Trending Hausa Novels

Acp Mubeena

Reading file: ACP_MUBEENA.txt

Chapter 13 of 18

Page 9

Ranshi ne ya qara Baci ganin yanda aketa maganar batanci akan papi anata yaga fostocinsa da aka mammana wasu na dage da wani poster hoton papi ne radau hannushi sanye da ankwa Mubeena na riqeda hannun,mutane nata ihu bamayi bamayi!

Takowa yyi har tsakiyan parlor ya tsaya a gabanta tana zaune idonta na kan TV bazaka taba tantance awane Hali take ciki ba Mubeena kenan Mai fuskar gizgo baka Gane fushi take ko farin ciki sai taso kasani zaka gane "burinki yacika ko yar sanda kin ci mutuncin mahaifina kin wulakantashi kin tozartashi duk akan abunda ni dake munsan bazai taba aikatawa ba"

"Kayi hakuri Mubeen inaso nayi amfani da wannan lokacin na baka hakuri wlh tallahi Mubeen da inada halin canza kaddara ta da na canza Nima kaina har ynzu na kasa yarda papi shi ya kashe daddy na Amma ya zanyi all evidence are pointing towards him banida yanda zanyi me dady ya aikatawa papi da zai kasheshi Mubeen me yayi mishi Amininshi Dan uwanshi surukinshi meyayi mashi Mubeen....ta fashe da wani irin kuka Mai ban tausayi

"Hmmm Mubeena idan duka jikina kunnene wallahi bazan taba yarda cewa papi shi yakashe dady ba hba yar sanda nafasan waye mahaifina kudai sake bincike dakyau Amma papi bazai aikata kisa ba Kona Dan kwuikuyo ne balle mutum"

Share hawayenta tayi tamike tsaye ta matsa Kusa dashi ta kama hannushi tace "sai dai am sorry to say shi ya aikata da idona naga evidence din bawani ya fada min ba Nina gani da idanuna Mubeen Dan hka kasani da Raina da lafiyataI can't live him to walk free bayan nasan da jinin mahaifina a hannushi wlh sai inda karfina yakare Amma sai an hukunta papi akan abunda ya..........bai bari ta karasa ba ya fusge hannushi daga nata dakarfi yace idan kin fasa Mubeena!! Ni Kuma zan nuna miki ni Dan halak ne daga yau idan ba ki gimtse numfashin da papi yakeyi ba Baki burgeni ba,ki tabatar kinyi proving Dina wrong kitabatar kin kawo prove na cewa papi shiya kashe mahaifinki idan ba haka ba yar sanda sai kinyi danasanin zuwanki duniya yanda kika wulakanta papi bazan kyaleki ba,duk inda wani kwararan lawyer yake afadin kasar Nan zan nemoshi domin a wankemin mahaifina tass kekuma Ina Mai Baki shawaran kiyi duk yanda zakiyi wajen tabatar da shiyayi kisan Dan wallahi idan kika bari muka ci shari'ar Nan Mubeena sai kinyi Dana sanin sanin Mubeen arayuwarki"

Wani irin shu'umin murmushi Mubeena ta saki ta Tako har gabanshi ta tsaya tasaka kwayar idonta Mai kaifi acikin nashi wanda Saida gabanshi yafadi idan har yakaranta daidai abunda kwayar idon matar tashi yake fada daban ya hango wani Abu Mai rikitarwa acikin idanun nata,Bata bashi damar Ida nazari ba tace "tabbasss zanso Hakan katsaya iya karfinka wajen proving Dina wrong zanso Hakan matuka Dan Nima ban fara wasan Dan na buga shi ni kadai ba sannan ban fara ba Saida nashirya mu hadu a kuto!!!

Tana kaiwa Nan tajuya ta nufi dakinta da gudu ta fada kan gado ta fashe da kuka Why why why papiiiii why! Meyasa kamin haka papi Ina zankai wannan nauyin mutumin danake matukar so da kauna yau Nike fito na fito dashi har ankai gabar dayake furta min kalmomin dasuka Fi komai Daci da radadi acikin zuciyata wayyo Allah rana zafi inuwa Kuna Allah ka kawo min dauki"

Idonshi na tsaye kyamm akan kofar dakin Mubeena abunda yagani a idonta ne kemishi yawo akwakwalwa kaiii anyaa Amma fa tace tagani da idonta papi ne yakashe dady Kuma a iya saninshi da Mubeena Bata karya Kuma yanda ta dauki abun Nan da zafi akwai alamun kamshin gsky kaiii Amma yasan waye papi bazai taba aikata kisa ba to meke faruwane haka kanshi ne yaji ya Sara dasauri ya dafe kan ya zauna Yana furta innalillahi"

