Acp Mubeena
Reading file: ACP_MUBEENA.txt
Chapter 14 of 18
Page 12
Da sauri Mubeena ta kutsa cikin mutane tana cin karo da yarinyar gabanta yayi wani irin mumunar faduwa tsigar jikinta ya tashi ganin yarinyar daga ita sai yar yaloluwar rigar da dakadan ta rufe mazaunanta gashi gaba daya jini ne duk ya Bata Mata cinyoyi da kafafunta da karfi ta furta "ya subhanallahi innalillahi waina illahi raju'un" wane azalumin ne ya aikata ma wann yar yarinyar haka Kuma ya zo ya yardata anan Kai jama'a".....
Wani ne yace "ai hajiya inaga tun jiya aka yardata anan ko yau da safe Kuma da alama ma batada rai Dan Bata numfashi"
Mubeena ta runtse idonta tanajin zuciyarta na wani irin tafarfasa tuni zuciyar Yan sandan ta motsa tace "Dan Allah ku taimaka min nasasa amota muje asibiti Kuma bansan me kukeyi ba da bawanda yayi tunani kaita asibiti kuka tsayakuna kallonta wasu ma naga pictures kawai suke dauka da video Ina amfanin irin haka mutum na Neman taimako bazaku taimaka maiba Amma ko wanne ya dauko waya Yana daukan hoto asamu na watsawa a media"
Dattijon Nan yace "wallahi yar Nan tun dazu fadan danake tamusu kenan sunki saurarena ynzu duniya ta lallace mutane babu imani duk Wanda yaga yarinyar Nan sai hankalinshi yatashi Amma wasu ahaka suketa daukan hoto,nikuma banida abin Hawa wani Mai mota Kuma damuka tsayar ya taimaka mana cewa yyi baruwanshi bazaije asibiti akamashi ba ace shi ya aikata beji ba be gani ba"
Wani saurayi agurin yace "ai hajiya ke kanki yanzu idan kukaje asibitin cewa zasuyi bazasu tabataba sai kunkawo report na yansanda ni"
Mubeena da tagama kaiwa wuya da takaici tace "Dan Allah ynzu duk ba wann ba ku kama min ita nasa amota muje asibiti aduba ko da sauran ranta" haka Suka kama mata har tashiga mota tajuyo ta Kalli dattijon Nan tace baba idan ba damuwa ko zaka bini muje asibitin?
"To" yace kamin ya Kalli danshi yamishi mgna da fillanci ya Bude gaban motar ya zauna tajasu da gudu suka wuce Bata tsaya ako'inaba sai general hospital Kano suna zuwa direct emergency aka wuce da ita Basu tsaya dogon turanciba kasan cewar likitoncin sun San wacece Mubeena wuri suka nema suka zauna don takasa tafiya wayarta ta jawo a aljihun doguwa rigarta da tun dazu aketa jero mata kira tabi bayan kira magana tayi dabata wuce ta mintuna biyu ba ta aje wayar tasa hannu biyu ta dafe kanta ta runtse idanunta.
Suna zaune tsawan Kusan awanin biyu kamin likitoncin da Akala sun Kai mutum hudu da suka rufa akan yarinyar suka fito duk sauran suka wuce babban likintan ne yatsaya yace was Mubeena su biyoshi office.
Ammm wato ACP maganar gsky da bake da kanki kika kawo yarinyar Nan ma da bazamu amshetaba Saida sa hannunku to Amma sai akaci sa'a hukumar da kanta ita ta kawo ta is a very serious case ACP!
Mubeena ta lumshe Ido tace "Ina jinka ACP Mai binciken ku yanuna and please is she alive"
Doctor sai da yacire gilashin shi yahade hannayenshi guri guda Yana murza yatsunsa yace " is a rape and attempted murder case but fortunately the girl is alive but she is in a critical condition right now"
Wani ajiyan zuciya Mubeena tasauke tana furta "Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah!!!
