Tantiriya A Gidan Yari Part 3 Complete Hausa Novel
Reading file: Tantiriya_A_Gidan_Yari_Part_3_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 6 of 20
PAGE NAKI NE
Chuzahraumar
*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*
Ihsan Ido ta zaro tana mamaki yanda yake sakewa da Yar aikin da jiya tazo ma,farfesun ya fara dandawa,tunawa yayi da kazantar gidan su Mero masu tace gasara da Skirt,yace ya batun tsafta kuwa nan dai ba skirt Kuma ba koko bane ko? Mero kamar ta sani tace ai tunda naje aiki Abuja na goge bana biyewa babar mu yanzu ma kullum gyara nake mata Ina so na koya mata yanda ake lamarin duniya,Ihsan tace uwar taki? Ae mana iyaye ma a ilimince idan anga suna ba daidai ba ta siga me kyau da tausasawa zaka fahimtar dasu,akwai wata kissa ta Sahabi na manta,Ihsan tace ke Jahila kice baki sani ba me kika iya kazama,Haneef ne yayi magana ya isa,itace kazama ko ke? Wanda yake gyarawa da Wanda Yana zaune sai dai ya zuba Ido ciki waye kazami?,Ihsan tace Yar aiki ce fa karka manta Haneef,yace to ita ba mutum bace,cin fuska ne wannan ai,ke baki aikin fari bare na baki Kuma ki damu mutane, Ihsan fushi tayi ta mike ta bar wajen tana cewa bazan ci ba bana ci,Mero tace ikon Allah Innallaha ma'assabrin Aunty Ihsan,Aunty Ihsan tawalkaltu alallah bazan biye ki ba Ina da hakuri ni,Haneef ya kalleta yace sit,na'am me kace? Zauna nace muci,Ido ta zaro tace muci fa kace,Uhum muci mana nace" zubawa kanki,Serve your self,Mero tace kana da kirki gaskiya,yace girkin yayi dadi kwana nan zan Kara miki salary double,kinyi abinda banyi zato ba,yanda nace zan biya ki ba haka zan baki ba zan Kara miki,Mero ta Sosa Kai tace na gode tana ta Jin dadi tana murmushi
Farin ciki ya kamata tace yanzu aka fara harkar girki Oga,tunda haka ne zaka ga Abinci iri iri dama na koya a Abuja zaka Sha dadin girkina iri iri,dariya yayi, tace Allah sai nazo na fara zuba Maka Egusi soup,da miyar waterleaf Alaji ya Sha wata tarwada an gama,mu muka iya sarrafa abinci,ni da kitchen yake a tafin hannuna,Kuma nice wacce nasan sirrin tukunya babba da karama,tukunyar kasa data karfe duk nasan kalar dandanon girkin su,Haneef yace yana murmushi to zauna kici,zama ta gyara ta fara ci,suna cin abincin su,Ihsan leken su take yi ta bedroom,tana ci Yana satar kallonta, Mero duk da a kauye take abubuwanta na birgewa take yi.
Sai da ya gama ci ya kwashe wayoyinsa yace Office zan tafi,Kallon film dinmu fa? Maybe na dawo kafin lokacin idan Kuma ban dawo ba ki kalla Kya bani labari
Mero tace to an gama a dawo lafiya Honorable mijin Ihsan Yar wanka sai dai babu mamora,wlh ka dinga morar ta shi yasa take ma gani gani,kamar zaman maguzawa,shi yasa aka ce me shi ya Kara aure sabo da irin haka,yanzu da kana da wata matar da yanzu Ihsan ta kawo kanta tana make ma Murya Darling Ina Kwana,amma yau ko gaishe ka banga tayi ba,haba ko Fir'auna sai da ya zabo mace ta gari Asiya ya aura bare Kai Musulmi,Haneef Yana dariya yace haka ne Khadija zaki tayani zabowa na Kara ni kaina naga Ina bukatar mace ta gari,Mero ta washe baki tace in kayi aure zaka Kara lafiya da nagarta da daraja a idon duniya,amma wannan Ihsan ni da ita ai daya muke,Nima da zaka siya min kayan daukan wanka wlh haka zan dinga cakarewa a gidan nan bamu da banbanci,to yanda nake kwana na tashi haka take kwana,Dan Allah Kai baka ga ta Raina ma hankali bama,ka kashe kudi ka biya sadaki ta zauna a gidanka,Kaci da ita ka shayar da ita ga sutura sannan baka amfanar komai Kuma,ai cikin biyu ayi daya kodai ta dinga karbar Ijakala ko Kuma ka dauki mataki,a kirata ayi maganar nan a gabanta.
