Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel
Reading file: Tantiriya_A_Gidan_Yari_Part_3_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 7 of 20
Page naki ne
Oum Aariz
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LAizQA6PofSLoFhQ7XeaQx
Ina kuke masu burin suga sun kawata gadajensu da hadaddun bedsheets? Ko Kuma blankets kike nema? Masu aurar da yara ko kannai da ke kanki uwargida indai kitchen utensils kike bukata
To kukanki yazo karshe.kuyi joining group din R&U exclusive kitchen and more
Ku more wa idanun ku da kayan kitchen Yan yayi na gayu da zannuwan gado na kowanne kasa Zaki samu acikin farashi Mai sauki
Kuma Maza Bata barku abaya ba idan Kuna bukatar a hada muku lefe nagani na fada na amarya Kona uwargida wato na fadar kishiya duk Zata hadamuku acikin kwanciyar hankali.idan ma akwatunan kawai kuke bukata duk inkuka tuntubi Rumaisa zaku ganewa idanuwanku
Tana Kano state Kuma Tana tura Kaya kowanne state afadin nageria harma da kasashen da muke makwagtaka dasu
Zaku iya tuntubarta ta wannan number
07034559202
Ihsan tana zaune tana sake sake,Haneef ya gama cin abinci kenan zai haura sama yaji Muryar Mamansa,Juyowa yayi yace Mamana ashe kina hanya,Hafsatu tace ae dama cewa nayi in nazo ka ganni,Ina sa ranar zuwa na kasa,Akwatin kayanta ya karba yace sannu da zuwa muje" ta bishi sama,daki ma yace Mama wanne kike so ko na bar miki nawa na canja wani,tana dingisa kafa sabo da tana dauke da ciwon kafa tace baka da dama Haneef Allah dai ya Maka Albarka,yace Ameen Mamana,Ina matar taka ne? tana daki bacci take maybe,tace to mashaallah suka shiga bedroom ya ajiye mata akwatinta,ya durkusa tare da gaida ta tana zaune gefen gado,yace wanka zaki fara yi mamana? a jirgi na taho yanzu nayi wanka bazan sake yi ba,yace to abinci fa? tace uhm ai ku girkinku na turawa ne ni nafi son na gargajiya da zan samu tuwon shinkafa miyar gyada taji Alayyahu da yakuwa ai da nayi farin ciki,yace sai ayi miki yanzu dama na kawo sabuwar me aiki,baki ganta ba Mama nutsatsiya,Mama tace dama a kasar nan yanzu akwai nutsatse? Jinake tsadar rayuwa tasa kowa nutsuwarsa ta gudu,babu sauran nutsatse a kasar Nan,Haneef Kai dai indai mutum a kasar nan yake kawai ayi sha'ani a rurruma a zauna da hakuri amma batun nutsatsu yanzu babu kowa a fusace yake rashin mutunci yake tatawa.
Dariya Haneef yayi,tace ya matar taka ta gyara halin kuwa? Yanda kika sani ba abinda ya canja amma kisa Ido zaki gani da idonki,Mama tace Allah ya shirye ta,Haneef yace an bani shawara ma na Kara aure kawai,Mama tace bazan hanaka ba Allah dai ya tabbatar da Alkhairi amma ni bana son aure auren nan,yace Ameen,tashi mu koma Palon kasa ta mike tana cewa wayyo Allah kafar Nan dai har yanzu ana ta magani kamar ba ayi ko ya nayi tafiya sai na gaji,an hanaki cin Jan nama sai kifi sai kaza,wlh watarana Karya doka nake,kasa ta sakko suka zauna,Salamatu ta fito ta gaisheta ta koma kiran Khadija,a daki ta samu Khadija tana gyara kaya tace ki fito babar Oga tazo ku gaisa,Mero tace to jeki zanzo,tana tafiya Mero ta dakko zanin kodaddiyar tamfarta ta daura tare da canja riga t-shirt ta fito a Yar aikinta sak ta fito.
Tunanin Haneef kar Mamansa ta ga Khadija da shiga me kyau idan Ihsan tayi korafi ko me tace yarda zata yi,farin ciki yayi ganin Khadija a shigarta ta Yan aiki,yace a ransa wannan tasan me take,Mero ta karaso ta durkusa da uban ladabi ya gaisar da Mama,ta amsa tace ke Kuma ya sunanki? Khadija Mero ta furta tana murmushi,daga wanne gari? Khadija ta Bada amsa tace mashaallah gaki kuwa da nutsuwa,Mero ta sake yin kasa da Kai,Sai ta birge Mama,tace na yaba da hankalinki gaskiya a kula da aiki sosai,Khadija tace to Inshaallah,yawwa tuwon shinkafa zaki mata miyar gyada da yakuwa cewar Haneef,tace ai ba yakuwa yanzu gashi dare yayi bare a siyo,to shike nan ki mata miyar gyadar da ganye kawai tace akwai Ugu sai ayi mata miyar gyadar,Mama ta furta a sa kifi banda Jan nama,to ba damuwa Mero ta mike ta nufi Kitchen,Ihsan ce ta fito Taga Mama,murmushi ta saki ta karaso tace sannu da zuwa Mama,Har gabanta tazo ta durkusa har kasa ta gaishe ta.
Mama tace Kuna lafiya ko? Ihsan tace lafiya muke Mama,Haneef ya kalleta kawai suka hada Ido,Baki ya tabe ya dauke Kai,me zaki ci Mama na dafa miki? mama tace an sa Yar aiki ma,Ihsan tace haba Mama aikin me nake yi ni ban fiye son Yan aiki su min girki ba a gidan nan,Haneef mamakin karyar Ihsan ya kamashi,Mama a ranta tace wato Haneef karya yake min dan kawai basa shiri ne shine yace bata kula da shi ai gashi na Gani da idona.
Mero tana kitchen tana girkinta,Haneef ya shugo kitchen din kamshinsa ta ji a bayanta ta kafadarta ya miko kansa tare da yi mata rada a kunne kina da hankali Khadija,kin gane Mama zata iya fahimtar wani abin idan Ihsan ta fada mata ko me zata yarda amma a haka Kinga shike nan.
