Trending Hausa Novels

Acp Mubeena

Reading file: ACP_MUBEENA.txt

Chapter 11 of 18

Page 7

Ai shugaba bawani Bata lokaci Da zaayi domin sunanshi ya Baci kawai mu canza Dan takara tunda ga Alh.kk nan ai na ganin kawai atsayar dashi dama tun farko shine Dan takarar namu kamin wancan Dan shishigin yazo ya mishi shigar sauri.....Alh Umar ya dire zancen Yana wani hura hanci "gsky bana tunanin Hakan shine mafita why not mujira muga yanda shari'a zata kaya cewar Alh.Aminu

Aa wane irin ajira sai angaama shari'a zabe fa Karatowa yake gsky ynzu yakamata ayanke hukunci atsayar da Wanda ya dace kawai shine daya daga cikin magoya bayan Alh.kk ya furta Nan Danan hall din ya hargitse da hayaniyya kowa na tofa albarkacin bakinshi.

Enough!!!! Shugaban jam'eya ya furta da karfi lokaci daya hall din yyi tsit bakajin motsin komai sai Karan Ac. Sai da ya dauki ruwa yasha sannan ya dago Yana dubansu daya bayan daya kamin daga bisani ya Bude Baki yace "tunda abun yazo da sabanin raayi zan daga zaman zuwa sati Mai zuwa sai ayi voting inaga Hakan shine maslaha kar kuzu ku raba mana kan jam eya"

Kowa yayi Naam da wannan magana ta shugaban jam eya Dan haka Taron ya watse kowa yakama gabanshi.

Achan waje Kuma Alh.kk ne da Alh. Umar suke magana kasa kasa don haka na karasa don najiyo muku mesuke fada.

"Kasan Allah Alh. Kk Ina gaya Maka sai ka tashi tsaye idan takama kasiya ya'yan jam eya ne duk ka siyesu don kasamu vote sosai sbd na lura akwai lauje cikin Nadi amaganan shugaban jam'eya da biyu yace ayi voting sbd yasan Alh.muhammad yafika magoya baya ah jam'eya kasan shifa yafi son Alh.muhammad Dan haka dole ne mu Nemi mafita kamin sati Mai zuwa".

" Ai ka kwanatar da hankalinka mutumina yanda kace din Nan haka zaayi duk siyesu zamuyi saboda a wannan karon ko ana ha Maza ha mata sai na tsaya takarar Nan Kuma sai naci sai dai duk wacce zaayi ayi ne,don haka ka shirya gobe akwai fita Dan dole inaga sai mun koma gurin malam Mai gobe da nisa Dan na lura sai na Kai sunan Alh. Dahiru Dan yanzu shine Wanda Nike ganin Yana kawo mana tsaiko!

"Eh to gobe sai mu leka malam din nasan duk abunda ake ciki ma zai fada manah" Nan sukayi sallama kowa yashiga motarshi suka bar wurin.

***ACP mubeena muhseen***

Zaune take a katafaren Office dinta wanda ya tsaru dakyau wayane a kunnenta da alama call take ansawa gefe daya wata matashiyar yar sanda ce xauna a gaban kujerar ta

Bayan ta gama wayar ta dago kanta hadi da furta “”yeah go ahead *Safna* ya ake ciki yanxu””

Yes madam haryanxu suraj bai kammala hada hujjoji ba da xarar ya kammala xaa shigarda case din kotu in Allah ya yarda

“”Ok hakamma yayi Allah ya dafa mana””

Safna ta amsa da ameen
“CP ya shigo kuwa””
“”Eh be dade da shigowa ba””
“”Ok ki koma office dinki xanje insame shi””

Tashi tai ta fice daga office din ita kuma mubeena saida ta qarashe shan coffeen ta sannan ta fice ita ma gabda xata shiga cikin office din CP ta jiyo hayaniya daga wurin su kopur bala,fasa shiga office din nashi tai ta juya inda take jiyo tashin hayaniyar tasu
Turus tai ganin mubeen ne dagashi sai yar tiler sheet ya cire rigar shi ya aje gefe sai tiqar dambe yake dasu kopur bala
Tsawa ta daka musu nan take su kopur bala da kopur audu suka shiga taitayinsu ainda mubeen ke mata wani kallo mai cikeda tsana jin itace ta hana kawoma papi abinci,dalilin fadan nasu kuwa shine a Daren jia khaleel dasu mami sunxo kawoma papi abinci amma akace musu ai mubeena tabada dokar kar a sake a karbi wani abinci aba papi saidai yaci na prisoners babu yanda basui dasukopur bala ba akan su daure su karbi abincin saboda papi ba kowani irin abinci yake iya ciba kuma akwai dokokin likitoci akansa ba kowani kalar abinci akeso yaciba amma firr sunqi yarda su karbi abincin dole babu yanda suka iya suka koma da abincin kuma batare da sunqara koda ganin papi din bane

