Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Rawanin_Zalinci_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 10 of 24
Cigaba da shafa gashin kan nasa ya yi yana mai tambayar kansa Jawad what's wrong with you ne? Ka tafi Mammie na jiranka, shi ne abin da zuciyarsa take gaya mashi. Nisawa ya yi kafin ya mayar mata da hijabin nata ya rufe mata kafafun nata, sannan ya janyo duv na Akka mai bala'in laushi, kamshi, kyau da kuma tsada ya rufeta da shi har izuwa wuyarta, kafin ya sa kai ya fice waje daga cikin É—akin da sauri.
Kai tsaye wajen Mammie É—insa ya nufa kamar yadda ta umarta.
Bakinsa a ɗauke da sallama ya shiga katafaren parlourn ɗinta, duniya guda, duk wannan Daula bai ishe Mammie ba har take sake neman duniya idanu a rufe, sai ka rasa me take da buƙata again, idan kuɗi ne sune suka jikata a yanzu, a cikin daula take, idan mulkin ne ai suna ciki, ta fannin siyasa ma ana damawa da su, amma ita duk fa bai isheta ba, bama shi bane a gabanta ba, burinta kawai koma yaya ɗanta ya zama shi ne the next king of kingdom of power, babbar magana akwai show, ga shi kuma da alama ita da mama kudurinsu ɗaya, kuma suna da ƴan leken asiri sosai da sosai a cikin masarautar, dan duk wanda zai yi motsi a kan idanunsu yake yi, ga dukkan alamu ma ita Mammie tasan da mama da ƴan leken asirinta sarai, saboda ta fi mama iya makirci da tsiya ba kaɗan ba.
Izinin shiga bedroom É—in nata ya ce da Kuyangun da suke yi mata hidima su nema mashi, ya yi maganar yana a tsaye, dan bai jin kamar zai zauna ma, duk baya jin daÉ—i a ransa, bai so ace ya jiwa Chuchu ciwo har haka ba, sam abin bai yi mashi daÉ—i ba.
Yana tsaye har kuyangar ta dawo wajensa tare da bashi amsar Mammie ta ce ya shigo.
Ba tare da ɓata lokaci ba bai bi ta kan kuyangur ba ya yi maza ya wuce ciki da sauri.
Zaune saman sofa da yake set a cikin bedroom ɗin nata ya iskota. Cikin nutsuwa ya yi sallama tare da ƙarisowa kusa da ita.
Saman carpet ya zauna tare da É—aga mata gaisuwa cikin girmamawa.
Tana shirye cikin wani arnen lace mai bala'in tsada, ta zuba gwala-gwalai a wuya da hannu, tana da son duniya over, idan ta zuba wani kwalliyar sai ka rantse da Allah ba za'a mutu ba, gata da iya shan kamshi kamar me, nuna isa da izza a kan abu. Allah yasa gabaÉ—aya su Sarina babu wanda yake kama da ita, su Jawad dukka uncle Abbas suka É—auko a kamani, shiyasa suke kama da Æ´aÆ´an King, saboda uncle Abbas da Akka yake kama haka shi ma King da Akka yake kama, sai suka cure waje guda kamar mahaifa É—aya.
A maimakon ta amsa gaisuwar tasa, sai ta jefo mashi tambaya kamar haka. "Menene a tsakaninka da Chuchu?".
A hanzarce ya É—ago da kallonsa izuwa kanta. ÆŠaure fuskar nan ta yi tamau kamar hadari, Allah dai yasa kyakkyawace ajin farko, badan haka ba yadda ta wani uban É—aure fuska nan ai da ba zata yi kyan ganuwa ba.
"Mammie akwai wadda ya ce maki akwai wani abin a tsakanina da Jannat ne?".
"Tambayarka nake yi ka bani amsa ba ka sake jefo mun wata tambaya ba".
Ta faÉ—a a dake, irin ita big star É—in nan, babu wasa.
