Complete Hausa Novels

Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel

Reading file: Tantiriya_A_Gidan_Yari_Part_3_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 2 of 20

PAGE NAKI NE
Mariamsanee50

*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*

Dan Indo Yana zaune wajen abokinsa kasurgumin Dan iska ne ya hango Naila ya saki salati sai da abokin ya Kalli Dan Indo yace lafiya? Dan Indo Naila kawai yake kallo yace wayyo Jamila wannan tafi karfin Jamilu sai dai Jamila, mikewa yayi Yana kallon Naila ya taka suna tafiya ya Sha gabansu,ko Spark bai kula ba yace subhannallahi kayyasa Chau Allah dai ya biya,Innalillahi wa innailayhirrajun,walahaula Wala kuwwata haka kike da kafirin kyau ban sani ba Ina Nan mun zama kartan banza,Naila tayi mukus ita tsoro ma abin ya bata,Spark fuska ya tamke ya Maida Naila bayansa sai ga Goje ta baya yace Dahara....Spark yace wannan wanne shirme ne? are you out of mind? Kun San wace kuwa she is my wife,Dan Indo yace and so? Ina ruwanmu da aurenta mu Jamilu Terror muka sani a bamu abinmu muyi ciki,dama Ina nemanka Dan wulakanci shine kaje ka aure ta uban waye ya saka ka aureta? Spark yace ubanka ne yasa ni stupid,Kai in ba jahili ba matar wani zaka kula,Ya ja tsaki ya fisgi hannun Naila yace muje,Dan Indo ya tare hanya yace wlh ba Inda zaku je sai ka bamu abar mu,Naila tace zanyi magana Dan Allah please hannunta ya matse da karfi ta saki ihu sai da ya ja hankalin Mutane,Scola ne ya tashi Yana taku da sauri Yana karairaya yace wayyo kawata Yar uwata haka madarar Nido ta Maida ke wata fresh and Beauty,gaskiya ne ai kin samu ta me kudi wlh abinki Shar yo Yar Nan kullum kaji da kayan marmari ba dole a fitar da Madara me inganci ba ,Spark yana Jan Naila,laaa Tantiriya ga Tantiriya,Shege Jamilu Terror Kaine haka? washer ya tafi da gudu Yana Jamcy Jamcy kamar zasu cinye Naila haka suke yi,Malam Garzali daga nesa yace Allah ya sanya Alkhairi amma kin dauki hakkin mu,ragowar bujenki suna Nan muna kallo sun zama kayan tarihi,

Spark samawa kansa lafiya yayi ya Maida Naila bakin gate ya sata a mota ya shiga shima ya rufe,yace wannan ai sai su cinye ki duk ga mata nan ke kadai ce mace,Naila tayi shuru yace da ke nake fa,tayi shuru,yace wlh sai na sa an Kai Dan Indo dakin duhu an gana Masa azaba,Yana ta faman masifa Naila tayi shuru yace bana son raini,tace Kai fa kace nayi shuru kar na sake nayi magana sabo da haka nayi shuru.

Dan Indo sai ashar yake durawa a filin ana rirrike shi,Yana cewa Dan wulakanci da cin hanci yarinya Bata gama wa'adinta ba ta gudu Kuma gashi tazo ana kallo ma'aikata suna kallo,Kuna kallo baza ku kamata ku dawo da ita ciki ba,sai na tona asiri yau nine Nan na fitar da ita ni na sa ta gudu,sabo da ta auri me kudi Yana Baku cin hanci shine aka kyaleta,ai nine na gayyato yarana yan Daba suka bude wuta a bakin gate da su Goje ta ciki muka samu bulalai muka Zane kowa,muka hargitsa kowa ta fice a sanadinta mutane da yawa sun gudu yau na fada kowa yaji nine....

Nan take securities suka kama Dan Indo suka ce zaka yi bayani,aka yi ciki da shi,Goje yace tab Dan Indo ya kira ruwa zai ci ubansa a gidan yari sai sun kusa kashe shi,Scola yace Allah na gode maka da ka sa min basira na koma mace.

