Age Mates Complete Hausa Novel
Reading file: Age_Mates_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 16 of 44
wannan book d'in na kudine! idan kina buk'atar siya serious 500 normal grp vip grp 1000
Acc n 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki 08100084251
dan girman Allah da dajarar iyayenki karki mun mgn idan baki shirya siyaba
Bana son kira a what's app kawai zakimun mgn
Idan kika karantamun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitar mun Allah ya isa banyafe miki ba
#Mommyn fareesa
#Dr Nura Darma
#Ahyaan
#mr Mahuta
#AA mashi
#mu'az
#Khairiyyah
#Ammah
#Ummah
#ikkhee🧍♀️ *AGE MATE'S* 🧍
*27&28*
*Littafin kud'i ne!*
....... subahanallahi! Harda su Amai kuma?"sannu! ta fad'a tana Ajiye plate d'in da flux saman center table ta k'araso gefen kansa ta duk'a"a wahalce ya d'ago kansa suka kalli cikin idon juna"broth sannu! ta fad'a cikin nuna Alhini da jin tausayi"be iya furta mata komai ba saidai ya maida kansa yana cigaba da kakarin Aman "Azuciyarsa yana mamakin zuwan nata sbd beyi zato ba"gefen zuciyar kuma yaji sanyin ganin yadda ta nuna tausayinsa a fuska da kuma cikin Idonta....motsin mik'ewarta tsaye ta shiga toilet yasaka shi lumshe Ido yana jin wani irin d'aci Abakinsa.....broth tashi ka kuskure bakin naka kasha ruwan Lipton "ta fad'a cikin sanyin murya da nuna rarrashi"bud'e idanun nasa yayi ya Azasu Akanta"ya ganta tsuggunne gabansa"rik'e da k'aramin towel da wata silver sai ruwa cikin wata y'ar buta"da k'yar ya tashi zaune ya mik'a mata hannunsa ta zuba masa ruwan ya fara kuskure bakin nasa"idan ya kuskure saiya zuba cikin silver d'in "sai sannu take jero masa"sau guda ya gyad'a mata kansa"ta matso gab dashi har jikinsu na gugar juna ta dinga goge masa goshinsa da gefen bakinsa "shidai ya lumshe Ido yana maida numfashi"bayan ta gama goge masa ta koma toilet d'in"shi kuma ya lallab'a da k'yar ya koma saman bed d'in ya takure jikinsa waje guda sbd sanyi yakeji ga zafin da jikinsa keyi"koda ta fito goge Aman tayi ,ta zuba mornin fresh ta goge wajen"sannan ta koma toilet d'in ta wanke hannunta ta fito"ta bishi da kallo tayi tsaye"sai kuma ta matso ta had'e pillows guda biyu ta jingina su gaban fuskar gadon"Ahankali tace"daurewa zakayi ka tashi zaune kaci wani Abun"yayi shiru"kaji broth katashi pls?"sanyi nakeji Ahyaan zoki rufeni dan Allah"ya fad'a da k'yar "sosai taji tausayinsa cikin damuwa tace" da zaka sha magani zaka warke"kaifa likitah ne "ta fad'a tana tab'a gefen wuyansa taji da zafi"beyi mgn ba saidai yaji wani iri da k'yar yayi jarumtar daurewa yatashi zaune ya jinginah bayansa Ajikin pillows d'in data kara masa"Ahankali ta matsa gefen fridge nasa ta d'auki cups guda biyu taje ta zuba ruwan zafin"kasancewar Akwai sugar ciki saita fara sheka masa sbd ya rage zafi"saida yayi daidai ta matso ta mik'a masa"ba musu ya Amsa ya fara d'an kurb'a Ahankali Ahankali"sosai yaji dad'in bakin nasa dake d'aci"matsawa