Ihsan dama tana labe tana ji tace to munafuka algunguma Ina jinki,Kuma wlh sai kin bar gidan Nan na Kore ki dole ne aikin wai,oh my God kina sani magana,Mero tace ai ba wani Abu aka ce ba fada za a miki ni bazai yuwu na dinga ganin ogana Yana da mata Kuma Yana kwana ya tashi shi kadai ba,kije ki dinga bashi hakkinsa salary na nake ji,ya samu nutsuwa yafi Jin dadin bamu akan lokaci,yau da fushi ya tashi a gidan Nan so kike watarana ya kore mu sabo da rashin samun nutsuwa,in kin San hakane me yasa kika aure shi ai sai ki barwa masu sonsa,kullum cikin fushin ubangiji kike,Ihsan tace ya neme ni ne naki zuwa,sai ya neme ki zaki je,ba hakkinsa bane a bashi mana kayansa,Baki Ihsan ta bude galala tana kallon Mero,tace are you normal?oh bagidajiya ce ke dole kiyi,Mero tace me zaki nuna min ai na fiki ko kina da Ilimin bakya aiki da shi ke,me zaki nuna min kina Kashi kina fitsari wanne kwambo zaki yi, ki bawa Oga hakkinsa kawai a samu salama,bazan bayar ba idan Jikin na ubanki ne kizo ki dauka ki bashi
Mero tace Allah ya kiyaye ma Ubana Sani yayi irin jikinki ai babu lafiya Kuma namiji da jiki irin naki,ke yanzu Dan Allah bakya ganin asarar man shafawa kike da kayan kwalliya? Miji baya yabawa ba ruwansa Dake kema ba ruwanki da shi,ai wlh in nice ke ko Mai bazan shafa ba,ko dangwali yaba bazan shafa ba bare Mai me kamshi,to asara ce babu me yabawa,ni da ke ba banbanci,Haneef Yana jinsu Yana latsa waya suna ta fama,ya fice abinsa,Yana fita Ihsan ta zazzaro ido tace ke ko uwar data haife shi ko uwarsa Hafsatu bata Isa ta fada min magana ba ki shiga hankalinki,bana hayaniya bana shiga Uzurin wani bana so Kuma a shiga nawa,in kika ce zaki shiga gonata wlh iyayenki sai sun bar kauyen ku tsirara,ki kama kanki bana shiga safgar rayuwar wani,Yar aiki ce ke ki tsaya a matsayinki duk da shi Haneef ya daure miki gindi,Mero tace a'a karki Masa sharri ta Ina ya daure min yanzu ma fitsari zanyi abina.
Ihsan ta tsaya tace ke...ke...ki shiga hankalinki wlh na fiki rashin mutunci,Mero tace nawa rashin mutuncin degree ne dan Cotonou,naki kuwa bazai wuce na nan Benue ba,ki bashi jiki ki huta,wlh indai Ina gidan nan sai ya latse ki ya taba kudinsa bazai yuwu ba a dinga ci da rabonsa,naga uban da zai sa ya tabani to,kanin ubanki ne shi Haneef din,Yar iska marar tarbiyya berar kauye.
Mero kalamai ta tausasa da lallashi tace Aunty Ihsan....Auntyna...kiyi hakuri haka zaki hakura ko dukiyar fulanin naki basu da girma ki daina Jin kunya,wai zai ganki kiji kunya ko ai abin kunya ne a gansu ba girma ba haka bane,nooo inji Spark....aure ne sirrinku ne ba wani zai fadawa basu yi masa ba,Kinga ko mu sai dai muyi hasashe cewar ba wasu manya bane amma bamu da tabbas tunda a riga kawai muke ganinsu,Ihsan tace na shiga uku yau Allah ya tsinewa uwarki,Mero ko a jikinta tace Kinga ki nutsu hakuri zakiyi haka Aunty kina so kema fa,Haneef fa ga kyau ga kamshi yanzu wata macen in ta ganshi sai ta fara zaucewa amma ke ana nuna miki hanyar arziki kina runtse Ido, kije kici arzikin Hallare Aunty,ki tuno farko farko sanda kika Kai kanki ya kika ji? Ki koma ki sake karbowa wlh,Ihsan gani tayi Mero kawai bata da Kai ta ja tsaki ta juya tana cewa idan ma hada baki kuka yi shi yace kizo ki lallabani to ki koma ki fada Masa jikina ban bayarwa in Yana so ya kawo kansa,ta juya a ranta tana murna cewar lallai Haneef da Khadija suka hada baki sabo da taje ya kwanta da ita,wata dariya tayi tace wlh tukunna ma Haneef,wasa kake da mata sai ka gaji ka kawo kanka kana roko na.
Salamatu tana gefe ta Dora hannaye a Kai tana tsoro da mamakin Mero,sai da Ihsan ta bar palon Mero ta dinga dariya kasa kasa tace ai wlh sai bakinki ya bude Ihsan,aikin banza baki san ni ba so nake ya kwanta dake ba kawai Dan na hanaki sukuni ne Kuma gashi na saki magana,sai na koya miki masifa a gidan nan, Kya fada mana aji,aji indai bana makaranta ba bane ai aikin banza ne,Salamatu tafiya tayi ta buya kar ma Mero tayi mata magana ace suna gulma.
Haneef kuwa har yaje Office Yana tuna Khadija Yana ta dariya shi kadai Yana Jin dadi,yace gaskiya fa yarinyar take fada na Kara auren nan yafi kawai,dama Mamana tana fada min ko waye ya bani shawara indai na duba naga ta kirki ce kawai nayi aiki da ita,kullum Ina bukatar mace amma ba dama,gaskiya zan dauki shawarar Khadija wannan ai me kaunata ce,Allah sarki tana so na samu nutsuwa Kuma gashi madarar Nido fa ta taru,wannan Yar iskar kuwa ko bata da lafiya wa ya sani ma ko aljani ya aureta oho,ba komai bari na dawo gida.
Mero tana kitchen ta dora abincin rana Ihsan ta shugo ta bangajeta ta wuce ta dauki lemo a fridge ta fita,tukunyar Mero ta sauke tace yau sai yamma zanyi girki kowa yaci nade da Mai yau kin jawo wa kanki,sai Haneef zai dawo nayi masa,ta kashe gas ta fito ta wuce dakinta da biscuits da Madara,taci ta koshi tayi Sallah ta kwanta ta dinga baccinta har da cire kaya daga ita sai vest da pant .
