Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Rawanin_Zalinci_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 1 of 24
ðŸ¤ðŸ”¥ð—¥ð—”ð—ªð—”ð—¡ð—œð—¡ 👑 ð—ð—”ð—Ÿð—œð—¡ð—–ð—œðŸ”¥ðŸ¤
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
🔥💔𑨠ð’•ð’ð’–ð’„ð’‰ð’Šð’ð’ˆ ð’‰ð’†ð’‚ð’“ð’•ð’” ð’ð’ð’—ð’† ð’”ð’•ð’ð’“ð’š, ð’…ð’†ð’”ð’•ð’Šð’ð’š ð’ð’ƒð’”ð’•ð’‚ð’„ð’ð’†, ð’‚ð’ð’… ð’“ð’ð’Žð’‚ð’ð’„ð’†ðŸ’”🔥
ð— ð—”ð—Ÿð—Ÿð—”ð—žð—œð—¡
â¤ï¸â€ðŸ”¥FATEEMA ZAHRA MUSA â¤ï¸â€ðŸ”¥
(â¤ï¸ð‘·ð‘¹ð‘°ð‘µð‘ªð‘¬ð‘ºð‘º ð‘»ð‘¬ð‘¬ð‘´ð‘¨ðŸ”¥)
🔥ðŸ¤T🔥ðŸ¤T🔥ðŸ¤W🔥ðŸ¤......💻
*Gargaɗi! Gargaɗi!! Gargaɗi!!! Ban yardaba! ban Amince ba! ban lamunceba! A juya mun labarin LITTAFINA tako wacce sigar, bana so, ban bada damaba, idan kana buƙata akwai numberta a jiki ki\ka nemi izinina, ban yarda a karanta mun shi a youTube ba, ko a haɗa mun Document, a kiyaye domin zama lafiya yafi zama ɗan sarki! In kunne yaji gaggan jiki ya tsira. Wannan littafin RAWANIN ZALINCI haƙin mallakarsa nawane FATEEEMA ZAHRA MUSA (PRINCESS TEEMA)!.*
*Ina godiya ga Allah subhanahu wata'ala da ya bani ikon fara wannan littafi lafiya, Allah ya bani ikon kamala shi lafiya.*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM. mun fara da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai, da shi muka dogara kuma a gare shi kawai muke neman taimako.🥰 Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Manzon Rahma É—an gata a wajen Allah, kuma fiyayyen halitta wato Annabi MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMAðŸ¤*
â¤ï¸ð‘«ð‘¨ð‘»ð‘¬ 28/6/2024.....âœï¸ðŸ“šðŸŒ¹
ðŸ¤ð‘ºð‘»ð‘¬ð‘· 1......âœï¸ðŸ“šðŸ”¥
â¤ï¸ð‘¬ð‘·ð‘°ð‘ºð‘¶ð‘«ð‘¬__________1🔥
Iska mai matukar ƙarfin gaske ne yake kaɗa dogayen bishiyoyin dake a kewaye da wannan ƙungurmin dajin! Tamkar za'ayi ruwan sama, garin ya haɗe ya yi duhu bakin kirin da hadari, sararin samaniya ya bada wasu launuka, ja, sky blue, navy blue, da kuma dark ash masu matuƙar ɗaukar hankalin, saboda hadirin!.
Daga gabas ta tsakiya wani tapkeken bakar gizo ne wato Rainbow ya fito a sararin samaniyar.
Sannu a hankali walkiya ya fara wanzuwa a sararin samaniyar, haka zalika tsawa ta fara bayyana, alama ce ta ruwan saman ya gabato.
Iskar kara tsananta take yi sosai, while shima hadarin kara baki yake yi sosai, yana mamaye ko'ina a faÉ—in garin, gabaÉ—aya korayen ganyayyaki da dogayen ciyayin dake cike a wajen, sai wani irin kaÉ—awa suke yi har suna kwanciya, tamkar za su tsigo daga jikin tushensu, da alama dai wannan ruwa ne mai karfin gaske yake zuwa, da iska da tsawa!.
Daji ne mai cike da yalwar itatuwa, dogaye, manya manya masu kauri, akwai yalwar ƴaƴan itatuwa kala kala sosai a cike a cikinta, akwai ƴelwar abubuwa masu matuƙar kyau da ɗaukar hankali, irinsu koramai dake zubar da ruwa mai ban sha'awa, duwatsu manya manya masu ɗaukar hankali, koguna wato kogon dutse manya da kanana, tsaunika masu tsawo, rafuna masu cike tab da ruwa mai matuƙar kyau da ɗaukar hankali, a saman mafiya yawan tsaunikan dake a cikin wannan dajin da akwai jiga jigan kogunan duwatsu a wajen, ga kuma bishiyoyi masu ɗaukar hankali, da dai sauransu.
Sai dai da alama akwai haɗari matuƙa a cikin wannan daji, domin kuwa ba za'a rasa muggayen namun dawa masu haɗari irinsu Zaki, Damusa, Kura, Giwa, Sloot, dabba mai nawa da saiɓi, Puma Tiger, Guanaco, dabba mai kama da raƙumi, Vampire Spader, masu kashe sauro, Honey vaja, Dage, Damusar chiter, Dila, Dilar Jakal, Birrai, Gorillas, Tsuntsaye, Macizan kubras, Hayanas da dai sauran mugayen namomin daji.
Wani irin sauti ne yake tasowa tamkar na sahun gudun É—an adam, sautin yana fitowa ne daga bayan wasu dogayen bishiyoyi na zaitin dake fuskantar gabas ta tsakiya, bishiyoyin suna a cunkushe ne waje guda, sai wajen ya bada duhu tamkar maraice ne a lokacin.
