Age Mates Complete Hausa Novel
Reading file: Age_Mates_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 14 of 44
*****************
zaune take gaban wani malamin tsubbu cikin wata bukka"kansa Aduk'e ya d'ukufa yana bugun k'asa"yayinda tayi tagumi tana jiran jin Amsar bayanin data kora masa Ayanzun"can ya d'ago kansa yace"wanene likitah ?"da mamaki ummah luba ke saurarensa tayi shiru"sai kuma ta tuna da Dr darma "Atake gabanta yafad'i tace"cikin gidanmu yake ,yaron Abokin Mai gidanane"to shine ya b'ata mana Aiki"sannan ya saka Aka maida Aikin k'aik'ayi koma kan mashek'iya"bi ma'ana Abin ya dawo kanki"kai Amma matsiyacin yaron nan taya yasan meye mukayi?"to gashi nan dai naga ya lalata komai"sannan yanzun muddin kina so mijinki ya dena jin kina warin jab'a Tofa dole sai An binne Abin inda yaron ya saka Aka rufe"idan mgn zakiyi masa yaje ya binne zaifi, idanma yaya zakiyi shawara ya rage naki"hankali tashe tace" mlm inani Ina tonama kaina Asiri kuma?"to Ai ya riga yasan kece kikayi Abin sbd haka ke kika sani"yarinyar kuma dole itama sai mun canza wani Abun game da ita"sbd gata nan tana gab da zama wata irin tauraruwa"cikin fad'uwar gaba tace"ya za'ayi kenan mlm?"ki fara bada kud'i kiga Aiki mana"shikenan Abani kwana 2 zan dawo"dato ya Amsa ,tayi masa sallama ta tafi"Allah ya kyauta ya shirye mu gaba d'aya....
Tun daga lokacin da Dr darma da Ahyaan suka tafi suka barta tsaye Awajen"Ikkhee taci mummunan Alwashi Akan Ahyaan"tayi Alk'awarin ba zata koma zuwa wajen saba ko kuma kiransa ,koda sonshi zai kasheta"saidai muddin tana lumfashi bazata bar Ahyaan Ahaka bata mata wani gib'i ga rayuwa ba" wanda zai saka Dr darma yaji muguwar tsanarta Azuciyarsa"dukda Ayadda ta saka Aka mata bincike kansu da Alak'arsu taji suba masoya bane"Amma zuciyarta tak'i yadda suba masoya bane"tafi zaton suna son juna ne sunki fad'ama kansu"ko kuma shi Dr darma ke sonta yabdai b'oye ne game da gudun wani abu"sbd tun lokacin da taga sun hau mashin tana masa shakulkul ta hanashi ya kulata zahiri ta tabbatar Akwai wani Abu Ab'oye"wannan kenan.......
Ayau ya kama Friday"misalin k'arfe 4:11 pm Ahyaan ta fito sanye da dubai Abaya black me zanen flowers golden brown da Adon stones "saita yane kanta da mayafin"tana sanye da takalmi masu masifar tsini golden brown "yayinda hand bag nata itama golden brown ce"ta d'aura bak'ar tsadaddar Agogo ta saka zabba da wani d'an hannu"fuskarta da make up sbd ta shafa red d'in lipstick "tayi wani irin shegen kyau kamar wacce zata gasar fidda sarauniyar kyau"ga wani irin sanyayyan k'amshi ke ratsa jiki da zuciya tanayi"gudan hannun na rik'e da waya ta Kara gefen kunnanta tana mgn murmushi kwance saman kyakykyawar fuskarta.....shiko tun fitowarta ya zuba mata idanu, murmushin da take yi ya matuk'ar k'awata kyawunta da motsa rauninsa. Hakama kwalliyar tata ta d'auki hankalinsa matuk'a"duk da ita hakan normal ne a gareta badan wani birge wasu maza ko wani abu tayi ba....ita sam Ahyaan batama lura dashi ba"dukda koda ta lura dashi d'in ba tankashi zatayi