Complete Hausa Novels

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Rawanin_Zalinci_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 7 of 24

Cigaba da yin shirinta ta yi tana faÉ—in. "E lallai auta kin girma, wato ji kike yi kusan É—aya kike da su ko? Wlh bari Omaid ya jiki, kin san halinsa da shegen son girma, ranar har da cewa ya yi wai ya girme ni".

Dariya sosai autar ta yi, Obaid and Omaid akwai shegen son girma kamar me, sai dai kuma kash sun yi rashin sa'a sune kanana, auta kawai suka fi shekaru a gidan, amma sai su dage su ce sun fi su Chuchu shekaru.

Ƙarisa shirinta tsab ta yi, sai ta fito a cikakkiyar jinin sarauta, ta ɗauko wani dankareran alkyabbarta fara tas ta ɗaura a saman doguwar rigar tata, ga rigar launinta baki ne, sai alkyabbar ta zauna sosai, ta yi kyau sosai da sosai. Feshe jikinta da daddaɗar Dubai perfume nata ta yi kafin ta fito da wani kyakkyawar tsadadden cover shoe na ƴaƴan sarakuna ta sanya a fararen kafafunta, cover shoe ɗin launin white color ne kamar alkyabbar jikinta.

Hular alkyabbar ta sanya a kanta kafin ta nufi hanyar fita daga cikin É—akin tana cewa auta ta zo su yafi wajen uncle Abbas.

Da saurin autar ta miƙe ta rufa mata baya. Elevator suka hau zuwa kasa. Suna sauka kasa suka nufi part na uncle Abbas ɗin, part ɗin yana ɗan gefe da nasu ne.

Ƴan'sanda da sojoji ne cike ta ko'ina a arear part ɗin, dan fa uncle Abbas babban ɗan siyasa ne wanda yake a matsayin vice president mai ci a yanzu, mulki a hannunsu take, kasancewar KINGDOM OF POWER tana da manyan ƙusoshin gwamnati da suka fito daga cikinta ne yasa masarautar ta kara karfin iko tare da karfin faɗa aji a duniya, dan babu wani gwamnatin da zai kawo masu wargi, dama can shi King Zuhair gwammati bata ishe shi kallo ba.

Duk in da suka zo wucewa sai sojoji da Æ´an'sandan sun sara masu, saboda kowa yasan su waye ne su É—in.

Kai tsaye cikin part É—in suka nufa, kowani kofa suka je sai É—an'sanda ya buÉ—e masu kofar, a haka har suka isa wajen elevator, nan ma wani É—an'sanda ne tsaye a wajen.

Shiga ciki suka yi tare da nufar hawa ta biyu abinsu, sai hira suke yi tamkar wasu taurari, ba zaka taɓa cewa ƴaƴan kishiyoyi bane su ɗin, sun haɗa kansu sosai, da yake ma dukkansu basu da matsala, basu ɗauki duniya a bakin komai ba, ba ruwansu da wani zancen ai su ƴaƴan kishiyoyi ne, iya abin da suka sani kawai shi ne ubansu ɗaya, kuma suna girmama mahaifiyar kowa daga cikinsu tamkar ita ta haifesu, su biyun nan na ce maku sun fita zakka a cikin ƴaƴan king Zuhair, suna da banbanci dasu Fanan, Sarina and bloody sosai, bama su haɗa hanya ba.

Kai tsaye babbar parlourn uncle Abbas suka nufa, bai jima da dawowa daga fada ba, yana zaune a tare da Jawad suna hira, da alama saboda zuwan nasa ne ma yasa Jawad É—in ha dawo daga office, ya zo su gaisa da mahaifin nasa su É—an yi hira. Ita kuma Mammie wato mahaifiyarsu Jawad É—in bata wajen, da alama tana cikin part nata.

A kasa saman wata lallausan Turkey carpet suka zauna, carpet nan ta amsa sunanta, ga laushi ga kyau da tsada, naunin ash color mai duhu kalar luntsuma luntsumar sofas dake a cikin parlourn, parlourn dai ba sai na gaya maku ba, kunsan ya haÉ—u over, ya ji komai na more rayuwa.

Jawad yana zaune a saman sofa mai zaman mutun biyu, shi kuma uncle Abbas yana zaune a saman sofa mai zaman mutun uku, babu maraba a tsakanin fuskar Jawad da ta mahaifinsa, suna kama sosai, sai dai Jawad da yake sabon jini ne ya fi uncle Abbas kyau sosai, kyansa ya fi fitowa sosai.

One think about familyn marigayi King ABDUL MALIK, kusan gabaÉ—ayansu idanuwansa mai design na kifi ne, irin idanun nan ne da zaka gansu tamkar zanen ice fish mara bindi, ga idanun nasu dara dara kuma farare tas, duk sun gado marigayi.

Cikin girmamawa gimbiya Chuchu ta É—agawa uncle Abbas gaisuwa.

Wani irin fara'a ce ta bayyana mashi a saman fuskarsa.
"Ku tashi ku zauna a saman sofa, a saman sofa ma ku dawo kusa da ni".

Shi ne abin da ya ce dasu, mutumin kirki, su kuma yaran kirki, sun sami tarbiya sosai. Ba musu suka koma saman sofar da yake zaune a kai suka zauna.

Cikin girma da arziki suka gaisa da shi, sai murmushi yake yi ya jawo auta jikinsa. Ko kallon in da suke Jawad bai yi ba, sai ma fitar da wayarsa da ya yi ya fara aikin latsawa.

"Yah Jawad ina wuni." Cewar Auta.

Ba tare da ya É—ago da kallonsa daga kan wayar ba ya amsa mata a takaice da lafiya.

