Trending Hausa Novels

Acp Mubeena

Reading file: ACP_MUBEENA.txt

Chapter 17 of 18

Page 19

Gidansu ta umarci driver ya fara kaita duk da tanajin ciwon kai kadan kadan Amma dole ta fita saboda Maida Aysha gidanta iyayenta batason saba alkawari tasan iyayen nacen hankalinsu ya tashe, ko da ta isa falon gidan tayi mamakin ganinsu Amatullah da gwaggo abaje a tsakiyar falon sunata breakfast da soyayyan dankalin turawa da feefesun gaji ga kunun gyada,sun baje sosai harda umma da Aysha da ke rike da zain tana mishi wasa da alama ita da umma sun Dade da karyawa Dan lokacin har shadaya ta Kusa "ah lallai Kuna sha'aninku mutanen gidan Nan wannan irin danashar arziki kunyi kulu washrabu kunyi hani'an abunku"

Gwaggo ta washe Baki taka Kara yagar kafar kazar dake hannunta tace "ah ah yar sanda kece yau da uwar safiyar nan haka harkin ji sauki kin fito?
Mubeena tace "aiki zancewa meye ya fito daku da uwar safiyar nan sai kace daku suka kwana da alama ma Baku karya agidanku ba kukazo ku cinyewa umma nata abun Karin"

"Yo Ina dalili zamuyi ta zama a wannan katon gida mukadai sai kace mayu ai da Barrister zai fito ne nace gsky mudai zamu bishi ya saukemu gidan hajiya umma,keni wani zubin gidan Nan ji nake kamar ba mu kadai bane ko Amatu? Gwaggo saude ta karshe tana duban Amatu daketa Shan kunun gyada dama ita da kunun gyada 5&6 suke,Amatu ta dago tace "Kai gwaggo to ni dawaye agidan kedai Allah ya zuba Miki shegen tsoron tsiya kiri kiri tsohuwar Nan bazata kwana dakinta ba haka zata zo ta nanukemin adaki nida zain gashi gadon ba isarmu yake mu uku ba" ta karashe tana ciskune fuska

Umma ta Bude Baki tana kallon Amatu da take zacenta tsakani da Allah iya gskyrta take fada tace "Kai Amatu kiji tsoro Allah ynzu wannan katon gadon ne yayi maku kadan?
Gwaggo data karashe shanye romon Naman Kazan tadire plate din tace "ke dallah rabu da ita zancen takeso kwana dai dole daki daya zamu ruka kwana Dan bazan barki da jaririn yaro ba kije ki danneshi da wannan mugun baccin naki ahtoh..
Mubeena da tagaji da Jin zancensu tace "Aysha kin kwana lpy? Da sauri Aysha tamika mata zain ganin ta kawo hannu tanaso ta daukeshi tace "lah! yi hakuri Aunty bamu gaisa ba Ina kwana"

"Lpylau Aysha Ina fa wayanan sarakan dumin sun cika mana kunne ince tun Asuba suke gidan Nan Hala? Amatu ce tayi charaf tace "aunty Yaya barrister nefa ya saukemu da zai wuce wai wani aiki yakedashi urgent! Shi dai haka yake bazai taba iya zama cikin iyalinshi ba ko Dan zain yada zauna suyi wasa...hmmm ta karashe da alhini afuskarta da alama tanajin haushin rashin zaman barrister agidan.

Umma tace " to idan Banda abunki Amatu aiki yataso sai bazai fita ba Kuma ai wane wasa zai zauna yyi da zain yaro Dan jariri kedai Allah ya yaye maki wautar Nan taki"

"Ameen dai umma ki tashi ki shirya mukai Aysha gidansu Dan inaso na karasa gurin aikine"

Umma ta Kalli yarta ya cikin tausayawa tace "ynzu ke har kinji saukin dazaki fito ni nayi mamakin ganinki ma keda yakamata ki kwanta ki huta"

Mubeena tace "dsauki sosai umma kinsan dole zan fito tunda ran Monday ne shiga court "

"To Allah ya Baki lpy ya Kara tsarewq bari naje na shirya na fito"

Hira suka cigaba dayi har umma ta fito suka dunguma gaba dayamsu Dan Amatu tace zataje Taga gidansu Ayshan Dan hka itama gwaggo tace bazata zauna gadin gida ba haka Suka fita gaba dayansu,suna hanyane CP yakirata tace mishi ta biya wani wuri Amma bazata Dade ba yace to,suna hanya ne dayake agaban mota ta zauna direban Dan sandan na tukasu ta gefen glass ta hango wata bakar mota na binsu Wanda tundazo taga motar abayansu sai yanzu tagane ana binsu to waye wannan? Sergeant Adam dake tuki tayiwa alama tuni ya Gane abunda take nufi Wanda shi yadade da lura da Hakan tunda suka baro gidan umma ake binsu abaya cikin yaransu na Yan sanda tace sergeant me kake jira "battt zaka musu kawai" yace yes ma, cikin dubara ya bace musu har suka iso gidan su Aysha Basu ga motar Wanda Mubeena ta dasa zargin shin ita ake bibiya ko Kuma Aysha da dama tasan dole Hakan zai iya faruwa indai har Wanda suka mata fyade suka Gane Bata mutu ba.

