Complete Hausa Novels

Age Mates Complete Hausa Novel

Reading file: Age_Mates_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 41 of 44

**************
Kimanin sati biyu kenan da tarewar Ahyaan Agidan Dr darma"bbu Abinda sukeyi sai zuba love"wanka ,cin Abinci,Aikace Aikace duk tare sukeyi"sai jiya daya koma Aiki mamy ta turo wata dattijuwa da zata dinga yimata Aiki"sbd Azatonta itama Ahyaan d'in ta koma wajen Aiki "sosai itada Dr darma sukayi kyau da haske"saidai batayi k'iba ba sai k'ugunta da yayi mugun girma har tana mamaki.sbd wasu kayan musammun siket ko gownt basu shigarta"ni kuwa nace tunda Dr na bada himma Ai dole ki bud'e...tunda tazo gidan uban gayyar baya sarara mata a shimfid'a "daurewa kawai takeyi"wani lokacin saita samasa kuka yake k'yaleta"kusan kullum saiya kwanta da ita sau biyu"har yanzun tak'i sabawa"ga kankana da zuma da kusan duk dare saiya bata"tun bata san manufarsa na bata itaba harma ta fahimta"saidai bata k'in sha zata Amsa tasha duk sanda yabata....tun ranar da zai koma office Ahyaan keson yi masa maganar nata zuwa Aikin Amma tana jin tsoron karta masa mgn ya nuna yaji zafi"saita hak'ura musammun data tuna da nasihar da mama ta mata"ki kasance me faranta ran mijinki,ki kasance idan yanada damuwa zaki shawo kansa har yayi farin ciki"yawan b'ata ma miji rai yana sawa ya rage sonki"duk idan ta tuna da haka sai taji bazata iya tambayarsa ba"kusan kullum sai sunyi waya da mamy....Afannin mubarak kuwa har Anyi zaman kotu An yanke masa hukuncin shekara10 Agidan yari"bisa Adalci da sassauci sbd yana cikin maye ya Aikata laifin.sashen su ummah kuwa tun kwananta ukku Agidan ta fara na damar baro d'akinta musammun sbd Abu biyu"kewar yaranta da kuma rashin samun ingantaccen Abinci" bbu wadataccen Abinci me rai da lafiya"sune babban Abinda yafara yimata karan tsaye"sai kuma kukan dabbobi da warin kashinsu da fitsarin su"idan tayi k'orafi inna salame tayi mata tas"ranar da taji irin hukuncin da aka yanke ma Mubarak Tasha kuka kamar ba gobe.ga Abba ya hana su Khadija zuwa su ganta"ya Amshe wayar Khadija d'in"bayan ya musu Jan Idon mama itace uwarsu yanzun, suka raina masa mata wlh zai iya tsinewa mutum"ita dai mamah iya kyautata tana musu"itama khadijah ba laifi idan taga Asma'u na taya maman Aiki tana kamawa"Abban kuma ba laifi mama na kwantar masa da hankali yad'an rage damuwa....yau yakama Wednesday "Dr darma na tsaye gaban dressing mirror"yaci zazzafan wanka na k'ananun kaya" Ahyaan na kwance saman bayansa tanata zuba masa shagwab'a son ransa"be jima da gama yamutsar taba sukayi wanka"Ajiye cum d'in hannunsa yayi bayan yagama taje sumar kansa dataji gyara"cikin taushin muryansa yace"bestie kefa kikace baraki jeba sbd mamy zatazo yau"shine kuma yanzun kike rigima?"Toba saika fasa zuwa ba mujira mamyn gaba d'aya ko?"ah ah ba'a yi hakaba"kota zo wareni gefe zakuyi tunda mamy bata had'aki da kowa ba"sannan kinga tun bayan Auren ban jebafa sai wannan satin"kuma na sanar musu zanje "rashin zuwan nawa bbu isasshiyar hujjah kinga