Best / Popular Hausa Novels

Hamdah Littafi Na 3 Complete Hausa Novel

Reading file: HAMDAH part 3 Complete - Copy - Copy (1).txt

Chapter 15 of 33

Zubewa nayi kan kado nakife fukata jikin pillow, kai na rika juyawa ina ta fafutukar son na mance da tunanin, amma ina sai daÉ—e tahomin yake, da karfi cikin karaji narika faÉ—in
"Wlh Allah Abba ban taɓa ai kata zina ba, Ya SALEEM ba wani ɗa na mijin daya taɓa sani na mace bayan kai, duk da karancin shekaru na Inna ta ta tsoratar dani haɗe da kyamatar dani illan dake cikin zina, Ya SALEEM kai ka sanar dani mene ne aure, a lokacin da kuma nasan mene ne auren akayi min kagen zina aka kuma sheganta min ƴaƴa, bazan taɓa aikata zina ko da ace bani da aure bare ina da shi ɗin."
wani irin kuka ne ya tsuɓuce min, na kankame jikin pillow'n ina cigaba da kuka mai tsanini.
nakai tsawon awa guda ina kukan kana da kyar na sai-saita zuciya ta na baiwa kai na da kai na hakuri, kana nagyara kwanciya ta wan da ba bacci nayi ba, sai tulin tunani daban-daban.
har yamma ina nan kwance, ganin tunani yana kokarin kassara ni sai na mike nanufi side É—in su Bappa,
a can na iske su Naseem, har dare muna can sai wajen bayan sallar isha kafin muka koma side din mu.
zuwa lokacin kam naji saukin damuwa ta kwarai dan su Inna wuro sun yaye min shi da hirarsu mai É—ebe kewa.

Washegari Lahadi ma ban yarda na zauna a side É—i na ba da sassafe na wuce part É—in su Inna wuro acan mukayi breakfast, a nan nawuni muna hirar mu cikin jin daÉ—i.

Yau Monday da misalin karfe 7 narako su Nasmah har sai da naga tashin su kafin na koma ciki, ina gama abun da zanyi nawuce side É—in su Bappa, ina shiga bayan mun gaisa Bappa yake cemin
"Dama yanzu nake da shirin niman ki, kan ai kin masallacin nan ne harfa an rigada an gama shi, wan da aka bashi kwangilar jiya yake sanar min da cewa an gama."
da murmushi sosai kan fuskata nace
"Kai masha Allah kai amma dai ai kin yamin sauri wlh."
Bappa yayi murmushi tare da faÉ—in
"In dai da kuɗi a kasa komai cikin sauki yake zuwa, in dai da kuɗi ai komai mai sauki ne Allah dai yaba da ikon cin jarabawar da yayi dan shi kanshi arziki babban jarabawa ne, yakan kai mutum wuta yakan kaishi aljanna, kuɗi kamar takwabi yake idan kayi jahadi da shi shigar aljanna mai sauki ne idan ka ai kata ɓarna da shi shiga wuta mai sauki ne, Allah yasa mudace."
Amin Amin. duk muka amsa da shi
cikin washe baki nace
"Bappa masallacin nan fa nagina ne saboda Inna duk ladar arika kai mata kabarin ta, shima asibitin da yanzu ake gina shi idan a ka gama komai kyauta za'a rika yi duk ladar arika kai mata cikin kabarin ta".
"Masha Allah masha Allah".
abun da Bappa da Inna wuro suka rika faÉ—a kena.
Bappa yace "Ubangiji Allah ya tabbatar mana da hakan Allah yajikanta da rahama ya kai mata dukkanin ladan kabarin ta ya kyautata namu bayan nasu, kai sannu HAMDAH kinyi tunani kwarai da gaske Allah ya saka miki da mafificin rahama."
Amin. nace ina mai jin sanyi da daÉ—in addu'ar da yake min.

Muna nan zaune a parlour ban ankara ba sai gani nayi karfe 12 har da É—ori,
wayata na É—aga da sauri ina faÉ—in
"Ikon Allah lallai guri babu wuya dubi 12 har ta gota an yama Yakubu yadawo kuwa bari dai na kirashi naji."
nayi maganar ina laluɓo lambar sa, wayar tayi ta ring bai ɗaga ba, nakira yakai sau biyar bai ɗaga ba, na sauke wayar ina faɗin
"Oh to ya ajiye wayar a ina ne shi ga lokacin É—auko su Nasmah daga School yayi, gashi nayi ta kiransa bai É—aga wayar ba."
Bappa yace "Ko ina ya aje wayar to shi, ina yaje haka ayi ta kirashin baya É—aga wa".
nace "Wlh É—azu ne na ai keshi gidan Hajiya Firdausi matar ministar Bukar, akwai wasu kayan da tayi min tallar su wan da tayi odar su daga jamani, to sun yi min na tura da kuÉ—in to É—azu take faÉ—a min direban ta baya nan ko zan turo nawa direban ya amso min, shine na tura shi to gashi har yanzu bai dawo ba nayi ta kiran shi ma bai É—auka ba".
nayi maganar ina kuma É—aga wayar nakuma niman lambar sa.
Hajiya Firdausi matar ministan Abuja ne,
na yar da idan Allah yayi maka rufin asiri babu irin mutanen da bazaka gani ba ka kuma yi tarayya da suba,
ire-iren irin waÉ—an nan matan manya muna hulÉ—a da su sosai wasu sun girme min nesa ba kusa ba, wasu ma sun haife ni sun juya amma haka muke cuÉ—an ya da su.

