Complete Hausa Novels

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Rawanin_Zalinci_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 9 of 24

Cigaba da dariyarsa mai sauti ya yi, tsabar dariyar muguntar ma ta yi yawa har da birgima a saman lumtsumemiyar mattress É—in nasu, ya wani dafe ciki, da alama wani shaiÉ—ancin ya tuna.

"Blood stop this laughing and tell me what are you laughing for?".

Miƙewa zaune ya yi tare da dafe cikinsa sosai, tsabar dariya har da hawaye suka cika mashi idanu.

Pillow Omaid ya É—auka ya fara bugunsa da shi yana faÉ—in.
"Please blood stop it now, ni bana son haka fa, ka gaya mun reason na dariyar sai nima na taya ka, amma kana ta yin abu kai kaÉ—ai".
Ya yi maganar cikin ƙaguwa na son ya ji me Obaid ɗin yake yi wa dariya haka har da hawaye.

Ganin yadda ɗan uwan nasa ya ƙagu da ya ji menene yake yi wa dariyar yasa ya daure ya tsagaita dariyar. Murya cike da shakiyanci ga kuma dariya da yake faman dannewa ya fara magana.

"Pleasure ba komai bane ya saka ni dariya face this guy called Yusuf, da wani gemunsa kamar na uncle Rahab, irin shi ustadz like Yah Muzaffar, kaga time da suka fito daga cikin car ɗinsu ina jinsa wai har da cewa baya son ɓata lokaci, da sauri zai sanya daddynsa asaka masu rana shi da Aunty Sarina, har da wani cewa tun da ita ta yi mashi ai ba wani jira da sun ga juna sai aure, wani useless da shi har yana da zaɓi, bari ma dai yanzu zai ji kansa a prison, a nan ne zai ga aure da wuri, hancinsa like Akka nose".

(Innalillahi da ji kunsan waɗan nan twins ɗin basa shiri da Akka, wai harda zagin hancinta irin na Yusuf, kai twin's sai shirin Allah 😅 Akka ma ashe tana layin waɗan da basu kauna, yo dama su ina zasu kaunaci mafaɗaci wanda zai takura masu?)

Dariya Omaid ya kwashe da shi, cikin dariya yake faÉ—in. "Not only nose É—insa ne like na Akka, even his head ma kato ne like Akka own, ka ji kazami wai zai auri Aunty Sarina, an gaya mashi ita É—in class É—insa ne? Amma gaskiya i pity this guy more, ina ga yau gunduwa gunduwa da shi ma dad zai yi, ai prison ma ya yi mashi kaÉ—an".

Shiru Obaid ya yi kamar mai tunanin wani abin, hannayensa dukka biyu ya kai saman kumatunsa ya tallabosu kamar mai tunanin wani abin, ya É—an tsuke fuska alamar tausayawa.

"Obaid are you okey?". Omaid ya yi maganar tare da É—an matsowa kusa da shi ya kuma dakatar da dariyar da yake yi.

"Pleasure yanzun nan naji tausayin guy ɗin ya shiga rai'na, yana ɗan masu muryar faɗa aji a ƙasar amma zai shiga prison? Gaskiya i pity him, amma dai ba zamu fasa yin abin da muka yi niya ba, gobe ya sake zuwa neman aure a gidan su zakuna bakwai, sai ya sha jibga wajen commander ZAFAR, daga nan dad ya ce a yanke mashi hukuncin zama gidan prison for 10 years".
Yana kai karshen maganar kamar abin haÉ—in baki kamar kuma wasu munafukai suka kwashe da dariya a tare, har da rike ciki suna rungumar juna da hannu É—aya, ai idan baka san halinsu ba wlh sai su haukataka, yanzu zasu canza fuska kamar masu tausayi da imani, cikin second É—aya kuma zasu iya sake komawa tantiransu, yanzu dai kunga Obaid wai ya tausayawa Yusuf, amma a take kuma sun sake kwashewa da dariya har da cewa ba zasu fasa abin da suka yi niyya ba, kai Allah ya shirya mana su, goyon kaka ne, kada ku ga laifinsu!.

A ɓangaren Gimbiya Sarina kuwa, suna tsaka da cin wannan abincin Yusuf ya matso kusa da ita kamar wanda zai yi mata raɗa a kunne. A hanzarce ta ja baya kaɗan, dan idan baku manta ba na gaya maku ita bata haɗa hanya da maza, bata bin maza, so ko kusa da ita bata yarda namiji ya zo.

Kara matsowa kusa da ita Yusuf É—in ya yi, da mamaki É—auke a saman fuskarta ta É—ago ta kalle shi.

Ta É—an tsorata da ganin yanayinsa, idanunsa sun sauya sun yi jajir da su, amma bata nuna alamar ta tsorata ba, sai ma ta dake ta ce mashi lafiya kuwa yake matsota haka?.

Shi ma abokinsa da mamaki yake binsu da kallo, dan yasan Yusuf dai ba zai matsa kusa da ita haka kawai ba, ba halinsa bane kusantar mata har haka, tare suka yi karatu suka yi komai, tun da yake bai taɓa ganin Yusuf kusa da mace har haka ba, amma da yake ita Sarina ya mace a kanta sosai, kuma abokin nasa ya sani, dan tun kan su zo ya bi ya cika masu kunnuwa da zancenta tare da yabon kyanta, hakan yasa abokin nasa ya yi tunanin ko dukka shaukin soyayya ne take ɗebarsa yasa ya matsa kusa da ita har haka.

Kuyangunta da suke tsaitsaye a É—an gefe ta bayansu ma baki suka saki suna ganin wannan ikon Allah.

Ita ma Gimbiya Sarina shiru ta yi tare da zuba mashi idanu tana jiran taga gudun ruwansa, sam bata san komai da yake faruwa ba.

Shi kuwa sai kara gaba yake yi, daga matsowa kusa da ita yanzu ya kai ya sa hannu ya rungumota jikinsa. A zabure ta ɗago da kanta daga jikin nasa tare da fara ƙoƙarin ture shi, saboda ita tun ainahi ma ta rai'na class ɗinsa, taɓa ta da ya yin nan sai take ganin ya cuceta ya zubar mata da class, ta fi karfin ya taɓa koda dan yatsarta.

Shi kuwa abokinsa bai san time ɗin da ya miƙe tsaye yana kallonsu ba, sunansa ya fara ambata Yusuf, Yusuf ba tare da yasan yana ambatar sunan ba, kawai ruɗewa ce tasa yake kiran sunan.

Ina ai Yusuf baya ji baya gani, kara ƙanƙameta sosai ya yi a jikinsa ya fara ƙoƙarin ta yadda zai yi ya rabata da kayan jikinta. Tashin hankali.

Zaro idanu kuyangun nata suka yi suna kallon ikon Allah, ga shi su ba halin su yi magana.

Abokinsa ma izuwa yanzu ya gama tsorata, bai san lokacin da ya yi kansu yana ƙoƙarin janye Yusuf ɗin ba, ita ma Sarina ƙoƙarin kwace kanta take yi daga gare shi, shi kuwa ƙoƙarin rabata da kayan jikinta kawai yake yi, idanunsa sun rufe baya ji kuma baya gani.

Ko da abokin nasa ya zo kama shi ma ina ya kasa, domin Yusuf ɗin yaki bashi wani dama, sai ma hankaɗesa gefe guda da ya yi ya fara ƙoƙarin yin rapen ɗinta da iya karfinsa.

Sosai abokinsa ya ruÉ—e tare da tsorata, ganin abin yake yi tamkar a mafarki, sam bai yarda cewa Yusuf ne yake aikata hakan ba.

Da dai gimbiya Sarina taga da gaske yake yi zai yi mata fyaÉ—e ya keta mata mutunci, sai ta fara ihun neman taimako, ga shi kuma da iya karfinsa ya riketa babu halin ta kwaci kanta, duk ya sauya lokaci guda kamar ba shi ba, sai haÉ—a uban gumi yake yi, ya zama kamar wani mayunwacin zaki, ga wasu zafafan gumi da suke tsastsafo mashi daga gefe da gefen face É—insa, jikinsa har wani tsuma yake yi, burinsa kawai ya rabata da kayan jikinta.

Ihu sosai take kurmawa tana neman taimako, kuma da iya gaskiyarta take yin wannan ihun, har ga Allah bata yi excepting haka daga gare shi ba, ganin ya yi shigar mutunci yasa ta yi tunanin yana da mutum koma yaya take, ashe ba haka bane.

Abokinsa ya kasa iya kwatarta daga hannunsa, domin kuwa Yusuf É—in ya saka dukka karfinsa ne a kanta. Ganin hakan yasa kuyangunta suka yi waje da gudu dan su je su sanar da family ga abin da yake faruwa.

A hanya suka ci karo da commander ZAFAR da ya fito daga fada zai je wajen mayaƙa ƴan uwansa, kamar kullum yana shirye cikin kayan yakinsa. Ganin yadda suke a birkice suna gudu yasa ya tambayesu menene yake faruwa?. Ba dan shi ɗin bane da ba zasu saurari kowa ba sai fadan King zasu kai rahoto, amma da yake sun san wanenen Zafar, sai suka dakata daga gudun da suke yi, suna ta aikin mayar da numfashi, da kyar suka iya gaya mashi cewa bakon Gimbiya Sarina ce zai yi mata fyaɗe a cikin parlourn baki.

Ai tun basu gama magana ba Zafar ya nufi wajen da sauri, su kuwa suka nufi fada da gudu dan su kai rahoto, duk suna ruɗe, sun ga abin da basu taɓa tunani ba, bako ya zo har cikin gida zai yi wa ƴar gida fyaɗe kuma a cikin parlourn iyayenta? Wannan wani irin abu ne? Lallai akwai kura ba kaɗan ba, za'ayi karamar yaki kuwa yau, King Zuhair da yake sanyawa a dandake gaban masu yi wa mata fyaɗe ne yau za'a zo har cikin gida za'ayi wa ƴar ɗan uwansa fyaɗe? Tab akwai rikici kuwa.

Ko da Zafar dattijon arziki ya shigo cikin parlourn ya tararda Yusuf ɗin ya rabata da alkyabbar jikinta yana ƙoƙarin cire mata doguwar rigar tata, sai ihun neman taimako take yi, ga abokinsa ma a kansu yana ƙoƙarin janye Yusuf ɗin daga gareta, sai abin ya yi kama da shi ma abokin yana son ya yi mata fyaɗen ne, dan a yadda yake duke a kansu sai Zafar yaga kamar tare suke ƙoƙarin yi mata fyaɗe shi da Yusuf ɗin, duk sun wargaje kayan abincin da yake waje, sun watsa komai a ƙoƙarin kiciniyar faɗa a tsakanin su ukkun, parlourn ya yi kaca kaca.

Cikin tafasar jini Commander Zafar ya ƙariso cikin parlourn, ransa idan ya yi dubu to ya ɓaci, nan take idanunsa suka kaɗa suka yi jajir, wannan ai rai'nin hankali ne ma, ace a samu wasu su iya keta duk wasu zaratar warriors da suke cikin KINGDOM OF POWER su sami damar shigowa wajen ƴar gida kuma har su yi ƙoƙarin yi mata fyaɗe? Lallai ma waɗan nan hukuncin da za'ayi masu karema ba zai shinshina ba, a gaskiya ran commander ya yi muguwar ɓaci, dan ganin rai'nin wayo ma ya yi wa abin.