zaija suji ba dad'i ko?"tayi shiru ta janye jikinta daga nasa ta koma gefen bed ta zauna"p cap d'insa ya d'auka ya iso gabanta ya duk'a ya kama hannunta yana jifarta da tattausan murmushi murya can k'asa yace"kar kiyi fushi da Aljannar ki bestie "samun p cap d'in na wuce hud'u harda kwata"wlh na miki Alk'awarin bbu ruwana da kowace mace kamar yadda kika sani Abaya to har yanzun haka nake"nida nake da kamar ke Aminatu babbar budurwa kuma sarauniyar mata towa zan kallah Awaje??kuma saiki fad'amun meye kikeso idan nadawo na miki tsaraba dashi ko?"saida ta turo baki kafin ta Amshi hular ta saka masa taja masa karan hancinsa murmushi na sub'uce mata"yayi dariya tare da cewa rakinki yayi yawa bestie"gaki da zak'i kamar zuma pls da dare karki mun raki kinji ko?"turashi ta dinga yi tak'i yin mgn"ya sumbaci lips nata da goshinta kafin ya mik'e tsaye ya duk'a ya d'auketa "ta saki k'ara tana zillewa"sai kuma ta kama murmushi dataga yana wani nishi Alamar ta masa nauyi"wlh broth kadinga Adalci"nice zance kanada nauyi "nida ko k'iba banyi ba"Eh bakiyiba Amma nan yayi kibar ko?"yafad'a yana shafa mazaunanta"ta bige masa hannu"ya direta bakin k'ofar tare da cewa saina dawo mr nurah darma"ta saki murmushi tare da cewa Allah yatsare mun kai"Allah yasa duk wacce ta kalleka ta makance"ya dinga dariya ya rungumeta Ahankali yace "kamar karna tafi na barki bestie"ke d'in farin cika nace"ilove you! Ilove you too "ya fad'a yana cikata yafita cikin farin ciki"ita kuma ta dawo cikin parlourn ta zauna "ko zaman mintina 5 batayi ba taji knocking"ta je ta bud'e batare data tambayi ko waye ba"tana bud'ewa saiga mamy tsaye itada khaleel daya kawota da mashin tazo taga d'akin Ahyaan"ihun murna tayi ta rungume mamyn suna dariya gaba d'aya suka wuce cikin parlourn....✍️

wannan book d'in na kudine! idan kina buk'atar siya serious 500 normal grp vip grp 1000
Acc n 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK kituro shaidar biyanki 08100084251

dan girman Allah da dajarar iyayenki karki mun mgn idan baki shirya siyaba

Bana son kira a what's app kawai zakimun mgn

Idan kika karantamun book baki biyani hakk'ina ba ko kika siya kika fitar mun Allah ya isa banyafe miki ba🧍 *AGE MATES* 🧍‍♀️

*75&76*

*Littafin kud'i ne!*

........saida Ahyaan ta cika gaban mamy da Abubuwan motsa baki sannan ta zauna suka fara gaisawa.gaba d'aya yau saita tsintsi kanta da jin nauyin mamyn"gashi ta lura tanata kallonta"saita sunkuyar dakai k'asa tana danna waya "mamy kuwa taji dad'in ganin yadda ta k'ara kyau,haske ,da murjewar jiki"saidai taga bata k'ara k'iba ba sai uban hips data k'ara "tun Anan ta fahimci lallai d'an nata fitinanne ne lamba d'aya"Ajiye cup d'in hannunta tayi tare da cewa" ni Ahyaan da baki kawo Abincin nan ba sbd Ak'oshe nake"kuma kwanaki kin kai mana Abinci balle kice sai naci girkinki"haba mamy niban yardaba "dan Allah ko kad'an ne kici"ta fad'a cikin shagwab'a"khaleel dake zaune yana danna waya ya matso ya d'auki robar lemo yana tashi tsaye yace"zanje nadawo mamy"karfa