Trending Hausa Novels

Acp Mubeena

Reading file: ACP_MUBEENA.txt

Chapter 15 of 18

Page 15

Doctor ne ya fara turo kofar ya shigo Mubeena na biye dashi abaya cikin Sakin fuska fara ma Aysha magana "ya jikin naki tace "dsauki" tambayoyi yashiga Yi mata nasu na likitoci itadai iyakarta eh aa wani Kuma tayi shiru sai da yagama dubata tsaf kamin yacire mata Karin ruwan yace wa Mubeena tabatar abinci taci zuwa anjima zai sallameta Dan jikin nata dsauki tace "okay thanks doctor"

"My pleasure " yafada yasa Kai tafita

Itakuma warmers din abincin ta jawo tazuba fatan Irish Wanda yaji hanta tajawo kujera tazauna tafara ba Aysha abincin da kanta abaki tun Yana nokewa har tasaki jiki tanaci suna Hira sosai Mubeena jata ajiki cikin kankanin lokaci Aysha tasake da ita sunata Hira kamar dama sun saba da juna,wannan Yana daya daga cikin baiwar da Allah yayiwa Mubeena saurin sabo ta iya Jan mutum ajiki ynda zai sake da ita sosai har ya fada mata abunda shi kanshi baiyi niyyah ba.

Sai da tabari tagama cin abinci Aysha tasaki jiki sosai Dan ynzu hirar tasu har dasu dariya ayshar keyi kaman ba abunda ke damunta Dan sosaii Mubeena ta zage tana ba Aysha lbrn Amatullah Wanda ashekaru ynzu zatakai Sha bakwai Amma wauta da sobalancin kamar yar fari yar shekara takwas haka Amatu take Aysha tace "Dan Allah anty kikawo min Amatullah din inason ganinta"

Mubeena tamurmusa tace "karki damu idan na maidaki gida zan kawo Miki ita sai ku kula kawance"

Waro idanu Aysha tayi tace "Kai aunty ai ta girmeni"

"Eh Amma ai kin fita hankali Dan ita wannan yanda kikasan yar shekarunki haka take to ke Zaki ringa sata ahanya ai nasan Zaki iya ko" dariya Aysha tayi tana gyada Kai.

Gyara zama Mubeena tayi tace yauwa yanzu inaso ki gayamin waye ya aikata maki fyade?
Raurau tayi da Ido tace "wallahi aunty ban sanshiba Amma idan naganshi zan iya ganeshi"

"Yauwa to bani lbrn yanda abun ya faru"

"Ina dawowa daga makarantar islamiyya ne dayake anguwarmu ba mutane sosai,dama ni da kaninah muke zuwa to ranar bashida lpy ni kadai naje Ina hanyar dawowa Dan har nakusa gidan mu sai wata mota tayi parking akusa Dani aka Bude kofar Mayan wani mutumi ne azaune da face mask afuskarshi yatambayani wai nasan gidan Alhaji ma'aruf nace aa har najuya zan wuce naji an fuzgoni da karfi cikin motar sannan aka Jata da gudu na Bude Baki zanyi ihu aka shaka min wani Abu,to daga Nan ban Kara sanin inda nake ba bansan iya dadewar danayi ba nidai abun ya sakeni dai dai lokacin da wannan mutumin yake aikata min wannan mugun Abu tabbass naga fuskarshi sosai Dan na dawo haiyyacina adaidai lokacin danaji wata irin azabar daban taba jiba nidai nasan jikina yamin nauyin da ko yatsana bazan iya dagawa ba Ina jinshi Yana aikata min abunda bazan taba mantawa ba nasan dai tunda na kwala ihu sau daya ban Kara sanin abunda ke faruwa ba sai farkawa nayi naganin a nan gadon asibiti.share hawaye Mubeena tayi wannan wace irin rayuwace Ina mutane zasukai son zuciya da rashin imani yanzu Mai abun dadi ajikin wnn yar tatstitsiyar yarinyar da ko irgan dangi ynzu ta fara Amma Dan rashin imani ya keta mata hadi ai sai inda karfina ya kare kuwa,ajiyan zuciya tasauke tashiga lallashin Aysha da keta razgar kuka sosai anfamo mata ciwon dake cin zuciyarta tace kiyi hakuri Aysha yanzu dai bansan inda zamu gano Wanda yyi Miki wnn mugun aikin ba Amma saukinta kince Zaki gane fuskarshi to in Sha Allah zamu dage da adu'ah Allah ya Toni asirinshi kowayeshi yanzu inaso ki bani address din gidanku anjima da yamma idan an sallameki zanzo namaidake nasan sunachan cinikin tashin hankalin rashin ganinki.