Juyowa Mero tayi tana murmushi gwiwoyin hannayenta Yana Sama kusa da gas da wuka a hannunta,Ido ya zuba mata sosai yana karewa surarta kallo,Mero ma shi take kallo,me kike yi? Ya tambaya,tace girkin Mama,uhmmm ko zaki koya min? me zai hana kawai ka kalla yanda ake yi,yace Alright tare da harde hannayensa a kirji Yana kallon Mero tana girki.
Tunda ta fara aikin ita yake kallo ba yanda ake girkin ba,ita Kuma sai bayani take Masa,tace yanzu yanka min albasa mu gani,Yana can ya kura mata Ido tace ka yanka min Albasa nace me kake tunani? dawowa yayi hayyacinsa yace sorry me kika ce? ka yanka min Albasa zo na koya Maka,yace kin San a kayan aikin nan ma kyau kika yi,Khadija tace Dan Allah? Yace t-shirt din ta miki kyau,na gode ta furta tare da mika Masa wuka tace kaga yanda zaka yanka haka,kamar haka to fara,fara yi yayi a hankali Dan bai iya komai ba,Kayi kokari gaskiya kawo ka gani,ta rike hannayensa da wukar a hannunsa suna yankawa a haka,dariya yayi yace na iya daga yau wow,Ihsan ganin shuru yaki fitowa ta shugo kitchen din,a zabure fakat da sauri ya dauki wani cup ya basar ka rantse dama shi yazo dauka tuni ya matsa daga kusa da Khadija,agogonsa yake gyarawa ga cup a hannunsa,Mero Kuma tukunya ta bude itama tuni a zabure a tamanin itama ta fuske,har goshinta take sosawa sabo da babu gaskiya,Ihsan kamar ta gansu manne da juna amma sai Kuma taga kamar idonta ne ya mata gizo,kallon su ta hau yi sosai tana so ta fahimci wani Abu amma sai ji tayi Khadija tace Oga kawai ka bar naman nan yayi kaga bai dahu ba ka daina jira in yayi zan kawo maka,Kallon Khadija yayi lokacin ta dago Kai suka hada Ido"Ido daya ya kashe Mata tare da murmushi,labbanta ta tamke tana mannewa kar ma tayi murmushi.
Ihsan anci da rabonta tana danna waya tana dagowa har sun gama ya fice abinsa,Mama ya samu tana kallon film,Ihsan kuwa Mero ta kalla tace munafuka yanzu wato Kinga uwarsa kin saka kayan aiki,Mero tace Daya muke bakya girki ko cokali bakya dauke wa kince bakya so Yan aiki suyi miki girki,me take so zaki dafa mata ni Kuma Kinga Ina da kayan gayu na canja nasa na aiki,wlh kina fadar Abu a kaina sai na tona miki asiri yau kiyi karyarki da kika Saba kawai Nima nayi tawa,Ihsan ta Kalli Khadija tace karfa mayya sarkin naci an Kore ki kinki tafiya,na tsane ki Yar Zina,Khadija tace oho miki Kuma.
Khadija sai da ta gama miyarta gefe daya tana tuka tuwon danyar shinkafa,shugowa Haneef ya sake yi ya bude fridge ya dauki lemon gongoni,ya sake cewa kawo na gwada tukawa ya ajiye lemon a gefe,ta bashi tana murmushi Yana farawa yaji tafiya kamar mutum na tahowa sakin muciyar yayi ya dauki lemonsa ya juya baya a zuwan budewa yake,Ihsan ce ta sake biyo sawu ta ga me yake yi wai.Khadija bata kulata ba haka ta gama girkin ta kaiwa Mama,taci itama sai yabawa take yi sosai.
Mero ta dawo ta gyara wajen bayan ta gama ci tace Mama kina bukatar tausa? Mama tace a'a Yar nan na gode kawai dai ga magani na shafa min a Kafafuna,Haneef Yana zaune Khadija tace Oga ga aikin Lada kazo ka samu Ina Maka fatan samun wannan ladan, tashi yayi ya karbi maganin,Mama sai murmushi take yi tace kaji yarinyar kirki me Ankarar da bawa hanyar samun lada,murmushi Khadija tayi,Wallahi kin birge ni Kuma duk Wanda ya aure ki yayi dace Khadija,Haneef da sauri ya tambaya yace Allah Mama? tace duk Wanda ya aure ta ya samu macen kirki,Ihsan tana gefe baki ta tabe ta dauke kai,Mero tace Mama na gode za a miki wani abu ne? tace a'a an gode jeki uzurinki yarinyar kirki,Mero ta shige dakinta ta dinga sheka dariya tana tsalle a Saman bed tana cewa na ninke Mama bata Yar iska bace ni,babu wani ta gari,wai nice nutsatsiya dama ba Tinkiya aka yanka min ranar suna na ba.
Washe gari Arham kin fitowa yayi Sam kar Basma ta ganshi ta fada tace ya taba ta,Basma kuwa tunda ta tashi take zuba Ido ko zata ganshi ita hirar jiya tayi mata dadi kwana tayi tana tunawa,Mima ta tambaya a Palo tace Mima tana Sosa Kai,Mima tace ya aka yi? tace dama jiya ya manta abinsa zan bashi Kuma ban ganshi ba,Mima tace bai fita ba ai Yana nan zai fito ne,naje na Kai Masa? Mima tace a'a ki bari ya fito,tace to ta zauna,Maman Rafeeq tana zaune tace karki sake naga kafarki a part dinsu ba a zuwa wajen namiji ki dinga taka tsantsan,Papa ne ya shugo da alama fita zaiyi ya samu Maman Rafeeq suna yiwa Basma fada karta je part din Maza,Mima tace ki bari ya neme ki da kansa,yaran zamani sai addua kuwa,Basma tace ai kuwa sai dai kar a Kuma jiya zip ya bude min yace kwaro ne a ciki wlh ya taba min kirji na,Amma karki fada Masa yace kar na fada,Ran Papa ya baci yace yanzu auren da za ayi Masa bazai iya hakuri ba,Basma tace ba haka bane ba fa yace kar na fada Dan Allah kuyi hakuri na yafe Masa nidai,Papa ya fusata,Mima tace Dan Allah kayi hakuri,yace ba ruwanki a gabanki yarjejeniya muka yi da shi da sharadi idan ya sake sai ya bar gidan Nan yace ya yarda,Kuma yanzu ya Maida ni dan iska,Mima tace to yanzu in kace ya bar gidan Nan Ina zai je? Kuma wa zaka yiwa auren? Papa yace na fasa bashi ita sai ta auri Shaheed shi ya bar min gida.