Mikewa nayi da sauri ganin na kuma kiran sa har sau biyu nan ma bai É—aga ba, nace "Bappa bari naje kawai na É—auko su har yanzu bai É—aga wayar ba, kar suyi ta jira kasan mutumin ka yanzu haka yana kan musu rigimar zai dawo gida".
Bappa yace "Maza hanzarta kam ga guri nata kan tafiya".
da sauri nafita ina shiga side É—ina mayafi kawai na yafa dan dama a kimtse nake na É—au É—aya daga cikin makullen mota da suke cikin drower, da sauri na sauka na nufi parking space.
kana nashiga motar nayi wa motar key, tun kafin na karaso bakin get maigadi ya wangale min get yana fadin "Adawo lafiya".

Saboda yanayin gosulo na bata lokaci sosai a hanya dan har karfe É—aya ta cika har ta É—an gota, kafin nan na isa makarantar su.
tun kafin nakaraso get É—in makarantar, na zubawa kofar makarantar ido sosai dan ganin wasu yara rike a hannun wani mutum "Kamar su".
nafaÉ—a a file, nayi saurin isowa gurin, da mamaki nazuba musu ido ganin suÉ—en ne, yana rike da su suko sai washe baki suke,
shikuma mutumin yana ta tafiya da su yana nufar wata mota dake fake taÉ—an can gefe da get É—in makarantar, yayin da yake ta girgiza kai alamun yana jin surutun da suke ta zuba masa.
cikin hanzari na isa gefe nafaka cike da mamakin ganin nufar motar yake gadan-gadan na ɓalle marfin mota na fita da sauri, cikin hanzari nasoma bin bayansu ina faɗin
"Kai Naseem Nasmah!, malam ina zaka kaisu kuzo nan ku wuce mutafi".
mutumin bai juya ba sai su yaran ne suka juyo sai kuma suka kawar da kansu suka juya suka cigaba da tafiya suna cigaba da zuba masa surutu.
da sauri nasha gaban su gani yan da suka batsar kamar basu sanni ba nace
"Kai ina muku magana kuna jina ina zakuje kuwuce mutafi malam ina zaka kaisu?".
sai sannan mutumin yaÉ—an dukar da kansa dai-dai tsawon su kana yasoma magana
"Kunsan ta ne?." batare da yaÉ—ago ko ya dube ni ba ya ce "Ke a ina kika sannu bamu hanya mu wuce."
ido na waro cike da mamaki jin abun da yafaÉ—a tare da mamaita kalmar nasa
"Nasan su? nasan su fa kace, da alla malam ka sake su ina magana kana cigaba da tafiya da su."
gefe na ya gota batare da yace komai ba ya karasa jikin motar nima da sauri na rufa musu baya ina cigaba da faÉ—in
"Kai malam ina tambayar ka ina zaka kai su wai kana tambaya ta nasan su ne, ni zaka tambaye ni nasan sune, tambaya ta kake nasan su? dalla kasake min yara muwuce,ina ne zaka dasu kake nufar cikin mota da su?,
idan baka sake suba yanzu-yanzu zan kira maka hukuma anan."
baiyi magana ba sai mika hannun sa yayi yabuÉ—e marfin motar, yaÉ—au ko kwalin chocolate yaciro chocolate guda huÉ—u yabawa Nasmah biyu ya baiwa Naseem biyu kana yace
"To ga tsarabar ku kuci wannan yanzu, wannan kuma sai kusa a aljuhu."
yafaÉ—a yana cusa musu wani chocolate É—in cikin aljuhun wandon su.
da mamaki nake kallon su ganin yan da sukayi tamkar basu sanni ba, sai murna da tsalle suke suna faÉ—in
"Ye am bamu da yawa ye am bamu da yawa."
cikin takaici nakai hannu zan fisge chocolate É—in, da sauri mutumin ya janye su gefe kana yaÉ—ago kansa tare da zuba idanun sa cikin nawa,
wani irin dirrr naji a cikin jikina tamkar jan wutan lantar ki.......!

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.