*****

Alhaji kabiru kalankuwa da Alh Umar ne durkushe agaban malam gobe da nisa suna kora mishi bayani malam ya nisa ya kyakyace da dariya yace

"tun kamin kuzo nasan meke tafe daku wannan kujera na Yan majalisa ka hau ta kagama indai ka cika sharudanmu"

Alh.kk ya washe Baki yace " ai malam babu abinda bazan iya ba indai zan samu kujerar Nan"

"Yau irinku mukeso to da farko dai zaayi yanka bakakaken shanaye guda Dari jar akuya guda Dari sai bakaken bunsurai Suma Dari" jiki na rawa Alh. Umar ya jawo wani akwati ya Bude Yan dubu dubu ne cike da akwatin ya mikawa malam "ajeshi Nan gefe angama da na farko na biyu zaka Nemi budurwa yar shekara 14 ka tabatar Bata wuce Sha hudun Nan ba ka kawar mata da budurcinta ya Miko mishi laya yace wannan layan ka goge jinin gabanta dashi sai kaje makabarta kasamu sabuwar gawar mace Wanda aka burneta aranan ka tura agabanta to indai kayi haka ka gama meeting din da Zaku zauna Kai zaa tsayar takarar Dan majalisa Kuma kamar Kaci ka gama"

Godiya suka mishi sosai kamin suka taso suka baro wurin suna Kara tattaunawa akan yanda zaa samo yar shila "karka damu kasan mun saba irin wannan Hakan bari akwai wani amintaccen yarona zansa ya kawo Maka kaidai kashirya zuwa gobe ka cika aiki kasan zaman meeting din Nan da kwana uku ne" cewar Alh.umar

"Yauwa godiya Nike abokina to sai Kuma gawar fa ya zamuyi"

"Haba gawa ai Abu ne Mai sauki abinda kullum sai anbirne gawa sama da hamsin arana wannan ba matsala bane Kai dai kawai ka shirya da zafi zafi akan daki karfe" suka kwashe da dariya suka tafa. Ba imanni ko tausayi azukatansu Allah yasa mu dace.

**************
Amatullah wuni tai tana shaqatawarta cikin katafaren palourn gidan da yagama rikirkita ni harna rasa yanda xan fasalta muku tsarinsa

Wuni tai tana sharholiyar ta batare da wata matsala ba kayan dadi kuwa saida suka ginsheta sai sambato take tana cewa gaskia naira duniya ce ai ita wannan haihuwar ita keda riba kafinta koma gida sai yan unguwarsu Sun rasa ganeta
Sai gabda magrib wayar ta tahau ruri koda taduba mai kiran ummantane nan take ta dauka ta sa a hansfree
Muryan umman a disashe ta fara mgn

“”Amatu kina inane””
“”Ina gidan anty aysha mana””
“”Ok gamunan xuwa gdn yanxu ”
“”To umma ta hai..........batare da takai qarshen tambayar ba qitt umma ta yanke wayar Dan numfasawa amatu tayi saboda bata gamsu da yanayin yanda taji muryan ummanta ba,
Kawai ta cigaba sabgogin gabanta ta barin ma ranta maybe ummah wahalar dawainiyar asibiti ne yasa taji muryarta some how tunjiya da safefa ai dole ta gaji.

Baa fi 30mins ba saiga qarar motocinsu ciki kuwa harda ta asibiti

Ummah ce tafara shigowa hannunta riqe da bby da gudu amatu taje ta karbi babyn ahannun ummah,

“”Yeah umma ashe tahaihu to Ina anty ayshar take””
Tafada sai a lokacin ta dago ta kalli ummah da idonta yagama rinewa daja’

“What umma mai yafarune naga idonki yai jajawur kardai kice min wani abun yafaru da anty aisha pls ummah”amatu ta fada a rude

Nanda nan hawayenda ummah ke qoqarin hanasu fitowa sukafara xuba cikin disash shiyar muryarta tace ma amatun ta miqo mata babyn ba musu ta miqa ma ummah babyn tatsaya tai sakado da ita ta kasa furta komai ma

“”Sai dai muyi haquri amatu wanda ya bamu aisha ya karbi abinshi”innalillahi wa inna ilaihir rajiun amata ta fada tareda xaunawa kan kujerar dake dabda ita

*****************
Mubeena tunda ta koma daki kuka kawai take tayi tarasa meke mata dadi a duniyar nan meyasa qaddarar ta taxo mata a haka ga kuma baraxanar mubeen da gab yakeda tarwatsa mata qwaqwalwarta tanason mubeen irin sonda bata taba xato ko tunanin xata iyayima wani ba face firs luv dinta,
Rasa mubeen kamar rasa ruhi da rayuwar tace baxata taba iya jurar rasa shiba koda kuwa na kwana 1ne
Mubeen wani qinshiqine kuma madogara ne gareta dkm rayuwar ta.