*Gidansu Aysha*

Da sallama suka shiga da kaninta suka fara cinkaro Yana wasa atsakar gida ganin Aysha yasa ya zuba ihu Yana "yaya Aysha mama mama ki fito ga Yaya ta dawo Abba ga yayaaaaa" dagudu ya rungumeta itama rugumeshi tayi tafashe da kuka, cikin sauri mama ta fito tana ganin Aysha tahau hamdala" Alhamdulillah Allah na gode Maka Aysha ke nake gani Aysha Ina kika shige yau Kusan kwana biyar Baki na lbrnki ba inda ba muje nemanki ba? Suna haka Abba Shima yafito dama Yana toilet ne "Alhamdulillah wanake gani kaman Aysha"mama tace itace Ayshanmu ce"

Nan dai aka zauna anata jimantawa bayan agaigaisane Mubeena ta Basu lbri tundaga yanda akayi aka sace Aysha har zuwa yau kuka sosai mama da Aysha har ma Amatu ta tayasu shikuwa Abba innalillahi kawai yake maimaitawa umma da gwaggo ne keta Basu Baki inda Mubeena ta tabbatar musu zata tsaya iya karfin domin ganin ta kwato mata hakkin ta Nan dai suka Basu Baki da shawawari sukayi exchanging number da Mubeena suka rakosu har mota suna godiya,Mubeena sai Kara kwanatarwa da Aysha hankali take tana jadadda mata Zata dawo haka Suka rabu Aysha nata kukan sabon da sukayi na Yan kwanaki itama Mubeena duk ranta ba dadi to ai dole ma ta sa Ido akan Aysha domin batasan su waye ke bibiyarsu ba🙄.

*POLICE STATION🚔*

Bayan sun sauke su umma station suka nufa ahanya ne take bawa Seg.Adam umarnin ya samata ido sosai akan gidansu Aysha domin Bata yarda da masu binsu din Nan ba tana ganin kamar Aishan ake bibiya,suna Isa da sauri ta shiga ganin yanda lokaci yaja tasan CP nachan na jiranta gashi ya tsani jira tana shiga Yan sanda suk hau Sara mata ana mata sanu da zuwa da gaisuwan yajiki daga musu hannu kawai tayi tana sauri tanufi office din CP kofur Musa ne ke kokarin sanar da ita CP nada bako Amma Bata saurareshi ba tayi ciki har takai hannu zata Bude kofar sai taganta ta abude zata tura kenan ta dakata Jin muryan wani babban mutum na furta " ai nagaya Maka duk yanda zakayi kayi Amma kada kabari tagane gsky nifa da sonayi kawai Shima a gimtse Mai numfashi tunda nagaya Maka yasan komai Kuma Shima akwai wasu sirrikanmu ahannushi barinshi arai hatsarine babba!!!

CP yace "na gayamaka ka kwantar da hankalinka everything is under control" ganin CP na kokarin mikewa yasata Bude kofar kawai ta cusa kanta idanunta akan fuskar CP yanda tashigo musu abazata ta shammacesu Dan haka duk suka daburce ita Kuma ganin haka yasa tasaki shu'umin murmushin Nan. Nata tace "sorry sir I kept you waiting" ganin alamun Bata ji Mai suke tattaunawa ba yasa yace "hba badamuwa ACP ya jikin naki "da sauki sir"
Good morning" ta juyar dakata tana gaida hamshakin Alhajin dake zaune akujera

"Morning ACP ya aiki?

"Alhamdulillah" ta furta tana kare mashi kallo ta wutsiyar Ido batare da su dukansu sun fahimta ba mikewa Alhajin yayi ya mikawa CP hannu sukayi sallama,ya juya ya fita.

Zama CP yyi itama ta zauna akujera Mai facing dinshi tattaunawa suka karayi akan case din papi tare da sanar dashi hujojin dake hannunsu,mikewa yyi ya nufi yar safe din dake office din ya sa babban yatsanshi yyi scanning tumb print kenan ya Bude ya fito da wani Dan karamin flash drive duk abunda yake tana kallinshi ta gefen Ido, takowa yyi har Kusa da ita ya mika mata ta amsa Yana furta "best of luck"

Tace "thank you sir" tare da Sara mishi ta juya tafita,binta yyi da wani irin murmushi.......

****

Littafin ACP mubeena paid book ne gamai buqatar karan tashi har qarshe yyi payment dinshi ankusa gama free pages
300 naira only 👌
Wanda ya shrya payment yy min mgn ko yyi ma @⁨Himlat❤️⁩

*X££l@h’s pen*

رَبِّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ أَنْ أَسْأَلَكَ مَا لَيْسَ لِي بِهِ عِلْمٌ ۖ وَإِلَّا تَغْفِرْ لِي وَتَرْحَمْنِي أَكُنْ مِنَ الْخَاسِرِينَ

****ACP mubeena****

*Littafin ACP Mubeena na kudine naira 300 kacal ki biya ta wnn account din 9161738928 Zainab Yusuf Alhassan opay.

*Last free page*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.