Shiru Chuchu ta É—an yi tana tunanin ta gaishe shi ne ko dai ta yi shiru tun da yanzu ba jimawa suka gaisa. Ganin cewa auta ta gaishe shi yasa ita ma ta ce.
"Yah Jawad ina wuni?".

Ita ma ba tare da ya ɗago da kallonsa ba ya amsa mata da lafiya a taƙaice.

Sai satar kallonsa Chuchun take yi, tana son ganin a ina ya ajiye mata wayarta ne? Me kuma zai yi da ita? And ina wayar Aunty Sarina ma da ya karɓa jiya?.

Uncle Abbas É—in ne ya katse mata tunanin da take yi ta hanyar tambayarsu ya school. Da murna suka amsa mashi da school Alhdulillah. Daga haka ya shiga tambayarsu yasu Momma da sauran abubuwa, suka kama hira dai a kan gidan da kuma familyn.

Miƙewa Jawad ya yi ya fice daga cikin ɗakin ya basu waje abinsa.

Nima na haÉ—a kayana zuwa wajen KAMRAN, wata kila kafin mu dawo sun gama hirar gari sun shiga wani sabgar.

🏞️FOREST🏞️

A hanzarce Kamran ya ƙarisa wajen da wannan yarinyar ta shiga. Da sauri Rocky ya rufa mashi baya.

Yana zuwa bai yi wata wata ba ya sa hannu kamar yadda yaga ta yi shi ma ya buÉ—e wajen.

Wayam cikin babu kowa kuma babu komai sai wani tsani mai É—an tsawo da aka kyara shi da itace da yake a bakin ramin, shi ake takawa a sauka ciki.

Babu tsoro babu komai Kamran ya afka ciki ramin abinsa, dan shi burinsa kawai ya kalli Mum twins, bai san ya yanayin wajen yake ba, bai san menene a cikin wajen ba, shi dai kawai ya afka, wannan shi ne komai ta fanjama fanjam.............

🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 11/7/2024.....✍️📚🌹

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________12🔥

Babu tsoro babu komai Kamran ya afka ciki ramin abinsa, dan shi burinsa kawai ya kalli Mum twins, bai san ya yanayin wajen yake ba, bai san menene a cikin wajen ba, shi dai kawai ya afka, wannan shi ne komai ta fanjama fanjam.

Rocky ya yi ƙoƙarin shiga cikin wajen ya bisa, sai dai ina, ba zai iya wucewa ba, jikinsa ta yi girma sosai. Wani irin kuka mai haɗe da wannan irin gurnani na Tiger ba Lion ba ya saki, da alama ya ji babu daɗi ne, dan ba zai so Kamran ya shiga wani wajen da bai sani ba a cikin dajin nan, kada wani abin ya same shi, hakan yasa sai bai ji daɗi ba sam da jikinsa ta kasa wucewa.

Kun san ita dabba fa a yadda kika reneta a haka zata taso maki, yanayin training É—in da kika bata tun tana karama a haka zata kasance, to shi Kamran a gaskiya duk inda zai shiga a cikin wannan daji a tare suke shiga da Rocky, cikin kogonsu ne kawai Rocky baya iya shiga, shi ma ai kunga saboda girman jikinsa ne, so tun da suka taso haka suke da Kamran É—in, hakan yasa a yanzu idan Kamran ya je wani wajen da shi ba zai iya shiga wajen ba, sai ya yi ta kururuwa yana kuka, ko gida ya je bai sami Kamran É—in ba irin ya fita cirowa Mamma wani abin, to ba shakka Rockyn sai ya nemosa sun dawo a tare, kamar wasu abokai.

A bakin ramin ya tsungunna tare da sa kansa a wajen ramin yana bibiyar numfashi da kuma yanayin kamshin dake wajen, É—aya daga cikin baiwar Damusa kenan, ba dai iya tantance abu da kamshi ba kam, yanzu zata gane menene.

Shi kuwa Kamran tafiya mai ɗan zurfi ya yi a cikin wannan rami, a nan ne ya fahimci e lallai hanya ce wajen, bama gida bane tukun nan, hanya ce wadda jiga jigan mutane madaka katti suka haɗa su, tun da yake a wannan daji bai taɓa ganin irin wannan hanya ba, hakan ya bashi tabbacin cewa lallai wannan hanyar hannu ne ya kyarata. To waye kenan?. Mu je dai zuwa, in dai ana tafiya komai nisan waje ai za'a cin mata, lokacin ne zai yi mana alkalanci.

Cak ya ja ya tsaya a lokacin da idanuwansa suka sauka mashi a saman ginin da yake a cikin wajen bayan tafiya mai ɗan nisa da ya yi a tsakaninsa da bakin kofar shigowa ramin. Da farko idan ka shigo cikin ramin ma wlh zaka yi zaton rami ne kawai wadda ƙasa ta burma, sai ka lura da kyau zaka ga wata ƴar siririyar hanya ta wucewar mutun ɗaya a wajen, da alama koma wanene ya yi wannan gini mutun ne mai matuƙar basira, domin ya yi ginin ne ta yadda komai nacinka ba zaka taɓa sanin akwai mutane dake rayuwa a cikin wajen ba, shi ma Kamran ɗin ba dan ya riga da ya ga shigarta wajen ba, da ba zai taɓa yarda cewa da akwai mutane a cikin wajen ba, da farko ma har yaso ya koma da ya ga cikin ramin babu komai, sai daga baya ya lura da wannan ƴar hanyar da take wajen, wadda take manne da jikin gini baka iya ganinta cikin sauki, sai mai kaifin basira.

Tun da yake bai taɓa ganin gini da ɗaki irin wannan ba, akwai komai a wajen, tamkar ɗakin gaske, komai da suke amfani da shi a wajen ya sha bamban dana Mamman Kamran ɗin, and then suna da ventilation sosai a wajen, wadda aka yi su tamkar da pipe na ruwa, ginin dai ya tsaru matuƙa.