tayi ta d'akko plate d'in indomie d'in ta Ajiye gabansa tare da cewa pls ko ba yawa ne kaci"bata rufe bakiba khaleel ya shigo rik'e da ledoji"sannu ya masa ya mik'a mata ledar "ta duba ta zaro goran ruwa faro"saita Ajiye lemon fata dake cikin ledar kan bed side drower "badan yasoba yad'an fara cin Abincin da fork d'in data saka ciki"saidai shima ba laifi da yake Akwai dan yaji sai yaji dad'in bakin nasa"ita dai tana daga tsaye tana satar kallonsa idan yad'an kurbi shayin saiya ci Abincin"Ahankali ta juya...Ina zakije?taji Amon tattausan muryansa Abazata"toilet d'in zan wanke na had'a maka ruwan wanka"idan kad'an watsa zafin jikin naka zai rage"bece komai ba,ita kuma ta shige bath room d'in"batafi mintina 10 ciki ba ta fito ta samesa yana shan magunguna ,ga Allura gefe da Alama zaima kansa ne"plate d'in Abincin ta kallah taga yaci fin rabi"shima shayin ya shanye"sannu! Uhmm"ya fad'a yana Ajiye goron ruwan"saita d'auki ledar lemon tace bara naje na yankosa kad'an sha zakaji dad'in bakin naka"okay thanks! to yanzun wankan zakayi?"ta fad'a ba tare data kallesaba"Ayi hak'uri da wankan nan Ahyaan sai Anjima "nidai broth kata shi kaje kayi mana"zaka fa ji dad'in jikin naka sosai dakayi wankan pls"kaji?uhmm! bani towel a ward rope ta tsakkiya "batace komai ba ta matsa ta bud'e ward rope d'in"k'amshin turaren kayansa ya daki hancinta"Masha Allah! Ta fad'a dataga tulin suturunsa "daga k'asa ta duk'a inda taga towels guda biyu ninke Ajiye.... Akwai wata Leda bak'a ki d'akko da ita "nanma batace komai ba ta duba ta had'o tazo gabansa ta Ajiye ,towel d'in kawai ya d'auka ya d'an kalleta yaga ba shine take kallo ba"kije da ledar Ankon kamun mu'az ne"yamutsa fuska tayi tace Amma broth ba'a kamun invitation card ba kamun Anko kuma?"k'in mgn yayi"itama sai batace komai ba ta d'auki ledar ta had'a data hannunta ta fita daga cikin d'akin.....dr darma ya bita da kallo yana sauke numfashi "Ahankali ya sauka daga saman bed d'in ya zare kayan jikinsa ya d'aura towel"sannan ya zauna yayima kansa Allura "befi zaman mintina 5 yayi ba yaje ya murza key ya shiga bath room"Atsabtace yabsamu toilet d'in,ga ruwan wanka ta had'a masa cikin bath tub"saiya shige ciki yayi kwance ya lumshe manyan idanuwansa da suka yi d'an ja.....yafi mintina 15 cikin bath room d'in sannan ya fito yana tsane ruwan jikinsa "gaba d'aya jikin nasa da sauk'i sosai"babu jirin da murd'awan cikin"shima zazzab'in gashi ya sauka"rashin k'arfine kawai da babu Ajikin nasa"turarukan jiki kawai ya fesa yasaka k'ananun kaya mararsa nauyi yayi zaune saman bed d'in yad'an jingina yana tsotsar lip nasa na k'asa yana cijesa"gaba d'aya kyakykyawar choko face d'in Ahyaan yake hangowa"lokacin da take goge masa goshinsa da sadda take goge Aman babu nuna jin k'yank'yami, saima tsananin tausayinsa daya hango cikin k'wayar Idanunta"wanda yayi mamakin hakan sbd Aganinsa ta tsanesa! Ayanzun ko dariya takeyi data