Age Mates Complete Hausa Novel
Reading file: Age_Mates_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 23 of 44
*************
Hahahahahahahahaha!!sautin wata iriyar murya marar dad'i ke tashi cikin jejin"yayinda suke zaune su biyu gaban wani shed'anin boka Acikin wani bak'in daji"wanda kafin su iso saida suka hau kwalo kwalo"kafin suzo inda bokan yake kowace tayi sartse sama da guda goma ga hannu da kuma k'afa"tunma kafin suyi masa bayani yasanar musu yasan komai. bayan ya gama dariyar tasa kafin yace "zamu karya sihirin da likitah yasaka Amayar kanki"baki washe ummah tace"yauwa boka"sannan ka taimaka ka hana faruwar Auren nan da shegiyar yarinyar nan zatayi"kuma inaso Akoreta daga wajen Aiki "idan buk'atata ta biya zan dawo kan uwar tata...hahahahaha! kin cika marar Imani "to ki sani mu Aikinmu yasha banban dana wasu"kuma Ahankali muke Abinmu ba farar d'aya ba"koke sai kin kai kusan sati d'aya ko kwana biyar kafin ki dena warin jab'a"Aure kuma zamu lalatashi"Eh boka Asa mata tsanarsa da k'insa Azuciyarta ita yarinyar...bazai yuyuba! ta zaro Ido "ya kece da dariya kafin yaci gaba da cewa"yanzun yarinyar jikinta Ashirye yake da Addu'oin tsari"kuma tana Azkhar "saidai zamuyi Aikin Akan shi yaron dazai Aureta"batun Aiki shima zamuyi Abinda za'a koreta"saidai komai daki daki zaizo. Amma boka...ku Ajiye sadaka ku tafi , Akwai masu son isowa nan suma suna hanya"ya fad'a yana gimtse fuska"hannunta na kirma ta Ajiye masa kud'i kusan dubu 50" K! kud'inki nera dubu d'ari ne"kuma kinzo dasu"haka zaki Ajiye ki wuce"Aiki ukku za'a maki"sbd haka idan baki shirya ba tafi ki bani waje"uwale tace haba luba ki Ajiye muje mana"ummah hannu na kirma ta zaro cikon ta Ajiye"Atake hayak'i yacika wajen,suka kama tari"ku rintse Ido sannan ku bud'e"da sauri suka rintse,suka kuma koma bud'ewa ,sai gasu gaban kwalo kwalo "ba k'aramin tsorata ummah tayiba"yayinda uwale ta kama dariya sbd batayi mamaki ba"zuwanta Anan na ukku ne Ayau"na farko zuwan kanta ne,na biyu wata ta rako,yanzun ma ta koma rakowar Akaro na ukku.sai zuzuta Aikin malamin uwale keyi har suka shiga cikin kwalo kwalo ya tsallake ruwan dasu"yayinda luba kejinta cikin farin ciki"dama burunta shine rayuwar Ahyaan ta k'untata"so takeyi Ab'ata komai Akanta sannan tadawo kan mama"sbd itama ba k'yaleta zata yiba.....