Spark kuwa Kallon Naila yayi ya ja Kwafa,sai da aka gama da Maza kaf suka koma sannan aka fito da mata,Spark ya kira Mero ta fito sannan suka karasa,Naila fuska a hade tana kishi da kyar tayi kokari ta danne,suka gaisa da Mero,Mero tace Naila Ashe kin San su Azima, Naila tace la na sansu amma a sanadin su Chika, ni Maza na sani a cikinsu na zauna a can muka hadu da my love ta furta,Mero tace kinyi dace Nima nayi dace,Naila tace ban gane ba,Mero tace to Nima Ina da nawa a prison,sai lokacin Naila taji dadi tace Allah yasa da shi za ayi kema in kinyi aure karki sake a Miki kishiya Kinga dai ni kiyi koyi Dani,Spark Yana jinta wai Mero take gayawa irin ta San mijinta ba aure zai Kara ba,duk ya gane hirar ta,a ransa yace Ina ma Ina da ra'ayin aure da na bawa Naila mamaki,Mero tana ji tasan ma da ita Naila take,ta mikawa Spark muficin da take sakawa tace gashi na iya? Spark ya karba yace sunyi kyau mashaallah na gode,tace nice da godiya,naso ace yau Innata zasu zo da ka gansu amma sun fasa wai sai gaba,kaga a ciki Ina zuwa makaranta na iya karatun Hausa yanzu na fara iya na turanci,ga addini,Kai na fara zama Malama yo duk su wankan haila,wankan janaba,wankan juma'a,Idi duk na iya ai inaga Nima watarana sai na bude makarantar koyarwa,Spark yace naga alama kinyi kokari sai ki dage Dan kin kusa fita an kusa fara shariarku,Naila kishi ya hanata sakewa taje ta kawo kayan da suka kawowa Mero harda abinci take away lafiyayye,ta mika mata tace mu tafi Spark na gaji kasan ba wata cikakkiyar lafiya gare ni ba,ta kankame hannun Spark mu tafi Dan Allah,ni mu tafi,muje gida kaina ciwo,tana Jan hannunsa,haka suka yiwa Mero sallama suka tafi ya shiga mota driver ya tuka su zuwa airport.

Yanzu muficin Nan ne ya dameta a ranta da Mero ta bayar" Spark yasan baza ta kyale muficin ba" ya bata a hannunta sabo da ya huta da kishin Naila,suna zuwa gidan ta wuce da muficin bedroom dinta,kasan bed ta wulla su kawai tace shegu baza ayi fifitar ba,muna da Ac,ai tunda hannun wata ne ya saka ba me amfani da Kai har duniya ta nade, muficin ma ko kyau,in banda Maita ma irin ta sarakai mene abin so a nan,naga dai Spark ko me unguwa basu gada ba a danginsu bare ace, tsaki ta ja ta shiga safgarta.

Washe gari Spark yace Ina muficin nan mu gansu na Mero,Naila tace naga dai ko me unguwa baku gado ba wlh ba me amfani da shi a gidan nan,na Kone shi ato kaji ka sani,dariya yayi a ransa yace ki dakko min abina,Naila tace wlh akan muficin Nan in banyi yaji ba Allah ya tsine min,sai nayi yaji na tafi gidan ubana,na gaji da ci min fuska da kake yi Ina Maka Kara da alkunya baka gani,mene bani da shi Wanda Mero ta fini,harda hawaye da kuka,Spark ya bude baki yace wai ke tsakani da Allah kishin Mero kike? Ni wlh ko sunanta ka kira gaba faduwa yake bana son zancenta bana kauna ka daina min ahhhhh....har da kururuwa kamar ta zare,Spark yace,to na daina ke Naila haka kike da kishi,yanzu idan nace aure zanyi fa,baza kayi ba...baza kayi ba Inshaallah daga ni sai Kai mutu ka raba takalmin kaza daga nan har tsufa, dariya ta bawa Spark,tace ba abin dariya bane ba a dariya a sharing din Hallare wannan ba abin dariya bane,ni bana wasa da harkar kishi,ta fututtuke sai kyaleta yayi.

Yana Office Yana so ayi aiki ya tsare Rafeeq ya zauna a Office din ya sashi gaba,Rafeeq yace Abu ba Kara ba mutunci,Spark bai kulashi ba Yana ta danna wayarsa,Ikhram ce take ta faman kira,Rafeeq ya Kai hannu zai dauka Spark ya rigashi yace yi aikinka zan kular ma da ita,ai wlh gwara ka koreni na koma wajen Misam na gaji da wannan takura,ace waya ma bazan yi ba,Spark wayar ya daga yace aiki yake fa madam,Ikhram taji Muryar Spark tace a ranta Allah ya so ni banyi subutar baki ba shi yasa ba a so daga daga waya baza ka tsaya Kaji mutum bane sai ka fara sakin zance.