"Aiko sai godiya ACP domin kuwa ba karamin arziki ta auna ba don ta zubar da jini dayawa sannan ga kankantan shekaru fyade na mugunta akayi mata an Bata Mata rayuwa sosai Wanda inafatan Allah yasa kar ta kamu da yoyon fitsari"
Innalillahi waina illahi raju'un kawai Mubeena ke Fadi tunda yafara wnn magana
Yace"yanzu dai munyi mata duk abunda yadace jini ma yanzu haka muke Kara mata don inaga sai ansa mata Leda biyar ko hudu na jini don ta zubar da jini da yawa sannan doguwan Suma tayi shiyasa kuke tunanin ta mutu Amma muna sa ran farfaduwanta zuwa gobe don munyi mata alluran dazaisa kwakwalwanta tasamu hutawa"
Mubeena ta numfasa tace "nagode sosai doctor"
"Haba ba damuwa ACP nidai fatana Dan Allah ki tsaya ki kwatarwa yarinyar Nan hakkinta duk Wanda ya aikata mata wnn abun karki barshi yasha nasanki da kokari akan aikinki Dan Allah wannan yarinyar is too young ni na tabbatar bazata wuce 15 ko ma 14years ba Amma dubi yanda aka Bata Mata rayuwa wlh muna aiki Nan nurses din kuka kawai suke ganin yanda aka yimata kaca kaca wlh" Mubeena Kara runtse idonunta tayi tabudesu sunkada sunyi jazir tace sai inda karfina ya kare doctor wnn yarinyar ji nake kamar Amatu aka yiwa haka wlh kowaye mazai Sha ba Allah dai yatasheta lpy zanje station na dawo kahada min duk wani report zan karba akula da ita sosai ynzu ma anyiman rasuwane sister Dina ko ban dawo yau ba zan turo Wanda zata zauna da ita akula da ita kamin na dawo please "
"Innalillahi Ya Karin hakuri to Allah ya jikan ta yamata rahama karki damu akwai nurses zasu kula da ita Nima Ina Nan"
"Tace Ameen nagode"
*******
—————————mubena💗
Direct daga asibitin station dinsu ta nufa a daidai wurin shiga sukuma motar mubeen ke fitowa daga cikin station din xuciar ta ce tadan buga ganin motar mubeen din addu’ar ta Allah yasa ba wani abun yaje yyi ba,
Ibrahim dake xaune gaban mota yakuma ga my mubeenar ke fadin too itakuma mubeena meya kawota station da safiyar nan itada ya kamata ace tana wurin rasuwa,
Mubeen cikin mamaki yace mubeena kuma aina??
Baga tacan a wancan motar ba yanxunnan tashigo,Dan tsayarda motar yyi ya waiga inda mubeena tai parking motar ta,.
Dan qwafa yyi ya cigaba da tuqa motar yana cewa Maybe sunkirata sun gaya mata munkai ma papi abinci ne wlh muddin naji lbrn tahanashi cin wannan abincin saina mata rashin motuncin da bata taba tunanin na iya shiba,yakai qarshe yana qara qwafa,a qufule mamin dake xaune a bayan mota itada easher tace mubeen juya kan motar nan ka koma cikin station sbd nasan marar kunyar yarinyar nan tsab xata iya hanashi cin abincin nan kuma wlh ta kuskura ta aikata hkn saina nuna mata kuskurenta mami ya fada dan ranta inyayi dubu to ya baci,
Shawarar juyawa sukai suka koma cikin station din, a tsaye suke tarar da ita tana tanbayar su copur bala wayabasu ixnin karban abincin da su mubeen suka kawo,
Dan sosa kai copur bala yyi yace madam ayi haquri ganin mukai baki shigoo ba shiyasa•••••••
“ will you close your dirty mouth or else•••••••
“Or else what? Ki qarasa mana qaramar marar kunya butulu wadda bata gaji mutunci ba yar matsiyata kawai,ke watooo har kinyi qarfin xuciar haka to bari ganin Ina rage mk ba kuma tankama so nike ki gama qananun rashin kunyar ki har kifara wuce iyaka kamar yanda kike qoqarin yi yanxu in nuna miki har gaban abadaba’ayi yar iskar da xata wulaqanta alhaji inbata ta cigaba da walwaala a qarqashinsa yar matsiyata kawai haihuwar asara “
Mami da shigowar su kenan takuma ji abinda ke wakana tsakanin kupur bala dakuma mubeena,
“”Mami ki sani ina ganin mutuncin ki amma muddin kika cigaba da yunqurin hanani aikine tabbas baxai mana kyauba nida ke am doing what is right you have to be petience for a while kafin mu shiga kotu duk abinda kikeson sani xaki sanine amma a court dan haka karki gaggawa sannan karki kuskura ki qara xagarmin iyaye if not hmmm I will show you the rudless side of me”mubeena takai qarshen maganarta a fusace hadi da juyawa wurin su kopur bala
“And you don’t dare allow those filthy once to come near the station again if not😡 ku kuka dakanku,”
Tana kai qarshen maganar ta ta shige ciki tabarsu nan sake da baki
(Anty mubeena manya 🤣,yau kuma tsiyar akan mami aka sauke shi,Allah ya kare mana ke assistant commissioner of police 👮)
*ACP mubeena*💗
https://chat.whatsapp.com/FSlzFMoMq7hEwo7lVhstQs
*X££l@h’s pen*
رَبِّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ أَنْ أَسْأَلَكَ مَا لَيْسَ لِي بِهِ عِلْمٌ ۖ وَإِلَّا تَغْفِرْ لِي وَتَرْحَمْنِي أَكُنْ مِنَ الْخَاسِرِينَ
****ACP mubeena****
Page 13
Basu mami bar har su kopur audu dakuma kopur bala maganar mubeena ba qaramin dukar xukatansu yyi ba tun suna daukar lamarin nata a komai lokaci ne mubeena xata sassauta abin da takeyi amma ganin kullum abin baqaramin worse yake qara yiba,abin na matuqar daure musu kai sanin papi shine gatan ta a duniya abinda kowa yasani ne dan mutane dayawa ganin suke itadin yarsace saidaga baya da sukaga ya aura mata dansa sannan suka gane ba yarsa bane amma gatan duniyar nan bbu wanda baya nuna mata a gaban kowa kuwa.