misalin k'arfe 10:11 am na safiyar yau Asabar "garin yayi lullumi sbd hadarin dake A sararin samaniya"ga iska me dad'i na ratsa jiki"Ahyaan ta fito rik'e da wata k'aramar leda fara ta shopping Ahannunta"tana sanye da doguwar riga ta Atamfa red& white,sai mini hijab red colour"wacce tayi masifar yi mata kyau"ta k'awata kyakykyawar Choco face nata"yayinda plate shoes ne sanye Ak'afarta.sai sauri takeyi da k'yar mamy ta barta zataje gun saloon.....tana k'ok'arin fitowa daga k'ofar shiga shashen nasu shi kuma yana k'ok'arin shigowa! kusan fad'a masa Ajiki tayi"cikin hanzari tayi baya kamar zata fad'i "Dr darma yayi saurin rok'o hannayenta"Atake idanuwansu suka sark'e "Ahyaan dake jin wani iri Ajikinta sbd hannayenta daya rik'e"saita janye idanuwanta daga cikin nasa ta fara k'ok'arin zare hannayenta daya rik'e....ya kafeta da Ido tamkar yau ne ya fara ganinta"yana sanye da wondo 3 quarter da t shirt me gajeran hannu wacce ta fidda shape d'in body building d'insa"ya k'ara haske da frash saidai fuskarsa da rama har yanzun "ga k'asumba ta cika masa fuska"be jima ba da tashi daga bacci ba ya watso ruwa ya shigo cikin gidan sbd yayi break fast"yana kuma fatan Allah yasa karya ganta"gashi Addu'ar tasa bata karb'uba.....pls ka cika ni naje broth "ta fad'a tana b'ata fuska"cikata d'in yayi sbd shima wani irin Abu yaji yana fusgarsa daya rik'e hannuwan nata"zuciyarsa na ingizashi daya rungumeta koya sami sassauci, Amma saiya dake....Ina zakije?"ya fad'a tamkar bayaso"kallonsa ta komayi saita turo baki tace"wai broth tamkar baka duniyar"kamar ya?"hmm ! rabon dana ganka harna manta ni"ta k'are maganar cikin mamaki tana d'auke Idanunta daga kansa"sbd ganin kusan 2 weeks rabonta dashi"wanda yayi daidai da wata biyu cif kenan da saka ranar su itada Abdallah Mashi "yawanci duk sadda zai shigo gidan da Asuba"ko bacci takeyi ko tana sallah"be kuma sake shigowa sai k'arfe 2:30 pm "lokacin kuma tadawo daga office tana bacci"sbd data dawo tayi sallah kwanciya takeyi sai la'asar take tashi"shiyasa sai tayi har sati biyu ko d'aya bata gansaba....uhmmm !idan kin damu da son ganin nawa Ai kinsan inda nake kwana ko?"sai tayi shiru,tarama rab'a gefensa ta wuce"ya d'age kafad'a irin ko Ajikinsa d'in nan "yama d'auka koda motarta zata fita"da wannan tunanin yayi gaba Abinsa"saidai hoton fuskarta na'a cikin zuciyarsa "gaba d'aya yau ta masa wani irin kyau"ga wata k'uruciya daya gani Atare da ita "sai ta masa kamar y'ar 20yrs.... Ahyaan na fitowa ta wuce bakin titi ta tari nafef"kai tsaye zainab beauty saloon Aka Ajiyeta "suna isowa ta sallami me nafef d'in ta wuce ciki.saida ta d'auki kusan Awa guda Aciki sannan ta fito sbd ta samu layi"daga gaban shagon taga me nafef ya kara gefe"har zata wuce taji yace Hjy tafiya zakiyi?"Eh "Ina zakije?"*baya jidda road*"to shikenan shigo muje kud'inki 500 ne"okay ta fad'a tana shigowa"basufi mintina 5 suna tafiya ba wata mace ta tsaidasu"tana sanye da face mask da eye glass bak'i"haka nan Ahyaan taji fad'uwar gaba da suka tsaya "saita dake kawai tana kallon matar da sauraren inda tace za'a kaita"wansa kusa da Anguwar sune"bayan sun gama mgn dame nafef saita shigo"da sauri Ahyaan ta kalleta sbd k'amshin turarenta yamata kama da wani k'amshi data tab'a ji"sai kawai ta basar taci gaba da kallon waje suna tafiya....can kawai taji an dafa kafad'arta "ta waigo da sauri"Ikkhee dake zaune gefenta ta watso mata wata powder fara"innalillahi wa inna ilaihir raju'un! ta furta tana tari"kasancewar jininta me k'arfi ne sai hodar batayi saurin gusar mata da numfashi ba"tana jin dariyar Ikkhee da ganinta bibbiyu"saita lumshe lulu eyes d'inta, Adaidai lokacin kuma Ikkhee ta kira Mr mahuta yana d'auka tace"yaya Abubakar gata nan mun kamota muna hanya ne...iya nan Ahyaan taji daga haka bata koma sanin inda kanta yake ba.......✍️