Yana isowa kansu da hannu ɗaya ya sa ya damko wuyar abokin Yusuf da yake ƙoƙarin janye Yusuf ɗin daga kanta. Cikin ɓacin rai Commander ya sanya kafa ɗaya ya take wuyar Yusuf ɗin, sai ga shi ya zube ƙasa wanwar, jinin Commander sai kara tafasa take yi, jikinsa har wani tsuma yake yi, kafarsa dake sanye da waɗan nan shegun takalmar yakin nasu masu kama da takalmar karfe yasa ya take wuyar Yusuf ɗin a kasan, shi kuma abokin nasa ya shakesa da hannu ɗaya. Maza kake ji, ai ba sai an gaya maku waye commander ba, dattijon kirki mai zafin nama haɗe da tafasashiyar jini da ya shafe sama da shekaru 20 yana bawa zaratan mayaƙa daban daban horo, namijin gaske jarumin jarumai kuke ji!.

A guje Gimbiya Sarina ta samu ta miƙe tsaye zata nufi waje, ƴar kaniya idanu sun rena fata, ta yi wani narai narai, duk ta yi laushi.

Bata kai ga fita cikin parlourn ba zaratan horarrun mayaka masu jini a jika da lafiya har guda goma ne suka shigo cikin parlourn, kowannensu ka gansa sai hantar cikinka ta kaÉ—a, a haka ma fa fuskokinsu na'a cikin hular kayan yakinsu, ba'a ganin ainahin fusatatciyar face É—insu, amma yadda kasan wasu mutuwa idan sun doso waje haka ake tsoronsu, saboda cikar halittarsu ga kwarjinin masifa mai razanarwa, sun sha horo wajen commander ai, dole su zama kamar wasu bujuman zakuna.

Daga King har uncle Abbas sai da suka baro fada domin su zo su ga abin da yake faruwa, a tare suka zo da waÉ—an nan jiga jigan zataran warriors É—in, hakan yasa Sarina tana ganinsu ta tafi wajensu da gudun gaske tana kuka hawaye bibbiyu.

Daga King har uncle Abbas rige rigen tarbanta suka yi. Jikin King ta faɗa tare da kara sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, daga jin yadda take wannan kuka zaka fahimci da iya gaskiyar take kukan, ba wai na munafurci bane, ba'a taɓa yin yunƙurin yi mata fyaɗe ba a rayuwarta sai yau, abin ya yi mugun tsoratata ba kaɗan ba, haƙiƙa kuma ita bata san me su twin's suka shirya ba, dama ba gaya mata suke yi ba, shirya shirinsu kawai suke yi, sai dai ta gani a aikace, sau da dama idan zasu kori samarinta bata sanin plan ɗinsu, idan ta gaya masu bata son saurayin shikenan sai ta rabu da su su yi nasu shirin, hakan yasa bata yi excepting Yusuf zai yi ƙoƙarin yi mata fyaɗe ba, ƴar kaniya yau idanu sun rena fata, taga mutuwa kusa, ai badan kuyangun nan nata da take renawa ba da ta yabawa aya zaƙinta.

Kafin su King su yi wa Zafar magana ma har Yusuf da abokinsa sun sume a hannunsa, shakar da ya yi wa abokin Yusuf ɗin ne yasa ya sume, shi kuma Yusuf taka mashi wuya da ya yi ne yasa shi ma ya sume, dan basu samu numfashin da zasu shaƙa ba, dole su suna, Allah Sarki abokin Yusuf da shi kwatarta ma ya je yi, wannan shi ne ya taka sahun ɓarawo, a wannan hali da ake ciki kuwa mai kwatarsu sai Allah, ko ubansu ne shugaban kasa yadda aka kamasu da hujjarnan wlh basu isa a barsu haka kawai ba, tab King Zuhair fa, lallai za'ayi yaki kuwa ba kaɗan ba, su Yusuf sai dai mu ce Allah ya kwaceku, dan sai dai ayi yakin duniya amma King ba zai barsu ba, koma ƴan uban waye!.

Uncle Abbas ne ya ce da Commander Zafar ya barsu haka nan, a kwashesu a zubasu a prison na masarautar zuwa anjuma idan komai ya lafa sai asan abin yi.

Cikin ɓacin rai King ya ce ina babu wannan magana ta a kai su prison, yanzu zasu karɓi hukunci, kun san halin King bashi barin ko ta kwana, jinin Modarawa ai basu da hakuri malam, su sha yanzu magani yanzu ne, ba ɗaga kafa, dama ga King da tafasasshen jini ai su Yusuf sai ta Allah kawai.

"Yaya please ka bari tukun nan zuwa anjuma mu nutsu sai a yanke masu hukuncin da ta dace da su".
Cewar uncle Abbas.

Cikin nuna isa da izza rai a matuƙar ɓace King ya ce. "Malam liman ka karanto masu doka irinta addinin musulunci a kan wanda ya yi yunƙurin yi wa yarinya fyaɗe a cikin gidan iyayenta, Commander ka zartar masu da wannan hukunci ba tare da ɓata lokaci ba, Abbas na gama magana bana son sake jin wani abin kuma!".
Yana kai karshen maganar ya juya rungume da Sarina dake ta faman kuka a jikinsa, ta tsorata sosai, kuka take yi ba kakkautawa, yadda take kukan nan sai ta baka tausayi Æ´ar kaniya.

Kai tsaye part É—insa King ya wuce da ita dan ya rarrasheta.

Tashin hankali, ga shi dai su Yusuf sun suma bare a iya fahimtar ko wani abin Yusuf ɗin ya sha, kuma kunsan idan ya farfaɗo a yanzu dai koma me ya sha zata sake shi, da bai suma bane to ko King zai iya fahimtar ba lafiya yake ba, amma yanzu babu wanda zai fahimci hakan, bugu da ƙari ga abokinsa da ake ganin cewa a tare suka yi ƙoƙarin yi mata fyaɗen, kunga kuwa hakan ma hujja ce da zata kara sanyawa ayi masu hukunci ba tare da anyi tunanin ko dai ba lafiya yake ba, a gaskiya dai Yusuf bashi da hanyar da zai wanke kansa a cikin wannan al'amari, sannan bugu da kari duk abin da ya ci a wannan waje tare da Sarina da abokin nasa suka ci, to shi ta yaya wannan abin ya faru da shi shi kaɗai? Da alama kuma dole wani abin aka bashi ya ci or ya sha, dan farkon shigowarsa ai ba haka yake ba, to idan wani abin aka bashi ta yaya aka yi hakan kenan? Ko dai dama ya zo da ɓoyayyar manufa ce? Anya kuwa hakan zata faru? KINGDOM OF POWER fa, masarautar da jin sunanta ma kawai yake sanya hantar manya ta kaɗa bare kananan kwarin irin su Yusuf ne zasu yi tunanin shiga har su yi ƙoƙarin yiwa ɗaya daga cikin gimbiyoyi masarautar fyaɗe? Masarautar da mayakanta suke tamkar ajali. Akwai cakwakiya gaskiya, ni dai bari na koma gidansu Khadija mu ga wani hali ake ciki, wata kila kafin mu dawo wasu abubuwa zasu ɗan yi sauki ta nan, amma dai a gaskiya twin's shegun kaya ne na bugawa a jarida, dan ni su nake zargi, suna shirya plan ne ta yadda duk bala'in nacinka ba zaka taɓa gane cewa su suka shirya shi ba, they're very very smart, suna da shape barin. Amma kuma anya zasu iya shirya wannan babban al'amari har haka kuwa?

(Allah yasa akwai Camera a cikin parlourn 😅 dan a wanke abokin Yusuf 😌 amma ko akwai Camera shi dai Yusuf ba zai wanku ba gaskiya, dan ya riga da ya zurma, su twin's ma ko akwai camera ba zasu kamu ba, dan ai basu a waje kuma basu leƙo ba, ita ma Sarina ba zata kamu ba, dan ta nunawa Yusuf so da kulawa, babu wanda zai yi tunanin bata son shi dan haka zata iya yi mashi sharri, ta nuna so a fili, dan haka ta wanke kanta, gaskiya idan ka shiga hannun Team ɗinsu twins kagama yawo wlh💔)

🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️

GIDANSU KHADIJAH💔😥

Izuwa yanzu komai ya kara lalacewa maman Zainab, karin auren baban Zainab babu fashi, haka zalika auren Haidar da Khadija babu fashi, damuwa sun taru sun yi mata yawa, tsananin damuwa yasa ta manta da Allah take tunanin bata da mafita da ya wuce ta bi shawarar Aunty Hauwa, a haukarta gani take yi shi ne kawai the only way da ya rage mata domin tsira, ga shi kuma kamar daɗa hura wutar gaba a tsakaninta da sirikan nata ake yi, duniya ta yi mata zafi, ta manta da cewa duk wani mumuni baya rabuwa da jarabawa ta Ubangiji, idan kaga Allah bai jarrabeka da wata musifa bama to wlh ka binciki imaninka akwai tankarɗa, duk wanda Allah yake so da rahma to yakan zarabce shi, dan haka kada kuga kun shiga wata jarabawa ku yi tunanin ko Allah baya son ku ne, ko kuma ma ku manta da Allah ku fara tunanin wani kato, Allah yana jarraba bayinsa ne domin yaga shin a kowani hali suna tare da shi ne ko kuma dai yaya? To dan haka shawara shi ne kuyi kokari ko a wani hali kuka tsinci kanku ku kasance a tare da Ubangiji, kada ku taɓa yarda ku yi tunanin wasu.

Ba tare da ta yi tunanin me zai je ya zo ba, bata yi tunanin ta gayawa mahaifiyarta halin da ake ciki ba, kawai ta kira Aunty Hauwa a waya a kan ta zo su je wajen malamin nan, dan gaskiya ta rasa mafita, zuciyarta na gab da tarwatsewa, gidan farinciki yanzu yana shirin zama gidan ƙunci koma ace ya zama.

Baban Zainab yana ta ƙoƙarin yaga ya lallaɓa mamarsa ta janye daga maganar karin aurensa, amma ta tirje a kan lallai sai ya kara, ya ce mata in dai matsalar rashin haihuwar Maman Zainab ne damuwarsu da har yasa suka ce ya kara aure, to su yi hakuri In Sha Allah nan bada jimawa ba zata samu ciki ta haihu komai ya wuce a dawo kamar da. Ina ai wannan tsohuwa taki yarda, ta ce ita yanzu bata damu ba ko maman Zainab zata haifo yara ɗari ne wlh sai ya kara aure gara ma ya ji da kyau, ta faɗa da babban murya kuma umarnin take bashi ba shawara ba.

Bashi da zaɓin da ya wuce ya amsa da to, amma yana cikin wani hali, duk ta in da ya juya babu daɗi, ga maman Zainab ta rike mashi wuta a gida, bata kula shi, za dai ta yi mashi duk abin da ya dace ta yi mashi, zata sauke nauyin da yake a kanta, amma ko sannu bata ce mashi idan ya dawo, bata yi mashi magana, wasan ɓuya ma take yi da shi, idan ta ji ya dawo zata shiga ɗaki ta rufe kofarta, ba zata fito ba kuma har sai ta ji ya fita, ya yi magiyar duniyar nan taki sauraronsa, yadda kuka san shi ya yi mata laifi, bawan Allah bata san shi ma yana tsaka mai wuya ba.

