Hamdah Littafi Na 3 Complete Hausa Novel
Reading file: HAMDAH part 3 Complete - Copy - Copy (1).txt
Chapter 16 of 33
Mommyn Twins ce
6
Yan da idanun sa yasarkafu cikin nawa haka babu zato ko sammani shi yasani shiga yanayin,
sai kuma na gyara tsayuwa ta da kyau, wani kallo yake bina da shi daga sama har kasa kana yace
"Na ɗauka kafin kiran hukuma ihu zaki yi ta yi kitara jama'a kice ga ɓarawo yazo satar yara, ke ba'a yi miki ihu ba har ke zaki wa wani ihu? karfe nawa ne yanzu wai wannan lokacin ne lokacin zuwa ɗaukar yara a makaranta,abar yara can kowa ya watse sai su kaɗai a cikin makaranta, sabo da baki san abun da kike yi ba an turaki ɗaukar su kin tsaya kin ɓata lokaci a hanya kina damuwar ki wata kila ma kinbi gidan kawayen ki kin gama sharholiyar ki,
kafin nan kika zo wai ke a hakan kinzo É—aukar su a makaranta, karfe nawa yanzu?. karfe nawa ne yanzu?!".
yakuma nanata tambayar, yana maganar ne ida nunsa a kaina da kuma alamun jaddada tambayon da yake jefa min,
gashi dai maganar cikin faɗa yake yin sa amma lamɓansa a hankali suke motsawa.
dogone yana da faffaÉ—ar kirji da zubin kakkarfan maza, fuskarsa na É—auke da É—an siririn saje wan da ya zagaye fuskar nasa har zuwa É—an gemun sa da bai wuce rabin kamu ba, irin gemun da gayu suke bare.
baza a kirasa da fari soll ba sanna kuma ba baki bane, hasken sa dai-dai.
kwantaccen gashin kansa baki sitif yasha gyara mai tsamtsi da tsulɓi sai wani yal-yal yake, sabo da iskar dake kaɗawa.
Kaina nakawar gefe tare da murguÉ—a baki nashi a wanne zai zauna yana wani masifa to ina ruwan shi ne ma.
É—an rutsunawa yayi yarage tsawon sa dai-dai tsawon yaran kana ya dubi ko wannen su yace
"Idan kunje gida kuce wa Mommyn ku kada a sake turo Aunty ku ta É—auko a School a rika ai ko me wayo yarika É—auko ku, wan da bazai barku kuyi ta shan wahala a nan ba, kunji ko?."
kai suka gyaÉ—a suna ta faman shan chocolate "Yauwa to kuje gida sai gobe zan kawo muku wani chocolate É—in, kada ku man ta in kunje gida kufaÉ—a wa Mommy kada a kuma turo wannan Aunty'n naku É—aukar ku a School a aiko mai wayo."
yayi maganar yana yi musu alama da suje in da nake yana binsu da murmushi,
ido na waro cikin masifa nabuÉ—i baki zanyi magana, dai-dai lokacin mota ta faka gefen mu, da mugun gudu, Yakubu direba yafito da sauri ya iso in da muka yana faÉ—in
"Ranki shi daÉ—e Hajiya wlh gosulo ne yatsare ni tun É—azu babu ta yan da zanbi na koma da baya na canza wata hanyar, gaba da baya motoci suka sani a tsakiya,jibi kumatu na har mari nasha dana nimi in juya dan na canza hanya, Hajiya a gafarce ni, wlh gosulo ne, ita kuma wayar sam na mance jiya da zankwanta bacci nacire ta a kara yau har gari yawaye kuma ban mai da kararta ba, Hajiya ayi hakuri da Allah."
maganar yake tamkar zai zuba guiwowin sa a kasa yana tafa bayan hannun sa a cikin É—aya tafin hannunsa alamun roko,
banyi magana sai juya wa nayi nanufi gun motar dana zo da ita, dan wannan mutumin yakure ɓata min rai.
Muryar Yakubu naji yana faÉ—in
"A'a ranka shidaÉ—e ina wuni barka da warhaka."
bude motar nayi nashige ciki batare da naji amsa gaisuwar da yake yi masa ba.
sai juyawar sa nagani yamatsa jikin motar sa yana kokarin bude marfin gidan baya, da sauri a ka buÉ—e gidan gaba wani ya fito cikin hanzari yarigasa kai hannu jikin kofar yabuÉ—e, kana yaÉ—an ja dabaya ya bashi hanya yashige motar ya mai da murfin ya rufe, kana shi kuma yakoma mazaunin direba yaja motar sukayi gaba.
Yakubu yakamo hannun su Naseem ya kawo su motar da nake yabuÉ—e gidan baya yasaka su, yace
"Hajiya bari na rufe wancan motar sai na kaiku gida a wannan na hau abun hawa na dawo na É—auki wanca É—in."
yajuya da sauri ya nufi in da motar da yazo da ita yake, fita nayi nakoma baya in da su Nasmah suke, yana kulle motar yadawo yashiga mazaunin direba yaja motar.