Yunwa ce ta damu Ihsan taga abinci shuru shuru gashi so take taci ta fita ta Sha wanka cikin material me tsada,fitowa tayi kwas kwas tana kwalawa Khadija kira,tafi karfin ma ta kira sunanta sai dai Yar aiki...Yar aiki ....Salamatu ce ta fito da gudu tace dalla ba ke ba ta gasken Yar aiki nake nufi,tsaki ta ja ta wuce dakin Mero da kanta ta ganta tana bacci daga ita sai dan guntun wando da vest,mamaki Jikin Mero ya bata kyau haka kamar ba Yar aiki ba,duka ta dannawa mero a cinya,ta bude Ido da sauri,Ina abincin dan uwarki? Me kika dafa nace? Mero tace nade da Mai,tsaki Ihsan ta ja tace Allah ya taimakeki kinyi girkin,wlh da baki dafa ba da Kinga rashin Mutunci,Mero dariya ta kamata wai Ihsan bata San mene nade da Mai ba,yunwa ce nade da Mai bata sani ba ta zaci wani lafiyyen girki ne.
Tana fita Mero ta sawa kofarta key ta koma baccinta,Kitchen Ihsan ta shiga taga tukunyar ba komai,ta buda flasks duk wayam,dining wayam,Salamatu ta kwalawa kira ta fito tana hammar yunwa,tace Ina abincin da tayi? Salamatu tace ban sani ba Hajiya,tace min ta dafa nade da mai cewar Ihsan,Salamatu ta shiga tafa hannaye tace Hajiya ai yunwa take nufi,ai in kika ji ance nade da Mai to ba komai naci yunwa ce,Ashar Ihsan ta dura ta koma dakin Mero taji kofar gam,key din mota ta dauka ta fita kawai ta wuce eatery lafiyayye taci acan,tana cin Abinci wani matashin mutum talaka,kana ganinsa kasan sai dai rufin asirin Allah amma kyakyawa ne Siriri bai ko kama kafar Haneef a kyau ba.
zama yayi a gefen Ihsan Ganinta babu mayafin kirki bata Masa kama da matar aure ba,sannu yace mata tayi murmushi ta amsa tana cin abincinta,order yayi ta fruits salat kawai sabo da baida kudin cin abincin,kallonsa Ihsan tayi tace ya fruits kawai? Murmushi yayi yace ba komai shi nake so ma,tace a kawo Maka irin wannan rice din akwai dadi,yace bata dame ni ba ne,tace a'a Kaci mana zan sa a kawo sai na biya Maka,yace nace miki bani da kudi Hajjaju? tace nidai nace ka dandana Kaci,okay fine ya furta Yana murna a ransa yau yayi gam da katar,tasa aka kawo Masa yaci ya koshi abinsa.
Yana gamawa ya mike yace thank you Hajiya ya fice da sauri,Bai tsaya ko Ina ba sai Dan gidan da yake rabawa dakinsa me dauke da toilet da dan gado irin na gwauraye.
Murmushi Ihsan ta saki ta mike ta wuce cikin rantsatsiyar motarta.
Spark suna zuwa gidan Rafeeq a can suka samu Khalid Yana zaune a Palo tare da Rafeeq da Ikhram,Rafeeq yace ya Lagos din? Spark ne ya zauna ya hakimce Naila ta zauna a gefensa suka gaisa da Khalid da su Rafeeq,Khalid yace Lagos tana can Ina Barack a daure Ina hutawa Allah yasa ma tare da matata nake,Rafeeq ya furta har yanzu bata sake haihuwa ba? Khalid yace akan me zata haihu yanzu ana zaune lafiya,Soja in kaga Bai nemi mata ba sai kiyayewar Allah,saura kadan rannan na afka,na tuna Dan bariki Misam yanda ya kasa dainawa sai na fasa na ja abata na Maida ta ciki,Ikhram da Naila sai da ya basu kunya amma su ko a jikinsu.
Spark tunda kayi aure banji ance kayi tafiya ka bar kasar ba bare kaki fadawa mutane,da kuwa kawai sai dai aji baka kasar Kuma baza ka fadawa kowa ba,Spark yace da kenan bani da nauyin kowa Gwauro ne ni Amma yanzu ko zan tafi kafata kafar me daki,Rafeeq Yana zaune Yana Shan fruits,Ikhram tazo ta kawo musu kayan Sha da na ci,Spark yace Tantiriya ga fruits Nan,murmushi Naila tayi tace bana son sha ni yau bana son cin komai,Why? ya tambaya tace haka kawai bana so.
Yau me kika ci kwata kwata? Daga fadar haka sai taji haushin Spark wai har taji haushi nan da nan mood dinta ya canja da kyar ta daure sabo da mutane bata ce ya dameta ba,Spark tunda ya kula da haka sai ya kama kansa,bai sake yi mata magana ba,suka ci gaba da hirarsu da su Rafeeq,Nan ma sai haushi anki kulata ta mike tana cewa mu tafi gida,Ikhram tace ke Naila kalau kike kuwa? Naila tace kalau nake tunda baza a kulani ba mene amfanin zuwana,nazo kin wani share ni ke da nazo wajenki,Ikhram tace yau naga ta kaina ni yanzu duk maganar da nake miki kina shareni banji haushi ba sai ke,Naila tace eh ai Kya ce haka mana yanzu bazan sake zuwa gidanki ba,Rafeeq Ido ya zaro yace wlh da kin kyauta min ni dama Kun isheni Allah raka taki gona,Khalid dariya yayi yace madam dai yau ba kalau take ba gaskiya Spark ba haka na Santa ba,Naila ta fice tayi waje,Spark bai ce komai ba bai tashi ba bare ya bita,horn yaji tana ta yi Masa yaki fita kawai suka ji ta fice da motar tayi tafiyarta,Rafeeq yace yau kaga ta kanka Spark,dariya Spark yayi yace rabu da ita taje na koma a taxi,Khalid yace sai na saukeka a gida,ka lallashe ta Dan uwarka maybe wani abin kayi mata,Spark yace ba abinda nayi mata ni.