A ɓangaren Haidar kuwa, sai shirye shiryen biki yake yi abinsa, duk ya sanar da mahaukan abokansa irinsa marasa kan gado, tsabar mugunta irin na Mammarsa ma har da wani cewa ai ba sai ya yi wa Khadijah ɗin kayan lefe ba, ai kanwarsa ce, kuma koba komai ya bautawa babanta a kasuwa, dan haka babanta ne ma yakamata ya yi komai na bikin, domin tun Haidar yana ƙarami yana wahala a shagonsa, dan haka lokacin da yakamata abiyasa ya yi, tsabar rashin imani irin na maman Haidar ɗin, yadda kuka san ba uwa ɗaya take da baban Zainab ɗin ba, yanzu so take baban Zainab ɗin ya yi wa Khadijah kayan ɗaki kuma ya dawo ya haɗawa Haidar lefen da zai kawowa Khadija, sannan ga nashi karin aure, bugu da kari ga shi hajiyarsa ta ce a sabon gidansu za'a kai amarya, dan haka dole ya ƙarisa gininsa cikin sauri, Allah ma yasa abu kaɗan ne ya rage a kammala ginin, amma duk da haka akwai cin kuɗi, duk basu ga hakan ba su kam, dan rashin adalci irin nasu.

A yau ne Maman Zainab da Aunty Hauwa suka shirya zuwa wajen malamin Aunty Hauwa, zasu je ne kuma da nufi ya yi masu aiki guda uku, na farko hana karin auren baban Zainab, na biyu hana auren Haidar da Khadija, na uku a saka dangin baban Zainab su sota sosai sosai kamar su haÉ—iyeta, wannan shi ne aikin da za'ayi masu.

Yau dai Maman Zainab ta ɗan saki fuska kaɗan, dan tana ganin kamar da sun je wajen malamin komai zai zama daidai cikin lokaci ƙaƙani kamar yadda Aunty Hauwa take ta faɗa mata, hakan yasa ta ɗan saki fuska yau.

Su Khadijah dai izuwa yanzu sun gama fahimtar komai da yake faruwa a cikin gidan nasu, da yake sun sami tarbiya mai kyan gaske, sai suka fawwalawa Allah komai nasu, suka dukufa babu dare babu rana wajen yin addu'a, kuma kawunsu Sadiq kullum idan suka kai mashi kukan halin da suke ciki yana kwantar masu da hankali tare da kara masu kwarin gwiwa a kan su miƙawa Allah al'amuransu komai zai warware.

Hakan yasa suke samun sassauci a kan halin da suke a ciki ɗin, Sadiq bawan Allah ne, ya yi ƙoƙarin nusar da Maman Zainab da ta yi hakuri ta fawwalawa Allah komai zai yi mata sakayya a lokacin da bata zata ba, amma ina kishi da takaici ya rufe mata idanu, bata ji bata gani, har saɓani suka samu da Sadiq ɗin a kan maganar, ba dan Sadiq yana da hankali ba kuma yana taimakawa baban Zainab ba da ya bar mata gidanta, dan ba ƙaramin zaginsa ta yi a kan case ɗin ba, ta ce babu ruwansa da ita, amma ya hakura saboda yana taimakawa baban Zainab, kuma ko ba komai baban Zainab ya yi mashi abin da ba zai taɓa mantawa da shi ba, shi ya ɗauki nauyin karatunsa tun daga nursery har izuwa master da yake yanzu, so koda baban Zainab ya saki maman Zainab shi gaskiya ba zai iya juyawa baban Zainab baya ba, ya yi mashi abin da babu wanda ya yi mashi shi a duniya, domin ilimi shi ne mutun, ya tsaya mashi ya yi karatu kuma boko da islamiya dukka, hakan yasa ya hakura ya cigaba da zama a gidan.

Misalin karfe 9 na safe bayansu Khadija sun tafi school, baban Zainab ya fita kasuwa, Sadiq duk basu nan suna kasuwa, sai ga Aunty Hauwa ta zo domin su je wajen wannan malami na kan dutse da ta faÉ—a.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

https://chat.whatsapp.com/LAEmIGs3z0KBdL3NQsRixW

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 29/7/2024.....✍️📚🌹

For information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________23🔥

Misalin karfe 9 na safe bayansu Khadija sun tafi school, baban Zainab ya fita kasuwa, Sadiq duk basu nan suna kasuwa, sai ga Aunty Hauwa ta zo domin su je wajen wannan malami na kan dutse da ta faÉ—a.

Maman Zainab bata gaya wa baban Zainab zata fita ba, kawai ta biyewa Aunty Hauwa ta saɓi mayafi suka fita. Ya Allah ka rabamu da makiran kawaye munafukai, rimi rimi zaka yi wa ƴarka tarbiya na tsawon lokaci, amma wata shegiya cikin ƙanƙanin lokaci zata zugata ta juyar mata da tunani, sai wadda Allah ya tsare ne kawai bata afkawa zugin ƙawaye, to a koma ina Allah ka haɗamu da mutane na Allah masu gaskiya da sommu da gaskiya!.

Haka dai suka kama hanyarsu suka tafi, sai kara zugata Aunty Hauwa take yi, abin ku da shaiɗan, sai buga mata gangan yake yi abinsa, tana ganin kamar suna zuwa shikenan matsalarta ta warware, ta manta da cewa idan Allah bai kaddara abuba to wlh idan duniya dukka gatanka ne, in zasu taru duk duniya su baka wannan abu karɓama ba zaka iya yinsa ba, saboda Allah bai rubuto maka a kaddararka ba, amma ita ina idanunta sun rufe, kishi ga kuma takaicin da Maman Haidar take kunsa mata nan, ga takaicin auren Khadija da Haidar duk sai ya haɗu ya rufe mata idanu ruf, bata ji kuma bata gani!. Allah dai ya kyauta.

To kafin su dawo daga wajen bokan nasu bari mu fara ƙutsawa cikin ainahin labarinmu, bari mu taɓo wani ɓangare kaɗan mu gani, dan ina son mu nemo in da RAWANIN ZALINCI yake, saboda har yanzu fa bamu ko alamun samo shi ba! A gefe gefe muke!.

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

Bari mu leƙa UAE wato United Arab Emirates, a cikin UAE ma bari mu leƙa Dubai, a cikin Dubai ma bari mu leƙa prison na Al Aweer Juvenile AAJ, wato prison na yara under 18 years kenan.

AAJ Prison ne kamar yadda kuka san kowani prison na yara waɗan da suka aikata laifi kuma ba su kai shekarun da za'a yanke masu hukunci ba, so ana ajiye su a AAJ ɗin zuwa su kai munzalin karɓar hukunci, ba kamar prison na manya yake ba, nasu yafi na manya kyau, tsaro, kula da lafiyarsu, lafiyayyen abinci, ɗakin kwana mai kyau, masu kula da lafiyarsu suna ƙoƙari sosai, da dai sauransu, ana basu kula sosai ba kamar manya ba, domin kunga su yara ne, wasu ma kaddara ce take afka masu su yi laifi ba'a son ransu ba, amma kowa yasan da cewa dokar kasar Dubai tana da tsauri sosai, musamman ma da ya kasance a yanzu jinin modarawa wato su Akka su ne suke rike da ƙasar, shi ne yasa dokar ta kara sauri over, dan kowa yasan jininsu basu da wasa kuma basa ɗaukar wasa, bugu da ƙari komai da zasu yi dai'dai da faɗar Allah suke yi! A ko'ina da akwai ɓata gari, akwai kuma na kirki, idan suka yanke hukunci fa to ba lallai ne su sake sauraran wani excuse ɗin ba kuma, sai dai idan ta ƙarƙashin kasa za'a bi kamar dai yadda aka saba idan wani ɗan masu hali ya yi wani abin, fatan kun gane?.

ÆŠaki ne na yara mai kyau, gadaje irin na sama da kasan nan har gado shidda ne a É—akin, sama da kasa sama da kasa guda uku kenan shi ne zai kama gado shidda, mattress da suke a saman kadajen mattress ne masu kyau ga kuma laushi, harta bedsheet É—insu ma mai kyau ne, tiles mai kyau da tsada ne a kasar floor É—in É—akin, suna da Ac kamar ba prison ba, ga bargon da suke rufuwa a lokacin da sanyi ya sauko masu ma mai kyau sosai da shi, pillows É—insu duk masu kyau ne, dama na gaya maku su ana kula da su sosai fiye da manya, wajen cin abincinsu a cikin prison É—in, in da kowa yake fitowa su haÉ—u su ci abinci ma an kawata shi da dinings tables daban daban sama da guda ashirin, kuma tables ne masu girma wanda kowanne yana da 24 to 32 chairs, da yake katafaren prison ne hakan yasa aka zuba tables É—in dayawa a wajen cin abincinsu.

Sai hada hada yara suke yi, suna ta kai komo kamar gida, wasu suna buga kwallo a filin ball da yake a cikin prison É—in, dan harda fillin ball ne da su. Part na maza daban na mata ma daban, kun san dama ba'a haÉ—asu waje guda!.

Ƴan matasan ƴan'mata da ba za su wuci 13 to 15 years bane su huɗu a cikin wannan ɗakin, da alama ƴan mata biyun cikon gadaje shiddan nan sun fita waje wasa, abinku da yara.

Waɗan nan ƴan'matan uku daga cikinsu sai kai komo suke yi tsakanin toilet da wajen gadajensu, kowacce da abin da take yi, ɗaya tana sanya da blue AAJ uniform a jikinta, ɗaya kuma tana ƙoƙarin shinfiɗa bed ɗinta, ɗayar kuma tana ƙoƙarin naɗe bargonta, da alama yanzu suka tashi daga barci, su dai babu takura babu komai, kawai za'a tsaresu ne sai sun girma sun kai munzali su girbi abin da suka shuka. Dukka waɗan nan ƴan'mata uku dake a cikin ɗakin larabawa ne saɓanin ɗaya da take zaune a saman bed ɗinta ta buga uban tagumi, da alama tana cikin mawuyacin hali ne, saboda yadda ta yi wannan uban tagumi ya nuna tana a cikin damuwa sosai, ba balarabiya bace ba, saboda yadda take bakar fata a cikinsu, sai dai kuma ta fisu kyau sosai, kyakkyawar gaske ce na kin ƙarawa, chocolate color ce dangin Africa, kalar fatarta kala ce mai tsada a duniya wanda yanzu samunsa yake wuya, tana da dogon hanci har baka, ga ɗan madaidaicin bakinta da ya yi ɗas a saman ɓul ɓul ɗin kumatunta, idanunta farare tas dara dara, kyakkyawa ce ajin farko, face nata ɗan dai'dai, bata da wani ƙiba, ƴar dai'dai da ita, ba zata wuci 15 years ba a duniya, tana sanye da kayan AAJ ɗin wadda kowasu prisoners suke sanyawa, kanta babu ɗan'kwali, tana da yelwar bakin gashi mai tsawo, gashin nata a nannaɗe yake irin kamar rubber hair ɗin nan, amma gashin nata akwai tsawo da kyau sosai, duk da ya kasance tana zaune ne hakan ba zai sanya ka kasa iya gane cewa dirarriyar mace bace, tana da dirarren jiki mai kyau wadda kamar ita ta yi wa kanta, coca cola shape ne da ita sosai, kirjin nan nata a cike suke fam kamar ba ƴar 15 years ba, kamar mai 18 years haka, ta buga uban tagumi kamar wadda aka saukowa da wahayin yinsa, her face looks she's so silent, innocent face ke gareta.

