Acp Mubeena
Reading file: ACP_MUBEENA.txt
Chapter 10 of 18
Page 6
Duk qoqarin mubeena na ganin ta qwaci kanta amma abu yaci tura dama qarfin mace da namiji ai ba dayaba
Idanuwanta sunyi luhu luhu jikinta harya fara saki saboda azaba
Anty amaryace ta fado dakin da gudun gaske (amaryam papi)wadda tun Safe bata gidan taje gidansu batasan abinda ke faruwa ba saida ta dawo gabda magriba sannan yaranta ke bata labarin abinda ya faru kamar kuwa tasan abinda mubeen xaiyi takira tala yar aikin part dinsu mubeenar tace intaga wani abunda badaidai ba tai gudu taje tasanar mata
Hakan kuwa akai tun lokacin da mubeen ya dawo daga masallaci take labe tana kallonsu lokacinda ya shaqo wuyan mubeenar ita kuma ta fita da gudu taje tasanarma anty anaryan shine ta taho
“”Mubeen me kake shirin aikatawa ne
ba kada hankaline?
Kasheta kakeso kayi?
Anty amarya ta jera masa wadannan tambayoyin hankalinta a tashe ganin jikin mubeena harya saki alamar babu numfashi a tare da ita
Sai lokacin ya saki wuyan nata ta fadi yarabbb a qasa bata motsi
“”Innalillahi wa inna ilaihir rajiun mubeen me ka aikata haka ka kasheta fa🙆♀️””
Anty amarya ta fada cikin kuka duk ta gama rikicewa
“”Ai gwara ta mutu inyaso a hada nida papina a ratayemu indai tabar duniya banida sauran damuwa””
“””talatu miqomin ruwa yi sauri”””
Anty amarya ta fada batare da ta biye maganar shirmen shiba
Bottle water mai sanyi talatu ta kawo ta miqa mata ta kwara mata duka ruwan a jikin ta aikuwa ta sauke wani wahalallen numfashi da qarfi
Su suka taimaka suka kaita dakinta suka kwantar da ita anty amarya ta kira family dr su Dan yaxo ya dubata har lokacin daqyar take numfashi jikinta Ba qaramin weak yyiba
Shima fam dr dayaga condition dinta at first dole ya qara mata drip da allurai tunda yasan bata shiri da magani sammm
Bayan tafiyar shi anty amarya batabar dakinba saida drip din ya qare ta cire mata kafin itama ta koma part dinsu
Ko a jikinshi babu alamar nadama ko kadan ga mubeen dan yanxu ya gama tsanar ta patan shi kawai ta mutu ace shiya kasheta inyaso a hada shida papin nasa a daure su
(Allah ya kyauta🧐)
Tunda aka gama treating dinta bata farka ba saida safe dan gaskia ba qaramar wuya taciba
Alhmdllh ta tashi da qarfin ta saidai fa wuyanta da haryanxu ke mata ciwo sosai bayan ta idar da sallah asubah wayar ta tajawo ta kira talatu mai aikinta ta fada mata abubuwan da take buqata daganan ta koma baccin gajiya
~~baiwar Allah tasha shaqa dole ai kunyar jiki🥺~~
Sai 8 ta tashi a hanzarce ta fada toilet ya gaggasa jikinta da yai tsami ta fito ta shirya cikin uniform dinta dake matuqar amsar jikinta
Kafin ta gama yan kintse kintsen ta tala tagama hada mata komai cikin babban lunching basket 🧺 ta fitar mata a dashi
Wurin motarta
Driver ne ya taso ya karbi basket din a hannun tala yasa a buth ya tsaya gefe yana jiran fitowar ta dukda yasan halinta bataso ai driving dinta tafiso tai driving da kanta papi yayi padan harya gaji
Fitowarta daga dakinta lokacin shima yake fitowa daga nashi dakin sanye da black suit a jikinshi
kallo daya yai mata ya dauke Kansa Dan beyi tsammanin xai ganta a hakaba(mugu to ta Allah bataka ba😡)
“”Morning “”
Ta fada a sanyaye
Bai waigoba balle ya amsa gaisuwar nata ya fice abinshi
Ci gabada tafiyarta tai aranta tana fadin oho dai ta Allah batakaba
**DPC HALL**
"Lokacin da Ina nuna muku cewa mutumin Nan be cancanci ku tsayar dashi takarar Dan majalisa ba watsamin kasa kukayi ah Ido kuka nuna ai mutumin kirkine Mai taimakon talakawa,to ynzu gashi nan ankamashi da laifin kisan babban abokainshi dama fuska biyu ne dashi ai" Alhaji kabiru kalankuwa yafada a harzuke, Alh.Aminu ya murmursa irin murumshin takaicin Nan yace aa Alh.KK zarginshi akeyi Dan babu wata hujja datake nuna shiyayi kisan nan!