On the other hand kuma,alqawari ta daukarma kanta cewan baxata taba bari jinin dadyn ta ya tafi a banxaba, it was a promise since lokacinda taga Gawar dadynta
She won’t go off the murderer of her father

Tun shigowarta dakin nata gabanta ke faduwa akai akai wanda ke alamarta mata there is something bad that will happen to her or someone very close to her,addu’ar ta Allah yasa kar abinda take tunanine inkuwa hakane tabbass rayuwarta ta gama xuwa qarshe Dan baxata taba iya rayuwa bbu mubeen ba

Qarar da wayarta tayi ne yadawo da ita cikin hayyacinta takai dubanta inda ta aje wayar nata,ummahna da tagani a screen din wayar yasata Dan murmusawa tace Allah sarki uwata kwana2 bansamu natsuwar kiranki ba
yanke kiran tai ta kirata

Bayan ta gama gaida umman tata banji abinda aka fadi a dayar bangaren ba
Ganin nai ta miqe a firgice tace meya faru ne ummah,still banjiyo abinda ummahn ke fadi ba saijin mubeena nai tayi ihu hadi da xubewa qasa sume

Daga alqalamin
X££l@h’s✍️✍️✍️✍️✍️

https://chat.whatsapp.com/KDkpfCh3PTgAMGI4xMc81W

*X££l@h’s pen✍️✍️✍️✍️*

رَبِّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ أَنْ أَسْأَلَكَ مَا لَيْسَ لِي بِهِ عِلْمٌ ۖ وَإِلَّا تَغْفِرْ لِي وَتَرْحَمْنِي أَكُنْ مِنَ الْخَاسِرِينَ

****ACP mubeena****
Page 10

Mubeen da tun lokacin da ta baro palourn ya kasa motsawa daga wurin da yake domin irin abubuwanda ya gani a idanunta

Tabbass akwai wani rikitaccen alamari daya gano a idanunta amma duk irin kaifin naxarinshi ya kasa karanto me hakan ke nufi,ya so ya gasgata maybe akan gaskiarta take amma tunowa akan wah ake magana Yasa yai gaggawar korar shedan yace xaiyi maganin tane soon
ihunda ta qwalane ya dawo dashi cikin hayyacinsa ya daga Kai yai ma qofar dakin kallo daya ya watsar a xuciyarshi yana cewa in kinso ki mutuma I don’t care 🤷‍♂️ Dan ni banga amfanin rayuwar wacce ta qasqantamin mahaifiba ya fada hadida ficewa daga part din Baki dayama

Ta dade a sume a cikin dakin ga wayarta nata rurin neman agaji sai can lokaci maidan tsayi tala ta shigo cikin dakin ganin uwar dakin nata shiru bata fitoba sannan ta San bata barci dawuri sannan a aladar tama idan xata kwanta dole saitayi mata saida safe a yayyafi juna

Dakin ta nufo kai tsaye sai da tafar knocking qofar Dan karta fada musu mubeen na ciki dukda tasan inhar suna tare xaiyi wuya su xauna a dakin madam din saidai dakin mubeen amma gwara daita tabbatarwa kanta bayanan din
Jin shiru yasa ta gasgata baya ciki hartaso juyawa ta koma dakinta Dan atunanin ta maybe duka basanan cikin dakin.
Tunowa da yar tsamar dake tsakaninsu yasa ta fada dakin da sallama Dan tasan xaiyi wuya su kasance tare saboda rashin jituwar dataga suna yawan samu kwana2