gansa take denawa"hakama idan tana murmushi ko mgn daya shigo zata gimtse Abinta"Afili ya furta komai girman namiji yaro ko babba yana buk'atar kulawar y'a mace "dubi yadda yanzun yakejinsa Alhamdulillah bisaga y'ar kulawar data bashi"ya tabbatar idanda beci wani Abuba yasha magani da yanzun yana nan kwance"yad'an lumshe Ido daya tuna d'azun yadda take ta rarrashinsa"gaba d'aya sai yaji fushin daya keyi da ita ya dena.... knocking d'in k'ofar da Akayi ya katse masa tunani "Ahankali ya Isa bakin k'ofar ba tare daya tambayi waye ba yabud'e"sbd ya d'auka ko itace"saidai yaga khaleel tsaye yana mik'a masa plate d'in data zuba yankakken lemon fata Aciki"Ina Ahyaan d'in?da barata iya zuwa da kanta ta kamun ba "ya furta ba tare daya shirya fad'in hakan ba"shi kansa Khaleel d'in yayi mamakin kalamansa"sai cewa yayi mamy ce data gama yankawa tace na Amso na kawo maka"bece komai ba ya Amshi plate d'in dan ya fahimci mamy tayi hakane sbd bata son yawan kad'aice warsu ne "kaje ka siyo kaza ka kai mata tamun farfesu" Amma ta saka yaji bakina ba dad'i pls"dato ya Amsa ya juya shi kuma ya rufe k'ofar d'akin.....
Ab'angaren Ahyaan kuwa tun bayan ta gama yanka lemon mamy tace" khaleel yaje ya kai masa"bata yi zaton komai ba ta wuce d'aki ta shiga wanka"koda ta fito sallar Azahar tayi sannan ta shirya cikin wani had'ad'd'en tsadaddan leshi me kyau daya haskata matuk'a "wanda sabo ne sawarsa guda"powder da maskara kawai ta shafa"saita gyara gashin girarta dake cike "sannan ta fesa turaruka ta saka y'an kunne kawai"ba k'aramin kyau tayiba "musammun datayi d'aurin d'an kwali goshi style d'aya bayyanah gashin gaban goshinta"fitowa tayi daga cikin d'akin"mamy ta bita da kallo tana fad'in Masha Allah "wuf d'aya idan ka kalleta zaka d'auka irin y'an matan Abuja d'in nan ce"mamyn nata kallonta Aranta tana mata Addu'ar zab'in Abokin zama na gari"mamy bara naje naga kosu Ammah d'in sun iso?"Ai Ahyaan sun jima da isowa gsky"sbd mama ta kirani tun d'azun tace sun iso"nima dama ke nake jira muje na gaisheta na dawo"to mamy muje ko?"dato ta Amsa ta d'auki hijab dake gefenta ta saka suka fito mamy ta rufe k'ofar parlourn da key"kafin ta rik'e hannunta Ahyaan suka fito"sai murmushi sukeyi suna mgn suka wuce....sam basu lura da Dr darma dake nufo cikin gidan ba"kasancewar dawowarsa daga masjeed kenan"ya bisu da kallo har suka bacewa ganinsa"ya lura koya Ahyaan ta saka sutura saita nuna kanta Ajikinta..... kyakykyawar motar daya gani Ajiye bak'a daga gefen tasa motar ya janye hankalinsa"wacce motar mata sukafi yawan hawanta"kuma itama bazata wuce sama da 8 million ba"sam be kawoma ransa motar Ahyaan ceba"sbd besan uncle mustapha ya siya mata mota ba"yadai san ta sami Aiki sbd saida iyayen nasu maza suka sanar masa....ringing d'in wayarsa yasaka ya d'auke kansa daga barin kallon motar ya wuce wajen resting chairs dake bakin d'akunan mazan gidan ya zauna yana Amsa kiran mu'az.....