CP lawal uthman da tun lokacinda aka fara wannan dambar wan a gabanshi batareda sunsan yana tsaye ba sai jiyo wata shu’umar dariyar sa dayai silar juyawar dukkansu gareshi
Dauke da wannan shu’umar dariyar ya fara magana
“”Uhmmmm mrs Muhammad yaaseer how did you feel ke a tunaninki irin horon da *ACP mubeena* ta samu xata dauki wulaqancin kune karfa ki manta saboda daukar fansa tasanya kakin jikinta,to kuwa yanxu takama mafaraucin ta da ta iya jurar komai dan ganin ya ci galaba akanshi kike tunanin sassauci a cikin alamarin nata,lallai iska na wahal da mai kayan kara,gwara ma ki koma gida ki cigaba da nemarwa hatsabibin mijinki sauqin wannan al’amarin Dan ba gudu ba jada baya dole xai girbi abinda ya shuka nan bada jimawa ba,
“And you mr Ibrahim yakamata kujawa uwarku kunne bana buqatar qara ganinta a station dinnan inkuwa ba haka ba xan dauki qwaqqwarar hujja akanta wlh Dan baxan juri ganin ana wulaqanta ACP ba,haduwar kotu xatafi armashi a lokaci alokacin ne xaku gane abinda ake nufi baa nanba ”””
Yakai qarshe hadi da wucewa ciki,uhmmmm mubeen ya sauke wata wahalalliyar ajiyar xucia hannun mami kawai yaja suka fita daga cikin station din Ibrahim dakeda rauni sosai kam hawayene keta fita a idonshi ganin duk wannan cin fuskar akan iyayensu akeyi,ganin yanda mami ke numfashi daqyar yasa suka wuce da ita asibiti kawai,baafi minti biyar da fitarsu ba saiga mubeena itama ta fito ta nufi parking space tabar station din baki daya direct papi mansion ta nufa kayan jikinta ta janxo sannan ta dauko kala biyu wanda xatai amfani dasu da dai sauran kayan amfanin da baxaa rasa ba Dan sai bayan anyi sadakar uku xata dawo,bata koma asibitin ba saidai tayi waya da dr yace mata everything is going fine sannan tasa officers 👮♀️ dinsu guda biyu sunje asibitin saboda tsaro,
Bayan ta isa gidar rasuwar ta taradda su anty amarya dasuka jima da xuwa gidan har lokacin duk wani abu da takeyi qarfin haline kawai amma lallai mutuwar aisha nanan a xuciyar ta
_____________________📌📌📌
Mubeena💗
Xuwan su anty amarya da anty bilkisu dasu maryam harda su yanmatan gidan yasata tadan saki jikinta ,dukda kasancewar basu wani saki jiki da ita most especially su maryam da yan matan gidan
Anty amarya ta buqaci ganin bbyn nan mubeena ta sa aka kira mata amatu ta kawo bbyn,haka ta taho buguxum buguxum,mubeena da batajin son magana karban bbyn kawai tayi ya Miqama anty amarya,so masha Allah anyi mishi wanka yasha wasu hadaddun baby set masu shegen kyau,karan kanshi abin daukar nashi abin kallo ne Allah sarki dan marayan Allah sai barcinshi yake sha cikin kwanciyar hankali,
Sai yanxu na tsaya naqarema bbyn kallon tsaf kyakkyawar gaskene kamar su har tayi yawa da dadyn shi irfaan,asali irfaan kyakkyawa ne ajin farko,hancinsa har baka sai dai bashida jiki sosai amma a murje yake,dogone gashi fari soll irin maxan nan da ake cema ajebours gayu kuwa baah magana,sai dai miskili ne maqura ma kuwa magana sai taxama dole yake iya yinta balle ma da yarasa abinda yake muradi tun a wancan lokacin ya qara xama so calm,Allah dai yasa kar new babyn mu ya dauko halin uban nashi😌
-BARISTER IRFAAN-the wealthy man,
Wannan kenan,
“Tabarakallahu ahsanal khalaqin”anty amarya ta fada ganin kyan yaron ba ita ba hatta su anty bilki da maryam duk saida kyan yaron ya tafi da imanin su,aikuwa nan take suka fara rige rigen karban yaron kowa saida ya dauke shi suna ta santin bbyn
“Ya sunan bbyn?”