Zuba ma yarinyar da ta gudu ta shigo cikin wajen idanu ya yi yana kallonta, canza kayan jikinta take yi kasancewar sun jike da ruwa, ga wata kyakkyawar yarinya mai kama da ita sak kwance a saman bed, sai dai ita gashin kanta golding white ne.

Abin mamaki tana kwance a saman wannan gado nasu mai kyau ba irin na Mamma ba, idanuwanta a buÉ—e tana fuskantar Kamran É—in, amma kuma bata yi magana ba, ga idanuwan nata dara dara kamar na wancan yarinyar, ga su farare tas da su, kwayar idanunta kuma sak na wancan yarinyar wato olive.

Ganin sai kallonsa take yi babu ko kyafta ido kuma bata yi magana ba yasa Kamran É—in ya É—aga mata gera guda, alamar ya aka yi ne?.

Ita kuma ɗayar yarinyar sam bata san da ya shigo cikin wajen bama, sai ƙoƙarin cire kayanta take yi. Ta cire sket da rigar, ya rage daga ita sai pant, tana ƙoƙarin ciro wasu kayar daga wani waje mai kamar da wardrobe da aka yi shi da katako.

Sai dube dube Kamran yake yi a cikin wajen ko zai ga mum É—insu, amma ina babu ko mai kama da ita a wajen.

Ciro wata doguwar riga mai bala'in kyau ta yi, Kamran bai taɓa ganin kayayyakin sakawa irin haka ba, shi dai na saka kawai ya sani wadda Mammansa take saƙawa, hakan yasa ya kara kurawa kayan hannun nata idanu sosai. Ba abin da ya bashi mamaki ma face irin yadda aka kyara saman ɗakin, ta yadda ya zauna zam zam, da alama ba ƙaramin aiki aka sha ba wajen haɗa wannan waje, koma suwaye suka yi shi sun sha aiki kam babu karya, kuma sun yi namijin ƙoƙari.

Zura doguwar rigar ta yi a jikinta tana faÉ—in. "Sweetie bari in zo ki ja mun zip na rigar nan".

Ta yi maganar ne cikin harshen turanci, to su da suke daji kuma a ina suka koyo turanci? Da alama dai Mum É—insu ba ta a tare dasu bare ace ita ta koya masu kamar yadda Mamman Kamran ta koya mashi.

Tana ƙoƙarin juyawa sai ji ta yi mutun ya ja mata zip ɗin rigar. A razane ta juyo, duk da cewa tasan ba ita kaɗai bace a cikin ɗakin amma ta razana, dalili kuwa shi ne ita sweetie bata gani, ga idanuwanta a buɗe dara dara farare tas, amma sam bata iya ganin komai, makauniya ce, kunga kuwa dole ta tsorata da jin an ja mata zip ɗin.

Tana juyowa taga mutun a tsaye a bayanta, tsoro ne ainun ya bayyana a saman fuskarta, hannayenta har sun fara kerma, da alama mayyar tsoro ce sosai.

"Where's your mum?". Shi ne tambayar da Kamran É—in ya jefa mata bayan ya kammala ja mata zip É—in rigar sama.

"We don't know where she is".
Ta bashi amsa muryarta a matuƙar tsorace, sai ma rawa muryar tata take yi. Hakiƙa ta kasance tana da zaƙin murya mai bala'in daɗi sosai.

Sweetie dake kwance a saman bed É—in ne ta ce.
"Pretty you and who, who are you talking with?". Sweetie tana da sanyi murya mai daɗi sosai ita kuma, Pretty zaƙin murya Sweetie sanyin murya.

Cike da tsoro ta kawar da kallonta daga kansa izuwa kan sweetie dake shirin ta yunƙura a yanzu zata miƙe zaune, dan ta ji ƴar uwar tata tana magana, kuma ta ji wata murya ta daban da bata taɓa ji ba ya yi magana, shi ne abin ya ɗaga mata hankali, dan ita dai tasan su biyu ne kawai a cikin wannan waje, to da waye pretty take magana? Ta tambayi kanta.

Cikin hanzari ta raɓa ta gefen Kamran ɗin ta wuce izuwa kusa da sweetien tana mai gaya mata.
"I don't know him, kawai nima ganinsa na yi".
Ta bata amsa tare da matsowa kusa da ita sosai.

Shi ma juyowa ya yi ya biyota izuwa in da suke zaune É—in, a gefe ya zauna yana mai cigaba da tambayarsu ina Mamarsu.

Sweetie ce ta ce mashi. "Who are you? And what do you want from our mum? Why are you asking where's she?". Ita ma muryarta na rawa ta yi maganar.

Kankameta Pretty ta yi kamar Kamran É—in ya ce zai rabasu ne, suka wani rungume juna.

Nisawa ya yi kafin ya bata amsa da cewa. "Please tell me where's she?, I want to talk to her".

Pretty ne ta karɓi zancen da cewa. "Mum isn't around, we don't know where's she, since last year ago we're looking for her, but we didn't see her".
Tana magana tana kara ƙanƙame sweetie sosai.

Shiru ya É—an yi yana tunanin maganganunsu, kenan sun girma a tare da mahaifiyarsu? Last year ne suka rabu da ita? To ina take? Ya aka yi suka rabu da ita bayan kasancewarsu tsawon shekaru tara a tare?.

"Who are you?".
Sweetie ne ta jefa mashi wannan tambayar, wadda hakan yasa ya dawo daga cikin duniyar tunanin da ya afka.

"Am Kamran, ku ba zaku sanni ba, but your mum know me well, zaku iya gaya mun ya aka yi kuka rabu da mum É—in taku?".