Mima ranta ya baci tace yanzu...dakatar da ita yayi yace shi yasa suka gagari kowa,ke baza a yiwa yaranki fada ba baza a hora su ba,ya isa in zauna inyi yarjejeniya da shi sannan ya sake gwadawa shi din banza,Ina Arham ya tambayi Haly da shigowarta kenan,Yana part din su,yace kira min shi maza,ai Arham Yana ji ance papa na kiransa yasan ba lafiya,Haly tace da alama Basma ta fada Masa,Salati Arham ya saki Wanda ke shiryawa wanka yayi dama,yace guard room zai sa a sani ko ya kaini Barack a gana min azaba,Haly tace wlh kayi ta kanka Kai kasan ba iya korarka zaiyi ba kasan kalar korar Barack za a kaika kayi sauri na bude ma kofa ta baya,Arham ya kwashi takalma a hannu Suka fice a hankali ta bude Masa kofar kitchen ta baya yabi ya fita,ta waccen gate din na baya ya bi ya bar gidan Yana fita Papa Yana kiran securities sojoji yana bada sanarwa a rufe gida kar a bari Arham ya fita.
Suka kulle ko Ina suka hau zaga gida da bindigu,sama ko kasa an rasa Arham,Haly tace na duba ko Ina baya nan,karya kike papa yayi kanta da jibga,Basma ta mike ta gudu tana cewa nidai bakuwar ce kar a hada dani ta arce daki,Haly da kyar ta Sha a hannun Papa ta kulle kofa tana kuka,Mufee tace Allurar Papa ta motsa ta sojoji,Arham kuwa Spark ya kira ya fada Masa,Spark yace me kayi to? Yace Basma fa kawai na rungume,karya kake Arham wlh idan baka Fadi gaskiya ba bazan rufa Maka asiri ba duk Inda kake sai an Nemo ka,Arham yace to abin na taba,Kuma wlh ni kawai ji nayi akwai ko babu ba da iskanci nayi ba,shine ta fada,Spark yace tab yanzu karka je gidan abokai Dan za a bika kana Ina? yace gani a taxi? zo Office dina kayi sauri,Arham yace na tabowa kaina masifa nonon Basma ko Masifa,Yana zuwa" Office din Rafeeq Spark yakaishi ya sa key ta baya ya kulle su har Rafeeq a ciki,Rafeeq yace ni a bude ni na tafi gida, ni ba da iskanci ba a kulle da ni,Spark bai ko kula shi ba.
Rafeeq ya Kalli Arham yace kwarto,Ka taba me tsada yau dubunka ta cika,Arham yayi dariya yace bana dana sani Kuma ban Jin na gama tabawa, samun lafiya a daura auren nan,an lasa min zuma,yace wai Shaheed zai bawa ita,wlh bani ba Shaheed matukar ya karbi auren nan mun raba gari,Dariya Rafeeq yayi yace daga taba abu,yace ba haka bane,ai cin fuska ne wannan a bani mace ace za a canja ai ba daidai bane,ni har naji ma Ina Jin haushin Shaheed din.
Rafeeq ya Kalli Arham yace baka Jin magana Arham,muga hannun ya canja tunda an Sha Laushi,Arham dariya yayi yace Kai da ka kwana a gidan surukai wa yasan me kayi, a gidanmu kowa Yana da abin fada ba Wanda zaiwa wani gori tun daga kakanni manya har yaran,Rafeeq yace Allah? Kaka Zeenatu ma karuwanci tayi,ai ance shahararriyar Karuwa ce da,harda kasa kasa da Murya yace Shima Maleek din ai a can suka hadu a Bariki suka yi aure,Rafeeq ma yayi kasa da Murya yace Allah Kai? Allah da dadironta ne ya aure ta daga baya,ta nace masa ai ance Zeenatu tayi Zuma ta more,duk Wanda ya dandana sai ya koma ta tara abin duniya da Bariki,Misam ne dai da ya shiga shi haka ya fito ba uwar komai sai nasa da ya kashe,Ashar Rafeeq ya dura Masa yace Dan iska munafuki duk a Ina kaji labarin nan Kai? Suna dariya Arham yace zancen duniya Yana buya ne,Mamanka ma uwar goyonka ai ance tayi Uhum Uhum kadan,Wlh zan tona ma asiri Papa yazo ya tafi da kai.
Papa kuwa yasa aka dinga neman Arham basu San Yana Office ba har gidan abokansa kaf sojoji sunje ba a ganshi ba,aka je gidan su Spark duk an bincika baya nan,Mima ranar fushi tayi da Papa ko kulashi bata yi ba.
Sai dare Spark yazo ya bude su,Rafeeq ya fice yayi tafiyarsa gida,Arham suka tafi da Spark gidansa.
Naila tana Palo tana dariya ganin an taho da Arham,Naila tace to Ina kayan sawar? Na mijinki zan saka,kaga dai ka jawowa kanka kana zamanka lafiya,Arham ya ce ya zanyi nazo a dan gidan Soja,yanzu in ba Soja ba wa zaiyi haka,to ya Basma din? Na San mata shegen baki kamar na tsuntsu,Allah ya kaimu ayi bikin sai na saita mata bakinta wlh,sai na ladaftar da ita Yar iskar yarinya,Naila tana ta dariya tace ga abinci can,yace ni zan iya cin wani abinci ne hmm ya mike ya shige bedroom.