Shiru ya É—an yi yana mamakin abin, shi da kansa wlh bai san me a tsakaninsa da ita ba, kawai tana burgesa ya sani, duk cikin Æ´aÆ´an King ita da auta ne suka fi burgesa, shiyasa in dai zasu haÉ—u sai ya É—aga idanu ya kallesu, bayan haka bai san wani abin ba kuma.
"Mammie Jannat is my sister, bayan haka kuma ni ban san wani abin ba, babu komai a tsakaninmu".
Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ta sauke wanda sai da ya bashi mamaki, to me matsalarta da Chuchu É—in da har zata damu kanta har haka dan ta gansu a tare? Ita Mammie É—in nan lamarinta akwai É—aure kai.
"Kana iya tafiya, amma kafin nan ka saurareni da kyau, naga kwana biyun nan kana yawan kasancewa tare da Chuchu, to bana da buƙatar hakan, bana son na sake ganinku a tare".
Da yake shi bai kawo komai a ransa ba, kuma bayan cewa Chuchu sistersa ce babu wani abin a ransa, sai ya amsa mata da okey kawai, sai dai abin ya ɗan bashi mamaki yadda ta ɗauki zafi a kan abin, sai ka ce Chuchu ɗin wata bare ce, kamar ba kanwarsu ba, kamar ba ɗiyar King ba, ai wannan ko kuyanga ce sai haka, lokaci guda ta wani ɗauki zafi daga ganinsu a tare, to wai ma ta ina ta gansu a tare har take zargin da wani abin a tsakanin nasu? Idan ma da wani abin kenan hanawa zata yi? Iko dai sai Allah, wannan lamari da ɗaure kai da ban mamaki, ga shi dai burinta ne su Sarina su auri ƴaƴan King, to shi Jawad kuma laifin me ya yi da ba'a yi mashi wannan fata?............🤔
Miƙewa ya yi ransa fes ya nufi waje bayan sun yi sallama, to dama shi me zai dame shi tun da a ganinsa dama babu wani abin a tsakaninsu? Ai shi normal ne, a ganinsa ko ta ce kada ya sake haɗuwa da Chuchu ma normal ne ba wata matsala.
Yana fita kai tsaye Company Jaish ya nufa, dan dama haka suke, wani lokaci sai su haÉ—e waje É—aya su yi zamansu a office suna hira.
Mammie kuwa yana fita ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da miƙewa ta haye saman bed ɗinta tana tunani, ko me take tunawa oho mata.
After some hours.
Da Gimbiya Sarina, Gimbiya Zunaira, Gimbiya Fanan da kuma Gimbiya Aneesa ne zaune a saman katafaren bed É—in Akka, wai sun zo duba kafar Gimbiya Chuchu, Akka ce nan ta gaya masu cewa kafar tata har yanzu yana ciwo bai warke ba, dama idan baku manta ba na gaya maku cewa sun fi yawan zama a part É—in Akka, so suna dawowa daga school suka shigo part É—in, a lokacin ita kuma Akka ta gama shiri zata nufi fada, dan ta je ta yi magana da King a kan su Yusuf, saboda a dokance za'a yanke masu hukuncin ba a familance ba, so dole sai a cikin fadar.
Sai hira auta da Gimbiya Chuchu suke yi, dama sun saba kamar wasu kawaye, Gimbiya Sarina tana latsa wayar Mammienta da ta shigo da shi, har yau Jawad bai bata wayarta ba, Fanan da Aneesa suna hira, dan suma suna shiri sosai.
"Aunty Chuchu kin ki ki gaya mana menene ya sameki a kafa ko?".
Cewar auta, ta yi maganar kamar zata yi kuka, sarkin son Æ´an uwanta kenan.
"Auta na gaya maki nima ban sani ba, da safe kawai na tashi naga kafar tawa tana ciwo, ba kema kin gani da safen ba?".
GyaÉ—a mata kai auta ta yi alamar e ta gani.
Zata sake yin magana Gimbiya Aneesa Æ´ar mama ta rigata da cewa. "Ba wani nan ki faÉ—i gaskiya, ba Yah Jawad bane ya baki punishment?".
Dama na gaya maku duk wani labari da kuke so ku tambayi Aneesa ta sani, ko daga ina ta jiyo wannan kuma oho mata dai, ahalin gidan nan lamarinsu sai su.