Ummah na zaune a tsakar gidan itada Khadija"tayi duhu da y'ar rama"sbd gaba d'aya Abin duniya ya isheta "ga matsalar tsakaninta da Abba ba zaman lafiya,ga jin zafin Ahyaan ta sami Aiki"gaba d'aya ta lura yaranta ne kawai cikin gidan koma baya"musammun da taga ga Dr darma ya fara fantamawa"ga khaleel shima yanada Abin hannunsa"Isma'il na karatu shida Affan sun kusa gamawa"hakama Abdul Aziz shima yanada nashi Abin hannun"tun wayewar garin yau ta fahimci mamah bak'i zatayi"sbd ganin yadda taketa y'an Aikace Aikace da kai da kawowa itada Asma'u "kasancewar dama bata dogara da girkin luban ba"gashi itace keda girki yau"shiyasa tayi girkinta daban"sbd tanada komai da Dr darma dasu Affan ke Ajiye mata"saida k'arfe 1 saura tayi sannan su Ammah suka iso gidan, ta fahimci dalilin su ya saka Ake wannan hidimar"saidai ta lura mahaifiyar zainab d'in nada girman kai ko gaisuwarta da k'yar take Amsawa"tana wannan tunanin uncle mustapha ya fito daga cikin parlourn mamah da nufin yaje yayi sallah sbd sun huta sunci Abinci"saidai yana fitowa mamy da Ahyaan na shigowa tsakar gidan "Ahhh Anty maryam! yanzun nake tambayarki ,sai nace bara na dawo daga sallah na shiga mu gaisa "sbd wannan zuwan naki ne, k'arar y'arki nakawo miki"mamy na murmushi tace na d'auka Ai kamanta dani musty "ya kama murmushi yace" Nina isa na manta da Anty nah"ya fad'a yana hararar Ahyaan ta kama dariya tace" uncle Niko?"Eh mana ba rashin m kika mun ba"nidai Ina motata?"tana bakin get"sai kawai ta wuce d'aki "shi kuma yayima mamy sallama ya fita....kasak'e da kunne ummah tayi k'irjinta na bugawa jin Ance motar Ahyaan na bakin get "gaba d'aya ta lura babu wanda yabdamu da ita da yaranta "ko mamy daga Ina wuni ba Abinda ke koma had'asu "kan idonta ta shige parlourn mamah.....Hjy Ammah kyakykyawar tsohuwa"meji da izzah da Isa "tana zaune hakimce kan kujerah sanye da wata super me tsadar gaske"dukda tafara tsufa Amma son Adonta da kwalliyarta na nan"da Alama Anan wajenta Ahyaan ta gado izzah"fuskarta na mak'ale da medical glass fari, sai k'aramar waya baby Nokia na hannunta "yayinda kan Ahyaan ke saman kafad'arta tanata zuba mata shagwab'a"mama dai na zaune tana kallon su tana kuma kallon TV "Ahaka Mamy ta shigo cikin parlourn da sallama"Ahhh Maryam ki koma kawai"da Ina cewa bara nina zo na gaisheki"haba Ammah! Nina isa nak'i zuwa ne"na bari kud'an hutane shiyasa"ta fad'a tana duk'awa ta gaida ita cikin girmamawa tare da tambayar mutanan gida"ta Amsa da Alhamdulillah" Ina likitah bokan turai ?"gaba d'aya ya manta dani na rasa wane irin Aure ne wannan? mamy na murmushi tace"yana nan Ammah dole yazo yakawo gaisuwa"to da yake yatashi yau bejin dad'i "subahanallahi! meke damun sa?"cewar mamah"Ahyaan tace zazzab'i ne harda Amai yayima d'azun"Allah yasawaka ya bashi lafiya"cewar Ammah"mama na k'ok'arin mgn kiran Abba ya shigo cikin wayarta"saita d'auka tayi sallama"daga bisani kuma tace"Eh"daga haka ta yanke wayar suka d'an tab'a fira da mamy "kafin mamyn ta tafi"bata juma ba saiga hamza Autah yadawo