A rude ta qarasa shiga cikin dakin ganin mubeena a yashe a qasa alamun takuma dade da kasancewa a haka
Kanta tayo da gudu tana girgixata tana kiran Anty kitashi pls,ganin jikin mubeenar harya Dan fara saki
Da gudu ta koma dakinta dake jikin kitchen din part din ta dauko wayarta ta dawo wurin mubeena,
Numbern anty amarya tai dialing harta gama ringing baa dagaba qara kira tayi still baa dagaba
Jefarda wayar tayi ta koma palourn ta dauko ruwa ta dawo ta yayyafamata ajiki cikin sa’ah kuwa tafarfado da innalilllahi a bakinta.
Wayar talace ta dauki rurin agaji(ringing)wurin data yada wayar ta nufa ta duba mai kiran nata, anty amaryace Dan haka ta dauka babu bata lokaci,bayan ta kara a kunne sallama tayi a dayan bangaren kuma aka amsada
“”Lafiya dai tala naga kiranki ina sallah Allah dai yasa ba wani abun bane ya qara faruwa””
Tala ta amsada
“” wlh anty ce naxo na tararda ita a sume bansan dai abin da ya faru ba amma gatadai na yayyafa mata ruwa ta farfado””
“”Subhanallah Allah dai yasa ba yaron nan bane ya qara mata wani abun””
“”To wlh dai bani labarin abinda ya faru””
“”Ok bari ganinan xuwa”,

***

Alh.Kk ne nagani sai zarya yake acikin wani katafaran parlour dake cikin guest house dinshi ya Kai ya kawo yafi sau ashirin, handkerchief dinshi ya sa ya kara goge gumin dake fitowa agushinshi tsaki yaja yakara dailing din no.Alh Umar akaro na hudu cikin sa'a ringing daya biyu ya daga cikin tashin hankali yace hba Alh. Umar inata kiranka baka dagawa to kayi sauri ka zo guest house Dina wlh akwai matsala"

"Wace irin matsala Kuma adaidai wnn lokacin hba Alh.kk inafatan dai ba aikin ne ya lalace ba"

" Nayi komai yanda yakamata Amma fa yarinyar Nan har yanzu jini me zuba ajikinta kamar an yanka rago Kuma wlh Bata motsi"

"Bata motsi fa kace Kai ko garin ya ya haka tafaru" Alh.umar yafada Adan rude

"Ni dai Dan Allah kataho yanzu" to ganinan zuwa, Kitt ya kashe wayar

Cikin mintunan da Basu wuce ishirin ba Alhaji Umar ya iso guest house din afalo sukaci karo da Alh.kk Wanda yakasa zaune ya kasa tsaye sai zarya yake kamar Mai tsohon basir Yana ganin A.Umar yace yawa shigo kaga direct bedroom suka shiga, yarinyace yar kimanin shekara 14 Shimfide akan gadon dayayi kacaca kacaca da jini sosai Kuma har lokacin jinin bai bar zuba ba.Dasauri Alh. Umar ya matsa Kusa da ita yafara dudubata arakice ya juyo ya Kallishi yace Kai wannan fa ta mutu!

Arude Alh.kk ya matso Yana fadin ban Gane ta mutu ba duba dai dakyau

"Wlh ta mutu" Alh Umar ya fada Yana mikewa tsaye "bari dai na kira likitana ya dubata Amma bana tunanin tamutu Dan kamar dogon Suma tayi"

Cike ta takaici "Alh.umar yaja tsaki yace Ina cemaka ta tamutu kana Kiran wani dogon Suma,Kuma wane likitan zaka kira ka dama mana lissafin ka Tona mana asiri dama Ina yawan gaya Maka karinka bi ahnkli Kai idan kasamu mace kaman tsohon maye kana sane wnn yar shila ce Bata San komi ba Amma ka haike mata Dan Allah ji yanda kamata kaca kaca kamar yar shekara arba'in"

"Wlh Nima bansan Hakan zai faru ba wani maganin Maza nasha Ashe yanada karfi jina na rinkayi kamar ingarman Doki nake gayamaka"

Alh. Umar ya bala mishi harara yace "ynzu Kai lalacewar taka hartakai haka zalmalulun naka ce bazatayi aiki akan wnn yar mitsitsiyar halitar ba har sai kasha wani maganin karfi kaiii Amma dai Allah ya wadaran naka ya lalace walh mtswwww....

Alh.kk da yakai iya wuya ganin yanda abokin nashi keta gayamishi magana yace " Kai nifa ya ishini haka nakiraka ne Nan Dan musamu mafita ba katasani agaba kana min tijaraba"

" Hba ai abun naka ne da ban haushi yanzu ka kira goska da yaranshi su zasu Yi wnn aikin idan Suka zo mu sai muwuce makabartan mukarashe sauran aikin tunda dare yayi ynzu nasan kafa ya dauke"

Alh.kk ya sauke ajiyar zuciya sai ynzu yaji sanyi danshi sbd tsabar rudani yama manta da yanda wanda suke yimishi irin wnn aikin amintatun yar wato goska da zazuuu Nan danan yakirasu Aiko Basu Dade ba suka zo.

Bayani suka musu sosai akan suje su jefar da gawan yarinya su tabbatar sunyi aiki da kyau kar asamu matsala sannan su gyara wurin,sukuma suka fice daga gidan suka nufi makabarta.