Naila gidan Misam ta wuce,tana zuwa tayi parking kofa ta kwankwasa,Chika ta bude kofar tace au Ashe kece shugo,Naila ta furta mu gaisa a nan wucewa zanyi fa na biyo bai ma sani ba,Chika tace bai sani ba? baki Naila ta tabe tace ai namiji ba dan goyo bane ke rabu da shi duk ya sire min ma, halin Maza ai sai su,Chika tace Spark din? Naila tace me aka yi aka yi shi dan Allah canja zance,Chika tace to da dalili ko fada kuka yi? Naila tace ko daya ni wlh da zai barni na tafi gida sai nayi wata ban dawo ba ya ishe ni,Chika tace tab shi kuwa Spark lallai ba karamin laifi yayi ba tunda Naila dai tace haka,Naila tace ai mu dai mata sai dai Allah ya saka mana abinda Maza suke mana,babu na gari duk sun kare,na gari sun kare yanzu.
Chika ta rufe baki tace ai sai hakuri Naila dama watarana dole a saba,Naila tace hakurin da nake da bawan Allah Nan ya isa,badan Ina hakuri ba Chika da yanzu zuciyata ta buga,Ki Kara hakuri kinji,ya zanyi na hadu da kaddara,sai anjima ta juya ta tafi abinta,Misam Yana Palo Yana Jin komai.
Mamaki ya kamashi yace ke Honey Anya Naila kalau take kuwa tun kwana uku da suka wuce na je gidan naga tana ta fushi,Abu kadan sai ta fara fushi ta fusata,Chika tace Ina zan sani laifin Spark ne gaskiya duk yanda aka yi,Naila haka kawai baza tayi haka ba da dalili,Spark ba abinda zai mata tab wannan yanda yake sonta kamar ransa me zai iya tsinanawa bare ya bata mata rai,Chika ta furta dan kawai dan uwanka ne shi yasa.
Misam Spark ya kira a waya yace wai me kayiwa Naila ne? Kai a Ina kaga Naila din? Yanzu tazo nan ta tafi tace badan tana hakuri da Kai ba da yanzu zuciyarta ta buga,dariya Spark yayi yace kyaleta fada take nema ni Kuma baza tayi da ni ba,Misam yace dama me zaka iya Kai kam akan Naila ai tubabbe ne.
Naila tana komawa gida tayi parking ta fito ta shiga bedroom dinta ta kwanta haka kawai ta fashe da kuka take ta faman kuka a kwance a haka Spark ya dawo ya same ta,mamaki ya kashe Spark,yace Allah ya kaimu gobe mu tafi asibiti Ina zan iya wannan abu haka,Ina ganin wannan abin ai sai na rame ai, tana jinsa tana ta kuka,a haka tayi Sallar Magriba da Isha,girkin ma taki yi sai take away ya musu ya dawo,da ya kawo ma da kyar ya lallashe ta taci,yace tashi mu tafi to mu kwanta,kafada ta makale tace naje ka taba ni bazan je ba,Spark Ido ya zaro ba shiri yace kamar wata Amarya,Au dattijuwa ce ni wato na tsufa kenan,kawai kace na tsufa,yace ba haka nake nufi ba,ni a nan zan kwana,yace to ai da nan da can duk daya,ni dai za a dameni ta furta,Wanka ta shiga ta fito tayi Shirin bacci har da saka wando tight dogo da riga t-shirt da bra da komai kar a taba ta,Spark ma Yana Shirin baccinsa ya kashe light bai kulata ba ya kwanta abinsa gwanin tausayi yau ba Kwalbewa,Ido ta bude tace haka muke bacci Kai baka iya kula da mace ba,Ina Shan wahalar aure nidai,kowacce da Mijinta lafiya ni banda ni,ta Hana Spark bacci sai korafi take Masa baya kula da ita,hakurin da nake a gidan nan shi yasa ake min wani abin,sabo da anga Ina hakuri bana cewa komai,Juyowa yayi yace taho to dan Allah idan baza ki bani komai ba ki rabu dani nayi bacci,Naila tace ai ba abin arziki kake shukawa ba ,shi yasa kasan me kake min duk zaluncin da kake min hmmm ba komai,rungume shi tayi ba riga a jikinsa,ta dinga shafa bayansa tana cewa bayan nan zaiyi dadin cizo,wlh kamar na cije ka,bayan nan naka da cizo ya dace gaba daya,ban taba kula ba sai yau,Spark tun Yana dariya marar sauti har ya saki abarsa,ci gaba tayi tana shafa bayansa tace da gani ma duk Wanda ya cijeka zai ji dadi,hakoranta ta saka na kasa tana Masa susa da su,tace dan dai zaka ji zafi ne da na gwada.