Wanka Spark ya fito Yana danna waya Naila ta shugo yace wai dollar ta sake tashi,Naila ta sheke da dariya tace ai dollar a kasar Nan Bata San Inda zata tsaya ba,anjima ta tashi anjima ta sauka,Naira Kuma tayi haka Naila ta lankwashe kafarta tana dingishi tace Baby kaga Yar Gurguwa to haka Naira ta koma,Dariya Spark yayi yace ta karye baras,kamar a kasar Nan aka kirkiri dollar,ya kamata dollar ta koma kasarta ta gado.
In kina so Kiga murna sai kin hadu da mutane baka San halin da ake ciki ba?,kice me dollar ta karye ana washe baki ana baki labari,anjima kadan dollar done High,Kuma ko wanne farashin kaya ya karu,Yan kasuwa sun rasa hankalinsu basu San me suke ba,yanzu ka mika kudi bani kaza ance Dari uku kana komawa anjima za ace dollar ta tashi dari biyar,har yaushe ya siyar da kayan suka kare ya dakko wasu,Naila tace ni da nake so in na haihu a yanka min sa da raguna to dollar tana ta hauka ya kenan? Spark ya kalleta yace wannan yaron na cikinki wai shi zan yankawa sa? Tunda aka same shi yake bani wahala ai Yana zuwa zai ga tsiyar Uba,dariya Naila tayi tace amma fa nayi kokari har yanzu ban fadawa kowa Ina da ciki ba,Spark yace karki fada rabu da kowa in ya fito sa gani kar ayi Masa baki kambun baka ya kama shi a haifo shi Dolo,tunawa yayi da Sunan surukinsa ne,Naila tace cin mutunci,yace sorry ba haka nake nufi ba,zata fara fushin yace Dan Allah yi hakuri,yi hakuri yi hakuri,yanzu sai Naila ta fara fushi ba gaira ba dalili.
Bayan wasu kwanaki Beauty an hada mata gidanta chas,an gama furniture ta zuba musu na gani na fada,gashi ta shiga watan hauhuwarta ma,suna Palo Mohsin ya rike Beauty tana motsa jiki irin na masu ciki yanda aka koyar da su a asibiti,Beauty ta rike kugu suna dariya tace wlh na gaji,riketa yayi tare da zaunar da ita tana yatsina tace Marata ciwo take,to ko haihuwar ce? Murmushi tayi tace Edd ma sai Nan da 25days zai cika,da saur.....mararta ta rike tare da dauke wuta duf Bata sake magana ba sai da aka dauki minti daya taji ciwon ya saki,Mohsin Yana kallonta yace ya dai? Ko a kira Umma mu tafi asibiti? Ai na daina ji ma na warke,okay haka nake so.
Kafin ta rufe Ido ciwon ya dawo da karfinsa tace Kai muje asibiti gaskiya ciwon nan ba na sauki bane ban taba Jin irinsa ba,sakkowa tayi kasa ta rike mara,tashi yayi yace tsaya na duba ki idan haihuwa ce sai mu tafi asibiti,da kansa ya duba ta yace to nidai haihuwa na gani,wayar Umma ya kira ta daga,yace asibiti zamuje ki shirya zan biyo na tafi dake Beauty ce Bata da lafiya kamar dai haihuwa ce,Umma tace to,Bata fadawa Hashimu ba kar yace zai je,tana shiryawa ta barwa Zarah karamar Yar ita muka fito,a shago ta samu Abba tace zanje unguwa,ko tambayar Ina baiyi ba yace a dawo lafiya Allah ya tsare ki siyo min tsaraba,murmushi tayi ta wuce.
A gefen titi Mohsin ya dauketa suka nufi asibiti,Beauty tana salati a hankali tana cewa Allah ka zama gata na,Allah ka dafa mini,Allah ka sa min hannu a lamari na,Allah ka dafa min....a haka suka Isa asibiti,Mohsin hankali a tashe ya manta ma Umma tana wajen,zai fito da ita a mota sai rungumeta yake Yana cewa I'm sorry ni na jawo ko? Umma ta tace Dan ubanka ka matsa ka bani waje,Beauty tace jeka kayi min addua kaji,bazan iya tafiya na barki ba,Umma tace Mohsin zan bar Maka matarka na tafi wanne irin iskanci ne wannan,Karki yi fushi Umma gwara dai Ina ganinsa cewar Beauty.
Gado aka bata,sun dade tun yamma suke asibiti tana Shan wahala,Beauty sai da haihuwa tazo ma'aikata suna wajen suna cewa yi Nishi...push....Beauty Bata ganewa sosai a wannan halin amma Taga yara ne Yan mata mace daya ce babba,tace a karance kuka gani Shegu Yan iska shi yasa kuke cewa nayi Nishi Ina naga karfin Nishi yanzu ni,baku San aure ba bare haihuwa kuce na dinga nishi,kawai Kunga Abu a rubuce kuzo ku dameni Nishin uwarku....tana Jin ciwo tana bala'i tace ban San me yasa Mohsin ya jawo wannan asibitin na Yan koyo ba,duk Yan koyo ne a ciki basu iya komai ba gashi Nan da wani asibitin ne da tuni na haihu,dama tunda aka sa Masa suna Aminu Kano teaching hospital,teaching ne fa na Yan koyo ake nufi ai bazan haihu da wuri ba,duk yara sun dameni ni,wayyoooo.....Ma'aikaciyar dattijuwa tace haihuwa tazo amma Kinga Yar iskar yarinya tana matse kafafu za fa ki kashe danki,Umma tace daina zaginta wahala ce ku har abada a kasar Nan bakwa girmama mutane,sai ku dauki mutum kamar wani Dabba,da iliminta wlh ta fiki Ilimi ma,kice ta gyara sai ki zage ta,Allah wadai da halinku wasu ma'aikatan lafiya marasa Imani mutum Yana wani hali Kuna zaginsa da hantara,sai lokacin likitar tayi shuru taji Umma ta fita masifa.
