Complete Hausa Novels

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Rawanin_Zalinci_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 3 of 24

Cigaba da kuka ta yi abinta, tana yi tana wani irin jan numfashi alamar fa ta kai kololuwa wajen jin haushi.

"Mamana ta shi ki je ki É—auko hijabinki mu je bakin kasuwa a tare mu sayo wani inabin kin ji?".

Ya faÉ—a cikin sigar rarrashi.

Maƙe mashi kafaɗa ta yi, da kyar ta iya cewa. "Ni baba ka bari sai gobe, kada ka fita da daddaren nan, kaga ranar ma da ka fita sayowa Zainab magani masu kwacen waya sun tareka a hanya ko? Tom ka bari sai gobe kawai ka dawo mun da shi daga kasuwa".

Tana magana wasu hawaye suna gangaro mata, kai daga jin maganar tata kasan ba daga cikin zuciyarta ya fito ba, ta faɗa mashi hakan ne kawai dan son da take yi mashi, bata son waɗan nan gurɓatattun mutane masu kwacen wayar su yi mashi illah, dan a wancan karon da suka tare shi har sun buge shi da sanda a hannu, sannan suka kwace mashi waya, haka hannun nasa ta kumbura tsawon sati biyu baya zuwa kasuwa, baya fita ko'ina, da kyar ya samu hannun ta yi sauki, shi ne yasa yanzu da sun yi sallar issha dai sun shiga kenan, zasu rufe gidan abinsu, a lokacin da abin ya faru Khadijah ta sha kuka kamar ba gobe, dan tana tsananin son baban nata, yana kyautata masu over.

"Amma mamana ki bari naje a sayo maki, dan nasan kina so, ga shi ma kin kasa dai'na yin kuka, kawai ki barshi bari na je na saya maki".

Cikin sauri ta kai hannunta a saman face nata ta fara goge hawayen nata tana faÉ—in.

"Baba ga shi nan ai na dai'na yin kukan, ni dai ka bari sai gobe ka sayo mun".

Ƙaƙalo murmushin dole ya yi tare da sanya nashi hannun ya fara tayata goge hawayen yana faɗin.

"Tom shikenan, gobe idan Allah ya kaimu guda biyu zan sayo maki, yanzu tashi muje mu ci abinci ko?".

"Baba Allah bana son wannan Aunty Hauwar, haushi take bani, kullum idan ta zo gidan nan sai mama ta bata abubuwanmu ta tafi da shi gidanta".

Ƴar murmushi ya yi kafin ya fara bata amsa da cewa.

"Haba mamana, kada ki zama mai rowa mana, menene dan mamanki ta bawa wata kyautar abu? Ai lada zamu samu, kin ga wannan Aunty Hauwar taku? Mamanku bata da kawa biyunta, tare suka taso unguwa guda, a tare suka yi wasan kasa, a tare suka yi karatu, Allah da ikonsa kuma sai ya kawosu aure gari guda, kin dai san mamanki bata da kowa a nan ko? Iya Æ´an uwana kawai ke gareta, nata Æ´an uwan babu ko mutun É—aya a nan, to haka ita ma wannan Aunty Hauwar, bata da kowa sai Æ´an uwan mijinta sai kuma mamanku, kinga dole zasu kaunaci juna su kuma haÉ—a kai da juna dan su É—ebewa junansu kewar iyayensu da Æ´an uwa, dan haka ki dai'na cewa kin tsaneta kin ji ko? A matsayin Æ´ar uwar mamanku take, ku É—auketa tamkar kawu Sadiq naku, ba kuna son Kawu Sadiq ba?".

Da suri ta gyaɗa mashi kai tare da faɗin. "E baba muna son kawu Sadiq sosai, kullum baya taɓa dawowa gidan nan ba tare da ya kawo mana abin kwalama ba, amma shi Yah Haidar sam baya bamu komai, sai shegen masifa ya iya, shiyasa ni nafi son kawu Sadiq nawa".

Shiru baban nata ya yi, har cikin ransa bai ji daÉ—in maganarta ba, ransa ya sosu, amma ya zai yi? Gaskiya take faÉ—a, dan Khadijah bata karya, Haidar É—in shi ya jawa kansa.

Nasan zaku so sanin wanene Haidar a gare su, wanene kuma Sadiq, to Haidar dai ɗane ga babbar ƴar babansu, wanda tun yana ƙarami baban nasu ya rike shi, a tare suke zuwa kasuwa, yana taya shi sayar da kaya, mutun ne shi mai irin halin mata, akwai shi da gulma, ga shegen iya eyes service, idan babansu yana nan zai kulasu, a bayan idanun babansu kuma sai hantararsu ya iya yi da zagi, baya wani kulasu, maman nasu ma ba wani ɗaukarta da daraja ya yi ba, ta rike shi tun yana ɗan shekara 8, yanzu har ya kai 18 years a duniya, amma hakan bata hana idan ta yi mashi ba dai'dai ba ya yi mata rashin mutunci, ga shehen kai gulma cikin dangi, ya ja ayi ta zagin Mamansu Zainab ɗin a kan ta mallake babansu, abu dai babu daɗi, yanzu duk ƴan uwan mijinta basu sonta, kuma duk wannan Haidar ɗin shi ne sila, ya je yana kwasan duk sirrin gidan yana kaiwa dangi, har da karawa da karyarsa son ransa.

