Best / Popular Hausa Novels

Hamdah Littafi Na 3 Complete Hausa Novel

Reading file: HAMDAH part 3 Complete - Copy - Copy (1).txt

Chapter 10 of 33

Kasan cewar ina fashin sallah gado na haye nayi kwanciya ta cike da kewar ahalina daya baibaye ni lokaci guda...
washe gari da rana Bappa ya iso Abuja, nayi murna matuka da ganin sa har nake jin wani ɓari na kewar ahalina dana kwana dashi ya yaye da ganin sa.
isowar sa ba da jimawa ba muka bar cikin hotel É—in har da kayan mu.
wani katafaren gida mai matukar kyau da tsaruwa gida ne babba wan da girmansa yakai ya kawo tsarin sa gwanin burgewa, a bakin ramɓasheshen get ɗin gidan motar gaban mu ya tsaya, wan da mutanen da suka ɗauko mu a airport da wan da muka haɗu dasu a banki jiya dakuma wasu karin mutun biyu da yau nafara ganin su, sune acikin motar, motar da muke ciki ke biye da su, sukayi hon, abakin get ɗin ramɓasheshiyar gidan........★

Mommyn Twins ce

HMD
WASA FARIN GIRKI!!!✍🏻

_(Book 3)_

🅿️4

Asannu a ka wangale tamfatsetsen get É—in gidan, motar gaban mu yakusa ciki, a hankali direban dake jan mu ya danna hancin motar cikin gidan, a tsakiyar farfajiyar gidan duk suka faka motocin, a sannu na zuro kafafuna waje, "Ya ilahi ya littahi".
abun da na furta kenan lokacin da na dai-dai ta tsayuwa ta a cikin gidan, bin gidan nashiga yi da ido har ina wai ga gefe da gefe na.
gaba É—aya gidan da tsaruwar sa yatafi da ni, tsaruwan gidan yawuci misali komai an tsarashi a inda ya kamata yana ajiye a in da ya dace,gida ne babba mai É—auke da part har huÉ—u, daga gefe can gabar da gidan side ne guda É—aya sai kuma gefe ta hannun dama shima side ne guda sai kuma gefen hagu shima side É—aya, sai dai Æ´an madaidaita ne ba wasu manya ba.
daga tsakiyar gidan kuwa wani side ne na musamman wan da yazamo sauran side É—in sun sashi a tsakiya shi kam gini ne mai hawa É—aya babbane ya tsaru iya tsaruwa, daga saman side É—in har kasan sa yaji ado da gilasai masu ban mamaki an kawata shi tamkar a turai,daga kasa kuma an zagaye shi da wasu flaw's masu matukar kyau da É—aukar ido,
gaban side É—in wani shinfiÉ—aÉ—É—iyar swimming pool ne wan da aka kawatashi da rubber grass malaye har bakin kofar shiga side É—in.
gefe can kuma parking space ne É—auke da lafiyayyun motoci da suka kai guda uhu a cikin sa,
daga farin shiga gidan kuma gefe da É—akin mai gadi masallaci ne shin fiÉ—aÉ—e agun,
sai kuma É—akuna guda É—ai-É—ai a jere guda uku a gefe da masallacin ta can.