Shine da safe bayan mubeen yabar part dinsu yashiga gaida mami take kora masa bayanin yanda sukai dasu kopur bala harda qari saboda ya qara tsanar mubeenar.
Nan take yace yanxu ina abincin da aka dafa mish tasa easherta kawo mishi already angama hadawa dama
Dauka yyi ya fice dashi ya nufi wurin motar shi yasa abincin sannan ya shiga bayan mota drivern shi musa ya jashi suka nufi police station din still kuma su kopur bala sukace ai dokace daga madam papi baxaici abincin gidaba,
Already kunsan yanda mutumin naku yake dama bashida sauqi ga saurin harxuqa ai kuwa shine ya tube riga ya fara tiqar dambe kamar Dan dambe dama kuma gashi da qarfin damben
(Mubeen dinnan ya cika jaraba amma xamui maganinkane😏)

*Amatullah*
Tsaye take da wasu manyan akwatuna guda2 sai fashion bags ta rataye daya a wuya dayan kuma ta riqe a hannu,sanye takeda purple hijab 🧕 dogone harqasa dan haka bangano muku kalan kayanda ke cikiba fuskarta dauke da light makeup black beauty ce
Gaskia ba laifi tanada sanyayyen kyau

Tsaye take bakin titi tana jiran mai adaidaita
Cikin saah kuwa batare da bata lokaci mai tsayiba saiga mai adaidaitan bbu kowa a ciki batare da bata lokaci ba ta tsayarda mai napep din
Fitowa yyi ya karbi kayandake hannunta yasa bayan napep din wato booth tai masa kwatancen inda xata,dai dai xata shiga cikin napep din saiga wani saurayi ya fito daga dan wani lungu ya nufo inda take ganin xata shige cikin napep yasa shi qwala mata kiran daya sata waigowa
Ganin yaxo gabda su yasa ta shiga ciki ta daura da
“”lpy kake qwalamin kiran matalauta haka?””
Dan murmushi yai kafin ya shiga shima ya xauna gefe ya daura da
“”Ba wannan ba Ina xakine da sanyin safiyarnan dakuma uban kaya saikace wadda xatabar gari””

Nantake naga fadada fara’ar fuskar ta kamar wadda aka taboma inda yakema qaiqayi kuwa ta fara xuba xance kamar wata soda

“”Ai nake gaya mk anty aishar muce ke asibiti tana naquda kasan dama tsohon cikine da ita too shine yaya irfaan ya kirani yace inxo da kaya shinefa kaganni da kayannan inaga ni yakeso inyi mata xaman jego””
Takai qarshe tana qara wage fararen haqoranta

Dariya naga ya tuntsure dashi kaman wani wawa sai da yayi mai isarshi sannan ya tsagaita dariyar tashi yakai dubanshi gareta ya daurada
“”wai ke dama haryanxu hankalin naki bai cikaba daga jin aisha na naquda ance kijeda kaya aikinsan kayan haihuwa ake nufi bawai kayan kiba amma xaki kwashe duka kayanki kice kecema wadda xatai mata xaman wankan amma gaskia kinci kai dayawa amatu””
Yakai qarshe yana qara tuntsurewa da wani irin mahaukacin dariya

Dan jimm kadan tayi tanajinshi saida taga yakai aya itakuma ta daura da

“”Wlh da alama musa kana cikin yan black stomach dina inba hakaba kuwa dagajin xankoma gidan madara xaka fara min irin wadannan maganganun kasan tun yaushe take labourn kuwa tunfa shekaran jiya da daddare take,kasani Kota haihune kasan halin mijin nan nata shida kurma banbancinsu kadan ne,shi ganin yake yafi qarfin ya bude baki yayi ma mutum bayani saboda mugun jida kai””
Tafada hadi da tabe baki daidai lokacin kuma suka kawo daidai gurinda taima mai napep kwatance..

Unguwace ta masu hannu da shuni iya tsaruwa qarshene unguwar bakajin hayaniyar komai sai kukan tsuntsaye kala kala daya cika unguwar,musane yataimaka mata fitoda akwatunan nata ya aje gaban tafkeken wani katafaren gate,kaida ganin wannan gate kasan cikin gidan baqaramin haduwa xeyiba

****police station****
Mubeen Muhammad yaaseer
Mubeena muhseen

Zata bude baki tai magana cikin tsawa ya dakatar da ita,afadace yafara magana da qarfi ta yanda har wadanda ke acikin cell suna iya jiyoshi
“””Mubeena who the hell did you think you are??am asking you me kike taqama dashi mubeena,me kike daukar kanki,you are over reacting mubeena abubuwanki sunfara wuce gona da iri wallahi ko ki bama wadannan karnukan naki umarnin su fito min da mahaifina na bashi abinci ko na sauya Miki kamani.....

Mubeena data cika iya wuya sbd ganin yanda Mubeen yazo ya zubar mata da mutunci wai dasu kofur bala yake dambe tace "do your worst Amma baza'a bashi abinci ba Wanda kowa yakeci acikin kurkukun Nan shizaici Shima"

"To kuwa sai dai ki zaba ko yaci abinci Nan ko Kuma igiyar aurenki!!!!

Daga Alqalamin✍🏻

X££l@h's
https://chat.whatsapp.com/KDkpfCh3PTgAMGI4xMc81W

*X££l@hs Pen*•••••••✍️✍️✍️✍️

رَبِّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ أَنْ أَسْأَلَكَ مَا لَيْسَ لِي بِهِ عِلْمٌ ۖ وَإِلَّا تَغْفِرْ لِي وَتَرْحَمْنِي أَكُنْ مِنَ الْخَاسِرِينَ

*ACP mubeena*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.