Wata yarinya wadda a kallah zata iya kai 17 years ce ta shigo cikin room É—in, fara ce tas balarabiya, kyakkyawa ce sosai, amma bata kai wannan chocolate color É—in yarinyar kyau ba, ita ma kanta babu É—an'kwali, ta É—aure gashin kanta two step, ta saki jelar gashin nata É—aya ta bayanta, É—aya kuma ta saman shoulder É—inta ya yo gaba, kyakkyawa ce sosai ita ma, ga dara dara idanu farare tas, tana da sura mai kyan gaske.

A kusa da wannan chocolate color yarinya ta zo ta zauna a saman bed ɗinta kenan. Cikin harshen larabci mai nuna cewa kwararriya ce a iya larabci ta ce "أنت لم تأخذ حماما Leesharh? (Leesharh bakiyi wanka ba)?"
Ta yi maganar tana taɓa shoulder ɗin Leesharh ɗin.

Ƴar firgita ta ɗan yi alamar ta ɗan razana, dan ta afka duniyar tunani ne bata ji shigowar yarinyar ba, shi ne yasa da ta taɓata ta firgita.

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ɗan sunkuyar da kanta ƙasa, cikin muryarta da kwata kwata baya fita, tamkar wata bebiya ko mai koyar yin magana, idan ba su da suka saba da ita ba wani daga waje ba zai iya gane me take faɗa ba, sam muryar tata bata fita kamar irin wadda mura ta shaken sosai ɗin nan, ga in'ina a cikin maganarta abin gwanin ban tausayi.

"اليوم أتذكر والدتي، ولهذا السبب مات جسدي كله، ولم أستطع الاستحمام
(Yau na tuna mahaifiyata, shiyasa duk jikina ya mutu, kuma na kasa yin wanka Jasrah)"
Ta bata amsa cikin harshen larabci ita ma.

ÆŠaya daga cikin yaran nan ne da suke a cikin É—akin before shigowar Jasrah wadda take shinfiÉ—a bed É—inta É—azun ta ce. "To ba kin kashe mahaifiyar taki ba? Menene kuma abin wani sake yin tunata?".
Ita ma cikin harshen larabci ta yi maganar, da alamu larabci kawai suke ji wata kila da turanci!.

"Aaradiya wai meyasa kuke yin haka ne?".
Cewar Jasrah dake dafe da shoulder É—in Leesharh.

Wani kallon banza wadda aka kira da Aaradiyar ta wurga masu daga Leesharh har Jasrar, sannan ta sa kai ta fice waje abinta ba tare da ta sake yin magana ba, dan ta gama gyaran gadon nata dama.

"Leesharh ki yi hakuri, ki je ki yi wanka ki zo mu je mu ci abinci".
Cewar Jasrah.

Leesharh kenan wadda rahotonta yake a rubuce cewa ta kashe mahaifiyarta da hannunta a cikin kitchen suna tsaka da yin aikin girki ta caka mata wuƙa a ciki, nasan dai dukkanku zaku sha mamakin yadda aka yi yarinya kyakkyawa karama kamar wannan ta kashe mahaifiyarta har a kawota prison ɗin yara, na san za ku so jin ainahin labarinta da yadda aka yi ta kashe mahaifiyarta da kuma yadda aka yi ta zo gidan AAJ, meyasa zata kashe mahaifiyarta? Uwa fa? Hmmmmm mu je dai zuwa.

"Jasrah bana jin zan iya cin komai yau, ki je ki ci abincinki, ni ki barni kawai".
Ta yi maganar idanuwanta suna kawo ruwa, alamar dai da gaske yau bata cikin yanayi mai daÉ—i, ko dai tana nadama ko makamancin hakan.

"Amma Leesharh yau tsawon shekara guda kenan tun shigowarki gidan AAJ kullun ina baki shawara da ki cire wannan tunanin a cikin zuciyarki, ki hakura ki rungumi kaddararki, ki manta da kowa da komai ki sake ki yi rayuwa kamar mu, ni dai kina gani na barwa Allah komai, Allah ya sani ni ba da gangan na kashe Ameer ba, amma saboda bani da hujja kuma iyayena basu da karfi kinga an kawoni nan wajen an tsare, kuma ni na hakura na rungumi kaddarata, a kullum ina tunanin iyayena sosai, amma bana bari hakan ya hanani farincikina, nasan akwai ranar sakayya, kullum da tunanin ƙanwata Alveena nake kwana nake tashi, amma ya zan yi to? An rigada an rabamu, sai idan Allah ya ƙaddara muna da rabon haɗuwa a gaba, idan kuma lokacin yanke mana hukunci ya cika ba'a gane gaskiya ba aka kashemu shikenan akwai lahira ai, akwai ranar da babu wanda ya isa ya yi karya ko ya cuci wani, rana ce ta kwatarwa waɗan da aka cuta hakkinsu ba tare da zalinci ko son kai ba!".
Ta kai karshen maganar tana goge hawayen da suka fara zuba mata a saman fuskarta, gwanin ban tausayi.

Zuba mata idanu kawai Leesharh ta yi tana kallon yadda take sharar kwallah, hawaye wani na bin wani kamar famfo, abin tausayi, wlh ba da gangan ta kashe shi ba, saboda wani saɓani da aka samu ne, kaddara ce ta faɗo mata kawai, dan iyayenta talakawa ne kuma yasa ba'ayi wani shari'a sosai ba, yanzu shekarunta uku a cikin wannan prison ɗin, tun tana da 14 years aka kawota, yanzu kuma tana da 17 years, saura mata shekara ɗaya ta cika 18 years a duniya shikenan sai a yanke mata hukunci wadda dani da ku dukka munsan dai wanda ya yi kisan kai hukuncin kisa shi ma ake yanke mashi, wannan ita ce dokar kasar Dubai, a kanta kuma suke tafiya, doka ce ta addinin Musulunci, duk wanda ya kashe rai shi ma a kashe shi! Dan rai bata fi rai ba!.

Ainahin Jasrah iyayenta larabawan ƙasar Turkey ne, zama ne ya kawosu kasar Dubai, wahalar rayuwa yasa suka baro Turkey suka zo nan Dubai neman abin da za su rufawa kansu asiri, kasancewar Jasrah ita ce babba sai take zuwa gidajen masu kuɗi tana yi masu aiki suna biyanta, a lokacin ma kwata kwata bata wuci 14 years ba, tana dai yi masu ɗan aikin da karfinta zai iya, to ita yarinya ce mai hakuri sosai, ga sanyin hali da tausayi, kanwarta ɗaya Alveena, su biyu iyayensu suka haifa, basu zuwa makarantar boko saboda halin rashi da mahaifinsu yake fama da shi, amma suna karatun islamiya sosai a wajen iyayen nasu, da yake mahaifinsu babban malami ne, akwai ilimin addini, so sun sami ilimin addini sosai.

A haka dai kullun tana zuwa wani babban gida na masu kuÉ—i da yake a unguwar tasu tana aiki, matar gidan sam bata kaunar Jasrah É—in, amma mijinta kuma yana son yarinyar, saboda shiga ranta, tana da hankali sosai, suna da yara maza biyu da mace É—aya, mazan manya ne, babban zai kai 20 years, sai mai bi mashi Ameer wadda aka ce ta kashe kenan, shi kuma yana da 17 years kamar dai ita a yanzu, macen kuma tana da shekaru 7, kullum idan ta je ta yi masu aikin goge gogen ma idan babansu baya gida basu bata komai, dan maman bata kaunarta, amma idan baban yana nan zai bata abinci dayawa ta tafi da shi gida su ci da iyayenta da kanwarta Alveena, zai kuma bata kuÉ—i.

Wata rana idan baban ma baya nan korinta mamar take yi idan ta je yin wannan aiki, amma da yake tana samun abincin da suke ci da iyayenta da kanwarta, tana kuma samun kuɗi wajen baban sai yasa bata gajiya da zuwa gidan duk walaƙancin da suke yi mata, tana hakura ta je, damo ce sarkin hakuri.

A haka suke rayuwa a takaice kwance tashi watarana suka sami saɓani da wannan Ameer ɗin, ya so ya lalata mata rayuwa ne taki yarda, duk da tana karama amma ta samu ilimin addini daga iyayenta, ta san illar yin hakan, shi kuwa a lokacin ya doshi 18 years yana ji da tashen balaga, kansa na rawa sosai yaron, ya fi yayansa ma bushewar idanu, da alama kuma yana yawan kallon fina finan batsa, hakan yasa ya yi ƙoƙarin lalata mata rayuwa.

Da taki yarda ne ya É—auki karan tsana ya É—aura mata, kullum idan ta zo tana aikin goge gogenta in dai zai gifta ta kusa da ita sai ya kai mata mari a mazaunanta, kamar shi ya halitta mata su, tun tana kuka har ta saba.

Wata rana ta ce ba zata sake zuwa gidan ba, dan ta gaji da azabtar da ita da Ameer ɗin yake yi, ga shegen sakata aiki da yake yi, ya yi ta dukanta kuma, wani lokaci a gaban mamarsa yake dukan nata, amma uwar bata cewa komai saboda zalinci, sai dai ta kawar da kai, dama na gaya maku uwar bata da hali mai kyau. Sai dai ko da ta ce ba zata sake zuwa gidan ba tana hakura ta sake zuwa, saboda abincin da take samo masu su ci da iyayenta, mahaifinsu ya manyanta sosai, baya iya yin aikin karfi, amma yana iyaka bakin ƙoƙarinsa!.

Wata rana mamarsa tana ƙasa ita kuma Jasrah tana sama tana goge goge, sai ya ce ta je ɗakinsa ta gyara mashi, kamar zata ce ba zata je ba, amma saboda tsoron mamar tasa yasa ta je ta fara gyara masa. A nan ya iskota tana faman gyara mashi bed ɗinsa, ai kuwa yana zuwa ya turata saman bed ɗin tare da ƙoƙarin yi mata fyaɗe ta karfin tsiya, tana ƙoƙarin yin ihu ne ya yi saurin toshe mata baki da hannunsa. Hakan yasa ta fara ƙoƙarin kwatar kanta ta karfin tsiya a in da suka fara kokawa, ya sanya karfi zai yi mata fyaɗe ita kuma ta sanya karfi zata kwaci kanta.

Da yake mummunar kaddara ta gifta a tsakani sai ta sanya hannu tana laluɓar abin da zata buga mashi, cikin ikon Allah ta ɗauko kwalbar mardbe da ya yi amfani da shi ya barshi a saman bedside drawer ba'a fitar ba, ai kuwa yana danne da ita yana ƙoƙarin cire mata riga, bata yi wata wata ba ta buga mashi kwalbar a kansa, hakan yasa ya tashi daga kanta a haukace, saboda azaban zafi da ta ziyarce shi.

Abinku da yarinta, zuciyar kuruciya tana ɗebansa, cikin fusata ya kwace kwalbar daga hannunta tare da fasata a ƙasa, tana ƙoƙarin guduwa ta fita daga cikin ɗakin ya rikota da nufin ya kasheta da kwalbar, dan yana ɗaukarta a ƙasƙantacciyar ƴar aiki mara galihu, koma me ai baiwarsu ce ita ɗin, ko ya kwasheta ya kashe banza a banza.

