Acp Mubeena
Reading file: ACP_MUBEENA.txt
Chapter 16 of 18
Page 17
Sosai su Alh.kk suka dage waje kamfen kauyika kauyika suna rabon abinci da sitiru da daukan alqawuran da bazasu iya cikawa ba buri dai ya cika kwaliyya dai ta biya kudin sabulu Alhaji kk ansamu tsayawa takarar Dan majalissar jihar kaduna.
Kafar wata jibgegiyar mota masu tsaron lafiyarsu suka Bude musu kofofi biyun atare shida babban abokinshi Alh.umar suka shiga aka rufe sannan aka ja motar tashige tsakiyan jirin motoci guda biyar din dake wurin suka harba titi da mugun gudu masu kasa kenan!
Alh. Umar yace Ina muka nufa ne Dan kaya fa sun sauka sun chan suna jiran mu..wata shakiyiyar dariyar Alh.kk ya kwashe da shi yace "mutumina kenan dadina dakai wurin wnn harka bakada wasa to Yan shilan ne ko burolas?
Dariya Alh.umar ya kwashe dashi yace "aa burolas din dai ai tunda anci Yan shila kwana biyu sai asirka da masu kwarin Kashi Kuma ya Alhajjj"
"Kuma fa haka ne driver guest house zaka kaimu"suna cikaba da zantutukansu na harkalolinsu,shikuwa driver tuni ya juya akalan mota zuwa guest house din Alh.kk cikin abunda be Gaza mintuna 20 ba suka Isa gidan idan suka iske zuka zukan Yan mata masu aji da kyau ko wacce tayi shigarta ta daukan hankali,Kai idan kagani bazakace ya'yan musulmai bane daga Mai mini skirt sai bom shot sunsha uban attachment ga shisha pot Nan agabansu sai zuka suke shigowar su Alhaji kk ne yasa suka mike da ihu suka tarbesu dama Yan matan hudu ne kowane ya rungumi biyu suka jasa kan kujera suka baje anata shakiyanci tun anan suka fara wasaninsu daga baya kowa yaja nashi suka shige dakuna suka rufo kofa ganin haka yasa Nima na juyo Dan bazan iya irin wannan binkwakwafin ba duk gulmata ban iya leko muku wanga harka Nima juyowa nayi nabar gidan gaba dayama da kar ku tambayeni ko naji wani Abu.
*****
Barrister Irfaan tun Yana Kiran wayar Mubeena cikin sa tsamanin zata dauka har ya yanke tsamanin sannan Kuma hankalinshi ya fara tashi saboda Mubeena ba irin mutanen Nan bane dazakayi ta kiransu suna kin daga waya sai dai idan akwai matsala ne,tun biyar na yanma sukayi zasu hadu gashi yanzu Kusan karfe takwas na dare Bata dauka Kuma ba ita ba alamunta,yanke shawaran zuwa gidanta dakanshi yayi Dan ganin ko lafiya take Dan Yana ji ajikinshi ba lau ba,Yana fara sakowa daga takalan benan yafara jiyo kukan zain sosai yake kukan Wanda har cikin zuciya Irfan yake Jin rashin dadi kukan Dan nashi wanda Hakan yasa shi karasa sakowa da Dan sauri turuss yaja yatsaya ganin Amatullah zaune Daram akasa ta tasa zain agaba Yana kuka tanayi itama kashirban take kukan tana surutai "tsakani da Allah zain kana kyautawa kenan tun dazu nake baka hakuri Kaki yin shiru ya kakeso nayi nibanason kukan Nan naka kaga Kai maraya ne Amma karka damu bazan taba barinka kayi maraiciba kaji nice uwar ka nice ubanka Dan nasan wancan uban naka bashida lokaci kullum yawo kasa kasa gari gari kamar Wanda yaci kafar kare shi ala dalo ga lawyer hmmm to ni batsayawa jiranshi zanyi ba zan rinka baka kulawa kaji yaro na Dan Allah kayi shiru kaga tun rana bamu ci abinci ba na hada Maka madaranka Kaki Sha shiyasa Nima Banga dalilin cin abinci na ba yanzuma na Kara hada Maka kasha ga shi ita wacen gwaggo sauden itama da shegiyar kafarta kamar sauro daga cewa bari taje tagaida umma ta dawo taje tayi zamanta kamar na aiki bawa garinsu, mtsww bare tazo ta duba min tagani ko meke damunka kaiii Toni kodai asibiti zamu je ne eyyeee tafada tana Jan majina tana Kara rungumo zain data dukunkune ajikinta"
Tunda yake da Amatu Bata taba bashi dariya ba irin yau yanda tazauna tanata zubama Dan yaro surutu yaran da bemasan tana yiba sai kuka yake,wato shinema Mai kafar Karen lallai yarinyar Nan Taga gadon baccina karasowa yyi duk bataji tafiyarshiba yasa hannu ya amshi zain din firgigita ta mike atsiyace tana rarumu hannunshi Kai lafiya waaayeee.....Chak ta tsaya ganin shi sai Kuma ta hau ware Ido tana share hawaye "auuuu Yaya I Ashe Kaine" dayake haka take kiranshi Yaya I ko tace yaya lawyer...
