Age Mates Complete Hausa Novel
Reading file: Age_Mates_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 15 of 44
************
Ahaka rayuwar taci gaba da wakana"Al'amarin cikin gidan su mamah saidai hak'uri kawai"ummah dai ta rasa taya zata yima Dr darma mgn ya tone Abinda ya binne?"saidai tana ganin yi masa mgn tamkar tayi ihu ta d'auki wuk'a ne ta dab'ama kanta"gaba d'aya Abba yayi mugun yin baya da ita"sai ya zama dole yake tankata"idan kwananta ne bema dawowa gidan tun safe idan yafita sai dare zai dawo"girkinta baya ci,kud'in cefane kullum da safe idan Khadija tazo gaisheshi in har kwanan luban ne zai bata yace ta kai mata"hakan ya koma k'ona ranta"duk mama na lura bata dai shiga Abinda be shafe taba "sai tayi kamar bata ganiba"idan kuma ita ke Aiki normal suke itada Abba "saidai kullum ummah ita y'ar sakin habaici ce,wani zubin su innah Asabe suzo gidan su had'u suyita yadama mama habaici"sai tayi kamar bata san me suke cewa ba"ko kuma ta kunnah wa'azi Abinta ta waya"gefe guda kuma kullum da safe sai mama ta bama Ahyaan rubutunta da ruwan magani me Addu'a"wanda Dr darma ke badawa duk dare a Ajiye da safe Abata "batare data san shine ke yowaba"dukda irin zaman da suke shida ita na rashin kula juna da kin shiga sabgar juna saiya kama"hakan be hanashi yi mata rubutun ba"Alhamdulillah zuwa yanzun kowa yaga canji Atare da Ahyaan "dan har littattafai na soyayya take zama ta d'an karanta"gefen AA mashi Atsarinsa beso yayima mace dole ta soshi"kawai ya fahimci kamar yarinyar bata sonsa ne"shiyasa be tab'a gigin ko sau guda yazo gidan suba"ya bari wata ran k'ilan su koma had'uwa da ita"dukda farar d'aya yaji ya kamu da soyayyar yarinyar Amma bayaso yayima mace tilas ta soshi"shi dama be tab'a soyayyaba "saima Akanta ya fara..... Ab'angaren me gayya me Aiki kam saidai muce Alhamdulillah"sbd Acikin wata biyu ya k'ara canzawa"Albashinsa 700k ne duk wata"ga chemist Alhamdulillah yanata zuba magunguna sbd ana samun k'aruwa sosai"Albashin farko daya Amsa iyayensa mazan ya kamawa yace" duk yadda sukace Ayi haka za'ayi"Abba yaji dad'in hakan sosai"ya yadda ko bayan ran Alh kabeer nurah na masa kallon ubah"sai cewa yayi ya d'auki 500k yak'ara a shagonsa ya zuba magunguna"sauran kud'in yarabama dangi da y'an uwa"ko mama 50k aka bata"tak'i Amsa saida mamy ta nuna fushinta"ko Ahyaan daba mgn yake mataba 20k mamy ta bata injishi"kamar tace bata so, saidai ganin idon mahaifiyarsa ya saka batace ba ta Amsa ta Ajiye kud'in"to Ahaka aka cigaba da tafiya"sadeeq na zaryar zuwa Amma daga gaisuwa Ahyaan bata koma kulashi"jefi jefi maza na yawan Aikowa taje "sai Mamy tayi mata Jan Ido"sannan take fita, saidai ita bataga zab'inta Acikin suba"izzarta da yangarta da Ajinta , had'e da kwalliyarta sai Abinda yayi sama"gefe guda kuma Abba dama daddy nata k'ok'arin ganin An sama mata Aiki"Ahaka har Dr darma yayi wata biyu da fara Aiki harma yashiga cikin na ukku"bbu ruwansa da Ahyaan "suna iya sati basuyi mgn ba"idan kuma ya zama dole suyi maganar da k'yar suke Amsa juna"idan Azumi yakeyi restorent yake shan ruwa"in kuma yana marmarin Abu zai kira mama yace Abu kaza yakeso"idan ta gama yaje yaci koya tura a Amso masa"gaba d'aya girkin Mamy yadena ci sbd yasan Ahyaan ce keyi"daga shi har ita ko wane baya jin dad'in hakan"kafaffiyar zuciyarsa ta hanashi yakoma su cigaba da shiri"tun mu'az be fahimci ya samu matsala da Ahyaan ba harya fahimta, sbd zancen Anko daya masa mgn yasiya mata sbd bikin befi saura 10 days Ayanzun ba "ita kanta Ahyaan d'in bata jin dad'in zaman k'in kula juna da sukeyi"saidai itama zafin kanta ya hanata jansa Ajiki sud'an shirya"ita kodan fad'an da sukeyi tana so suma dawo yi"Ana cikin hakan kyakykyawan labari ya sami Ahyaan Ashekaran jiya da yamma Abba ya dawo da labarin ta