kajima kazo mu wuce gida"wai mamy basai dare zaki tafiba?haba Ahyaan zaman me zan muku Agida harna kai dare?"danma kin matsa ne Alh yace Eh yaka mata nazo naga d'akinki "ta fad'a tana gyara zamanta tace"kin koma wajen Aiki ne?"ah ah mamy zan dai koma d'in"yo meyasa baki koma ba?"tayi d'an jim sai kuma tace"dama Ina jiran broth ne yace" zaya nema mun transfer d'in wajen aiki.dato kawai mamy ta Amsa taci gaba dacin Abincin suna fira jefi jefi harta idar"tana fad'an khaleel shiru be dawo ba saiga shi ya shigo"Ahyaan ta wuce d'aki ta sako sabilai na wanka cikin ledar shopping ta mik'a ma khaleel tare da cewa rik'e ma mamy"in sha Allah week end zamuzo da broth"Abaya cewafa yayi duk week end zai barni na dinga zuwa shine banjeba"mamy na murmushi tace"wannan dai week end d'in zai kawoki"ranar friday kuma Autah na zaizo sbd yayi kewarki"ko jiya saida nace masa Akawo Auta yace sai week end "karki damu wata ran saima kin gaji dasu"Amma Ahyaan bazan Amsaba ba d'awainiya nazo na kamiki ba....daure fuska tayi ta juya baya"shikenan nagode Allah yayi muku Albarka"kai kaje gani nan zuwa"ta fad'a tana kallon khaleel"bayan ya fita tace"Ahyaan Ina fatan babu wata matsala ko?"idan kuma Akwai ki sanar mun dan Allah karki ji kunya "niba surukarki bace ni uwace Agareki"na sani mamy wlh bbu komai "to Alhamdulillah Ayita hak'uri dan Allah"in sha Allah"ta fad'a tana yo mata rakkiya har bakin k'ofar parlourn "bayan ta fita ta rufe k'ofar ta dawo ta zauna cikin parlourn tana danna waya.....k'arfe 6:48 pm Dr darma yaturo k'ofar parlourn ya shigo rik'e da manyan ledoji Ahannunsa fuskarsa k'awace da tattausan murmushi yana kallon gimbiyar tasa data gaji da jiransa....babbar budurwa bana fushi bane taso ki tarbi babyn ko ? ko kuma nace ogah?"sbd haka naji magulmatan mata na cewa maza wai ogah"murmushi ya sub'uce mata ta d'an kallesa ta gallah masa harara"sorry Amun dago wlh saida nayi da gaske na samu na kufto gida sbd bana so ki gaji da jirana"dukda nasan kina tare da mamy "na kirata tace bata jima ba ta tafi"yak'are maganar yana nufota"ta taso ta Amshi ledar"saiya rungumeta ya rad'a mata wata kalma cikin kunne ta saki dariya tana b'oye fuskarta Ajikinsa tace" nidai babu ruwan bestie "kece kuwa kike da ruwa harma da tsaki, ya k'are maganar yana cikata ta Amshi ledar daya shigo da ita ta wuce kitchen shi kuma ya nufi upstairs....kaza ce da kifi duk gasassu sai kankana,K'wallo guda"ta girgiza kanta ta sakata cikin fridge"naman ta juye cikin tray ta rufe ta fito da nufin itama taje tayi Alwallah"Adaidai lokacin ya sakko k'asan fuskarsa da lemar ruwa ya matso ya yarfo mata ruwan yana d'age gira yace"y'an matan doctor ki tabbatar kinsha had'in nan kafin nadawo pls"waini broth meye Amfanin sane dakake ta d'irka mun shi bbu ji bbu gani kullum??tun Ina marmarinsa harma na dena wlh"uhmmm bestie nasan kin sani kika tambaya"to Amfaninsa saman bed ne"kin gane ko?"yafad'a yana k'asa da murya"saita k'i mgn ta wuce d'aki shi kuma yafita.Awannan dare Ahyaan ta gurzu Ahannun Dr darma....