Shiru kaÉ—an Chuchu ta É—an yi kafin ta ce. "Haka ne, Yah Jawad ne ya saka kneel down, shi ne yasa kafafuna suke yi mun ciwo".
Zaro idanu waje Auta, Sarina and Fanan suka yi, basu yi zaton hakan ba, Sarina da Fanan sun É—auka su kawai Yah Jawad ya tsana yake horarwa idan sun yi laifi, to yau dai ga shi harda Gimbiya Chuchu ta hau layi, hakan yana nufin kowa daga cikin bai tsallake ya horar da shi ba.
"A gaskiya Yah Jawad mugu ne". Cewar Sarina, ta yi maganar tana kwaɓe fuska, dama basa shiri sam sam, bata sonsa dan yana takura mata.
"Wlh Aunty Sarina ni babu ruwana idan ya jiyoki, kema kin san sauran idan ya ji abin da kika ce mashi".
Cewar Fanan, tana magana tana zare ido, alamar tsoron Jawad É—in sosai take ji.
Wani irin kallon up and down Sarinar ta wurga mata kafin ta ce. "Ni narasa ma meyasa su Yah Jawad suka zauna a gidan nan, kowa ya koma nasa gidan mana, ko kuma su tafi Dubai wajensu mai ran karfe sun fi buƙatarsu mu bama da buƙatarsu".
Aneesa ce ta ce. "Zaki iya zuwa ki gaya masu su tafi su baki waje ai".
"Dake nake magana ne? Ko mi sa'ar wasarki ce". Ta faÉ—a cikin izza. Dama nagaya maku da Sarina da Aneesa basu zama inuwa guda, kamar wuta da audiga suke.
"Ba dani kike yi ba, amma kuma na baki amsa ko kina da abin yi ne? Ke har ma kin isa ki yi da ni?". Cewar Aneesar.
A fusace Sarinar ta buÉ—i baki zata yi magana sautin tafiya ya daki doduwan kunnuwansu, wadda ya sanyasu nutsuwa tsit, da alama sun san mai wannan tafiya, dan harta ita kanta Chuchu dake kwance É—an gefe da su sai da ta kara nutsuwa sosai, yadda kuka san waÉ—an da aka yi wa wahayin ganin mala'ikan mutuwa, duk suka wani yi tsit, Auta ce kawai bata canza daga yadda take ba.
Ƙasa kasa ya yi sallama kamar mai ciwon baki, yana sanye da wando three cuter a jikinsa, daga ta sama kuma polo shirt mai bala'in kyau, wandon ash color ce rigar kuma fara kal, ya yi kyau sosai, da alama bai jima da dawowa daga office ba.
Har suna rige rige wajen haÉ—a bakin cewa. "Good evening Yah Jaish".
Kallo É—aya ya yi masu ya kawar da kansa tare da tambayarsu ina Akka take ba tare da ya amsa gaisuwar tasu ba, yana magana kamar wadda bakinsa yake ciwo.
Tsabar tsoronsa da suke yi sun kasa iya bashi amsa, Auta ce kawai ta ce. "Yah Jaish Akka tana fada".
Bai sake yin magana ba ya miƙo mata hannunsa a kan ta zo su je ta raka shi. Da sauri ta sauƙo kasa daga saman bed ɗin ta nufesa, hannunta ya rike suka nufi waje, kowa a gidan bashi da ɗan rakiya biyun auta, ita ce mai raka kowa duk in da zai je a cikin gidan, babu ruwanta, ita fa kowa sonta yake yi, ita ma kuma tana son kowa abinta.
Suna fita daga part É—in suka ci karo da jarumi abin alfaharin KINGDOM OF POWER, wato HOORAIN yana tsaye shi da wani dakakken jarumin mayaki suna magana.
Cool murmushin nan nata mai kara fito mata da tsantsar kyanta tare da É—an dimples É—inta ta sakar mashi tare da cewa.
"Hoorain tun jiya ban sake ganinka ba".