Munbar harabar makarantar da ɗan nisa kana na juyo na dubi su Nasmah dasuka gama kwaɓe jikin su da chocolate, ganin ina kallon su sai Nasmah ta miko min na hannuta tace
"Mommy akici". cikin masifa nace "Ai sai kun sha duka ba kun iya kwaÉ—ayi ba bakusan mutum ba kuka ma binsa, waya sani ma ko mai satar mutane ne yayi gaba da ku wata kila ma badun na iso da wuri ba da yanzu yayi gaba da ku, yaje yayi kuÉ—i da kanku,
idan kuka kara ganin mutum baku sanshi ba kuka bishi sai na zane ku, bare har ya baku abu ku karɓa sai na yanke hannun ku, yajaku mota zaiyi gaba da ku Allah ya so ku ai da kuna can Allah kaɗai yasan halin da kuke ciki, badun na iso da wuri ba, ɗan rainin hankali wai arika ai ko mai wayo yarika ɗaukar ku to ina ruwan sa ma daku tukun, mttsss." nayi maganar tare da jan tsaki.
baki Naseem yawashe cikin É—an sallen murna daga zaunen da yake yace
"Ai Daddy yace dai caya mana mota."
wani irin faɗuwar gaba naji da ya ambaci sunan Daddy da sauri nace "Kai Naseem waye kuma Daddy?." Nasmah ce ta caɓe zancen da faɗin
"Daddy daya bamu chocolate yace dai cayamin jigi haida mota da chocolate da yawa."
da karfi jin yan da zuciyata ke tafarfasa kai na ke sara min nace
"Kai ya isa! idan na kara jin kalmar wani Daddy a bakin ku sai na fasashi, ku bani chocolate É—in nan."
nafaɗa ina karɓe chocolate ɗin hannun su na zuge glaas ɗin motar nayi wurgi dashi.
maganar Yakubu najiyo wan da tashin hankalin da nashiga ciki yanzu sama-sama nake jiyo shi yana faÉ—i
"Hajiya ai shi wannan mutumin bamai satar yara bane mutumin kirki ne, shine Ahmad Tijjani Sabil mai kamfanonin nan wan da ake nuna shi agidajen talabijin, ai ko É—azu dana kawo su makaranta na tarar da motar kamfanin shi tana sauke kujeru dawasu kayan amfani na makaranta,ai kin sa kenan yana da yawan taimako kuma taimakon sa yafi yawa a inda yara suke."
"Ahmad Tijjani Sabil."
na mai-mai ta sunan a raina ina ta son tuna in da nasan sunan, sai a lokacin na tuna ɗazu da safe ake labarai a kansa a gidan tv anan nataɓa jin sunan.
Naseem yace "Ai nima Daddy yace dai taya min mota in tuka akaina."
cikin tsawa nace "Ban ce kada naji wani ya kara min maganar wani Daddy anan ba?, rufamin baki idan ka kara sai na fasa ma baki bari ka gani."
Yakubu kuwa ci gaba da zuba yake wan da ma gaba É—aya hankali na baya cikin motar da jikina gaba É—aya.
Muna komawa gida nakira *HAM'NAS* Store Complex nace a kawo min motar wasan yara guda biyu da wasu kayan wasa, batare da ɓata lokaci ba motar ShopRite ɗin ya iso, a ɗakin kayan wasan su aka jibge musu,
ihun murna suka sake ganin motocin cikin tsallen murna Naseem yace
"La iyin motan da Daddy yace dai taya mana babba."
da sauri na mike daga kan kujerar da nake zaune cikin É—akin kayan wasan su, hannayen su duka na riko nadawo na zauna, inajin zuciya ta na min mugun É—aci da kuna a duk san da naji sun furta kalmar Daddy a bakin su,
duban su nayi dukan su nace
"Kuna ji ko Naseem Nasmah?, shi wancan mutumin ba Daddy'n ku bane baku sanshi ba kuma ku bakuda Daddy, nice Mommy'n ku kuma nice Daddu'n ku bakuga na siya muku mota ba, idan kuka sake faÉ—ar Daddy bazan sake siya muku mota ba, kuma zan sa akwashi waÉ—an nan ma a tafi dasu, baku da Daddy nice Daddyn ku kunji ko?."
kai suka gyaÉ—a nace "To maza kuje kushiga motar ku." ai ko da sauri suka ruga in da motar suke suka shiga,
ina tare da su a É—akin sai zaga É—akin suke a cikin motar, suna dariya.
numfashi nasauke ganin suna cikin farinci sosai, Nasmah ta danna motar ta motar tatafi tsuu zata garu da jikin garu-bango da sauri na mike na tafi da gudu na taro ta, na ciro ta ciki ina faÉ—in
"To ya isa haka muje kuyi wanka kuci abinci sai kuma anjima zan sa afito muku da shi can tsakar gida kuyi wasan acan."
nayi waje da su.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.