Bayan xuwan anty amarya daqyar mubeena ta iya fada musu abinda ya faru

Salati anty amarya taitayi jin abinda ya faru itama ba qaramin rudewa tayi ba

“Wai wace aishar kike magana ki bude baki ki min bayani yanda xan fahimta pls”
Anty amarya ta fada da iya qarshen rudu ta shiga jin rasuwar Aisha da yaxo musu bakatatan kamar a mafarki
Wayar mubeenar ta karba ta kira numbern umma dan qara gasgatawa,
Harta gama ringing baa daga ba sai ta juyarda akalar kiran ga amatu cikin saah kuwa ta daga wayar,
“Hello anty ashe kinji babbar rashin da muka qara samu ko,anty aisha ta tafi ta barmu da kewar ta,ta tafi tabarmu lokacinda mukafi buqatar ta””amatu takai qarshe tana fashewa dawani irin kuka mai tsuma xuciar mai saurare

Katse wayar anty amarya tai takai dubanta ga mubeena da tagama fita hayyacinta kukamma ya gagare ta
Anty amarya ce ta lallasheta hadi da bata baki daqyar ta samu ta shawo kanta sukai shirin xuwa gdn mutuwan Dan shikadai mubeenar ke buqata dukda dare ya somayi har 9tayi

Anty amaryace ta koma part dinsu Dan ta shiryo suje gdn gaisuwar dan bai kamata mubeena ta tafi ita kadai ba

A babban palourn papi ta tarar dasu mami harda mubeen dasu ibrahim nan take sanar dasu maganar rasuwar Aisha
Qarshen shock sunshiga most especially mubeen da yake da shaquwa sosai da Aisha
Hk ma Ibrahim mami ce dai ta nuna ko ajikin ta sai cewan datai Allah ya jiqan musulma
Anty amarya wuce wa part dinta ta canxo kaya dan dama sleeping dress 👗 ne ajikin ta,ta kuma sanya hijab
A bakin motarta anty amarya ta tarar da ita sanye dogon hijab harxasu shiga cikin motar saiga Ibrahim da mubeen nan suntaho wurin
Car key din mubeen ya karba a hannunta ba tare dayace qalaba suka shiga gaban motar ita da anty amarya kuma suka shiga baya
Mubeen ke driving dinsu har suka isa gdn rasuwar bbu mai mgn a cikin su

Qofar gidan cike take da mutanen dukda kasancewar dare ne kuwa,yanxu aka dawo daga kaita gdnta na gaskia shiyasa qofar ke cikeda mutane

Anan qofar gdn sukai parking din motar su matan suka shiga ciki sukuma maxan suka tsaya anan wajen

Allah ya jiqan musulma da suka rigamu gidan gaskia ya rahma musu mukuma intamu taxo yasa mucikada imani

X££l@h’s pen✍️✍️✍️

*X££l@h’s pan*✍️✍️✍️✍️

رَبِّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ أَنْ أَسْأَلَكَ مَا لَيْسَ لِي بِهِ عِلْمٌ ۖ وَإِلَّا تَغْفِرْ لِي وَتَرْحَمْنِي أَكُنْ مِنَ الْخَاسِرِينَ

****ACP mubeena****
Page 11

(Allah ya jiqan aisha yyi Mata rahma Allah sarki haihuwa yaqin mata,Allah ya sakama iyayenmu mata da
Mafificiyar alkhairi 🤲😥)

•••••••••su mubeena cikin gida suka nufa itada anty amarya ainda mubeen da Ibrahim suka xauna a waje wurin amsar gaisuwa

Kukan bbyn yafi komai daga musu hankaki cikin dakin hankalin kowa a tashe yake,ummah dake jin kukan bbyn har cikin xuciar ta,ta rasa abinyi sai tsantsar tausayin bbyn,amatu keta aikin jijjiga shi tun lokacin da aka fita da gawar mahaifiyar shi yake kukan kamar yasan abinda ke faruwa,
Da sauri ta qarasa shigowa cikin palourn jin yanda jaririn keta tsala kuka tundaga main entrain palour,karban bbyn tayi a hannun amatu ta rungume shi kamar xata mayar dashi cikin ta,cikin wani iko na ubangiji sai yy tsit kamar bashi keta tsallara ihu ba,
Kuka mubeena ta saki mai qarfin gaske jin yanda bbyn ke sakin ajiyar xuciya,baqaramin tausayi ya bata ba,
Shifa yanxu bbyn nan cikin maraici xai tashi yaxo duniya bai tabajin dumin wacce tai sanadin xuwanshi duniyar ba,shi kalar tasa qaddarar kenan,ita da koda mahaifinta yabar duniya ta gama mallakar dukka hankalinta amma haryanxu tana jin maraici mai girma inaga danda ko dumin mahaifiyar shi bai taba jiba kuma baxai taba ba😥
“Innalillahi wa’inna ilaihir rajiun”ta fada hadi da sakin wani kuka mai tsuma xuciar mutanen dake ckn dakin,
Dukda kasancewar mutuwar ta dare ce amma aisha tayi mutane na banmamaki,yarinyace mai shiga rai ga nutsuwa uwa uba sanin darajar dan adam batadamu da ta girmeka ko ka girmeta ba tana mutunta kowa gashi batada girman kai ko kadan shiyasa mutuwar ta ba qaramin dukan xukatan mutane dayawa tayiba kowa ya shigo shaidar arxiqi yake bayarwa akanta

