Best / Popular Hausa Novels

Hamdah Littafi Na 3 Complete Hausa Novel

Reading file: HAMDAH part 3 Complete - Copy - Copy (1).txt

Chapter 9 of 33

Bayan wasu ƴan awanni jirgin mu yasamu sauka cikin yar dar Allah da buwayar sa, cikin babban birnin tarayya Abuja da ke cikin kasata ★NIGERIA★.
bayan saukar jirgen da kamar minti 15 fasinjojin ciki suka fara sauka.
da sauri ganin Naseem da Nasmah sun mike kan kace me sun rufa da gudu sunyi bakin kofar fita in da mutane keta sauka,
cikin hanzari na rufa musu baya da sauri ina faÉ—in
"Kai kutsaya fa kar kuje ku faÉ—i."
ai ko da gudu suka fara sauka daga matattakalar jirgin suna dariya.
bayan su nabi ina dariya ganin inda suke sauka cap-cap-cap daga matattakalar kamar zasu kefe kasa ina cigaba da faÉ—in.
"Zaku faÉ—i fa kutsaya."
kan kace me sun sauka kasa, sauri na kara ina sauke kafata kan shinfiɗaɗɗiyar kasan kasata abun alfahari na ƙasata Nigeria, naja wani irin numfashi tare da shakar daddaɗan iskar dake kaɗawa acikin ƙasata.
ganin suna kokarin cigaba da gudun nayi hanzari na ruko su tare da faÉ—in
"Idan yaro ya faÉ—i yayi min kuka zan kara masa."
baki suka washe cikin kyakyata dariya Naseem yace
"Mommy baya mu faÉ—i ba." goshin sa na dungure nace "Zaku faÉ—i mana in zaku faÉ—in zaku sani ne wan nan gudun da kuke ai sai dai kuji ku a kasa kuzo nan ku tsaya."
na janyo su gefe guda.

Daga can gefe guda
da sauri aka buÉ—e wata motar da suke jere É—an nesa da mu, wasu mutane biyu suka fito da sauri suka karaso in da muke, sannu da hanya sukayi min, na amsa ina kokarin janyo su Nasmah mu matsa gefe, daya daga cikin su ya mika min waya, kallon wayar da yake mika min É—in nayi kana na mai da duba na kansa,
kai ya É—aya tare da faÉ—in
"Ana maga na." ya fada yana kallon kan screen É—in wayar, a hankali na sake Nasmah dake rike a hannun dama ta na amshi wayar, shikuma yayi saurin ruko hannun ta yaÉ—an matsa gefe kaÉ—an in da É—ayan mutu min ke tsaya ya harÉ—e hannu da bakin gilashi a aidon sa,
a sannu nakai wayar kunne na tare da yin sallama, daga cikin wayar akace
"Barka da isowa kasa Nigeria ki bisu su isa da ke masauki."
É—an shiru nayi kamar naso nagane muryar mai maganar, sai kuma na sauke wayar batare da nace komai ba na mika masa wayar.
a hankali na soma tafiya suna biye da ni har gurin mota, da sauri É—ayan ya buÉ—e min murfin motar muka shiga in da tuni suka saka jakar mu cikin motar.
jere motocin suka fita kamar yan da aka kawo mu airport a can kasar Saudiyya.
muna fita daga cikin airport ɗin muka ɗau hanya, shiru nayi cikin motar ina raba ido cikin ƙasata yayin da zuciya ta ke kunshe da ɗin bin farin cikin gani na cikin ƙasata, ina jin wani farin ciki tabbas ƙasata abun alfahari na ne.
munyi tafiya mai nisa kafin muka isa wani katafaren hotel, hotel ne irin wan da manyan kusoshin kasa suke sauka a cikin ta...

Awani haÉ—eÉ—É—en É—aki aka sauke mu sai da suka rako mu har bakin kofar room É—in kafin suka juya, wan da ke rike da jakar mu kuma yashi ga ya ajiye, kana ya miko min waya yace "Ana magana." na amshi wayar a raina nake faÉ—in
"To yanzu kuma ina zai kuma cewa na bisu."
a sannu nakara wayar a kunne na sai jin muryar Bappa nayi yana faÉ—in
"HAMDAH sannun ku da hanya ya gajiyar hanya."
washe baki nayi dajin muryar Bappa da sauri nace
"Laaa Bappa mun iso lafiya kalau Bappa kana ina?."
nafaÉ—a ina washe baki cike da murna jin muryar Bappa da nayi yace
"Kuhuta ku kwanta ku huta sosai ina nan zuwa."
nace "To Bappa." na mika masa wayar ina cigaba da washe baki, mutumin ya fita tare da jamin kofa, numfashi na sauke tare da bin É—akin da kallo, na isa bakin gado na zube bakin gado, in da tuni Naseem da Nasmah suka haye gadon sai salle suke.
kokarin tuɓe kayan jikina nake dan so nake naɗan watsa ruwa, naji ana knocking mayafi na naɗauka na mayar jikina, na mike na nufi kofar na buɗe ma'aikacin hotel ɗin nagani tsaye rike da babban tray, baya naja na bashi hanya yashigo ya dire try ɗin kan table kana yafita na mai da kofar narufe na murza key.
na dawo bakin gadon na tuɓe kayana nashige bayi,
wanka nayi sosai nafito na tuɓe su Naseem suma nayi musu wan kan.
bayan na shirya su nima na sauya kaya, kana na zuba mana abinci mukaci.
muna gama ci muka koma gado...