Gaisawa suka yi Yace Yana jinki Rafeeq din,bana ji bazan yi magana ba idan baza a bani waya ba to Yana danna system Yana magana,Dan Allah kayi aikin Nan ba a tura ba har yanzu sabo da su na shugo Office banyi niyyar fita ba,ni wlh gwara ka koma wajen Misam din ma na kawo Arham ko Shaheed better sai kace yaro da matarka da komai aiki sai an tsaya a kanka haba Rafeeq,Rafeeq yace wai ba gashi Ina yi ba,to ci gaba yau sai yamma ba hutu,sai gaf da break Ikhram ta aiko da abincin basket guda,Spark yace Inye kaga masu mata,Rafeeq yace Kai muga naka,ai kasan ana kawowa nine nace kar a kawo yau kaga ma bata Dade da yin bari ba hutawa take,to ga Abinci nan in kana ci,Spark yace ai ni duk Inda naje yanzu bana iya cin abinci da yawa sai dai kadan maganin yunwa In na koma gida banci nata ba akwai matsala hanyar lafiya a bita da shekara,Rafeeq ya dinga dariya yace tsoro kawai kake ji Yaya,Spark yace banyi kuri ba ai ta cancanta a ji tsoronta,Rafeeq ya zuba abincinsa Yana cewa Yaya Anya kuwa Ikhram ba ciki ne da ita ba,Spark yace tooooo...yanzu aka ce har ta samu ciki da na bani sabo da Allah Ina wani amarci da na ci.

Spark yace duk watannin da ka kwashe,Anfi 4mnths Ina laifi ai ka dangwali arziki,Dan tayi ciki mene a ciki ai sai tafi dadi ma kana hauka,Rafeeq yace Kai inaga ciki ne da ita Allah Kare ni bana so yanzu,baka so kaje kana kwanciya da ita, Rafeeq yace to gani ga Allah amma yau bata son kamshin kaza gobe Yalo zata ci,jibi tace wancen abincin ma ta daina ci ko ta dafa sai irin wannan ciye ciyen,ga masifar son sex,yanzu yau hakkinta ka dauka ka rikeni a Office ,Spark yace ta Nan ka bullo uban wa zaka yiwa wayo,tayi ta cikinta ba ruwana,Rafeeq yaji dukul a ransa yaso yaci nasara ya gaji,yace ka taimaka min Yaya Dan Allah,wlh ba Inda zaka sai 5pm ka gama aikinka.

Basu tashi ba sai 5pm sannan ya kyale Rafeeq,basket dinsa ya dauka ya nufi gida abinsa Yana shiga Ikhram ta tarbe shi ta rungume shi yace yau Spark ya kusa halakani yau mine,fuskarsa ta shafa tace kayi hakuri ai nema ne muje kayi wanka ka huta, daukanta yayi suka shiga bedroom,wankan ma itace ta tayashi ya gama shiryawa cikin jallabiya ruwan Zuma,tace abinci fa? Yace na koshi sai anjima ya haura Saman bed ya kwanta Yana hutawa Ikhram ta hau yi Masa tausa daga tausa ya fara bacci tace nifa ba bacci nace kayi ba,I think i need you,Rafeeq ya bude Ido a hankali yace Anya ba ciki ne da ke ba kuwa wifey, yau ya kika yi da bana nan? Ikhram tace na Sha wahala sai addua nayi,Dan Allah ka tashi muyi,Rafeeq ya zaro ido yace da kin bari nayi bacci na tashi zanfi samun nutsuwa,Ikhram tace to yi baccin zan jira,ya koma ya fara baccinsa ta tasa shi gaba kamar mayya tana ta kallonsa tana kallon agogo.

Minti talatin tana cika ta fara murna tace lokaci ya ja,tana zaune a tsakiyar gadon a gefensa tana kallonsa kwanciya tayi ta shige jikinsa tana ta Allah Allah ya tashi itama tayi baccin,har magriba ya rigata tashi ma,ya tashe ta yace lokacin Sallah yayi ya wuce masallaci,bayan ya dawo abinci ta shirya musu suka ci suka koshi sannan suka fara Kwalbewa abinsu,Ikhram yanzu bata gajiya,jinta yake kamar sabuwa ta Kara sweet shi yasa kullum sai Kara nacin masifa,ko bata nema ba sai ya kunnata bare ma kullum a cikin bukata take.
Washe gari sabo da Spark yaki kunna wayarsa bai fita ba,Spark har gida yazo daukan Rafeeq yana mota driver na tuka shi,yasa me gadi yaje yace Rafeeq ya fito,Rafeeq daga wanka ya fito ya shirya a gurguje ya fita Yana cewa a kawo Masa breakfast Office,mota ya bude ya shiga Yana fushi,Driver ya ja suka tafi.