"Mtssww zargi fa kace shine daughter in law dinshi zata kamashi abainar jama'a ta garkameshi ko? Alh.kk yafada Yana Mai watsawa Alh Aminu kallo cike da Jin haushi domin kuwa Alh Aminu abokin papi ne na kut da kut.
DPC Democratic people congress jam'iyace datayi fice a arewa,sun jawo Alh.muhammad yaseer (papi)da karfin tuwo suka sashi siyasa suka tsayar dashi takarar Dan majalisa ba irin tarjewan da beyiba Amma suka ki sai da suka shawo kanshi da taimakon Alh. Aminu suka samu ya amince saboda mutum neshi Mai taimakon talakawa ga gsky da rikon amana shiyasa mutane suke sonshi.gefe guda Kuma Alhaji kabiru kalankuwa Wanda Shima yaso jam'eya ta tsayar dashi Amma suka nuna mishi yayi hakuri domin kuwa dayawa Yan jam'eya papi suka zaba dama shi Alh.kk yanajin haushin papi zabanshi da jam'eya tayi yakara samishi tsanarshi ya zuciyarshi,shiyasa kullum cikin sukan papi.
Shugaban jam'eya Alhaji Dahiru Wanda tunda suka fara wnn mahawarar be cemusu kanzil ba yayi gyaran murya tare da fadin ynzu dai abinda yasa na taraki a Nan shine don musamo mafita akan wannan abu da ya kuno cikin jam'eya kamin abokanan hamaiyya su farga....
"To shugaba na nawa Kuma gaba daya kasa ta dauka da maganar Kamen da akayiwa Alh.muh'd ai kawai masalaha itace muyi gaggawan canza Dan takara dan kar abun yazo yashafi siyasarmu" Alh. Umar ya Kai karshen maganar Yana kallon Alh.kk shikuma ya murmursa Yana kashe mashi Ido.
"To ynzu wa kuke ganin yakamata atsayar ne tunda ynzu gsky lokacin zabe Kara karatowa yakeyi Dade nasu mu tsaya muga yanda shari'a zata kasance domin ni inada yakinin cewa Alh. Muhammad be aikata laifin da ake zarginshi dashi ba" shugaban jam'eya ya karashe zancen jikinshi a sanyaye.
Ai shugaba bawani Bata lokaci dazaayi domin sunanshi ya Baci kawai mu canza dan takara tunda ga Alh.kk Nan ai Ina ganin kawai atsayar dashi dama tun farko shine Dan takarar namu kamin wancan Dan shishigin yazo ya mishi shigar sauri.........
Daga Alkalamin ✍🏻
X££l@h's pen••••••••••✍️✍️✍️✍️
https://chat.whatsapp.com/KDkpfCh3PTgAMGI4xMc81W
*X££l@hs Pen*•••••••✍️✍️✍️✍️
رَبِّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ أَنْ أَسْأَلَكَ مَا لَيْسَ لِي بِهِ عِلْمٌ ۖ وَإِلَّا تَغْفِرْ لِي وَتَرْحَمْنِي أَكُنْ مِنَ الْخَاسِرِينَ
*ACP mubeena*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.