Shi kuma Sadiq kani ne ga maman nasu, yaron kirki, ko da yake dama dole ya zamana yana kaunarsu Zainab ɗin sosai, saboda ƴar uwarsa, tun da aka aurota tana amarya ta taho da shi, dan bata da kanwa mace, sai shi kaɗai, shi ne ta roki babanta lokacin tun yana da rai, ta roƙe shi ya bata Sadiq ɗin, da kyar aka yarda aka bata shi, a lokacin yana da shekaru 7 a duniya, ta rike shi har yanzu ya kai yana da 17 years, yaron kirki mai yin komai tsakaninsa da Allah, yana kaunar su Khadijah ɗin sosai, ko fita ya yi waje zai sayi abu, to ba zai dawo cikin gidan ba sai da sweet ko biscuits, ya kawo masu, su yi ta murya, yana kyautata masu sosai, duk abu mai kyau idan ya gani zai saya masu ya kawo masu, ko kaya ya gani a kasuwa an kawo sabbi masu kyau, da kuɗinsa yake cirewa ya saya masu, wani lokaci har faɗa yake yi da Haidar ɗin akan hantararsu Khadijah ɗin da yake yi idan babansu baya nan, kullum kuma idan suka yi faɗa sai Haidar ɗin ya yi mashi gorin cewa wai iyayensa basu da karfin rikesa ne yasa suka haɗawa kawunsa wato banansu Zainab ɗin kenan nauyi, wai yazo yana cinye masu arziki shi da ƴarsa, wani lokaci har ikirarin cewa sai ya yi sanadiyar barinsu gidan daga shi har ƴaƴar tasa Haidar ɗin yake yi, shi ala dole ana cinyewa kawunsa kuɗi, saboda jahilci, bai san me ake nufi da mata ba!.

Wani lokaci har kuka Sadiq ɗin yake yi ya ce ba zai zauna a gidan ba zai koma garinsu, dan yana da zuciya, Mamansu Zainab ɗin ce take bashi hakuri ta yi ta lallaɓa shi, ta ce mashi idan ya koma ya barta ita da waye zata zauna? Waye zata gani ta ji daɗin rayuwa? Ya sani ƴan uwan mijinta duk basu sonta, idan ya tafi ya zata yi da rayuwarta?. Da haka take lallaɓa shi ya yi hakuri ya zauna.

Shi Sadiq ya yi karatu, yanzu haka yana Ss3, shi kuwa Haidar tun daga primary 4 ya fasawa malamin English nasu kai dan bai yi class work da aka basu ba malamin ya zane shi, shi ne ya fasa mashi kai da katako ya gudu ya bar makarantar, tun daga lokacin ya ce ya ajiye karatu, ba yadda ba'ayi da shi ba ya koma makaranta, amma fir yaki yarda, har canza mashi makaranta banansu Zainab ya sake yi, amma sam yaron nan yaki, ya ce shi neman kuÉ—i zai yi, ga jahinci a cike da kai, shiyasa yake gulmace gulmace da tsugudidi tare da kananan maganganu, da ace yana da ilimi ya yi karatu, da sam ba zai yi wannan shirme ba, yanzu yana nan babu boko babu Arabic, shiyasa a haukarsa yake ganin cewa wai Mamansu Zainab tana cinyewa kawunsa kuÉ—i ne ita da kaninta Sadiq, to bai ma san me ake nufi da mata ba, ba ilimi, matar ma wadda ta haifawa kawun nasa Æ´aÆ´a har guda biyu, ai ta wuce wasa.

Allah ya gani baban Zainab yana iyaka bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya kyautata masu, daga Haidar ɗin har sauran ƴan uwansa, shi yake ciyar da Mamansu Haidar ɗin, dan mijinta dai sai a hankali, bashi da ko sisi ba aikin yi, hakan tasa baban Zainab ɗin yake ɗawainiya dasu, amma duk basu gani, sai suce Maman Zainab tana hana shi ya taimaka masu, ta kanainaiye komai ita da ƴan uwanta.

A kasuwa duk wani harkar kuÉ—i da lissafi da Sadiq baban Zainab yake yi, dan Haidar kam kan fanko ce, bai san komai ba, hakan ne ma yasa Æ´an uwan baban Zainab É—in suka dage a kan lallai maman Zainab asiri ta yi wa É—an uwansu, wai tun da harta harkar kuÉ—i a kasuwa da Sadiq kaninta ake yi, Haidar ya zama bare saniyar ware É—an kallo, ita dai maman Zainab sai dai ta toshe kunne kawai baiwar Allah, shi ma Sadiq É—in yanzu dan dolensa ya ko yi toshe kunnensa, baya kula kowa, idan maman Haidar ta isko shi a kasuwa, zagi da cin mutuncin kala kala take yi mashi, idan ta gama sai ya ce Allah ya bata hakuri kawai, dan bai san me zai cigaba da ce mata ba kuma.

Wannan shi ne kaÉ—an daga cikin tarihin Sadiq da Haidar, to mu je dai zuwa.

"Baba ya ka yi shiru?". Cewar Khadijah.

Doguwar numfashi ya ja tare da saukewa a hankali. "Babu komai mamana, muje parlourn ki ci abinci ko?".

Kai kawai ta gyaɗa mashi alamar to suje. Miƙewa ya yi tare da riƙo hannunta ya sauketa kasa, sannan suka nufi parlourn.

A yadda suka bar Zainab da Maman Zainab haka suka dawo suka samesu, kasancewar baban nasu yana nan ne yasa Haidar ya ce.

"Khadijah uwar rigima, daga cewa ba'a sami inabin ba har kin fara kuka". Cewar Haidar sarkin eyes service.

Wata uwar harara ta wurga mashi ba tare da ta amsa mashi ba, yanzu haushin kowa take ji, har maman nata da ta bawa Aunty Hauwa wannan inabin, ita ma duk haushinta take ji.

A baki baban nasu ya rinƙa bata abinci yana rarrashinta, yau an yi sa'a ƴan mutunci suna gaba goshi, dan haka sai ta hakura ta ci abincin, ba musu.

Bayan sun kammala ne suka zauna yin kallo kaɗan, ita kuma Maman Zainab ta hau tattare kayan abinci. A cikin wannan daren ta yi wanke wankenta, ita bata barin kayan abincin da aka yi anfani da su da daddare su kai wayewan garin gobe, a daren take wanke su tsab, haka kayan wanki, waɗan da aka cire a ranar bata taɓa bari ya kai gobe ma bare har ya taru mata sosai, a ranar take wanke su abinta, so haka ta wanke kayan abincin nan fes tare da dawowa ta sake yin mopping na parlourn sosai, sannan ta kunna buner ta zuba turaren wuta mai daɗin kamshi kafin ta haye saman sofa kusa da baban nasu ta zauna.