ba"sbd jiya da yau data gansa be tankataba. ko jiya da yayi Azumi wajen cin Abinci yaje yasha ruwa"ta lura kamar ya tsaneta yanzun sbd daya ganta saiya had'e rai....Dr darma kuwa yana zaune kan resting chairs dake k'ofar d'akinsa "t shirt ce me gajeran hannu fara da wondo 3 quarter Ajikinsa "yana d'an shan iska ya cire kayan da yaje masallacin juma'a dasu"ganin tana k'ok'arin wucewa ya saka yataso batare daya san meye zaice mata ba idan ya iso wajenta?"saidai kawai yana son sanin Ina zataje? sallama tayi da wacce suke wayar ta kashe ta bud'e hand bag nata ta saka wayar"dagowar da zatayi da nufin ta iso bakin get taga mutum gabanta"saida taji fad'uwar gaba "saidai bata kallesa ba"ita yanzun bata son yawan had'a Ido dashi bata san dalili ba"saidai ta d'aure fuska tana k'ok'arin giftashi da nufin ta wuce"Ina zakije ne?"yafad'a kamar Ammasa tilas yana zuba mata Ido"cikin masifa tace inda ka Aikeni"na d'auka Ai yadda ka nunamun tsana zahiri bazaka damu da inda zanje ba"to kaima Awa da zaka ta sani gaba kana tambayata Ina zanje?"tunda dai mamy ta barni ta kuma bani kud'in transport me ruwanka da inda zanje??"tunda take masifar ya zuba mata Ido yana kallo lips nasa na k'asa na cikin bakinsa"idanunsa sun yi d'an ja"har cikin zuciyarsa bayaso suna samun matsala da ita, saidai bazai d'auki raini ba"kar taga yadamu da ita ta nemi gaya masa mgn"ganin yak'i mgn kuma yak'i bata hanya ya saka ta tab'e baki zata giftashi ta wuce yakoma tarewa murya Akausashe yace wlh koki sanar mun Ina zakije kona baki mamaki?kin Isa ki tasani gaba kina mun ihu ne?"har tafiyar saina hanaki naga yadda zakiyi....tunanin zai b'ata mata lokaci ya saka kamar zata had'iyi zuciya sbd b'acin ransa da takaicinsa tace" sunan k'awarmu data haihu zamuje nida Khairiyyah"idan kana yiwa Allah ka jaraba hanani zuwa mana"ta fad'a cikin zafin zuciya"sai yaja tsaki yabar wajen zuciyar na tambayarsa wai me yarinyar nan ta d'auki kanta ne?"Akanme zaka shiga sabgarta wai??"wata zuciyar ta tambayesa"gaba d'aya jinsa yadin gayi cikin b'acin rai"kawai saiya koma ya zauna"befi mintina 5 da zama ba Akirashi Asibiti Ana son ganinsa da gaggawa"hakan yasa ko kaya be sauyaba ya wuce ya shige mota ya tafi.... "sai bayan sallar magrib ya shigo gidan"zuciyarsa ta dinga in gizashi yaje yaga kota dawo?"saidai koda ya shigo mamy ce zaune kawai a parlourn "tana lura dashi yana ta y'an kalle kalle yak'i mgn sai kuma ya fita"bakin get ya fito yayi tsaye daga waye yana danna waya"kawai yaji motsin mota ,sai kuma yaji horn"Anutse ya d'ago kansa yana zubama motar Ido har tayi parking "sai Aka bud'e gefen driver Aka fito"kallo d'aya yayima matashin da suka gani shida Ahyaan last 2 days ya d'auke kansa cike da shan k'amshi "saidai yana kallonsa ta gefen Ido yaga ya bud'e gefen me zaman banza"saiga Ahyaan ta fito daga cikin motar.....✍️
wannan book d'in na kudine! idan kina buk'atar siya serious 500 normal grp vip grp 1000
Acc n 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki 08100084251
