Acp Mubeena
Reading file: ACP_MUBEENA.txt
Chapter 3 of 18
Page2
Ko waiwayen inda ake ihun faduwar mami bataiba hannun data sanya ma papi handcuff kawai ta ja sukai hanyar ficewa daga palon baki daya
Fadin irin tashin hankalin da wannan ahalin ke ciki ba abune mai yiwuwa ba most especially mubeen da xuciyarsa ta kusa bugawa
Wannan wata irin baqar rana ce agareshi wanda ko a mafarki bai taba hango xuwanta ba
Ace matarsa ce tai arresting mahaifinshi a gabanshi ba tareda ya iya aiwatar da komai ba
Wannan wata kalar qaddarace hk
Ko a duniyar daba tashiba bai taba xato ko tunanin mubeenar shi xataima papin shi kwatan kwacin irin toxarcin hk ba duba da yanda ya daukakata fiye da sauran yaranshi da ya haifa ya kyautata mata fiye da yanda yk kyautatama yaranshi tun ma kafin tasamu kanta har xuwa lokacinda ya hada aurenshi da ita yasa shi kuma dole yasota
Sannan bai taba daukarta matsayin Sirika ba saidai ‘ya wacce yk ji da ita sama da komai a duniyar shi
Amma yau an wayi gari itace tai masa wannan qasqancin da hankali ya kasa dauka
Ihun da easher ta qwalane ya dawo dashi daga duniyar Tina in daya shiga
Waigowa yyi yana kallon easher dake qwalla ihu tana kiran sunan mami
Xagaye suke da ita ainda suka kwantar da ita saman doguwar kujerar 3seater
Sun rufar mata akai ta inda ko iska baya shigarta km a cikinsu bbu Wanda yyi hausar yayyafa mata ruwa tsabar rudun da suke ciki
Jiki ba qwari mubeen ya nufi friedge din dakin ya bude yadauko ruwa mai dan sanyi amma ba sosai ba ya nufi inda suka xagaye mamin
“”””ku matsa baya””””
Ya fada in his deep voice
Matsawan sukai batare da sunce komai ba
Ya qaraso inda mamin ke kwance hadi da bude gorar ruwan daya dauko ya fara yayyafa mata a jikin ta da fuska
A firgice ta farko hadi da kiran sunan Muhammad a bkn ta,
“”””””””””a bangaren mubeena mubeena kuma bayan fitar su daga palourn inda sukai parking motomsu suka mufa ainda papi ya fara shiga daga ciki ita kuma ta xauna kusa dashi
Bbu mai magana a cikin su kowa da kalar tunanin da yake yi
Ko kadan papi baiji haushin abin da mubeena tai masa ba sam domin shi papi mutum ne dabaida son xuciya samm kuma ya dade da kwana da shirin xuwan irin wannan rana tunda dadewa
Dama duk boye boyen mutum dole watan watarana xata bayyana ita gaskia dayace
Kuma har wannan lokacin babu abinda ya canxa na son da yakema mubeena patansa da kuma burinsa shine Allah ya dafa mata
Daidai nan suka shigo police station din wannan lokacin ita ce ta fara fita daga motar kafin papi ma ya fito har kuma lokacin hannunta na riqe da handcuff din papi
Direct cikin cell ta sanya shi hadi da sa key takulle qofar
Cikin Dan daga murya ta fara magana
“Kaga saka makon aikin da kadade kana binnewa a tunaninka gaskia baxai taba bayyana ba ka muntada duk abinda ka shuka shixaka girba ko ba jima koba dade wannan kadan ka fara gani sauran sakamakon naka na nan tafe
Waikai da a tunanin ka jinin mahaifina xai tafi ne a iska,kaida a tunanin ka duk alwashin da nake dauka kawai cika baki ne kawai baxan iya aiwatar wa ba
Kayi kuskure alhaji Muhammad yaaseer
Kasan menene kuskuren ka????
Kuskuren ka shine na taba jinin *ACP mubeena* the worst part you are the murderer of my beloved father and it was a promise that I won’t spare you
Ta kai qarshen maganar da qarfin gaske
Yanxu aka fara wasan mutanen mu ku biyo mu danjin yanda xata kaya
Written by X££l@hs writersss
Domin neman qarin bayani ku tuntubi wannan numbern
*XEEl@hs pen....................*✍️✍️✍️✍️
رَبِّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ أَنْ أَسْأَلَكَ مَا لَيْسَ لِي بِهِ عِلْمٌ ۖ وَإِلَّا تَغْفِرْ لِي وَتَرْحَمْنِي أَكُنْ مِنَ الْخَاسِرِينَ
***ACP mubeena****
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.