Wani American film suke kallah a MBC, sun nutsu tsit kamar babu kowa, ita kuma Khadijah kaf hankalinta baya a kan Tv, sai tunanin islamiya take yi, dan an kara masu karatu yau, kuma da daddare ne kawai take samun damar yin karatun, da safe zasu tafi makarantar boko, ba zasu dawo ba sai karfe uku, idan suka dawo kafin su ci abinci su yi wanka haɗe da shirin islamiyar, karfe huɗu ta yi, dole islamiyar zasu wuce a dai'dai wannan lokacin, so babu time, yanzu haka Khadijah tana primary 2 a makarantar boko, ita kuma Zainab primary one zata shiga yanzu, suna da ƙoƙari sosai, saboda kula da suke samu daga wajen iyayensu, babansu ba wai ɗan kasuwa bane kawai, degree gare shi a fannin electric engr, kuma ya fito ne da first class, kawai yanayin kasar ce tasa ya zama ɗan kasuwa mai sayar da atamfofi, lace, shadda, da dai sauransu, babu aikin yi, ya gama karatu bai sami aiki ba, shi ne ya zaɓi ya fara kasuwancinsa kawai, ya tattara result na makarantar ya ajiye a gefe guda.

Mammansu kuwa ta gama secondary school nata, tana da ilimi dai'dai gwargwado, sannan macece mai ilimin addini, ga saukin kai da tausayi tare da fawwalawa Allah komai nata, so a takaice dukkansu daga maman har baban duk ba jahilai bane ba, suna da ilimi, shi ne yasa suke kula da karatun su Khadijah sosai da sosai.

Sai misalin ƙarfe 9:30 su Khadijah suka miƙe suna yi wa iyayen nasu sai da safe, dama already sun rigada sun sani, karfe 9:30 suke shiga su kwanta, saboda tashi zuwa makaranta, tun suna yara mamansu ta tsara masu tsari mai kyau na rayuwa, wani abin ba sai ance su yi ba, sun riga da sun saba yi.

"Mamana kada ku manta ku yi addu'ar kwanciya, nima zanzo in yi maku nawa idan zamu shiga". Cewar babansu.

Da to suka amsa mashi tare da wucewa cikin É—akin nasu. Wata riga da wando mai laushi sosai Khadija ta É—auko masu daga cikin drawer saka kayansu, iri É—aya ne kayan launin navy blue.

Miƙawa Zainab nata ta yi, karɓa ta yi suka hau canza kayan ba ɓata lokaci, kayan barcinsu ne.

Bayan sun canza Zainab ta haye saman gado, ita kuma Khadijah ta É—auko takardun islamiyarsu tare da É—auko littafinta na Nahhu ta buÉ—e shafin filul mahdi dan ta kara duba karin karatun da aka yi masu.

Ta É—auki a kallah minti goma tana ta karanta wannan filul mahdi'n kafin ta rufe takardar ta mayar cikin jaka, sannan ta mayar da jakar mazauninta, a lokacin har Zainab ta fara zuba barcinta abinta.

Zama ta yi a tsakiyar gadon ta fara karanta kulhuwallahu kafa uku, falaki da nasi suma kafa uku uku, sai ayatul kursiyu kafa É—aya, sannan amanar rasulu shi ma kafa É—aya, ta tofa a hannunta kafin ta shafa a jikinta gabaÉ—aya, ta juya ta shafawa Zainab ma, kamar wata babban mace, bayan ta shafa mata ne ta jawo masu bargo, dan garin akwai sanyi sosai, gari ne na damina, Khadijah tana tsananin son Zainab over to over wlh, ita kaÉ—ai ce ke gareta.

Su kuma iyayen nasu, sai da suka kai har karfe 11 suna kallo, sai da suka ƙarisa kallon wannan film ɗin, shi ma Haidar saboda tsabar gulma yaki wucewa ɗakinsu, yana nan a tare suka ƙarisa kallon, sannan ya miƙe ya nufi ɗakin nasu yana yi masu sai da safe.

Mamance kawai ta amsa, baba bai amsa ba, dan shi har ga Allah baya son wannan hali na Haidar, kawai ba yadda zai yi ne, ya yi iyaka bakin ƙoƙarinsa a kan yaron nan ya canza hali, ya koma makaranta lokaci bata kure mashi ba, amma sam yaki yarda, ya zauna sai shirmen banza da wofi yake yi, yana mayar da kansa irin local matan nan masu shegen tsugudidi. Ga shi babu halin baban Zainab ɗin ya kore shi daga gidan, dama yaya lafiyar kura bare ace ta yi zawo? Yanzu ma ana cewa maman Zainab ta yi mashi asiri ta mallake shi, to ina ga kuma idan ya kori Haidar? Ai shikenan abu ya sake kwaɓewa, sai aje ayi ɓatattciya da dangi, zaman lafiyarsa kawai ya cigaba da bin Haidar ɗin da idanu har lokacin da zai girma hankalin manyantaka ta shigesa, wata kila a lokacin zai iya gane dai'dai da ba dai'dai ba.

Miƙewa baban Zainab ya yi ya je ya rufo masu kofar parlourn bayan tafiyar Haidar ɗin kenan, dama already ya rufe masu kofar gida kam tun tuni, suna dawowa daga sallar issha suke garƙame kofar gidansu, saboda tsaro, akwai gurɓatattun matasa ɓata gari a unguwar tasu sosai, shi ne yasa basu wasa da rufe kofar gida.

Kowannensu É—akinsa daban, baban nasa daban, ita ma Maman nata daban, amma dayawa lokuta a É—aki É—aya suke kwana, inma na maman or na baban, a dai É—aki É—aya suke kwana, yau ma É—akin baban suka wuce a tare bayan sun kashe kayan kallon nasu tare da wutar parlourn haÉ—e da tattare komai nasu, suka shiga wajensu Zainab suka yi masu addu'a, sannan ne suka nufi É—akin barcinsu. A suba ta gari............

♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥︎♥♥︎♥︎♥♥♥♥♥♥♥♥♥♥

🏞️Forest🏞️

Tun da Kamran ya yi wannn barci bai farka ba har washegari da safe, abin abin ban mamaki mai rikitarwa, ko da ya farka kuma ya jima sosai idanuwansa biyu ya kasa motsawa, jikinsa duk wani irin azabbabben ciwo yake yi mashi, duk ya ji wani irin tamkar ba shi ba, kamar wanda ya sha kayan maye overdose suka sanya shi barci, jin jikinsa yake yi tamkar ba shi ba, kamar an canza shi, da kyar ya iya samun dama ma ya waro idanuwansa waje, wani irin nauyi idanun nasa suka yi mashi, da farko ma ji ya yi tamkar an manne mashi su da super glue, sai da ya yi da gaske ne ya iya buÉ—esu.

A hankali hankali ya fara kallon wani irin jiri jiri tana É—ebarsa daga kwance, saman É—akin nasa ne ya fara juya mashi kamar fanka.

To me ya sami Kamran É—in mu?.

Dishi dishi idanuwansa suka fara ganin masa, like idan mutun yana ƙoƙarin sumewa, haka zai fara gani dishi dishi, yunƙurin miƙewa ya fara yi domin ya lura abin tana so ta fi karfinsa, sai dai ina, bai iya ko motsin kirki ba, tamkar an sanya igiya ne aka ɗaure shi ɗaurin goro, ƙoƙarin buɗe bakinsa ya yi domin ya kira Mamma, nan ma ina ya kasa, dan kuwa ji ya yi tamkar an ɗaure harshen nasa ne kam, ya kasa.

Sanya dukka ilahirin karfinsa ya yi da nufin ya miƙe da karfin gaske, duk da haka a banza man kare, ko motsawa bai iya yi ba, ya juyar da idanuwansa ya kalli gefe guda ma ya kasa, iya saman ɗakin nasa kawai yake iya kallah, duk wata jijiya a jikinsa sai da ta tsaya sak da aiki! Jinin jikinsa duk ya dai'na gudu, nan take idanuwansa suka kara firfitowa waje sosai tamkar zasu faɗi ƙasa, tamkar wadda aka matse sosai, sai ƙoƙarin ya yi magana yake yi, yana son ya kira Mamma ta kawo mashi agaji, amma ina ya kasa, harshensa ma a ɗaure take gam.

Dai'dai lokacin Mammar ta faÉ—o cikin É—akin tana faÉ—in.

"Tun jiya barci yaki karewa kamar ba lafiya ba, maza ka tashi lokacin motsa jiki ya yi, ka kama ka tafi yawonka ba dole ka gaji ka yi ta barci ba, kafa baya zama waje É—aya, baka bawa jikinka hakkinsa na hutawa!".

Jin motsin shigowar Mamma tana waÉ—an nan surutan ne yasa gabaÉ—aya ya ji jikin nasa ta sake, nan take ya ji ya koma normal kamar ba shi ba, abin da É—aure kai da kuma mamaki.

Waro idanuwnsa da suke jajir saboda barci ya yi a kan Maman tasa dake tsaye a kusa da bed É—in nasa tana faÉ—in ya tashi su tafi, ya zo sai wani zuba barci yake yi tun jiya da yamma, da daddare ta tashe shi har ta godewa Allah yaki ya tashi, har ruwa ta shafa mashi a fuska, amma yaki tashi, sai dai ya É—an motsa kaÉ—an ya sake cigaba da barcin abinsa, da farko abin har ya fara bata tsoro, sai daga baya kuma ta kyale shi kawai ta je ta ci abincinta ta kwanta, to shi ne fa bai iya farkawa ba sai yanzu, e gaskiya kam abin da abin mamaki sosai Wlh, akwai kuma É—aure kai!.

Kada ku manta daga cikin littafin RAWANIN ZALINCI wanda alkalamina ni PRINCESS TEEMA ya rubuta maku kuke karanta wannan daddaɗar labari mai cike da ruɗu da ɗaure kai, to yanzu muka fara, bamu ma fara kutsawa cikin labarin ba tukun nan, bamu ma yi komai ba, ku dai ku kasance dani, na tabbata In Sha Allah ba zaku taɓa yin danasanin karatan wannan littafin ba!.

Har yanzu lokacin harshensa ta yi mashi nauyi wajen magana, da kyar ya iya furta.

"Mamma ya naji kina cewa tun jiya nake barci sai yau na tashi? Kina nufin kwana É—aya ta wuce kenan?".

"E mana Kamran, kwana É—aya ta wuce, wai me kasha jiya ne? Ka je ka sha Æ´aÆ´an wata itaciyar mai bugar da mutun ko? Ina ta tashinka daga barci kaki ka tashi" .

Zaro idanuwansa ya yi tare da furta what?! Da É—an karfin, kwana É—aya ta wuce kuma? Ya sake tambayar kansa.

Ganin haka yasa Maman ta ce. "Kamran anya are you okey kuwa? Menene kuma ya faru?".

ÆŠago dara daran idanuwan nan nasa ya yi a in da ya sauke su a saman fuskarta, shiru ya É—an yi kafin ya ce.

"Mamma yau ba zan motsa jiki ba, ina zuwa, bari na je nan baya yanzun nan na dawo, sai na zo na yi wanka......."

Wani irin kallo da ta wurga mashi da waɗan nan sexy eyes ɗin nata ne yasa bai san lokacin da ya haɗiye sauran maganar tasa bai ƙarisar ba.

"Wuce muje ka fara aikin motsa jiki, idan ka gama ka yi wanka ka ci abinci sai ka tafi in da zaka je, dama zaka je kawo mana nama ai, babu abin da zai hanaka yin training, wai shin ni ina ma ka je jiya da ka dawo mun kamar a buge ne?".

Da kyar ya iya miƙewa zaune yana turɓune fuska tare da ɓata rai. "Mamma ni ina kuma zanje da ya wuce in da muka saba ni da Rocky, wai Mamma please yau ki kyaleni da zancen motsa jikin nan mana".

Shiru ta yi mashi bata sake ce mashi ko uppan ba. Yasan fassarar shirunta, hakan yana nufin dole sai ya motsa jikin nan ko yana so ko baya so, ga kuma ciwo a yatsarsa.

Dole tasa ya miƙe jiki duk ciwo take mashi, gaɓɓansa duk suna yi mashi zafi, haka ya wuce gaba yana kara turɓu ne fuska.