Anty amarya ta tambaya tana duban mubeena,”ko haryanxu irfaan din baisamu yi mishi hudubar ba,
“ daxu amatu takai masa shi tace yyi mishi huduba,sunanshi ‘zain(beautiful)”
“Wow gaskia yaci sunanshi zain saboda dama sunan baki daya maanar shi kyaune sannan kyawawa kawai ake sama shi,Allah ya raya yyi ma rayuwa albarka,yajiqan mumynshi yasa tana a kyakkyawar makoma,aisha halinki nagari ya biki”acewar anty bilkisu,duka suka amsa da ameen ya Allah,
Nan take idanun mubeena suka cika taff da qwalla tunowa da last haduwar su da aisha bayan tadawo daga office ta biyo wurin aishar saboda umma tace aishar bata jin dadi kwana2 koda taxo tasameta a kitchen tana girki tare da masu aikinta,hartana xolayarta da
“Aah uwar biyu har kin watstsake kinkoma kitchen,” take ce mata to ya xaayi anty mubee ai mu dama yau lpy gobe ciwone sai Allah ya rabamu da shi xamu samu mu koma normal gashi dr yace in dinga motsa jiki shiyasa bana kwantawa kuma abban ZAIN bayason cin girkin kowa sai nawa shiyasa nake lallabawa,
“uhmmm lallai su juliet sannu da qoqari Allah ya qara danqon soyayya kuma shi babyn tun kafin xuwan shi duniya harkun rada mishi suna,ikon God sai kallo” Mubeena tafada tana dan dariya kadan
“Eh mana anty mubee ai wlh ina matuqar son sunan ne saboda nasan in sha Allah bbyn ba qaramin kyau xeyiba dadynsh ba baya ba wurin kyau shiyasa nacema dadyn shi kobayan raina idan na mutu lokacin haihuwar shi yasa mishi wannan sunan”takai qarshe da yar damuwa a fuskar ta.
Su kyau manya Allah dai ya rabaku lpy,zaki fara shirmen naki ko,uhmmm ni bari inxo intafi gida dama akan hanya nike tunda kin murmure abinki ta luv kike, Allah ya qara afuwah”Mubeena tafada tana miqewa daga saman stool dinda taxauna na kitchen din,”anty mubee dakin tsaya kinyi sallah sbd gab ake da kiran magrib sai kici abinci,.
“”””ke qyaleni gwara in je inyita a dakina insamu ladaddaki in irfaan din ya dawo ace ina gaidashi”””””””
Tafada tana ficewa daga kitchen din,dole aisha ta biyota tai mata rakiya har wurin da ta ajiye motar ta sukaima juna sallama,(ko sati baayi ba da faruwar wannan kuma tun lokacin basu qara haduwa ba saboda mubeena datai busy sosai saboda wannan case din na papi,tun kafin ta kamashi,amma sukanyi waya akai akai),
“Allah sarki Aisha Allah ya jaddada rahmar shi a gareki ya karbi baquncin ki,yakuma raya mana ‘zain’,tafada idanunta cike tabda qwalla😥,su anty suka amsa mata da ameen
~*<Mubeen Muhammad yaaseer>*~
Bp dinta ne yyi high sosai dan haka dole suka kwantar da ita da gaggawa,daqyar aka samu numfashin mami ya koma normal Dan haka suka bata bed rest nadan lokaci kafin sui discharge dinta su mubeen suka wuce sukabar easher ta kula da mami danshi yana da muhimmin xama da lawyer dinshi a office yau,bayan sallan Azhar yasamu zama da kwararan lawyer din daya dako tundaga Abuja Dan ya tsayawa papi Barrister Kelvin John sosai suke tattaunawa da Mubeen Yana dada jadadda mashi ko nawane zai biya Dan ya wanke mahaifinshi daga zargin daake mishi Bar.kelvin yace "Don't worry I will do my best to see we win this case"
"I trust you! Ynzu muje station din don ku hadu da papi din" Mubeen ya fada tare da mikewa Shima Barrister mikewa yayi suka fita.
