Hamdah Littafi Na 3 Complete Hausa Novel
Reading file: HAMDAH part 3 Complete - Copy - Copy (1).txt
Chapter 14 of 33
A cikin satin akayi musu komai da komai nashiga makaranta, sai dai wata makarantar daban badaga cikin nawa ba, dan *HAM'NAS* International School Of Science Of Technology. suna da nisa saka nin mu, duk da dai shima makarantar da aka sasun yana da É—an nisa sai dai baikai su nisa ba,
Islamiyar da a kasasu kuma anan unguwar tamu yake.
ranar da zasu fara zuwa kuwa zo kaga murna wajen su, da misalin karfe 7 na safiya Talatu taga ma shirya su tsaf, Zulai kuma ta shirya musu lafiyayyen breakfast É—in su.
ina rike da hannun su muka fito in da Talatu ke biye da mu rike da school bag É—in su da baske, parking lot muka nufa, tun kan mukaraso Yakubu direba dake goge mota yayi hanzarin buÉ—e marfin motar, cike da ladabi yaÉ—an duka yana faÉ—in
"Barka da safiya Hajiya."
"Yauwa barka." nafaÉ—a cikin É—an jin nauyin yan da suke yimin idan zasu gaida ni, duk kanin ma'aikatan gidan sun girme min nesa ba kusa ba wasu ma sun haife ni sun juya,nakan ji nauyi a duk san da sukayi min irin wannan gaisuwar.
Nasmah naÉ—aga nasaka ta cikin motar, Naseem kam cemin yayi shi da kan sa zai shi, Talatu tayi dariya tana saka musu school bag É—in cikin mota tace
"Naseem iyayen rigima kai bazaka bari a saka ka ba da kan ka zaka shi ka girma ashe".
kai ya gyaÉ—a yana gyara zama tare da faÉ—in
"Eh nagima da kaina naciga."
tace "To babban zance ke kuma Nasmah yaushe zaki girma?". Nasmah ta cuno É—an karamin bakin ta gaba tace "Gobe dan gima ai".
murmushi nayi tare da shafa gefen suskar ta nace
"Au ke sai gobe zakiyi girman naki?". kai ta gyaÉ—a tana murmushi, kansu na shafa dukansu nace
"To sai an dawo ayi karatu sosai kunji".
sukace to. direba yaja mota ina É—aga musu hannu suma suna daga min
mai gadi yawangale get suka fita..
Kwana uku kullum cikin ɗoki suke zuwa makarantar ranar na huɗu kuwa ɗoki tafara kare wa, ina kwance sai ga Nasmah ta shigo da gudu ɗaure da ɗan karamin towel ɗin wankan su tahaye gado ta ɓoye a baya na tana faɗin
"Ni bajan je school in ba."
zanyi magana sai ga Naseem shima da wandon uniform ajikin sa babu riga, sai muryar Talatu daga bakin kofa tana faÉ—in
"Kai Naseem kazo nakarasa saka maka kayan".
mikewa nayi zaune ina faÉ—in
"A'a yaya ne tsaya mana". ai kan kace me shima ya É—ale gadon
cikin cuno baki gaba Nasmah ta daɗa laɓewa jikina tana faɗin
"Ni Mommy bajan je School in ba".
ido na waro ina duban Naseem shima da yake faÉ—in
"Nima bayan jeba".
kai na langwaɓar gefe nace
"Oh yanzu wa School É—in kuke gudu ne, bazaku je ba kuma, yaushe ne kuka fara zuwan da har zaku fara fashin sa?, kuna ji ko kuzo ku je makaranta".
kafaÉ—a suka make alamar o'o, rungumo su nayi dukan su ajikina ina murmushi kana nace
"Ina kallon da mukayi jiyan naaan na sojojin naaan, to waye meson zama irin su a cikin ku?".
da sauri Naseem ya mike a jikina yana washe baki tare da nuna kanshi yana faÉ—in
"Nine-nine". "Yau wa to har in kana son kazama soja to ko sai kaje makaranta, kaje makaranta kayi karatu sosai daga nan zaka zamo soja, in kuma baka so to kazauna kawai a gida ina baka so kazama sojan zauna abin ka kada kaje School".
kai yashiga girgizawa da sauri yace "A'a a'a Mommy ina so to danje School in nine toja".
"Yauwa to kada ka sake cewa bazakaje School ba dan soja baya fashin School, Nasmah ta kefa? baki son zama sojan ne?."
da sauri tace "Ina to." nace "To ke bama soja zaki zama ba Dr Nasmah ce a nan, ina kina so kizamo likita kirika yiwa mutane allura."
ta gyada kanta da sauri, nace "Yauwa kinga in kikaje makaranta kikayi karatu da yawa to zaki rika yiwa mutane allura".
kuma gyaÉ—a min kai tayi da sauri tun kan in karasa maganar, murmushi nayi ina shafa kansu.
kallon kofa nayi tare da É—aga murya nace
"Talatu kawo musu uniform É—in su saka".
daga can bakin kofar in da take tsaye ta waje ta amsa da to kana taturo kofar tare da sallam, nakarɓi uniform ɗin nafara sakawa Naseem rigar sa wan da shi dama ta saka masa wandon shine yagudu,gyara masa zamar rigar nake ina faɗin
"Um kaga soja wannan yaro zai iya rike bindiga in ya girma ya zama soja".
baki yarika washewa yana É—aÉ—É—aga kafaÉ—a da faÉ—in "Nine toja ai nine toja". "Ai kam ga sojan gasken gaske".
a haka nagama kimsashi
kana nasakawa Nasmah ita ma inata faÉ—in mata itace Dr zata rika yiwa mutane allura.
nariko hannun su muka fito parlour nan muka iske Zulai da kayan break É—in su, Talatu kuma ta É—auko musu School bag É—in su, muka nufi parking space, da murna suka shige cikin motar Naseem sai faÉ—i yake
nine toja, Nasmah kuwa ta dube ni tace "Mommy ni meye?". kumatun ta naja nace "Kece Dr me yiwa mutane allura".
sai washe baki suke cike da murna direba yaja motar suka tafi.