Rufa mashi baya ta yi, a saman tsaunin ta bayan kogon nasu suka tsaya, ga wasu manya da kananan duwatsu a wajen, a nan suka tsaya ya fara aikin training da waÉ—an nan duwatsu, ita kuma Mamma ta wani tsaya kamar jarumar sadaukiyar yaki, yacce kuka san wata commender masu bawa mayaka horo, haka ta wani tsaya tana aikin kirga sau nawa ya É—aga wata katuwar dutse.

Sai da ya É—aga sau hamsin cif tana kirgawa, sannan ta ce ya fara press up, haka ya fara yi kamar zai yi kuka, yau duk jikinsa ciwo take yi mashi, ga shi Mamma ta zo tana kara mashi azaba a kan azaba, haka dai ba yadda ya iya, dole ne ya yi idan yana son zaman lafiya.

Da Mamma ta lura fa baya yi da sauri zai ɓata mata lokaci, sai ta koma cikin ƙogon nasu.

Tana tafiya ya yi zamansa yana tunanin maman twins, sai wani mai da numfashi yake yi da sauri da sauri, irin ya sha aiki ya ƙoshin nan.

A hanzarce ya tashi ya cigaba da yi jin alamar takun dawowar Mamma wajen, ba shiri ya É—aura daga in da ya tsaya.

Kusa da shi ta zo ta tsugunna hannunta na rike da wata iriyar doguwar takobi na mayaƙa, sai dai takobin tana a cikin gidanta, bata fito da ita ba, da ƙotar gabaɗaya ta ɗauko. Ɗaga takobin ta yi ta fara kai mashi wajajen hannunsa, hakan yasa ya fara yi da sauri, dan idan ya bari takobin ta taɓa hannunsa zata ji mashi ciwo, dama ga ciwo a yatsar hannunsa tana yi mashi zogi, dan ma dai da diddigen tafin hannu ya dafa ƙasan ne, bai isa ya tsunsa sun taɓa kasa ba, saboda ciwon yatsar nan.

Mamma ta wata fuska idan ka gani sai kaga kamar bata son ɗan nata, amma kuma ita ce ainahin mai sonsa da gaske, yanzu duk in da ya shiga zai iya kare kansa ba sai ya jira wani ya zo ya kare shi ba, sai dai ni PRINCESS TEEMA ina ganin akwai wani dalilin da yasa Mamma ta zaɓi Kamran ya zama jarumi sosai har take bashi irin horo haka mai haɗari, hannunsa yana ciwo ma ba zata kyale shi ba, sai ta sanya shi yin wannan abin, haba mana Mamma..........💔😭

Yau sai da ya kusa saka mata kuka, sannan ne ta rabu da shi tare da kama Æ´atsar tasa dan ta cire wannan bandejin nasa ta kara yi mashi dressing na wajen.

Shi dai burinsa ɗaya kawai, shi ne ta barshi ya je ya ga maman twins, ko yunwa ma baya ji, yana son ya koma ya sake ganin yaran ne, amma bai isa ya tirjewa Mamma ba, dole ya bita a yadda take so dan kada ta yi zargin yana aikata wani abin a ɓoye, dan haka sai ya hakura ta sake yi mashi dressing na wajen ciwon nasa, ta gasa wajen sosai da ruwan ɗumi, sannan ta ce ya je ya yi wanka ya zo su yi breakfast.

Ba musu ya je ya aiwatar da duk abin da ta ce cikin zafin nama, dan ya yi sauri ya gama ya laƙa mum twins.

Zama suka yi suka ci abincinsu kamar yadda suka saba, sannan Mamma ta ce mashi ya je gonarsu ya kawo masu masara ɗanya, ya duba ƙosassu ya ciro, sai ya haɗo masu da nama, daga karshe ta yi mashi kashedi a kan ya kula da yatsar nan tasa sosai, dan yatsar kamar tana son samun matsala.

Okey kawai ya amsa mata da shi kafin ya miƙe ya koma cikin ɗakinsa, kwari da bakarsa masu lafiya ya ɗauko domin farautar nama, sai wata ƴar wuka mai kaifin gaske da ya ɗauka dan tsaro, a kugunsa ya sanya ƴar wukar, ita kuma kwari da bakar ya ratayota a bayansa, sannan ya sanya takalmarsa mai kama da waterproof shoe, a hanzarce yake yin komai, duk dan ya yi sauri ya fita.

A wajen madafa ya isko Mamma, kwandon da suke ciro tomatoes a ciki ya ɗauka dan zubo mata masarar da ta ce ya ciro masu a gonarsu, sannan ya ɗauki wata karamar kwando ma wanda zai zubo masu fruits, dukka kwandunar da itace aka saƙasu, sai dai sun saƙu da kyau.

Sallama ya yi wa Mamma tare da nufo kofar fita. Sosai ta sake yi mashi kashedi a kan kada ya yi wasa da hannun nan nasa fa, ya kula sosai.

Okey ya amsa mata da shi tare da ficewa, yau ya fito sak maharbi. Wajen wata bishiyar lemu ya tsaya ya fara ciro lemun da suka nuna, yana cirowa cikin nutsuwa. Ɗan dai'dai ya ciro kafin ya je wajen bishiyar gwaiva, ita ma ba dayawa ya cire ba, sai mangoro da ita ma bata fi biyar ya tsinko ba, dukka nunannu yake bi yana cirowa, haka ya tara fruits ɗin dayawa, sannan ya nufi hanyar wajen mum twins dan ya je ya kai mata fruits ɗin, ita ya cirowa wannan, na Mammansa sai yana dawowa zai ciro mata, yaron kirki...........😅

Tafiya yake yi cike da jarumta, yana wani bubbuÉ—e kirji kamar wani mayunwacin zaki, ko alamar tsoron wannan daji babu a idanunsa, tsuntsaye sai shawagi suke yi abinsu, shi ma sai tafiya yake yi abinsa.

Wani irin mahaukacin birki ya ja lokacin da ya isa wajen da mum twins ɗin take, sam bai san lokacin da ya saki kwandon fruits na hannunsa ta faɗi ƙasa ta tarwatse ba, fruits ɗin duk suka watse a wajen.