(Haqiqa shaidar duniya itace abuna farko da ake fara dubawa bayan mutuwar ka/ki,yan uwa mu daure mu gyara mu’amalarmu da wadanda muke xama dasu dan samun shaidar farko bayan kwanciyar mu a qabari,Allah yasa mucika da Imani🙏🥺🙏)

“”””why aisha meyasa kika tafi kika barmu a lokacinda mukafi buqatar ki,meyasa baki dubi halinda wannan dan jinjirinda bai wuce yan awanni a wannan duniyar ba,shin kinsan irin halin da xai shiga,kina tunanin akwai wanda zai iya kula dashi sama da yanda xaki kula dashi,pls come back to us,we really need you at the moment🥹,

Ta fada tana fashewa da wani matsanancin kuka mai sautin

^^^^^^^^irfaan da ke kwance saman lallausar gadonshi da ke shimfide da wani hadadden dovet,idonsa sun kada sunyi matuqar jaaaa kmr tattasai,dafe yake da kanshi dake matuqar sara mishi kamar xai fado qasa,tun lokacin da suka dawo daga wurin jana’ixa a daddafe ya iya kawo kanshi gida kasantuwar maqabartar bbu nisa daga gidansu yasa tafiyar ta kasance ta qasa,
Bayan dawowa bai iya tsayawa xaman makokin ba cikin gd kawai ya nufa dan yanda yake jin kansa na sarawa baxai iya xama ba,
Kuka yake amma bana xahiri ba na xuci wanda ke saurin illata mutum,
Haqiqa aisha ta kasance matar hadi wanda shi da ita bbu wanda yakeson juna lokacin da sukai aure amma bayan auren nasu yake jinta har cikin ransa,bai taba kawo rabuwar su a kurkusa irin haka ba,addu’oi yaketa jerowa duk wacce taxo bakinsa,ihun kukan tane ya dan dakatar dashi daga bisani yc gaba da abinda yk yi,

“””haba,haba mubeena baaima mamaci irin wannan kukan sai kace bakida sani akan hkn yanxu bbu wani gata da aisha ke buqata a wurinmu face addu’ah sai kuma rungumar wannan marayan Dan data bar mn wanda nakeda tabbacin bi’ixnillahi baxai taba maraiciba tunda yanada ke gakuma amatu”
Acewar wata mata dake xaune gefen ummansu

(Mubeena dasu aisha uwarsu daya ubansu daya,mubeena itace babba sai aisha,amatu ce autarsu),
Tun daga lokacin sai mubeena ta natsu bata qara cewa komai ba sai wuri data samu gefe daya ta xauna,rungume da bby har wannan lokacin,
Wani ne yyi sallama bakin qofar dakin amatu ce ta miqe taje ta karbo saqon daya kawo jin ta dago muryan mai gadi ne da aka aika siyoma bby ‘NAAN Milk’,bayan ta karbo direct kitchen ta nufa ta hado mishi madarar cikin bby feeda,ta miqama mubeena ,bakin bbyn takai feedar farko yaqi karba sai daga baya ya fara sha (Allah sarki kamar in qwace bbyn,Allah ya rayashi akan sunnah yajiqan mumyn shi🥹)

Ranar mubeena a nan gdn ta kwana anty amarya dasu mubeen ne kadai suka koma gida da xummar xasu dawo da safe
A ranar mubeen da Jimamin rasuwar ya kwana dkm tausayin matarsa da qanwarta sanin yanda sukeda matuqar shaquwa da junansu gaskia jure rashin aisha xasu dade basu sababa Allah ya jiqanta da rahma

