Acp Mubeena
Reading file: ACP_MUBEENA.txt
Chapter 9 of 18
Page 5
“@Inkuwar har mubeena is on her sense take aikata wadannan abubuwa I swear to Almighty I won’t spear her she must pay for her bad act””
A cewar mubeen da ya gama harxuqa da lamarin
“Mubeen karkai abinda xakaxo daga baya kayi danasani shi komai a hankali ake binsa sai kaga ya xama labari kaidai keep praying insha Allah komai xai daidaita soon”
Acewar papi da yasan halin danshi mubeen,mubeen na daya daga cikin mutanannan da Sam basu iya fushi ba ta mahaukata suke yi insuntashi yinsa sai daga baya suxo suna danasanin da bashida amfani,
“Maganar papi baqaramin qara qonama mubeen rai yayi ba Dan haryanxu baiga alamar qi ko tsanarsa ga mubeena ba duk irin abinda tai masa kuwa
Sundan tattauna da papi sama sama indayake qara kwantar musu da hankali da basushawarar subi komai a hankali komai xai daidaita insha Allahu
Sun yi masa mgnr kawo lawyern shi amma yaqi amincewa da batun yace su bari akwai shirin da yakeyi karsu damu kansu
Abin yayi matuqar basu mamaki da kuma daure kai taya xaice baya buqatar lawyer kuma yanadashirin da yakeyi mutumin dake garqame acell
Babu yanda suka iya dole suka haqura suka qyaleshi amma cikin xuciyoyinsu da qodurin yin magana da lawyern nashi Dan baxasu iya barinshi a wannan halinnba yauma babu yanda suka iya ne yasa xasu barshi ya kwana a station
Copur balane yashigo ya isar musu da saqon CP lawal usman nacewa lokacinda aka dibar musu ya wuce Dan haka xaa a maida shi cikin cell
Babu yanda suka iya dole suka tafi sukabar papi acikin cell
Allah sarki yanxu ace hamshaqin mai kudinna kuma adalin dattijonda duniya ta sanshi dakuma irin tarin alkhairanshi shine xai kwana a cikin cell
Wa iyaxubillah su uncle abbas haka suka tafi suka bar papi cikin cell axuciyoyinsu kuwa tsinuwa ce sukaita ma mubeena yafi cikin drom
~~~su uncle abbas a sassauta ma mubeenar mu mana wannan tsinuwa haka😂,dadin abin masoyiyar tamuma batasan kunayi ba🤪~~~
*Papi mansion*
Bayan komawarsu gida kowannansu jiki a sabule suka rabu kowa ya nufi part dinshi Dan sunsan in suka je part din papi qara tayar ma kansu da hankali kawai xasuyi
Daidai xai shige cikin part dinsu ita kuma tafito sanye da dubai abaya baqa ba qaramin kyau taiba ta yana vail din abayar a kanta dauke take da lunching basket 🧺 a hannunta wanda ke dauke da wasu hadaddun food warmers a ciki
Mubeen kallo daya yai mata ya watsar ya cigaba da tafiyarsa
“”yallabai barkanka da dawowa””
Ta fada cikin sigar wasa hadi da wannan crazy smile dinnan nata mai qonama su mami rai
Ko wai wayen inda take beyi ba ya cigaba da tafiyarshi dan yaga alamar muddin ya tsaya biyema mubeena yanxu xai iya mata illah da duka dan yanxu ya gama kawo wuya
Yaga alamar bbu wanigushewar tunani a cikin hayyacinta take kawai tsabar rainin wayau ne dakuma butulci ke damunta
Wata shuumar dariya tai maidan sauti tace oho dai
Ta cigaba da tafiyar ta
Lallai iya quluwa mubeen yakai qarshen linter kai dolema in koyama marar kunyar yarinyar nan hankali insaukar mata da haukan dake kanta kafin abu ya hayaqa ya fada qasa qasa hadi da qyacci
“””xaki dawo ki sameni ne”””
Ya fada sannan ya qarasa shigewa cikin part dinnasu
Ita kuma cikin mota ta sa basket din ta shiga driver Seat 💺 ta bar mansion din
Kai kawo yake tayi cikin palourn su kusan 1hr kenan yana jiran yaga dawowarta amma shiru ko gidan ubanwa ta tafi oho
Sallar magriba akafara kira ya sashi ficewa daga part din ya nufi masallacin dake a cikin mansion din nasu
Bayan idar da sallah bai motsaba yaita laxumi akan Allah ya sassauta mishi abinda yakeji a xuciyar shi kafin ta dawo dan ya tabbata muddin yana mood dinnan ta dawo xai iya mata illah
Haqiqa ya dan samu sassaucin xuciya kafin ai sallar isha’i ya baro masallacin ya koma part dinsu
Xaune take saman dining tanacin abincin ta cikin kwanciyar hankali hadi da Dan daddanna wayar ta
A harxuqe mubeen ya qaraso inda take xaune ya tsaya gab da ita hadi da riqe qugu
“””lallai butulu ke watooo har kinsamu dama irin haka ta wulaqanta mutumin da yai mk fiye da abinda wanda kike taqama mahaifin daya haifeki bai miki shiba
Ya yantaki ya daukaka ki sannan ya tsaya miki akan komai na rayuwarki fiye da mu da muke ‘ya’yanshi
Kin wulaqanta shi Sannan har kinsamu damar xaman cin abinci cikin kwanciyar hankali
Wani vanxan kallo mubeena ta dago taima mubeen na sheqeqe ta watsar ta cigaba da cin abincinta kamar ma batasan yanayi ba,
Wohoohoooooooo😧
Lallai wannan abunda tai ba qaramin qara harxuqa mubeen taiba dole ya koya mata hankali
Gab da ita ya qara matsowa ya tura dining chair dinda take xaune akai jikin bango hadida shaqo wuyanta shaqa bana wasa ba sai da idonunta suka firfito sukai ja ta fara kakarin wuya
Tofa team mubeena kuxo mu kawo ma masoyiya dauki kar mubeen ya kashe mana ita🙆♀️🙆♀️🙆♀️🙆♀️🙆♀️
Daga alqalamin
*X£l@hs pen*✍️✍️✍️✍️✍️
https://chat.whatsapp.com/KDkpfCh3PTgAMGI4xMc81W
*X££l@hs pen*•••••••••✍️✍️✍️✍️
رَبِّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ أَنْ أَسْأَلَكَ مَا لَيْسَ لِي بِهِ عِلْمٌ ۖ وَإِلَّا تَغْفِرْ لِي وَتَرْحَمْنِي أَكُنْ مِنَ الْخَاسِرِينَ
****ACP mubeena****
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.