Wani irin kara zaro idanuwansa waje ya yi, nan take fuskarsa ta bayyanar da alamar zallar madarar mamaki, cikin hanzari da zafin nama ya kara matsowa wajen dan ya tabbatar da gaske ne abin da yake gani.

Tabbas gaskiya ce, babu mum twins kuma babu twins, É—akin bukkar da aka yi masu ma duk an kakkarya shi, an karya itatuwar gabaÉ—aya, tamkar waÉ—an da suka yi faÉ—a da Damusa ko kuma Damusa ya faraucesu, duk komai a kakkarye, ga kwaryar magangunanta a wajen duk a farfashe, an fasasu, ga kuma towel É—in da aka rufe baby's É—in duk suna nan, babu abin da aka É—auka a wajen face baby's É—in da Mamansu.

Tamkar a mafarki haka Kamran yake ganin wannan al'amari, tambayar kansa yake yi to ko Damusa ce ta shigo wannan yankin ta cinyesu? Kasancewar shi bai san da cewa biyo maman nasu aka yi daga masarauta za'a kwacewa mata baby's ba, sai bai yi tunanin ko mutanen masarautar tasu ne suka zo suka É—auketa ba, shi dai tunaninsa wata dabbace a cikin wannan daji ta hallakasu ta kuma É—aukesu suka tafi cikin dabbobi Æ´an uwanta suka cinyesu.

To waye ya ɗauki mum twins? Shin da gaske wata dabbace ta cinyesu ko kuma dai waɗan nan warriors na masarautar tasu ne suka dawo suka ɗauketa? Allah mai iko, Allah masani sai kuma alkalamin PRINCESS TEEMA taku ta amana❤️

Wani irin bakin ɓacin rai ne ya bayyana a saman fuskar Kamran, tamkar ya saba da su, tamkar ƴan uwansa haka yake jin mum twins ɗin nan, kawai daga jiya da la'asar zuwa yau ace bata nan? Ina take?. Idanuwansa ne suka kaɗa suka yi ja sosai saboda tsananin ɓacin rai, har wani huci ya fara fitarwa. Cikin matsananciyar damuwa ya fara kewaye wajen yana nemansu, a cewarsa idan ma damusa ce ta faraucesu zai ga ragowar kasusuwansu, shi ne ya bazama ya fara nema, duk wasu lunguna da saƙuna, bayan bishiyoyi da bayan duwatsun, ƙoguna da ramukan itace dake arear wajen, ko'ina shiga yake yi yana leƙawa, nemansu a haukace kawai yake yi, duk yana kiɗi me, baya damuwa da in da yake shiga, ba ya damuwa ko akwai maciji ko wata muguwar dabba da zata cutar da shi, shi dai kutsa kai a ko'ina kawai yake yi yana nemansu, har cikin ramuƙan dake arear wajen irin ramin da ta faɗa ciki ta haifi twins ɗin, har ciki duk sai da ya bi ya rinƙa leƙawa, amma ko alamarsu babu a wannan arear, tamkar ma ba'a taɓa yin wasu halittu irinsu a wajen ba.

To fa babbar magana, tashin hankali da ba'a saka mashi rana, my people ina mum twins?.

*Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.*

🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 4/7/2024.....✍️📚🌹

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

*My people's duk abin da kuka ga na rubuta a cikin wannan littafi na RAWANIN ZALINCI ba sai kun tambayeni a kan meyasa aka yi kaza ba, idan kuka nutsu za'a warware maku komai, ita labari ai ba lokaci guda ake warware komai ba, ku da kanku ba zaku so labarin da komai nata yake a wangale ba, duk abin da marubuciya zata rubuta maku a cikin storynta, ku sani tana sane da wannan abin da ta rubuta, kuma idan kuka yi hakuri zata zo da kanta ta warware maku komai a nutse ba sai kun yi ta tambaya ba, fatan kun gane?. And lastly littafin RAWANIN ZALINCI babu complete nasa, masu tambayata complete babu, yanzu nake rubuta shi!!*

E____________7🔥

Sosai Kamran ya bazama ciki dajin nan yana nemansu, duk ya shiga damuwa bawan Allah.

A takaice dai ya kwashe shekaru yana neman mum twins, kullum da su yake kwana yake kuma yashi a ransa, sun zo lokaci guda sun shiga mashi cikin tunaninsa da kuma rayuwarsa, lokaci guda kuma sun tafi sun bar shi, kamar ba'a taɓa yinsu a wannan daji ba, a cikin waɗan nan shekaru da suka suɗe babu wata rana da zata zo ta wuce Kamran bai yi tunaninsu ba, duk idan suka fita farautar nama shi da Rocky, to sai sun yi ta kewaye a cikin dajin ta arearsu ko Allah zai sa ya ga koda tsinke ne daga cikin kayansu ko wani abin nasu.

Amma ina, bai ga komai ba sam, kuma tsabar ƙoƙari irin nasa bai taɓa cire tsammani tare da sa ran ganinsu ba, yana ji tamkar ko ba jima ko ba daɗe zai gansu, dan yana ji a jikinsa basu mutu ba suna raye, to Allah dai shi ne masa.

And One think about KAMRAN and MAMMA, both of them are not Muslim, ba musulmai bane ba su ɗin, basu da addini dukkansu biyu, Mamma bata yarda da kowace addini ba a rayuwarta, a kan haka ta reni Kamran, sai dai Allah da ikonsa shi Kamran zuciyar musulunci ke gare shi, dan tsantsar son taimakawa na ƙasa da shi yake da, ga son ganin mutane cikin farinciki, wasu abubuwan nasa idan yana yi kamar cikakken musulmi.

Kullum ya zauna sai ya bawa Mamma labarin mum twins, tun Mamma bata kula shi har kunnunwanta suka saba da jin labarin, sai dai bata taɓa bashi goyan baya a kan ya shiga sauram yankunar dake a cikin dajin ya dubasu ba, hasalima ɓacin ranta ne yake bayyana a duk lokacin da Kamran ɗin ya yi zancen wasu bama mum twins kawai ba, sam bata son jin yana magana na ko da maharba ne, amma ba yadda ta iya, mum twins ta riga da ta shiga cikin tunanin ɗan nata, ya rigada ya sanyasu a ransa, ko Mamma bata so dole dole sai ya bata labari, dan dole take saurara.