Nan ta karanta mata address din ita Kuma ta rubuta awaya tamike tamata sallama tare da Kara kwantar mata da hankali akan tana tare da ita Kuma zata tsananta bincike Akai kamin tasakai tafita, direct office din likita ta wuce ta amsa report din tafita gaba daya daga asibitin hanyar gidan Barrister Irfaan ta cilla motarta Dan yau zasuyi magana sosai akan case din papi.

⭐️💫🌟💫⭐️🌟
*mubeen Muhammad yaaseer💗💫*
Bayan tasowa daga gurin aiki ya yanke shawarar xuwa gdn ummah yau ya qara mata gaisuwa tun komawar ta baisamu yaje ba,Sannan yanaso yyi mgn da ita dan ganin yake har lokacin bata san abinda ke wakana ba,daga wajen gidan yai parking motar shie ya qarasa ciki,Dan madaidaicin gidan xaman mutum daya mai gadi ne daya sai mai bama flour ruwa da sharan tsakar gidan, sai mai musu dan aikace aikacen gdn kuma duk aikin papi ne,a gaskia gdn nada matuqar kyau,most especially yanayin tsarin ginin yyi matuqar burgeni duk da kasancewar shi Dan madaidai ci,direct akai masa iso har cikin palourn umma,bayan yan gaishe gaishenda suka gama yi da qara jajanta rashin da sukai nan ya fara mata bayanin case dinsu papi daga farko har inda aka tsaya,atunaninshi xaiga tashin hankali da al’ajabi a fuskar ta amma da mamakin shi sai yaga murmushi kwance akan fuskar ta ta amma baice komai ba,
Dan nisawa umma tai ta fara magana cikin natsuwar nan tata,
“Uhm mubeen tun kwanaki kafin ma lokacin ta kamashi inada lbrn komai kuma ina sane da duk abinda ke faruwa kayi haquri kamar yadda mubeenar tace idan akaje kotu komai xai warware,Dan hk kuqara haquri “Toh kawai mubeen yace yatashi yabar mata dakin dan muddin ya cigaba dajin wadannan magan ganun nata tabbas xuciar yan maxa xai motsa,
Cikin motar shi yashige ya dade yana mamakin matar danshi wlh duk tunanin shi batasan abinda ke faruwa ba lallai ashe dai mubeena a nono tasha butulcin nata,yanxu ace duk irin halaccin papi garesu irin sakamakon da xai samu kenan,baiyi tunanin a irin halaccin da papi yyi musu ba tundaga kan mahaifin dasuke taqama dashi har sudin shine gatansu daga sama har qasa,
Koda ace papin ne yayi kisan yaci subar halak Dan kunya,a tunanin shi ummah morning ita ce xata gyara komai ta hana mubeena abinda takeyi amma ashe da hadin bakinta komai ke faruwa,’

To ai shikenan wlh yadau alqawarin sai ya koya musu hankali dukansu xasuji a jikin sune 😡

*💫________________⭐️*
Garin yyi baqin qirin kasantuwar dama daidai wannan lokacin dole gari ya kasance baqin qirin domin goma harta gota na dare,
Tafiya take sannu a hankali a babban titin birnin kano da alama qarfen nasara na neman bata matsala Dan irin kukan da engine din motar keyi dkm yanayin yanda take tuqin,
Addu’ah taketa karantowa Dan a gaskia inhar motar nan ta tsaya mata a wannan gurin bata tunanin xata samu adaidan da xai qarasa gida da ita,yau tayi ayyuka da dama wanda suka riqeta harta kai wanna lokacin awaje,daidai zata shiga titin daxai sadata da papi mansion motarta ta tsaya cak “oh sht ta fada hadi da tsaki dole ba yanda xatayi ta fita daga cikin motar,yan kayayyakin ta ta tattara dake acikin motar ta fito locking motar ta tayi taso takai kusan minti 10 atsaye Dan ganin ko xata samu adaidai ta ya qarasa da ita gd amma Ina bbu wanda ke wulgawa a hanyar,ta miqi dogon titin da xai sadata har gida,shiru bakajin motsin kowa,kasantuwar dama anguwar masu kudi ta gaji hakan da’ace irin unguwar muce ya yayan malam shehu daidai wannan lokacin ne maxa ke hada majalisa amma sukan masu hannu da shuni shiru kakeji kowa na kulle cikin gidanshi da iyalanshi harda masu tsaron lpy da dukiyar shi,.

dukda kasancewar darene amma titin dauke yake da manyan light 💡 bobs,tafe take sanye da kakinta na yansanda da akullum yake sa kwarjinin fuskarta yawaita duk lokacin da take sanye dashi.

