Trending Hausa Novels

Acp Mubeena

Reading file: ACP_MUBEENA.txt

Chapter 5 of 18

Part dinda mubeen yashiga daxun nan naga suma sun shiga

Xaune yake a cikin katafaren parlournsu wanda tsayawa fadin kyau da dukiyar da aka barka abune da baxai yiwuba ga wani qamshi dake tashi a palourn na burner da sanyi
Xaune yake akan kujera 2seater ya hade kai da gwiwa abun duniya ya gama isar shi yana rasa wani irin tunani xeyi da xaisa xuciyarshi tadan sassatau daga xafin da tai
Haqiqa ranar yau ta kasance ranace wadda aka kafa wani mummunan tarihin da bai taba xaton xai kasance a kanshi ba

Ko sallamar dasu mami sukaita qwalawa baisan ma su nayi ba saida mamin taxauna Dan dashi hadi da bubbbuga bayanshi sannan yai firgigit ya dawo hayyacinshi

Sassauta murya mamin tai ya fara mgn kamar wata munafuka ni karan kaina banji abinda take cewa ba

*ACP mubeena*
Bayan fitowarta daga cikin station dinsu inda tai parking motarta ta nufa, cikin wata danqareriyar mota naga tashiga wanda kaidagani kasan ba qananan kudi akasa akasiya ba saboda tsabar haduwarta
Bayan ta rufo motar takai more than 30 minutes bata tada motar ba tana xaune sai saqe saqe takeyi sai daga baya ta tayarda ita ta kama hanyar komawa gida

*papi mansion*
Horn tai a katafaren gate din gidan nan da nan gate man ya wangale mata gate tasa kai cikin gidan a parking space tai parking motar ta ta nufi part dinsu

Tsayawa tai cak gab da xata shiga part din nasu su mami ne dasu matar uncle abbas harda matar khilil babban wan mubeen
Da sauran yammatan gidan gefe daya kuma mubeen ne yai folding arms dinshi kai da ganinshi kasan ba qaramin bacin rai yake cikiba

Dukda a yanda ta gansu taso ta Dan tsorata sai ta hana kanta hakan tare da qarfafama kanta gwiwa ta cigabada tunkararsu
“”barkanku da yamma ptan nasameku lpy “”
Ta fada tareda cigaba da tafiya xata wucesu , mamice ta hankadota baya tare da fadin
“””gidan ubanwa xaki je ne eh, nace gidan ubanwa xaki, for your information bakida wata mafaka ko gurin xama a wannan gidan domin dai bana ubanki bane na wanda kika wulaqantane Dan haka banga amfanin xamanki a gidanba
Anty balkisu matar uncle abbas ta daura da
“””qyale yar marasa kunya ta qara one step daga inda take taga yanda xamu sauya mata kamanni

Wani banzan kallo Mubeena ta watsa masu tare da Sakin wani shu'umin murumshi tace kuyi hakuri fah Amma ai banida gidan zuwa sai Nan gidan mijina Kuma gidan makashin mahaifina idan kunga na bar gidan Nan to an hukunta Mai laifine wato an bimin hakkin kisan mahaifina beside ma Ina kukeso naje da igiyar aure na ai zama darammm..... Mami wacce ta kullu iya kuluwa ta Kai iya wuya sai numfashi take mayarwam kamar mesa tace Mubeen kana Jin abinda wannan yar iskar matar taka take Fadi ko to wallahi sai ka saketa yau din Nan ba sai gobe ba,ynzu ke Dan kin cika butulu ki rasa wazaki lakabawa sharrin kisa sai papi kisan ma na Amininshi kaii kaico Mubeena kaico nayi takaicin kasancewarki matar Dana tirrr da wnn mugun halin naki da kika koya silar wannan bakakaken kayan naki Mai suna kakin yansanda da nasan wannan ranar zatazo da ban goyi bayanki kin shiga wannan aikin ba Ashe da biyu kika shiga kin zame manh mage Mai kwanciyar daukan rai!! Mami takarashe tana Sakin wani kuka Mai cin rai.Mubeen da ke tsaye agefe gaba daya duniyar ma juya mishi take har yanzu ya kasa yarda wai matarshi masoyiyarshi abun kaunarshi itace ta kama hannun mahaifinshi ta buga mishi ankwa tajashi tafita dashi a matsayin waiii me laifin kisa....kaiiii inah!! Duk yanda akayi Mubeena Bata cikin hayacinta kokuma dai shaye shaye ta fara ne ban sani ba,Yana cikin zancen zuci tazo wucewa tagabanshi dama ga kukan Mami da gaba daya yake Ji kamar ana soka mishi mashi azuciya azafaffe ya fizgo ta ajuyata suna facing juna yamata wani irin roko na jaruman Maza gaba daya idonshi ya Bude akan nata ya Bude Baki cikin dacin rai yace "ke Mubeena bari kiji nagaya Miki idan ma shaye shaye kika fara to kinsha tagayamiki karya wlh kinyi kadan da wani karamin matsayinki na yar sanda ki kama papi akan kisan dady Wanda ni dake munsan papi bazai taba iya aikata Hakan ba ko a mafarki balle azahiri don haka ki gayamin meye hujjarki ta kama mahaifina!

Hujja Hujjah Hujjah!!! To yanzu dai banida lokacin tsayawar gayamaka ko baka Hujjah tah saidai kasani inada hujja Mai karfin da bazan iya cigaba da zama Ina kallon makashin mahaifina na yawo free ba!!!!

Anan X££l@hs pen writers muka aje alqalaminmu.........✍️✍️

Tofa jama’ah mubeena ta taro match fa in Allah ya kaimu gobe xamuga yanda xata kaya

Daga Alqalamin✍️
*X££l@hs pen*✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

https://chat.whatsapp.com/KDkpfCh3PTgAMGI4xMc81Ws

*X££l@hs pen....................*✍️✍️✍️✍️

رَبِّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ أَنْ أَسْأَلَكَ مَا لَيْسَ لِي بِهِ عِلْمٌ ۖ وَإِلَّا تَغْفِرْ لِي وَتَرْحَمْنِي أَكُنْ مِنَ الْخَاسِرِينَ

******ACP mubeena*******
******Paid book 📚********

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.