Spark yace bari ki gani dai naga kamar Kinga na kyale ki yau shi yasa,kayan jikinta ya hau cirewa tana hanawa suna kokawa sosai Naila harda kuka da cizon da yakushi baza a taba ta ba,Spark Kuma yace wlh bazan biye Miki ba,da tirje tirje da masifa da kukanta a haka Spark ya kwalbe yau yaci wahala,duk ta yakushe shi,sabo da fada yau Bata gamsu ba shi ya gamsu ta dawo Kuma tace sai anci gaba,yace ba abinda zanyi na gaji duk kin yakushe ni kin ji min rauni,ai Kaine da naci Spark naci ne da Kai baka Jin magana sai da nace bana so,to Kuma yanzu me kike nema? Ai ni ban kawo ba yau sai yanzu nake so,Yace bazan yi ba,Hallare ta gaji baza ta iya komai ba,wlh sai tayi haba haba tace baza tayi ba ai sai a tsine mata tabi duniya,please Baby,to fada min me na miki kike kuka yau kina fada da mutane me aka miki? In kin fada min shike nan,Naila tace domin Jin dadin zuciyata nayi,yace shine kika je gidan Misam kika zazzageni ko? Ka yafe min haushi naji Kuma wlh ban zageka ba nace dai baka min adalci Kuma nima ban San me yasa na fada ba ai kana min kai,Misam shine ya fada Maka sabo da gulma.
Komawa tayi jikinsa tana cewa please,Spark yace duniya sabuwa ni ai yanzu zan kwalbe kwantar da hankalinki ke da harijinki.
Washe gari Spark Yana niyyar Kai Naila Asibiti sai ya ganta ta dawo normal kamar da sai ya share yace ai mood ne dama ana samun haka,sai da yaje Office ya dawo wurin magriba ya dawo ya sameta a turbine Kuma ba mutunci.
Arham ne yayi wanka ya zuba kyau shadda yasa fara,ba karamin kyau yayi ba,ya fito Yana goge takalmi sai kamshi yake,Mima tace Ina zaka je? Yace birthday party,amma kasan abinda Papan ku yace ko baka Jin magana kenan,cewa yayi fa yau kaje kuyi zance ku fahimci juna da Basma Kuma na fada mata ta sani,wanne irin iskanci ne wannan, wani ne yasa kace a zabo Maka kana son aure,sabo da Kun Raina mutane ba a isa a fada muku kuji ba kenan,indai kana son ranka ya baci ka tafi birthday party,Arham yace a gida take fa gobe sai na nemeta,ai ba gobe yace da kai ba,ka sani Kuma,Arham hakura yayi yace shike nan kice mata tazo,'Yarka ce ni da zaka aikeni ta juya ta bar wajen,Arham yace kai sai kace wata yarinyar azo a Gani,su Mima an Mima yabi yace to a Ina zamu yi zancen? gidan ubanka sai na fada Maka,shuru yayi ya kira Mufee a waya yace Ina Basma take? tace gata Haly tana shafa mata powder, kice Ina jiranta a palon baki na sama,Mufee tace uhm Ashe zance za ayi bari muzo muga wankan,yace wlh ba ita nayi wa ba,party zanje Mima Kinga yanda take fada akan yarinyar nan,laifinka ne ai gata nan zuwa yace to ya kashe wayar ya koma palon da yace taje ya zauna Yana danna wayarsa.
Fitowa tayi tana Jin kunya tana bin Jikin bango akan an mata kwalliya yau ta sa sabuwar doguwar riga ta atamfa Mima tayi mata dinkuna kala kala,Haly har dauri tayi mata,shine take Jin kunya bata saba ba.
Bata taba yin zance ba sai yau,yanda kawayenta sukeyi ta tuna,daga ance zata yi zance shine sai kace yaje gidansu tazo tana kasa da Kai ta durkusa a gaban Arham tare da furta Ina yini,Arham yaga ta tsula kyau kamar ba ita ba,a ransa yace ashe fuskar ma abar yabawa ce ba iya gaba da baya ya dace a so ba,muryarta yaji tace Ina yini,Shima ta Yan kauyen yayi mata yace lafiya kalau kalau Alqur'an,tace an yini lafiya? Yace lafiya kalau,ya mutane gidan? Yace gaku an lafiya,tace ya....latseta yayi yace ke kin isheni da gaishe gaishe ban Saba ba,tun Ina biye Miki Ina miki Kara Abu Kuma sai Nisa yake,in kika ce Ina yini ko ka yini lafiya kawai kiyi shuru haka,tace to ai Ummati tace haka ba tarbiyya bane,yace ni a wajena tarbiyyar kenan,tace to bari na kawo Maka ruwa,Arham ya bude baki yace ni da gidanmu,ai wajena kazo,Kuma ance bakinka Annabinka yace to jeki,tashi tayi tana gyara mayafinta ta tafi taje ta dawo dauke da ruwan da lemo a faranti su Mufee suna ta boye dariyar su har leke suke yi.
Tana kawowa ta ajiye Masa ta zuba Masa lemon a cup tace kasha Dan Allah,Arham a ransa yace ubana ya zuba abu a dinga rokona na Sha karfin hali,dauka yayi ya Sha,yace ke baza ki Sha ba? tace a'a an hanamu cin Abu a gaban saurayi ance ba tsari,Arham ya Sosa gashinsa yace na shiga uku zanga rayuwa a gidana.
