima an koyawa yara gaisuwa,suna tafiya Haidar yace a ransa ba ruwana Ina Dan shege wa zai bani yarsa,kuje da kyawunku bazan so kowa ba,Jauro ya Kalli Haidar yaga Yana kallon Mufeeda,Jauro yace karka bada mu mana,Haidar ya fuske yace ni me nayi suna Kus Kus,Mufeeda Kuma su Haly anga zuka zukan samari harda nutsuwa,ana nuna halin kwarai.

Mima sai yau taga Baban Naila,tace Inshaallah zamu zo har gida a gaisa,Abba yace Allah ya kaimu,Papa yazo suka gaisa a ranar su Abba suka ce sai dai a kwana suka koma gidan Spark kafin su tafi hotel,Naila ganin su Jauro sun fita sai Haidar, Annoor,Iman Spark da ita tace amma a Nan zaki kwana ke Iman,Iman tace ae mana ai ni Ina Nan,Spark da bai San zance ba yace mata da Mijinta ki raba su Ina ruwanki wannan ai shishigi ne ko ke kadai kike kwana ke? Annoor yaji dadi yace so take ta rabani da ita yau Yana dariya,Spark yace a'a idan anan zata kwana Shima ya kwana anan,Annoor yace shine maganar gaskiya,Iman takaici ya kamata da bakin cikin Spark,tayi shuru tana fushi,Haidar Yana jinsu yace ni yanzu Yaya ne bazan ce komai ba kanwata ta rainani,kaji da shi dan iska cewar Annoor.

Naila ce tayiwa Spark rada tace Kai baka gane ba Baby hutawa fa zata yi ya dameta da naci baya bari ta huta shine zata kwana a nan yau,Spark baiyi kasa kasa da Murya ba yace to kawai sai ta huta? akan me zata huta?..Baki Naila ta rufe Masa da hannu,Annoor yace na gane kan zancen Kuma ai,ya leka fuskar Iman Yana dariya yace baki kuka hada ashe, Spark yace karka biye mata Dan Allah indai mata ne haka suka ke,kafin ayi abu suna wani nokewa ana farawa Kuma sai....Naila ce ta rufe Masa baki tana dariya tace wai mene haka Dan Allah ka kyale yarinya a barta ta huta,Annoor Yana dariya yace bamu zo duniya Dan mu huta ba,bauta aka turo mu muyi sabo da haka ita muke yi.

Washe gari tun kafin su tafi Aliyu Sudan ya nemi su Haidar ya sake Bada hakuri sannan yace dukkan abinda ya mallaka ya bawa Haidar Rabi Iman ma Rabi,ya dauki iya harkar business dinsa shi zai ci gaba da neman kudinsa amma kadarorinsa duk ya damkawa Haidar da Iman takardu kowa da nasa,Haidar yace shike nan na yafe Maka" Baba Dodar har lahira,Iman ita duk basu dameta bama iyayen tunda taji shirgin ba raga ta rabu dasu Uzurinta take to taji suna son juna duk da haka harda batun aure su cikin shegen ma bai dame su ba ta soyayyar su suke.
Yau suka koma gida yace zaizo har gida cewar Sudan.

Suna komawa Kuma Baban Annoor yazo shima Yana rokon Annoor ya yafe Masa Annoor yace tunda ka haife ni ta hanyar aure ai ni ka gama min komai na yafe ba abinda ka min wlh,yace to Yar uwarka fa Maryam ka yafe mata,Annoor yace wannan Kuma bata Isa ba tunda ta sa nayi Zina bazan yafe mata ba,yanzu da kanwata ce uwar daya uba daya da shike nan,sannan ta min asiri bazan yafe mata ba,aka buga aka buga akan Annoor ya yafe yace bazai yafe ba,Iman ma haka ya zugata yace wlh in kika yafe munyi hannun riga da ke,Baban Annoor yace Inshaallah watarana zaka yafe mata ne,Annoor yace to ban sani ba ikon Allah amma Banda yanzu bazan yafe ba.

