Hamdah Littafi Na 3 Complete Hausa Novel
Reading file: HAMDAH part 3 Complete - Copy - Copy (1).txt
Chapter 21 of 33
Yace "Kar ka damu kaje ka abin ka."
yace To. yashiga mota in da tuni malamin ma yakoma cikin makarantar.
shiko Ahmad a hankali ya isa jikin motar sa ya shige ciki...
Da misalin karfe 12
a hankali na mike na shige bayi wanka nayi haÉ—e da É—auro al'wala nafito,nashirya cikin wani doguwar rigar atamfa pauda da man lip kawai na goga sai turare dana fesa a jikina,
a hankali na isa jikin window labulen window'n naÉ—an janye shi gefe tare da zuge glass.
ido na kurawa furannin da suke ta kaÉ—a wa gwanin ban shawa,
idanuna na sauke can bakin get jin karar buÉ—e get É—in, da murmushi nake kallon kofar,
dan nasan su Naseem ne suka dawo, É—an gimtse annurin fuska ta nayi ganin ba motar kai su makaranta bane wata motar ne daban ta shigo.
a sannu motar ta isa ta gyara parking a gefen farfajiyar gidan,
an É—au tsawon minti 10 kafin aka buÉ—e motar,
ido na waro cikin tsananin mamaki da shiga shoc ganin wan da yafito daga cikin motar, cikin matukar kufula nake kallon sa yayin da yazaga É—aya gefen ya buÉ—e, sai ganin Naseem da Nasmah nayi sun fito daga cikin motar suna ta washe ba ki.
"What! me nake gani haka, yaran da nasa a canza musu makaranta domin sa wai bin su yakuma yi?."
cikin matukar ɓacin rai nasaki labulen da sauri na juya nafita a ɗakin na nufi kasa,
da sauri na ke sauka har ina haÉ—a step cikin hanzari nakarasa sauka nayi waje da sauri.
Suna tsate jikin mota sai zuba masa surutu suke shiko sai binsu da murmushi mai haÉ—e da dariya yake,
tun kan na karaso in da suke nashiga faÉ—in
"Kai malam wai meye hakan ne, wai meye gamin ka da yaran nan ne kam?!."
dai-dai lokacin na iso in da suke, kugu na rike cikin masifa nacigaba da faÉ—in
"Meye da lilin ka na wani shishige musu da kake kana ta wani cusa musu
wani ra'ayi meye nufin ka da su?."
maganar nake a tsai-tsaiye kuma cikin É—aga murya cikin masifa nakuma faÉ—in
"Bana bukatar wani ya raɓe su da manufa irin naka kagane ko malam?."
tun da na fara maganar ido kawai ya zuba min batare da yace komai ba, idanun sa kan lip É—ina, a sannu yaÉ—an yi baya ya jin gina bayan sa jikin mota hannayen sa ya sarkafe a kirjin sa, harshen sa yaÉ—an zuro waje yalashi pink lip É—in sa,
har lokacin fuskar sa na É—auke da murmushi wan da dimple suka daÉ—a kawata annurin fuskar sa.
cikin kuma É—aga murya na dubi su Naseem nace
"Idan baku wuce kun shiga ciki ba na rantse sai na ɓaɓɓala yaro anan gurin ku wuce mutafi nace!."
nafaÉ—a ina nuna musu hanya.
Nasmah tace "Mommy ja mu jo."
ido na waro wato ma na jira su kenan sai sun gama abun da suke.
shiko wani murmuahi yakuma sakewa.
tsayuwar sa ya gyara tare da duban yaran kana ya mai da duban sa kai na sannan yafara magana
"Zaki ɓalla su?."
ya faÉ—a tare da kuma sakin wani murmushi kana ya É—an sun kuya yarage tsawon sa dai-dai tsawon yaran ya dubi ko wannen su yace
"Kuje ciki ayi muku wanka kuci abinci ku kwanta ku huta kuyi bacci idan kun tashi kuyi karatu gobe zan tambaye ku karan tun da kukayi kun ji ko?."
kai suka gyaÉ—a masa suna faÉ—in
"Tom." yace "Yauwa to maza a je ciki."
Naseem yace "Daddy dakajo anjima?."
kai yagyaÉ—a yana mai cigaba da wannan murmishi wan da kamar da shi aka gina fuskar sa yace
"Sosai ma zan zo mana."