dan girman Allah da dajarar iyayenki karki mun mgn idan baki shirya siyaba
Bana son kira a what's app kawai zakimun mgn
Idan kika karantamun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitar mun Allah ya isa banyafe miki ba
#Mommyn fareesa
#Dr Nura Darma
#Ahyaan
#mr Mahuta
#AA mashi
#mu'az
#Khairiyyah
#Ammah
#Ummah
#ikkhee🧍 *AGE MATE'S* 🧍♀️
*25&26*
*Littafin kud'i ne!*
.........wani irin fad'uwar gaba had'e da tsinkewar zuciya suka sami Dr darma duk Alokaci guda"tsaye kawai yayi turus Awajen yana binsu da wani irin shegen kallo"fuskarsa bbu yabo babu fallasa....k'amshin mayen turarensa da Ahyaan ta shak'o yasakata saurin kallon bakin get d'in gidan nasu"Atake taji k'irjinta yabuga sbd tozali datayi da kyakykyawar fuskarsa yana dannah waya tamkar besan da zaman suba"saita dake ta rufe murfin motar kawai"Adaidai lokacin AA mashi ke furta gashi zaki tafi baki bani contact d'in ba?"yamutsa fuska tayi tak'i yin mgn...yayan mu barka da dare! cewar AA mashi yana kallon Dr darma daya d'auke kansa daga barin kallonsu" saidai yana sauraren su"ya d'auki kusan second 5 kafin cikin shan k'amshi had'e da basarwa yace"barka dai Atak'aice"tamkar Ahyaan tace masa *Age mate* d'inta ne ,sbd ta fahimci AA mashi ya girmeshi"sai kuma taga rashin dacewar hakan" sai kawai ta nufi cikin gidan batare da kota gode tace masa ba...dama ya ganta bakin titi ne tana jiran Abin hawa ga magrib tayi"saiya tsaya ! kasancewar tunda ya ganta yarasa nutsuwarsa yana neman ta yadda Allah zai sanya yakoma had'uwa da ita"sai gashi ya taki sa'a ya ganta tsaye bakin titi"saida ya dinga yimata magiya sannan ta yadda ta shigo motarsa"tunda ta shigo kuma shine ke surutunsa ita dai tayi masa shiru, saiya dameta zata ce uhmm ko ah ah har suka iso gida....pls ji mana! ya koma fad'a sbd ganin zata shige ciki"saidai bata juyoba ta Ida shigewa cikin gidan"Dr darma ya tab'e baki ba tare daya kalli gefen da yakeba shima yabi bayanta"kusan Atare suka shigo cikin parlourn mamy"dandai ita ta rigashi shigowa"sai yanzun Ahyaan bayan nace karkiyi magrib??"wlh mamy matsalar nafef ce shiyasa kiyi hak'uri dan Allah"ba komai tunda kin dawo lfy"kije kiyi sallah,dato ta Amsa ta wuce ciki tana lura da Dr darma na zaune ya wani sha mur yanata y'an Harare Harare"saidai bata tankashiba ta wuce sbd wani irin haushi yake bata.....ba Abincin zaka cibane?"yayi shiru"baka jine?"na k'oshi"wai dan Allah mamy meyasa kike barin yarinyar nan tana yadda take so?"wani nefa ya sauketa daga cikin motarsa"yanzun haka tarbiya ce me kyau?"da kallo mamy ta bishi har saida yayi shiru kafin tace"sbd wani ya kawota ya Ajiye shine ke nufin batada tarbiya ko bamu bata tarbiya ba?"shin kasan kota sanshine ,ko kuma sbd kar tayi dare shiyasa ta shiga motar tasa??"kaifa malamine nurah yaka mata ka dinga uzuri da kyautata zato"Ahyaan ni banga laifinta ba"sbd haka idan naga tayi ba daidaiba Ina tsawatar mata "mgn ta dakai ta k'arshe karka koma ce mata yarinya sbd kaida ita sa'annin juna ne"idan bakaso tayi magrib d'in meya hana kai kaje da taka motar ko mashin ka d'akko ta?"