Da kaÉ—an da kaÉ—an sautin nan ke tahowa, har ya fara karaÉ—e kewayen wajen.
Bayan wani ɗan lokaci wannan sauti ya kara matsowa kusa sosai, kasan cewar gari ne na damuna, ta ko'ina akwai ruwa wanda ya kasance ya yi ramuka kanana, sannan wasu gurare daga cikin wannan katafaren dajin sun kasance da akwai taɓo, wasu kuma farin kasa yashi ne tas, kamar dai sauran manya manyan dajuka da kuka sani.
Wannan ramuka kanana masu ruwan, duk in aka takasu sai ruwan ya yi kara palcam, hakan yasa sautin gudun ya kara fitowa ɓaro ɓaro sosai da ya karaɗe yankin wajen!.
Jim kaÉ—an ta bayyana a tsakiyar dogayen bishiyoyin nan.
Mace ce fara tas tamkar balarabiya, a kallon farko idan ka yi mata sai ka yi wani irin razana, saboda tsannin kyau da kuma yanayin da ta bayyana a wajen, tamkar wata rafaniya ko ace irin kyawawan aljanun nan masu kamar su suka yi kansu dan kyau.
Launin hasken fatartata gwanin ban sha'awa, luwai luwai, jajir da ita a cikin korayen ganyayyaki, ya kuke tunanin bayyanarta zai kasance a idanun É—an adam?, dole duk wanda ya ganta a wajen sai hantar cikinsa ta kaÉ—a ya tsorata aihun, dan kyau na É—iga.
Da kallo É—aya zaka yi mata ka fahimci cewa daga gidan hutu ta fito! Dan jiki duk madara da ice cream ce! Kyakkyawar gaske ce, gata da tsawo, doguwa da ita, a shekaru ba zata wuci 22 to 23 years a duniya ba.
Sanye take da kaya masu bala'in kyau da tsada, kaya ne irin na hamshaƙan gimbiyoyi, ire iren waɗan nan dogayen riguna ne da ƴaƴan manya manyan jiga jigan sarakuna suke sanyawa, rigar kawai abar kallo ce, dan ta tsaru iya tsaruwa, ta sha kwalliya da wasu shegun duwatsu masu bala'in haske har suna wani ɗaukar idanu.
Daga kanta har ƙasa wani dankarere kuma haɗaɗe tsadadden alkyabba ce mai hula, launin Golden color, while shi kuma doguwar rigar jikin nata launun ligh ash ne, sai launin alkyabban ya hau da rigar sosai.
Kunnenta hannunta zuwa wuyarta, shake suke da dankara dankaran kayan ado na gold masu bala'in tsada, shi sarkar wuyarta ma yana da tsawo har saman breast nata, ga shi da faÉ—i, na zallar madarar gold ne babu sirki.
Takalmar dake kafafunta ma kawai abin kallo ne, irin takalmar nan ne da manyan gimbiyoyi da ake ji dasu a duniya suke amfani da su, takalma ne masu matukar tsada wanda kwalliyar jikinsu ma da gold aka yi su, sai wani É—aukar idanu suke yi. A takaice dai jikin wannan mata daga sama har kasa narkakkun makudan dukiya ne ba na wasa ba aka kashe, bakina ni dai PRINCESS TEEMA ya yi kaÉ—an ya zayyana maku irin kuÉ—in da aka narka a kwalliyar dake jikinta.
Daga cikin hular alkyabbar jikin nata, kana iya hango wani kwantatcen bakin gashi siɗif da ya zubo mata ta saman shoulders ɗinta har izuwa kirjinta ta gefen dama. Tana da dara daran idanu sosai, launin kwayar idanunta ash color ne, irin light ash ɗin nan da zaku kalli kamar basu iya ganin mutane, saboda kyallin idanuwan nasu, dan ya yi light, sai ya yi kamar yana. Tana da dogon fuska, amma ba sosai ba, sannan ba laifi tana da ɗan cikar fuskar, haka zalika tana da innocent face sosai, da kallo ɗaya zaka yi mata ka fahimci she is so silent, bata da hayaniya, bata da ƙiba sosai, ƴar caras cas da ita. Karshen haɗuwa ce ita ɗin!! Kamar ba mutun ba dan kyau!.
Daga saman kanta har izuwa fararen lausasan kafafunta, gabaÉ—aya gumi ne ya jiketa sharkaf, daga gefe da gefen face nata, wasu zufa ne suke kara tsastsafo mata kamar ruwa, fuskarta gabaÉ—aya ya jike sharkaf da gumi, tamkar wadda aka watsawa ruwa a face É—in tata, wani irin uban haki take fitarwa sama sama, idanuwanta har wani irin juyewa sama suke yi, saboda wahalar gudun nan da ta sha, gabaÉ—aya a tsananin razane take, wannan innocent face É—in tata ta koma a wani irin razane gwanin ban tausayi.
Daga gani kasan gudun cetan rai take yi, ga tsohon cikin a jikinta, wanda a kalla ya kai watanni haihuwa, kuma da alama ma ta fara naƙuda, ko kuma wahalar gudun ne ya bayyana a jikinta tamkar mai naƙuda. Amma a haka take wannan uban gudun, daga ganin kasan bala'in da ya korota ta shigo cikin wannan bakin daji ba ƙaramin abu ba ne.
Duk da wannan tsohon cikin nata, haka ta jure take tika uban guda, ta gaji iya gajiya, amma bata tsaya ba, ta yi wani wiki wiki da ita gwanin ban tausayi, duk ta fita daga cikin hayyacinta.