rik'e da tray me marfi shak'e da snacks inji mamy Abama Ammah"baki washe ta Amsa tana godiya"bayan yaron ya fita ya sake komowa rik'e da leda bak'a ya kalli Ahyaan yace"inji yaya nurah yace" kiyi masa farfesu ki zuba yaji bakinsa ba dad'i"dato kawai ta Amsa tana karb'an ledar "Adaidai lokacin Abba da dr darma suka shigo cikin parlourn"Ahyaan tayima Abba sannu da zuwa "ta saci kallon mutumin nata Ashe ita yake kallo"broth ! uhmm "ya jikin?"da sauk'i "bata koma mgn ba ta mik'e tsaye tana d'an murmushi sbd jin yadda yaketa tsokanar Ammah da tayi kicin kicin da rai sbd ganin Abba"ita wlh tsohuwar har mamaki take bata"ta rasa me mahaifinta yakashe mata Arayuwa??.....sau kusan ukku Abba nayima Ammah sannu sai tayi kamar bata jiba ta biyema Dr darma suna surutu"mama tayi k'asa da kai gabanta na fad'uwa "lura da Abba na mgn yasaka Dr darma ya fita yana murmushi...Hjy sannu da zuwa"da k'yar tace yauwa"bayan sun gaisa shiru ya biyo baya"cike da isah Ammah tace"dama nazo ne Akan batun yarinyar nan Ahyaan"Alhamdulillah! tayi karatu ta gama ,gashi ta samu Aiki"to shima mijin ta samu"inaso ko bayan Auren Amata transfer d'in Aikin zuwa can kd sai ta dinga yi tun yaron Acan yake kuma nan zasu zauna"shidai Abba shiru yayi sbd yakasa fahimtar zancen nata"idanma ya fahimta to waye wanda takeso Ahyaan d'in ta Aurah?"....yauwa iliyasu Akwai yaron dana yaba da hankalinsa Abokin mustapha ne kuma yana sonta sosai"to shine nakeso yazo kuyi mgn yaji yaushe zai turo iyayensa?"yaro ne saurayi ya jima beyi Aure ba"yanada Abin hannunsa,kuma d'an boko ne"sanin kankane na tsayama Ahyaan tayi karatu bazan bari tayi Auren wahalaba kamar yadda zainab tayi.... d'ago kanta mama tayi sbd rashin jin dad'in kalaman Ammah"Abba na lura da ita tana girgiza mata kanta da kyafta mata Ido"ya saki murmushi me ciwo be furta komai ba"saidai yaci burin nunama surukar tasa iyakarta"jin tayi shiru Alamar tana son jin ta bakinsa sai yayi k'asa da murya cikin ladabi yace"to Masha Allah ! zan kira Ahyaan gabanki naji idan har tana sonsa "idan har yamata kuma nayi binciken halayen sa sun min to zan bashi ita"oh wato mu bamu iya bincike ba kenan?"sannan wayace sai Anji ta bakinta?"yayi shiru"dakai nake mgn"gaskiya Hjy saidai kiyi hak'uri sai naji ta bakin yarinya tukum"zancen yanada dukiya be dameni ba"dana bama me kud'i y'ata ya wulak'anta, gara na bama me rufin Asiri ya kula da ita da rik'e mutuncinta.... Ak'ule Amma ta d'ago kanta da nufin ta sauke masa kwandon masifar dake ranta sai uncle mustapha ya shigo"wanda daga shashen mamy yake, yana can shida ita sun tasa Ahyaan Agaba"harda kukanta da rantsuwar bata son Abokinsa Ahmed "kadawo ne?"Amma ka jima"cewar mamah"beyi mgn ba ya zauna suka gaisa da Abba cikin girmamawa har saida shi Abban da ita kanta maman suka ji dad'in hakan"kafin ya kalli mama yace"Anty zainab Ina can shashensu Anty Maryam Ina fama da Ahyaan ita bata son Ahmed"tsaki Ammah taja tana fad'in matsalarta ce"ita ta sani tunda tafi son tayita zama Agida ko kuma tayi Auren fatara"na