Da alama sweetie ita ce babba a kan pretty, domin yanayin maganarsu ne ya nuna haka, and da alama sweetien ta fi nutsuwa da sanin yakamata, gata so silent bata da hayani, Allah sarki ga laluran rashin gani.

"Fita waje ta yi zata je ciro mana kayan marmari da sauran abubuwan da muke amfani da su a gidan nan yau da kullum, shi ne bata sake dawowa ba, mun nemeta har mun gaji bamu ganta ba". Cewar sweetie. Ta kuma kai karshen maganar idanuwanta a cike tab da kwallah.

Da sauri Pretty ta ɗago tare da ɗan raba jikinsu daga ƙanƙame juna da suka yi, murya cike da damuwa ta ce
"Sweetie don't cry please, kin san mum ta hanaki kuka ko? Idan kika yi kuka idanunki ba zasu taɓa warkewa ki fara gani ba".
Ta yi maganar kamar zata yi kukan ita na.

Da mamaki É—auke a saman fuskarsa yake kallon su, ya kasa gane me suke faÉ—a ma, dan duk hankalinsa ya karkata ya koma tunanin mum É—in tasu, ina ta je tsawon shekara É—aya haka ta barsu? Duk soyayyar uwa da Æ´aÆ´an tan nan dai ta tafi ta barsu? Abin da mamaki.

Pretty ne ta katse mashi tunanin da yake yi da cewa.
"Mum ɗin mu ta ce akwai wani da ya taɓa taimaka mata a lokacin da ta haifemu a cikin wannan dajin, mun sha nemansa sosai bamu gansa ba, ko zaka taya mu nemansa? Dan mum ta ce mu nemesa ko bayan babu ita".

Ƙasa da kansa kaɗan ya yi yana sauke nannauyar ajiyar zuciya, koba komai ya ji daɗi da ya kasance mamansu bata manta da shi ba, har ma ta gayawa ƴaƴanta su neme shi, ya ji daɗin hakan sosai.

"Kin san kamanin wanda ya taimaketa É—in ne?". Ya tambaya yana É—ago da kallonsa a kanta.

Da sauri ta girgiza mashi kanta alamar a'a bata sani ba, har yanzu gashin kanta akwai danshin ruwa sosai, hakan yasa ya mammanemata a wuyarta har izuwa bayanta, dan bai bushe ba.

"Tom shikenan zamu nemo mutumin kin ji? Amma yanzu faÉ—a mun me ya sami Sweetie a ido da yasa bata gani?".

"Wani itaciya mai guba ta je ta taɓa a lokacin tun muna da 7 years a duniya, da ta taɓa kuma sai furen itaciyar ya zuba mata a cikin idanunta, hakan shi ne yasa ta dai'na gani, mum tasha kuka sosai a lokacin da ta dai'na ganin".

Nisawa ya yi, ko ba'a gaya mashi wace itaciya bace yasan wacce ce, muguwar guba ne da itaciyar, har kurumta mutun tana yi, tana kisa sosai, dan yadda kuka san poison haka take, ba'a cika samunta a kananan dajuka ba, sai a manya manyan irin wannan dajin, bata da yawa sosai itaciyar, tana nan tamkar itaciyar dalbejiya, sai dai jikinta ma yana yin wani irin farin abu kamar kumfa, gabaɗaya jikin itace a mamaye yake da wannan abu kamar kumfar fari kal, a yankin Arewacin duniya suna kiranta silent killer, anfi samunta ta gefensu kuma, irinsu wani ɓangare daga cikin Asiya, irinsu noth korea duk sun shiga ciki, north Korea dama kunsan yana ta East asia ne, da irinsu Canada, Greenland, Mexico, Central America, Bahamas da dai sauransu, anfi samun irin itaciyar ta wajajen.

Shiru dukkansu suka yi, kowannensu da abin da yake tunani, can Kamran ya katse masu shirun da cewa.
"Wanenen ya gyara maku wannan É—akin?".

Sweetie ce ta amsa mashi da cewa. "We don't know them, mum É—inmu ce kawai ta sansu, da ita kawai suke yin magana idan suka zo, and suna zuwa su kawo mana abubuwa irinsu kayan sakawa da kuma abinci da sauransu, su ne suka gyara mana É—aki, amma tun da mum ta tafi suma basu sake zuwa ba, so only me and pretty ne kawai muke rayuwarmu a yanzu".

Shiru ya É—an yi yana tunanin ranar da ya fitar da mum É—in tasu daga cikin wannan ramin, da Mamma ta kira sa ya je, kafin ya dawo ya samu an gyara yaran da Mamar tasu, abin ya bashi mamaki, ashe ga wani abin mamakin ma a nan, to wanenen wannan da yake taimaka masu É—in kuma? Su waye suma tukun nan?.

Ganin ya yi shiru ya lula duniyar tunani ne yasa pretty ta ce."Zamu je mu nemo mutumin ne yanzu? Dan mum ta ce lallai mu nemo shi ko da bata nan, wai da shi kaÉ—ai ta yarda a dajin nan".

Zuba nata idanu ya yi yana kallon ɗan bakin nan nata, ba abin da ya faɗo mashi a cikin ransa face ranar da aka haifesu da ta rinƙa kuka kamar wadda ake zanewa, bai san lokacin da gajeran murmushi ta bayyana a saman fuskarsa ba, yanzu ta girma an dai'na kuka.

"Sai gobe zanzo muje neman mutumin a cikin daji, yanzu dai zan je gida, idan shirun ya yi yawa Mamma zata nemeni, amma anjuma zan dawo na sake duba ku?".

Da alama baya son gaya masu shi ne wanda suke nema, kome dalilinsa oho, suma kuma ko me dalilinsu na nemansa oho.