washe gari misalin karfe 8:42 am"mamy na zaune a parlournta bayan ta gama break fast Dr darma ya shigo da sallama"yaci wankan suit milk colour "yayi masifar yin kyau tamkar d'an saurayi"har wata y'ar k'iba yayi sbd samun nutsuwa da kwanciyar hankali "kasancewar yanzun tunda yayi Aure Aka maida masa lokacin zuwa office 9am"ya tashi 2 pm.Anutse ya zauna suka gaisa da mamy ya mik'a mata wata leda yana murmushi yace"gashi inji y'arki "in sha Allah week end zan daure tazo dai gidan datake kwad'ayin zuwa"Allah sarki Ahyaan bata gajiya da hidima mena samu kuma?"ko jiyama wlh bakaga sabilai da mayukan data bani ba"dana k'i Amsa ta nuna tayi fushi"ko yanzun ma cewa tayi jiya taso ta baki tasan bazaki Amsa ba shiyasa ta bari nataho dashi"hakane nagode Allah yayi muku Albarka "dan Allah Ayita hak'uri nurah"kansa Ak'asa yace "in sha Allah"madallah ! Amma meyasa bata koma wajen Aiki ba?"ya d'ago kansa ya kalleta kafin yace"me Ahyaan d'in tace miki mamy?"kamar ya kenan?Ina tambayarka kana tambayata"me kuwa zatace mun?"na tambayeta ta koma wajen Aiki tace" ah ah "wai kace zaka samu Amata transfer "Akan me zaka mata transfer?"sannan kanada yak'inin har zuwa yaushe zata kai kafin Asamu transfer d'in harta koma?"Amfanin karatu shine Asami Aiki"ita kuma ta samu to Akanme zaka tsiro da batun wani transfer?"Ada ta jima bata samu Aikin ba yanzun kuma Allah ya bata sai tayi Amfani da damarta ko?"sbd haka kabar min yarinya ta koma bakin Aikinta kana jina?"wata ran idan An samu wadatar fin haka kana iya cewa ta dena Amma banda yanzun tunda bata juma da farawa ba...yayi shiru ya sunkuyar dakai k'asa "saidai ransa ya b'aci"haushi biyu ne Aransa,na Ahyaan dana fad'an mamy "Ahankali ya mik'e tsaye tare da cewa" kiyi hak'uri zata koma in sha Allah" daga haka ya fita daga cikin parlourn"dukda mamyn taso ta dakatar dashi.Amma be tsayaba yafita.....
kamar ko yaushe idan ta gama tsara girkinta zata je ta d'auki wankanta taci gayunta ta zauna zaman jiran dawowarsa "dan yau harma da lalle na yanke ta sanya ga yatsun hannunta da tafin hannunta"yayi maroon gwanin kyau "tun wajen k'arfe 1:35 pm take zaune sanye da k'ananun kaya ta daure gashinta Atsakkiyar kai"tanata zuba k'amshi fuskarta Tasha make up"har k'arfe 2 Dr darma be dawo ba"har tad'an fara jin damuwa"dama tayi mamakin yau tunda yafita be kirata ba"tadai tura masa text message na kalaman soyayya da nuna tsantsar kulawa ga mutum"be maido reply ba "sai tayi zaton may be yana busy ne"saidai ganin har biyu ta wuce be shigo ba saita danna masa kira....harta shiga ta gama ringing ba'a d'auka ba"ta koma kira nanma haka"gabanta yafad'i! ta Ajiye wayar tana tunanin kodai Fatima matar mu'az zata kira tace ta turo mata contact d'in mu'az ta kirashi,ko yaje Asibintin ya binciko yaji