Gudu take yi bata san ina ta dosa ba! Duk wanda ya kalleta a cikin wannan hali da take a ciki, sai ya matsa mata kwallah, babban abin tausayin ma shi ne wannan tsohon cikin nan da yake jikinta.
Kutsawa ta sake yi ta cikin wasu bishiyoyin mangoro dake É—an nesa daga in da ta fito, sai wani irin haki take yi mai matukar razanarwa, sama sama take fidda numfashi mai sauti, da sauri sauri tamkar wadda aka shake na tsawon lokaci bata sami iska ba, daga baya aka saketa, haka take fitar da numfashi, da alama ma faÉ—a take yi da numfashin nata, domin ta dai'dai ta shi ya dawo dai'dai, wani irin razanannen tashin hankali ne bayyane a saman fuskarta. Tabbas wannan mata tana cikin bakin bala'in tsaka mai wuya!!.
Wani uban sautin gudun lafiyayyun dawakai ne yake tasowa daga ta hanyar da ta fito É—an nesa kaÉ—an, da karfi-karfi dawakan nan suke gudu, kai daga ji kasan suma suna gudune domin cinma wani abin da idan ba su cin mishi ba, suna iya rasa rayukansu, ma'ana suma dai gudun cetan nasu rayukan suke yi kenan.
A lokacin already matar ta kutsa ta cikin bishiyoyin dake fuskantar yamma kenan. Da karfi karfi gudun waɗan nan dawakai ke kara dimfarowa kusa, sai wani irin uban haniniya dawakan suke yi, da alama waƴan da suke a kan dawakan, a ƙage suke da su je in da suke da buƙatar zuwa, suna ba wa dawakan wuta sosai ne, ma'ana suna sanya dawakan gudun wuce ka'idar dabbobi.
Jim kaÉ—an!.
Duk wani mutun mai rai matuƙar yana wannan waje, to sai ya yi mahaukacin razana a lokacin da waƴan nan dawakan suka bayyana a tsakiyar filin bishiyoyin nan. Wasu irin mahaukatan manya manyan dawakai ne, masu tsantsar lafiya tare da ƙoshi! Da alama sun kiwatu fiye da tunanin mai tunani, dama can kun san doki da shegen karfin tsiya, bare ace ya samu kiwo mai kyau, ai abin sai wanda ya gani kawai.
Wasu irin shirga shirgan jiga jigan manya manyan sadaukan yaki ne a saman waƴan nan ƙosassun dawakan, wanda ganinsu kawai sai ya razana duk wata halittar ɗan adam mai rai. Gabaɗayansu sanye suke cikin kayan yaki a jikkunansu, kayan yaki kuma irin wanda ake yin su da dafaffen karfe, wadda bullet ko kifiya or takobi bata huda su, daga ganinsu kasan daga wani katafaren Kingdom (Masarauta) suka fito, fuskokinsu gabaɗayansu a rufe da irin waɗannan hular kayan yakin nasu da suke sawa, kayin hular nasu yana da kaho guda biyu kamar na ɓauna, baka iya ganin fuskokinsu, sai ido, hanci da kuma tsagen baki, dan hular nasu tamkar mask haka yake, dan ya tare musu kansu idan ana yaki, kun dai gane hular mayaka dai ko? To su dai.
Daga bayansu kuma manya manyan lafiyayyun kwari da kifiyoyi ne tsakale a bayan nasu, wanda ba sa saɓa saiti, shi suka ratayo a bayan nasu, dai'dai kugunsu kuma, wasu irin mahaukatan zaratan takuban nan ne, masu kaifin bala'i, wanda kaifin su zai iya fille wuyar mutun nan take, kafafunsu na sanye cikin irin waƴan nan takalmar nasu na mayaka, masu kama da waterproof shoe, sai dai nasu yana da igiya wanda aka ɗaure har saman kaurin damatsan kafafunsu.
Ko baka ga fuskokinsu ba, kasan waÆ´an nan basu da imani ko miskala zarratin a ransu, saboda mawuyacin abu ne mai imani ya biyo mace mai tsohon ciki tana naÆ™uda a irin wannan dokar bakar daji haka, babu tausayi ba imani su biyota da dawakai suna neman hallaka ta, innalillahi wa inna ilaihir rajiun........ðŸ˜
Dawakai shidda ne, haka zalika Warriors (mayaka) shidda ne a kansu, sun horu a fagen yaki sun ƙoshi, kamar wasu bujuman mayunwatan zakuna haka suke.
Tamkar sun san hanyar da ta bi, suma nan suka nufa da wani mahaukacin gudu.
A ɓangaren wannan mata kuwa, tun da ta kutsa ta cikin waɗan nan bishiyoyin, wani azababben kuma balaƴaƴƴen ciwon ciki ne ya turnuketa lokaci guda, wani irin kullewa mararta ta yi, ta riƙe gam tana yi mata bala'in ciwo na gasken gaske kuwa.
(ALLAH SARKI KO DAN JIJJIGA CIKI NATA DA TA YI NA WANNAN UBAN GUDU DA TA SHA, DOLE NEMA CIKIN NATA YA YI CIWO......ðŸ˜)
Da kyar take jawo wani wahalallen yawu tana haɗiyewa, saboda bala'in kishin ruwa da take ji, maƙoshinta ya bushe sosai.
Ƙasa cigaba da guduwa ta yi, wanda hakan yasa ta zube kasa a saman gwiwowinta gaban wasu bishiyoyin kashu, tana mai fafutukar jawo numfashinta, ta daidai ta shi dan ta ceci rayuwarta da na abin da yake a cikinta.