🫣🤫🤔 Sharhi kawai🤓
wannan book d'in na kudine! idan kina buk'atar siya serious 500 normal grp vip grp 1000
Acc n 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki 08100084251
dan girman Allah da dajarar iyayenki karki mun mgn idan baki shirya siyaba
Bana son kira a what's app kawai zakimun mgn
Idan kika karantamun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitar mun Allah ya isa banyafe miki ba
#Mommyn fareesa
#Dr Nura Darma
#Ahyaan
#mr Mahuta
#AA mashi
#mu'az
#Khairiyyah
#Ammah
#Ummah
#ikkhee
🧍 *AGE MATES* 🧍♀️
*41&42*
*Littafin kud'i ne!*
.......tafiya suka cigaba dayi me Nisa, wacce Ak'allah sun kwashe kusan mintina 30 suna yinta"daga bisani har suka iso wani gidan gona da Aka zagaye da get"daga can ciki Akwai gida d'an flat"wanda Acan Mr mahuta ke watsewarsa da matan banza"Dan ba kowa yasan yana bariki ba"yana yin Abinsa Ab'oye"kasancewar me gadi yasan da zuwansu saiya bud'e musu get suka shigo"Adaidai bakin k'ofar shiga parlourn suka tsaya"Ikkhee ta d'auki Ahyaan ta shiga da ita ciki ta kwantar da ita saman kujerah 3seeter tana sakin wani shu'umin murmushi"yayinda me nafef yayi gaba...bayan ta zauna ta d'auki wayarta ta fara kiran Mr mahuta"bugu ukku ya d'auka yana fad'in ya Ake ciki ne?"saida ta yamutsa fuska kafin tace" gata nan kwance bata san inda kanta yake ba"okay idan ta farka ki kirani zan k'araso "bayan na k'araso sai ke ki tafi gida"da komai ya kammala zan saka Amayar da ita titin Anguwar su"okay tace tana yanke wayar"kafin ta zuge hand bag nata ta zaro wasu kwalabe k'anana ta fara shaye shayenta.daga nan bacci ya d'auketa "sai wajen k'arfe 1:15 pm ta farka Afurgice sbd ganin bacci ya d'auketa....wata nauyayyar Ajiyar zuciya ta saki sbd ganin har lokacin Ahyaan na kwance kamar marar rai"ta yamutsa fuska had'e da tab'e baki "Adaidai lokacin wayarta tayi ringing"ta d'auka tana fad'in yaya Abubakar bata farkaba"nafiso kazo yanzun d'in"bazan ma tafi ba sai naga komai ya kammala"idan harba gani nayi ba kasaka Anyi raping nata hankalina bazai kwantaba....shiru tayi sbd ganin Ahyaan na motsi"wacce tun sadda wayar Ikhkheen ta fara ringing ta farka"tayi dai tsit sbd taji meye zatace idan ta d'auka?"saidai jin ta Ambaci raping ya saka k'irjinta bugawa "ba shiri tafara motsi"da sauri Ikkhee ta gyara face mask d'inta tana fad'in ta farka ma"daga haka ta yanke wayar..... *innalillahi wa inna ilaihir raju'un! La'ilaha illallah Antassubaha naka inni kuttu Minal zalimin*" cewar Ahyaan tana tashi zaune ta kalli Ikkhee"ta kalli kanta da cikin parlourn "kafin tace"bewar Allah lafiya?"meye ma'anar ganina Anan da nayi??uhmmm ! Ayanzun bada jumawa ba kuwa zakiga ma'anar hakan"saidai karki damu muba masu garkuwa da mutane ko kuma kashe mutum bane"shiru Ahyaan tayi k'irjinta nata fat fat fat!! sai kuma ta sauke Ajiyar zuciya Ab'oye data d'an lalibi gefen Aljihun rigar jikinta taji nokia d'inta"kallon Ikkhee dake zaune tana girgiza k'afafuwanta tayi kafin tace "Ina toilet zan kama ruwa nayi Alwallah?"banza ta mata tak'i kallonta"sai Ahyaan ta tab'e baki tare da cewa"inaso ki sani! ganina Anan tare dake bashike nufin kinci nassara Akan koma