Trending Hausa Novels

Acp Mubeena

Reading file: ACP_MUBEENA.txt

Chapter 12 of 18

Page 8

"To kuwa sai dai ki zaba ko kibashi abincin nan ko Kuma igiyar aurenki!!!

"Damm gabanta yayi wani irin faduwa Dan har Saida kanta yasara mata tace saki fa kake Neman furta min da bakinka Mubeen"

"Yess to uwata ce ke da zakiyita wulakanta min mahaifi na zuba Ido Ina kallonki wallahi Mubeena ko kece autar mata nagama auranki daga yau indai Baki dauki abincin nan da hannunki kika mikawa papi yaci ba na rantse da girman Allah sai na sakeki"

"Mubeeeeennnnn.... Papi ya kwalamishi kira domin duk abinda suke nacikin cell din sunaji tunda da karfi suke magana Kuma bawani nisa atsakaninsu

"Itako Mubeena kamewa tayi awurin saboda tsabar kaduwa da magagunun mijin nata Bata taba tunanin zai fushin da yayi da ita ya Kai har haka ba wani irin hawayene Mai dumi ya zubo mata dasauri tasa hannu tashare batare da tabari kowa ya lura ba.

"Mubeen kana cikin hankalinka kuwa to wallahi Koda gigin wasa kasake ka furtawa batarka kalman saki sai na saba Maka Kai wai ni uban wa yace kazo station din Nan bana gayamuku kar nakara ganin ku anan ba bance kar Wanda ya Kara zuwa ba eyye"" da sauri Mubeen yakarasa kofar cell din idonshi gaba daya ya rune yayi jajir nace ohh ran Maza fa yabaci "hba papi yazakace kar mu Kara zuwa Kuma sai kake tunanin hakalinmu zai kwanta kana wnn bakin wurin wallahi sai na hukunta duk wani Mai hannu cikin kulla Maka wannan sharrin yafada Yana ballawa ACP harara da itama ta iso wurin ta tsaya tana kallon papi.

Papi ya lumshe Ido Yana murmushi yace karka damu Mubeen in Sha Allah gsky zatayi halinta ynzu dai ka dauki abincin nan ka koma gida Kuma Dan Allah ka kula da Maminku ka tabatar tana cin abinci Kuma tana Shan magungunanta Dan Ibrahim yacemin BP dinta ya hau ko?

"Papi karka damu muna kula da Mami sosai ynzu dai Kaci abincin nan Dan ba inda zan koma dashi yafada Yana watsawa Mubeena harara"itadai batace komi ba, muryan CP sukaji daga baya Wanda tun dazun Yana tsaye daga bakin office dinshi duk draman da suke Yana kallonsu Yana fadin Alh. Mubeen daga yau pls karka Kara zuwa station din Nan abinci Kuma baza'a bashi ba tunda bamu barshi da yunwa ba ana bashi abinci kamar sauran masu laifi.

"Saboda ba uban ka bane abayan kanta ko? Mubeen ya fada Yana tasowa cikin fushi

Mubeena tace "pls Mubeen zo katafi Dan Allah!

"Ke ki fita harkata Mubeena wlh kika Kara samun Baki Ina magana sai na wanke Miki fuska da Mari ki kama kanki yar sanda taohhh"

CP yamurmusa yace ACP din zaka mara lallai Dana daureka har sai igiya tayi rara Kai bakasan darajanta kukeci har muke barinku zuwa ba ko? Laifin mahaifinka ba laifin da ake bari aga mutum bane Amma sbd ita muke barinku zuwa to daga yau na soke zuwan kowa idan ba lawyer dinshi ba sai ku bari sai an hadu a kotu...

Mubeen ya Bude Baki zai Yi magana papi ya katseshi "Mubeen indai ba kanason ganin bacin Raina bane zoka fita a gurin Nan dauki abincin katafi dashi na gode"

A zuciye Mubeen yajuya yakai hannu zai dauki kwandon abincin Mubeena ta rigashi dauka "kabarshi zaici abinci"wani kallo ya watsa mata tare da fusge kwandon yafice da sauri zuciyarshi na tafarfasa.

Yasha alwashin yanda ya fita da kwandon nan ya fita daga rayuwar Mubeena kenan Kuma yanda ta guma mishi bakin ciki sai ya shayar da ita bakin cikin rayuwa sai ta gwamnaci Bata sanshiba arayuwarta sai ya wulakanta ta kamar yanda ta wulakantashi da mahaifinshi alwashi kala kala Mubeen yake ci akan Mubeena da taimakon Allah ya kawo kanshi gida domin har wani dishi dishi yake gani Yana tuki Yana sambatu shi kadaii.