lafiya??tana wannan tunanin taji motsinsa yana saka key ya bud'e k'ofar "da sauri ta mik'e tsaye tana kallon bakin k'ofar"Adaidai lokacin ya shigo cikin parlourn suka had'a Ido "gabanta yafad'i sbd ganin fuskarsa bbu walwala ko kad'an ya wani d'aure fuska"dama ta lura yau da y'an miskilancin ya tashi"taji haushin yadda ya shigo ya wani d'aure fuska bayan be saba mata da shigowa ahakan ba"ko sallamar ma can ciki yayita"saita daure ta Amsa tana cewa sannu da zuwa bestie"beko kalli gefen datake ba ya wuce saman Abinsa.....batayi fushi ba sbd ita rayuwa uzuri Akeyi "sai tayi zaton toko wani yabata masa rai Awaje? matsayinta na matarsa yaka mata taje taji damuwarsa kamar yadda itama idan tanada damuwa yake k'ok'arin ganin ta fita daga cikin damuwar.tunanin hakan yasa itama ta wuce saman"Ahankali ta turo k'ofar d'akin "yana tsaye gaban mirror ya cire suit coat nashi yana k'ok'arin cire ta cikin ta shigo"be juyoba yaci gaba da Abinda yakeyi "rungumesa ta baya tayi ta saki kukan shagwab'a tana cewa"wai broth meke faruwa zaka sani cikin damuwa bayan baka saba shigo mun Ahaka ba??na kuma kiraka shine kak'i d'auka ko?"beyi mgn ba sai hannayenta data masa zobe dasu ya janye tamkar bayaso yace"kinfi kowa sanin meya faru?"Ai sbd dai Aiki kika gayama mamy ko?"to ba damuwa kije kiyi Aiki tunda shi Aikin ya fini mahinmanci Awajenki.yana fad'in hakan ya rab'a ta gabanta ya wuce ya shiga bath room "Ahyaan ta sauke numfashi tana jin wani tuk'uk'in bacin rai nataso mata"dama sbd mamy ta masa fad'an yabarta ta koma bakin Aikinta shine zai shigo yana mata haka?"ita idan tasan sbd ita yake hakan bazamq ta tambayesa meke faruwa ba zata barsa."tasan kuma mamy ba wani abu zatace masa tace mata ba"kawai zata nuna masa yabarta ta koma Aiki shine zai fassarata da duk yadda yaga dama"hawayen bak'in ciki suka wanke mata fuska "ta tuna da nasihar mahaifiyarta.*kiyi hak'uri Ahyaan da zaman ta kewar Aure"wata ran halin Namiji idan yanuna miki zaki d'auka tamkar be sonki"saidai fa dole kiyi hak'uri tunda kece ak'asa*"ta furzan da huci daga bakinta ta zauna gefen bed d'in"bata jima da zama ba ya fito yanata wani ciccin magani "kallo be ishetaba tace"kayi hak'uri ban sanarwa mamy da komai ba saida ta tambayeni na koma wajen Aiki nace mata ah ah"tace meyasa?"sai nace mata kace zakayi mgn Amun transfer ne.bayan haka ban k'ara da komai ba"kuma nasan itama bazata sanar maka sama da hakan ba"Ai sbd batun Aiki ne ko?"to ba damuwa na hak'ura da Aikin gaba d'aya"xanima tura musu sak'o na Ajiye Aikin. bana so na zama sanadin b'acin ran kowa balle kuma mjijin danake Aure "Ina k'ara baka hak'uri Akaro na biyu"ga kuma Abincin ka can idan ka gama saika fito kaci"tana kai Aya Azancen nata ta mik'e tsaye ta fita sbd kukan daya ci k'arfinta....