wane irin k'uduri kike dashi Akaina ba."sannan dakin bud'e fuskar taki na ganki ta haka zan tabbatar ke d'in tantiriya ce kum.....shiru tayi sbd shigowar wasu katti su ukku da makamai Ahannunsu "saida taji k'irjinta ya buga"saidai ta dake tana koma maimaita kalmar Ina toilet?"da hannu kawai Ikkhee ta nuna mata tana tabe baki....Ina jakarta?"cewar k'ato guda"babu jaka Atare da ita,gadai ledar da muka gani wajenta"ta fad'a Ahyaan na k'ok'arin shiga toilet d'in....kin tabbata babu waya Atare da ita?"da sauri Ahyaan ta shige toilet d'in ta rufe da key d'in dake jiki bataji wace Amsa Ikkhee tabama y'an daban ba....hannunta na kirma ta zaro wayar ta fara rubuta ma Dr darma sak'o kamar haka.....*broth! ka ceci rayuwata" Ina cikin tashin hankali, wasune suka saceni a hanyata ta dawowa gida"naji suna fad'in zasu saka Ayi raping d'ina. Pls kayi wani Abu Akai karna rasa martabata"naji suna kiran sunan wani Abubakar ta waya "kaceci rayuwata dan Allah,sannan karka kirani sbd karsu gane*......tana gama rubutawa ta tura masa hannunta na kirma"saida taga sak'on ya shiga sannan ta sauke numfashi"shima AA Mashi ta fara tura masa sak'o makamancin irin wanda ta turama Dr darma "saidai nashi gajere ne bamai tsayi ba.tun kafin ta gama sending d'in takejin suna mata wani mahaukacin knocking"tana gama sending ta maida wayar cikin rigar mama dake jikinta"sbd bata so ta kashe wayar ko kuma su san wayar na hannunta "sbd jikinta yabata daga Dr darma har Abdallah Mashi zasuyi treaking su gano inda take... tana gama tura wayar cikin bra ta wanke fuska da hannu da k'afa"sbd tace Alwallah tayi"bacin fad'uwa bbu Abinda gabanta keyi ga zulumi had'e da tsoro duk mak'ale Aranta"saidai tana so tasan meye ta tsare musu Arayuwa da suka zab'i su kawota Anan su cutar da ita?"tana wannan tunanin ta bud'e k'ofar Aranta tana Addu'ar da duk tazo mata Abaki....wani irin mugun kallo Ikkhee ta watso mata irin na tuhuma"saidai da yake Ahyaan tafita esperions bata bari tayi mgn ba, saita kauda kanta tana fad'in "mena muku kuma ku suwaye,me kuke nema wajena??? bamuda Amsar wannan tambayar"sallah kuma baza kiyi ba sbd banma yarda da shigarki a toilet ba"kamar ya?"ta fad'a cikin fad'uwar gaba"Ikkhee batayi mgn ba ta fisgo hannunta zata zare mata hijab nata"Ahyaan ta hankad'ata,tayi k'asa ta fad'i "K! wani k'ato yadako mata tsawa"batayi mgn ba tayi tsaye tana huci tana k'ara gyara hijab nata"ki tsaya ta dubaki ko kuma kiyi nadama"tashi ki dubata"Ikkhee taja tsaki tana tashi zaune ta matso gabanta"da kanta ta zare hijab nata duk suka bita da kallo"sai lokacin Ikkhee ta lura da rigar jikinta me Aljihu ce saita fara dubawa Amma bataga komai ba"yayinda Ahyaan zuciyarta keta bugawa tana Addu'ar da duk tazo mata....babu waya Ajikinta "Ahyaan ta tab'e baki tana maida hijab nata"k'ato guda yace ke karkiyi mana taurin kai yanzun na sareki na sari banza"sallah ki bari idan kin koma inda kika fito kyayi Abinki"Anan yamiki kama da inda zakiyi sallah?"shiru tayi musu sbd dama ita ba Alwallah tayi ba"hasalima batada nutsuwar da zatayi sallah tana Acikin wannan tsaka me wuyar datake"k'asa saman carpet ta zauna ta rak'ub'e tana Am batom sunan Allah"batayi zaman mintina 5 ba saiga wani namiji ya shigo da wata roba ta swan suka mik'a ma Ikkhee"ki bata tasha"sannan yace"idan tasha ki fito yana bakin get ki samesa"wata iriyar zabura Ahyaan tayi k'irjinta na tsananta bugawa Atake ta fad'i sumamma sbd furgitan da kalaman d'an Aiken sukayi Azuciyarta.....