Yace to zauna,ta nemi kujera daban zata zauna yace a nan zaki zauna ya nuna gefensa,ta ja gefen gyalenta ta sa a baki tana wasa da shi tana Jin kunya tazo ta dan dora duwawun ta kadan a gefensa,ga kujerar 2seater yace zauna sosai,zama ta gyara,Arham a ransa yace to ni me zan ce mata ma ne,tambayar ta yayi tunda yaga ita daga Waka sai shiririta ta iya yace ya Dan maliyo maliyon naki? Murmushi ta saki tace ai acan muke yi da shallu da reriye reriye me gudu ya gudu marar gudu ya tsaya sai a buya,Arham yace hmmm sai me? Sai tirke wasa da marmari fita da hawaye Idan aka Kamaka yaro wlh duka zaka ci sai dai kaji tas tas an hada ma jini da majina,Arham yace nine yaron? da mene to Kai?,ni na taba zaton a duniya zan auri kamarka ma,ana ganinka ai an San saurin girma kayi girman birni ne da nawa zaka girmeni ma,ai tun farko da Papa ya nuna min Kai aka ce Kai zan aura tun daga lokacin gwiwa ta tayi Sanyi,da farko na zaci mijin wannan Naila dinne kaga shi shekarunsa dai dai Dani,amma sai wai aka sake cewa ba Misam bane ba Rafeeq duk sunyi aure nace Papa to suyi ta biyu dani mana,yace a'a ai Kaine tun a lokacin na rike baki nace Kaine aka ce Kaine wlh ba karamin mamaki nayi ba nace zan karba da hakuri,Arham yace 5-0 ,kin min 5-0 yafi karfin 1-0 wannan sai biyar da kan Jaki,nufinki mijin Naila ya fini kyau? Murmushi tayi tace ba kyau nake nufi ba ai kaima kyakyawa ne duk Kuna da kyau wlh Allah shekaru nake nufi,Kuma ma namiji Ina ruwansa da kyau,neman kyau a namiji ai sai dan Daudu tunda dai an min kyautar ka shike nan,Arham yace ke zaki aureni ko ni zan aure ki? Aka dai bani Sadakar ki,Basma tace wlh ba sadaka aka baka ni ba sai ka biya sadaki cab, Arham yace to ke yanzu kina so na? da kika ganni kinji kina so na? Basma tace to ni dai ban San gaskiya ba, bana ganewa Ina so bana so ni ban sani ba kawai nidai rayuwa ta nakeyi ko da Kai ko ba Kai yo zan rayu mana,babu batun in ba Kai sai rijiya wlh ba ruwana ko bakin pampo bazan tsaya ruwa ya Jikani akanka ba balle ta kaini ga fadawa rijiya guda akan ka wallahi Bada ni ba,Arham yace 20-0.
Yace to yanzu idan aka daura aure gado daya zamu dinga kwana,baki ta bude tace ni ba Yar iska bace ko babata dakinta daban dakin mijinta daban,Arham yace ke banza sai dare ya tsala take miki wayo tana tafiya,ai arcewa suke cikin sanda,Basma ta tsura Masa Ido tace babata Yar iska ce kake so kace? Yace iskancin aure ba,da bata je ba za a haife ki ne,ke wai cikin kogon dutse kike rayuwa? A karkashin dutse kike? duk iskancin mutanen kauye na zancen banza da labarin aure baki san me ake yi ba,Basma tace na sani mana ai hauka na manna Maka Kaine baka gane ba,ka gwada min iya duniyanci,mu mene bamu sani ba,mun San komai,dariya yayi yace haba? yanzu naji sanyi to me akeyi? tace ai in anyi auren Kaine Jagora Shugaba sai ka koya min ka sani a layi sai nabi,Arham a ransa yace ashe Yar duniya ce a haka kamar sakarai,yace uhm Lissafa min me miji da mata suke yi in anyi aure?
Kai ta daga sama ta rike yatsanta daya tace na daya girki,na biyu tsafta,kwalliya,gyara gida,tattausan lafazi,fari, kisisina,wankan tsarki shi yasa aka ce kar a fiye yin kitso sabo kullum sai anyi,Arham yace wa ya fada miki? Kawata ce Karima dan kaji in fada Maka da aurenta yaranta biyu tana fari da Ido tana fadawa Arham,tace uhm to Ina ji sai me? Yin wanka da ango ai Karima ma mijinta Yana cudata nidai ban dani wlh bazan iya ba ni Kam haka kawai ai sai Hawan jini na ya tashi,yace to Ina jinki,da bacci shike nan,yace bacci ma akeyi?to da Kai me zaka yi? In baka yi bacci ba me zaka yiwa wani ko gadina zaka dinga yi? Arham yaga dai Basma duk yanda ya Kai ga son iskancinsa sai ta dakko wata tashar tana ta faman raina Masa hankali,yace bacci nake ji,tun yanzu zaka tafi ko goma fa bata yi ba wlh sai na fadawa Papa nace minti biyar kayi,Arham shuru yayi ya fasa tafiya yasan sai ta iya fada ta hada Masa sharri.
Shuru yayi Yana danna waya tace kunno mana,kanta ta leko ciki,Arham ya fisge mayafin ba zato ya cire ya rike yace a gida ma sai kin fito da mayafi a Nan kike guje guje a gaban mutane,Dan Allah ka bani mayafina wlh zan fadawa Mima...ta furta da shagwaba,hannu ta Kai tana ja Yana ja,ga kwaro nan ya shigar miki riga,wayyo ta wajen Ina tana tambaya tana tattaba wuyanta,kawo na cire miki gashi ta bayanki ya furta ba wasa,ta juya da sauri yaga jela gashinta doguwa har baya an tufke yace a ransa Ina ruwana da gashi ni ko
mace tana da shi ko bata da shi indai zata gyara gashinta normal.
Zip din ya zuge ta wani yi sakato za a cire mata kwaro,ita ba bra ta saka ba,anyi anyi ta saka tace ita yarinya ce baza ta saka ba,yaga bayan ba birki,hannaye biyu ya zura ta bayanta ya taba Boobs dinta,mamaki yayi yace Kai to Ina suke makalewa ba a gani,a'a'a Papa idonsa Yana gani,wlh yana gani tar,Ita Kuma shashar wai ka cire min? Yace a'a kokawa muke ta yi da shi,kar ya cijeni dan Allah ta furta,Ina wajen Ina nan garkuwarki in bari ya cijeki,Yana ta tabe mata Boobs,ji tayi kawai abu daya yake yi ta tuna da kirjinta ne fa,wayyo Ummati ta kwalle da kuka wani ya taba min,sai da kika ce kar na bari gashi naci amanarki,Arham ya toshe mata baki da hannu daya hannu dayan Kuma ya gyara mata zip din yace ke daga taimako,ka taimaki kanka dai wlh sai na fadawa Mima da Papa ka taba min nono bazan yafe ba,wlh idan dai na samu ciki Kaine ta fashe da kuka.