Direct police station din suka nufa Basu Sha wahala ba aka hadasu da papi Wanda duk ya rame yyi Baki acikin sati daya daganinshi kasan bakaramar wahala yake Sha ba Kallo daya Mubeen yamishi ya sunkuyar da kanshi ya kasa Kara dagowa ya kalleshi gaba daya tausayi mahaifin nashi ne ya rufeshi da Kuma wata irin tsanar Mubeena,tambayoyi Bar.kelvin yashiga yiwa papi Yana bashi amsa shi Kuma Yana rubutu a yar jotter din hannunshi Basu wani Dade ba suka fita sai jibi zaa shiga kotu.
*DPP HALL*
Acike hall din dauke yake da manya manya Yan jam'iyace chan na hango Alh.kk ansha uwar babbar riga sai kyali shaddan take sai wani hura hanci yake Yana hada giran sama da ta kasa shi adole bayason raini gefensa Alh. Umar ne Shima yasha nashi wankan shaddan sai buga kamshi suke manyan manyan Alhazaii kenan Wanda suke damawa cikin siyasa,shigowar shugaban jam'eya ne yasa suka mike tsaye saida ya zauna sannan kowa yazauna, bayan ya Bude taro da adu'ah ne yace to batare da Bata lokaci ba zamu fara voting Nan aka gabatar da akwatin da suke irin wannan zaben,Bayan kaman mintuna talatin angama zaben ankuma irga kuri'un duk alokacin kasan cewar baa jinkirtawa sbd magudi anan take aka sanar da Wanda ya lashe zaben Alhaji Kabiru kalankuwa Haba Nan da Nan gaba daya wurin ya hargitse da hayaniyya magoya bayanshi nata farin ciki kasancewa fa gaba daya Alh.kk ya siyesu kadan ne daga ciki Basu bishi ba Yan Amanar papi,
karkuso Kuga bakin Alh.kk nake gayamuku yaki rufuwa yanda kasan gonar auduga sai zuwa ake anatayashi murna,shida shugaban jam'eya kwata kwata ba haka yaso ba Dan haka ma ana gama sanarwa be tsaya wani Bata lokaci ba yafita shida jama'arshi ko congratulating din Alh.kk beyiba yakara gaba abunshi.
~kalankuwa's residence~
Hajiya bilki ce keta kaiwa tana kawowa tunda maigidan nata yakirata ya mata albishir din shi aka tsayar atakarar Dan majalisa takasa zaune takasa tsaye ita da ma'aikatan gidan suna hada abunda zaaci Adan kwarya kwaryan walimar da Alh.kk din ya shirya fuskar Nan tata itama tacika da farin ciki sun gama cika dinning table din taf da abinci da kayan kwalam da makulashe.
Jin dirar motocinsu Alh.kk ne yasa ta sallamar Yan aikin suka koma bangaresu itakuma ta koma sama takara gyara kwaliyarta ta feso turaruka duk da ba abinda kwalliyar tayi hasalima idan ka kalleta zaka dauka gasar kyau zataje,ahankali tasako kasan tana Jin dariyarsu da shewar mijin nata da abokanansa cikin sigar Jan hankali Da kwarkwasa takaraso Kusa da mijin nata da shigowarsu kenan sauran duk sun zauna Shima sama yake shirin Hawa yakirata tace "congratulations my one"
Yawani kashe mata Ido kamar zai jawota jikinshi yace "thank you first lady andai gama shirya komai ko? Tace angama ranki shi dade ku karasa dinning din Nan ta matsa suka gaisa da sauran abokan nashi.