Wage baki ta yi a in da ta zunduma ihu da karfi, a zuciye ya kai mata duka a bakin nata da ta yi ihun, ba shi ta haɗiye ihun da take ƙoƙarin kurmawa a karo na biyu, gadan gadan ya yi niyar kasheta, sai dai cikin ikon Allah ta samu ta ɗauko ɗaya daga cikin kwalaben da suka yi saura a kasan wanda ya fasa, a ƙoƙarin ta yi mashi barazanar kada ya kara matsowa kusa da ita, sai kuma mummunar kaddara ta gifta ta caka mashi wannan kwalbar a cikinsa, wannan ita ce sanadiyyar mutuwarsa kenan.

Wannan ihu da ta yi na farko yayansa ya ji ihun nata, hakan yasa ya nufo ɗakin, ya shigo kuma dai'dai lokacin da ta caki Ameer ɗin da kwalbar har ya faɗi a saman bed ɗinsa da yake yana a kusa da bed ɗin dama, hakan yasa yayan ma ya kurma ihu mai sauti wanda ya ja hankali kowa da yake gidan. A guje suka nufo ɗakin, kafin ma ayi wani yunƙuri Ameer dai ya ce ga garinku, rai ta yi halinta, wannan shi ne abin da ya faru, ko da aka kira jami'ai sai cewa mamansa ta yi ai daba Jasrah bata kaunar Ameer, kuma ta taɓa cewa sai ta kasheshi a baya lokacin da ya mareta, to shi ne yanzu ta bishi har cikin ɗakinsa yana kwance ta kashe shi.

Da jami'an suka tambayi cewa ina shaidar maman na cewa Jasrah ta taɓa yin ikirarin zata kashe Ameer, sai ta gabatar da shaida na farko yayan Ameer ɗin, da kuma sauran ƴan aikinta wanda dan dole suka amsa da anyi hakan, dan kawai basu da zaɓi da ya wuce hakan in dai suna son cigaba da rayuwa su kuma cigaba da yin aiki, haka suka bi bayan karya suka rufawa Ameer asiri na cewa shi yake neman lalata Jasrah, suka ɓoye wannan magana, kuma kowa na gidan yasan da cewa tabbas Ameer shi yake neman Jasrah da faɗa, saboda wani lokaci idan tana tsaka da yin aiki tare da sauran ma'aikatan gidan ya zo wucewa zai kai mata mari a mazaunanta a gaban kowa, kuma ya wuce ya mari banza, so sun san komai, amma basu da zaɓin da ya wuce su amsa maganar maman Ameer ɗin a matsayin gaskiya.

Wasu matan wlh munafukai ne na karshe, Maman Ameer dai da kanta ta goge ɗaukar CCTV camerar da yake parlourn wanda ya ɗauki video Ameer ɗin lokacin da yake cewa Jasrah ta je ta gyara mashi ɗaki, sai ta goge wannan ɗauka dan ta kara tabbatar wa da jami'ai cewa tabbas haka kawai Jasrah ta shiga ɗakin Ameer ta kashe shi saboda ƴar tsama da ta taɓa shiga tsakaninsu har ya mareta, ko da aka tambayeta wace tsama ce, sai ta ce ai Jasrah ɗin ce ta zubawa Ameer ɗin tea mai zafi a jiki bisa rashin sani, shi ne shi kuma ya fusata ya mareta, shikenan ta ce ba zata barshi ba. Haka dai suka shirya karya da gaskiya tare da shirya hujjojin da dole sai ka yarda da maganar tasu, wannan dalilin yasa aka kai Jasrah kotu ba tare da ɓata lokaci ba aka yanke mata hukunci kisa daga nan sai gidan AAJ za'a tsareta zuwa lokacin da zata kai munzalin karɓar hukunci kisa kamar yadda ta kashe Ameer ɗin.

Iyayenta sun yi kuka ne har mahaifinta ya kwanta jinya na tsawon lokaci, haka kanwarta Alveena, mahaifiyarsu har yau bata dai'na kuka ba, suna zuwa AAJ É—in ziyartar Jasrah É—in, amma ba koda yaushe ba, saboda basu son zuwa su ganta a cikin wani hali, idan suka koma gida a ranar da suka ziyarceta kwana suke yi basu yi barci ba bayin Allah. WANNAN SHI NE LABARIN SUHANA DA KUMA DALILIN ZUWANTA AAJ, BA SAI NA TSAYA YIN DOGON BAYANI BA NASAN KUN FAHIMCI IN DA AKA DOSA!.

Mu koma kan labarinmu.❤️‍🔥

"Shikenan Leesharh, bari na je lokacin cin abincin yana kurewa, kuma kin san komai yana da lokacinsa a cikin gidan nan, dan haka bari na je na ci nawa kada time ya kure banci ba a hanani". Cewar Jasrah. Ta kai karshen maganar tana miƙewa tsaye.

Da idanu kawai Leesharh ta bita har ta fice daga cikin ɗakin, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da sanya hannayenta dukka biyu ta dafe ƙuncinta, duniyar tunani ta afka, yau gabaɗaya tana cikin damuwa sosai da sosai.

🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️

IDAN MUKA WAIWAYA WAJEN SU KAMRAN KUWA WATO FOREST.🔥🤍

Zaune suke a ƙasar wata ƙatuwar dutse mai girma dake kusa da wannan ƙoramar na kusa da wajen su Pretty, da alama an fasa yin harbi da kifiyar kenan, akwai itatuwan mangori sosai a ta kusa da wajen, hakan yasa suka samu ishasshen ƴalwar inuwa sosai a wajen.

Yana zaune ya jingina da jikin dutsen ya kuma lumshe idanunsa tare da ɗan ɗaga kansa sama kamar mai yin tunanin wani abin, Sweetie na zaune a gefensa na hagu saman farin yashin da yake a wajen. Hannunta na rike da lemun zaki tana ɓarewa duk da bata gani, Kamran ɗin ne ya ciro masu lemun a wata bishiya dake ɗan nesa da ƙoramar. Ita kuwa Pretty sarkin kauɗi tana zaune kusa da shi sosai, ta ɗaura ƴan kyawawan kafafun nan nata a saman nasa ƙafafun tana ɓare nata lemun, idan baku manta ba Kamran ɗin bai fito da wukarsa bane yasa suke ɓare remun da hannu, ba halin yankawa.

Shi dai Kamran ya afka duniyar tunanin abin da yake damunsa tun daga haɗuwarsa da su Pretty, kullum yana yawan mafarkinsu sosai, ga shi a duk lokacin da ya haɗa idanu da waɗan nan sexy eyes ɗin nata sai ya ji gabansa ya faɗi, tana rikita shi, ya rasa me dalili. Haƙiƙa idanunta suna da rikita mai kallonsu, wasu irin shegun sexy eyes ke gareta, amma shi nasa rikitarwar na daban ne, har tsoron kallon cikin idanun nata yake yi, gata da shegen daddaɗar zazzakar murya wanda idan ta yi magana sai ya ratsa jikin duk wani mai sauraro, ko baka son haɗa idanu da ita idan ta yi magana sai ka ji duniya baka da burin da ya wuce ka ɗaga idanu ka kalli face nata, saboda muryar nan tata akwai ratsa zuciya, sannan ga ɗan banzan shiga rai garesu daga ita har Sweetie, bugu da ƙari ga ɗan banzan wayo kamar wasu renon tsofaffi.

"Kamran ga lemun nagama ɓarewa".
Cewar Pretty, ta yi maganar tana kai hannu zata taɓa lallausan kumatunsa.

Ajiyar zuciya ya sauke tare da waro idanunsa a hankali, dai'dai lokacin ta kai É—an kyakkyawan lallausan hannunta saman kumatunsa, a tunaninta barci ya É—an yi shi ne zata tashe shi.

Karaf idanunsa ya sauka cikin nata. Ɗauke hannunta daga saman kumatun nasa ta yi tare da miƙo mashi lemun da yake a ɗayan hannun nata tana mai do da kallonta izuwa saman gashin kansa, duk da yana sanye da hula baka iya ganin gashin kan nasa sosai, amma ya ɗan fito ta gaban goshinsa.

"Kamran kana da gashi sosai kamar mu".
Ta faÉ—a tana mai cigaba da kallon kan nasa.

Nisawa ya yi tare da karɓar lemun. "Waye ya gaya maki gashina kamar naku ne?".

Gyara zamanta ta yi tare da É—auka kafafunta daga saman nasa, ta yi zama irin na masu cin abinci ta lankwashe kafafunta dukka biyu suna fuskantar juna.
"Babu wanda ya gaya mun, kawai na gano yawan gashin naka ne duba da yadda ya cika hular kanka, hakan yana nufin gashin na dayawa sosai".

"Pretty ke dai kin cika sa ido".
Ya bata amsa yana mai raba lamun da ya karɓa daga hannun nata gida biyu. Bayan ya raba biyu sai ya miƙo mata rabi.

Maƙe mashi ɗan kafadarta ta yi alamar bata so tana faɗin.
"Ni bana saka ido, daga magana kawai sai ka ce na iya saka ido? Kuma ni ba zan sha lemun ba".
Ta kai karshen maganar tare da yunƙurawa zata miƙe, ita a dole ta yi fushi tun da ya ce mata mai sa ido.

Cikin hanzari ya kai hannunsa ya riƙo nata hannun yana faɗin.
"To sarkin fushi yi hakuri, am so sorry baki da sa ido shikenan?".

Tana ƙoƙarin sake yin magana Sweetie ta katsesu da cewa.
"Hmmmm ita kam ma ai ta ji daÉ—i tun da tana da idon da zata yi kallo har ace mata tana sa ido, ni kam sai dai na kalli abu da zuciyata".

Wani irin yanayi mara daɗi dukkansu suka ji da jin maganar Sweetien, haƙiƙa maganar ta taɓa zuciyar Kamran sosai, wani irin tausayinta ne ya kamashi, ya sani rashin ido babu daɗi sam, ga shi a yadda ta yi maganar kamar zata yi kuka sai ka ji kalaman nata sun ratsa maka zuciya sosai, sai ka tausaya mata duk taurin zuciyarka, ita ma Pretty da take sarkin kauɗi ta ji kalaman har cikin ranta bare shi Kamran da dama already yake sarkin tausayi mai zuciyar musulman farko, ai dole ya tausaya mata.

"Our Sweetie idanunki zasu buÉ—e nan bada jimawa ba kin ji ko? Kada ki damu kanki, zan nemo maki magani".
Cewar Kamran, ya yi Magana da wata iriyar murya wadda da ka ji ta zaka san lallai maganar tata ta taɓa mashi zuciya.

"Allah yasa ka samu maganin Kamran, ina son idanuna su buÉ—e, ina son na ga ya fuskarka take? Ina son sanin kamanninka, saboda kai kawai nake burin idanuna su buÉ—e".

Har lokacin yana rike da hannun Pretty bai saki ba ya bata amsa da. "Nan ba da jimawa ba our Sweetie, zaki samu lafiya sosai kamar baki taɓa yin ciwo ba".

"In Sha Allah, zan tayata da addu'a sosai nima". Cewar Pretty.

Maido da kallonsa a kanta ya yi yana kallon É—an bakin nata da ta furta In Sha Allah É—in.
"Take your orange".
Ya faɗa yana mai miƙo mata rabin lemun.

Sarkin rigima kara maƙe mashi ɗan kafaɗar tata ta yi tare da girgiza mashi kai. "I don't want, ba ka ce mun sarkin fushi ba? So don't talk to me again".
Tana magana tana turo baki.

"Oh sorry ba zan sake ba ai".
Ya faɗa tare da miƙo mata lemun.

"To sake mun hannu na sai na karɓa".

A hanzarce ya saketa, shi kwata kwata ma ya mance da cewa ya rike mata hannu, ya ji hannu mai laushi luwai luwai.