rasa wace irin zuciya ce da yarinyar nan ana nuna mata gabas tana canza hanya?"to nidai bada gummu ta gado wannan mugun halin ba....Hjy ya Isa haka pls"cewar uncle mustapha sbd yasan halinta ba k'aunar Abba takeba tuni"sosai Abin ya faranta ran Abba"yaji dad'i da Ahyaan ta nuna bata son zab'in Ammah"Anutse yace"to Hjy kinji bayanin mustapha? sbd haka bama saina tambayeta ba"tundai bata so inaga Ayi hak'uri Allah yabata Wanda yafishi"sbd zancen gaskiya bazan yima y'ata Auren dole ba"mitsssssuww! kai tashi muje"Abba beyi mgn ba ya mik'e tsaye ya fita ransa Ab'ace "uncle mustapha na ganin ya fita ya fara fad'a rai b'ace yake cewa Alamomi sun nuna zancen kika masa bayan nace ki bari nazo Ayi mgn Agabana"wai meyasa kike haka Hjy ne hjy?"so kikeyi yaya iliyasu ya dena ganin mutuncinki.....saime idan ya dena ganin mutuncin nawa Allah na tuba? wlh idan naga dama sai nace yasakar mun y'a wata tsiyace"talakan banza da wofi"mamah dai ranta yab'aci sosai tayi dai shiru sbd gudun kar tayi wani Abu cikin fushi tazo tayi dana sani...dana san haka zakiyi daban biye miki nazo ba"kuma wlh Alh (mahaifinsu) yasan kinyi hakan kinsan yadda zaku kwashe"sbd haka tashi muje gida nasan zuwa 7pm mun iso gida"Anty zainab kiyi hak'uri dan Allah "kuma hakan bazai koma maimaita kansa ba"wanda Ahyaan ta kawo in sha Allah shine za'a bata"karki damu zan kirashi ta waya"Ammah ta mik'e tsaye tana gyara mayafinta tace"idan kin gama fushin juye mun snacks d'in aleda babba na wuce da Abina"ke y'ar dad'i miji sbd shi kike wannan fushin ko?"sai kace wata uwa ya miki Arayuwa...dan Allah Hjy kiyi shiru"ta tab'e baki batace komai"mamah ta juye mata ta mik'a mata ledar ta Amsa tana musu Allah ya tsare hanya"har bakin get ta rakosu ,tana gani Ammah ta hana uncle mustapha zuwa yakira Ahyaan suyi mata sallama"saidai batace komai ba ta wuce cikin gidan"su kuma suka fita wajen get inda motarsu take..... Misalin k'arfe 4:13 pm"Ahyaan na zaune d'aki ta gama sallar la'asar kenan" fuskarta bbu walwala sbd uncle mustapha yabata haushi"hamza ya shigo d'akin da yunifoam Ajikinsa yace Anty Ahyaan yaya yace kizo yana can zaune k'ofar d'akinsa"dato kawai ta Amsa ta tashi ta maida kayanta na d'azun"ta gyara d'aurin d'an kwali ta fito"ta kalli mamy suka had'a Ido"mamy zanje wajen broth"saikin dawo Ahyaan"naji Ai sadda yaturo hamza"Amma ki dena wannan fushin tunda dai kin nuna bakyaso shikenan"fatanmu Allah yabaki nagari"duk zagaye zagaye da guje gujen masoyanki da kikeyi da lokacin Auren yayi za'a yi"d'an murmushi tayi tace ba Amma bace duk keso"uhmm kawai mamy ta furta"ita kuma ta wuce kitchen ta d'auki basket d'in data shirya warmer d'in farfesun ciki"ga plate da service spoon ta saka"ledar bread sabo guda da ba'a tab'a ba ta d'auka ta saka masa"sannan ta d'akko goron ruwa da lemo fanta na gwangwani duk ta saka ta fito"mamy dai na zaune tana kallon ta Aranta tace" sun shirya kafin su koma b'atawa kuma"Allah dai ya shiryamun yaran nan......✍️
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.