Wani sati na gewayo wa muka fara shirin tafiya ziyarar gani da ido nan muka É—auki hanyar zuwa Lagos,
sai dai wannan karon bantafi da su Nasmah ba saboda School, ni da Bappa da wasu jagorori biyu muka tafi, mun isa Lagos lafiya awani kayataccen hotel akayi mana masauki, mun isa yau washegari muka nufi Company da ake ta kan ginashi tamfatsetsen Company wan da girman sa ya kai ya kawo, an kai ni gurare da dama acikin sa an nunnuna min, masha Allah komai yayi saura kaÉ—an a kammala.
a gajiye muka koma masaukin mu kansan cewar da kafa akayi ta yawo damu acikin Company'n.
kayan jikina na tuɓe nashiga baya na watsa ruwa kana nafito na sauya kaya na haye gado dan na ɗan huta, waya ta na ɗauka na laluɓo lambar Talatu bugu ɗaya ana biyu ta ɗaga, da sallama bayan mun gaisa nace
"Ina mutanen naki?". tace "Gamu nan muna tare da su a parlour muna kallo, ungo Naseem karɓa ga Mommy tana magana."
tasaka masa wayar a kunne,
"Mommy da mu biki kijo jike da mu".
murmushi nayi jin muryar Naseem nace "To zan zo naje da ku, kuna karato sosai ko?".
kai ya gaÉ—a, Talatu tace "Ka amsa da baki ai bata ganin ka". yace "Eh." "To a dage sosai, bawa Nasmah wayar." ya mika mata Nasmah tace
"Mommy kina ina, damu biki kije da mu".
nace "Nasmah to zan dawo nazo naje da ku kinji."
"Mommy yaushe zaki jo?."
"Gobe zan dawo naje da ku kinji". to tace, haka sukayi ta zuba min surutu da gwalaɓen su ni ma ina biye misu kun kai minti 30 a haka daga bisani na kashe wayar.
na gyara kwanciya ta dan bacci nake ji.
kwanan mu uku a Lagos muka juya Abuja.
Yau asabar ba makaranta muna tare da ƴaƴana a parlour munata sharholiyar mu cikin farin ciki da jin daɗe, duban daular da nake ciki a rayuwa da nake yin ta yan zu nayi, Allah yabani duniya ya ɗaga ni ya ɗaukaka min daraja ta, a lokacin da duniyar ke kokarin suɓuce min a lokacin da rayuwa ta tazomo tamkar kwai a cikin tray, wan da yazamo baki-baki saura kiris ya suɓuce kasa ya tarwatse.
numfashi na sauke lokacin da tunanin Inna ta ya zomin, wasu zafafan kwalla ne suka zubo min,
Allah sarki Inna ta tabbas na yarda wani hanin ga Allah baiwa ce, ya É—auke ta a lokacin da nake tsananin bukatar ta arayuwa ta, lokacin da duniya ta juya min baya lokacin da narasa madafar dafawa lokacin da na gwammaci mutuwa ta da rayuwa ta.
ya É—aukaka darajata abayan bata nan ya azirtani da arziki mai tarin yawa, wa zai iyayin duk wannan in banda *RABBUSSAMAWATI WAL'ARDI*.
Allah sarki Inna ta Allah yakai haske kabarin ki ya sa mutuwa yazame miki hutu.
wasu kwallan nakuma sharewa lokacin da na kuma tunawa da wata uwar wato Mama mai awara, Allah sarki rayuwa
ta cito ni lokacin da duniya tafara wasan kwallo da ni, matar data jajirce wajen ganin an ceto rayuwa ta gun haihuwa, da awancan lokacin bata samo kuɗin da za'a min cs ba wata kila da yanzu na mutu da ni da su duka aciki, tarike ni tamkar ɗiyar da ta haifa a cikin ta. lokacin da tayi nisa wajen ceto rayuwa ta sai ta tsuɓuce min.
sai gashi yau Bappa yamaye gurbin su, yazame min uba kuma uwa, ya jajirce yatsaya kan lamari na yazamo silar isata matakin danake yanzu, matar sa ta zame min uwa Æ´aÆ´an sa suka zame min yan'uwa.
Rungume su Naseem nayi a jikina ina jin wani irin kuna, rumtse idanuna nayi da karfi jin kaina yana wani irin tsara min, lokacin da tunanin abun da yayi silan rabani da ahalina yashiga yimin yawo a kwakwalwa da zuciya ta. zunbur na mike nashige bedroom É—ina, sam bana son narika tunawa da hakan duk ranar da na tuna nakan kwana cikin kunci da bakin ciki da matsanancin ciwon kai, dan ranar zan kwana ina kuka.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.