....bana ganta da zata fitaba na mata mgn Ina zataje,? shine ta caccab'amun maganganun data gadama cikin raini tayi tafiyarta"sai idan na mata wani abu kuma mamy kiyita mun fad'a "sbd haka taje tayi Abinda ta gadama rayuwar ce Ai"yana fad'in hakan ya mik'e tsaye cikin zafin zuciya ya fita"ba k'aramin mamakinsa mamy tayi ba"saidai ta kasa fassarah me hakan ke nufi?"Amma zata zuba musu Ido taga ita gudun ruwansu shida Ahyaan d'in.....Adaren ranar Dr darma ko dinner beyi ba"harta chemist da yake d'an fita da dare shima be jeba"yayi wani irin fushi da Ahyaan"yaci burin yafita harkanta har Abada bbu ruwansa da ita"idan ta masa mgn zai Amsa"idan bata masaba zai nuna kamar besan Allah yayita ba"shidai yasan ba gaba yakeyi da itaba kawai kiyaye mutuncin kansa yakeyi"washe garin ranar dayake week end ne saima wajen 12 pm ya shigo ya gaida mamy fuska ba walwala"ita dariyama yake bata Idan yana hakan"saidai Ahyaan dake tsakar gidan tana feraye doya kallo bata isheshiba"itama sai tayi biris dashi.....bayan sallar la'asar da yamma"Ahyaan na zaune tsakar gidan sanye da doguwar riga irinta larabawa milk"sadeeq na gabanta zaune kan kujerah yanata zuba mata surutu"tayi masa shiru tana yanka fruits da mamy ta sakata...tafe yake a nutse kan k'afafuwan sa. daka gansa kaga tsayayyen mutum mai cike da jatumta da lafiyar gabb'ai. A komai nashi babu hayaniya babu d'agawa duk da wasu kan fassara shiru-shirun nasa da girman kai"saidai Abin ba haka bane agaresa halayyar ce hakan"Anutse ya shigo cikin gidan" yaci zazzafan wanka na bakin yadi da Akayima Aiki da golden brown d'in zare"ya Aza hula k'ube golden brown"yayi wani irin shegen kyau tamkar saurayin da zaiyi 33yrs"ya fito sak a cikakken bakatsinensa!hannunsa guda zube cikin Aljihun wondonsa "ga wani irin k'amshi mai ratsa zuciya da yake zubawa"fuskarsa ta k'ara kyau da haske sbd gyaran fuskar da yayi"tamkar baya so haka yayi sallama Atsakar gidan"k'irjin Ahyaan ya buga! saidai bata d'ago kanta ta kallesaba"yayinda sadeeq ya juyo ya kallesa yana furta masha Allah Azuciyarsa"shi kansa dake namiji yaji ya burgesa inaga mace??"shi kuwa uban gayyar dakewa yayi sbd lura da sadeeq ya gansa" sai kawai ya iso gefensa yayi tsaye yana jin kamar yadinga bashi puncher's "sbd ganin yadda ya zage yanata zuba mata surutu Amma ta masa banza....yanda yayi tsayiwar k'asaita ya hard'e k'afafuwansa waje guda, idanunsa na'a kan waya yana danna"saika rantse da kamar baya a wajen.....likitah bokan turai! yanzun gaisawa zamuyi ko da wayar zan barka?"d'an sakin fuska yayi k'ok'arin yi ya bashi hannu sukayi musabuha "ya Aiki?"Alhamdulillah "to Allah ya taimaka"Ai jiya naga firanku A tv "game da matsalar k'oda....."karon farko Ahyaan dake saurarensu ta d'ago kanta da mamaki "sai Akayi sa'a shima Dr darma ya waigo da nufin yabar wajen ma"sai suka had'a Ido "saurin d'auke kanta tayi "ya yamutsa fuska zai nufi parlourn mamy zai shiga "Adaidai lokacin wani yaro ya shigo yace Ance Ahyaan tazo"kace bata nan kana jina?cewar Ahyaan tana zarema yaron da aka Aiko