A safiyar washe garin ranar kusan kowa ya tashi da niyyar xuwa wurin gaisuwa dan ita anty amarya tun asuba tasa aka dafa abinci masu yawan gaske aka xuxxuba a manyan kuloli aka sassaka cikin moto haka su maryam matar Ibrahim dasu anty bilkisu matar uncle abbas duk sun shirya xuwa gaisuwar

A palournta ta tarar da ita xaune tana kallon tv hankalinta kwance da mamaki anty amarya ta dubeta hadi da qarasowa inda take xaune “aah maminsu ya naganki xaune kedaya kamata inxo in tarar dake ashirye”anty amarya tafada tanama mami kallon mamaki,dan yatsina fuska mami tayi tadaura da “xuwa ina kenan”tana kwabe baki,anty amarya batai mamakin jin abinda mamin tafada ba kasantuwar sanin halin mamin tun fil’axal da riqo amma komadai menene yafaru bai kamata taqi xuwa wurin gaisuwar ba kodan albarkacin umma dan umma ba bayaba akan alamarin gidansu,bbu yanda anty amarya batai da mami ba amma ta kafe akan bbu inda xata,xatai mata addu’ar daga nan idan kuma tasamu lokaci xata kira tai mata ta’axiyyar ta waya,
Bbu yanda anty amarya ta iya da mami dole suka tafi sukabarta a gida
Time dinda anty amarya ta fito daga part din nasu shikuma ya shiga,cikin shirin fita yk shima,
bayan sun gaisa yake tambayar ta mami fa nan take gaya mishi yanda sukai da ita,abin bai mishi dadiba samm koma dai me mubeenar tai musu bai kamata su huce akan wadda batajiba bata ganiba,sallama yaimata yace suma yanxu xasu je gdn rasuwar shida su uncle abbas,qarasa shigewa yyi cikin
Yanda anty amarya ta fita ta barta haka ya shigo ya sameta amma saidai wannan karon a kishin kide take,bayan ya gaidata yake tambayarta ya yaga bataje gdn gaisuwar ba
Taso taqi tanka mishi sai kuma ta nisa tace “sbd bana ra’ayin fita yau shine dalili na,”
“Amma gaskia umma hkn ba hujja bace karki manta na daga cikin haqqin musulmi idan ya mutu kai gaisuwar,sannan ba wannan bama aiba mubeenar xa’ai mawa ba,ummansu xamui ma gaisuwar,baiwar Allahnda na tabbata bata sanma abinda ke faruwa ba”
“Inji waya gaya maka batasan abinda ke faruwa ba dama akwai abinda mubeenar xatayi bada sanin taba,qyale wannan munafukar da saninta ake komai wlh”mami takai qarshen maganar a qufule,
“Haba mami inace shekaran jiya abinnan ya faru kuma tun a lokacin ma suna asibiti da margayiya dan haka gaskia batada masaniya akan komai sannan intaji ma nasan in sha Allah xata tsawatar”
“Uhm” kawai mami tace dan bata yarda da ummansu mubeenar batada masaniya akan duk abinda ke faruwa ba saidai tagaji da ja injan datakeyiwda dannata,
Saida mubeen yayi da gaske kafin mami ta yarda xataje wurin gaisuwar amma da shardin sai sunfara biyawa ta police station 🚉 wurin papi muddin har lokacin suna riqe da dokar da mubeena tasa na papi baxai ci abincin gd ba to tayi rantsuwar babu inda xasu daga ita har yayan nata
•••••••••••••••••••✍️

Basu wani Sha wahala wajen maigadin makabartar ba saboda sun bashi kudi masu yawa ya barsu suka shiga tare da jagorancinshi Dan shi ya nuna musu sabon kabarin wata mata da’aka kawo aranar da yamma,cikin farin ciki suka shiga tone kabarin dama tafe suke da kayan aikinsu har suka ci nasarar fito da gawar suka kwance suka cusa layan kamar ynda boka ya umurcesu "wa'iuazubullah".
:::::::Allah ya tuni asirinku masu baqar xucia😓

Goska da zazuuu kuwa sai da sukayi tafiya Mai nisa inda ba mutane sosai kamin goska ya tsayar da mota Yana kokarin fita zazuu yace "kaii yane yanaga ka tsaya anan"

"Ehmnh zamu hattama aikin ne mukara gaba"cewar goska yqna maganq irin ta Yan daba

Zazuu ya waro Ido yace"kaga mlm karka Bata mana aiki anan zamu yarda ita kasan su Alhaji cewa sukayi musamu qaton rafi mujefata ciki"

"Kaii zazuu aiki bayason wasa kadai San wani aikin muka baro muka zo Nan kana gani tun dazu Oga yake rafkamin kira naki dagawa"

"Eh kumafa gskynka ne ynzu idan oga dawo bamu gama Mai aikinshi ba akwai kura yaseen"

Haka Suka fito a motar suka dauki yarinyar da har ynzu jini be dena zuba ajikinta ba suka gangara da ita suka jefar dsauri suka shiga mota suka bar gurin da mugun gudu.