Sosai suka Bude cikinsu suna ta kullu wash rabu hani'an da abinci da kajin da aka shirya musu kala kala suna ci suna Mai da yanda akayi Alh. Umar ne yace "ai Nike gayamaka Alh. Mun ruga mun gama da lbrn na kejin chan yanzu sai dai wani ba Shiba"
Alh.kk ya kwashe da dariya yadan kurbi ruwa yace "aina keji gobe ake shiga kotu koya shari'ar zata kaya daga Nan dai nasan sai daurin rai da rai.....nagaya masa bakin rijiya ba wurin wasan yaro bane be jiba ynzu ai kaga an saitashi ahanya"
Daya daga cikin abokan nasu yace "gashi daughter in law din tashi Bata wasa bace ance ba karamin wahala take bashi ba"
"Ai Tamin daidai jinin uba ai ba wasa ba Kuma tasan aikinta,wai Niko naga ko murna shugaban jam'eya be Taya kaba adawar har takai haka ne? Alh Umar ya karashe maganar Yana kallon Alh.kk "umm dallah kyaleshi ni batashi nake ba wallahi innuwar rakumi tayi nisa da kasa sai gani sai Hange kasan shi ai na wurin na keji ne Dan haka ni ko ajikina iyaka idan ya shigo gonata zanyi maganin shine kawai !wai ya kunyi waya da wadancan yaran kuwa? Yakarashe maganar kasa kasa Yana sa kanshi Kusa da Alh.umar,murmusawa Alh. Umar yayi yace karka damu komai ya tafi daidai..murmushi yayi Yana jinjina Kai.
Daga alqalamin 👇
X££l@h’s pen
Littafin ACP mubeena paid book ne amma bashida tsada ankusa a gama free pages naira dari ukune dukanshi a daure a biya don samun cigaban shi
300 only
https://chat.whatsapp.com/FSlzFMoMq7hEwo7lVhstQs
*X££l@h’s pen*
رَبِّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ أَنْ أَسْأَلَكَ مَا لَيْسَ لِي بِهِ عِلْمٌ ۖ وَإِلَّا تَغْفِرْ لِي وَتَرْحَمْنِي أَكُنْ مِنَ الْخَاسِرِينَ
****ACP mubeena****
Page 14
💗*~mubeena muhseen~*💗
Haka aka cigaba da xaman makokin Aisha cikin alhini su uncle abbas dasu Ibrahim harma da mubeen sun qara xuwa gaisuwar, su anty amarya kullum suna kan hanyar xuwa da shatara ta arxiqi bbu qyashi ko baqin ciki ko kadan a xuciar anty amarya,mamice ko leqe itada autarta easher,dantane tadan qirqiri qaryan ciwon da takeyi ne ya hanata xuwa amma tace inta ji sauqi xataxo,bayan addu’ar uku kowa ya watse yan uwa da abokan arxiqi mubeena taso abata bby zaid ta tafi dashi amma irfaan yace bbu wanda xe iya barin ma yaron ,hajiar shi bbu yadda Batai ba amma yace shifa abarshi da danshi,hajiyar shi ta kular mai dashi inma baxata iya ba to xai nema msh nany kawai amma shi sam bai yarda abar gidan da Dan ba,bbu yanda su umma suka iya dole sukai shirin komawa gidan su batare da bby zaid ba.,
Hajiar irfaan ne xaune a katafaren bedroom din ta dayaji kayan alatu harya gaji da haduwa,bbyzaid na hannun ta,ta xuba mishi ido bbu qaqqautawa tana mutuqar tausaya ma rayuwar danda ya taso amaraici duk gatan da wasu xasu bashi shi dimin jikin mahaifiya na musamman ne,tunowa da irin dawainiyar Aisha gareta yasa idanuwanta cika tab da qwalla haqiqa Aisha yace ta halakk yarinyar kirki bata taba jin lbrn ance ga abokin fadar taba,kyautatawar Aisha agareta tamkar na ya da uwace bawai sirika ba,aisha kan hidimta mata da qarfin ta akwai abubuwan da Sam bama aikin ta bn amma ta daura wa kanta,koda bata buqaci ta taimaka mata ba takanyi balle kuma ta buqata ai sai inda qarfin ta ya qare, a Dan xaman da sukai da aisha bara tace ga rana daya da aishar ta taba saba mata ba koda a kuskure gaskia samun irin sirika kamar ya awannan xamanin abune mai matuqar wahala itadai ptan ta Allah ya jaddada
Rahmarshi agareta,
Sallamar ummace ta katseta daga duniyar tunanin da ta dulmiya a ciki,da sauri tasa hannu ta dauke qwallar da ke a saman kuncinta ta gyara fuskar ta kafin ta amsa sallamar hadi da bada umarnin shigowa
Kallo daya umma taima hajiya laila ta gane tana acikin damuwa amma tasan na lokacine sbd irin sonda takema aisha dole mutuwar baxatai saurin sakar taba,xama tayi Dan gefen gadon da hajiya lailan ke akai