Afannin su mamy kuwa tayi mamakin ganin Dr darma ya shigo da walwala Adaidai lokacin "sai kuma ranta yabata tabbas ya had'e da Ahyaan da zata fita.tunda kafin ya shigo yanzun ta fita"saidai batace masa komai ba"shi kuma ya zauna yamata barka da gida sannan ya wuce wajen dining table yaja kujerah ya zauna "d'an tak'aitaccen murmushi yasaki sbd ransa yabashi Ahyaan ce ta had'a break fast d'in"sosai yazuba Abinda yakeda buk'ata yaci ya k'oshi "koda ya gama be fitaba saima zama yayi ya kunnah kallo"yayinda mamy ke kitchen tana miya"har 12: pm ta wuce yana nan yana kuma mamakin meyasa Ahyaan bata dawo ba?"yana so ya tambayi mamy kodai ta biya wani waje ,Amma kuma yana jin kar tayi zaton wani abu sbd yanzun ba sosai yake shiga sabgartaba saiya kama"to itama mamyn tayi mamakin ganin har 12 tayi bata dawo ba"sai ta bari idan d'aya tayi bata dawo ba zata kirata taji lafiya6?...."Dr darma kuma k'arfe d'aya na idawa ya fito tsakar gidan yayi Alwallah ya tafi masjeed....tun bayan ya gama sallar yana Azkhar yaji Alamar shigowar text message"har zaiyi biris dashi sbd wasu duk y'an mata ne masu turo tambayoyi"sai kuma zuciyarsa yaji tak'i nutsuwa"kawai saiya zaro wayar tafara dubawa....be bari yakawo k'arshe ba ya zaro Ido cikin tsinkewar zuciya had'e dajin wani irin k'aimi da tasowar mazan taka ya maida wayar cikin Aljihun wondonsa yana furta innalillahi wa inna ilaihir raju'un! "Arikice ya baro masjeed d'in harda gudunsa ya nufo cikin gidan sbd basuda Nisa da masjeed d'in ,Anan cikin layin yake"kai tsaye d'akinsa ya bud'e ya shiga ya nufi saman bed side drower ya d'auki laptop d'insa ya saka number nata ya fara treaking"cikin sa'a ya gano Anguwar da wajen da suke "yana huci yace"wane Abubakar ne inba mahuta ba?...."zan nuna masa cewa shi k'aramin d'an iska ne"yak'are maganar yana fitowa daga cikin d'akin, ko key be sakaba ya jawo k'ofar ya nufi wajen motarsa rik'e da laptop d'in ya shiga yajata Ahaukace da wani irin mahaukacin gudu...yana hanya mu'az ya kirashi "yaja tsaki yak'i d'auka"ganin yak'i dena kiran nasa ya saka ya d'auka "Abokinah irin wannan sharewa haka?madam ce babu lafiya shine nakeso kazo gida ka dubata pls l...."babu lafiya mu'az"Mr mahuta yasaka Ansace Ahyaan! Innalillahi wa inna ilaihir raju'un! wlh kuwa inama hanya zanje wajensu na gano inda suke danayi treaking"sbd ta turomun text message yanzun.... Amma darma kaje kai d'aya? bayan kasan yana tare da y'an daba"kamata yayi Ai kaje police station kayi report ko?"banida wannan lokacin mu'az"indai zan ceto rayuwar Ahyaan koda nizan rasa tawa rayuwar ba damuwa"na sanar maka ne sbd koda bandawo ba kasanarwa su daddy....yana fad'in hakan ya yanke wayar.