Umma ce ta taimaka itama a nutse har aka samu Beauty ta haifo Danta namiji katon gaske, duk abinda ya dace anyi mata ita da jaririnta suka canja mata dakin hutu,Mohsin ana masallaci Yana ta addua Bai San ta haihu ba,har sai da Umma taga wajen 11pm sannan ta kira shi a waya tace ta dade da haihuwa fa Ina ka shiga, Alhmdllh ya furta yace tana lafiya? lafiyarta kalau gashi har Hidaya sunzo ma abinci take ci,fitowa yayi da sauri ya je dakin,a zaune ya samu Beauty tana cin faten doya Wanda Hidaya ta kawo,tare da Iman suka zo, Annoor ne ya kawo su, Mohsin sai murna ake taya shi baki yaki rufuwa an yiwa Amal kani,addua yayiwa Jaririn sannan yace an fadawa Naila? Umma tace Naila ka iya tunawa kawai? Murmushi yayi yace itace besty na,ban fada mata ba kuwa,Kiran Naila yayi yace kinyi da Your love ya haihu,murna ta fara tace me muka samu? yace me Hallare,dariya tayi tace Allah yasa ba Yar mitsil bace,ni ya gado ai,Kai Yaya ko kunya,Mohsin yace ke kika koya min ai, wa ya kaiki iskanci, kasa hakuri tayi tace zan fada Maka wani sirri karka fada tukun ciki ne dani ya kusa wata uku,Mohsin dariya yayi Jin Naila har rada rada ake fada,congrats kunyi kokari,Naila tace na gaske ma idan ban samu ciki ba kamata yayi a kama Spark ayi yamma da shu'umi kawai,dariya Mohsin yake sosai yace baza ki nutsu ba Naila,Naila tace to magana ta Allah baya hutawa da Kwalbewa Yaya ai idan ban samu ciki ba kawai ayi can da shi Inda ake cin mushe,Naila tana gama wayar ta juyo taga Sparka a bayanta wayar ta Maida kunnenta tace ai Dan Albarka ne ayi gabas da shi,Allah dai ya Masa Albarka Ina sonsa wlh,mijina ai duk duniya bani da kamarsa.
Dariya Spark yayi yace ba laifinki bane Dana nane yake min zai zo duniya ne Allah ya kaimu,zanga me biya Masa school fees,Arham ne ya fito har yau yana gidan Spark Papa yaki hakura an kwashe kwanaki.
Naila tace gobe su Basma zasu zo gidan Nan inji Mima,Arham yace Allah ya kawo su ni Ina ruwana da ita,Spark yace tana sonka fa wlh yarinya Mima tace tunda aka Kore ka ta kasa sukuni kullum sai taje Wajen Papa tana cewa ta yafe Maka a dawo da Kai,rannan ma kayanta ta hada tace zata tafi tunda dai ance Shaheed za a bata,Arham yace ita taga duhu wa yace ta tona min asiri,duk abinda za ayi da Yar kauye sai ta nuna hali yanzu da Yar birni ce waye ma zaiji kullum sai na taba kuji shuru Kuma kamar na biya sadaki amma dake ita ba a abin arziki da ita sai kuka wayyo ya taba min Dan iska sai na fada
Naila tace a Yan kauyen ma taka ce haka Arham mu ba muka yi ba,Spark ne ya dingure mata Kai yace ka fadi Alkhairi ko kayi shuru,wannan cikin harda tone tone yazo,Arham yace au har anyi sabon? Naila tace tsokanata yake,Arham yace ni Ina ruwana ko cikin ne ma,Spark yace ciki ne da ita Arham almost 3mnths duk fushin nan da take yi da fada ai duk cikin laulayi take,Arham yace Allah ya raba lafiya,Spark yace Ameen wlh na matsu ta haihu na gaji da wannan mood din da take shiga,yanzu aka fara fa cewar Arham,kafin ta haihu nasan sai na dawo tsinke sabo da rama cewar Spark,dariya suka yi,Naila tace ya batun business din naku Arham? Shaheed ne yake ta aikin business din ai muna waya.
Mima dai tace in Arham yayi tafiya baza ta damu ba ko kiranshi baza tayi ba amma kullum itace take fara kiransa,a rana sai ta kira shi yafi sau uku,yanzu ma kiransa tayi ya daga yace kika ce idan nayi tafiya ko nema na baza kiyi ba amma gashi yanzu kullum ke kike fara kirana,Mima tace ai ba wani missing Dinka nayi ba kawai dai Dan na tabbar da kana gidan Spark dinne kar ka tafi wani wajen,dariya yayi yace to na gode Ina Nan ai,ya fara hakura ai Basma tace zata bar gidan ta tafi baza ta hada Da da Uba fada ba,shine ya sakko yace ka dawo gida gobe,Arham yace ni nafi Jin dadin nan ma sai abinda naga dama a nan,to dai in ba so kake ka sake bata komai ba ka dawo gobe yace,Sai dai mu taho da Spark,to koma dai mene ta kashe wayar.
Washe gari da wuri su Basma suka zo,Arham Yana bedroom abinsa Yana kwance Yana danna waya,Yana Jin surutun su,Basma taji ance yana nan amma bata ganshi ba,gajiya tayi tace Aunty Ina Arham din? Naila tace Yana bedroom waccen room din,Basma ta mike taje ta kwankwasa yace come in,ta tura kofar ta shiga,Ido ta zaro tace bleaching kayi? Naga ka sake haske,wlh saurin girma ne da Kai kwana nawa da barin gida amma har ka Kara girma,Arham yace me zaki ce dani kin Sa an Kore ni daga gidanmu,a gefen bed din ta zauna tace ban zaci haka ba ganin Kuna abinda kuka ga dama na zaci baza a Maka komai ba shi yasa,amma ai gaskiya tana da zaki Kuma tana da daci ko baka yi ba? Baza ma ki bani hakuri ba? Da kayan sata ka kamani da zan baka hakuri,nifa mijin Naila shine dai dai ni dai dai shekaru na ba Kai ba Dan ma ka samu Ina kula ka,alfarma nake Maka fa,Arham yace na gode zaki San kina min alfarma, dariya tayi tace hmm ta mike tace na tafi,tashi yayi ya mike ta ganshi da tsayi tace kana zuba saurin girma a duniya,kullum sai ka Kara tsayi,ki bari sai an daura aure ki fada min haka.