"To zamu jiraka, amma dai ita Sweetie bata fita waje fa, dan kaga bata gani, kada ta je ta ji ciwo, so ita a nan zamu barta". Cewar pretty kenan, ta bashi amsa.

Girgiza kai ya yi yana faɗin. "A'a dole yanzu zata rinƙa fita waje, saboda idan bata fita tana ganin hasken rana da sauransu, to idanun nata kara lalacewa zasu yi".

Jinjina kai dukkansu biyu suka yi, alamar sun yarda da zancensa, sun yarda Sweetie zata rinƙa fita waje ita ma, ba kullum ta yi ta zama waje ɗaya ba.

Miƙewa tsaye Kamran ɗin ya yi, jikinsa duk a mace, duk ya yi sanyi, kamar an zare mashi laka, sai dai a cikin ransa ya kudurci niyar kula da twins ɗin nan tamkar yadda zai kula da kansa, kuma ya kudurci niyar neman mum ɗin ta su ko tana a cikin wannan dajin ne, ko wani dabba ne ya cinye ta? Yara bayin Allah gwanin ban tausayi.

Nufar hanyar fita daga wajen ya yi. Da ido Pretty ta bishi da kallo. Sai da ya tafi ya É—an yi nisa, sannan ya É—an juyo da kallonsa a kansu, har lokacin ita ma Pretty shi take kallah.

Sai da ya ji tsikar jikinta ta tashi wannan haɗa idon da suka yi, shi idanun nata ma suna sanya shi faduwar gaba, idanun ne kamar ta sanya masu kwalli, ga su dara dara farare tas, olive ɗin kuma ya fito kalarsa sosai, sai hakan yana sanya ya rinƙa jin faɗuwar gaba, bare ma idan ta kafe shi da su, duk sai ya nemi nutsuwarsa ya rasa, sai ya fara wasu ƴan kame kame kamar wani mara gaskiya, sai ka ce ba jarumi Kamran ba, kaifi ne da idanun nata da idan ta tsare mutun da shi sai jikinsa ta amsa.

Ganin sai kallonsa take yi babu ko kyaftawa ne yasa ya ce mata lafiya?.

Girgiza mashi kai ta yi alamar babu komai.

Shiru ya ɗan yi yana jin kamar kada ya tafi ya barsu a wajen, sai dai kuma babu yadda ya iya, ko zai mutu Mamma ba zata karɓesu ba, ai da ba abin da zai hana bai ɗaukesu daga wajen nan ba, har cikin ransa yake matuƙar kaunarsu kun sani, sai dai hakuri kawai zai yi, dan ba yadda ya iya da Mamma, bawan Allah baruwansa da hayaniya. Mamma kuma babu sauki lamarinta.

"Pretty why are looking at me like that?".
Ya faÉ—a shi ma yana cigaba da kallon face nata, sai dai ya kawar da kallonsa daga ganin cikin kwayar idanunta, dan shi dai har ga Allah idanun nata suna rikita shi bawan Allah, shi ne yasa baya iya kallonsu sosai, ga su kuma da shegen kyau, duk wanda ya kallesu zai so ya sake kallah, amma shi Kamran ina, yana son kallo amma rashin kallonsu É—in ya fi mashi alkhari.

Babu komai ta bashi amsa, sannan ta É—an kawar da kallonta daga kansa.

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya cigaba da tafiya yana aikin tunani a kan wanda yake zuwa taimaka masu a lokacin da mum ɗin take nan, to meyasa yanzu da mum ɗinsu bata nan ya dai'na kawo masu agaji? Ai a yanzu ne ma ya kamata koma wanenen ya rinƙa kawowa yaran ɗauki, yanzu ne suke da buƙatar taimako tun da mum ɗinsu bata nan, amma kuma sai a ɗauke masu tallafi, kenan dan mum ɗinsu dama ake yin hakan? To wai ina mum ɗin? And meyasa daga ɓatarta masu taimaka masun ma suka ɓata? Wannan abin da ɗaure kai yake, su dai warriors da suka biyota a farko alamu sun nuna ba ita suke da buƙata ba, abin da yake cikin cikinta suke da buƙata, hakan yana nufin twin's ɗin zasu ɗauka idan ma ɗauka ne ba mum ɗinsu ba, wai me yake faruwa ne?!!!!.

Yana juyawa ya cigaba da tafiya ita kuma ta dawo da kallonta a kansa, cigaba da kallonsa ta yi har ya kai dai'dai kwanar da zai ɓacewa ganinsu, hakan yasa shi ma ya sake juyowa a karo na biyu domin ya yi masu kallon bye bye.

Ganin ya juyo yasa ta kawar da kallonta daga kansa, ta sunkuyar da kai ƙasa tana wasa da ƴan ƴatsun hannunta. Ita dai Sweetie da yake bata iya ganin komai, sai ta yi shiru abinta babu ruwanta.

Ya É—auki a kallah two mins yana kallonta kafin ya sa kai ya wuce. Kafin ta É—ago kai ta yi mashi kallon karshe har ya wuce ya bar wajen.

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta dawo da kallonta a kan Sweetie dake fuskantar hanyar shigowa, sai dai baiwar Allah bata iya ganin komai, abin gwanin ban tausayi.

"Sweetie ki koma ki yi kwanciyarki, mutumin ya tafi ai, ni kuma bari na yayyaka mana irin gayyakin da mum take yanka mana É—in nan".

Ta yi maganar tana mai taimaka wa Æ´ar uwar tata dan ta kwanta. Duk wani abin da yake cikin É—akin nan nasu daga cikin gari aka kawo masu shi, waÉ—an nan masu taimaka masun ne suka kawo komai, amma sun kasa iya É—aukarsu su fitar da su daga cikin wannan dokar dajin, sai dai su kawo masu taimako a cikinta su kuma tafi su barsu a cikinta, abin da abin mamaki da kuma É—aure kai!.