tafiyar mintina 20 ta iso dashi Anguwar "ba mutane sosai sbd duk dajine sai gidajen da Aka fara gini Aka dena"gaba d'aya yama rasa Ina zaiyi?"sai Akaci sa'a wata had'ad'd'iyar zukek'iyar mota ta wuce ta gabansa"Atare ransa yabashi motar nan ta Mr mahuta ce"saida tayi Nisa saiya cigaba dabin sawun motar"daga bisani yayi parking yakoma treaking number"Adaidai nan wajejen Ake nuna masa Alamar number da yake treaking d'in tana nan"ya sauke Ajiyar zuciya gabansa gadi yafito daga cikin motar yayi lock nata"ya doshi get house d'in da ransa yabashi nan ne"cikin sa'a yaturo k'ofar get d'in saiya bud'e ya hango me gadi zaune,ga motar daya biyo fake a gefe"babu wani d'ar yanufi inda me gadin yake ya bashi hannu sukayi musabuha kafin yace"pls ko yallab'ai na ciki?"munyi waya yanzun yacemun yana hanya"Eh yanzun ya shigo Amma yasan da zuwan naka ne?"Eh yasani"dato kawai me gadin ya Amsa sbd bama yaro bane"Dr darma kuwa k'irjinsa keta bugawa babu wani tsoro yadoshi wata kwana da zata sadaka da hanyar parlourn gidan"yana shan kwanar ya hango Mr mahuta tsaye shida wani saurayi yana mik'a masa wata roba ta swan suna mgn"saidai bejin me suke fad'a....tsaye yayi cak yana tunani"sai kuma yasaki wani Miskilin murmushi irin na tsantsar mugunta yaci gaba da tunkaro su "kan idonsa saurayin ya shiga cikin parlourn "Mr mahuta na juyowa yayi Arba da Dr darma na nufo inda yake"gabansa ya yanke yafad'i! ya zaro Ido yana yin wata zabura"Dr darma yakoma sakin murmushi Akaro na biyu yana zaro wayarsa da mu'az ke kira"hellow! sai kuma yace"ta wannan layin nawa zakubi diddik'i harku gane inda muke"dakun iso zakuga motata gaban get d'in gidan me orange d'in get"ya fad'a yana yanke wayar"saiga katti ukku sun fito daga cikin parlourn suna tunkarosa da manyan makamai Ahannunsu"yayinda Mr mahuta ya wuce ciki da sauri cikin tashin hankali yana tunanin yaya Akayi wannan gadararren yaron yagano inda suke??"yana shigowa ya sami Ahyaan da Ikkhee na dambe sbd tak'i yadda ta bata ruwan d'aya turo dasu Abata"wanda dama tun d'azun data sume , Ikkheen ta yayyafa mata ruwa ta farka shine k'attin suka nuna mata maka mai wai saita sha ruwan"shine tak'i yadda har suka fara dambe da ita"suna cikin damben Mr mahuta yakira k'attin"suna fita Ahyaan ta fisge face mask d'inta"Atake fuskarta ta bayyanah"Ahyaan ta kama murmushi ta matso ta finciketa ta d'auketa da wani gigitaccen mari "suka kacema da dambe"Adaidai nan Mr mahuta ya shigo yabisu da kallo sbd ganin Ahyaan ta haye saman Ikkhee tanata jibgarta cikin zafin zuciya "wanda ita kanta Ahyaan d'in bata san tanada wannan zuciyar ba....bilkisu !meye haka kukeyi?"da sauri Ahyaan ta d'agata ta juyo suka had'a Ido da Mr mahuta"gabanta yafad'i ta zaro Ido tana mik'ewa tsaye "Ikkhee tayi kukan kura zata cafkota Mr mahuta yadakar da ita"hakan yayi daidai da shigowar Dr darma cikin parlourn "daga tsakkiyar tafin hannunsa na d'igar jini"da Alama yasha Artabu da k'attin ne"Ahyaan na ganinsa ta saki kuka da gudu ta nufesa"tun kafin ta iso yabud'e mata hannayensa"tana isowa ta fad'a jikinsa ta k'ank'amesa tana fad'in broth kai kad'ai kazo?"ciwo suka jimaka ?"ta fad'a tana kama hannun nasa me zubar da jinin tana dubawa"be iya furta komai ba dukda suna cikin yanayin tashin hankali saida yaji tsikar jikinsa ta tashi da wannan rungumar da Ahyaan ta masa....saidai ya dake sosai ,yabi Mr mahuta da kallo sbd ganin yana sai tashi da bindiga"murmushi ya saki me ciwo kafin yace"Ina mazan suke?"daga kai har su duk lusarai ne banga