dab'as ya zauna gefen bed d'in jikinsa Asanyaye. gaba d'aya sai yaga kamar be kyauta mata ba"shi yayi hakane sbd yaji haushin yadda ta nace ga son komawa wajen Aikin"bayan tasan yana kishinta matuk'a "ga ya lura mamy bata son laifin Ahyaan komai tayi daidai ne awajenta.ya lura kamar ma tayi kuka da yana Abath room "saidai yaji dad'in yadda ta bashi hak'uri"kawai zai hak'ura ta koma saiya cigaba da bincika transfer d'in idan har za'a samu"da wannan tunanin ya sakko k'asan"saidai bbu ita bbu Alamar ta"ransa yabashi tana d'aki"saidai izzarsa da jin kansa sun hana yabita"shi kad'ai yaci Abincin,bayan ya gama ya fita yayi sallar la'asar"sai A lokacin Ahyaan data gama cin kukanta ta fito ta taje taci Abinci sannan ta koma d'aki "koda ta idar da sallah zamanta tayi nan bata fitoba har isha'i...duk Abinda yaka mata tayi kafin kwanciya saida tayi"kasancewar d'akinsa dama suke kwana ,suna dai shigowa nan d'akin nata Amma basu kwana"taso Ace ta share da lamarinsa Amma kishin kar yayi waya da wata"da kuma bata so ta saba masa da idan suna fushi da juna su dinga raba makwanci"wand'annan dalilan suka saka bayan ta shirya ta fito ta turo k'ofar d'akin nasa ta shigo da sallama "yana zaune jingine Ajikin fuskar gadon yana danne danne Awaya"Azuciyarsa yana tunanin wai Ahyaan fushi kenan takeyi dashi tunda gashi tak'i zuwa su kwanta "kodai yaje ya duba yaga lafiya??yana wannan tunanin ta shigo cikin d'akin"cikin basarwa ya Amsa sallamar tata"ya saci kallon ta ya lumshe Ido sbd k'amshin turarukan jikinta da suka iso masa"sai bata kulashiba ta nufi can k'arshen gadon taja pillow ta kwanta Abinta.tafi mintina 30 da kwanciya sannan shima ya kwanta nesa da ita...gaba d'aya daga shi har ita kowane da irin kalar tunanin da yakeyi Azuciyarsa"itace ta riga shi yin bacci"shi kuma feeling ne ke damunsa sbd yasaba duk dare baya k'yaleta "Amma yau yana jin baya iya neman wani Abu daga wajenta tunda shi zata shama k'amshi...yajima yana juye juye da k'yar yayi bacci gashi bashida magani balle yasha.washe gari da Asuba Ahyaan tabar d'akinsa ta koma nata d'akin tayi sallah sannan ta koma bacci....tana cikin baccin taji Ana shafar ta da lalubarta"tad'an bud'e Ido"Dr darma ne gabanta ya mata rumfa da faffad'an k'irjinsa "idanunsa sunyi jajir sun k'ank'ance"maida Idanunta tayi ta rufe....duk yadda yake romancing d'inta k'in nuna masa ta shagala tayi"bata hana shiba saidai bata taya saba kamar yadda suka saba yi Abaya"be damuba yaci gaba da hidimar gabansa"saida ya kwashe Awa biyu sannan ya rabu da ita ya kwanta gefenta"ita kuma taja bed sheet ta rufe jikinta"murya can k'asa yace"bestie nan zamuyi wankan ko d'akina?"sosai tayi mamakin jin kalamansa"Amma da yake itama ta shirya nuna masa saiya gane kuransa"saita yamutsa fuska tace"niba yanzun zanyi ba"sai yaushe?"kinsan fa ba'a son zama da janaba Ajiki ko?"tayi shiru "sai bece komai ba ya sauka daga saman bed d'in ya suturta jikinsa ya fita sbd ya fahimci wankan ne ke bata so tayi dashi....
