Best / Popular Hausa Novels

Hamdah Littafi Na 3 Complete Hausa Novel

Reading file: HAMDAH part 3 Complete - Copy - Copy (1).txt

Chapter 12 of 33

Mun zaga gidan man na yaba da tsarin sa kwarai yana rufe ne ba'a fara aiki da shi ba,
daganan kuma wasu gidajen man mukaje har guda uku duk masu É—auke da ( *HAM'NAS Co Petroleum Nigeria LIMITED* ) daga nan muka kuma zuwa asibitoci suma masu É—auke da sunan ( *HAM'NAS International HOSPITAL* )
suma asibitotin guda uku a gurare daban da ban manyan gaske, sai dai duk a kulle suke anzuba kayan aiki komai da komai acikin su sai dai ba'a fara ai ki da suba.
daganan kuma makarantu da kamfanoni muka nufa duk kanin su da tambarin *HAM'NAS* International School Of Science's And Technology, *HAM'NAS Store Complex's su ma duk ba'a fara ai ki da suba. sai kuna masallatai manya guda uku anzuba komai a ciki suma ba'a fara amfani da su ba.

Zuwa yanzu kam nidai komai ganin sa nake kamar almara nafara yarda kan cewa komai da gaske ne, sai yamma muka dawo gida, mun dawo a gajiye suke faÉ—a min cewa muhuta nan da kwana uku sai mu fara tafiya guraren kaddarorin dasuke garurruwa nesa da nan, nace to Allah ya kaimu..

Damin Bappa narikayi nace nidai yasa su Inna wuro da Fatu suzo kafin mutafi nan da kwanan ukun,
yace a'a abarsu tukun ba yanzu ba,
haka dai dole yasa direba yaje ya taho da su dan na tubure a la dole sai an kawo su, ko da direba zaije É—auko su nace yace musu kada suzo da komai, dan cikin side É—in dana matsawa Bappa sai ya zabi É—aya daga cikin side É—in gidan wan da zasu zauna ciki, akwai kaya komai na bukata sai suzo suyi amfani dashi abun da babu sai a karo musu kamar kayan sawa shi da babu a sauran side É—in.
hakan kuwa a kayi ranar da su Inna wuro sukazo murna kamar nayi yaya, suma agefen su ba'a magana, na rungume Fatu inata murna, tarika É—aukar su Naseem cikin tsananin farincikin kuma ganin su.
a ranar ma Uncle Mahmoud yazo har da matarsa da yaran su, dan su anan Abuja suke gun ai kin sa.
nan muka wuni da su wunin ranar yayi min daɗi matuka, sai narika jin su tamkar wani ɓari ga ahalina,
ganin su yaÉ—an rage min kewa da begen family na.

Yau asabar hakan yayi dai-dai da kwanaki ukun da zamuyi tafiyar, da sassafe muka É—auki hanyar suwa Kano, motoci biyu muka tafi dasu motar mu ni da Naseem da Nasmah dakuma Bappa,sai É—aya daga cikin jagororin ke zaune a gefen direba, É—aya motar kuma mutane huÉ—u ne a cikin ta suna gaba muna biye da su.
mun isa cikin garin Kano da misalin ƙarfe 12:30pm sai da muka tsaya mukayi sallah kafin muka nufi inda zamu,
gidajen mai muka fara ziyarta kafin asibitoti dakuma kamfanoni.
bamufi awa biyu a cikin Kano ba muka É—au hanyar Kaduna a kaduna muka kwana, washegari muka nausa Katsina.