Mubeena na zaune adakin marigayi ya idonta duk ya kumbura yayi jajir saboda kuka da sauri naga ta Mqe tanufi wurin umma tayi mata magana kasa kasa sannan ta juya tafita daga dakin ahanyar fitarta parlor ne suka ci karo da Amatu tanata zuba sauri da tafiyar Nan tata ta rashin natsuwa "Aunty Mubeena Ina Zaki ne haka"

"Gida zani Amatu zan dakko kayana da magunguna na kije ki amsa baby agun umma ki goyshi"

"To Aunty sai kin dawo Kuma kardai kije ki samu wuri ki zauna kar Azo ayita tambaya Ina kike" cewar Amatu tana cigaba da tafiya kamar ba ita tafada ba.

Ko ta kanta Mubeena bata biba saboda saurin da take tunawa tayi tun jiya da safe rabonshi da abinci Dan tasan definitely indai ba ita tajeba baza'a bashi abinci ba, tana zuwa haraban gidan ta hadu da Irfan dake tafiya daqyar sbd damuwar da yake a ciki Ina zata Nan dai ta danyi briefing dinshi hannu yasa a Aljihu ya Ciro makullin mota yace "ai bakya hau adaidaita ba ga key din motar Aysha nan Allah ya tsare tace Ameen ngde dsauri Mai gadi ya Bude mata gate din tafita.
Da Dan gudu take Jan motar duk da tana cikin jimami Amma hankalinta na gurin papi sannin cewa kwana biyu jikin nashi ya motsa duk ta Kosa ashiga kotun ma gashi ran Wednesday ne zaman farko gashi Basu samu zama da Irfan ba mijin Aysha Wanda yake babban lauya ne Kuma sananne ne sosai akan fitar da gsky da bincike da tsage gsky da tsayawa tsiyan daka wajen ganin yaci shari'a ba'a taba kadashi a shiri'a Ba Barrister Irfaan Basheer Wanda akafi sani da Barrister IB sun fara magana da Mubeena akan shari'a su papi lokacin Yana Abuja wata shari'a sun tsaya akan idan yadawo zasu karashe magana ranar da ya dawo aranar Aysha ta rasu.sauke ajiyan zuciya Mubeena tayi tare da share hawayenta tana Kara Maida hankalinta akan tukin da take dandazon mutane ta hango agefen titi kare ware idonta tayi ganin kamar kafar mutum take hangowa kwane akasa,dsauri tanemi waje tayi parking tafito ta karasa wurin tana fadin lafiya? Meke faruwa anan?

Wani dattijo ba fulatani ne yajiyo Yana fadin "yarnan wlh gawan wata yarinya muka tsinta anan mun fito kiwo kinganta Nan kwance abun dai ba dadin fade kaman anlalata mata rayuwa ne ma akazo ka yasar daita anan......dasauri Mubeena ta kutsa Kai cikin mutane tana cin karo da yarinyar gabanta yayi wani irin mumunar faduwa tsigar jikinta ya tashi dakarfi ta furta "ya subhanallahi, innalillahi waina illahi raju'un"

To ana Dara ga dare yayi fah!!!!

*Ga Mubeena Nan ta baro gidan zaman makoki zataje duba papi ta hade da yarinyar da su Alhaji kk suka yiwa aika aika*

*Chan gefe Kuma gasu Mami chan anufi station aga shin Mubeena na ba papi abinci ko aa to tambaya ma anan shine zaa bari suga Papi din ko Ya ya?*

*To su goska dai sun Bata aiki wallahi🤬*

~Kucigaba da biyo mu inda zamu cigaba da kawo muku kullin da har yanzu ba'a gama kullawa ba warwareshi sai Kun biyomu~

Daga alqalamin 👇
X££l@h’s

https://chat.whatsapp.com/FSlzFMoMq7hEwo7lVhstQs

*X££l@h’s pen*

رَبِّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ أَنْ أَسْأَلَكَ مَا لَيْسَ لِي بِهِ عِلْمٌ ۖ وَإِلَّا تَغْفِرْ لِي وَتَرْحَمْنِي أَكُنْ مِنَ الْخَاسِرِينَ

****ACP mubeena****

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.