Abba kwance yake a katifarsa ta shago Yana Jin radio,Kubra ta leko tace kaji kunya wlh ko ni mace bazan yi wannan lalacin ba,Abba yace na zaci ma zuwa kika yi ki tayani kwanciya nafi Jin dadin auna hatsi,bazan zauna a benchi ba ga zafin rana so kike cutar rana ta kamani na dinga kashin majina wlh bazan yi ba,bazan zauna a rana ba sai Rumfar kwano me shegen zafi,ke yanzu ba ci gaba bane a Ganni a killace a cikin shago amma a rumfa kowa Yana kallona tsirara iska tana bushe ni da rana,idan ana ruwan sama Yana min feshi,Nan kuwa a cikin sutura,Yar Inna ko dai kin daina so na nane ban sani ba? in kin daina kaunata ki Fadi gaskiya sai na Kara aure babu Bata lokaci,naga kwana biyu wani gani gani kike min,Kubra tace me yayi zafi daga magana daya,yace to kija baki kiyi shuru, dubu biyu nazo karba,Abba yace to ana sana'a Kuna korafi sai Kuma a baku-a baku gashi ya mika mata" ciki ta shiga ta samu buhun Masara ta zauna

Abba yace ahhhh....ta mike da sauri Dan taji tsoro ma yanda yayi yace abincin ci ne fa ki zuba Masa wannan mazaunai ai ba tsari tashi gaskiya in baza ki zauna a katifa ba ki tafi gida,Kubra tace bazan tashi ba wlh na zauna,Dan Allah ki dawo Nan Kinga Sha wuya ya nuna mata katifar da yake zaune,tace bazan dawo ba a nan zan zauna.

Abba ya kalleta harda harde kafa yace to ya soyayya ta Yaya tunanina ? Dariya Yar Inna tayi ba shiri ka fa girma ka daina irin wannan ka barwa su Mohsin,Abba yace sabo da sune mutane ni ba mutum bane soyayya ba tsoho ba yaro kowa ya ji da tasa ai bakya kunyar ciki sai soyayya,in ciki ne yanzu zaki ta amai a gaban mutane ki ta asarar abinci kici ki amai,Bai fa kamata na yafe miki ba da aure na kike tafiya wajen gardawa amma na yafe miki Dan Kinga nayi shuru da zancen Ina sane,dariya Kubra tayi tace rana tana yi bari na tafi girki zanyi,Abba yace ke rabu da girkin nan yau a siyo abincin, mu nawa ne kwata kwata a gidan zauna muyi soyayyar mu,Yar Inna tace dama na gaji wlh,Abin nema ya samu Abba yace ba shegen da zan siyarwa ko da gero ne bazan siyar ba yau tunda kika kawo min ziyara,Kubra tace a gida fa muke wannen shagon a Jikin gidanka yake Ina wata ziyara a nan,Abba yace duk da haka idan ba haka ba duk Wanda ya siyi kwano Daya biyu zan bashi,Kubra tace a'a ai gwara karka siyar ni tafiya zanyi,yace kina tafiya zan rufe na dawo gida.

Jauro ne ya kira Abba,ya daga yace hello" kana magana da Hubby,Abba yace waye Hubby? Hubbyn ubanwa kamar wani Dan Daudu ni bana Daudu Allah ya tsare ni,Jauro yace Kai dalla daraja na Kara na samu Karin suna,ai duk suna Daya in ka samu Kari to darajarka ta karu,Amaryata ce take fada min,Abba yayi dariya yace to sai aka yi me? Kai dadi kake ji nufinka? Karya take" fada tayi Dan kaji dadi wannan lokacin soyayyar an wuce lokacin ka gama abarka da Habiba tun da jajayen sawunka,itama ta gama soyayyarta da me Yalo uban Annoor ka daina murna Jauro,ni kaga nawa kowa yaji yasan ba karya a ciki Abban Mohsin Kuma ni na haifi abina akwai wani shege da ba ni ba,Abban Naila, mutane suce mijin Kubra,Yar Inna in soyayya ta Kai mata tace Dan siriri na kaga duk ba karya siririn ne ni,Kai kuwa wlh ka kiyayi Hubbyn nan da gemunka da furfura a dinga fada Maka Hubby ko dacewa baka yi da Sunan ba,ai gwara me gida ma ya fiye Maka.