Dama sallama taxo yi mata tace har amatu fitar da kayansu irfaan yasa driver ya kaisu,
“Wai kina nufin harda amatu xaku tafi ne,aikuwa da sake dan kam dole kiyi haquri ki qara aramin ita idan ta tafi waxai kular mata da dan nata”acewar hajiya laila Dan batai tunanin xaa tafi harda amatun ba,
“Toh hajiya ganin nayi xaman me xata tsayatayi tunda anyi uku ai kuwa kinga bata xaunaba gashi suna gab da fara exams ma”
“Ai komadai mexasu fara dole kibarma danta ita inace dama takwaso kayanta tace xaman jego taxo yi,kinga kuwa tunda Allah yyi ikonsa akan mai jego ai tabar wanda aka kwaso kayan danshi,tunda duk tsawon xaman da mukai bata taba cewa xata xauna ananba sai a dalilin xuwan danta kinga kuwa abarta ta xauna dashi har yyi qwari gaskia inaso ya shaqu da uwar tashi sosai”
Umma ta gamsu da maganar hajiya lailan sosai dukda tana tsoron shirme da shiririta irin na Amatun,
“Toh hajiya laila amma bakya gudun shirme irin na amatu kinfa santa hankalin a samar gashinta yake baa qwaqwalwa ba,”
Yar dariya hajiya laila ta saki tace nikuwa xan iya da yar autar taki saidai inbakiso ki aramin dinne”
“Haba ni na isa ai dole na ara mk ita,Allah yasa yar taki ta yarda kinsan wani lokacin bugun iska ce”
Dariya suka sa dukansu hajiya laila tajanyo wayar ta ta danna call,
~~~Amatu da tun daxu ke xaune bakin gate tana jiran umma ta fito su wuce dukda har cikin ranta bata son barin bby zaid dinta,amma bbu yanda ta iya,gefe daya take tsaye fuskar nan daure tamau bbu annuri a kanta,mai gadi dake lura da mutuniyar tashi sai Dan sakin murmushi yk da alama ran mata a bace yake,daga inda yake ya qwalla mata kira ko wai genshi batai ba,ana cikin hakan ne kiran hajiya laila ya shigo wayar ta,kmr mai jira tai wuff ya dauki wayar amma batace komai ba,banji abinda hajiya lailar ta fada mata ba naga anurin fuskar ta tadawo kmr ba itace keta faman kumbure kumbure ba yanxu,ganin nai ta sauke wayar daga kunnenta ta xura a guje bangaren hajiya laila din,bata dakata a ko Ina ba sai bakin qofar bedroom din hajiyar sannan ta tsaya tanata maida numfashi kmar wadda tai gudun fanfalaqi bugum ta fada cikin dakin dukansu saida suka firgita,
“Ai kinga abinda nk fada mk amatu batada natsuwa kokadan xatai ya saki surutu ne kawai”
Dan murmushi hajiya tai tace bbu komai haka nakeso n kayana,harga Allah hajiya laila na matuqar son haihuwar mace amma sai ta haifi na miji kuma daga kan irfaan bata qara haihuwa ba shiyasa tadauki son duniya ya daura mashi,
Bayan tafiyar umma amatu ta cigaba da rainon bbyn ta tana matuqar ji dashi duk rawan kannan nata bata taba yarda tai wasa Dan nata kuma duk bayan kwana2 sukanje gd wurin umma su wuni a can,.
____________
💗*~mubeen Muhammad yaaseer~*💗
Tun bayan da mubeena tadawo bai qara bi ta kanta ba Dan ya bawa banxa ajiyar ta tuni,baya da lokacin ta ayanxu burinshi Kawai lokacin shiga kotu yyi ya dau damarar yagalgala ta acan shiyasa ma yace ma mami tafita sabgar ta yanada shiri akanta,kuma last xuwan da yayi station wurin papi ganin yanda papin yyi matuqar Rama ga wani baqi dayayi ba qaramin tayar msh da hankali hakan yyi ba,papi ne ya kwantar masa da hankali cewa karya daga hankalin shi komai xai wuce da ikon Allah,da anje kotu dole xaa wanke shi daga xargin da ake mish,sannan papi yaja hankalin shi tare da roqon shi akan mubeena,yace indai bashida alhakin kowa akansa xatai nadamar abinda tai mishi Dan haka dan Allah karya qara kulata kuma ya fadama mamin tashi ma ta daina tada hankalin ta komai ya kusa qarewa in sha Allah,Dan haka ya tattareta ya ajeta agefe guda Kuma shida lawyer dinshi suna kokari wajen ganin sun tare hujoji.
