Age Mates Complete Hausa Novel
Reading file: Age_Mates_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 22 of 44
sharhi 😎
pls bana son k'orafi kunl zuba👁️👁️
wannan book d'in na kudine! idan kina buk'atar siya serious 500 normal grp vip grp 1000
Acc n 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki 08100084251
dan girman Allah da dajarar iyayenki karki mun mgn idan baki shirya siyaba
Bana son kira a what's app kawai zakimun mgn
Idan kika karantamun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitar mun Allah ya isa banyafe miki ba
#Mommyn fareesa
#Dr Nura Darma
#Ahyaan
#mr Mahuta
#AA mashi
#mu'az
#Khairiyyah
#Ammah
#Ummah
#ikkhee🧍♀️ *AGE MATES* 🧍
*39&40*
*Littafin kud'i ne!*
.......tamkar saukar Aradu ! haka Dr darma yaji kalaman mamy cikin kunnuwansa"ga wani irin mahaukacin bugu da k'irjinsa keyi fat fat fat!!!....cike da dauriya had'e da b'oye yanayin daya tsintsi kansa Aciki ya had'a haruffan guda ukku wajen furta"Allah yasa Alkhairi! yafad'a da k'yar ba tare daya Amshi ledar da mamyn ke mik'o masaba"yadai girgiza kansa Alamar baya buk'ata"daga haka ya mik'e tsaye yabar parlourn "Abincin da baiciba kenan ya wuce d'aki ya kwanta ciwon kai me tsanani ya masa sallama"sai gab da sallar magrib ya watsa ruwa ya fito sbd ya tafi masjeed"idanunsa sunyi wani irin jaa"inda da yawan mutanan dake a *gida biyu* sun gansa Alokacin da sun tabbatar da babu lafiya"gaba d'aya jinsa yakeyi wani iri kamar bamai rai ba"Ahaka ya tursasa zuciyarsa yayi sallar magrib ya zauna yafara karanta Alkur'ani me girma sannan ya jira Aka gabatar da sallar isha'i"ba laifi yaji zuciyarsa tayi sanyi"saidai tunanin Abin na'a ransa daram"ji yakeyi yanzun daya Ida tabbata ita ba tashi bace yake jin wani sonta na fusgarsa"sunan Allah kawai yake Ambata Azuciyarsa yana jin tausayin kansa"sbd yasan Abanza yake damuwa sbd wacce yakeyi Akan ta ita ba tasan yana yiba..... Awannan dare Dr darma yayi shi cikin wani irin yanayi.
mamy kuwa bata ji haushin k'in Amsar kayan saka ranar da baiyiba"hasalima tausayinsa taji"saidai tasan matar mutum kabarinsa"kuma idan har Ahyaan na sonshi da bazata kula kowa ba"iyaka zata cigaba da yimasa Addu'ar dangana da samun wacce ta fita"sbd ta jima da fahimtar matsalar yaron nata shiyasa yake yawaita Azumi "kasancewar sa me jin nauyinsu yasaka ya kasa fitowa zahiri ya nuna musu matsalarsa"Amma tana lura da komai"tasan da dalili da yasa yake yawaita yin Azumin nafilah"ta kuma tabbatar da kafaffiyar zuciyarsa ta hanashi ya bayyanah soyayyar sa ga Ahyaan"gashi ta sub'uce masa "wanda tanada yak'inin k'ilan sbd kar tace bata sonsa dan suna AGE MATE ita dashi shiyasa yak'i sanar mata da soyayyarsa...tana cikin wannan tunanin Ahyaan ta fito daga cikin d'akin ta zauna tana fad'in mamy broth be shigo bane?"ya shigo ya fita Amarya"nama bashi nasa kason yayi murna ya tafi"sai tayi d'an murmushi bata ce komai ba"Ahaka kiran Abdallah Mashi ya shigo cikin wayarta"ta harari wayar tak'i d'auka "ki d'auka mana Ahyaan" ko Ammah ce?"ah ah"ba wannan Abdallah d'in bane kullum zafin waya baya gajiya shi"Ammah kuma Ai tuni ta hak'urah mamy ta dena fushi dani"musammun data san waye Abdallah da family nasa"shiru mamy tayi Aranta tace" Anya koda Nura yace" yanama son yarinyar nan kakarta zata Amince kuwa?"ta Ayyah Aranta sbd tasan halin Ammah burinta Ahyaan ta Auri me hali"dukda tasan babu wanda zai kushe nurah Amma gani takeyi da kamar wuya Ammah ta Amince.....kallonta ta maida Akan Ahyaan fuska Ad'aure tace meye haka Ahyaan?"ki d'auka mana yanata kira ba dad'i "kamar zatayi kuka ta d'auka ta wuce bed room d'insu.....