Fitowa suka yi Yace kar a zargeni tunda ni yanzu na zama abin zargi a wajen mutane akan nono,abinda ma kowacce tashi tayi taga ya fito ba roka tayi ba Taga an bata shike nan sai a damu mutum sabo da anga mu bamu da shi sai mata su dinga wulakanta mu.
Sai dare su Basma suka tafi tare da Spark da Arham,Arham sai buya yake a bayan Spark Yana cewa Papa ko bai hakura ba wa ya sani wlh Allurarsa ta motsa,part din Papa suka shiga matan suka wuce bangarensu,Papa Yana Palo shi da Mima suka shugo,Arham yace Ina yini barka da dare,Papa yace zo nan Arham,Arham ya ja da baya yaki zuwa,Kazo nace rigar Spark ya rike,Spark yace baza ka sake ni ba,Dan Allah Papa kayi hakuri wlh bazan sake tabawa kowa ba nayi alkawari,dama wannan ma sharrin shedan ne ji nayi an ja hannuna ban San dalili ba,bana cikin hankalina nidai kawai sai Jin Abu nayi a hannuna ban San komai ba,please Papa dama ni shedan ya dade da yi min fitsari a ka,amma yanzu zan dage da Azkhar na Kore shi,Papa mikewa yayi yace zaka ga shedan ya Maka fitsari a ka,Arham ya rike Spark zai gudu,Papa yace ai ba abinda zan Maka ni,da zan Maka da tuni nayi tunda nasan gidan da kake kyaleta kawai nayi,ruwa ya dauka ya zauna,Spark ya fisge rigarsa ya zauna,Yana cewa Papa kayi hakuri mana haka ya tuba bazai sake ba cewar Spark,Arham yace wallahi tallahi in sake tabawa sai na halak,baza kayi shuru ba kenan? Mima ta furta,shuru yayi ya zauna a gaban Papa Yana bashi hakuri,Papa yace ai na daina yi Maka fada Arham na gaji,Arham yace a'a Wanda ya rasa mafadi ya shiga uku ai sai na tabe,Kaci gaba da yi min na daina wlh,dama rashin hakuri nane amma Shekara biyu Ina Shan na uwata,Yaya Rafeeq ne ya zugani yace kar na bari kaina ya kulle Shima haka yayi,Misam ma Yana wajen lokacin yace Shi da yayi Bariki ma ya tuba ba abinda ya faru da shi bare ni,shine na kama zancen su suka kaini suka baro ni,to sarkin karya cewar Mima,tace haka fa ya fadawa Basma yarinyar da zata zama surukata yace wai ni na zuga shi ya aikata mata haka,Papa yaso yayi dariya ya boye yace ai Allah ya Kara tunda bakya son laifin su,Arham gobe yaushe? Yace Friday ka shirya gobe daurin aurenka,idan aka daura daga baya ayi bikin sai a Kai Maka Amaryar,Arham yace a bari Papa in aka gama shiryawa sai ayi bikin a Kai Amarya lokacin kaga maybe na fara sonta,baka sonta ka taba ta,Spark yace gaskiya a bari sai an gama shiri wannan sai a kaita tana laulayi,Arham yace a'a da kunyata ni ba ruwana da ita ni,Papa yace na gama shiri wlh gobe ana Sallah za a daura yanda nace haka za ayi tunda shi baya Jin magana.
A daren Umma ta fadawa Abba cewar Beauty ta haihu,Abba yace amma kin ci amanata da baki fada min tun wuri ba, Kubra wlh watarana in kika yi min wani abin sai naji kamar na ambato kakanki Sarkin gandu Tanimu na zage shi,Yar Inna tace ai ka riga ka zage shi Kuma tunda ka Fadi Sunan,yace da Kuluwa me Kwan zabi,dariya Kubra tayi tace sai kazo ta kashe wayarta,duk kakannin Yar Inna ya ambata, minti kadan Abba yazo asibitin.
Ya kalli Mohsin yace ya suruka ta lafiyar ta kuwa? Mohsin yace tana ciki zaka iya shiga,Abba yace o'o'o Yar Inna ce kadai zata shiga wannan dakin na gumurzu na iya shiga kowa ya ji da tasa tunda dai lafiya take shike nan in ta fito na ganta,ya kira Jauro yace kayi jika na biyu Jauro,Jauro yace Matar Dan namu ta haihu ne? ta haifi Da namiji,yace Allah ya raya tunda lafiya take ai anyi arziki,gobe zamu zo Inshaallah. Washe gari aka sallami Beauty fes da ita da Baby,direct gidan Umma aka kaita in tayi sati biyu sai ta koma gidanta.
Abba yace wai nan aka kawota? wato mu a bata mana gida su Kuma su koma nasu gidan fes wannan ai wayo ne,kunci darajar babban bako me sunana,tun lokacin Abba ya bawa jariri suna Hasheem,ya kankane yace sunansa za a saka Masa,Mohsin yace dama ai sunan zan saka da mace ce Naila zan sa my love,Abba yace ai dama nasan sai ka mayar da sunanta itama haka Allah ya muku Albarka ya sake hada kanmu gaba daya,Mohsin yayi dariya yace harda Kai? Ku iyaye ai dole Kuna son mu ba matsalar komai mu yara mu za ace Allah ya hada kanmu,Abba yace harda ni mana idan na fandare fa na daina yi muku addua ai kaga gwara ace harda ni kanmu ya hadu,Mohsin yace to shike nan Ameen Yana dariya,Abba yace Azo a shiryawa Me jego farfesu suruka zata ci kudina a banza Nan da sati biyu tattalin arzikina Kuma ya kare ai,to kullum Yan barka zasu cika gida ayi ta girki ana saukewa ana dorawa,Allah ya taimake ku Abba ba irin na da bane Yan barka da Kun yini da yunwa a gidan Nan sai dai Kubra ta ci da ku ko Wanda aka haifar wa.
