Acp Mubeena
Reading file: ACP_MUBEENA.txt
Chapter 18 of 18
Page 20
*Guest House*π‘
Kaiii bazai yuwu ba wallahi tallahi duk wacce zaayi sai dai ayi ta wane tudu wane gangare aka hau aka sauka har yarinyar nan ta rayu iyee wai ka kira su goskan ne ko ya ya?Alh. Kk ne ke magana hankali a matukar tashe
Alh.umar ne ya Kara manna wayar shi kunne Yana Kara Kiran goska har ta tsinke be dauka ba Dan haka ya fara kwada layin zazuuu , shiko Alh. Kk ya kasa zaune ya kasa tsaye sai kaiwa da kawowa duk jikinshi ya jiqe duk sanyin AC dake falon Amma tsiyaya yake.
"Hello zazuu Ina kuke ne tundazun nake kiranku Ina goska kuzo ynzu muna guest house muna jiranku"kit ya kashe waya ya Maida dubanshi kan Alh.kk yace " ka kwantar da hankalinka Honourable abinda ga sunan zuwa.
Alh.kk yace "na kwantar da hankalina fa kace wane irin, yarinyar Nan Ashe Bata mutu ba,bayan Kai da kanka kacemin ta mutu sai gashi ana nunata a news an tsinceta anyi mata fyade an yarda ita a bakin hanya ynzu haka tana asibiti!!! Dai dai Nan su goska suka shigo falon harda Yar sallamarsu,Aiko dama zuwansu yake jira Nan ya hau sauke musu ruwan masifa " dama aikin Dana Baku cewa nayi ku jefar da yarinyar Nan a rafi inda ruwa zai Yi gaba da gawarta ko cewa nayi kuje ku ajiyeta inda Zaa tsinceta?? Goska yace " ehhhh ya Hajj ai can teku mukaje muka jefar da gawarta chan wajan gari ai inaga ynzu ma mutanen ruwa sun gama party da gawarta" Alh.kk da yagama zuwa iya wuya ganin karyar da goska yake shirga Mai yace "Kai Kaci kutumar ubanka goska yaushe na fara wasa da Kai wallahi idan baka fadamin yanda kukayiba sai nasa anbatar min da Kai" tuni goska ya shiga hankalinshi sai yanzu ma ya lura da yanayin su Alh.kk din.
Shi dama zazuuu tunda yaji bayanin da Alhaji yafara Yi yasan zaa Rina saidai yace suje su jefata cikin ruwa goska sarkin gaggawa yace ba haka ba gashi yanzu anyanka ta tashi" tiryan tiryan kuwa ya fara bayanin yanda sukayi Aiko idan ransu Alhaji yayi dubu to ya Baci suka hau musu fada sosai sukuma sunata Basu hakuri Nan da suka sallamesu sukuma suka cigaba da tattaunawa inda Alh.umar ke kwantar Mai da hankali akan ai sun Bata kwaya bata cikin hayacinta so bazata ganeshi ba da wannan magana ne hankalinshi ya Dan kwanta Amma fa baya tunanin zai barta da ranta saboda yanaji ajikinshi kamar yarinyar Taga fuskarshi lokacin inko hakane dole ya kawar da ita din bazai taba wasa da abinda zai zama barazana ga siyasar shi ba.
*The hearing*
Ranar Monday 11 ga watan February da misalin karfe 10:00am Barrister Irfan ne da ACP Mubeena tafe acikin mota Wanda bar.irfan ne ya biya har gida ya Dakota suka nufi kotu da zaayi zaman karfe 11am saura one hour kenan afara sauraren karar su papi tafe suke suna tattaunawa inda ta hada duk wani bayanai ta damkawa Irfan din tun daren jiya,sosai Irfan din yake mamakin evidence din da Mubeena ta gabatar mishi na karshe jiya da Kuma bayanan da tamishi masu daukan hankali,tun jiya yake jinshi sukuku saboda abun yadake shi lallae wannan shari'a akwai tirka tirka da chakwakiyya acikinta Wanda shikuma zai dage iya iyawarshi Dan ganin anbiya Mubeena hakkin kisan wulakancin da akawa mahaifinta.