Yace "meye kika tasashi agaba kina kuka kefa bakida hankali haka ake rainon"
Turo Baki tayi tace "to ba kuka yake tayi ba yakiyin shiru tun dazun ko abincima yakici"
"To shine akace kita sashi agaba kina kuka dayake ke katuwar bazance ko"
Kara sumburo bakin tayi tace "to ai tausayi yake bani bawan Allah ba uwa ba uba sai ni kadai"
Wane harara ya watsa mata yace "ke kika kasheni da zakice baida uba?
"Yo to Kai zama kake kullum fa kana gun aiki hmmm"
"Mtswww dallah matsa kibani guri Kona make ki jeki kiramin gwaggo saude"
Tace ai Bata Nan!
"To dako hijabinki mukaishi asibiti inaga kaman cikinshi ke ciwo"
Waro Ido tayi tace " ya akaiyi ka sani Kai" be tsaya Bata amsa ba yyi gaba Yana Kara jijiga zain din,ita Kuma tashiga ciki da Dan gudu ta ta dako hijabinta dogo har kasa navy blue Wanda ya Kara haska farar fatarta tafito cikin sauri ta Bude motar ta shiga ya mika mata zain kamin ya tada motar suka fice.
GH.hospital suka nufa nan aka duba bby zaid bawata babbar damuwa ce ke damunshi ba sai yar xaxxabi ne kawai nan likita ya rubuta musu maganin da xa’a siya mishi bayan fitowarsu daga office din likita irfaan na rungume da bby zaid a qirjinshi amatu kuwa sai dube dube yake kamar wadda ke neman wani abun can garin dube duben ta tahango wata mata a xaune kamar ummahnta a receiption xaune d qarfi tace
“Laaa yaya I ji wata kamar umma”tsaki yaja yace
“Kishiga hankalinki amatu mexai kawo umma asibiti a wannan lokacin,
Amma Ina amatu ko sauraranshi bata tsaya tayi ba Dan tagama tabbatarwa kanta umman tace,da gudu ya kwasa ta nufi inda matar ke xaune aikuwa ummance kuwa,
“Ummah me kikeyi a asibiti 😳,ta fada tana Dan xare idonta,umma dake xaune cikin matsanan ciyar damuwa gashi haryanxu mubeena bata farka ba dukda dr yace mata bbu damuwa su suka qara mata da allurar bacci saboda ta qara samun relief kuma in sha Allah xata tashi da qarfin ikon Allah,
Damuwar ummah biyu ce na farko wake neman halaka mata ya bata gama jimamin rabuwa da aisha ba ana neman aqara kashe mata wata,wani laifi ta aikata da tacancanci irin wannan mugun hukunci haka,abu na biyu shine halin ko inkula daga wajen su mubeen dukda tasan baxasu rasa sani ba amma ko karansu bbu wanda yaxo,
Hargagin amatu ya dawo da ita cikin hayyacin ta,da mamaki take kallon amatu Dan tasan dai bata kira su tafada masu abinda ke faruwa ba,
“Daga Ina haka kamar wacce aka jeho”umma ta fada tana kallon amatu,bata bata amsa ba sai tambayar da itama ta jefa mata
“Umma lpy me kikeyi anan,wakika kawo,”bata samu bama amatu amsa ba sai ga wata nurse ta nufosu da faraar ta tace
“Alhmdllh hajiya petience dinku ta farko yanxunnan”
Littafin ACP mubeena paid book ne 300 only gamai buqatar cigaba da karantawa har qarshe yayi payment dinshi sbd free pages na gab da qarewa
For more information contact 09161738928 or 09038727860
X££l@h’s pan*✍️✍️✍️✍️
رَبِّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ أَنْ أَسْأَلَكَ مَا لَيْسَ لِي بِهِ عِلْمٌ ۖ وَإِلَّا تَغْفِرْ لِي وَتَرْحَمْنِي أَكُنْ مِنَ الْخَاسِرِينَ
****ACP mubeena****
Page 18
Cikin farin ciki umma tafara ambatan alhmdllh Allah mungode maka ko tsayawa bin na amatu daketa jera mata tambayoyi batai ba,itama amatun ganin umma ta nufi cikin asibitin yasata binta Dan ganin wacece ake mgn akai,irfaan ma daya ga hk shima ya rufa musu baya,
Kwance take a saman gadon asibiti kanta sanye da bandage 🤕 hannunta daure da ruwa dake gabda qarewa idonta na kan P.O.Pn dake saman rufin dakin tunani ne kala daban daban a xuciar ta amma bban abinda take fata Allah yasa kar ace xaa riqeta a asibitin nan dan ita kanta ta qagara a gama wannan case din na papi kowa yasan abinda take nufi hkn xaisa kowama ya barta ta huta lokacin da gaskia tai halin ta,agefe guda kuma tunanin yarinyar nan aisha take yi batasan halinda yarinyar ke cikiba yanxu Dan daalama yarinyar batada saurin sabo tana gudun karta qara komawa halinda tafito, tana cikin wannan tunanin ne su umma suka fado cikin dakin suka nufota baki dayansu,sannu umma take mata cikin kwantar da murya hadi da tausasa wa da mamaki amatu ta nufi gadon tana tambayar anty mubee lpy kk meya sameki naganki a haka,Dan murmusawa tai cikin qarfin hali Dan ba qarya mubeena najin jikin bbu dadi tace,
“Bbu komai amatu ai nasamu sauqi na”
Irfaan daya qaraso ckn dakin ganin mubeena a saman gadon gabanshi baqara min faduwa yyi ba,
“Subhanallah umma meya saneta ne lpy naga fuskar ya da bandage 🤕 Allah yasa ba hatsari tayi ba?”
“Uhmmm kaidai bari irfaan wlh ba hatsari bane ba jia wasu axxaluman suka aikata mata haka nima Alh.aminu ne yakirani ya sanar dani duka abinda ya faru,
“Subhanallah su waye sannan me tai musu da suke neman nakasta ta”irfaan yafada a rikice
“Wlh bansan su waye ba brr amma sun tabbatar min da aikosu akai amma basu fadamin wanda ya aikosu ba saidai cikinsu bbu wanda baxan iya gane fuskar shiba kuma wlh sai sun gane wanda suka taba daga su har wanda ya aikosu,hat inda suke xama nasani sbd mun taba kamosu kwananki muka kulle so karku damu xan kamasu kuma xasui bayanin koma waye wannan da ya aikosu din”
Suna tsakar mgn sai ga Alh.aminu shida mubeen sun shigo ckn dakin,Alh.aminu ne ya taso mubeen yasashi dole yaxo ganib mayar shi bbu yandaa ya iya sbd irin girma da mutuncin dake ga uncle Aminu din a gunsa,cikin abokan papi xai iya cewa shine shaqiqi kuma babban aminin papi na biyu daya sani,dadyn mubeena shine bbn abokin papi koma kace Dan uwa dan alaqar su da papi alaqa ce marar misali to dagashi kuwa sai Alh.aminu,masoyine na haqiqa ga papi,tun kuma da aka fara case din papi dinnan bai taba gajiya da yin hidima kullum cikin shige da ficen ganin sunyi winning case dinnan,