Jaish yana jinsu bai yi magana ba, bai ma É—ago yaga Hoorain É—in ba, sai dai ya É—an ji babu daÉ—i a ransa da autar tasu ta cika sakewa kuyangun gidan har ma da mayaka fuska, ita kowa nata ne, baya son hakan sam, amma bai nuna ba, yana rike da hannunta suka cigaba da tafiya kawai.
Ƙasa da kai Hoorain ya yi, har wa yau yana cikin kayan yakinsa tare da wannan hula da ta hana a kalli face ɗinsa, sarai ya lura da Jaish bai so auta ta yi mashi magana ba, hakance ma tasa ya iya bakinsa bai amsa mata ba, sai dai ya bita da kallo ta ƙasan ido kawai, yarinyar tana burgesa yadda ta fito daban a cikin ƴan gidan, bata da girman kai ga girmama mutane.
Sai da suka ɗan wucesu ne wannan mayakin da suke a tare ya taɓa shoulder ɗin Hoorain ɗin tare da faɗin. "Kabi a hankali abokina".
Jinjina mashi kai Hoorain É—in ya yi tare da cewa. "Nagode manta kawai mu cigaba da maganar mu".
Ya yi maganar kamar dai yadda ya saba yinta cikin sanyin murya kuma ƙasa ƙasa kamar baya son yi.
Ita kuwa auta a duniya tana son ganin face É—in Hoorain, sai dai duk kuma lokacin da ta ce mashi ya cire wannan hula ta kallesa sai wani abin ya gifta a tsakaninsu ya hana shi cirewa, tana jin daÉ—in kasancewa da Hoorain É—in a matsayin mai bata tsaro sosai, saboda yadda yake kula da ita ya fi sauran mayakan da suke kula da su Gimbiya Chuchu.
ðŸ¤KADA KU MANTA WANNAN DADDAÆŠAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi ðŸ‘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥ðŸ¤
ðŸ¤ðŸ”¥ð—¥ð—”ð—ªð—”ð—¡ð—œð—¡ 👑 ð—ð—”ð—Ÿð—œð—¡ð—–ð—œðŸ”¥ðŸ¤
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
ð— ð—”ð—Ÿð—Ÿð—”ð—žð—œð—¡
â¤ï¸â€ðŸ”¥FATEEMA ZAHRA MUSA â¤ï¸â€ðŸ”¥
(â¤ï¸A-K-A ð‘·ð‘¹ð‘°ð‘µð‘ªð‘¬ð‘ºð‘º ð‘»ð‘¬ð‘¬ð‘´ð‘¨ðŸ”¥)
🔥ðŸ¤T🔥ðŸ¤T🔥ðŸ¤W🔥ðŸ¤......💻
â¤ï¸ð‘«ð‘¨ð‘»ð‘¬ 31/7/2024.....âœï¸ðŸ“šðŸŒ¹
For information 08161390581 Whatsapp me only!!.
ðŸ¤ð‘ºð‘»ð‘¬ð‘· 1......âœï¸ðŸ“šðŸ”¥
اللَّهÙمَّ صَلّ٠عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌ، اللَّهÙمَّ بَارÙكْ عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا بَارَكْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌâ¤ï¸
E____________25🔥
🕊ï¸ðŸ•Šï¸ðŸ•Šï¸ðŸ•Šï¸ðŸ•Šï¸ðŸ•Šï¸ðŸ•Šï¸ðŸ•Šï¸ðŸ•Šï¸ðŸ•Šï¸ðŸ•Šï¸ðŸ•Šï¸ðŸ•Šï¸ðŸ•Šï¸
A ɓangaren su Aneesa kuwa, kamar dai yadda suka saba ne, kullum in suka haɗu da Sarina waje guda matuƙar iyayensu basu a kusa to fa rabuwarsu bata daɗi, dan haka a wannan karon ma Yah Jaish yana fita suka dasa daga in da suka tsaye da surutan nasu, ko wacce sai shegen son girma da nuna isa da izza.