Nabeel sai dai a bashi labarin abinda ke tafiya Yana gida abinsa wajen Hidaya Yana jinya,sai da ya daga mata kafa ta warke sannan ya sake nemanta ko hanashi Bata yi ba sai abinda yace da ita sai yanda ya juya ta,in yace kaza shi za ayi,tafi Naila Jarumta sosai bata raki,fitowa tayi daga kitchen da plate tana tafiya a hankali sabo da ta Sha wahala jiya a hannunsa,fitowa tayi tana kiran su Zarah Dan Allah su zo ace duk sun ki zuwa gidanta tunda aka kaita,Nabeel yace da kaina ma zan dakko miki su ai,Dan Allah ka dakko min su yara baza suzo suga Yar uwar su ba ana ta gasa mata Aya a hannu,dariya Nabeel yayi yace wacce Aya na gasa miki a hannu daka jiyar Dake dadi,Wahala dai ka Jiyar dani ta zauna a gefensa tare da Dora kanta a kafadarsa suna Hira.

Beauty ganin ba kowa sai ita a gidan ga gidan part biyu tsoro taji tace karfa ya karo kishiya yaga waje available ba komai a ciki,Chika ta kira a waya tace Chika nifa part din Hanan data bari Yana bani tsoro ya taba yin mata biyu kar yaje yaga fili a banza ya Nemo wata,Chika tace na dade Ina wannan tunanin tun wuri kisa a hade part din nan da naki tunda ba Nisa ki samo me zanen gida ya zana gidan yanda za a hade ya koma part daya kawai sai ki nuna Masa nasan zaiyi,ko baiyi niyya ba da yaga nonuwa ai shike nan,Beauty tace me kika Maida shi shike Nan daga yaga boobs wlh Kun Raina mijina ke da Naila,Na kusa haihuwa Kinga kafin na haihu sai a hade part din,Misam Yana jinsu suka sako labarin motar Naila da aka siya mata,bayan sun gama waya

Misam yace ke da Ikhram naga Kuna son motar Nan ta Naila ba ruwanku ku ko kishin faccalancin ma bakwa yi,ku dinga yi mana Dan Allah mu fara sasanci,ko sai Nan gaba zama yayi zama ne? ance faccalanci yafi kishiya masifa,Chika tace sai kace jahilai kowacce da Mijinta Kuma ko wacce muna da rufin asiri wa zaiyi wani faccalanci,Kun taimaki kanku Dan wannan abin takaici ne faccalanci a dinga kishin ko wacce mijinta daban ai aikin banza ne,kinji abin kunya ya fada gidan su Rafeeq Uwar goyon Rafeeq Kuma itama aurenta Yana ta karkarwa Yana rawa ,Chika tace naji labari Ikhram ta fada min Haidar dinma Dan uwanta ne,Misam yace Allah ya taimake ni na gama karuwanci na lafiya na fita lafiya daga Bariki,Chika tace daina zancen nan please, yace har yanzu in na tuna sai nayi nadama,Chika tace sahihin tuba kenan haka ake so nawan me Hallaren da Madara,murmushi yayi yace kwana Nan zamu dinga shiryawa Naila makircin Dani miji ni da Rafeeq,wannan gatan ya mata yawa ta mallake mana dan Uwa,Chika dariya tayi tace kunyi a banza.

Beauty kuwa me Zane ta samo kwararre yazo yaga gidan ya zana yanda zai koma ta biya kudade masu tsoka ta karbi zanen tace sai na nemoka,yace ba damuwa,sai da Mohsin ya dawo yayi wanka ya shirya yaci abinci suna kallo,hannayensa a cikin rigarta yana sarrafa na shanunta ta jawo zanen ta nuna Masa tace Kalli gidan nan da part dina da waccen part din a hade su kaga Nan wani corridor ne zuwa kofa,Kalli nan Palo,Mohsin yace wow yayi kyau ai yafi kyau ma gidan a haka,Beauty tace so nake kafin na haihu ka gyara min,gyaran ai kadan ne babu yawa ba wani kudi za aci da yawa ba,in da hali Please.

Mohsin bai kawo da manufa take so a canja tsarin ba,yace shike nan amma kin San na kusa tafiya Saudiyya ko,karka damu ai lokacin na haihu,wai ba kudi bane za a samu,ni bazan karbi kudin kowa ba da nawa zanyi amfani,lallai tun yaushe Naila tana ta kawo ajiyar dollars har ta hada kudin wajen 500usd tana Nan a ajiye Kuma zata karo wasu kawai kayi min ginin nan ba wani kudi za aci ba,in Kuma ba damuwa ni Ina da kudi zanyi,yace a'a bana son kwandalar mutum a gidan nan zan miki ai,tace thank you lokacin na haihu an gama,yace yeah za'ayi inshaallah.