Karɓar lemun ta yi tare da komawa ta gyara zamanta da kyau, sarkin rigima ce sosai Pretty.

Ta ƙasan idanunsa yake satar kallonta yadda take tsala lemun nata tsala sala, a hankali take kai sala ɗaya ɗan bakinta, idan ta kai ɗin ma ba dukka take turawa a cikin bakin nata ba, sai ta gutsira ta raba biyu, ta rike rabi a hannu ta bar rabi a cikin ɗan bakin nata tana tauna a hankali hankali kamar bata son motsa ɗan bakin, da alama akwai yauki a tattare da ita, tana kara girma kuma hakan yana kara bayyana.

Sosai yake jin daɗin kallon yadda take shan lemun, hakan yasa ya mance da nasa baya sha, saukar zazzaƙar voice ɗinta a dodon kunnuwansa ne yasa ya ɗan firgita tare da dai'dai nutsuwarsa cikin hanzari kamar wani mara gaskiya.

"Kamran muje ka cigaba da koya mun harbin kwari da bakar ko?".
Shi ne abin da ta faÉ—a wanda ya fargar da shi daga satar kallonta da ya lula. Ta yi maganar ita kuma ba tare da ta kalli in da yake ba.

Ƙasa da idanunsa ya yi tare da sanya hannu ya fara sala lemunsa kamar yadda ya ga ta yi, bai taɓa shan lemu irin haka ba, bai ma taɓa ganin an raba lemu a haka ba sai yau da ya gani a wajenta, shi kullum Mammarsa ce take yanka masu da wuƙa sai su ɓare su sha, yau ya ga sabon salo na tsala ta tsala sala.

"Pretty koya maki harbi da kifiya sai na shirya, gara mun na fara koya maki busa tukun nan".
Ya kai karshen maganar tare da kai lemu sala É—aya É—an bakinsa ya tura ciki, a hankali ya fara sha.

"Amma kuma É—azun kai ne fa ka ce harbi da kifiya zaka fara koya mun?".
Ta yi maganar a ɗan shagwaɓe kamar yadda take zubawa Sweetie shagwaɓa, sannan ta yi maganar tana kallon kyakkyawar fuskarsa tana aikin turo ɗan baki.

A hankali ya É—ago idanunsa ya saukesu a saman kyakkyawar fuskarta. "Zan koya maki, amma ba yanzu ba gaskiya, sai na yi magana da mamana na tambayeta wani abin tukun nan, yanzun na ji na kasa ne, ba zan iya ba".
Ya faɗa muryarsa a ɗan kasale, alamar kwata kwata dai baya son ya tuna da zancen koya mata ɗin, dan shi kaɗai yasan me yake ji a duk lokacin da suka haɗa jiki, komai ƙanƙantar haɗuwar fata da tsokan jikin nasu sai ya ji jikinsa ta amsa.

Matsowa kusa da Sweetie ta yi tare da kwantawa a kasa a wajen ta tada kai da laps na Sweetie, dama kun santa sarkin son jiki ce kamar mage.

"Ki tashi a jikin Sweetie kada ki ji mata ciwo sarkin rigima kawai". Cewar Kamran, yana magana yana cigaba da shan lemunsa.

"Sweetie in yi kwanciyata ko?". Ta tambaya tana mai da kallonta izuwa samar fuskar Sweetien.

"Kullum da kike kwanciya a jikin nawa izinina kike nema ne?". Sweetie ta bata amsa tana mai kai hannunta a saman fuskar Prettyn, dogon hancinta ta laluɓa ta ɗan ja.

"Wash Allah na, Sweetie kin fara ko?". Ta faÉ—a tana rike hancin nata da hannu É—aya, tana kuma turo baki.

Shiru Kamran ya yi yana kallonsu gwanin birgewa, suna son junansu sosai, akwai fahimta sosai kuma a tsakaninsu, dan Sweetie tana da hakuri ga hangen nesa sosai yarinyar duk da bata gani, Pretty kuma shagwaɓa, kauɗi, saurin kuka, son jiki, rashin iya juriyar yunwa, da dai sauransu duk ta haɗa, hakan kuma baya sa su yi faɗa a tsakaninsu, duk kuma hakurin Sweetie yasa basu yin faɗar, da ace kamar Prettyn take ba hakuri ai da tuni kullum sai sun yi ta faɗa, ita fa Pretty ko yunwa ta fara ji sai ta yi kuka saboda rashin hakuri.

"Daga yanzu ki dai'na kwanciya a jikin Sweetie tun da kin ga bata da lafiya, idan kina jin kwaÉ—ayin kwanciya ki zo ki kwanta a jikina, kada ki kara mata nauyi kan nauyi". Cewar Kamran, yana magana idanunsa yana a kansu sosai, saboda sun burgesa sun kara burgesa sun kara burgesa over to over.

"Yauwa Kamran gaya mata dai, ni yanzu ma ka duba mun ita ta yi ƙiba ne ko? Dan naji ta kara mun nauyi, da idan ta kwanta a kafata bana jin nauyi sosai, amma yanzu sosai take yi mun nauyi in ta kwanta". Cewar Sweetie.

Lumshe idanunta kamar mai jin barci ma ta yi abinta ta kyalesu, kamar bata jin me suke faÉ—a, tana jin Kamran yana gayawa Sweetien ai ta girma ne yanzu shi yasa take kara nauyi, amma sam taki kulasu, dan barci barci ma take ji, yanayin weather wajen ya yi mata daÉ—i sosai.

Sweetie da Kamran kuwa cigaba da hira a tsakaninsu suka yi cikin mutunta juna tare da nuna kula ga juna.

Kamar daga sama gurnanin Rocky ya doki doduwan kunnuwansu. Ai a dubu ɗari Pretty ta waro idanunta. Cikin sanɗo ta miƙe daga kwanciyar da ta yi, abin gwanin ban dariya ta fara rarrafawa a kasa kamar wata mage ta nufi Kamran, tana rarrafawa tana zaro idanu nan nata kamar ka ruga a kuje idan ka gansu, tana kuma rarrafawa tana ƴan waige waige tana neman ta ina zata gano ɓullowar Rockyn?.

Abin ya so ya bawa Kamran dariya, sarkin tsoro kenan, ji yadda take sanÉ—o tana rarrafawa kamar wadda ta je ta yi sata, kai wannan yarinya sai shirin Allah.

Yana tsoron ya yi mata dariya abin ya zamar masu rigima, dan haka sai ya yi kamar bai ganta ba, ya kawar da kansa. Kusa da shi sosai ta zo ta zauna, har da sanya hannu ta riƙo nasa hannun a cikin nata, cikin dabara tana yi tana zaro idanu ta kwantar da kanta a saman shoulder ɗinsa, sai muzurai take yi tana jiran taga ta ina wannan damusa mai gurnanin zai bayyana? Cikinta har ya ɗuri ruwa.

Ita ma Sweetie tsoro ne ya kamata, barema da ta ji Pretty ta tashi daga kafarta, sai ta ruÉ—e, a ruÉ—e ta fara ambatar sunan Prettyn da kuma tana tambayar Kamran Damusa ce ta sake dawowa zata cinyesu ko?.

ÆŠan satar kallon sarkin tsoro Pretty ya yi, ta wani kwantar da kanta a saman shoulder É—insa tsit da ita, kamar ba ita ba fa, duk ta nutsu, wasu malaman ladab ne suka shigeta lokaci guda Æ´ar kaniya, sai muzurai take yi.

"Sweetie it's Rocky my friend, don't worry babu abin da zai yi maku".
Ya bata amsa yana kai hannunsa izuwa kusa da fuskar Prettyn.

Kyasta mata yatsun hannunsa guda biyu ya yi a dai'dai fuskarta, dan yaga ta kafe waje guda da kallo.

Kara ƙanƙame shi ta yi sakamakon gurnanin Rocky da ta kara ji ya matso kusa, ta kara lefewa a jikin nasa da kyau.

"Kamran wlh tsoro nake ji, ni dan Allah ka dai'na zuwa mana da wannan Rockyn, ina tsoronsa sosai".
Ta faÉ—a kamar zata yi kuka, har idanunta sun ciko tab da kwallah.

Hannun nasa da ya kyasta mata a saitin face nata a hankali ya ƙarisa kai shi saman fuskar tata, lallausan kumatunta ya ɗan fara shafawa kafin ya fara yin magana.

"Pretty ko da na zo nan wajen ba tare da Rocky ba, ko na gudun mashi sai ya samoni ya biyoni, in dai a cikin dajin nan ne babu in da zanje na ɓuya mashi, kamshin jikina yake bi ya nemoni, ba dan haka ba ko dan ki yi farinciki zan dai'na zuwa da shi, amma hakan ba zai yi wu ba, yanzu dai abin da nake so da ke ki dai'na jin tsoronsa kin ji ko? Babu abin da zai yi maki".
Cikin sigar rarrashi sosai ya yi maganar, ga tausasawa sosai a voice É—insa.

Shiru ta ɗan yi kafin a shagwaɓe kamar zata sa mashi kuka ta ce. "To ka ce ya dai'na zuwa kusa da ni idan ya zo, kuma ya dai'na taɓani, ina jin tsoronsa sosai".
Ta kai karshen maganar hawayen da suka taru a cikin idanunta suka fara bin ƙuncinta.

Hannunsa da yake a saman kumatun nata ya fara goge mata hawayen da shi yana faɗin. "Please Pretty stop crying, ba na son ganin hawayen, in dai Rocky ne baki son ya zo kusa da ke ba zai zo ba, zan gaya mashi kada ya taɓaki, amma ki dai'na kuka kin ji? Baki ga Sweetie bata kuka bane?".

Da yake ai suna da banbanci, ita Sweetie bata da tsoron da Pretty take da shi, tana da tsoro amma bai kai ko rabin na Pretty ba, kuma ta yarda da maganar Kamran ɗin, tun da ya ce Rocky babu abin da zai yi mata sai kawai ta yarda abinta, ta kuma nutsu ta kwantar da hankali saɓani hjy Pretty sarkin raki da rigima ga saurin kuka.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 30/7/2024.....✍️📚🌹

For information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________24🔥

Kara matsowa kusa da shi sosai ta yi tamkar zata shige jikinsa.

"Pretty na gaya maki babu abin da Rocky zai yi maki, kuma tun da baki so ne ya zo kusa da ke ko kuma ya taɓaki na gaya maki ba zai zo ba, please ki daina wannan kukan".

Ya yi maganar muryarsa a cike da damuwa, alamar sam baya son kukan nata.

Dai'dai lokacin kuma Rocky ya iso wajen, yana wani tafiyar ƙasaita, ya ci nama ya ƙoshi, har wani lashe baki yake yi abinsa, wasa wasa kwana biyun nan har wani ƙiba yake karawa, yana wani murmurewa.

Kai tsaye Kamran ɗin ya nufo abinsa, yana wani numfashi mai haɗe da gurnani alamar ya ƙoshi sosai.

Haba kara ƙanƙame Kamran ɗin sosai ta yi, ji take yi ma kamar ta haye jikinsa kawai, zuciyarta ta kasa yardan mata cewa Rocky ba zai yi mata komai ba, ta kasa iya yarda cewa ba zai cinyeta ba, ita dai tsan Tiger suna cin mutanen.