Ganin mubeen a asibitin ba qaramin sanyaya xuciar mubeena yyi ba,saidai bbu faraah ko kadan a kan fuskar shi sannan tun shigowar su bece da kowa qala ba har umma kuwa ko kallon inda suke beyi ba sai faman daddanna wayarshi da yake ba qaqqauta wa ganin hk shima irfaan yai banxa dashi dama uban yan girman kaine sannan bawata cikakkiyar shiri suke ba sbd abubuwan da suka faru tun abaya,sai dai suna gaisawa kam amma yau dayaga mood din mubeen shima sai yai banxa dashi,umma ce ta katse shirun tafara gaida Alh.aminu da masa gdyr irin dawainiyar da yyi da mubeena tun jia,yace hb hajiya ai yima kaine ko albarkacin Alh.muhammad xaisa inmuku fiye da hk,
“Indai alfarmar Papi naci kai dawainiya dani to kuwa ban gode ba kuma baxan taba godewa ba,bana buqatar cin alfarmar shi a gunka ko dai dai da minti daya ne,Dan haka kafadi ko nawa ka kashe xan tura mk kudin ka bana buqata”mubeena da tun shigowarsu batai mgn ba sai yanxu tafadi a Dan fadace,bbu Wanda mgnr tata bai daki xuciar shiba, da mamaki kowa ke kallon ta most especially ummah da mubeen dan ita amatu bama ta cikin dakin tun dasu Alh.aminu suka shigo ta Anshi bby zaid ficewar ta waje, shikam irfaan Dan kallon mubeenar yyi kawai yadan murmusa aranshi yana fadin mai hali dai baya fasa hln shi,shikam Alh.aminu bai iya cewa komai ba sai mubeen ne ya taso a harxuqa ya fara balbaleta da bala’i,
“Ai saida na fada mk uncle amma kaqi saurarata wadda ta butulcewa wanda yyi mata halaccin rai da rai ma balle kai,kar ka manta irin dawainiyar da papi yyi da yarinyar nan amma ka dubi irin halin da ta sanyashi balle kai dan ka taimake t jia jian nan,saida nafada mk ka fita sabgar ta amma kace dole sai na biyoka to ga abinda biyokan da nayi ya janyo gobe ko kasheta kaga xaayi baxaka qara kusantar gurin ba”
Mubeen ya fadi a hau kace,sannan yyi mata kallon xamu hade ni ya fice daga dakin,Shima Alh.aminu fita yyi daga dakin amma maimakon ya wuce inda mubeen yk kawai dr office yanufa yyi mishi complain cewar Anya kan yarinyar nan b samu matsala ba kuwa sbd yanayin yanda take magana Sam kamar ba ita ba,aiya sanin da yyi mubeena yarinya ce mai ladab da biyayya sannan raini bai taba shiga tsakanin suba irin haka shiysa yace dr ya qara bincika mishi qwaqwalwar ta kotadan tabu ne,dr yyi mishi bayanin bbu wani abu daya samu kanta saidai ko buguwar da taine amma koma dai menene ba serious bane akwai magungunan da take sha komai xai daidaita,gdy yaqara yima dr sannan sukai sallama,
Umma da gwaggo saude suka yima mubeena fada sosai akan abinda tai haquri taita basu sannan tace sudan basu wuri xasui magana da irfaan,bata musa ba kuwa tafita nan suka fara tattaunawa akan shariar da xasu fara satinnan da xamu shiga,sun tattauna sosai daga qarshe ta buqaci sallama daqyar likita ya yarda ya basu sallaman Dan jikinta da saura amma ya qafe dole ya basu da sharadin xata kula sosai.