Fanan da ta lura zasu cika mata kunnuwa sai ta miƙe ta nufi waje abinta, dan ba zata iya ba, ba yau bane farau. Ita ma Gimbiya Chuchu gyara kwanciyarta ta yi tare da basu baya tana fuskantar headboard na gadon, dan ma kada su takura mata sosai sai ta janyo duvet ɗin Akka ta rufe har kanta tana sauke nannauyar ajiyar zuciya, abokiyar hirarta wato auta ta tafi, dama ita idan ba da auta ba bata cika yin hira da kowa ba, ɗan gara ma Fanan, wani lokaci suna hira sosai, amma Sarina da Aneesa wlh babu mai iya halinsu sai su, murɗaɗɗun mutane ne wanda ba zaka taɓa gane ina alkiblarsu take ba.
Duk kuma faɗar da zasu yi fa a iya baki ne kawai yake tsayawa, ko da sunan wasa basa daka hannu a jikin juna, ba wai kuma dan basu iya faɗar ba, ina ai su faɗa a jininsu ma take, kawai dai basu taɓa ko da gwadawa bane, dan sun san zasu daku dukar mutuwa ma kuwa a hannun Jaish in suka yi faɗa, ina ga bugun da zai yi masu ko ganga iyaka, hakan yasa sai suke tsayawa a iya surutan nasu kawai.
Yanzu haka suka yi surutun nasu tsab suka kammala ba tare da ɗaya ya taɓa koda alkyabbar jinin ɗaya ba. Aneesa ce ta fara miƙewa ta fice daga cikin ɗakin. Ita kuwa hjy Sarina sai ta gyara ta kwanta a saman bed ɗin tare da cigaba da taɓa wayar Mammie abinta.
Da daddare misalin karfe 9 kowa ya kammala cin abincin darensa, masu saurin yin barci ma har sun yi barci, wasu kuma suna shirin yin barci.
Akka tana part na uncle Abbas, dan tun da yamma ya ce kansa na yi mashi ciwo, kuma gobe yake son komawa, so Akka tana wajensa, ta je duba ciwon kan nasa.
Gimbiya Chuchu ce kawai kwance a saman bed ɗin Akkar, ita kuwa Gimbiya Zunaira tana wajen Mommarta yau, ta je ta wani haye mata saman bed tare da tada kai da cikyarta suna ta hira na tsakanin uwa da ƴa, kamar wasu ƙawaye, sai shafa lallausan bakin arab hairnta momma take yi, tana ta bata labarin ƴan uwata su uncle Rahab kenan da suke can Dubai.
Ita dai Momma har ga Allah tana wahala rayuwarta a wannan masarauta, shiyasa take yawan zuwa Dubai, ko da kuma ta gayawa mahaifinta ga abin da yake faruwa da ita, sai dai ya ce mata ta kara tsananta addu'a sosai, yau tsawon shekaru talatin kenan tana fama da wannan matsala, sai dai yana yin sauki, ya fi taso mata ne a duk lokacin da ta samu ciki, har ta haifi wannan ciki tana fama da wannan mahaukacin razanar da ita da ake yi, ba kalar halittar da bata gani, wani lokaci idan abin ya yi tsamari har suma take yi, sai an danganata da likitoci, amma kuma idan bata da ciki tana fin shekara biyu zuwa uku bata ga wani abin tsoro ba, sai jefi jefi.
Da yake tana tsananin kaunar gimbiya Zunaira sai aka fi yawan tsorata da fuskar Zunaira ɗin, da tsakar dare zata jiyo muryar autar tata tana ta faman kuka a cikin toilet, idan ta tashi ta je ta duba kuma sai ta ga yes fuskar Zunaira ɗin ce, amma kuma babu gangar jiki, sai jini dake zubo mata daga hancinta, bakinta izuwa wuyarta, wani lokaci idan ta taso daga kan gado da addu'ar tashi daga barci, sai bata tsorata zaka ji ta furta sunan Allah sai abin ya ɓace, amma duk ranar da ta manta bata tashi da addu'ar tashi daga barci ba to ba shakka tana mahaukacin razana har ta kurma ihu, kuma abin baya ɓacewa sai dai ya kara razanar da ita, baya rabuwa da ita har sai ta samu ta furta wata addu'a ko sunan Allah. Haka baiwar Allah take ta fama, ta kuma ƙasa iya gayawa King Zuhair ga abin da take fuskanta, mahaifinta kawai ta iya gayamawa, shi ma kuma da alama saboda babban malami ne sosai kuma sarki mai karfin iko ne yasa abubuwan basu iya rufe mata baki a kansa ba, ta iya gaya mashi. Ko mahaifiyarta bata iya gayawa ba.