Kasancewar a ƙoshe sosai yake, sai ya zo kusa da Kamran ɗin kawai ya kwanta, bai bi ta kan kowa ba, bai kula su Prettyn ba, dama sai yana ɗan jin sakalam a cikinsa ne yake neman tsokana, amma tun da yana ƙoshe sai ya yi kwanciyarsa, yau dai babu shinshinar jikin Pretty.

"To kinga ma shi kwanciyarsa ya yi, ki dai'na kukan haka ya isa ko?".
Yana magana yana cigaba da goge mata hawayen nata, duk wani iri yake ji a jikinsa, ji yake yi kamar mai zazzaɓi.

Hannun nasa da yake goge mata hawayen da shi ta kai nata hannu ta riƙo shi cikin nata, a hankali ta lumshe idanunta ba tare da ta saki hannun nasa ba kuma bata tashi mashi daga saman shoulder ɗinsa ba, ta yi shiru kamar mai barci.

Shiru shi ma ya yi yana tunanin lokacin da yakamata ya koma gida ya yi, dan kada Mamma ta nemesa. Jin saukar numfashinta irin na mai barci da ya yi ne yasa ya dawo da kallonsa daga kan Sweetie dake zaune shiru izuwa saman fuskarta, ta yi mashi barci a jiki, ga shi ta ƙanƙame mashi hannu kamar nata ne.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, zuba mata waɗan nan kyawawan fararen idanun nasa ya yi yana mai karewa fuskarta kallo, ba ƙaramin kyau wannan ɗan bakin nata yake yi mashi ba, sarkin raki har ta yi barci kamar ba ita ba, ya faɗa a cikin zuciyarsa. Can kuma ya sake cewa she's so very very beautiful more than anybody that I saw in my life. Ya yi maganar yana jan doguwar numfashi tare da saukewa a hankali.

Jin shirun ya yi yawa ne yasa Sweetie ta ce. "Pretty ya naji kun yi shiru?".

Ba tare da ya kalli in da take ba ya amsa mata da cewa.
"Pretty ta yi barci".

"Dama bata da wuyar barci ai rigimammiya kawai". Ta bashi amsa tana mai gyarawa ta kwanta a wajen ita ma.

Ta wutsiyar idanunsa ya kalli ta kwanta, ya kasa iya kawar da kallonsa daga saman fuskar Prettyn ne, ji yake yi kamar idan ya kawar da kallonsa wani abin zai ragun mashi, dan haka sai ya kasa iya kai kallonsa kan Sweetien ma.

Shi ma Rocky barci ya fara yi abinsa, an ci an ƙoshi sai me? Ai sai barci. Wajen ya rage saura Kamran ɗin ne kawai idanunsa biyu, dan da alama ita ma Sweetie ta yi barci............. PRINCESS TEEMA CE TAKU TA AMANA🤍🔥

🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️

KINGDOM OF POWER 💪🔥

Kamar yadda King ya umarta haka aka wuce da su Yusuf prison na cikin masarautar in da ake rufe bayi da mayaka ana horar da su idan sun yi laifi.

Bayan King uncle Abbas ya bi domin ya je ya samu su tattauna, dan ya nemawa su Yusuf afuwa da sassauci a matsayinsa na wanda ya basu izinin shigowa, kuma a matsayinsu na ƴaƴa ga abokinsa, koma dai me tun da basu aikata fyaɗen ba ba zai so ayi masu wani tsastsauran hukunci ba. Bai san cewa shi ma King zuciyarsa a cike da tunani kan cewa ba lafiya su Yusuf suke ba, saboda yasan jin sunan masarautarsu ma kawai tamkar jin isowar mutuwa ga bawa ne, bare kuma jin sunan shi King ɗin da kansa, so ya fara tunanin ba lafiya Yusuf yake ba, dan yasan abu ne wadda ba zai yi wu ba ace a sami wani mai karfin zuciyar da zai iya tunkarar KINGDOM OF POWER har ya yi ƙoƙarin yiwa wata daga cikin gimbiyoyin masarautar fyaɗe, ko mahaukaci ne ba zai yi wannan gangancin da rayuwarsa ba!.

A ɓangaren twins namu kuwa, sarakan sharp brain, suna kwance abinsu, duk bom da yake tashi a gidan suna sane da komai, suna jin hayaniyar komai, amma tamkar babu su a cikin gidan, sai shakiyancinsu kawai suke yi a saman bed, suna ta uban dariya kamar ba lafiya suke ba, Obaid sai ya yi kamar zai yi ladab ya sake kwashewa da dariya kamar zararre, shi kam Omaid dama ba gwanin yin dariya bane ba, sama sama yake ɗan taɓawa idan ɗan uwan nasa yanayi, dan ya fi Obaid iya mugunta shiyasa baya dariya sam sam.

Su Gimbiya Zunaira kuwa suna school abinsu, bama su san me yake faduwa a cikin family part ba, su momma ma sam basu sami labari ba, amma ita Mama ta sami labarin daga bakin wata munafukar kuyangarta mai yi mata leƙen asiri, duk wani motsi a cikin gidan Mama tana sani, tana da CID da suke yi mata aikin leken asiri sosai, haka zalika Mammie mahaifiyar su Yah Jawad, duk wani abin da yake faruwa in ma a part ɗin King ko kuma a cikin fada dukka tana sani, kamar wata aljana, sai ta riga uncle Abbas jin labarin abin da aka zartar a fada, sai ka rasa ta ina take samo labaran, ta fi mama iya bala'i sau dubu, ita nata mai lasisi ne. Yanzu haka duk abin da yake faruwa a wannan part na bakin har Mammie ta samu labari, ta ji komai da ya faru daga farko har ƙarshe, zuciyarta fari kal abinta, wani irin sanyi ne ya ratsata, dama ba ƙaramin kai ruwa rana da uncle Abbas suka yi ba a kan cewa ita bata yarda wani Yusuf ya zo wajen Sarina ba, saboda idan baku manta ba ita burinta Sarina da Fanan su auri ɗaya daga cikin Prince na kingdom of power, so ita bata burin kowani namiji ya kusanci ƴaƴan nata, shiyasa ta kafewa uncle Abbas a kan lallai ita fa bata son wannan Yusuf ɗin.

Shi kuma ya ce ba makawa Yusuf sai ya zo, idan kuma Sarina ta yi na'am da shi to aure babu fashi. Wannan dalilin yasa da ta ji cewa ga abin da ya faru da su Yusuf É—in ta fara sakin wani irin shu'umin murmushi wanda babu mai iya fassara me murmushin yake nufi sai ita da ta yi shi, ita kaÉ—ai tasan nufin kayanta, amma dai murmushi ne mai tattare da abubuwa da dama a cikinsa, dan bana alkhari bane.

Haka zalika duk wani abin da kake son sani a dangene da fada to ka tambayi Aneesa Æ´ar Mama zaka samu labari dallah dallah idan ta yi niyar faÉ—a, sai ka rasa daga ina ita ma take jiyo labarin komai.

Idan muka koma ɓangaren Yah Jawad da Gimbiya Chuchu a hospital kuwa, yana zaune rike da waya yana latsawa, amma shi da kansa bai san ina yake shiga a cikin wayar bama, bai san me yake taɓawa ba, saboda kwata kwata hankalinsa baya a kan wayar, yana kan waɗan nan nurses ɗin da suke ta faman shafawa Gimbiya Chuchu wasu mayuka a kyawawan kafafun nata.

Baiwar Allah idanunta sun yi jajir sun ciko da kwallah, ji take kamar ta saka ihu, amma tana tsoronsa kada ya yi mata wani muguntar.

Daga karshe kasa daurewa ta yi saboda wani mai mai zafi da suka sanya mata, hakan yasa ta kasa iya cigaba da rike hawayenta, nan take suka fara simtiri a saman ƙuncinta.

Ta wutsiyar idanunsa yake kallon yadda take ruwan hawayen, ga gwiwowin nata sun yi jajir da su kamar zasu fitar da jini.

Sam bai san lokacin da a takaice ya ce da nurses É—in su kyaleta haka ya isa ba.

Ɗago idanu suka yi suna kallonsa, sai a lokacin ya fahimci ashe ya yi magana, ɗan kara ɗaure fuska ya yi kamar ba shi ya yi maganar ba, ya wani tsare gida tare da miƙewa tsaye daga saman bed ɗin, ji yake yi kamar ya fita waje ya basu waje su cigaba da yin aikinsu, amma kuma ya kasa iya yin haka, kuma har ga Allah ba zai iya ganin abin da suke yi ba, hakan yasa ya ɗan juyo da kallonsa a kanta.

Siraran hawayen azaba sai simtiri suke cigaba da yi a saman kumatun nata.

"Jannat bana ce kada ki bari na sake ganin hawaye a fuskarki ba? This tears is for what again?".
Ya yi maganar yana kara É—aure fuska sosai irin shi boss É—in nan kada a rai'na shi.

Cikin jin zafin ciwon nata ta fara yarfe mashi hannayenta tare da kara tsuke ɗan bakin nan, hawayen suna tsananta gudu a face ɗin tata, a shagwaɓe ta fara magana.

"Ka yi hakuri Yah Jawad, zafi sosai kafata take yi mun, ni ban san lokacin da hawaye suka zubo na, amma na tuba ba zan sake ba....."

Da kyar ta iya kai karshen maganar tata, saboda wani irin kuka da ya so kubce mata.

Wani irin tausayinta ne ya ji ya dira mashi a ransa, amma bai nuna hakan ba, sai ya danne ya ce.
"Okey now goge hawayen kuma kada ki bari wani ya sake fitowa".

Cikin hanzari ta kai hannunta ta fara goge hawaye da shi, sai dai tana gogewa wasu suna kara zubowa sosai, saboda zafin da kafafun nata suke yi mata na dalilin wannan mai da nurses É—in nan suka shafa mata.

Ganin hannayenta sun kasa iya goge hawayen ne yasa ya ciro wani kyakkyawar white handkerchief mai laushi kamar jikin mage daga aljihun suit ɗin jikinsa, sai tashin kamshi handkerchief ɗin yake yi, a hankali ya tako izuwa kusa da ita sosai ta wajen da kanta yake. Miƙa mata handkerchief ɗin ya yi a kan ta karɓa ta goge hawayenta da shi.

Hannu ta miƙo da nufin ta karɓa, a nan ya lura da yadda yannunta ke kerma kamar mai kermar zazzaɓi. Ɗan guntun mamaki ne ya kamashi, a tunaninsa zazzaɓi ne ya rufeta, hakan yasa ya kai ɗayan hannunsa saman 4 head ɗinta dan ya ji ko jikin nata da akwai zafin zazzaɓi.

Babu wani zazzaɓi a jikinta sai ma wani irin ɗumi mai daɗi da jikin nata yake da shi, kawai shegen tsoronsa ne yasa hannunta yake kerma.

Fuskarta ya kallah da kyau kafin ya ce. "Jannat lafiyarki kuwa?".

Karɓar handkerchief ɗin ta yi tare da fara goge hawayen nata tana mai gyaɗa mashi kai alamar e lafiyarta lou.

Su kuwa nurses É—in nan sun saki baki suna ganin ikon Allah, ya dakatar da su daga yin aikinsu, basu karisar da shafa mata magungunar ba, su ga shi bai basu izinin tafiya ba, duk ya sakasu a tsakiya, sai kawai suka saki baki suna ganin ikon god.

ÆŠan karemata kallo ya yi a yadda take kwancen na a kallah one mins kafin daga bisani ya É—ago ya kalli nurses É—in.
"Muna iya tafiya ko?". Calmly ya yi maganar.