Sati biyu muka ɗauka muna yawon zuwa garuruwa ganin in da aka zuba ayyuka, masha Allah duk garin da mukaje daga gwamnatin su muke samun tarba da karɓa mai muhimmanci, daga karshe muka biyo garin Bauchi,
lokacin da motar mu tashiga cikin Bauchi state, tashin hankalin da nashiga bazai misaltuba, wani irin tashin tsikar jiki da sanyi mai matukar shiga jiki su suka ziyarce ni, wani irin ɓari da kakkarwa nasomayi lokaci guda har hakorana suna garuwa da juna, sai kuma wani masifaffen zufa yashiga keto min, hankalin Bappa yayi musifar tashi ganin halin dana shiga lokaci guda,
cikin tsananin tashin hankali jin bakon yanayin daya ziyarce ni lokaci guda tamkar ƙwaƙwalwa ta zata fashe jin wani irin abu mai matukar nauyi da kara ya dankare min a kai, kunnuwa na tamkar ana busa wani irin busa mai matukar kara da firgitar wa, da karfi nakai hannuna na toshe kunnuwana cikin matukar jin azabar dake kokarin tarwasa min rayuwa nashiga faɗin
"Bappa mu tafi Bappa kace musu kada mu tsaya Bappa mutafi wayyo Allah na".
kaina nashiga juyawa da karfi jin yan da zabar da nakeji na karuwa nan take nanimi tunani na na rasa.
cikin É—aga murya ganin numfashi nakokarin barin jikina Bappa yace
"Direba yi hanzari mufita a cikin garin nan yi maza da sauri!".
gudu direba ya kara bai tsaya ba sai da muka fita a garin, gabaki É—aya, hankalin kowa yayi masifar tashi ganin halin da nake ciki,
Bappa ko karatun Kur'ani yasoma yanayi yana tofa min, hankali na bai dawo jikina ba har sai da mukabar eriya'n Bauchi gaba É—aya.
A hankali narikajin abun da nake jin na sassauta har ya washe.
numfashi Bappa ya sauke tare da saida karatun da yake, kai ya girgiza tare da faÉ—in
"Kai mutum abin tsoro ne Allah kashiga sakanin nagari da mugu akwai hisabi ranan gobe kiyama".
yadubeni da kula yace
"Sannu ko HAMDAH".
kai na girgiza yace "Me kike ji yanzu?". nuna masa kaina nayi da hannu dan shi ke yimin ciwo sosai.
"Zai bari insha Allahu".
yayi maganar tare da buÉ—e tafukan hannunsa yasoma karanto Suratul (Khafi) aya goma na farkon surar haÉ—e da ayatul Qursi'yu ya tofa kana yashafamin a kan. cikin yar da da buwayar Allah naji ciwon kan na sauka.

Ko da muka shiga jahar plateau state, farkon shiga garin Jos NARKUTA. wasu zafafan kwalla ne suka gangaro kan fuskata tuno da Mama mai awara, da sauri nayi yinkurin yin magana a tsaya amma abun mamaki sai naji harshe na yayi min mugun nauyi gaba É—aya jikina ya sake babu alamar karfi tattare da ni, abun da na fahimta tun lokacin da nayiwa Bappa maga shigar mu Bauchi zan kuma wata maganar naji na kasa, har kuma yanzu ina jin yanayin...
da daddare muka shiga Abuja, da kyar da taimakon Bappa na iya sauka cikin mota muka shiga ciki.
Inna wuro ta firgita da ganin yanayi na, ko da Bappa yayi mata bayanin abun da ya faru, hankalin ta yayi masifar tashi, yace ta taimaka min naje na kwanta, shikuma yafita can ya dawo da ɗan karamin ƙwarya da magani a ciki yabawa Inna wuro yace
"Kibata tasha babu komai insha Allah zata ware garin ne kwatakwata basa so tashiga sai dai tayi nesa da shi sun mance cewa Allah baya bacci".
Inna wuro tace "Ikon Allah wannan irin shiga sakani sai sakayyar Ubangiji".
ko da Inna wuro ta bani maganin inasha bada jimawaba bacci yaÉ—auke ni, ranar a kaina ta kwana, Fatu kuma tana tare da su Naseem a É—aya É—akin dake kusa da nawa.
washegari kuwa cikin yarda da buwayar Allah namike garau...
muna tare a parlour ni Inna wuro Fatu dan har lokacin basu koma side É—in suba, labarin garuruwan da mukajejje narika basu ina washe baki da faÉ—in
"Allah Inna wuro bakuga abubuwan yan da sukayi kyau ba kai har da garin da ban taɓa zuwa ba".
nayi maganar ina washe baki, dariya suka rika min, nan
Bappa yashigo ganin jikina shima yazauna mukayi ta hira....

bayan kwana biyu

Mutane biyu daga cikin jagororin nan suka zo su da wasu mata guda biyar sukace na zama a cikin su wan da zasu rika yi min ai ki,
mata ne irin wan da suke karkashin paundation, irin waɗan da mazajensu suka sake su dakuma wan da mazajensu suka rasu, akan ɗauke su ai ki irin gidajen masu kuɗi ɗin nan, a cikin su na zaɓi guda uku dasukafi kwanciya min a rai, kana nace zan gwada ai ki da su.
É—aya na É—auke ta a matsayin mai kula da su Nasmah dakuma kula da tsaftar side É—in,
na biyun kuma mai girka abibci, sai kuma É—ayar na turawasu Inna wuro ita zata rika kula da tsaftar side É—in su dakuma girkin su.
nan suka kuma gabatar min da masu maza wan da nazo nasame su a cikin gidan, direba sai mai baiwa fulawa ruwa shi zai rika wanke mota, sai mai gadi dakuma mai kula da tsaftar farfajiyar gidan gaba É—aya.
mun zauna da su na É—an wani lokaci na fahimci mutane ne masu kirki da rukon amana.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.