Mummy bayan kwana biyu aka fara zaman kotu Spark kin zuwa yayi Sam,su Misam ne suke zuwa,lokacin Alkali rana Daya yake saurarar karar Mero da karar Haneef,kusan tare ake kawo su kotu,gidan yari sosai suka tsayawa Mero,sai da aka dawo kan batun Naila amma sabo da Spark ya gama biyan kudi in akace case din za a dawo da shi sai an kama Naila akan ta gudu daga gidan yari sannan Kuma ta shiga wajen Maza a suffar Maza shi yasa aka kashe case din,Mummy ko sharia bata wahalar ba ta amsa laifinta gaba daya har kashe mijinta da tayi.
Mima sai kuka suke yi sun San itama Mummy sai taje gidan yari,amma Mummy ita ta hakura ma ko kuka bata yi ta saduda tasan ya zama dole ta daure zuciyarta.

Duk da haka Alkali Bai yanke hukunci ba ya dage sauraron Kara sai nan da sati biyu lokacin zai yanke hukunci gaba daya,sannan ya Bada dama ayiwa Mummy gwajin kwakwalwa.
Mummy tace ni kalau nake wanne gwaji za a min Ina sane nayi zuciya ce ta kaini me yayi saura, Alkali ya gama Kuma ya zama dole tunda Mummy har an tsareta itama a layin su Mero.

Mero suna komawa ciki ta wuce makaranta ta dage sosai ba dare ba rana karatu take,Azima ta sameta tace ke Mero wai me ya sameki kamar me aljanun karatu,Mero tace tunda na samu na Sallah da sauransu ai na Kara da Ilimin zaman aure ko,ai Nan tarihin magabata nake bibiya naji Yaya suka yi zaman auren su na samu nayi koyi da su,nidai gaskiya hakurinsu yayi min yawa bazan iya ba uban kishiyata zan ci ba ruwana,Azima tayi dariya tace au nan Haneef din zaki aura? Mero tace Ras ma kuwa ai in kika ga ban shiga ba na kwana da shi a gado daya ba to Allah ne baiyi ba sannan ba Sunan uwata Jummai ba,ai Inshaallah sai naga Ijakala babu wando,Azima tace wayyo Khadija tana dariya tace Ijakala har kin riketa Dattijai ne fa suke fada a gidan Nan,Mero tace tafi min dadi a baki,taci gaba da karatunta na tarihi tace muje yau akwai tarihi,kina gani na kusa barin gidan nan shi yasa nake dagewa na koyi abinda zan koya,yau Malam ya shiga uku da tambaya duk abinda ban sani ba sai na tambaya.
Kwana wurin biyar Mero bata je wajen su Scola ba tana ta karatunta na addini littafan iri iri,da koyon wanka harda kwalliya dauri duk koyo take,indai Mero taga kin iya Abu to sai ta Allah ta dinga naci kenan sai an koya mata.
Su Spark kuwa bikin Kamal suka Sha aka gama lafiya.

Mero yau taje wajen su Scola,tana magana Goje yace I miss you,Mero tace tab zaka cuci kanka wlh dan na kusa barin gidan nan,Ina fita Kuma aure za ayi min ko gidanmu bazan zauna sosai ba zan kama gaba na,Balarabe yace a'a Dan Allah Khadija karki tafi zamu yi rashi,Mero tace kanwa na kawo kuci gaba da dakon soyayyar Naila Tantiriya,Jamilu Terror ko? Goje yace Allah sarki ai ko su Malam Sharu wlh karya suke suna kaunar Jamilu ba wani Imani,suna wani kasa kasa da kai karya suke son Jamilu suke,ana magana suna subhannallah Subhannallah,Scola yace Malam Garzali fa idonsa har ja yake sabo da kallon Naila Ina kallonsa Bai San Ina kallo ba,Goje da tausayi yace yanzu spark nasan ma yayi mata ciki,Balarabe yace ai ni gaskiya fatarta ta me ciki ce,Scola yace wlh tsabar Jin dadi ne sirrin 'ya mace na 'ya mace ne ni na gane kawai hutu ne ba ciki ba.
Mero kwana biyu bata Jin motsin Haneef sai da ya rage saura kwana Daya a yanke hukunci Mero taje tace to sallama nazo ko ka rigani fita ko na rigaka,ya alkawarina? Haneef yayi murmushi yace Yana Nan alkawarinki,tace to sai ka jini yace shike nan har kin tafi? tace ae karatu nake yi,yace bye ta furta bye bye ta fice.