Baiwar Allah da hannu bibbiyu ta tallaɓo katon cikin nan nata ta kasa, ji take yi tamkar cikin nata zai faɗi kasa ne, dan tsabar bakar wahala har ji ta yi cikin nata ya rabu da mahaɗar haƙarƙarinta ya yi kasa,.............. Wayyo Allah, ya ilahi ya lillahi.
Zufar azaba da wahale ne yake cigaba da tsantsafo mata daga gefe da gefen kunnenta, fuskarta kuwa tuni ya kara jikewa sharkaf da gumi, tamkar wanda aka watsawa ruwa, wani irin wahalallen marayar kuka ta saki, wanda kuma muryarta kwata kwata bata fita, babu sauti a tattare da ita, wahala ta yi wahala, ta ma nemi hawayen a jikinta ta rasa, yau hawayen kukan ma babu shi, dama kuma duk wahalar da ake yi wa hawaye, to bata kai wahala ba, muddin ta kai wahala, da kanka zaka nemi hawayen ka rasa shi.
Tana a tsaka da wannan hali, kunnuwanta suka fara tsinkayo mata sautin gudun tare da haniniyar waÆ´an nan dawakan daga can nesa da ita a karo na biyu!.
Jin sautin na kara dinfarota gadan gadan ne yasa ta ji wani irin mahaukacin karfi ya zo mata, a wahale ta daure tare da ciza laɓɓanta da karfi tamkar zata fasasu, da iya karfin da ya rage mata baiwar Allah ta miƙe dan ta cigaba da gudu ko zata tsira da ranta.
Bata san ina ta nufa ba, bata san ina take takawa ba, haka ta cigaba da gudu, ta cigaba da tsaga tsakanin manya manyan dogayen bishiyoyi tana wucewa!.
Wannan Baiwar Allah dai ta ci bakar wahalar da ko makiyinka ba zaka yi mashi fatar faɗa wa makamancin wannan wahala da bala'i ba, sai nishi take yi sama sama, da alama tana da yakinin da kuma burin cigaba da rayuwa, alamu sun nuna akwai tsantsar burin son ta cigaba da rayuwa a tattare da ita, kuma daga kwayar idanunta zaka fahimci akwai wani babbar Al'amari da take buri da kuma fatan cinma shi a rayuwarta, daga yanayin yanda take gudun take ƙoƙarin ganin ta rayu duk da mawuyacin abu ne ta zullewa waƴan nan mayun azzaluman dakarun yakin, sai dai wani ikon Allah, amma dai bata sare ba, kuma bata yanke kauna ba, haka zalika bata cire rai daga samun Rahmar Ubangiji ba. BABBAR MAGANA KO YA YA WANNAN AL'AMARI ZATA KASANCE? FARKO KENAN DAGA CIKIN LITTAFIN RAWANIN ZALINCI, (🤠PRINCESS TEEMA CE 🔥💘 HAR WA YAU.)
Bata yi nisa a gudun nata ba ta isko karshen hanyar, wanda kuma ya kasance wani katon dutse ne da baka ganin iyakarsa a faɗi, ƙasan dutsen kuwa, katafaren teku ne mai girman gaske, tekun cike yake maƙil da farin ruwa tas, har wani ɗaukar kalar sararin samaniya ruwan nan yake yi, saboda haskensa! Sai dai kuma tsakanin tekun da wannan dutse da take a kai, akwai nisa sosai, sannan kuma, akwai dogayen bishiyoyi ta gefe gefe ruwan, bayan haka akwai abubuwa da dama dai irin na ko wace babbar daji da ta amsa sunanta daji.
Dakatawa ta yi daga gudun da take yi tana mai kallon wannan tapkeken tekun, tana sakin wahalallen nishi. Wannan shi ne gaba babu hanya baya ma babu hanya, gaba teku baya warriors! Ya kenan?.
A hankali tamkar mai tsoron juyowa ta juyo dan ta kalli waɗan nan masu bin nata, wanda suma a daidai lokacin suka cin mata, har lokacin tana cije da laɓɓanta bata saki ba, hakan zai fahimtar da kai tana cikin azaba.
Juyowarta ya yi daidai da É—aya daga cikin warriors É—in ya ciro kwari da baka daga bayansa, ya É—ana kifiyarta tare da ja da karfi, ya saitata, kai tsaye ya harbeta sai saman katon cikin nan nata ta gefen hagu.
Wani irin jini jajazir ne ya fallatsa ya fito daga jikinta, da alama jinin nata ma, ya jijjiga sosai, dan kuwa yanda ya fallatsar nan tamkar jira yake yi a huda mishi hanya ya fito.
(*PRINCESS TEEMA CE....âœï¸ðŸ”¥ðŸ’˜* )
Saboda gajiya da kuma bakar azabar wahalar da ta sha, muryarta baya fita sosai, wani irin wahalallen ihu ta saki wanda sautinsa bai fita ba, cikin bakin azaba da wahala ta sanya hannunta bibbiyu ta dafe cikin nata tare da riƙo kifiyar da suka harbeta da shi ɗin gam tana nishi, lokaci guda fuskarta ta sauya, har wani kumburi ta yi cikin ƙanƙanin lokaci, dama kuma ga na ciki a gefe, sai abin ya haɗu ya yi mata yawa, duk wanda ya kalleta a halin da take a ciki, komai rashin imaninsa matuƙar musulmi ne yasan kalmar shahada, kai ko ba musulmi ba sai ya matsa mata kwallah ba kaɗan ba, domin tana cikin wani irin bakin mawuyacin hali wanda baki ma ba zai iya misilta shi ba.