Tafiyar ta take bbu alamun tsoro ko damuwa ko kadan akan fuskar ta
Daidai lokacin da takai tsakiyar titin kwatsam wadannan globs din dib kakeji sun dauke baki daya kamar hadin baki,innalillahi nan take ko Ina ya gauraye da duhu baqin qirin kotafin hannunka baxaka iya gani ba,
A wanna karan kuwa gaban mubeena yyi mummunar faduwa Dan idan dakwai abin da take tsoro a duniya to duhu ne,tana matuqar tsoron duhu fiyeda komai a duniyar ta,amma bbu yanda xata yi Dan a tsakiyar titin take.
Tsayawa tayi cak Dan tama rasa me xatayi adai dai wannan lokacin dan haka tayi tsaye ita batai gababa sannan batai bayaba.,
Jin tai kmr motsin mutane gab da ita nan take tsoro ya qara kama mubeena gashi ta kasa dauko wayar ta,ta kunna touch light,
Ta gama sadaqar wa dole there is something behind the darkness saboda a iya sanin ta bbu yanda xaayi wutar titin ya dauke koda kuwa bbu wuta akwai solarn dake aiki duk qarfe 6 in aka kunna sai sfe sannan ake kashe wa.,tana cikin wannan tunanin kwatsam sai ga wutar ta dawo tarrr amma saime juyawar da mubeena xatayi kwatsam taga tarin maxa wanda aqalla sunkai su biyar,daganin su xaka tabbatar da yan dabane na qarshe fuska bbu imani suke kallon mubeena kowanne da gora a hannun shi,cikin dakiya irin ta mubeena da taurin xuciya ta kallesu tace malamai lpy meke faruwa ne,kunada matsala dani ne,dukda a tsorace take da ganin su bbu shiri,
Daya daga cikin sune ya karkata baki irin nasu na yan daba yafara magana
“Kedallah fita su waye malamai, to inma kince ne Dan mu fasa abinda ya kawo mu to yasin bbu fashi sai mun aiwatar,”yakai qarahe yana daga goran dake hannun shi sama,
“Su waye ku?.
Waya aiko ku?.
Me kuma kuke shirin yi?
Mubeena ta jeru musu wadannan tambayoyin tana kallonsu daya bayan daya.
Daya dake gefen wanda ya fara magana yace “dallah oga rabu da yar rainin sense dama na dade ina dakon ta itace kwanaki tasa akai ram damu sai da mukai laushie a bayan kanta sannan aka sake mu tun lokacin nake dakon ta sai gashi cikin saah ankawo mana kwangilar ta”
Nan suka dauki dariya baki dayansu,
“Bana son shiririta ku bani hanya in wuce inkuwa ba haka ba xan koya muku hankali,mubeena ta fada dukda a tsorace take,
“Bbu inda xakije sai mun aiwatar da abinda mukai niyyah akanki,Dan haka kar inqarajin komai daga gareki”batare da shiri ba kawai taji saukar gora a tsakar kanta,nan take ta fadi qasa dafe da kanta basu bari tadawo cikin hayyacinta ba suka fara kaimata duka ta ko ina saida suka tabbatar ta daina motsi sannan suka dakata da dukan nata,
Daya daga cikin sune ya dauki waya ya lalubo wata number ya danna kira jimm kadan aka dauki kiran
“Hello boss mun qaddamar mata fa kuma aiki yyi kyau bana tunanin ma tana da saurar rayuwa inkuwa akwai shi to bama tunanin xata dawo cikin hankalinta Dan nk gaya mk manu ne ya sakar mata gora tsakar ka”nan take suka sake kwashewa da wata muguwar dariyar bosawa,nan ya cigaba da maganar
“Dan haka a shirya mn sauran balance dinmu gobe xamu xo mu karba sauran haqqinmu ”maganganun da mubeena taji kenan kawai tai give up(ta sume)

Tofa jama’ah wake neman kashe mana mubeena kuma😩🤔

Daga alqalamin 👇
*X££l@h’s pen✍️✍️✍️✍️*

Littafin ACP mubeena paid book ne kudaure ku biya 300 danjin yandaxata kaya har qarshe❤️

https://chat.whatsapp.com/IIzvJ7l40854gOZahJJxq2

*X££l@h’s pen*

رَبِّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ أَنْ أَسْأَلَكَ مَا لَيْسَ لِي بِهِ عِلْمٌ ۖ وَإِلَّا تَغْفِرْ لِي وَتَرْحَمْنِي أَكُنْ مِنَ الْخَاسِرِينَ