Ummah ce zaune tsakar gidan mahaifiyarta tayi tagumi duk Abin duniya ya dameta"tun bayan tayi sati biyu da fitowa sha'awa ke damunta ta rasa yaya zatayi da ranta "ita damuwarta inma zata samu wanda zata Aura idan ta gama zaman iddah da sauk'i....Assalamu Alaikum! Ina luba?"cewar mak'ociyarsu me suna mmn imaan me dashe" gani ince lafiya dai,tunda ban jima da baro gidan kiba?"itace ta kawo haka"wlh ki fito mun da wayata da kika sace ko kuwa wlh hukuma zata rabamu.kina fita na nemi waya na rasa"bayan kuma daga ke bbu wanda ya shigo cikin gidan "kuma wayar nanan saman fridge kika shigo kika kawo kud'in dashe.....uban kuturu yayi kad'an balle na makaho"ke dan kutumar ubanki kin Isa ki samun sata da mutuncina da komai? mutunci fa kika ce?ban ganshi Ajikin kiba"ba zawarci kike ba kin fito kina zaman idda kokin d'auka bamu sani ba?"ta fad'a tana binta da kallon raini sama da k'asa"kafin taci gaba da cewa" tun muna mu biyu bani wayata salin Alin ko kuwa wlh hukuma zata rabamu"na fiki tashanci da fitinah"ummah ta mik'e tsaye ta matso tana nunata da yatsa tana lailayo Ashar tana danna mata.....ah ah wai fitinar me nakeji ne haka?"cewar inna salame tana fitowa daga cikin d'akin ta"wai inna y'ar iskar matar nan daga na shiga yanzun nakai mata kud'in dashen da kika bani wai na sace mata waya?"wannan wane irin iskanci ne"na miki kama da b'arauniya ne?haka kikace ?"Eh haka nace"batayi mgn ba ta juya ta fita"ummah taja tsaki sbd tasan harga Allah duk rashin imaninta bata tab'a satar Abin wani ba.....kusan shud'ewar Awa guda da rabi saiga y'an sanda 2 suka zo suka tafi da ummah cikin cin zarafi"sbd mijin mmn imaan yabada shedar yana nan ta shigo"kuma wata mata Anan mak'otan su sunga sadda ta shiga gidan harma gaisawa sunyi da ita.Police sunce kota biya 85k kud'in waya ko kuma tayita kwana station saita biya su saketa....tunda ummah take Aduniya bata tab'a shiga damuwa , b'acin rai, bak'in ciki da tozarci irin wannan na yau ba"babban tashin hankalinta saida taga inda zata kwana"gashi har dare bbu kowa nata daya zo"daga k'arshe saida tayi kwana 2 sannan inna salame da babban wanta mlm Amadu suka zo"wanda dama fushi yakeyi da ita sbd yasan mugun halinta itace sanadin kashe Aurenta"kaintsaye ya sanar mata bazai iya biyan kud'inba ta kansa yakeyi"itama inna salame tace wlh bazata iya biya ba batada halin su na Abinci take nema"saidai idan tunkiyarta data siya tana kiwo data siyar da kayan d'akinta data fito"to sai idan ita za'a siyar Abiya ta fito"batayi gaddama ba tace Asiyar Azo Abiya. Awannan rana ummah taci kukan b'akin ciki "ta tabbatar da Mubarak baya gidan yari koda beda su zaiyi Aikin wahala yasamo sbd afito da ita.tunda ta Rabu da Abba bata tab'a damuwa ko nadama ba sai yau"sbd taga sanadin zawarci yaja mata taka sawun b'arawo"ko kuma sharri ne matar tayi mata oho"ta tabbatar idan gidan Aurenta take Akwai ubanda ya Isa yazo har gidanta yaci zarafinta.Awashe garin ranar Aka kawo kud'in Aka biya suka saketa.tunda ta koma tayi sanyi ta kumayi baya da mahaifiyar tata"yanzun damuwarta rashin da take ciki da kuma rashin y'ay'an ta,ga kuma sha'awa na damunta"matsala goma da ishirin....

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.