Su kuwa waƴan nan shaiɗanun azzaluman, ko a jikinsu, tamkar ba mutane bane, tamkar babu zuciya a kirazansu, tamkar wasu dafaffun karafuna ne ko ace duwatsu ne a matsayin zukatansu ba zuciya ba, saboda tsantsar zallar madarar rashin Imani dake tattare da su, sai ma ƙoƙarin ciro wani kifiya ɗaya daga cikinsu ya yi domin ya kara sake mata a cikin nata, duk da halin da take ciki basu da niyar raga mata ko su tausaya mata.
Cikin fitar hayyaci ta saki wani marayar wahalallen kuka tare da yin baya baya ta faɗa kasan wannan katafaren kogi ko ace teku, dan ko rani ya yi damina ya ɗauke, wannan tekun bata ƙafewa, shi kuma kogi yana iya kafewa a lokacin da ba damuna bane.
FaÉ—awarta kasar wannan dutsen ya yi dai'dai da kecewar ruwan sama kamar da bakin kwarya, ga tsawa da walkiya mai karfin gaske.
Tsakanin wannan dutse da kuma ruwan dake a ƙasansa, zai iya kai a kallah 3.6 meter, amma haka ta faɗa kasan, hakan kuma zai kara tabbatar muku da cewa tabbas bata son mutuwa a hannun waƴan nan azzaluman, tabbas tana da bukatar cigaba da rayuwa.
Ganin ta faɗa kasan ne yasa suka ƙariso waje ba tare da sun sauƙa daga kan dawakansu ba, babu alamar tsoro, tausayi, imani a tattare dasu, sai ma alamar jarumta tare da taurin zuciya.
Ruwan saman na dukansu, haka suka tsaya a cikinsa dan cimma burinsu, sai wani irin numfashi mara daÉ—in ji dawakan nasu suke fitarwa, su kansu warriors dake a saman dawakan, sai wani numfashin suke yi alamar sun wahala a gudun da suka sha.
Suna ƙarisowa ɗaya daga cikinsu ya sauƙa daga saman dokin nasa yana wani irin taku wanda yake nuna cikakken warriors ne, wato (Mayaki) lafiyayye mai jini a jika, duk in ya taka kasa, sai wajen ya amsa, yana da tsawo ga faɗin kirji sosai, sannan ga cikar halittar namiji, wanda yake nuna maka cewa cikakken gwarzon mayaki ne, ya horu ainun.
Kasan dutse ya zo ya leƙa a yayin da su kuma sauran suke a saman dawakansu suna jiran su ji me ake ciki.
Ko alamarta bai ga ni ba, da ya leƙa, alamu sun nuna ruwa ya tafi da ita, a nasa tunanin, katafaren teku ne wanda ya kai har mararrabar Masarautar su da kuma ƙasar dake makwabtaka da su, ma'ana wannan tekun ya zama kamar itace bordersu kenan.
Juyowa ya yi ya nufi bujumin dokinsa yana girgiza masu kai, alamar su je kawai babu wata matsala.
Juya kan dawakan nasu suka yi, a guje suka bar wajen suka nufi hanyar da suka fito.
Sun É—an yi gudu mai nisan kafin su zagayo ta kasan dutsen, wajen ruwan kenan, dan su duba ko za su iya ganin wannan matar.
Duk da idanunsu ya gane masu faÉ—awarta kasar tekun, ba gaya masu aka yi ba, gani suka yi, amma basu yarda da cewa ruwa ya tafi da ita ko makamancin haka ba, shi ne yasa suka zagayo dubawa.
Warriors (Mayaƙa) guda biyu ne suka sauƙa daga saman dawakansu, suka nufi bakin ruwan dan su duba da kyau da kyau.
Kash ko alamar wannan mata babu a wajen, da alama ruwa ya tafi da ita da gaske ne, ga kuma baiwar Allah tana nakuda, ga kifiya a cikinta, ya ilahi ya lalliahi.......ðŸ˜
Juyawa É—aya daga cikinsu ya yi ya dubi waÆ´an da suke akan dawakan.
"Da alama fa ruwa ya tafi da ita, ku muje kawai, domin ina da tabbacin ba zata taɓa rayuwa ba, ba'a taɓa wanda ya shiga cikin wannan ruwan ya fita da rai ba! Ko da kifiyar da muka harbeta da shi bai kasheta ba, mugayen dabbobin cikin ruwan nan za su hallakata!".
Ya yi maganar cike da nuna jarumta da izza, kalaman nasa akwai kaushi, kuma suna nuni da cewa ya jima a sadaukan yaki, domin kuwa babu tsoro ko É—ar É—ar a tattare da shi, ko ace da su bakiÉ—aya, babu wani shayi a maganarsa.
ÆŠaya daga cikin waÆ´an da suke a kan dawakan ne ya girgiza kai yana faÉ—in
"No, ya zama dole mu nemota, mu fasa cikinta mu ciro abin da yake ciki mu koma da shi masarauta, idan dai muna son rayukanmu da lafiyarmu!!".
Kenan hakan yana nufin abin da yake cikin cikin nata suke da buÆ™ata?.........🤔...... Kenan ba niyar kashe abin da yake cikin nata suka yi ba? To in dai haka ne meyasa zata gudun masu? Meyasa ba zata tsaya ta haifa ta basu ba tun da ba kashewa zasu yi ba? Su meyasa suke son karÉ“ar babyn dake a cikin natan? Me zasu yi da shi? Waye ne ma mamallakin cikin nata? Ma'ana uban cikin?. Tab akwai cakwakiya ba kaÉ—an na. PRINCESS TEEMA ce taku ta amanaðŸ¤
Da alama wanda ya yi magana yanzu shi ne babbansu, dan tun da ya fara magana suka wani sunkiyar da kai, suka kara nutsuwa tamkar masu karɓar umarni.