Washe gari zaman kotu na karshe,gwajin Mummy na kwakwalwa ya nuna lafiya kalau take Alkali ya yanke mata hukuncinta na daurin shekaru Hamsim a gidan yari,Mummy tace kawai kace daurin rai da rai a shekaruna a Kara Hamsim ai bana raye wannan ai bakin munafurci ne ta furtawa Alkali kiri kiri,yayi shuru ya kyale ta,tace Kaine zaka ja kwana na zaka ce Shekara Hamsim kaima kasan karya kake lokacin bana raye,kawai in zaka ce daurin rai da rai kace za a mana iyayi,makarantar legal din da kayi,legal fa kayi,Alkali yasan zafin hukunci ne Suna Haduwa da haka Bai ce kala ba ,kotu ta wanke Mero fes aka sallameta,suka fito suna Murna,Mummy aka tafi da ita ciki,su Mima sai hawaye suke yi,Mero ta fito tace ko ciki baza ta koma ba gida zata tafi.

Dukkan dangin Mummy suka tafi ba Wanda ya kula Mero ciki,Spark bai zo ba ma sabo da kar yaga bacin rai dan zai iya kuka Mummynsa guda.

Mero fitowa tayi dama ta karbe ragowar kudinta dubu ashirin na asusunta tsayawa tayi jiran shari'ar Haneef tunda harda shi yau,ba a dade bama shi gaba daya aka kashe case dinsa cewar ba shi ya batar da yaro ba bincike ya nuna yaro Yana Lagos ma ya tafi neman kudi an ganshi a Lagos.
Tana tsaye sai ganinsa tayi ya fito shima,Yan uwansa sunzo,Mamansa ce bata zo ba amma mijinta yazo,suna ta tayashi murna,Mero ya kalla ya karasa Inda take Yana murmushi yace to sai a koma gida aci gaba da tace gasara da skirt,dariya tayi tace to yaushe zan fara aikin? yace in kin shirya ki min waya,tace to yace ashe dai kina da kyau,Mero tace da me ka dauke ni,ta juya ta fice,Shi kuwa mota ya shiga cikin Yan uwa suka ware,Mero Napep ta shiga ya kaita Tasha Inda zata hau motar garinsu,tana zuwa ta samu Napep har kauyen su ta shige.

Spark kuwa tunda yayi waya da Mima ta fada Masa hukuncin da aka yanke duk da ya San zai faru sai da ya shiga damuwa,Yana Office gida ya dawo jikinsa a sanyaye ransa babu dadi,Naila tana Palo tana danna waya ya shugo,ta ganshi wani iri tace wa ya taba min Mijina? Mikewa tayi tsaye ta rungume shi,kankameta yayi kawai taji Spark Yana kuka,Naila bata San an yankewa Mummy hukunci ba,sai da taji tsoro ta janye jikinta da sauri ta rike hannayensa tace lafiya? Me ya faru?
Baby mutuwa aka yi? yace Mummy ta tana gidan yari live in prison,Naila tace oh my God Baby I'm so sorry,Allah yasa wannan hukuncin ya zama silar shigarta Aljanna, Inshaallah baza ta Sha wahala ba ai VIP za a Maida ta ko? Naila ta sa hannaye ta goge masa hawayensa tace ai ba mutuwa tayi ba Baby,kullum in kana so zaka je ka ganta ko? Naila harda hawayen karya wai Dan ta nuna ta damu da damuwarsa, tace gobe ma zamu je ai ko duk abinda take so za a bata.
Rafeeq ne yazo gidan yace Spark kayi rashin Mamanka,tashi yayi ya haura sama kawai kar ma a dame shi zai iya yin kuka a gaban mutane.

Naila tace Kai fa kuka yake baka sani ba,Rafeeq yayi dariya yace Spark da kuka cab,sai kace ta mutu,waye yace tayi kisan Kai,abubuwa ma iri iri duk tayi Kuma yasan hukuncin nan mene abin kuka kawai shagwaba yake miki sabo da kina lallashinsa,naga mota Allah ya sanya Alkhairi,Naila tace Ameen,yace kin fa ishe mu kin kankane mana kayan Dan uwa,Dariya Naila tayi tace Dan bakin ciki sai dai ya mutu,Rafeeq yace zaki ga makirci,Misam ne ya dawo daga kotu yazo direct Shima wajen Spark.

Yace Ina Spark Dan wulakanci sai yaki zuwa,Rafeeq yace kuka yake Yana daki,Misam yace Allah sarkiyiyiyiyi...dole yayi kuka wlh tunda aka tsige shi a nono aka bata,Kai Spark yasha gata a duniya gaba daya Bata bari ya rayu a kasar Nan sosai ba,taje ta tare da shi a kasar waje yayi karatu ta sakar Masa kudi sai da ya zama me kudi ta ko Ina,Kai ku kyale shi yayi kuka Dan Allah.
Ke Naila sai na ganki a nan kije ki kwalbe shi wlh ras zai dawo karya yake,in ya Kara ko kwalla Allah ya bani abinda nake nema cewar Misam.