Asibitin da Aysha take Mubeena tace su fara biyawa su dauketa kamin suka wuce gida Wanda Irfan ne ke tukun bayan ya saukesu agida ne ya wuce gidanshi shida gwaggo saude da Amatu da zain,yaje yafara shirye shiryen shiga kotu ran Monday duk da wasu hojojjin na gurin Mubeena sai ta Kara hutawa zata bashi su kasancewar wnn abun da yafaru da ita ya hanasu karasa sauran binciken nasu.Mubeena na shiga gida wanka ta Dan tsakuri abinci kadan Tasha magungunanta tana Bude laptop dinta zata fara aiki kira ya shigo wayarta CP tagani ajikin wayar dagawa tayi cikin girmamawa ta gaidashi Nan yake tambayanta meyasa Bata shigo aikiba Kuma anata Neman wayanta baya shiga Nan ta mishi narrating abunda ya faru da ita cikin jiman tawa yake cemata gobe xaisa afara bincike tace "karka damu sir nasan yaran farin sani sai dai Wanda yasasu aikin ne bansan waye ba Amma tabbass sasu akayi"
Yace "to ki fadamin su waye yaran gobe nasa akamasu ayi musu horon da dole sai sun gaya manh waye da alhakin sasu wnn aika aikar"
Murmushi Mubeena tayi ganin yanda commission ya dage yanata kumfar Baki tace " ka kwantar da hankalinka sir ahnkli zan zo kansu ne ni yanzu case din papi dayake Monday zaa shiga court shine agabana sir gashi Kuma baka bani flash drive din Nan ba Wanda zamu gabatar a court din"
Dafe Kai yyi yace "ohh nooo! Namanta kinsan dama nace bazan Baki ba kar asamu matsala wani agidanku yagani ya dauka to yanzu ya zaayi gashi kince bakida lpy Kuma hannu da hannu nakeso na Baki banson asamu matsala"
"Ba damuwa sir zan shigo gobe na amsa da kaina don Nima banso asamu matsala"
"Zaki iya ACP naji kince sunki Miki rauni Akai ga muryarki ma daji baya Jin dadi"
"No! Karka damu sir zan zo goben in Sha Allah "
Nan sukayi sallama kowa ya aje wayar aiki kadan tayi kasan cewar tanason ta huta da gobe ta samu ta fita da wuri,dama tasa umma ta wuce da Aysha gidanta azuwan gobe ko ita Bata samu zuwa ba umman. Da kanta zataje gidansu Ayshan tagayamusu halin da yartasu take ciki duk da Mubeena din tace dolema tare zasuje Maida Aysha din.
******
Washe gari da safe gurin karfe gonna Mubeena ta shirya tsaf cikin kayanta na yan sanda tafito falo anan tasamu Mubeen kwance Saman 3 sitter murmusawa tayi tace "good morning my man"
Juyowa yyi ya watsamata wata uwar harara sannan yace "lallai nayarda bakida kunya Mubeena" batace komai ba ta Kalli Saman dinning din daya tashi tun Asuba tashirya mishi breakfast din dayafiso ta jeresu tsaf a dinning Amma ga dukan alamu ko tabasu baayi ba yace "aa my man baka karya bane naga kamar ko taba abincin ma bakayi ba"
Yace "ki dena dafa abinci kina almubazaranci dashi tunda kinsan ko giyar wake nasha bazanci abincinki ba Dan na lura tsaf Zaki samun guba naci na mutu" waro Ido Mubeena tayi tace guba fa kace !!!! Ni Mubeena matarka nice zansa Maka guba hba Mubeen ynzu tsanar dakayimin hartakai karinka furta irin wadannan kalaman"
Yace "to meya rage ai kin gama kasheni Mubeena ba abunda ya rage sai ki haka rami ki burneni Amma Ina Mai tabatar Miki wallahi sai kinyi Dana sannin abunda kikayimin nida ahalinah Mubeena bazan taba yafe Miki ba tozarcin dakikayi mana Kuma bazan kyalekiba karkiyi zata kinci buluss" Yana kaiwa Nan ya Mike yafice daga gidan gaba daya,jikin sanyin jiki tasa kafa tafita itama Nan ta tarar da Yan sanda biyu Wanda aka turo don tsaron lafiyarta bayan mota suka Bude mata ta shiga zuciyarta duk ba dadi.
Littafin ACP mubeena paid book ne gamasun jin cigaba har qarshe sui payment dinsu Dan jin yadda xata kaya
300 kacal ba tsawwala wa 👌
Yar uwa ki guji cima kanki haram Dan nasan akwai masu jiran na bati kuma bawai Dan sun rasa abin siya ba,aah kawai son xucia ce kawai,naira dari uku dai nasan kinfi qarfinta
https://chat.whatsapp.com/IIzvJ7l40854gOZahJJxq2
*X££l@h’s pen*
رَبِّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ أَنْ أَسْأَلَكَ مَا لَيْسَ لِي بِهِ عِلْمٌ ۖ وَإِلَّا تَغْفِرْ لِي وَتَرْحَمْنِي أَكُنْ مِنَ الْخَاسِرِينَ
****ACP mubeena****
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.