Jinjina kai suka yi suna mai nuna alamar sun ji maganarsa sun kuma gamsu. A tare dukkansu suka diro ƙasa daga saman dawakan nasu, ji kake yi dip, dip, dirowar manya.
Fara kewaye wajen suka yi, dan su ga ko zasu yi nasarar samun wata makama, dukkansu basu da wani burin da ya wuce ace sun ga wannan matar, kowannansu burinsa ace shi ne ya yi nasarar ganinta ya kuma ciro babyn dake cikin cikin nata ya mayar da shi masarauta, da alama ba karamar kyauta aka sakawa duk wanda ya kawo babyn dake a cikin wannan matar ba, saboda yadda suka zage da iya karfinsu tare da kwarin gwiwa suna aikin nemanta.
Amma duk da hakan kuma sun kasa yin gigin yunkurin shiga cikin ruwan, dan sun san zurfin ruwan nan ya wuci tunanin mai tunani.
Sun jima suna kewaye a wajen, amma babu komai a cikin ruwan sai manya da kananun jiragen ruwa dake shawagi a can nesa da in da suke, ta tsakiyar ruwan.
Daga karshe dai suka hakura ba dan sun so ba, suka haye saman dawakansu, suka kutsa ta cikin wasu dogayen bishiyoyi dake a wajen, suka tafi.
*TO FAH, FARKO KENAN DAGA CIKIN LITTAFIN RAWANIN ZALINCIN, KU DAI KASANCE DA ALKALAMIN PRINCESS TEEMA DAN JIN YANDA ZATA KASANCE, KUN DAI JI TA YADDA LABARIN NAMU YA SOMA, NA SAN ZAKU SO JIN AINAHIN KAN LABARI, WACECE WANNAN MATA? MEYASA SUKA KASHETA? SU WAYE SU? MEYASA SUKE SON ABIN DA YAKE A CIKIN CIKINTA? ME ZASU YI DA SHI? ITA MEYASA TA ZAÆI MUTUWA A KAN TA BADA ABIN DA YAKE A CIKIN CIKIN NATA? SHIKENAN YANZU RUWA YA TAFI DA ITA? TA MUTU DA GASKE? GA KIFIYA A CIKINTA SUN HARBETA DA SHI? GA SHI TANA NAKUDA BAIWAR ALLAH. TO DAI MU KASANCE A TARE DAN WARWARE WANNAN SARKAKIYA A TARE, KADA FA KU YI WANI TUNANI TUKUN NAN,🥱 MASU YI MUN PREDICTION ME ZAI FARU A GABA NA LITATTAFINA SAY HII😂 KAMAR YANDA TRIPLETS YA RIKITA MAKU TUNANI, KUKA KASA HASASHEN GABA, TO WANNAN KO FARA HASASHENSA BA ZAKU YI BA, DAN KUWA SALONSA DABAN NE!🔥 AKWAI RIKITA KWAKWALE, MU JE DAI ZUWA, NAYI GABA SAI KUN ZO!!.*
*PRINCESS FATEEMAH, PRINCESS TEEMA DUKKA SUNANA NE, DAN NAJI WASU SUNA TAMBAYA💫â¤ï¸*
To!! To!! To!! Ina masoyana? kai harma da makiyana, ina kuke? Ina masoyan littafin TRIPLETS? Ina masoyan Noorish and Meesha? Ina masoyan babyn baby and his baby? Ina masoyan Heartbeat and Heartbeat? Ina masoyan Sudais and Anaya? Ina masoyan Uncle T and Aafia? Ina masoyan sir Arvin and Maryam?, Ina masoyan Alex and Adiva?, ina masoyan Imran and jelly, Akila and Umaisha, Irfan and Pinky, masoyan Hjy gwaggo mai zamani, duk dai Ku matso da sauri, dan a yau PRINCESS TEEMA ta sake dawo maku da wata zazzafar littafin mai tashin kai, shi wannan ba zazzafa bane ba, tafasa yake yi yana bada tiriri, salonsa daban ne, ina mai tabbatar maku salonsa daban ne, ku my peoples kun sani already ba sai na sake faɗa ba, PRINCESS TEEMA taku mai abin ban mamaki ce, kun san zaku sha mamaki a wannan karon ma, kun san idan nace salonsa daban ne, to fa daban ɗin ne, trust me ya sha banban da sauran labaran da kuka sani, dan fa a shiryena na taho In Sha Allah,🤠zan tashi kanku in sanya maku hayakin kwakwalwa my peoples, yanzu dai ba QUADRUPLE bane fa😂 kada ku yi mani irin ruɗewar da kuka yi a TRIPLET'S🥺 wannan ina kara gaya maku yasha banban da kowani irin littafi, dan haka kada ki yarda ki bari a baki labari, da a baki ai gara ki bayar, gani ya kori ji, dan haka ki hanzarta maza ki kasance a cikin tafiyata, dan ki gani ba ki ji labari ba👌 ina kara jaddada maku wlh ba zaku taɓa yin danasanin bibiyar wannan littafi mai suna RAWANIN ZALINCI ba In Sha Allah, tabbas zaku yi alfahari da ni fiye da tunaninku, kun sani Alkalamin PRINCESS TEEMA alkalamina mai ilmantarwa, fadakarwa, wa'azantarwa, tare da nishaɗantarwa ne, na san kun san da hakan, dan kune ma kuka shaideni da hakan, bani na faɗa da bakina ba, shaidarku ce wannan, kun shaidani bana rubuta shirme da abubuwan banza a labarina, bana rubuta abin da hankali ba zai ɗauka ba! Bana rubutu kamar tatsuniya! Ina rubutu ne kamar gaske, abin da yake kewaye damu!! Kada dai na cikaku da surutu, mu haɗe daku a cikin littafin RAWANIN ZALINCI page 2 kawai.🔥🌹 Ku daga jin sunan RAWANIN ZALINCI kun san da akwai abubuwa ba kaɗan ba wadda baki ya yi kaɗan ya kwatantasu.
*Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.*
ðŸ¤PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥
Share fisabilillahi ðŸ‘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥ðŸ¤
ðŸ¤ðŸ”¥ð—¥ð—”ð—ªð—”ð—¡ð—œð—¡ 👑 ð—ð—”ð—Ÿð—œð—¡ð—–ð—œðŸ”¥ðŸ¤
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
🔥💔𑨠ð’•ð’ð’–ð’„ð’‰ð’Šð’ð’ˆ ð’‰ð’†ð’‚ð’“ð’•ð’” ð’ð’ð’—ð’† ð’”ð’•ð’ð’“ð’š, ð’…ð’†ð’”ð’•ð’Šð’ð’š ð’ð’ƒð’”ð’•ð’‚ð’„ð’ð’†, ð’‚ð’ð’… ð’“ð’ð’Žð’‚ð’ð’„ð’†ðŸ’”🔥
ð— ð—”ð—Ÿð—Ÿð—”ð—žð—œð—¡
â¤ï¸â€ðŸ”¥FATEEMA ZAHRA MUSA â¤ï¸â€ðŸ”¥
(â¤ï¸ð‘·ð‘¹ð‘°ð‘µð‘ªð‘¬ð‘ºð‘º ð‘»ð‘¬ð‘¬ð‘´ð‘¨ðŸ”¥)
🔥ðŸ¤T🔥ðŸ¤T🔥ðŸ¤W🔥ðŸ¤......💻
â¤ï¸ð‘«ð‘¨ð‘»ð‘¬ 29/6/2024.....âœï¸ðŸ“šðŸŒ¹
ðŸ¤ð‘ºð‘»ð‘¬ð‘· 1......âœï¸ðŸ“šðŸ”¥
اللَّهÙمَّ صَلّ٠عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌ، اللَّهÙمَّ بَارÙكْ عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا بَارَكْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌâ¤ï¸
E____________2🔥
Baƴan lokaci mai tsawo da tafiyar waƴan nan jiga jigan worries ɗin, har lokacin ruwan sama na cigaba da zuba tamkar da bakin kwarya, ga garin sai kara wani uban duhu na hadari yake yi, tamkar yanzu za'a fara ruwan ma, wani irin walkiya mai matuƙar haske ne yake ta famar walwali a sararin samaniyar, ga wani irin uban rugugin tsawa mai sanya hanjin cikin duk wata halitta razana, sai ka rantse da Allah tsawar nan zata faɗo kasa ne.
Da kaÉ—an da kaÉ—an haki da nishi yake tasowa daga É—an nesa da bakin wannan teku, da sauri da sauri nishin yake fita tamkar idan mutun ya rike numfashinsa na É—an lokacin daga baya ya saki, to a wannan lokaci numfashin zata fita da sauri sauri kuma da karfi karfi, dan hanya da ta samu, haka wannan numfashi da hakin yake tashi!.
Kara yawaita wannan numfashin yake yi, daga can nesa da wannan tekun.
Wasu ramuka ne masu É—an zurfi kamar rijiya a É—an nesa da bakin ruwan, mafiya yawan manyan dajuka irin hakan ana samun irin waÉ—an nan ramuka sosai, wasu ramukan zaka tarar irin bishiyoyi masu fitowa a kwancen nan suna rufe kofar shigarsu, wasu kuma ganyayyaki da dogayen ciyayine ke cika rakukan, bare yanzu da ya kasance gari na damuna, akwai yelwar ganyayyaki koraye shar a ko'ina a dajin, hakan yasa baka iya ganin wasu ramuka ma sosai.
Kwance take a cikin wani katafaren rami mai kama da rijiya, ramin yana da É—an zurfi kuma yana da faÉ—i, haka zalika akwai yelwar dogayen ciyayi a cike a ciki wanda suka rufe har baki, muddin mutun yana ciki ba zaka iya ganin shi ba har sai idan shi ya yaye waÉ—an nan ganyayyaki ya leko kansa waje, sannan ne zaka gan shi.
Abin da ya faru shi ne, a lokacin da ta faÉ—a kasan dutsen ne iska ya kwasheta zuwa cikin ramin, dama kunsan idan kazo faÉ—awa waje irin wannan akwai igiyar iska mai karfi tamkar ta ruwa da take fisgar mutun, bugu da kari ga iskar ruwan sama mai karfin gaske, Allah ya taimaketa ya kuma ceceta ta yi sa'a a in da ta faÉ—a cikin ciyayin ba tare da ta ji ciwo ba, ta kuma faÉ—a ta baya baya ne ba ta gaba ba, Allah ya kare mata cikin nata, ikon Allah kuma bata ji wani jiri ko wani abu makamancin shi ba, sai dai suma da ta yi saboda razana na irin tsayin wajen da ta faÉ—o É—in, dama kunsan irin wannan akwai razana zuciya.