Naila tace space na bashi naga Yana bukatar a barshi shi kadai,Arham ne yazo yace Kuzo ku taimakeni,sai da ya basu tsoro sun zaci wani Abu ne,yace Papa ya kashe ni wlh ya zabo min wata aladiya Kuma wlh wai sai na aure ta ni ban isa aure ba,a fada Masa ban balaga ba,ya samu waje ya zauna ya zuba tagumi,Rafeeq yace Kai har gata ne da Kai haka sai an zabo Maka mata? Misam yace Kai ba dai wannan Basma ba ta kauye? Na ganta an kawota Papa yace karatu zata yi a Nan,Arham yace ita ce,wannan kucakar,wai na Kai Masa samfur din Naila wai ai yaga itama fara ce yo ni fari nake so Nima ai fari ne,yarinya sododuwa, Rafeeq ya sheke da dariya yace ya batun kudin? Arham yace na gagara ganewa kirjin Maza ne ko na mata,kawai an dakko min mata Maza,Misam yace a'a Arham wlh karya kake wannan yarinyar kace kawai Yar kauye ce zan yarda amma tana da komai me kyau wlh,Arham yace Kai nifa nono inchi inchi ba Wanda ban taba naji ba,ta ya za ace a nan kirjin wata Basma akwai shi,ai Kai Misam ka Saba Bariki kowa me kyau ce a wajenka dole kace haka,Ashar Misam ya dura Masa yace Dan uwarka ba na tuba ba Yar ubanka na taba yanzu.

Ai abin Yana jininka ni dai ku fadawa Papa kawai ya canja min wata,yace bazai canja ba ya riga ya sanar da iyayenta aure ba fashi,dama Kai Dan Iska ne Arham mata kake tabawa kirji? Arham yace duk Yan ajinmu kowacce naji nata,yanzu dai nayi aji class ne dani ba na kowa zan kula ba,amma ni wlh duk Wacce bata da shi bana so,ya zauna ya zuba tagumi,yace ni da nake so a samo min wacce kamar zan hau na zauna a kai sai a dakko min allo,kaje ka fadawa Papa mu ba ruwanmu cewar Rafeeq,Arham yace cewa yayi fa zai sa a kulle ni a guard room dole sai na aure ta ya Ilahi ni ba girma nayi ba,na mene ake gaggawa sai an kaini dakin aure.

Misam ya sheke da dariya yace kar ma a turoka Office dina aiki,ni da an bani jari zan tsaya da kafafu na me zanzo wajenka nayi,ni da Shaheed an bamu jari an kaimu kasuwa an gama mana komai farawa kawai zamuyi,yanzu koya ma mukeyi har motoci zamu dinga siyarwa,to kaje ka fadawa Mima ta rokar ma Papa a canja,Arham yace dariya take ta yi tana murna yanzu yarinyar ma kaunar ta take yi har da yi mata kitso yau fa,nidai Ina zan sa kaina bakina ya ja min.

Har su Rafeeq suka tafi Arham yace shi bazai koma gida ba yayi yaji,Naila tace to ai mu Nan akwai wajen zama Arham abinci Yana kitchen bari naje wajen spark kuka yake,Arham yace kuka Kuma? Sabo da Mummy? tace ae yace Dan Tani su jefar da mukullin gidan yari a teku,zanyi dai dan missing dinta kadan tunda Ina more cinyarta watarana,jeki kina bashi Uhumhum dinsa zaki ji luf wlh karya yake so yake ki bashi hakkinsa cikin sadakinsa,Naila tace Allah ya shirye ka ta haura sama tana dariya,Arham yace ga samfur an Kai sabo da idon Papa yayi shutdown shike nan sai ya dakko Basma daga kauye,kauye fa...

Naila tana shiga ta samu Spark a kwance yayi shuru Yana tunani cikin damuwa,a gefensa ta kwanta ta fara lallaba shi sai gashi ya bige da romance ya daina kunci...

AsmaBaffa
[2/18, 7:33 PM] AsmaBaffa: 🏫TANTIRIYA🏫
A GIDAN YARI

BOOK 3
~TAIMAKO~

21-25

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA AIDA MAMAN TASNIM

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.