~General hospital~
Washe gari yarinyar tafarka cikin tsanin fargici da tsoro wani gigitacen Kara ta kwala daya jawo hankalin nurses da yar sandan da ke waje harsuna rige rigen shigowa fisge fisge takeyi harta cire Karin ruwan jini ya fara zuba ahannunta dakyar suka samu suka danneta suna lallashinta Wanda har yanzu Bata bar ihun ba duk ta firgice sai zazzare idanu take Mubeena ce takaraso dakin cikin sauri itama sbd tunda tashigo wurin ward din take jiyo ihunta "lafiyaaa me yasa meta haka" ta furta tana karasowa gaban gadon da sauri.
"Welcome ma! Muma muna waje mukaji ihunta Dan inaga farkawanta kenan" yar sanda tafada
Daya daga cikin nurses din tajuyo tana tace "mah taimaka ki rikemana ita dakyau bari na kira doctor inaga sai an mata alluran bacci Kuma"dasauri Mubeena ta riketa sbd dama Koda ta iso gurin su uku tagani akanta tana riketa dakyau tace musu su Dan matsa suna matsawa tayi sauri ta rungume takarfi yanda bazata iya kwacewa ba tasa bakinta daidai kunnene yarinyar tafara karanto mata adu'oi,tadauki lokaci sosai tana mata adu'ah Dan har likitan yashigo ya samesu ahaka ganin ta dena fusge fusgen sai wani irin kuka da take Mai ban tausayi da tsuma zuciyar Mai saurare yasa yace musu su fita dukansu subasu wuri,duka aka fita aka barsu su biyu adakin.
Jin tafara kuka yasa Mubeena dakata da adu'an da take tafara lallashinta cikin sanyi murya da kalamai masu kwantar da hankali ahnkli ta raba jikinsu sai takama hannuwan yarinya ta rike tace kanwata ko zan iya sanin sunanki? Shiru tayi Bata amsataba sai tace to ni bari na fada Miki sunana ni sunana Mubeena Kuma yar sanda ce ni wacce ta shirya hukunta duk Wanda ya aikata Miki wnn muguntar! Dasauri yarinyan dago ta Kalli mubeena Bata daiyi magana ba Amma idanunwanta da alaman tambaya Mubeena tayi murmushi tace dgsk nake duk Wanda ya Miki wnn rashin imanin kowaye shi saina kamoshi na hukuntashi dai dai da laifinshi yanzu dai inaso ki kwantar da hankali ki kinji kanwa tah"
Shiru ya Dan ratsa har Mubeena ta fida ran samun amsa sai taji murya Mai sanyi da dadi tace mata "sunana Aisha" zuba mata Ido Mubeena tayi sosai kamin ta sauke ajiyan zuciya ta dafata tace kanwata tatafi kanwata ta dawo lallai zan tsaya Miki sai inda karfina ya kare kodan albarkacin wannan suna naki sai Kuma akaci sa'a an aikata Miki laifin Dana tsana arayuwata "fyade" kedin inajinki kamar kanwata ne so dole na tsaya Miki yanzu dai bari na fara Kiran doctor ya kara dubaki sai na zuba Miki abinci kici inji kanwatah!!! Gyada mata Kai Aysha tayi itakuma ta Miki tafita zuciyar cike taff da tausayi da kaunar Aysha.......
Gamai buqatar cigaban ACP mubeena 300 only
Free pages sun kusa qarewa adaure a biya Dan jin yaxata kaya
Shin papi ne da gaskia ko mubeena ko biyo zainab &laurat( Z££l@h,s) danjin ya xata kaya
https://chat.whatsapp.com/IIzvJ7l40854gOZahJJxq2
Daga alqalamin 👇
*X££l@h’s pen✍️✍️✍️
*X££l@h’s pen*
رَبِّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ أَنْ أَسْأَلَكَ مَا لَيْسَ لِي بِهِ عِلْمٌ ۖ وَإِلَّا تَغْفِرْ لِي وَتَرْحَمْنِي أَكُنْ مِنَ الْخَاسِرِينَ
****ACP mubeena****
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.