*Papi's mansion*π’
Mami ce tafito cikin shigar larabawa dogowar abaya Mai mugun tsada da taji stones tayi rolling kanta da gyalen abaya din sannan ta daura wani gyalen akafadarta tanata kokarin Saka agogon hannu ta dago ta dubi Mai shigowar Anty Amarya ce da Ibrahim suka shigo atare "yauwa Mami kin gama shirin muje ko" cewar Anty Amarya Ibrahim yace Mami "Ina kwana" agaggauce ta amsa tana tahowa direction dinsu tace " Aunty amarya ya Banga Mubeen ba badai be fito ba"
."aa ya fito Yana waje ai shi yaje ya kiramu ma kinsan Mubeen bazakiyi wasa da ranar Nan ba Yana chan yafito da mota ma duksu abbas ma suna waje ke kawai muke jira" Mami tace "to muje kawai naga saura ma 30 mins shiga court din"Haka suka dunguma motoci biyu gaba daya iyalan papi suka nufi kotu.
*Federal High Court*
*11:02am Monday*
Shigowar Alkali ne yasa gaba kidaya mutanen kuton mikewa tsaye bayan da Mai karanto laifuka ta furta kotu!!!
Sai da Alkali ya zauna sannan kowa ya zauna bayan anshigo da Mai laifi ne Wanda ya kasance Papi domin da shari arsu zaa fara sannan Mai karanto laifi ya Mike ya Fadi papi ya karanto laifin da ake tuhumarshi dashi kamin ya koma ya zauna, sannan lauyan papi ya Mike yace "ni sunana Barrister kelvin John nine lauyen dake kare Wanda ake Kara tare Dani akwai mataimakina Barrister Anas hamza" yana zama lauyan Mubeena ya Mike yace" sunana Barrister Irfaan Basheer" nine lauyen dake karar Wanda ake tuhuma tare Dani akwai Barrister Hanan Tafeeda Nan shima ya koma ya zauna inda Alkali ya juya ya Kalli papi yace to kaji laifin da ake tuhumarka dashi shin ka amsa laifinka? Papi Wanda tunda aka shigo dashi kanshi na sunkuye sai yanzu ya dago bai sauke idonshi akan kowa ba sai akan Mubeena wacce ita dinma shi ta zubawa Ido sai da suka dau Yan sakanin suna kallon juna kamin ya dauke idonshi ya Kara sunkuyar da Kai inda Alkali ya Kara maimaita maishi tambayan a sannan ne yadago ya dubi alkalin sanann ya girgiza Kai yace "aa ya Mai shari'a ban aikata ba!!! Wani irin ajiyan zuciya Mubeen ya sauke.
Nan Alkali yaba wa lauyoyi daman yin tambayoyinsu, Barrister Irfan ne ya fara mikewa cikin tafiyar nantashi ta Isa da izza ya Tako har gaban papi fuskar Nan tashi amurtuke yace "Alhaji Muhammad yaseer kotu zataso sannin meye alakarka da marigayi Alh.muhseen?
Papi yace" Amininah kuma dan uwa Kuma surukinane domin yarshi na auran danah" bar.irfan ya jijiga Kai alaamar gamsuwa yace "zanso karka wahalar da kanka ka Kuma wahalar da shari'a ka amsa laifinka,meyasa ka kashe Amininka? Papi ya dago ya Kalli barrister cikin wata irin murya ya furta bani na kashe shiba.....