Niko nace Mubeena wane wacce irin zuciya gareki ne hka kodayake mahaifinta aka kashe fa mahaifi ko ba wasa ba!

*Amatullah*
Akwatunanta taja xuwa cikin gidan tai knocking qofar qaramin gate din gidan nan da nan habu mai gadi ya taso ya bude dan qaramin gate din

“”Aah qanwar anty daga Ina haka da wadannan lodin kaya kamar mai shirin barin duniya””
Ya fada yana dashare baki kaman daushe 😁

Dan Harara ta watsa mishi sannan tafara mgn
“”Maimakon ka xo ka amsammin kaya katsaya kana daushare baki kaman wani soko ni dallah kaxo ka rabani da kayannan””
Ta fada a gajiye

Matsowa yai ya amshi sauran akwatunan nata hadi da jefa mata tambayar anty ta sauka kuwa??

Cak ta tsaya danjin tambayar da habu mai gadi yake mata kenan dai dagaske anty aysha bata saukaba to wasu kaya yaya irfaan ke nufin indauko kardai ace maganar musa gaskia ce qilafa yaya irfaan kayan haihuwa yake nufi🤔

Batare da ta iya amsa tambayar habu ba hannunta tasanya cikin Jakarta data rataye a wuya ta ciro wayarta qirar iphone 6 ta lalubo numbern irfaan ta danna mishi kira,saida wayar takusa katsewa sannan aka dauka batare da anyi magana ba
Itace tai sallama sanan tafara magana Dan tasan dama xaiyi wuya ya tanka mata muddin baiji dalilin kiran ba,danma taci saah yau kira daya ya dauka’

“”Yaya irfaan gani cikin gidanku da kayan nawa dakace nadauko kuma naxo baku dawo ba...............””
Qitt taji ya yanke wayan Dan tsaki tai tace aikin kenan mutum kullum cikin baqin rai nkm ai bakomawa gida xanyi ba sai nagama xaman jegooo Dan nasan baqaramin kaya xanhauba wlh ta fada tana qarasa shigewa cikin katafaren gidan da inkaji ance Aljannar duniya to canne

***mubeen Muhammad yaaseer***
Ya riga ya gama yankema kanshi hukuncin matakinda xai dauka akan mubeena Dan hk office ya koma direct yacigaba da aikinshi cikeda baqin cikin mubeena .
Sai yamma liqis sannan ya koma gida kodaya tambayi securitys din gate ko mubeena ta dawo sukace eh tadawa amma ta qara fita ma,dajin hk ya shige da motarshi direct part dinsu ya nufa bai biya part dinsu mami ba saboda anfara kiran sallahn magrib

Bathroom din dakinshi ya nufa ya dauro alwala,
Giftawar ta ya gani lokacin da ya fito daga dakinshi bai tsaya ba Dan karya rasa jam’i kawai ya fice ya nufi masallaci’
Yauma kmr jiya bai dawo ba saida aka idar da sallahn ishi’i sannan ya nufi part dinsu mami sun dade suna tattaunawa da ita kafin ya tashi ya koma part dinsu

Koda ya shigo a main palour ya tarar da ita tana kallon news
Ranshi ne ya qara baci ganin yanda aketa maganar batnci akan papi anata yaga postocinsa da aka mammanna wasu na dage dawani qaton poster hoton papine radau hannunshi sanye da ankwa mubeena na riqeda hannun,
Mutane nata ihun bamayi bamayi(xanga xanga sukeyi akan dole a janye Alhaji Muhammad yaaseer daga takarar da aka tsayar dashi saboda ya xama bara gurbi bayansa fari cikin sa baqi qirin)

Hmmmmmm Allah sarki papi mutumin kirki☹️

https://chat.whatsapp.com/KDkpfCh3PTgAMGI4xMc81W

*X££l@hs Pen*•••••••✍️✍️✍️✍️

رَبِّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ أَنْ أَسْأَلَكَ مَا لَيْسَ لِي بِهِ عِلْمٌ ۖ وَإِلَّا تَغْفِرْ لِي وَتَرْحَمْنِي أَكُنْ مِنَ الْخَاسِرِينَ

*ACP mubeena*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.