Jauro yace bakin ciki kake min Hashimu na gano ka,ni ban San ma wanne kuskure ne yasa kazo a abokina ba,gaba daya abota da Kai kaddara ce ma,Hashimu yace to ya zaka yi Dani baka da kowa sai ni sai na zo cin girkin Amarya,Jauro yace Dan Allah kazo kaji dadi,Kai kaga wani Yankan salat me sifirin kamar ba hannu ne yayi ba yir yir yir indai yanka kayan lambu ne a barwa Ruhina,Abba yace ita Kuma Habiba fa mece? Jauro yace ita zuciyata ce Amarya Kuma Ruhina an barka a baya ka zauna da mace daya tilo kullum Kubra Yar Inna wai Dan Allah baka gajiya? Abba yace ka ganta tana jinka tana shagona zance tazo ma yau nace ta huta mu soye bana gajiya da abata ko? Abba ya Kalli Yar Inna,murmushi tayi tace Jauro ta Allah ba taka ba inshaallah baza a min kishiya ba,in naga dama sai na raba abotar taku,Abba yace wannan Kuma kinyi karya karki mike kafa dai ba a bawa namiji Amana Nima ba wata Amana zan rike ba ko yaushe zaki iya Jin kishiya ta taho" karki yarda dani bani da tabbas,Kubra dai tana jinsu suna ta surutu.

Misam ne ya Kai Chika asibiti daga Nan ya kaita gidansu,Kamal suka samu da Spark a kofar gida suna ta hira da tsare tsaren bikin Kamal da za ayi Nan da sati daya,Misam ya budewa Chika mota ta fito ko kula su baiyi ba ya sa Kai zai wuce,Kamal yace Amma baka da mutunci yaron nan,Misam yace to Kunga real namiji sai na tsaya Ina kula ku Kai baka da mata a kwararo kake kawai,shi Kuma wannan yayi auren Dan cikin ma ya kasa ba rashin kunyar da basu yi ba an kawo Amarya amma ni zuwa daya kawai har ta karba,Dariya Kamal yayi Chika ta gaishe su, Spark yace masu ciki gashi Nan duk kin dashe mu kuwa dama karkar muke ko da shi ba a ganewa,Misam yace wlh a'a kasan dama ba Wanda ya isa ya kirata da baka ato,matar taka fin ta wani tayi,Spark yace Allah ya baka hakuri masu Hallare da Madara,Chika tuni ta wuce ciki tana dariya, Misam yace Ina Rafeeq? Yana Office na bashi aiki yanzu ma wajensa zan koma nasan halinsa yanzu sai ya tafi gida.

Annoor yau Iman taci sa'a ya kyaleta ta kwana lafiya,suna zaune Jauro ya kira Annoor yace Ko me kuke ku bari muje asibitin mahaukata Maman Iman ance ta dawo hankalinta,Annoor yace to bai fadawa Iman ba sai yace ta shirya suje gidan mahaukata su gano mamanta,sai murna take yi ta shirya,Annoor bayan ya shirya ya saka Shadda wata sky ya zuba kyau harda dora Yar hula a Saman kitsonsa yace zanje wajen surukata tunda ta warke ai taga surukinta kamili,Kansa ya kalla a mudubi ya juyo ya Kalli Iman yace ya kika ganni? tace Kamilu Sunan wani,dariya yayi yace tambaya nake nayi kyau please? tace to Kai akwai ranar da baka kyau ma ai kullum kyau kake yi,mudubi ya sake lekawa yace wow Allah yayi kira,dariya tayi ta ture shi tace kalle ni fa,me zan saka ne ma na sutura? Yace Abaya,ai kuwa ita ta zabo wata maroon Egyptian ta saka tayi kyau sosai kamar a sace ta.

Suna kamshi suka fita shi ke driving a wata sabuwar motarsa da ya siyo,Kawu suka dauka suka tafi can.
Suna zuwa aka kaisu wani daki na daban,sannan a kirata ta fito sanye cikin riga da zani na atamfa har da Hijab,kana ganinta kasan yanzu da hankalinta,shuru tayi tana kallon su,Nurse tace gata Hajiya ki musu magana su suke zuwa dubaki,Jauro yace sannu tace yawwa Dan Allah ku su waye ku kaini gidanmu,Iman farin ciki ya kamata,Maman Iman tace ni Yar kauyen Libiya ce tallan maganin gargajiya ne ya kawo mu kasar Nan da iyayena,Jauro yace zauna Dan Allah ki nutsu ki bamu labarin naki ko zamu San Inda zamu kaiki.