"Kai ka kashe shi mana mutumin da ya amince dakai ya kaunaceka ya soka kamar Dan uwanshi shine ka kasheshi da hannunka.....Objection my Lord!!! Barrister Yana kokarin tursasa client dina ya amsa laifin da bashida hujjanshi ya aikata Bar.kelvin ya furta a fusace.Alkali ya Kalli Irfan ya furta a kiyaye Barrister,sunkuyar da Kai tare da furta to ya Mai girma Mai shari'a zan kiyaye,sannan ya juyo ya Kalli Bar.kelvin tare da Sakin wani shu'umin murmushi yace "Niko nikeda Hujjah nagani da Ido bana fade abaki ba idan kabani dama my Lord zan gabatar da hujjata ta farko"
"An baka dama"Alkali ya furta juyawa Barrister Irfan yayi ya fara takawa har zuwa wurin brief case dinshi inda gaba daya hankalin kowa yake kanshi ya dako Dan karamin flash din ya mika sannan aka mikawa Alkali inda shi Kuma ya Bada daman asaka akayi connecting da tangamemiyar TV din dake cikin kotun Nan danan kuwa ya fara playing.
Kotu gaba daya tayi tsit kowa hankalinshi nakan screen din Nima chan na Maida hankalina inda fuskan Daddy wato Alh. Muhseen ta bayyana awani daki Wanda yafi kama da hotel zaune yake Yana hada wasu takardu ga dukan alamu sauri yake duba da yanda yake hada takardun kofar dakince tabude da sauri ya daga kanshi ganin Alh.muhammad ne ya shigo yasa ya Mike tsaye Yana tura takardun cikin brief case din dake gabanshi,papi ya karaso gabanshi magana sukeyi Amma cikin fada fada sukeyi kuma baaji abinda suke cewa kasan cewar daukar na Kara wani irin cafka papi ya kaiwa daddy kokowa suka kamayi kamin Allah ya ba papi nasarar yadda dady akasa wata wuka yazaro daga cikin Aljihun rigarshi Mai kaifi bai tsaya wata wata ba ya cakawa dady kirjinshi dai dai saitin zuciyarshi da sauri Kuma ya Mike ya dauke brief case din yafita da sauri batare da ya Kara kallon inda dady yake ba,Kuma adaidainan video din ya tsaya Aiko gaba daya kotu ta hargitse da hayaniyya inda umma,momy da Aunty amarya suka fashe da kuka Mubeen kuwa juyawa yyi ya zubawa Mubeena Ido ko kiftawa bayayi jikinshi gaba daya ko Ina rawa yake "This is impossible! Abinda kawai ya iya furta WA kenan, Mubeena kuwa Bata masan yanayi ba domin hankalinta nakan papi wanda tunda video din ya tsaya ya sadda kanshi kasa ahankali ta furta kunya duniya kenan papi ai da wane Ido zaka Kalli wayanan dubin mutanen da suka baka yarda da aminci!!!!
Muma anan zamu diga Alkalaminmu sai zuwa gobe kubiyomu don Jin
*me dady yayi wa papi da zafi haka har ya kashe shi,masoyan papi ina tayaku jimami domin dai Mubeena ba hasashe take ba ta tabbata surukinta shi ya kashe mata uba, ko meye dalili?*
*Anyaka ta tashi su Alh. Kk ana cikin tashin hankali Aysha na Raye ga zabe Kuma yanata matsowa*
*Shin wai me CP ke kullawane? Kuma waye Alhajin da yazo gurinshi*
*Da wanne Ido Mami da Mubeen zasu Kalli ACP Mubeena?*
*wanene yasa aka aikata na mubeena wannan mummunar dukan?*
Duka amsann tambayoyin Nan suna cikin ACP Mubeena Kashi na biyu #300 kachal Zaku karanta abunku cikin kwanciyar hankali.
Daga Alqalaminβπ»
π*Himlat* da *Dr.zee*π
Idan anbiya aturo shaidar biya ta wannan numbobin
09038727860
09161738928
*Magic PEN π *
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.