Hamdah Littafi Na 3 Complete Hausa Novel
Reading file: HAMDAH part 3 Complete - Copy - Copy (1).txt
Chapter 20 of 33
Mommyn Twins ce
8
Nan nake shai da masa bukata ta nakan canza su Naseem makaranta.
shugaban makarantar nasu yace "To ba bubu da muwa amma dan Allah muna so musan dalilin da yasa ake son sauya musu makarantar ko kuma makarantar tamu babu koyo ne yan da ya kamata?".
nace "Ko kaÉ—an ba haka bane ba kawai dai ina so ne na canza musu makarantar ba wai kodun rashin koyo ba, ai ba za'a ce makarantar ku babu koyo ba, yara suna fahimta sosai, kawai dai yaÉ—an yi nisa ne."
yace "To in dai kuwa haka ne to dan Allah kada a ciresu a makarantar gaba É—aya, akwai É—aya makarantar mu dake wata unguwa mafi kusa da ku in dai kina so sai a maida su can É—in, ranar Monday idan suka zo sai ayi transfer É—in su can É—in."
shiru na É—an yi cike da nazarin maganar sa, sai kuma nace
"To shi kenan a mai dasu can É—in."
har munyi sallama zan kashe wayar yayi saurin cewa
"Dan Allah Madam a daure a kawo su sai a kaisu wancan makarantar, idan akace an cire su gaba É—aya kokon to zai shiga zukatan iyayen yara zasuyi zaton ko wani matsala ce mai girma aka samu cikin makarantar, tun da bawai barin garin zakuyi ba,
zamu iya samun dakilewar customer, adai duba lamarin da kyau Hajiya."
"Babu damuwa in sha Allah za'a kawo su sai a kai su wan can É—in."
godiya yashiga yi min kana mukayi sallama na kashe wayar.
Ina sauke wayar number Ukhtee na kira yayi ta ringing ba'a É—aga ba,nakuma mai da kiran shima har yakusa yanke wa kafin ta É—aga, da sallama.
na amsa cikin harshen larabci nace
"Oh kai Ukhtee ina kika aje wayar haka ina ta kiranki baki É—aga ba?, ko yanga kike min an ce miki ni saurayin kine."
dariya tayi tare da faÉ—in
"Saurayi kuma haba dai kedai wayar tana bedroom ne nikuma ina parlour, nama shigo É—aukar abune cikin É—akin naji wayar tana ring, ai da haka zaki ta kira ma ban sani ba, ya kuke ina yarana suke?."
"Lafiya lau duk muna lafiya, yaran ki suna can gurin Bappa sunki biyo ni suna can suna damin sa da surutu, ni nagaji da hirar ne nadawo side É—ina naÉ—an huta suna can."
larabcin nake ina ta haryaÉ—a shi.
dariya tayi jin yan da nake ta kwamusa larabcin, tace
"Oh kin dawo kasar ku yaren kasar ku yana so ya korar miki da yaren kasar muko?."
nima dariyar nayi tare da faÉ—in
"Ashe kin gane inata yi da kyar amma fa su Naseem sunanan da shi a bakin su domin makarantar isilamiyyar su larabci zalla ake, shi yasa yake nan zaune a bakin su."
tace "Kai naji daɗi wlh gara ai su zauna da larabcin a bakin su, ke kizauna da yaren kasar ku tun da shi kika zaɓa."
nace "To ya zanyi mahaifa ta dole naso yare na ke ma ba kina son yaren kiba?."
tace "Sosai ma."
"Oh to shine nima baki so naso nawa yaren."
mukayi dariya. hira kukayi tayi sosai da Ukhtee wani maganar idan nayi ita zata gyara min shi dan larabcin bai gama nuna baki na ba.
sai can da jinawa mukayi sallama.
Yau Monday kamar yan da nasa ba na rako su Nasmah gun mota, Yakubu dake goge motar yayi saurin buÉ—e motar nasaka su ciki,bayani na yiwa yakubu kamar yan da mukayi da shugaban makarantar su idan sun je za'a haÉ—a su da wani domin yayi musu jagora zuwa É—aya makarantar.
ina tsaye ina É—aga musu hannu har suka fita...