(Sai dai ni Princess Teema ban yarda da cewa ita ta shiga cikin ramin nan ko iska ya kai ta ba, dan dole akwai ayar tambaya, amma dai bari mu cigaba da bibiyarta mu gani!)
Bayan faɗawarta da ɗan tsawon lokaci ne ta farfaɗo daga sumar da ta yi saboda ruwan sama dake zuba yana taɓata, har a lokacin babu alamar hawaye a idanunta ko kaɗan, idanunta suna bushe, da alama ta saba da wahala sosai, zuciyarta ta bushe sosai, dan duk wannan abin da ya faru bata sare ba, bata karaya ba, muradin cigaba da rayuwa ne ziryan a cikin kwayar idanunta, da alama jaruma ce ta gasken gaske! Dan kuwa ko da ta faɗa cikin ramin babu alama na wahala ko nuna gajiya a tattare da ita, tana da taurin zuciya da taurin rai, da alama an gwabza abubuwa da ita ba kaɗan ba, an kara da ita ba kaɗan ba a baya, ga dukkan alamu ba karamar yaki aka buga da ita ba kafin a iya kaita ƙasa ko in ce a iya samun nasarar jefata cikin wannan hali da take a ciki!.
Jini ne yake zuba sosai daga cikin nata, sai dai da ikon Allah ta iya cire kifiyar da suka harbeta da shi, kuma ta yi sa'a kifiyar bata soketa sosai ba, da alama wanda ya harbeta da kifiyar duk yadda aka yi akwai wani abin a ƙasa tsakaninta da shi, domin kuwa bai harbeta a in da zata raunata sosai ba, bai harbeta a in da zata mutu ko kifiyar ta yi mata illah ba, kuma da alama kwararren maharbine, yasan kwari da baka sosai, yana da saiti, domin kuwa yadda ya harbeta a gefe guda babu saɓa saiti ko kwana kwana, alamu sun nuna yana sane ya kaucewa harbinta a in da zata iya mutuwa ko ta cutu, wata kila da wata manufa ya aikata hakan, amma lokaci ne zai nuna mana komai.
Tattare iya karfinta ta yi tare da miƙewa zaune ta cire alkhabbar jikinta, sai haki take yi sosai, dan a lokaci da ta farfaɗo ta fahimci waɗan nan azzaluman mayakan sun nufo in da take suna nemanta, hakan ne yasa ta rike numfashinta ta hanyar toshe hanci da bakinta da gefen alkyabbar tata, shi ne yasa yanzu take numfashi sama sama, dan sai da ta ji motsin barinsu wajen, sannan ta saki numfashinta, kunga kuwa dole ta yi haki sosai, dan rike numfashi ba wasa ba.
Da kyar ta iya zare alkyabbar daga jikinta, a in da ta É—aure gefen cikin nata da yake zubar da jini da shi, sai buÉ—e baki take yi alamar kishin ruwa kamar zata mutu. Idan ya jima ya jima sai ta É—aga kanta sama tare da buÉ—e baki tana tarar ruwan sama dan ta samu ruwan ya shiga bakinta ta É—an sha, so abin ku da ruwa idan ba'a indararo yake ba, sam baya zuba sosai duk karfin gudun ruwan sama, amma Alhadulillah ta É—an sha sosai har ta ji duniya ya É—an saki mata ta dawo cikin hayyacinta.
Ƙoƙarin miƙewa ta yi dan ta fita daga cikin ramin, lokacin ta ji ta ɗan sami sauki bayan wasu mintuna kenan, amma ina ta kasa miƙewa, koda kuwa ta miƙe ba zata iya fita daga cikin ramin ba, saboda yafi tsawonta sosai zurfi, da wannan katon cikin nata kuma ba zata iya buɗe kafafunta ta taka gefe da gefensa dan ta fita ba.
Komawa ta yi ta zauna sai a lokacin ta lura da ta kukkuje a hannunta, jajir kuma lallausan fatarta na singalalin hannu zuwa yatsunta duk sai jini yake yi, dama ga fatar luwai luwai da shi, zai yi saurin jin ciwo, ba iya hannu ne kawai ta kukkuje ba, har da kafafunta da sauran sassa na jikinta.
Har lokacin bata iya wani numfashin kirki, runtse idanuwanta ta yi a inda ta fara karanto addua'o'i kala kala dan neman taimakon mahaliccinmu, domin kuwa idan ba Allah ba, babu wanda ya isa ya ceceta daga cikin wannan hali da take a ciki.
A hankali ruwan sama ya fara cika wannan rami, da yake a gangaren tekun ramin yake, sai ruwan gudu ya fara shigowa. Jin hakan na ruwa na shigowa ne yasa ta yi yunkurin ta sake gwada miƙewa a karo na biyu, amma ina, ko motsin kirki ta kasa yi. Hasbunallahu wani'imal wakil shi ne abin da take ta maimaitawa a cikin zuciyarta.
Wani irin azababben murÉ—a da cikinta ya yi ne yasa bata san lokacin da ta kwallah kara wanda har sai da muryarta ta fita duk dashewa da ta yi ba, da yake ta sha ruwa ne sai muryar tata ta É—an saki har sauti yana fita.
Dafe cikin nata ta yi tana mai cigaba da furta sunan Allah a ranta.
Da kaÉ—an da kaÉ—an ciwon cikin nata yake karuwa yayinda mararta ya kulle gam yana yi mata wani irin azababben ciwo. Nan take idanuwanta suka kara raina fata a in da a wannan karon suka yi jajir kamar wuta, saboda azaba.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.