Maganar Bappa naji yana faÉ—in
"Muje ciki ko HAMDAH." da sauri nadawo daga duniyar kallon gidan dana tafi, da murmushi kan fuskarsa dan ganin yan da na tafi gaba É—aya na shagalta da kallon gidan.
na ce "To Bappa". a hankali nabi bayan su side É—in da ke gefe ta hannun dama muka nufa a hankali nake taka kafata ina cigaba da baza ido cikin gidan har muka isa cikin side É—in.
masha Allah É—an madaidaicin side É—in ya tsaru matuka.
side ne mai É—auke da 3 bedroom ko wanne da banÉ—aki a cikin sa, É—an madaidaicin parlour haÉ—e da dinning
da kitchen da komai da komai, an tsara komai yan da yakamata duk wani abun bukata an tanadar babu abun da babu.
É—akunan cikin parlour'n muka rika shiga wan da komai akwai hatta gadon É—akunan duk da shinfiÉ—ar su, sunsha lafiyayyun bedsheets.
bayan mungama zagaye cikin side É—in gaba É—aya, muka fita É—ayan side É—in dake gefen hagu muka shiga, shima kamar wancan side É—in yaji komai. kowa sai faÉ—in masha Allah yake, nidai kasa magana nayi sai binsu nake inata baiwa idona abinci sabo da gaba É—aya yanayin tsarin gidan yatafi dani.
daga nan É—aya side É—in dake can gabar da gidan muka nufa, shima tsaruwan sa da tsarin sa kamar sauran part biyun nan,
koda muka fito daga cikin part É—in baki na washe nadubi Bappa dake ta faÉ—in
"Kai komai yayi masha Allah komai fa yayi yadda yakamata". baki nakuma washewa ina faÉ—in "Kai wlh Bappa gidan nan Allah yayi kyau kaga fa nan irin wancan can ma irin wancan kai tsarin gidan yayi kyau komai iri É—aya, sai dai kawai kalolin kayan cikin sune daban-daban".
dariya Bappa yayi kana yace "Da gaske gidan yayi kyau ko?."
"Wlh kuwa Bappa." nafaÉ—a da sauri ina cigaba da washe baki, shima dariyar ya kuma yana girgiza kai kana muka rufawa mutanen baya in da suka nufi wannan kayatacce rantsatstsen babban side É—in nan dake a tsakiyar gidan wan da yazamana da sauran side É—in sun sashi a tsakiya.
a hankali muka isa bakin kofar da sauri É—aya daga cikin mutanen ya isa bakin kofar side É—in wan da yake na glass ya É—aura hannunsa gefe kan wasu madannai ya daddanna sai ga glass É—in yafara bada sauti É—an baya yaja kana ya dubeni yace
"Bismillah Madam É—an zo ki tsaya a nan."
ya nuna min kan step É—in da yasauka akai wan da saika haura kansu kafin ka isa bakin kofar,step ne guda uku, nuna kai na nayi alamar ni?. yace "Eh." a hankali na matso na haura kan step É—in, daga in da yake yamika hannunsa yakuma danna wasu lambobin kana yace na É—aura hannuna kan nan yanuna min wani É—an zagaye da hoton yatsu, a sannu nakai hannuna na dai-dai ta yatsuna kan zanen yastun, nan yafara bada sauri É—it-É—it sai kuma yakuma danna wata lambar data fito mai alamar Okay. nan take kofar tazuge gefe ai ko da sauri na É—aga hannuna.
ya juyo yana duba na kana yace
"Madam wannan kofar special ne mai amfani da zanen yatsune mutum É—aya ke amfani da shi, sai kuma wancan". yanuna wata kofar dake gefe ya isa gurin muma mukabi bayan sa,ni dai cikin rashin fahimta nake jin sa, yace
"Shi wannan common door ne kamar yanda aka sani kowa zai iya amfani da shi."
ya murÉ—a handle É—in kofar yabuÉ—e muka shiga ciki.
sai gamu mun bayyana cikin wata katafaren parlour ya ilahi ya lilahi, har bansan san da na furta "Kai! amma wannan duk yafisu kyau!".
nayi maganar cikin hakikance gaskiyar abun da ke cikin zuciya ta wan da maganar fitowa kawai tayi,
Bappa ko karamar dariya yayi tare da jijjiga kai.
suma sauran dariya suka bini da shi, nan muka fara kusawa cikin katafaren parlour'n, baki da hanci gaba É—aya na buÉ—e wajen kallon katafare kayataccen parlour'n, faÉ—an tsaruwar sa da misalta tsarin parlour'n ma ba zai misaltuba, yaji kayan alatu da more rayuwar duniya tsaruwan sa ya zarce sauran side É—in da muka shiga babu haÉ—i ko kaÉ—an.
bedroom É—in dake cikin parlour'n muka rika shiga É—aya bayan É—aya, bedroom ne zafafa har guda huÉ—u masu É—auke da tsalatsalan bathroom,
daga gefe da parlour'n kuwa katon dinning area ne sai kitchen babba a gefe.
sama muka hauwa wan da shi kanshi step É—in haurawan sama abun kallo ne domin kuwa shima an kawatashi na musamman.
wow masha Allah shima tsarin saman kamar kasan sai dai banbancin kalolin kayan dake cikin su, kalar kujeru da labulayen bedroom and parlour kasan white and ash da É—an ratsin lemon-green. saman shima 4 bedroom ne a cikin sa kalan kayan bedroom and parlour'n kuma white and sky-blu.
Antsara komai yadda yakamata sai tashi da sassanyan kamshi mai haÉ—e da kamshin sababbin kaya yake.
kai gidan ya haÉ—u fa nidai bakina yakasa rufuwa wajen kallon tsaruwan gidan, bayan mun gama zaga lungu da sako na saman muka gangaro kasa anan muka yada zangon mu cikin parlour'n kasa.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.