Ido "kai je kace gata nan zuwa"cewar mamy data lek'o daga cikin parlourn "fasa shiga cikin parlourn Dr darma yayi saima ya fita daga sashen"Ahyaan nata b'ata fuska ta Ajiye Abinda takeyi ta wuce ciki ta d'akko mayafi ta Aza saman kular kanta ta yane kanta dashi "tunda ta fito sadeeq ke kallonta yana jin inama ya mallaketa Amatsayin matar Aurensa....yana zaune yana danna waya kan resting chairs zaka d'auka bema san da wad'anda ke wucewa ba"Amma sarai yana kallonta ta k'asan Ido ta wuce ta gabansa ta fita.....gaban Ahyaan ya fad'i da taga Mr mahuta tsaye shida Amininsa honorable rabiu "ko wane yayi shiga ta Alfarma"kallo d'aya zaka musu kasan masu dashi ne"yamutsa fuska tayi had'e da yi musu sallama....ikon Allah! sai kace Aljannah"lallai dole mahuta ya gigice A kanta"cewar honorable rabiu Azuciyarsa "sakamakon tunda Ahyaan ta fito yake kallonta"ranki ya dad'e barkanki! Ayangace cike da Aji tana wani shashshan k'amshi tace "sannunku da zuwa"yauwa baby"wani banzan kallo ta jefi honorable rabiu dashi sbd babyn daya kira"Ina yininku?"lafiya qlau yasu mamah?"Alhamdulillah! to Masha Allah" kwana 2 ban koma dawowa ba Ahyaan "naso na hak'ura dake saidai zuciyata ta kasa hak'ura"yanzun haka tafiyar gaggawa ta sameni zuwa k'asar Ghana "zanyi kusan 3 month Acan"so pls inaso ki samun contact naki mu dinga waya"ki kuma Amshi sak'on ki ko?"nasoma mud'an fita dake ko zuwa shopping ne to nasan da wuya ki Amince.....tunda yake surutunsa Ahyaan ke yamutsa fuska cike da masifa sbd ba k'aramin haushi da k'insa tajiba" ka gama bayanin naka?"gaba d'aya suka bita da kallo" ta yamutsa fuska tare da cewa Abu biyu zan rokek'a"idan kak'i zan nuna maka Ainahin kalata"na farko kayi hak'uri ka fita daga rayuwata"na biyu ka cireni daga zuciyarka sbd ba'a yin dole....ke kuwa taya zakiyi haka?"komai sannu Ake binsa fa"yanzun ga wannan yace Abaki....shiru yayi sbd turo k'ofar get d'in da Akayi "ke kije inji mamy"cewar Dr darma daya fito fuska bbu Annuri "ita kanta Ahyaan d'in kasa yi masa musu tayi "saidai batace komai ba ta nufi gefensa ta wuce "Dr darma ya kallesu ya saki wani makirin murmushi had'e da d'allar yatsunsa guda biyu "ya wuce cikin gidan ba tare daya furta komai ba.....Mr mahuta ya sauke numfashi yana sakin murmushi me ciwo babu wani d'ar yace"kota halin k'ak'a saina ja yarinyar nan k'asa"shi kuma wannan k'aramin d'an iskan zai gane ba'a ja dani"Allah yakaimu nadawo daga tafiyar"yanzunma sbd babu lokaci ne shiyasa zan barku.....muje ciki mu Ida mgn"cewar honorable suna shigewa cikin motar da sukazo da ita.....har cikin ranta Ahyaan ta d'auka da gaske mamy ke kiran nata"tana shigowa ta sami sadeeq zaune inda ta barsa yana shan fruit da mamy ta zuba masa."kallo be ishetaba ta wuce cikin parlourn"har bak'on yatafi ne?"Eh"gani broth yace kince nazo"d'an shiru mamy tayi ,sai kuma tace"naga ko ruwa baki d'auka ba da nufin kaima bak'on, shine nace yakiraki "to Ashema ya tafi"uhmm kawai ta Amsa ta wuce d'aki ta cire mayafin.....
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.