"Sir bamu kammala shafa mata magungunar ba ai".

Satar kallonta yadda take aikin goge hawayen ya yi kafin ya ce. "Wajibi ne sai an shafa su dukka?".

A hanzarce cikin girmamawa tare da ladabi da biyayya suka girgiza mashi kai alamar aa ba wajibi bane sai an sha dukka, sun rigada sun shafa masu muhimmanci.

"Bayan waÉ—an nan abubuwa da zaku shafa mata ko nace wadda kuka fara shafa mata da akwai wani abin da zaku yi mata ne? I mean injection or drugs?".

Nan ma a hanzarce suka girgiza mashi kai alamar a'a babu, iya waÉ—an nan mayukan ne kawai.

Shiru ya yi bai sake yi masu magana ba, hannu ya miƙa masu a kan su nashi mayukan da suka rage basu shafa mata ɗin ba.

Cikin rawan jiki suka ɗauko suka miƙa mashi. Karɓa ya yi tare da sa kai ya wuce ya fita waje.

Jim kaɗan ya sake dawowa ba tare da mayukan a hannunsa ba, kai tsaye wajenta ya nufa, tana kanƙame da handkerchief ɗinsa a saman ƙuncinta ta kasa cirewa, saboda hawayen nata ya ki dai'na zuba, shi ne yasa ta bar handkerchief ɗin a face ɗin tata, da hawayen sun zubo sai ta yi maza ta goge dan kada ya gani, bata san cewa duk abin da take yi yana ganinta ba, yana ganinta sarai, amma ya nuna kamar bai ganta ba, tausayinta ma sosai yake ji a yanzu.

Hannayensa dukka biyu yasa ya ɗauketa cancak ya saɓata a saman shoulder ɗinsa, kai tsaye ya nufi waje da ita ba tare da ya sake bi ta kan nurses ɗin ba, sai cikin motarsa.

A guje driver ya buÉ—e masa kofar motar tasa, a gidan baya ya zaunar da ita, sannan ya zagayo ta É—ayan side É—in ya shiga.

A hanzarce drive ya shiga tare da yi wa motar key, cikin kwarewa da iya aikin sosai ya figi motar suka bar hospital É—in, kai tsaye family part suka nufa, dan wajen Akka zai mayar da ita kamar yadda ya É—aukota, dan idan ba haka ba wannan tsohuwa ba zata rabu da shi ya zauna lafiya ba, so gara ya mayar mata da ita ya samawa kansa salama.

Ko da driver ya yi parking É—in motar a tampatsetsan parking space da yake a fam part É—in, basu fito ba, tamkar Yah Jawad bai san da an iso family part É—in ba.

ÆŠan satar kallonsa gimbiya Chuchu ta yi, dan ita tana son ta je ta kwanta, barci sosai take ji, Allah ya gani ba zata iya jurar zaman nan ba.

"Sir zan iya tafiya ko kuma akwai in da zan kai ka?".
Cewar driver.

Da hannu ya yi mashi alamar yana iya tafiya ba tare da ya yi magana ba. A hanzarce ya fito daga cikin motar ya mai da marfin ya rufe.

Sun ɗauki a kallah 10 mins a haka shiru yana taɓa waya wanda shi da kansa ma bai san me yake yi a cikin wayar ba, kawai taɓa ta yake yi.

Sautin canzawar numfashinta daga dai'dai izuwa na wahala ne yasa ya É—an nisa tare da juyo da kallonsa a kanta, ya wani sakata zunbula hijabi gwanin ban dariya, sai ta kara zama Æ´ar karama a ciki.

Kallon second biyar ya yi wa face nata kafin ya fara magana a nutse.
"Wannan punishment da na yi maki is for fitowa with sleeping dress da kika yi ne kawai, now saura na haɗani da Akka da kika yi and ɓata mun lokacin da kika yi kika hanani zuwa office, by 8:30pm ki sameni a part ɗina".

Tsabar bakin ciki bata san lokacin da ta saka mashi kuka ba, dan tasan punishment É—insa shi da Yah Jaish babu kyau, ji na jiya ma da ya yi mata sai da ta dangana da asibiti bare kuma ya kara yi mata wani, wai tsabar mugunta har da wani cewa iya na fitowa da kayan barcin da ta yi ne kawai, to shi kuma na haÉ—a shi da Akka ya zai kasance? Ga hanashi zuwa office da ta yi, wlh ba zata yarda ba, hakan yasa ta kara sautin kukan nata sai dai ya kasheta kawai ya huta, tun da su dama basu iya komai ba sai mugunta.

Zuba mata idanu ya yi yana mamakin yadda take kukan, ita kuwa ta rufe idanunta gam dan ma kada su yi ido huÉ—u ta ji tsoronsa ta yi shiru, ba shirun da zata yi!.

Da dai yaga da gaske take yin kukan kuma bata da niyar dai'nawa, and kuma yasan yana ɗaukarta suka shiga ciki a haka tana kuka confirm sai ya haɗu da su uncle Abbas or uncle Taheer, ko ma dai King da kansa a hanya, da wuya ya gifta har ya kai part ɗin Akka bai haɗu da ɗaya daga cikinsu ba, barema Momma, idan ya haɗu da ita ai sai ta saka shi a kwana da masifa, dan bata son abin da zai taɓa mata autarta Gimbiya Zunaira da kuma Chuchu, tana ji da ƴan mata biyun nan, bare ma Akka, ai yana zuwa wajen Akka ya shiga talatin ma ba uku ba.

Dan haka sai ya kai hannu dan dole ya jawota jikinsa dan ya rarrasheta ta yi shiru ya samu ya mayar da ita wajen Akka ya kama kansa, da dai Jaish ne wlh ko kukan mutuwa zata yi bata isheshi kallo ba, sai dai ma ya kara mata da mari, kuma hakan ba zai hana shi ya sakata ta taka da kafafunta har izuwa cikin gida ba, ai idan ma Jaish É—in ne wlh asibitin ma ba zai kai ta ba, sai dai Akka ta yi ta surutu har ta gaji ta yi shiru, tafiya ma zai yi ya basu waje sai dai duk abin da zai faru ya faru, Jawad yana da saukin kai sosai a kan Jaish.

Ɗan bubbuga bayanta ya fara yi alamar rarrashi, duk Akka ce sila, wannan tsohu ta koma Dubai su huta, yanzu sai ta kai karansu wajen iyayensu haka take yi, ta ja masu wahala, shiyasa dan dole suke lallaɓata.

"Ya isa haka kukan! Ki yi shiru ki faÉ—a mun kukan me kike yi?".
Ya faɗa can kasan maƙoshinsa.

"To Yah Jawad ba kai ne ba, na ce ka yi hakuri ba zan sake ba, amma kaki ka hakura, ka ce zaka kara bani wani punishment É—in, ga shi kuma kafata tana yi mun ciwo".
Ta yi maganar cikin muryar kuka, da kyar da kyar ma take iya maganar saboda kukan, har da shessheka.

"Yanzu da na ce kizo cikin part É—ina ki sameni cewa na yi zan baki wani punishment É—in ne?".

Girgiza mashi kai ta yi alamar a'a tana daga kwance a kirjinsa ya É—aura hannunsa É—aya a saman bayanta, É—ayan hannunsa kuma yana rike da wayarsa.

"Kin san me zan yi maki idan kika zo part É—in nawa ne?".
Ya sake jefa mata tambaya yana mai cigaba da kallon face É—inta.

Nan ma girgiza mashi kai ta yi alamar a'a bata sani ba.

"Amma kike yin kuka a kan abin da baki sani ba?".

Shiru ta yi tare da fara goge hawayenta da handkerchief É—insa da yake a hannunta wadda ya bata É—azun.

"Ka yi hakuri ba zan sake ba, na tuba".
Ta faÉ—a a kasale, saboda kukan da ta sha ma duk yasa barci take ji over.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ganin cewa ta dai'na kukan, sannan ya kai hannu ya ɗago haɓarta daga saman kirjin nasa, ya zama suna fuskantar juna.

"Kada ki yarda ki bari na sake ganin hawaye a saman wannan kumatun naki, in kika bari hakan ta faru to zamu ɓata, yanzu dai mun shirya tun da kin ce ba zaki sake ba, sannan kamar yadda na faɗa anjuma ki sameni a part ɗina, ta shi mun a jiki mu wuce cikin gida".

Ya kai karshen maganar tare da sakin haɓar tata yana mai kawar da kallonsa daga kanta.

Ajiyar zuciya ita ma ta sauke tare da tashi mashi daga jikinsa cikin sauri, ta ji daÉ—i koba komai ya ce ya hakura ba zai yi mata hukunci ba, kuma ya ce sun shirya, amma fa har yanzu akwai sauran haushinsa a ranta.

Buɗe kofar motar ya yi ya fito, ya zagayo ta side ɗin da take ya buɗe kofar, a saman shoulder ɗinsa ya saɓota suka nufi cikin gida.

Bai direta a ko'ina ba sai a saman katafaren bed ɗin Akka, yana sauketa call ta shigo wayarsa, a lokacin kuma Akka bata a cikin ɗakin, tana part ɗin King saboda abin da ya faru da Sarina, ta sami labari, shi ne ta yi maza ta je ta duba ko dai da gaske anyi mata fyaɗen ne su shiga uku, Akka sarkin zafin rai, tana jin labari tun bata ƙarisa wajen ba ta ce ba makawa kashe Yusuf za'ayi, wannan tsohuwa tafi King zafin nama da zafin zuciya ga iya faɗa kamar me.

Zama ya yi a gefen bed É—in tare da yin picking na call É—in saboda Mammie É—insa ce take kiransa, dama wayoyinsa guda biyu ne, wanda ya kashe a asibitin nan ita ce wayar da yake amfani da ita ma mutanen waje, wadda take hannunsa kuwa iya familynsa ne kawai suke da wannan number, su kawai yake kira kuma suke iya kiransa da shi, gabaÉ—aya Æ´aÆ´an su King suna da tsari sosai a rayuwarsu, komai daki daki suke yinsa, basu haÉ—a abu kaza da kaza, kowanne suna ware mashi matsayinsa da ta dace da shi, wannan dalilin yasa a koma ina suke suke zama the most responsible parsons.

"Yanzun nan ka same ni a part É—ina". Shi ne abin da Mammie É—in tasa ta ce.

Da akey ya amsa mata da shi tare da miƙewa tsaye, zura wayar a cikin aljihunsa ya yi bayan ya karse kiran kafin ya juyo da kallonsa a kanta. Idanunta a lumshe, da alama ta yi barci, dan dama barcin take ji.

Ganin alamun ta yi barci ne yasa a hankali kamar wani mai sanÉ—o zai yi sata, hijabin jikin nata ya É—an yaye sama dan ya kalli kafafun nata, wato ba zai dubata idan idanunta biyu ba, dan kada ta rai'na shi, shi ne sai da ta yi barci ne zai duba kafafun.

Ajiyar zuciya ya sauke tare da mai da kallonsa a saman fuskarta, tana rungume mashi da handkerchief É—insa ga sauran guntun hawaye a face É—in nata.

Hannu ya kai ya ɗan shafi lallausan gashin kansa kafin ya furta "Am so sorry my sister, nasan babu wanda ya taɓa sakaki kuka a gidan nan sai ni, gaskiya ban kyauta ba". Ya yi maganar a fili kuma kasa kasa ta yadda babu wanda zai iya jinsa, shi da kansa yasan ya yi laifi.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.