Zama suka yi sannan tace sunana Rahma,Jauro yace yawwa ko kefa Rahma suna me asali,taci gaba Babana sunansa Mahmood tun Ina karama ya rasu,Mahaifiya ta ma Ina karama ta rasu a wajen kakata na girma wacce a kauye muke da zama,tana bada maganin gargajiya,tana amfani da Aljanu,kasa kasa muke zuwa,watarana muka sauka a Nigeria a Daji muke zama da dabbobin mu shanu da rakuma,akwai wani bawan Allah Dan asalin Sudan ne zai wuce Abuja ya ganmu a hanya ya tsaya ya karbi maganin haihuwa a wajen kakata,ta bashi yace Yana so na sai tace baza ta bashi ni ba ya nace a haka dai sai da yasan inda muke zaune a Daji.

Watarana yazo wajena ya samu Kakata bata Nan ya bani wani abinci me dadi da nama tunda na ci ban sake sanin Ina nake ba Ashe magani ya bani yayi amfani dani ya lalata min rayuwa,Sai da kaka ta dawo ta sameni cikin wani hali na fada mata komai amma sabo da taurin Kai Ina sonsa yana so na tace baza ta bashi ni ba,ni Kuma nace tunda Hakan ta faru ai gwara kawai ya aureni a huta,shi Kuma dan Sudan Marwan kenan yayi min haka ne Dan Kaka ta bashi ni ya aureni amma taki yarda.

Ana nan watarana na dinga kuka nace wlh sai na bishi mun gudu,tace indai na sake na bishi sai ta Sa Aljanu sun haukata ni,ban yarda ba watarana muka hada baki da shi muka gudu ya dauke ni a mota,kwana daya tsakani na fara ciwon hauka ban San Inda kaina yake ba,da kansa ya dawo dani wajenta,ranar da ya kawo ni ranar Kuma ta bawa wasu Yan fashi magani sun gwada bai musu ba suka dawo a ranar a gabana suka yiwa kaka Yankan rago suka fece,har a lokacin bana gane abubuwa da dama hankalina ya fara barin jikina,daga nan nidai ban sake sanin Inda nake ba sai yanzu da Allah yasa na warke jiya kenan.
Jauro yace iKon Allah to ko dai Marwan din Dan Sudan shine uban yarki? Tace wa? Ya nuna mata Iman ya kwashe labarin komai ya fada mata,Rahma tace ya kamanninsa suke? Jauro yace Yana da haske dogo yana da gashin Baki goshinsa da tabo,Rahma tace wlh shine masoyina nane Ina sonsa har yanzu a Abuja yake zaune cikin gari yanzu Ina zan ganshi.

Jauro yace Yan uwanki fa? tace bari tukun wannan duk suna Libiya Kuma ma duk sun tarwatse bada magani yanzu burina a Nemo min Baban wannan da kuka ce Yata ce,yanzu wannan 'Yata ce?Jauro yace yarki ce gashi Nan Kuna kama ma,Iman sai murna take yi tace Kinga mijina surukinki ne wannan ta nuna mata Annoor, Annoor yace Ina Kwana harda kasa da Kai.

A ranar aka gama komai aka sallami Rahma suka wuce gidan Habiba aka Kai mata ita ta zauna a nan,sai Iman ake tayawa Murna.
Jauro yace Haidar ya shirya dama za aje wajen ubansa mahaifi a Abuja sai a tafi da Rahma ko za a ga uban Iman a can,Habiba tace ya kamata a bari ta murmure sai a je.

Mahaifin Annoor ya dawo daga US ya samu Yarsa Maryam tana cuta ta gaske an rasa dalili ta rame ta fike,ga wasu kuraje da suka cika mata jiki kamar me Karzuwa ba kyan gani,komai sai anyi mata,haka mahaifiyarta ba maganin da bata karbo mata amma shuru,yace Maryam me ya same ki haka? Maryam tana kwance Saman bed tana kuka ta kwashe komai ta fada Masa,salati yayi yace ai gashi kinwa kanki,Dan uwanki ne shashasha,Allah ya Baki lafiya amma abinda ya sameki kin cancanta ya same ki,bani address din Annoor din,tana numfarfashi ta bashi tace ga wayata Nan a jaka akwai number dinsa ciki.