****ACP mubeena****
Page 16

Anan suka bar mubeena kwance suka kama gabansu sai can guraren shadaya dawasu mintinin sannan saiga wata baqar mota qirar marcedez Benz ta kunno kai cikin unguwar ,har motar ya wuce inda mubeenar ke yashe a qasa sai kuma ya dawo ya tsaya daidai wurin,driver site naga anbude daga nan wani dan matsakai cin mutum y fito da alama drivern mamallakin motar ne dayake gurin da wadataccen haske yasa xaka iya ganin komai tarr dama daxu su manu ne suka kashe ta kuma sun qara maido dashi,
Hankalin shi baqaramin tashi yyi ba ganin fuskar wadda ke kwance a wurin dan yasan mubeena farin sani saboda alaqar da ke tsakanin papi da mai gidanshi,da sauri naga ya nufi motar su daga nan naga ansauke glass din motar qasa,shima fitowa yyi da sauri mamallakin motar,
Alh.Aminu ne(shuhaban jam iyyar su papi kuma aminin shi ) ya fito a gigice ganin irin halin da mubeena ke cike batare da tsayawa yin wani tunani ba ya ciccibe ta ya sanya a bayan motar shi,.
Juya motar su sukai suka koma inda suka fito wata babban p.v hospital 🏥 mafi kusa dasu suka nufa da mubeena suna xuwa batare da bata lokaci ba suka karbeta sanin matsayi irin na Alh.Aminu dkm ganin p.unifoam dinda ke jikin petience din tasu basui wani jinkirin karbar taba kuma Allah yasa hospital din basuda wasa ko kadan kuma akwai wadatattun drs a hospital din 24hrs kuwa
Nan take suka shiga emergency room da ita likitoci Sun shafe kusan awa akanta hardai Allah ya basu ikon ganin numfashin ta ya daidai ta kuma har lokacin Alh.Aminu na xaune bai bar asibitin ba,sai da babban likitan ya fito yace su sameshi a office dinshi
Nan Alh.aminu ya bishi bayan yan tattaunawar dasukai dr yatambaye shi baasin abinda yafaru iya abinda yasani kawai ya fada ma dr daga bisani drn yake bayyanawa Alh.Aminu abinda ke akwai aiya binciken su na likitoci Sun gane a sanadin dukar da akai mata aka badan Allah ya taqaita wahala ba da tabbas tayi loosing memories dinta saboda sun saba amsar ire iren cases dinnan, cikin ikon ubangiji mai tausayi dakuma jinqai,mai ikon juya fari xuwa baqi ga wanda yaso a duk lokacin da yaso,yasa hakan bai faru ba saidai gaskia ba qaramin buguwa taiba akaan nata,for know gaskia she is unconscious and xai iya daukar Dan lokaci b4 ta dawo daidai,xasu riqeta har sai lokacin da taji sauqi sannan su sallameta,
Alh.Aminu ya gamsu da bayanan dr sannan saida yabiya duk wani abu daake buqata kafin barinshi asibiti da xummar gobe in Allah ya tashemu lpy ya sanar da iyalanta abinda ake ciki Dan yanxu kam dare yayi sosai,nan sukai sallama da drn ya fita nan waje yasamu drivernsa sai gyangyadi yake ba qaqqautawa suka wuce gida,