Arham yace dan Allah karki fada kinji ki rufa min asiri? In rufa Maka asiri azo a Ganni Ina laulayi Ummati tace ciki ake samu,wayo aka yi miki sabo da karki yarda wani ya taba da Hallare ake ciki,Karki fadawa Papa,tsoro Arham yaji Papa ya Masa warning yace wlh indai ya sake taba wata mace sai ya Kore shi daga gidan sa,shi yasa yake rokonta karta fada masa,Miman dai ko kin fada Mata ba damuwa,au haka kace wato baka tsoron babarka,yace kawata ce Kuma uwata,kashewa muke mu rufe itace ma ta zugani,dariya Basma tayi tace Allah zaka shiga wuta kace ta zugaka ka taba min nono? So na take da yawa tace inyi komai ba komai duniya ce in Mori kuruciyata,ke in banda ma kece daga naji yanda suke ai ya halatta,naji na gani dan Tabesting dai,ke da zaki ce ungo Sha ma,Ido ta rufe da hannu tace sai kace saniya da danta Allah ya kiyaye ba ruwa a nawa,yace akwai,a'a babu wlh ko shekaranjiya da naje wanka na gwada tatsowa,zan kawo Koko a cika min,dariya tayi tace nidai kana ta koya min iskanci sai sirrina nake fada Maka,Arham yace Kinga da na zaci Baki da komai a kirji,mummunan fahimta kayi min amma Ina da shi,yace naji zahiri saura gani da Ido,ashe zaka dige,yace ba wani digewa kina bacci zanzo na gani in naga dama,ance nauyin bacci ne dake,in kayi hakuri ma zaka gani what are you eating na mouth Yana zuba,dariya Arham yayi yace Iyye turawa sai kwai tace hmm baka San Ina makaranta ba Ina yin candy Papa ya dakko ni Kuma Ina Jin Dan turancina,na iya karatu da rubutu,suna haka har 11pm ta kusa sannan Mima ta zaci ma sun gama ta leko ta gansu a manne ba space,komawa tayi ba tare da sun ganta ba ta kira shi a waya tace kun gama ne? Yace a'a sai anjima,Sha daya na dare ta kusa ka tafi ka kwanta mana ka kyale yarinya,yace kufa kuka ce mu fahimci juna ban gama fahimtar ba,ka tashi ka sallameta ka tafi karka yiwa yarinyar nan wani abu ban yarda da Kai ba,Arham yace to,ta kashe wayar tana cewa sai ya tabewa yarinyar nan kirji wlh yaran zamani bare Arham nasan hali,Bata San aikin gama ya gama ba,tashi yayi yace tafiya zanyi,Basma tace kamar karka tafi Allah muna hirar mu,yace Mima tace muyi bacci haka,tace to sai da safe,yace ba kiss? Da gudu ta arce ta fada dakin su Haly tace cewa yayi wai ba kiss,Mufee tace uhm tsokanarki yayi tace wlh Kai wannan yayan naku Dan iska ne in fada muku gaskiya.
Allah yasa bata ce ya taba ta ba,Haly tace ya miki wani Abu ne? tace yace kar na fada Kuma rufin asiri Yana da dadi indai mutum yayi Abu to a rufa masa asiri kar a tozarta shi,Haly suka yi dariya suka tabbatar Arham ya Kai hannu,Mufee tace ke dai ki Fadi gaskiya tace ai ya wayar min da Kai yace ba ta nan ake samun ciki ba Kunga kuwa da sauki,suka ce ae da sauki suna dariya.
Spark a ranar yaga bazai iya da sabon halin Naila ba ya dauke ta yace muje asibiti kawai ko kwakwalwarki ce a auna in ta kama rukiyya za ayi miki ayi miki,ki sani a gaba da fushi da neman fada ga kuka,karshe kice zan dace da cizo sai kace Yar secret society, vampire kike nema ki dawo,driving yake tana jinsa tace Allah lafiya nake yace a'a sai fa munje asibiti,suna zuwa lokacin likitar tasu bata duty da wata ta hada su a lokacin,Naila bata yi bayanin me take ji ba tace ita kalau take,Spark ne yayi bayanin komai,Likitar tace Anya ba ciki ne da ita ba,Spark yace ku taimakeni ku gano gaskiya na samu salama kullum hakora take kafa min zanyi dadin cizo,Likita tayi dariya ta kaisu wurin test aka yi mata na jini,Likita result Yana fitowa tace to ka huta ma Oga ciki ne da ita 2mnths,yanzu in tayi wani Abu ka daina damuwa,Spark yace ba laifin glove bane batir ne Kai Kuma Baby zaka zo duniya akwai zama ni da Kai,zamu yi zama naji dalilin tsanata da kayi,ba laifin zaune ba na tsaye kasa matata ta dinga zagin ubanka,tana cewa na sire mata,Kullum bana baccin kirki sai Mita,sai fada,Kwalbewa babu,ga son a cije ni,Naila murna ta hanata fushin ma ta daina fushi gaba daya sai farin ciki kawai ta rasa me zata yi,so take kawai su bar asibitin,abin nema ya samu Naila murna ta hanata magana.