washe gari misalin k'arfe 12:11 pm Dr darma ne zaune a office nasa yana d'an hutawa be jima da gama ganin patient's ba"yadi ne coffee brown Ajikinsa,rigar me gajeran hannu "kansa babu hula"idanunsa na b'oye cikin eye glass bak'i sbd Jan da sukayi "har yanzun beci Abinci ba"ko yau da Asuba yaje ya gaida mamy be koma komawa gidan ba sbd beson ganin Ahyaan "ji yakeyi yadda zuciyarsa tayi rauni har rungumeta zai iyayi kodan ya sami sauk'in rad'ad'in daya keji Azuciyarsa"dukda idanunsa nason ganinta,kunnuwansa nason jin sautin zazzak'ar muryarta. Amma Aganinsa yin baya da ita shine Mafi Alkhairi Agaresa "tun ruwan Lipton daya sha da safe be koma cin wani Abu ba"duk yayi zuru zuru..laptop yake dannawa Amma hankalinsa ba'a kanta yake ba"har mu'az ya shigo yayi sallama sau biyu bejiba"saida ya daki k'ofar shigowa cikin office d'in "sannan Dr darma ya Ankara dashi"ya sauke wani zazzafan huci daga bakinsa yana lumshe sexy eyes nasa yana koma bud'ewa.Abokina lafiyarka dai ko?"yafad'a yana zama kan kujera"Alhamdulillah! kawai Dr darma yafad'a Atak'aice "mu'az yace"bakada kirki tun bayan kunzo cin girkin Amarya shikenan baka koma lek'o muba?"na d'auka ma ko Ahyaan zaka kawo mana ta mana wuni " yayi shiru yak'i mgn"hakan ya k'ara tabbatar masa ba y'an k'yaliyar kawai bane Akwai damuwa Atare dashi"dama yazo yamasa k'orafi wai An sakama Ahyaan ranah itada Abdallah Mashi Amma be sani ba sai yau da safe yaga Ana fad'in saka ranar tasu Agidan TV d'in da suke Aiki"A lokacin da yaji sai yake ganin hasashen sa Akan Dr darma nason Ahyaan yakeyi ba gaskiya bane"tunda gashi zatayi Aure"saidai kuma damuwar daya zo ya samesa Aciki yanzun ya tabbatar da cewa Abinda yake zato ba haka bane....Nurah! Nurah!! ya zare eye glass d'in ya kallesa bece komai ba "wai dan Allah bazaka mun mgn ba, ka sanar mun da damuwarka ba darma?"shin ko ban Isa nasan damuwarka bane?"Ajiyar zuciya ya sauke yana girgiza kansa Ahankali yace"damuwata *Ahyaan ce*! Ita kad'ai ce damuwata Abokinah" sai yanzun na tabbatar da zuciyata tayi shishshigi,ta kuma saka nayi kuskuren Abari ya huce"gashi Allah ya kawo rabon wani"tun bayan nadawo daga London nafara jin sauye sauyen daban tab'a jiba game da ita"sai na dinga k'aryata zuciyata musammun idan Ina jin kishinta"ban Amince yes Ina son Ahyaan ba saida nafara ganin Abubakar Ibrahim mahuta yafara sonta har yasaka Aka saceni sbd ita"(ya labarta masa komai)"kafin yaci gaba da cewa" daga nan kuma sai muka dinga yawan samun matsala da ita tana neman ta rainani"Ahaka har wannan mutumin ya bayyanah Aka saka musu rana jiya dashi"ban tabbatar da nayi sake ba saida na samu labarin hakan"kuma Ashe mahutan ma yarinyar nan bilkisu dake bibiyata Ashe k'anwarsa ce sai jiya daya kawota nan babu lafiya na fahimci hakan"yaya zanyi da Raina mu'az? Ina ganin zan Amshi tayin zuwa k'asar India da Akamun last week "naje nayi course d'in wata shidda Acan"kafin na dawo nasan sunyi Aurensu"yak'are maganar cikin wani yanayi yana cije baki....Ajiyar zuciya mu'az ya saki yace"ko yanzun bazaka fidda rai ba sai An d'aura tukum"Ina maka jaje Abokinah"sbd najima da fahimtar ka mace a soyayya Ahyaan "ta kishinta da kake nunawa da kuma k'wayar idonka ta nan nagane"Amma duk idan na maka zancenta saika basar ka canza topic d'in "na jima Ina hasaso ku Amatsayin couples sbd kunyi masifar dacewa da juna"na kuma tabbatar da cewa Ahyaan kawai ce zata iya da fitinarka....dogon tsaki Dr darma yaja yana wurgo masa harara"saidai kayi hak'uri my man gaskiya na fad'a maka"Amma jin kanka yasaka ka b'oye mun"da tuni kasanar mun kana sonta da wlh munsan yadda zamuyi koda bata sonka har ka cusa soyayyar ka Azuciyarta"to san girmanka ya hanaka"saidai Ayanzun Addu'ar zab'in Alkhairi da dangana zakayi tayi"idan har Ahyaan rabonkace in sha Allah zaka sameta duk rintsi "haka idanma ba rabonka bace kome zakayi bazaka same taba "dama tunda naga suna yawan shirye shirye da Abdallah Mashi Raina yabani sonta yakeyi....pls mu'az kaje kawai "taya zaka k'aramun da wani zafin?"ya katse sa cikin zafin rai....kayi hak'uri Abokinah"Amma ka kwantar da hankalinka"yanda nasanka da jure Abu to haka zakayi karka bari Ahyaan ta fahimci ka damu ko kuma baka son tayi Aure"tunda dai ita bata san sonta kakeyi ba, zata d'auka da wani Abu"kansa kawai ya gyad'a masa bece komai ba.duk yadda mu'az yaso ya sake masa suyi y'ar fira k'iyawa yayi"hakan yasa ya barsa yatafi kawai cike da tausayinsa.....
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.