Hanif zaune yake a dakinsa Yana Shan yogurt da Dan wani spoon na roba yaji dadinta yace Inama wannan Khadija din tana Nan a bata ta Sha taji,a fili yace to Ina ruwanka da ita wai,Mero ce tayi magana tace hello ta sake daukan Karfenta taci gaba da bulawa sosai yanzu ta Burma wajen yanda hannu zai iya shiga guda Daya tace Hakan ma ya isa.

Hannunta me kyau ta mika tace Yaya Hanif Inama sunana Hanifa sai aka sa min Khadija,Babana da kyar ya yanka min ragon suna ance sai da nayi Shekara uku a duniya aka yanka min Kuma wai Yar tinkiya ce ma,shi yasa ma akace bani da kan gado sabo da tinkiya aka yanka min,Hanif ya kwashe da dariya yace wai ke Dan Allah mene birgewarki Dan kin fada,bakya gajiya da surutu a rayuwa,Mero tace ai gaskiya ce dole na fada,yanzu gashi Ina ta koyon yanda zan kame harshe na,tsohon skirt ma da muke tatar Koko da shi ai an Dade yanzu da dankwali na muke yi,ai an samu ci gaba,Kuma da wlh kwandon wanka da muke saka soso da sabulu daga bandaki ake dakko shi mu tace taliyar mu muci Kuma gani lafiya kalau ba ko malaria,Kuma mu bama banbance botikin wanka Dana aikin gida sai muyi wanka da baho mu fito da shi mu kwaba danwake a ciki mu zilillika abinmu.

Hanif yace gaskiya ku kazamai ne,Mero tace ai na waye yanzu tunda aka kaini aikatau na gane komai,da naje ganin gida baka Gani ba yanda na dinga cin gyaran Innar mu,tasowa yayi yazo Inda ta fasa tace Miko bakinki kiji,Mero ta cuno Baki ta cikin kafa tace wlh bakina karami ne karka min kiss wallahi Allah ni bana son Kiss yanzu,ban shirya Shan yawu wani ba,ba a haifi Wanda zan Sha yawunsa ba ni ba Yar iska bace nidai,Hanif tsaki yaja yace ke me zanyi da bakinki baki da hankali,ko wacce zan aura kafin ta mutu ban taba mata kiss ba,Mero tace Alhmdllh Rabin wata ne,Khairat ba rabo ba tana murna tace gaskiya ka fado duk wayewarka ka bari ta koma ga Allah haka ko da yake ba rabo ba.

Share ta yayi Yana jinta tana dariya Spoon din ya sa ya ebo yogurt din ya miko ta kafar Mero ta bude Baki ya zuba mata ta shanye harda zaro harshe tana cewa wash dadi...dariya yayi yaci gaba da bata tana ta sha a haka,Mero kasa kasa tace na sace zuciyarsa saura furta I love you,Azima ta duba ko Ina Bata ga Mero ba dakin ta duba ta samu Mero manne a Jikin bango ana Miko mata yogurt tana Sha tana Santi.

Azima tace Mero me kike yi haka? Mero hannu ta daga ta baya tace ciyar dani ake yi,shi dai Hanif bai san me suke yi ba Azima tuni ta ture Mero ta mika nata bakin yaci gaba da antayawa Azima itama a baki,Mero tace Kai Hanif Kalli labbanta bakake bafa ni kake bawa ba Azima kake bawa haka labbanta suke bakake? Sai lokacin Hanif ya duba da sauri ya janye yogurt dinsa,ya hau masifa kin cuceni kin Bata min lokaci,Mero tace rashin fahimtarka ce amma ai ka dinga kula,Hannu Mika ciki tace ungo,Hanif ya kama yatsanta yaji Laushi,yace ke a haka Yar aiki ce? to gona nake zuwa me ka Mai dani so kake kaji kamar bayan kada,Hanif ya dan rike hannun Mero yace Bismillah zunubi a kanki,dariya tayi Azima tace Dan Allah kizo mu tafi.
Hanif yace wai Ina ruwanki ne kiyi tafiyarki kin takura mata fa,Azima kike ko wa ki shiga hankalinki.