Kamran kuwa, yana fitowa Rocky ya yi maza ya miƙe yana shinshinarsa, wucewa gaba ya yi ba tare da ya bi ta kan Rockyn ba, dan yanzu baya a cikin natsuwarsa sosai, ƙwaƙwalwarsa cike take tab da tarin tambayoyi game da tunani, ya saka wancan ya kwance wancan, ya rasa amsar da zata gamsar da shi, ya rasa amsar da zata sanya mashi nutsuwa, ƙwaƙwalwarsa ta shiga ruɗani sosai a kan al'amarin twins ɗin nan da mum ɗinsu.

Da kyar ya iya farautowa Mamma namar da ta aike shi, jikinsa duk babu kwari, a mace yake.

Yau nama É—aya ma ya kama, kuma akuyar daji ce ya kama, a saman bayan Rocky ya É—aurata, dan shi yau baya da kuzarin iya É—aukar abu mai nauyi.

A haka suka isa wajen tsauninsu, Rocky ne ya fara hayewa dan ya je ya sauke wannan akuyar dajin dake a saman bayarsa. Shi kuma Kamran ɗin yana ƙoƙarin hawa ya ji alamar motsi ta bayan tsaunin nasu.

Shiru ya kasa kunne yana son ya ji motsin menene?. Tabbas akwai motsin dake fita da sauti kaÉ—an kaÉ—an, sai dai bai iya tantace motsin menene bane, hakan yasa ya fasa hawrawa saman tsaunin, sai ya nufi wajen da yake É—an jiyo motsin dan ya duba.

Kai tsaye ya nufi wajen, bai yi tunanin komai ba, dan a cewarsa ai motsin babu sauti sosai, dan haka koma menene a wajen ƙaramin alhaki ne.

Sai dai kash ya yi tunani mara kyau a wanna gaɓar, dan kuma yana dimfarar wajen wasu jiga jigan zataran warriors ne guda huɗu a wajen, suna tsastsaye kamar wasu zakuna, duk sun sauƙa daga saman dawakansu, ɗaya daga cikinsu yana gyara wukar takobin dake a ƙugunsa, ɗaya daga cikinsu kuma yana ɗaure takalmar dake a kafafunsa da kyau da kyau, biyun kuma suna tsaye suna bin dajin da kallo, sun rike linzaman dawakan nasu.

Ba halin Kamran ya koma da baya, dan ya riga da ya dimfarosu gadan gadan, bai yi tunanin mutane bane a wajen, sun kuma rigada sun gan shi, ba halin ja da baya. Hakan yasa ya tsaya cak a in da yake É—in yana binsu da kallo.

Cikin zafin nama biyu daga cikin warriors É—in suka nufesa tare da zare takubansu, kamar waÉ—an da suke jiran shi dama, yadda kuka san dama suna jiran kiris ne su farwa duk wanda suka samu.

Shi kuwa Kamran ko alamar tsoronsu babu a idanuwansa, ganin kananan kwari ma yake yi masu, kada ku manta renon Mamma ne shi É—in.

Suna zuwa basu yi wata wata ba suka yi yunkurin sare mashi wuya dan zalunci, sai kace ya yi masu wani laifi.

Ai kuwa shi ma bai yi kasa a gwiwa ba wajen ƙoƙarin kare kansa, nan take faɗa ya kaure a tsakaninsu mai munin gaske, dan ƙoƙarin kashe shi suka so yi, shi ma ya fito da nasa wukar dake a ƙugunsa ya fara ƙoƙarin kare kansa da ita.

Da yake shi ma ya san dabarun faɗa, yasan cewa faɗa ba karfi ake sakawa ba a cinma nasara, dabara ce kawai da zaka yi wajen ganin ka kai abokin faɗan naka ƙasa, sai Allah ya taimakesa ya kashe ɗaya daga cikinsu da wannan ƴar karamar wuƙa da take a kugun nasa, saboda shi ma yasan dabarun yaki ba kaɗan ba. Amma fa duk da haka yasha wahala kafin ya kashe ɗayan nasu, domin kuwa suma ba ƙananan kwari kamar yadda yake tunani bane, suna da karfi, kuma a matsayinsu na warriors kuma kunsan ai dole su san dabarun yaki, dan tsayayyen namiji ne shi ɗin yasa ma ya iya samun damar kashe ɗayansu, bugu da kari kuma bai tsokane su ba, bai shiga hanyarsu ba, kawai su suka kawo mashi farmaki, shiyasa Allah ya taimakesa a faɗar.

Kashe ɗayansu da ya yi ne ya kara harzuwaƙasu, gadan gadan suka nufe shi gabaɗayansu, bawan Allah bai yi masu komai ba saboda shegen zalunci sun farmakesa, a wajen kare kansa ya kashe ɗaya kuma sun sake harzuƙa sun yi kansa da nufin kashesa, a cewarsu wannan ƙaramin kwaron har ya isa ya yi wani yunkuri a gabansu, basu san cewa giwa yake mai tafiyar ƙasaita ba, basu san cewa shi ne king of this Forest ba, basu san cewa shi ɗin gayyace mai zaman kansa ba, guru ne renon zakanya Mammarsa!!.

FaÉ—a suka fara yi cikin tsantsar kwarewa da nuna fifiko a tsakaninsu, su uku bawan Allah shi kaÉ—ai.