Spark a waya ya kira Mohsin da Beauty ya kira su Umma ya musu barka,Abba ya kira Shima ya Masa barka.
Kudin auren Rahma da Nabeela aka kawo sun fitar da mazajen Aure,Rahma Wanda suke rage zafi da shi suna Tabesting shine yaga gwara ya aure ta kawai bazai iya rabuwa da ita ba Sam,Shima Likita ne matashi bai fi mate din Annoor ba,Nabeela kuwa wani Wanda suke School tare ne da kadan ya girme ta sa'anta ne tare suka yi secondary har university,iyayensa suna da hali sosai shi yasa suka amince da yace zaiyi aure.
Jauro sai murna yake zai rabu da wasu yaran nasa lafiya shi dai.
Kwanan Beauty uku da haihuwa Nabeel ya sake kawo Hidaya da kansa,Abba Yana kofar gida shi da Jauro duk me zuwa barka a idon su take wucewa ta fito,Jauro yace gaskiya Dana ya iya kiwo har tana ta zama gwazarma,Abba yace uhm gata nan dai wlh tsila tana ta kauri,Hidaya tace Abba sannunku ta durkusa ta gaishe su,Abba yace wato Hidaya kasa zaki watsa min a Ido,kin nuna a gidana kafin ayi miki aure wahala kike Sha wato baki da kwanciyar hankali,gidan miji yafi gidan Uba,Anya in na mutu kuwa zaki yi kuka? sai da kika je gidan miji kika nuna kinfi Jin dadi acan,Ina rabaki da gorin da namiji yace a gidansa kika yi kiba,Jauro yace ai mu kowa ya shugo gidanmu sai ya canja.
Nabeel ne ya karaso suka gaisa basu ce Masa komai ba anyi sa'a yau.
Mohsin shopping mall ya shiga Yana yiwa me jego wasu siyayya da tace tana so,Hanan ce ta tsaya a kusa da shi da Mijinta Jibson suna siyayya,Jibson Yana cewa karki dauki abinda yafi karfina fa,a'a mayar da wannan wallahi ko kin dauka bazan biya ba,Hanan tayi murmushi tace to da uwar kudi na ni zan biya,Jibson Yana rike da hannunta,Mohsin ko kallon su baiyi ba Kuma yaji Muryar ya gane Hanan ce,Sai da zai bar wajen Yana Juyowa suka hada Ido da Mohsin,Hanan wai tunaninta zata cusawa Mohsin takaici ganin tayi kiba da kyau harda sake makalewa a Jikin Jibson ta furta my love muje,Mohsin tuni ma yayi gaba abinsa ko a gefen takalminsa.
Yace a ransa dan kin auri me kwal kwal har wani birga zaki min ni da nake da me kayan arziki,aikin banza kin dameni a raina zan barki ki auri wani,ya biya kudi ya wuce da ledojinsa,Yana fita suma sun fito ya tsaya a Jikin tsaleliyar motarsa,Hanan ta saci kallonsa takaici ya kamata tace da tuni ni zan shiga motar Nan na cuci kaina,wai mene a kishiya da na zauna na dinga kishin hauka,gashi yanzu ni a Napep zamu koma gida mijina ko Lifan baida shi,kishin hauka baiyi ba na cuci kaina,anzo min da arziki na kasa hakura,matar tasa taso mu zauna lafiya amma naki" gashi yanzu ban samu ko Wanda ya kama kafarsa ba,Mohsin motarsa ya bude zai shiga ya juyo suka hada Ido da Hanan tana tafiya da Jibson zasu shiga napep Amma Mohsin take kallo,gwalo ya mata ya saki murmushi ya sake mata gwalo karo na biyu,da sauri ta dauke kanta kamar zata yi kuka,Mota ya shige ya ja sai ya Kara gaba sai dariya yake Yana driving yace kinyi asara Hanan yarinya yaro me kama da Nailan sa kyakyawa gashi yanzu gidana wow ga mota Alhmdllh,dama ni ba ajinki bane kuruciya ce ta sa na nace Ina sonki,sai da Abba yace ban iya zabe ba amma lokacin Ina yaro ban San ciwon kaina ba yanzu kuwa sai Beauty,wacce in ka kirata kace Beauty mutane zasu juya harrr kallon wace Beauty ana kallonta za a tabbatar da taci sunanta,ke kuwa da kika dace ma da suna Larai aka taimaka aka saka miki Hanan.
Kidansa ya karo Yana bin wakar da yake ji har da rawa da kai yace Hanan kin mutu kin lalace an kare a me kwalkwal ko banza sanda kina matata ai kina shafa gashina,yanzu kuwa me zaki shafa kina kamowa zaki ji kamar kin shafa bayan kwarya,Mohsin sai dadi yake ji Hanan bata ci gaba ba, Yana Allah ya Kara, wannan dabiar Maza ce dama.
Annoor Iman dinsa ya daga sama ya cafe ta tare da dorata Saman bayan motarsa ya tsaya a Jikin Kafafunta hannunsa daya a gefenta dayan ma haka suna karewa juna kallo suna Hira a cikin gidansu,ya dawo daga unguwa ta fito tarensa shine ya Dorata Saman bayan motar.
Iman tana magana tana shagwaba kamar wata Yar yaye,tace Mamana tazo dazu wai kaji auren Sudan zata yi sun gama magana,yace mene na damuwa to yanzu ki gwada a kanki kice a ni da ke Hakan ta faru Dan na dawo baza ki aure ni ba? Iman tace da gudu ma ba wanda ya isa ya hanani wlh sai na aureka ba yara ba ko sabon gari market na Haifa dole na aureka,ai sai dai a sani a taskar labarai amma aurenka ya zama lahu,in aure abina in bar yaran suyi ta fushinsu,yace to ki kyaleta tayi aurenta duk abinda zai faru ya riga da ya faru,Haidar ya zama Yaya a gaske Kai jama'a Haidar surukina Dan iska ko gaishe shi bazan dinga yi ba,Iman tayi dariya tace Yayan guda,Juyawa yayi ta haye Bayansa suka wuce ciki abinsu.