sami Aiki Agidan TV "ranar monday zata fara zuwa....tun jiya Friday taje gidan tv d'in, duk wasu tsare tsare da shirye shirye da za'a fara yi wanda ya kama da ita Aciki da kuma lokacin zuwanta da tashinta saida ta gani"saidai lokacin data fito shi kuma AA mashi na kawowa zai wuce"sukayi kallon kallo ita dashi"saiya sakar mata murmushi kawai"Abayanta taji wani na cewa *AA mashi* kayi latti sai mun cika Tara"Atake ta fahimci nan yake Aiki kenan"sai kawai tabar wajen......tun wayewar garin yau satday bayan sun gama break fast take zaman jiran isowar uncle mustapha shida Ammah zasu zo mata tare da sabuwar motarta.dama tace" sai zata fara Aiki za'a kawo motar"gaba d'aya yau cikin farin ciki take"saidai kuma ta lura da darma tun jiya da safe rabon da ta gansa ya shigo cikin gidan " tana ma zaton kamar be san ta samu Aiki ba"tana wannan tunanin Isma'il ya shigo cikin parlourn yana fad'in Mamy koda Akwai ruwa marar sanyi?"ah ah gaskiya duk suna a fridge"meye zakayi dasu?"yaya nurah ne zaisha magani"baya lafiya ne?"cewar mamy"Eh yanzunma haka magani da Allura na kamasa zai yiwa kansa ,jikinsa ringis da zazzab'i"shine zai sha magani"to kuma khaleel shine zai sha magani beyi kari ba?"wlh kuwa Mamy"Allah ya sawak'a"shiyasa koda dare naga be shigoba da Asuba ma haka be shigo ba"saina d'auka sbd yana week end ne ko baccin gajiyane yakeyi"ah ah gaskiya baya lafiya yana jin jiki ma"Ahyaan tashi maza had'a masa wani abun ki kai masa yad'an ci saiya sha magani"ta fad'a tana kallonta"dato ta Amsa ta mik'e tsaye ta wuce kitchen "khaleel ya kalli mamy yace"bara naje bakin hanya na Amso masa ruwan marar sanyi"daga haka ya fita....cikin mintina goma sha biyar Ahyaan ta dafa masa indomie da taji serdine da Attarugu da Albasa "sai tashin k'amshi takeyi,gata tayita da ruwa ruwa"sai kuma ta juye masa ruwan zafi masu citta da karanfani da Lipton da na'a na'a Acikin flux"indomie d'in kuma saita Aza plate sama ta kife ta fito daga cikin kitchen d'in"mamy na zaune inda ta barta ta kalleta tace sannu da k'ok'ari "murmushi kawai tayi ta Ajiye ta koma bed room,bata jumaba ta fito sanye da rober hijab milk wacce iya karta gwiwar hannunta"ta saka ne sbd doguwar rigar Atamfar jikinta ta kamata sosai"plate da flux d'in ta d'auka gaba d'aya tace mamy bara naje na kai masa"to shikenan saikin dawo....
kwance yake saman lallausan royar bed nasa ya rufe jikinsa da devut "idanunsa na'a lumshe"lips nasa ya tsukesu sun k'ara yin jaa,yayinda fuskarsa tayi fiyau ta k'ara haske da shek'i,saidai tayi y'ar rama ,hakan yasa karan hancinsa koma fitowa sosai"riga ce Amlas Ajikinsa da wondo 3 quarter"jiran zuwan khaleel yakeyi sbd yaturashi ya Amso masa wani abu ya gwada ci kafin ya samu yayima kansa Allura ",Dukda Asalin ciwon nasa ba zazzab'i bane daga baya yadawo zuwa zazzab'in"yana jin wayoyinsa na yawan yin ringing Akai Akai Amma beda nutsuwa ko k'arfin dubawa balle yasan waye"saidai ransa yabashi duk yawanci mata ne"da yanzun Al'amarin ya fara bashi tsoro"yana gudun shaid'an ya rinjayesa"daga Asibiti har islamiyar da yake zuwa yayi wa'azi mata sun damesa"Asibiti yaran nurses da wasu doctors biyu mata daya fahimci zawarori ne"suna yawan shige masa"dukda baya sakar musu fuska iya karsu dashi gaisuwa, Amma sai suyita k'ok'arin ganin wani Aiki ko wata mgn ta had'a su.....cak! tunaninsa ya tsaya sbd jin Amai nataso masa"da hanzari ya yaye devut d'in ya sauka daga saman bed d'in"saidai kuma yana mik'ewa tsaye yafara ganin hajijiya"ga cikinsa na murd'awa sbd yunwa"rabonsa da Abinci tun jiya da rana"da sauri ya duk'e k'asa daga gefen carpet ya fara Aman yellow"Adaidai lokacin Ahyaan data doso d'akin gabanta na fad'uwa taji kakarin Amai ta turo k'ofar ta shigo da sauri......✍️
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.