Cikin ikon Allah, Allah ya bashi iko ya sake kashe mutun ɗaya daga cikinsu, hakan yasa suka fusata sosai, a harzuƙe suka yi kansa a in da suka damƙe shi, ɗaya daga cikinsu ne ya damƙe shi tare da yin baya da hannayensa, suka murɗe mashi hannayensa dukka biyu baya, hakan yasa dole ya nutsu, amma sai tafasa zuciyarsa take yi mashi, kunsan dama Kamran ba dai zuciya ba, akwai ta kam na kin karawa.

Ɗayan ne ya matso kusa da su tare da ɗaga takobinsa zai cirewa Kamran ɗin wuya, shi kuma ɗayan yana rike da shi gam ya murɗe mashi hannu ta baya, sai haki suke ta yi tamkar waɗan da suka sha gudu suka ƙoshi, ba karamar wahala suka sha ba wajen samun damar kama shi, dan Kamran fa ba baya ba wajen faɗa, idan ka taɓo shi tab kafin a iya kwantar da tarzomar faɗarsa sai an shirya.

Wani irin haniniya da dawakansu suka fara yi suna ƙoƙarin guduwa ne yasa warrior da ya ɗaga wuƙa zai cirewa Kamran ɗin wuya ya dakata, a dubu suka juyo da kallonsu izuwa kan dawakan nasu, domin suga menene yasasu irin wannan haniniya suna ƙoƙarin watsewa su bar wajen?.

Wayam basu ga komai ba, sai dai basu ankaraba kuma suka ga gabaÉ—aya dawakan su watse da gudu kowanne ya yi ta kansa.

A zabure warriors É—in suka fara waige waige suna neman menene dawakan nasu suka gani da yasa su suka yi irin wannan watsewa haka? Ko dai maciji suka gani ne? Kunsan doki bata shiri da maciji ko kaÉ—an, basu haÉ—a hanya.

Suna tsaka da wannan waige waige nasu basu ankara ba kamar daga sama Rocky ya faɗo gabansu yana wani irin numfashi mai rikitarwa. Ai wannan warrior da ya rike Kamran ɗin bai san lokacin da ya sake shi a dubu ɗari ba, shi ma wanda ya zaro takobi zai cire mashi wuya bai san lokacin da ya yi wata uwar ja da baya ba. Damuwa akwai kwarjinin bala'i, komai jarumtarka idan ka ganta sai ka ji fitsari na ƙoƙarin zubo maka, yo ka yi haɗuwar mutunci da damusa ma ya ka kare da bugawar zuciya da sauri da sauri, bare kuma ace ka yi haɗuwar rashin mutunci da ita? Ai shikenan faɗuwar gaba da bugawar zuciya ce ma kawai zata kasheka har lahira, kun san Damusa ta fi Zaki faɗa sosai, shi Zaki yana da hakuri, ba kasafai ya cika faɗa ba, sai zuciyar bala'i ke gare shi, amma ita Damusa, habawa ai koba tsokaneta ba wlh ta ganka sai ta farma, zaka iya tsokanar Zaki ya hakura kamar bai ganka ba, amma Damusa tab hmmmm ba'a magana.

Wani irin tsalle Rocky ya daka kan kace me ya kafawa É—aya daga cikin mayakan waÉ—an nan garma garman hakwaran nasa a wuya, sai jini, tuni ya tsinke agarar wuyar. Ai a dubu É—ari É—ayan ya fasa cikin dajin da masifar gudu yana kurma ihu.

Gudu biyu Rocky ya yi ya capkosa, dama ina za'a haÉ—a gudun mai kafa biyu da kuma mai kafa huÉ—u? Ai ba zasu haÉ—u ba sam.

Nan take Rocky ya kashesu dukkansu biyu, ya samu nama, ya maye gurbin namar Pretty da Kamran ya hana shi ci.

Duk wannan faɗar da suke yi fa Mamma tana tsaye a sama nauninsu tana kallonsu, sam abin bai yi mata daɗi ba, bata so Rockyn ya kwaci Kamran ɗin daga hannunsu ba, tafi son Kamran ɗin ya kwaci kansa gabaɗaya, dan a tunaninta irin horon da ta bashi ya ci ace zai iya kashe warriors ire iren waɗan nan har guda 20 ba tare da ya gaji ko ya nuna sarewa ba, a tunaninta a irin horon da ta bashi waɗan nan mayaƙa kananan kwari ne a gabansa, sai kuma ta ga kash da sauran aiki a gabanta, ba yadda take tunani bane, dole sai ta sake ɗaura ɗamara sosai in har tana son Kamran ya kai matsayin da take kai shi ɗin nan. MAMMA LAMARINKI BABU SAUKI🤦 LAMARINKI ABIN DUBAWA NE, YANZU INA LAIFI A NAN? AI YA KWACI KAN NASA KO? YA KASHE ZARATAR MAYAƘA DA AKA SHA DAMAWA DA SU A FAGEN YAKI YA KASHE HAR MUTUN BIYU AMMA A HAKA KICE BAI YI ƘOƘARI BA?🤔 YA MAMMA TAKE SON KAMRAN YA KASANCE KENAN?🤔

Nufar saman tsaunin Kamran ɗin ya yi yana mayar da numfashi, ya baro Rocky yana cin nama, yau dai sallar Rocky, namomi baja baja abinsa, yo me yafi ransa? Ai yau shar zuciyarsa, Rockyn mu na amana.........😅

Dawakan warriors É—in kuma sun watse sun bazama cikin daji, sun yi ta kansu kenan.

Ganin Mammarsa tana tsaye tana kallonsu ne yasa ya bita da kallon mamaki.
"Mamma what are you doing here?".
Ya faÉ—a yana mai cigaba da mayar da numfashi.

"Yanzu Kamran waɗan nan ƙananan kwarin ne ba zaka iya kashesu ba har sai da Rocky ya taimaka maka?". Yadda ta yi maganar zaka fahimci tabbas ranta ya sosu sosai da rashin kashesu gabaɗaya da Kamran ɗin ya yi.