Cikin hatsala haɗe da ɓacin ran ganin yau ma kamar na ranar da na same su tare da shi a kofar makarantar su, ina nayi musu magana sukayi kamar basu san ni ba,
sai shi da suke ta biye masa suna bashi amsar duk abun da yace musu,
bugu da karin bacin raina kiransa da sunan dana hane su a gabana.
cikin tsawa nace
"Kai Naseem me nace maka waye Daddy'n ka wato bakaji ba ko, ban ce muku kada ku kuma cewa wani Daddy ba, wato duk maganar da nake muku aban za bakwa ji ko, idan naji kasake cewa wani Daddy sai na fasa maka baki,wuce mutafi nace!."
ko da nake masifar harlau idanunsa a kai na, sai ya saki wani murmushin gefen baki yayin da gefen kumatun sa na dama ya lotsa, har kuma lokacin yana rike da kafaÉ—ar su.
a sannu yaÉ—an sun kuyo yadubi Naseem kana yakuma dubi Nasmah kana yakuma sakin wani murmushin sannan yace
"Naseem Nasmah mene ne ma suna na?."
suka haÉ—a baki wajen cewa "Daddy Daddy tunan ka."
yace "Kai yaran nan to Allah yayi muku albar ka, to maza ku tafi ciki ayi muku wanka kuci abinci maza kuje."
ya faÉ—a yana tura keyar su.
ai ko da gudu suka yi ciki suna dariya, ganin rainin wayon nasu da yawa yake wato umurnin sa ma zasubi ba nawa ba. nadube shi tare da rike kugu nace
"Kai malam kana ji ko, kada ka sake zuwa in da yara na suke kada ka sake kasake zuwa in da suke, kada ka sake cusa musu ra'ayin cewa wai kai Daddy'n su ne, kai ba Daddy'n su bane basuma san ka ba, ni ban gayyaci wani acikin lamarin Æ´aÆ´ana ba,karabu da harkar yara na idan kuma ba haka ba wlh zan É—auki tsatstsauran mataki a kanka, kada ka kuskura ka sake zuwa in da yara na suke, kada ka sake yi musu karya kan abun da ba haka bane, bana kara kan haka dan Æ´aÆ´ana nice kaÉ—ai uwan su kuma uban su,
dan Allah malam kada ka sake cusawa Æ´aÆ´ana wannan gurguwar ra'ayin, ka gane ko?!."
na karashe maganar da nuna masa yatsa haÉ—e da murguÉ—a masa baki, na juya a hatsale ganin duk maganar da nake madadin ya shiga taitayin sa sai ma daÉ—a sakin wannan murmushin nashi yake.
tafiya na soma cikin fushi dan nalashi takwabin yau sai na zane yaran nan tun da har ni zasu gwadan wani yafi ni muhimmanci agurin su har zasu ji maganar sa akan nawa.
sai jin maganar sa nayi daf dani
"Kece uwan su kuma uban su to ya akayi kenan hakan ta faru, ke kika ba kan ki cikin kenan,faÉ—a min da ma a she mace tana bawa kanta ciki da kanta, dama a she uwa tana bawa kanta ciki ita kaÉ—ai batare da uba ba??."
wani irin juyi nayi jin sautin sa kusa dani batare da zato ko sammani ba, maganar yashige ni tamkar shigar shoc cikin jini na, wani irin mugun kallo na watsa masa tare da jan dogon tsaki, najuya na nufi kofar side É—ina da sauri...
shiko bayana yabi da wannan murmushin kana ya juya yashige motar sa yaja yabar gidan.
Koda na shiga banbi takan su Naseem ba dan nasan koda na yi musu hukuncin danayi niyyar ma bashi zai sa su dai na abun da na hanasun ba,
sai kawai nashige É—aki nazube bakin gado, kamar an zabure ni kuma na mike na isa gaban mirror in da wayoyi na suke ajiye, number Yakubu na kira, nafara zazzage masa masifa
"Wato Yakubu dana ce kaje ka É—auko su shine bakaje ba kabar wannan É—an rainin wayon mutumin wai Ahmad yake ko wa yaje ya É—au ko su ko?,
idan ka gaji ne kafaÉ—a sai a sallame ka."
da sauri yatari numfashi na da faÉ—in
"Dan Allah Hajiya kiyi hakuri wlh yanzu haka ina hanyar dadowa ne ina ma kokarin kiran ki kenan sanar miki sai ga kiran ki, naje makarantar aka ce min yazo ya É—auke su, ai Hajiya baki sani bama É—azu da zamu kai su sabon makarantar yazo ya mai da su cikin makarantar yace mutafi mu barsu anan."
ido na waro da ɗinbin mamaki mai haɗe da mugun ɓacin rai,
ban san san da na dakawa Yakubu tsawa ba nace
"Dalla malam ya isa ni da kai na nace ayi abu kan Æ´aÆ´ana sannan wani can daban yazo yace ba hakaba kai kuma ka yarda, umurnin sa kabi kenan? ok to ka wuce gidan sa daga nan kaje can yacigaba da baka umurnin!."
nakashe wayar rai ɓace,
"Lallai ma wato ashe ma ba'a kai su makarantar ba shike nan ya hana ko me?."
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.