Jauro yau matarsa Amarya da Habiba uwar gida ya dakko suka taho gidan Hashimu zasu yini,Hashimu yana gida yasan da zuwansu an shirye su Jauro ana tsakiyar mata,Habiba na gefe Amarya na gefe,Abba ya kalle su yace tattabara sarkin aure,Jauro yace Kai in ka isa kayi mana mace daya ce kwal baza ka iya adalci ba,Kai ba adali bane,Abba yace Kai adalcin kake yi, karka bari na fadawa Habiba abinda kake cewa,Habiba tace nasan zai aikata,bayan sun zauna Abba yace da jiya kuka zo baza ku same mu ba na Kai Yar Inna Saloon,Jauro yace uhmm tsofai tsofai haka? Abba yace daga can muka wuce Shan ice cream kasan ta da son Sanyi,Nima Ina Sha sabo da bana ciwon baya,Jauro yace bana son wulakanci Kuma tunda nace Ina ciwon baya Abu yaki wucewa a wajenka wai shike nan bazan warke ba to?matan ne suka gaisa suka fara hirar su suma su Jauro hirarsu suke yi,Jauro harda kiran Habiba da kanwata tace na'am,Abba yace Habiba Anji kishiya an fara canja hali ana so ayi soyayya ba a iya ba Kuma,dariya suka yi.
Haidar kuwa Abuja ya shirya yaje katsam gidan Mima ya wuce wai yazo gaisar da matar babansa ya bata hakuri ta koma gidan mijinta,a zahiri Kuma wajen Mufeeda yazo,yaci sa'a tana nan kuwa a gida yazo har Palo aka sauke shi,Haidar ya nutsu bayan duk sunzo an gaisa,ya Kalli Maman Rafeeq yace dama hakuri nazo baki Dan Allah kiyi hakuri da abinda Baba yayi miki,ki koma gidansa,Maman Rafeeq tace na gode wlh ka nuna min kauna ka nuna cewa Kai me Ilimi ne,Haidar a ransa yace karya nake ba wajen ki nazo ba, amma badan da dalili ba me zai kawo ni wani ki koma hannun Baba Ina ruwana da zaman ku,kin dade baki koma ba,a fili Kuma yace ayi hakuri Mama a karasa haka,tace wlh bazan iya ba ka daina bani hakuri ma,bai ga Mufeeda ba ya zauna Yana ta jayayya da Maman Rafeeq har Mufeeda ta shugo ta dawo daga biki,tayi mamakin ganinsa sosai,kallon juna suka tsaya yi,Maman Rafeeq tana cewa bazan koma ba gaskiya ka fada masa,Haidar tuni ya samu abinda ya kawo shi ya ma manta da zancen.
Mero tana zaune tana kallo ta gama girkinta ta shiryawa Haneef a dining sai lokacin me gadi da Salamatu suka ci abinci,tayi wanka ta canja jemammun kayanta ta zauna a Palo tana kallon ci gaban film din jiya,sai da aka gama film din ya dawo gidan,tace sannu da zuwa bayan ta amsa Sallamarsa,yace tashi kije Jikin mota zaki ga driver kice ya baki kayan Nan,Mero taje ta karbo kaya Niki Niki a Ledoji,ta kawo Masa,tana shugowa yace naki ne,tace na gode na gode Allah ya Kara arziki,ta shige part dinsu da kayan tana murna,tana zuwa ta duba readymade ne dogayen riguna na material iri iri,sai Abaya gasu nan kala hudu,sai undies,da flat takalma kala uku masu kyau da mayafai,Harda kayan kwalliya,mayukan shafawa da sauran kayan bukata,Nan take Mero ta saka rigar material wata white and green tayi mugun kyau kuwa kamar Yar birni,mayafi ta yafa fari a kanta ta gyara sauran kayan sannan ta fito,tana fitowa Haneef ya bita da kallo,ta Sha kyau matuka fuskewa yayi Yana cin abincinsa,Ihsan ce ta shugo tsoro ya kamata ganin Khadija Cikin wannan tsaleliyar shiga tayi kyau sai a zaci matar gidan ce,Mero tace kayi wanka kuwa ka zauna cin abinci? Yace yunwa nake ji bazan iya ba sai na fara cin abinci,Ihsan ce ta fisgo Khadija ta juyo da ita,ta kalleta kawai ta kwasheta da Mari,a gidana zaki dinga yin shiga haka dan kija hankalin mijina,dan uwarki muje,uban waye ya siya miki kayan ta nufi dakin Mero taga kayan a take away Leda tasan Haneef ne ya siyo,fitowa tayi da su tayi waje compound ta zazzage su a kasa gaba daya ta dakko ashana,Haneef ne ya fito yace wlh indai kika kona kayan nan a bakin aurenki,Ashanar ta jefar ta ja tsaki tace dama karya kake Karuwarka ce anzo a cuce ni a matsayin Yar aiki,Mero tace in kinyi zuciya kije ki bashi hakkinsa,in Kuna bakya so mu zamu bashi,Ihsan tace Karuwa Allah ya tsine miki ta wuce dakinta.
Tunani Ihsan ta fara tace idan banyi da gaske ba yarinyar naga Bata da hankali da gaske take lamarin nan,wata zuciyar tace amma Kya zubar da ajinki kije wajensa ai sai dai yazo ya rokeni sannan na je tsaki ta ja tare da kwanciya a Saman bed.
AsmaBaffa
[2/21, 8:05 PM] AsmaBaffa: 🏫TANTIRIYA🏫
A GIDAN YARI
BOOK 3
~TAIMAKO~
31-35
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA NE GA AIDA MAMAN TASNIM
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.