"Mamma me zai hanani iya kashesu? Ai goma irinsu ma zan iya faÉ—a da su, kina tunanin zan bari su kashe ni ne? Ai ba zan tsaya ba, kawai dai shi Rocky shi ya yi shigar faÉ—ar shigar sauri, kuma kinsan ba wanda ya isa ya hana shi shigar mun faÉ—a ko? Ba dan haka ba da kai'na zan gama da su".

Ya kai karshen maganar tare da wucewa ya nufi wajen da Rockyn ya yardar mashi da akuyar dajin da ya kamo.

Juyawa Mamma ta yi ta nufi cikin ƙogon nasu, tabbas ta yarda da zancen ɗan nata da yake cewa zai iya kashesu, dan ita tasan ba horon wasa ta bashi ba, tun yana ɗan shekara uku a duniya ta fara koya mashi faɗa, tana da burin taga ya zama shahararren guru, bujumin Zaki, Barde tsayayyen jan wuya wanda jarumtarsa zata gigita duk wani halitta mai rai, wannan dalili yasa ta tsaya tsayin daga a kansa babu wasa.

Aikin gyarawa Mammar tasa namar ya fara yi, yana feɗe fatar akuyar kamar yadda ya saba yi mata idan ya kawo namar, shi yake gyarawa ya yanka gunduwa gunduwa, sannan ya kai mata wajen madafanta ta ƙarisa sauran aikin.

Sai dai yana yin aiki zuciyarsa gabaÉ—aya yana wajen tunanin su pretty, burinsa kawai yanzu ya gama taya Mamma iya abubuwan da zai tayata, ya yi wanka ya je wajensu, shi ko tunanin cin abinci ma bayayi, so bai sanya abinci a lissafinsa ba, shi dai ya gamawa Mamma aiki ya yi wanka ya nufi wajensu kawai. Bawan Allah ba, baruwansa da rigingimun duniya, kamar wani Musulmin kwarai.

Ni kuma kafin nan bari na leƙa gidansu Khadija, kafin mu dawo kila Kamran ya gama gyaran nama ya yi wanka, sai mu bishi wajensu pretty a karo na biyu mu ga me ake ciki.🤨🧐

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

🔥GIDANSU KHADIJAH💔🥲

Misalin karfe biyuna rana dai'dai baban Zainab ya dawo gidan, kamar yadda ya yi mata alkawarin kawo mata wasu kayan haka ya dawo mata da su, sai dai kuma da kallo É—aya zaka yi mashi kasan cewa yana cikin tsananin damuwa da tashin hankali, da alama haÉ—uwarsa da mahaifiyar tasa sam bata yi mashi daÉ—i ba.

Ganinsa a haka yasa Maman Zainab tasha jinin jikinta, dan bata taɓa ganinsa a irin wannan yanayi ba.........

🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 12/7/2024.....✍️📚🌹

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

For information 0816139058 Whatsapp me only!!.

E____________13🔥

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

🔥GIDANSU KHADIJAH💔🥲

Ganinsa a haka yasa Maman Zainab tasha jinin jikinta, dan bata taɓa ganinsa a irin wannan yanayi ba.

Kamar ko yaushe sannu da dawowa ta yi mashi kafin ta karɓi kayan hannunsa, bata jima da kammala girki ba, fitowarta daga wanka kenan, ko kaya bata sanya ba, towel ne a jikinta sai ta sanya hijabi jin cewa ana buga kofar gida, sai ta je ta buɗe kofar.

A parlourn ya zauna yana mayar da numfashi, kamar wanda ya yi gudu, duk ransa a matuƙar jagule yake.

"Ina Haidar yake maman Zainab?".
Shi ne tambayar da ya fara jefa mata.

Shiru ta É—an yi tana mamaki, domin ita ko in da Haidar É—in yake ma bata sani ba, time da ya bar gidan tana barci, a tunaninta ai baya zuwa ko'ina sai kasuwa ko wajen mamansa, bata san Haidar kam kasuwar ma sai ya yi ra'ayi yake zuwa ba.

"Haidar ya fita, kuma ina barci time da ya fita, so na É—auka ai yana kasuwa".

Shiru ya É—an yi mata na a kallah tsawon good 5 mins, sannan ya nisa kafin ya ce. "Jeki gama shirinki kizo mu yi magana kafin su Khadija su dawo daga school, dan naga lokacin dawowarsu ya kusa, yanzu ba jimawa Sadiq zai je É—auko su".

Cikin nutsuwa ta amsa mashi da to, sannan ta miƙe ta nufi cikin bedroom tare da kayan da ya shigo da su, shi kuma ya kishingiɗa a saman sofa tare da miƙe ƙafafunsa ya ɗaura hannu guda a saman idanuwansa kafin ya lumshesu.

Cikin ƙanƙanin lokaci Maman Zainab ta kammala shirinta, yau ko make up bata tsaya yi ba, saboda saurin da take yi ta ƙariso wajensa, dan ya ce magana zasu yi, so bata wani ɓata lokaci ba ta shirya ta fito.

A saman kujerar dake kusa da wanda yake kwance ta zauna, cikin nutsuwa dai ta ce mashi gata nan ta fito.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya miƙe zaune daga kishingiɗar da ya yi tare da gyara zamansa da kyau da kyau ta yadda yana fuskantarta.

"Fitana daga gidan nan da safe wajen Mama naje kafin na wuce kasuwa kamar yadda ta buƙata kafin ta bar gidan nan da safen".

Kara nutsuwa Maman Zainab É—in ta yi tare da tattara mashi dukkannin hankalinta a waje guda, dan ta saurare shi da kyau ta kuma fahimce shi.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.