namiji Acikin kuba"kaji kunya daka tsaya had'a kai da jahilar k'anwarka da shaye shaye ya gama burkitama brain"kai kana ganin zakaci nassara Akan mu ko?inaso kasani duk wanda yadogara ga Allah in sha Allah saiya isar masa da komai"wannan bindigar banzan bazai saka na fasa fad'an Abinda nayi niyaba"nan gaba kad'an zaka san lallai kayi kuskuran had'o wasanka da d'an karamin yaro,kuma yaronma talaka"karka manta last time daka saka aka saceni na barka"saidai tunda har Abin naka yazo kan bestie nah! Uhmmm"ya k'are maganar yana d'allah yatsun hannunsa guda biyu cike da izzah yana hura hanci"itadai Ahyaan na mak'ale Ajikinsa tana mamakin izzarsa da rashin tsoronsa"dukda dama tasan jarumi ne beda tsoro Amma tayi mamaki dayaga bindiga be tsorotaba....ke kuma tunkiya dak'ik'iya muna mata"dake za'a had'a baki Aci mutuncin y'ar uwarki mace"saidai banyi mamaki ba sbd dama duk d'an shaye shaye beda maraba da Dabba.....kaiiiiiiii! ya isheka haka"kana zaton ka Isa ka shigo har nan ka sameni kana mun wannan burgan banzan ka kuma fita salin Alin?. Idan ma kana wannan tunanin to kayi gaggawar denawa"da kai da ita Ayau....shiru yayi ya kama b'abb'aka dariya dukda maganganun Dr darma na sukar zuciyarsa "Amma saiya basar yakama dariyar k'eta sbd ganin wasu y'an daba su biyar sun shigo cikin parlourn"wanda yanzun yamusu flashing suka iso"yayinda Ikkhee ke zaune tana kallonsu tana kuma tuninin dama yayanta yasan Dr darma kenan?"shine yayi Amfani da ita sbd yacimmah wata manufarsa.....me kuke jira dashi ne?"inaso ku farka mun cikin banza"kuyi gutsi gutsi da namansa"Dr darma yayi saurin cika Ahyaan data fara kuka sbd Azatonta bazai iya da k'attin ba "suna da yawa ga ciwo yaji ga kuma bindiga Ahannun Mr mahuta"wani irin mugun kallon tsana ta watsoma Mr mahuta tare da fad'in ban tab'a jin tsanar waniba kamar yadda nakejin taka" in sha Allah saika wulak'anta a idon duniya"mugu ! Azzalimi.....shiru tayi sbd ganin Dr darma da k'attin suna Artabu"Mr mahuta na tsaye yana kallonsu gabansa na fad'uwa tana mamakin jarumtar yaron"yayinda Ikkhee ke zaune tana binsa da kallon tuhuma"Adaidai lokacin sukaji Harbin bindiga da jiniyar motar y'an sanda"Antar cikin Mr mahuta ta kad'a"yayinda k'attin suka saki makamansu zasu gudu"da sauri Ahyaan ta duk'a ta d'auki wani k'arfe ta jefi Mr mahuta dake k'ok'arin bud'e wata k'ofa shida Ikkhee zasu gudu"Adaidai gwiwar k'afarsa ta dama k'arfen ya sauka"yasaki k'ara yafad'i "yayinda Dr darma ya rik'e k'atti biyu"sauran suka fita da niyar su gudu"sai sukayi clashing da polices kusan guda 12 dake k'ok'arin shigowa cikin parlourn ,Atake suka sai tasu da bindiga"yayinda wasu suka shigo tare da mu'az"Dr darma ya hankad'a k'attin suka fad'i k'asa "mu'az kuwa da hannu yanuna musu Mr mahuta dake yashe k'asa rik'e da gwiwar k'afarsa"yayinda Ikkhee keta zare Ido gabanta na dukan Tara Tara.
gaba d'aya Aka kamasu suka fito daga cikin parlourn "Ahyaan kuwa hijab nata Dr darma ya matso gabanta ya gyara mata suna kallon cikin idon juna cikin wani yanayi "Idanunta cike da k'wallah"saiya girgiza mata kansa Alamar kar tayi kuka"ta lumshe Ido ta koma bud'ewa"murya can k'asa tace"broth sannu da k'ok'ari kaji?"yanzun sai muje kayi dressing d'in hannun naka ko?"kansa kawai ya gyad'a mata beyi mgn ba"haka kawai ta rungumesa ta rushe da kuka"shidai mu'az na tsaye yana kallon su yana d'an murmushi"Adaidai lokacin kuma AA Mashi da wasu police suka shigo cikin parlourn.....✍️
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.