Kai tsaye Yakubu yaÉ—au hanyar makarantar, kamar koda yaushe hira yake da yaran yanata washewa da dariya kamar yan da suma suke ta washe baki.
suna isa bakin get É—in makarantar yayi parking yafito, kana ya buÉ—e musu suka fito, suna fita suka shige cikin makarantar direct office suka nufa daga nan aka haÉ—a su da wani malami da zai kai su É—aya makarantar, suka fito tare.
suna fita bakin get É—in school É—in,
wata lafiyayyi zazzafar mota tayi parking a gefe, tun kan motar ta kakarasa parking Naseem yafara murna yana faÉ—in
"Laa ga Daddy yazo laa ga Daddy yazo."
Nasmah ma kuwa ihun murna ta sake tare da sa gudu sukayi gurin motar.
da sauri ya buÉ—e motar ya fito yaware hannayen sa ai ko da gudu suka shige jikin sa ya rungume su, duk suka saki dariya har dashi, kana ya mike yashiga É—aga su yana cillasu sama sai kya-kya ta dariya suke.
sai da yayi wa kowannen su haka har sau uku kana yadire su kasa,
Yakubu ya karaso in da suke yana washe baki da faÉ—in
"Ranka shi daÉ—i barka da war haka."
amsa wa yayi fuska a sake sai dai gaba É—aya hankalin sa na kan su Nasnah da suke ta zuba masa surutu.
shima wannan malamin da aka haÉ—o su da shi ya karaso yana faÉ—in
"Barka da zuwa yellaɓoi."
yace "Yau wa, yaya ji da É—aliban?."
malamin yawashe baki tare da faÉ—in
"Muna kai kam."
yace "Masha Allah."
malamin ne ya dubi yakubu da kuma yaran yace
"To muje ko."
yayi maganar yana duban motar su.
sai a lokacin Ahmad ya É—ago da kallon sa kan yaran yadawo da shi kan su Yakubu kana yace
"Ina kuma za'a je ba makaranta za'a shiga ba?".
yayi maganar yana shafa kan su Naseem.
malamin yace "A'a zamu tafi da sune É—aya makarantar mu."
duban sa Ahmad ya kuma da alamun tabbayoyi É—auke a fuskar sa,
kana yace "Wacce makarantar kuma?."
yace "ÆŠaya daga cikin makarantar mu ne za'a mai da su."
da fuskantar mamaki Ahmad yace
"Har sun gama wannan makarantar ne da za'a tura su wata makarantar daban?."
kai malamin ya girgiza tare da faÉ—in
"A'a ai za'a sauya musu makarantar ne anyi musu transfer can ne."
É—an shiru Ahmad yayi kana yace
"Malam É—in yana ciki?."
kai malamin ya gyaÉ—a tare da faÉ—in
"Eh yana ciki." yace
"Okay to muna zuwa." yafaÉ—a tare da gyara rukon Naseem da Nasmah a kowani hannun sa guda, ya janyo su suka shige cikin makarantar.
Malamin ya dubi Yakubu dake ta washe baki yace
"Wai nikam da ma Æ´aÆ´an Ahmad Tijjaji Sabil ne kake kawowa makaranta?."
Yakubu ya daÉ—a washe baki yace "A'a Æ´aÆ´an me *HAM'NAS* Company ne fa."
"Au Æ´aÆ´an mai *HAM'NAS* Company ne to shi Ahmad Sabil dangin su ne? lallai Allah mai yin yan da yaso yahaÉ—a family guda da tarin dukiya."
Yakubu yace "Eh Æ´an uwa ne."
yafaÉ—i hakan ne kawai dan bashi da amsar bashi, dan shi kansa bai isa yace suna da dangan taka ko basu da shi ba, a matsayin sa na mai ai kin gidan ba lallai dole yasan dan gin gidan ba, san nan kuma baya so ya disga kan sa gaban malamin, ko ba komai shi ma za'a rika yi masa kallon wani...
suna nan tsaye
zuwa can Ahmad yafito shi kaÉ—ai batare da yaran ba.
ido suka zuba masa ganin yafito shi kaÉ—ai, yakaraso in da suke, duban malamin yayi tare da faÉ—in
"Ka koma kacigaba da koyar da É—aliban ka, kai kuma ka koma gida ka dawo da wuri ka É—au ke su."
yakara she maganar da duban Yakubu.
Yakubu yace
"Ranka shi daÉ—e hajiya tace na tsaya sai mun kai su kafin na komo gida."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.