bayan haka da kamar awa 2 akayi knocking na mike naje na buÉ—e, É—aya daga cikin mutanen da mukazo tare nagani tsaye yace
"Madam kun kammala zamu iya tafiya?".
kai na gyaÉ—a masa, juyawa nayi dan kiran su Naseem sai ganin su nayi a bayana suna kokarin fita daga É—akin,
mutumin ya ruko hannunsu nikuma na koma na É—au mayafi na nabi bayan sa muka fita..
tun daga bakin get É—in da muka iso na fahimci banki muka zo dan gashi a rubuce (First bank) buÉ—e baki nayi a raina nake faÉ—in "To me mukazo yi a banki." bakin na rufe jin yana faÉ—in
"Bismillah fito muje ko." sai lokacin na lura ashe ma har sun fita har ya buɗe marfin ɓarin da nake ban sani ba, a hankali na zuro kafafuna waje na fito.
direct cikin bankin muka shige batare datsaida mu ko bincike ba, akasin jama'ar da nagani tsaye bakin bankin an tsaida su an hana su shiga.
tun da nashiga cikin bankin aka bani gurin zama ban motsa ba, duk wani cike-cike da kai kawo wasu suke tayi su da wan da mukazo da su, sai dai abun da yakamata ni nayi da kaina shine nake tashi naje nayi, awa 1 da zuwan mu aka kammala komai aka bani ATM,
muna fita daga bankin zato na masauki za'a maida mu sai ganin mu nayi a get É—in wani banki, shima kusan mintunan da mukayi a bankin da muka baro mukayi a nan É—in kafin muka kammala, nan ma da ATM É—in bankin muka fita. ina mai jin mamakin kuma zuwan mu wannan bankin.
mamaki na bai karu ba sai da nakuma sin tar kaina cikin wata banki, wunin ranar muka kare ta a bin bankuna dan sai da muka je banki biyar kuma duk wan da mukaje da ATM É—in sa muke fita..
sai yamma liss muka dawo masaukin mu, a gajiye na zube bakin gado in da É—aya daga cikin mutanen da muka tafi da su yashigo da su Nasmah, wata laidar dake rike a hannunsa ya mika min yana faÉ—in
"Gashi ance na baki."
bin laidar nayi da kallo kana namika hannu na amsa shiku yafita,
zamata na gyara tare da zuba ATM É—in da suke hannuna kan table É—in gabana.
a sannu nashiga buÉ—e laidar dan ganin abun da ke ciki,
kwalayen wayoyi ne har guda biyu nagani ciki a sannu na ciro su ina jujjuyasu, rabon da narike waya haka a hannuna a matsayin nawa har na mance, sai kuma cikin hanzari nashiga buÉ—esu dan tun ban ciro su ba wayoyin suka tafi da ni, da sauri na ciro cazar wayoyin duka namike cikin hanzari naje na saka su a cj, ina saka wa kuwa suka nuna min acike suke, da sauri na dawo in da na tashi na kunna wayoyin, ai ko ina kunna wa sai ji kake É—uÉ—ut-É—uÉ—ut alamun shigowar message alert akai-akai.
ido na kurawa musu ganin alat ne na kuÉ—i suke ta shigowa, na bankunan da muka buÉ—e É—azu, ido na zubawa sarautar Allah ganin kuÉ—aÉ—en da suke ta shigowa ni bama zan iya kiyaste adadin su ba.
sai da naji wayoyin sunbar kara kafin nashiga latsa su, contacts nashiga da sauri sai gani nayi babu number ko É—aya, jiki a sanyaye nake kallon wayar, abu na farko da ya fara zuwar min shine lokacin da Abbu ya siya min waya yasaka min number family na aciki,haka narika bin lambobin Æ´an'uwa na ina kiran su.
hawayen da yagangaro kan fuskata na share ina mai jin kewar ahalina, a sannu na mike na isa in da jakata yake na buÉ—e naciro number Ukhtee da ke rubuce a takarda, na saka cikin wayat kana na dannan mata kira,
tana É—aga wa dajin nice mai kiran atare muka saki ihun murna.
hira mukayi tayi da ita har magriba kafin na mukayi sallama...

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.