Kwanan Babar Haneef biyu ta tafi,tana tafiya a ranar Mero ta Sha wanka ta shirya cikin Abaya me kyau ta fito,Ihsan tana Palo Shima Haneef Yana Palo tazo ta wuce ta tsakiyar palon ta wuce kitchen,gaba daya hankalin Haneef ya koma kanta,Ihsan ta kalle shi tana mamaki,Mero tana sani ta wuce kitchen ta fito da ruwa Wanda ba Sha zata yi ba,ta fito again Haneef ya kura mata Ido Yana so ya fuske amma ya kasa,zata wuce yace Dan taimaka min da juice,Mero ta ajiye ruwan a gefe ta kalle shi suka hada Ido kasa tayi da kanta ta dago da iya idonta murmushi suka yi a tare,har ta tafi ta juyo tace juice kace ko? yace yes,wanne kalar tana kashe Masa Ido,Haneef yace dole na Kara aure ba waliyyi bane ni wlh,a fili yace Apple,tace haba me za ayi da wani Apple gaskiya ni na Strawberry zaka Sha yafi dadi,kasa musawa yayi sai me cewa yayi Allah? yafi dadi ko? Mero tace sosai ma,kamar nafi son Apple din ni,shagwaba ta fara Allah a'a ni gaskiya strawberry pleassssssssse kaji....tsigar jikinsa ce tace wani yarrrrrrrrr.....yace okay it's fine kawo min to shike nan? Kai ta daga a shagwabe,Ihsan mikewa tayi tsaye tace wai meke faruwa ne a gidan Nan? Mero tace da aka yi me fa? Yar aiki ce ni nazo miki da shawara kika ki ji,ai mu indai muka Bada shawara aka ki dauka to mutum sai yaga tsiya wlh,bama son mutum ma da ya yake karewa damu bare yayi mana,abinda kika kasa nake miki a aikace Kuma Baki ga komai ba,duk kudinki da kike ji da shi da iliminki ni ba ruwana da shi aiki zan miki wlh.
Baiwar da Allah yayi mana ita ake fitowa da ita ana sarrafata tunda ke kin kasa kin wulakanta taki ta zama Bata da amfani,Ohhh kice dama son shi kike yi? ya halatta mana in ma Hakan ne ai ba haramun bane,wlh baza ki iya kishi Dani ba na tabbatar ko a kishiyarki nazo wlh sai kin sallami kanki,muke sa mutum yayi laifin dole fa,ki bar Raina mutun ko ya kika ganshi,ya kike so ayi miki? An fada miki gaskiya kinki ji,an miki fada an miki ta lallashi kinki to zama zaiyi yana jiranki ko me? bazai Mori kuruciyarsa ba jiranki zaiyi,so kike sai furfura ta fara feso Masa tukun,Yana da bukatar yara Yan dagwai dagwai,Haneef yace madalla da samun Yar aiki irinki wlh,ke Alkhairi ce,kina da hankali da hangen nesa.
Ihsan tace haka ka ce? Dama Amana ta kuke ci ka kawo min Karuwa a matsayin Yar aiki wlh Iyayenka sai sun San wannan zancen,Mero ta juya ta dakko lemo ta kawo Masa,ya karba Ihsan ta ja tsaki ta juya tace fasikai wlh sai ka sakeni bazan zauna da mazinaci ba,Mero tace ai kinji Illar baki San ma waye mijin ki ba zai iya Zina ko bazai iya ba baki sani ba har kin fara zargi.
Haneef tv ya canja channel yace sun fara film din nan,Mero tace ai Bata mutu ba? Bata mutu ba yarinyar to tunda bata mutu ba zanci gaba da kallo,Mero ta zauna suna Kallo abinsu,Ihsan ta shige daki tana kuka tana faman kiraye Kirayen kawayenta tana fada musu halin da take ciki.
Haneef yace Khadija Aure fa zanyi na dauki shawararki, gaban Khadija ya Fadi dam,tace wace zaka Aura din? yace akwai wata Yar kawar Mamana ta Dade tana son na nine naki yarda Kuma har yanzu tana nema na a waya,Mero tace ba irinsu zaka nema ba ai sai ka Kuma auro irin Ihsan,yanzu karka nemi kowa addua zamu tashi a tsaye mu fara Allah ya kawo Maka ta gari to daga nan Kuma ko kawarka ce kaji baka so ku rabu sai ka aure ta,Haneef yace Kawa? Ni bani da Kawa sai ke kadai fa,Mero tace ko nice ba addua za ayi ba kan wacce ta fada ayi da ita,Nima ko ba na so zan taimakeka,harka ce ta taimako kana cikin wani hali,Haneef yayi dariya a ransa tunanin Mero zata iya Masa wayo,kawai kallonta yake,ta kwanta Masa a rai ne kawai,yace to shike nan Allah ya tabbatar da Alkhairi,tace Amin ni Yar taimako ce abokina nane Kai zan iya taimaka Maka a ko wanne irin lokaci,yace da gaske tace to in Kuma wata ce Allah dai ya baka ta gari ni bana bakin ciki,dama Ina da saurayina a kauye,Haneef yace wanne irin kauye ana zaune lafiya kina da aboki kamar ni.
Ihsan ce ta fito a fusace ta haura sama ta shige bedroom din Haneef tayi Shirin bacci ta kwanta a Saman bed dinsa,Mero tunda taga ta hau sama tasan da dalili,dariya ta dinga yi a ranta tace tun ba a je ko Ina ba kenan.
Haneef sai da ya shige dakinsa ya samu Ihsan a bed dinsa a kwance tayi mala mala cikin rigar baccinta me kyau.
AsmaBaffa
[2/23, 8:35 PM] AsmaBaffa: 🏫TANTIRIYA🏫
A GIDAN YARI
BOOK 3
~TAIMAKO~
36-40
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.