Azima ta juya ta fice Hanif yace Khadija ya kirata a nutse,ta amsa Masa yace ki dinga zuwa kullum zan koya miki rayuwa naga baki Santa ba,ya zaka ce ban San rayuwa ba gashi Ina cikinta kace ban sani ba,Kaine ma zance baka San rayuwa ba tunda Kai kana da kudi rayuwar kudi ka sani,ni da muke talakawa mu muke cikin rayuwa,yace baki gane nufina ba,tace to zan dinga zuwa ai inshaallah.
Bayan kwanaki Mero kullum sai taje sunyi hira sun hade hannu waje daya ta Yar kafa wai kawaye ne.

Spark gajiya yayi yace wai Baby har yanzu Jinin Bai dauke bane wannan bari ko masifa,haba sabo da Allah sati biyu ai nayi tawakali,murmushi Naila tayi ya Dade da daukewa tace bai dauke ba tana ta faman gyara kanta,sai da taga ya damu ta tsokane shi tace bai dauke ba,Spark yace ya Ilahi in ba Dan iska kike so na zama ba ya dauke haka mana,ni ba a halicceni nayi hakuri da Bado ba,ba hakurinsa nazo duniya ba wlh in zai dauke ya dauke kawai,Dan Allah ni a bani haka,Naila Ido ta zaro, yace wlh na gaji ni na gaji,Naila tayi dariya tace ya dauke fa yau,dama dazu nake cewa zan fada Maka,Spark yace da Ina da hanci da nayi guda,Allah ya miki Albarka a bani kar ya dawo ko labewa yayi ban sani ba gwara nayi abina.
Kaya ya shiga cirewa Naila yace a gidan ma sai an toshe ko Ina,Ina ta so nayi sabon ciki ba hali,sai kace yau aka kawo Masa Naila gidansa yanda ya wani susuce ya zauce.

Naila tace ka nutsu please,Ina zan nutsu yanzu ni bani da nutsuwa,Naila tace haka kake baka da nutsuwa yace ae Ina naga wata nutsuwa ni dama ba nutsatse bane,ai idona idon Boobs ko bado to sunana mahaukaci lokacin,Naila tace amma iya nawa ko? Spark ya tsokaneta yace harda uhmm ..uhmm..harda...uhmm...Naila tace bana mood,dariya yayi yace ai kin sani kema ko munyi fada ba abinda zan canja,ki kalleni so na ya miki yawa,Naila tace Allah ya kiyaye,yace handsome Irina,komai haduwa,ga kyau ta ko Ina Hallaren ma me kyau ga iya Uhum,ga sarrafa uhumhum,ga umm...uhmm,dariya suka yi sosai,Naila tace shi yasa nake sonka wlh Dan Allah karka min kishiya Dan girman Allah Ina rokonka Dan Spark dina,Dan nishadin Nan bazan iya gani an raba shi ba.

Arham ne ya shugo da mota Yana parking ya shiga ciki Yana fushi Mima ya samu da Papa a Palo suna hira ya shiga ciki yayi Sallama zai wuce,Papa yace zo nan,wajen Papa ya nufa yace me aka yi Maka ne? Yace kawai a waje ne,wai Papa wata kwaila ce daga ganina ta zageni,Papa ya zaro ido yace Kwaila? Arham yace to dai ta fara kudi kadan,kudi sun Dan fito mata,kawai ta zageni bafa cewa nayi Ina sonta ba ko kulata ma banyi ba wlh wai dalla Dan iska,Kuma tazo ta bangaje ni.

Mima tayi dariya tace to ba sai ka rama ba,na Isa na rama kasa ramawa nayi ta min kwarjini Yar mitsil da ita Kuma Baku Gani ba wlh Kuma taci banza ko gobe na ganta bakina kanin kafata,Papa yayi dariya yace to ko da ita za ayi ne? Allah ya kiyaye wannan banda kunya me zata yi,Au baka son kunya kunya ai ado ce,a'a ni bana son me kunya nafi son tsagera,Papa yace Allah ya shiryeka Arham yace Ameen ni Papa in kaga tsagerar ma ka samo min,Papa yace ka bani zabi? Arham ya zaci wasa yake yace ae,shi kuwa Papa dadi yaji an bashi zabi yace karka damu sai ka yaba yace to ko wace zan so ta,kayi alkawari? Arham yace Inshaallah Yana dariya,Papa yace an gama jeka ya wuce.

Masu sharhi Ina godiya

AsmaBaffa
[2/15, 9:48 PM] AsmaBaffa: 🏫TANTIRIYA🏫
A GIDAN YARI

BOOK 3
~TAIMAKO~

11-15

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA AIDA MAMAN TASNIM

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.