Mum twins dai shiru, ba ita babu labarinta, babu wanda yasan in da ta yi tsawon shekaru, ko ina suke? Allah masani.

To bari dai mu ɗan kutsa ta wani ɓangare na cikin wannan littafi na RAWANIN ZALINCI ko zamu sami wani ɗan haske a kan abubuwan da suka faru a baya, ko kuma dai har yanzu lokaci bai bamu dama ba, bari dai mu gani.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

KINGDOM OF POWER💪👊🔥

Masarauta ce da babu biyunta a tarihi, ku daga jin sunan POWER kun san me sunan yake nufi, kalmar POWER ta tattara karfi! Isa! Izza, taƙama dukka!.

Masarauta ce mai cike da karfin da jin sunansu kawai ya kan sanya duk girman Daula ta girgiza, suna da horarrun jaruman sadaukai yaki sama da dubu uku, mayakansu mayaka ne da ba su sarewa a pagen yaki, matuƙar sun fara yaki, to fa komai wuya komai daɗi ba su juya baya har sai sun cimma abin da suka je nema, mayakansu ne ake yi wa lakabi da Dangerous warriors, wato mayaka masu haɗarin gaske, jin sunan mayaƙansu kawai ya kan sanya hantar manya manyan masarautu su kaɗa, basu da tausayi ko kaɗan, aiki ziryan suka iya.

Commander ZAFAR shi ne commander na mayaƙansu bakiɗaya, dattijo ne wadda a kallah zai kai shekaru 50 zuwa 55 a duniya, amma da yake dakakken horarran mayaki ne, ya sha training ya ƙoshi, jikinsa duk ta murɗe sosai, idan ka gan shi, sai ka rantse da Allah ba zai wuce ɗan 35 years ba, saboda kyan jikinsa, ya murɗe sosai, damatsan hannun nan nasa tamkar za su fashe, yau sama da shekara 30 yana training tare da bawa mayaƙa horo da dabarun yaki, ai kunga dole jikinsa ya murɗe sosai.

Commander ZAFAR yana da wani dakakken horarran jarumin yaro ɗaya tamkar da dubu mai suna HOORAIN, HOORAIN dakakken namiji ne, tsayyayye, kuma shi ne mataimakin mahaifin nasa, wato assistant commander na mayaƙan KINGDOM OF POWER a yanzu, matashi ne mai jini a jika, shekarunsa 28 a duniya, tun yana ɗan yaro Commander ZAFAR yake koyar da shi yaki, shiyasa ya taso a sadauki kuma cikakken jarumin namiji da KINGDOM OF POWER take alfahari da shi, bashi da mahaifiya, kuma bashi da kani or kanwa, shi kaɗai Commander ZAFAR ya haifa.

KINGDOM OF POWER dai Shinfiɗaɗɗiyar masarauta ce wanda ta kasance na cikakkun jarumai da suka tsaya tsayin daka wajen ganin sun tsayar da masarautarsu ta yarda babu wani mahaluƙi a duniyar nan da ya isa ya nuna su da hannu, koda gate na farko na shiga wannan masarauta ka nuna da hannu, to wannan hannun naka sai ta tashi a aiki, dan sai an sareta daga diddiginta. A bakin gate na farko na shigowa cikin wannan katafaren Masarauta dai gumakan zakuna ne guda biyu waɗan da aka sassaƙasu, suna daga zaune sun buɗe baki ga waɗan nan gabza gabzan hakwaran nasu, an yi fentinsu da fenti launin gold color, daga bayan zakunan kuwa gunkin mutun mutumin wata jarumar macece wadda aka sassaƙata tana a zaune saman dokinta rike da takobi cikin shiga ta doguwar riga.

A takaice KINGDOM OF POWER katafaren masarauta ne wanda yake da gate ɗin shiga ɗai, ɗai, ɗai har guda 5, girman masarautar ta wuci tunanin mai tunani, fadoji har guda uku ne a cikin wannan katafaren masarauta, ko wani fada ya haɗu haɗuwa ta wuce misali, ya kawatu da kayan kwalliya na alfatma irin na sarakuna, masarautu manya manyan guda goma ne a karkashin KINGDOM OF POWER, ga su da tarin uban dukiya na wuce misali tare da maadanan cikin ƙasa. Babbar fada wanda sarki ya fi yawan zama a cikinta, girmanta ya wuci misali, an zuba kayan iya kayan more rayuwa wadda suka amsa sunansu, komai na cikinta Golden color ne, hakan tasa suke wani irin kyalli tamkar gold, suna ɗaukar ido, akwai wasu kwalliya na jikin kujerar sarki waɗan da aka yi su ne da zallar madarar gold, shinfiɗun alfarma dake a tsakiyar fadar nan kuwa kawai abin kallo ne, bare azo kan irin kwalliyar da aka kawata gabaɗaya cikin fadar har izuwa jikin bangon, abin sai dai baki ya furta masha Allah kawai, su kansu luntsuma luntsumar sofa sets dake a cikin wannan fada kyansu ya sha gaban tunani, komai na cikin wannan fadan daga ƙasar Dubai yake.

BARDE KING ZUHAIR ABDUL MALIK, shi ne sarkin KINGDOM OF POWER daya karɓi mulki daga hannun marigayi King ABDUL MALIK BADEEN, wato mahaifinsa kenan.