🌟*mubeen Muhammad yaaseer*💗
Tun bayan barinshi gdn su mubeena direct mansion dinsu yanufa rai a jugule Dan gaske baiwar Allahn nan ta shayar dashi mamaki ba yar kadanba,Dan a gaskia sanin da yaima umman mubeena macece mai haquri da tawakkali sau dayawa mami kan mata abubuwa kala kala tashanye sa’annan batada hayaniya samm amma dai tana matuqar qaunar ‘ya’yanta sosai bata yarda sui cuta ba kuma bata taba yarda wani mahaluki ya cutar mata dasu ba amma dukda hakan bai hana ta tarbiyyan tar dasu akan tsari irin na addinin islama.,
Bayan xuwan shi gida saida yafara sanar da mami duk yanda sukai da umma din nan da nan zuciar ta taqara harxuqa sai bambami take daga qarshe tace wlh sai ta hukunta su fiye da yanda ake tunani daga uwar har yar sai sunsan sun tabo m kansu rina,
Bayan komawar shi part dinsu yake tambayar tala ko mubeena ta dawo tace mishi aah,nan ya xauna a palourn ya cigaba d sabgogin shi,ya dade a palourn xuciar shi cunkushe ptan shi kawai a shiga kotu a wanke mahaifinshi daga xargin da ake mishi nan xai bude babin wulaqanta mubeenar da hujja, kusan ma a palourn ya kwana baccin rabi da rabi yyi.,
Yyi mamakin har wuraren asuba baiji shigowar mubeena ba nan ya tashi ya leqa dakinta wai Kota shigo lokacin yana bacci amma yaga wayau,nashi dakin ya koma nan dinma dai bata ciki,cikin basarwa yace ita ta jiyo maybe ummahn ta tafada mata yanda sukai ne yasa ta yanke shawarar komaw can,dage wuya yyi Aransa yace aikuwa datafi nono fari Dan duk lokacin da yaganta harga Allah jiyake kamar ya shaqure wuyar yar banxa ta mutu kowama ya huta,
(Da kayi life in prison kuwa😏)

Fitowar shi wanka keda wuya wayar shi tafara ringing nan saida ya gama share ruwanda ke saman kanshi da towel kafin ya nufi inda wayar ke aje by then kiran ya katse,kafin ma yyi unlock din wayar yaduba mai kiran sai ga wani kiran yaqara shigowa,uncle Aminu ke kiranshi baiyi mamakin ganin kiran nashi ba sbd tun lokacin da aka fara case dinnan tare suke fighting’ Dan ganin anyi freeling papi,
Bayan ya dauki wayar a ladabce ya gaida Alh.Aminu ckn girmamawa,shiru yyi danjin abinda yake gaya mishi
“Son jiya da daddare a hanyata ta komawa gida na tararda wani mummunar al’amari,nan ya kwashe duk yanda akai ya fadama mubeen”
Da mamakinshi maimakon yaji hankalin mubeen din atashe jin abinda yafaru da matar shi amma sai yaji akasin hakan

Cikin ko inkula da al’amarin yace
“And then uncle why did you count me in,I have no more relationship to share with her for know dan haka ka kira ummahn ta kawai ka fada mata xaifi danni bana tunanin akwai wata alaqa atsakanin mu,”

Da mamaki Alh.Aminu yace
“Aah mubeen yada haka magana fa nike maka ta matarka mubeena bawata ba”

“Eh nasani uncle shine nace ka kira ummahnta ka fada mata xaifi nibani da abinda xam mata,yauwah uncle anjima barister xai shigo inya shigo xamu xo tare dashi muji yanda xata kaya Dan am eager to see my dear papi out of gel,saika jini bari in shirya am running late,”ya fada tare da yanke kiran kafin ya aje wayar saida ya turama Alh.Aminu numbern mman mubeena, cikin ransa yana ayyana ai wlh kadan ma tagani tunda ta rasa wanda xata wulaqanta sai that innocent soul papi kuma tayi tunanin xata cigaba da ganin daidai,ina ai wannan farawa ce ma ya ja qaramin tsaki yaci gaba da shirin shi,

(Anya mubeen bbu sa hannunka a aikatawa masoyiya wannan aika aikar kuwa🤔,gaskia nasa maka ayar tambaya❓,ace al’amari kmr wannan ya faru ga matar ka amma ka nuna halin ko inkula🤔)

Alh.Aminu da tunda ya fara jin bayanan mubeen yakusan sanqare wa wurin dan mamaki harta ishe shi jin magangunun mubeen din,kafin yasamu damar yimashi mgn kuma yaji ya canxa topic hadi da yanke kiran,murmushi yyi irin tasu ta manya yace lallai mubeena ki qular min da son kafin aje wayarshi shima yaji qarar shigowar message daya duba yaga numberce mubeen din yaturo mishi ya tabbata ta mmn mubeena ce nan bada bata lokaci ba ya danna mata kira bayan gaisuwa da sukai ya sanar mata abinda ke faruwa da yarta ykm bata address din asibitin da aka kwantar da ita

Wannan kenan 🥰

https://chat.whatsapp.com/IIzvJ7l40854gOZahJJxq2

*X££l@h’s pen*

رَبِّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ أَنْ أَسْأَلَكَ مَا لَيْسَ لِي بِهِ عِلْمٌ ۖ وَإِلَّا تَغْفِرْ لِي وَتَرْحَمْنِي أَكُنْ مِنَ الْخَاسِرِينَ

****ACP mubeena****

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.