KING ZUHAIR ABDUL MALIK jarumin ubane jajirtatcen sarki ne wanda ya tsaya tsayin daka akan ƴaƴansa da kuma al'ummar kasarsa bakiɗaya, yana da adalci fiye da tunanin mai tunani, shi ma kafin ya karɓi mulki wajen mahaifinsa, jarumin sadaukin yaƙi ne, ya taɓa zama commander warriors nasu a lokacin da babansa ABDUL MALIK BADEEN yake a kan karagar mulki, yana matashi lokacin, sai dai bai ruke muƙamin commander sosai ba, kasancewarsa ɗan sarki ne, dama kuma su ƴaƴan sarakuna suna karɓar horon yaki ne domin kawai su kare kansu ba dan su yi mu'amala da mayakan dake a cikin masarauta ba, sai dai idan suna ra'ayi, za su iya shiga yaki idan za'a je, wannan ra'ayin kansu ne, amma banda haka sunfi karfin wani mayaki ma ya kalli in da suke, to dai shi ma King ZUHAIR ABDUL MALIK jarumin sadaukin yaƙi ne, hakan kuma yasa ma ake ce mashi BARDEN namiji, domin kuwa BARDEN ne da gaske, ba wasa, jininsa a tafashe yake, bugu da ƙari KING ZUHAIR ABDUL MALIK bamodare ne, nasan dayawanku baku san su waye modarawa ba, modarawa larabawa ne wanda tun zamanin kakanni sun yi suna wajen jarumta da ba'a barin ko ta kwana, da ka taɓa bamodaren balarabe gwara maka ka kwana da yunwa, tun zamanin da can kowa yasan modarawa basu yafe laifi idan aka yi masu, komai ƙanƙantar laifi idan ka yi masu sai sun rama, ga zuciyar bala'i, jininsu a tafashe yake, ga su da shegen haɗin kan bala'i, idan ka taɓa bamodaren balarabe guda ɗaya wlh sai goma sun hayayyaƙo maka, to haka suke, jarumai ne da suka shiga kundin tarihin duniya.

So haka BARDE KING yake, tsayayyen namiji ne mai cikar zarra da halitta. Ƴarsa ta farko shararriyar sadaukiyar yaki ce kafin ta yi aure, jaruma ce a cikin jarumai, ta iya takobi fiye da tunaninku, jininta a tafashe yake tamkar na mahaifinta, bata da wasa kuma bata ɗaukar wasa, har gunkin mutun mutuminta aka gina a bakin gate na farko na shigowa cikin KINGDOM OF POWER, an ginata tana a zaune saman dokinta rike da takobi, ta fi iya takobi sama da komai, tsayawa zayyana maku jaruntar gimbiya Miemie ma ɓata lokaci ne, dan baki ba zai iya faɗen shi ba, duk da ta yi aure, amma tana a cikin KINGDOM OF POWER da mijinta har yanzu, saboda ɗa ga abokin mahaifinta ta aura, wanda shi ma a cikin KINGDOM ɗin yake, jarumine na gaske, kuma su a al'adarsu ce hakan, su zauna inuwa ɗaya, wato family su haɗu su cure waje guda, har gobe Gimbiya Miemie tana wasa da tokobi tamkar mai wasa da ƴar baby, shekarunta 37 kacal a duniya, saboda auren da yake a kanta ne yasa ta dai'na duk wani abin da ya shafi yaki da sauransu, sai dai ta koyar da kananan yara mata masu tasowa ruke tokobi da kuma amfani da ita, wato ta bawa mata horan yaki, amma fa duk wani yaki da za'a tafi, sai mahaifinta ya nemi jin ta bakinta, dan ita ɗin mace ce mai kaifin fikira da basira tare da sanin dabarun yaki, to haka dukka ƴaƴansa suke, jarumai ne na kin karawa, a tsarin KINGDOM OF POWER basu tunkarar waje da yaki kuma su juya, basu ja da baya a yaki, idan fa suka dumfari waje, to komai girman Daular sai sun jijjigeta sun jefar da ita, idan suka ja wa masarauta kunne taki ji, to sai sun rugujeta sun shafe babinta a doran duniya, basu shiri da rashin adalci, duk in da ake yin zalunci, to zasu daka masu warning, idan suka ki ji, to za su shafe babinsu, jininsu a tsananin rafashe yake, baki ba zai iya gaya maku jarumtarsu ba.

King ZUHAIR ABDUL MALIK su huɗu ne a wajen mahaifinsu wato Sarki ABDUL MALIK BADEEN kenan, mahaifiyarsu kuma sunanta Gimbiya JALILA, ƴa ce ga sarkin Dubai, balarabiya ce, kyakkyawar gaske, hakan yasa su King ZUHAIR duk suke kyawawan gaske, King ABDUL MALIK BADEEN mahaifiyarsa ainahinta Sarauniyar Saudi Arabia ce, shi ne ya auri Gimbiya JALILA ƴar sarkin Dubai, ita ce kaɗai matarsa, dukkaninsu tushen iyayensu mata larabawa ne modarawa, shi ne yasa suke da tsananin kyau, ga su jajir kamar ka taɓa jini ya zuba, fararen tattabaru ne da babu ɗigon baki a jikinsu.

Gabaɗaya ƴaƴan King ZUHAIR ABDUL MALIK haka suke, kamar ka taɓasu jini ya zuba, saboda haske da tsantsar kyau, sai ka rantse da Allah basu taɓa taka kasa ba, kamar basu taɓa fita rana ba, saboda tsantsar kyau da haske ga kyan fata luwai luwai. King ZUHAIR ABDUL MALIK shi ne babba, yana da mata uku, kunsan sarki dama baya yin mace guda ɗaya sai dole, matarsa ta fari ma a rana ɗaya aka ɗaura auransu su biyu da ta biyu kenan, da Gimbiya Umaima, wadda ta kasance ƴa ce ga Aminin mahaifin King ZUHAIR ɗin, so ita ba wata ƴar manya ba ce cancan, ita ce kuma uwargida, suna kiranta da Mummy, sai Gimbiya Aleezarh da ta kasance ƴa ce ga prime Minister of Saudi Arabia, suna ce mata mama, so a rana ɗaya King ZUHAIR ya aurensu, daga baya ya auro ƴa ga sarkin Dubai na yanzu, Gimbiya RAHILARH, wato ƴa ga uncle nasa yayan Mahaifiyarsa Gimbiya JALILA kenan, suna kiranta da Momma. So Mummy wato uwar gida yaranta uku, Jaruma Gimbiya MIEMIE ƴar ta ce, kuma ita ce ƴar farin King ZUHAIR ABDUL MALIK. A takaice kenan na fayyace maku wannan Masarauta, sauran bayanai zai biyo daga baya!.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.