Sai hira suke zubawa kamar wasu ƙawaye, a haka Jaish ya shigo ya samesu, sanye yake da kayan barci masu bala'i kyau da tsada, already ya nemi izinin shigowa ta hanyar turo mata massages a wayarta, saboda ko da ya zo parlourn bai sami su kuyanga Mama Haulat ba, sai kawai ya turo mata sako, ta kuma amsa mashi da ya shigo, shi ne yasa ya shigo.
Kasancewar suna a saman bed sai shi kuma ya zauna a saman bedside drawer kusa da lamp dake a kunne yana bada wuta light green.
"Good evening my Momma".
Ya faɗa yana sunkuyar da kansa ƙasa.
"Yah Jaish É—azun baka bani amsata ba". Cewar auta.
"Evening Jaish how was the night?". Cewar Momma.
Alhdulillah ya bata amsa kafin ya ce da auta. "Which amsa kenan?".
ÆŠan turo baki ta yi kafin ta ce. "About my journey to Dubai, ina son dawowa a tare da yaya Omar ne fa".
Shiru ya yi mata bai amsa ba, dan ya rigada ya yanke hukunci babu in da zata je, abin da next week Omar É—in zai dawo, dan haka ta jira shi a nan kawai.
Hannun Mommarsa da take ta faman shafa lallausan gashin auta ya riƙo cikin nasa, a hankali ya zura mata wani haɗaɗɗen dankareran diamond ring irin nata da ya cire mata ranar, dama idan baku manta ba ranar ya cire mata nata ring ɗin saboda ya yi mata kaɗan, to shi ne ya yi waya wa a powerful king of Dubai ya aiko mashi da wani irin wannan sak, wato kakansa kenan wanda ya haifi Momma ɗin kuma uncle ga King Zuhair kani ga Akka kenan, dama idan baku manta ba na gaya maku King Zuhair Momma ƴar uncle ɗinsa ce ya aura, aure dangi ne.
Sosai ta ji daɗin wannan ring ɗin, wani sanyi ne ya ratsa mata zuciya yadda ƴaƴanta suke nuna mata so, ya cire wancan da kasa ya kuma kawo mata mai ɗan girma ya saka mata, baban abin birgewa ma ko da ya sanya mata ring ɗin sai da ya ɗan sumbaci hannun nata da wannan ɗan ƙaramin bakin nasa, sannan ya ce.
"Momma ring bai taɓa burgeni ba before, but a hannunki is so very very beautiful da har na ji ina sha'awar sakawa ni ma, you're so special our Momma". Cikin nutsuwa tare da sanyin murya ya yi maganar.
Wani irin madarar daɗi ne ta ji ya kara lulluɓeta, yabo yana da daɗi, amma kuma irin yabon da Jaish yake yi mata ya fi na kowa daɗi. Shi kuma Jaish ɗin a duniya iya ita da King kaɗai ya iya yabawa, ko auta idan ta yi kwalliya suka haɗu ta tambayesa ta yi kyau, kai kawai yake gyaɗa mata, wani lokaci ko kallon kwalliyar tata ma baya yi, amma idan Mommarsa ce ya rinƙa yabon kyanta kenan koda bata yi kwalliya ba, ita da King kaɗai ya iya yabawa a duniyarsa, bayan su ko kansa bai iya yabo ba, yo shi da a duniya ma kwata kwata da mutane huɗu zuwa biyar yake iya buɗe baki ya bawa amsa, saura sai dai ya bisu da ido ko kuma ya gyaɗa masu kai, idan kun ji ya buɗe baki yana magana voice nasa na ɗan fita da sauti kaɗan ma to da Mommar ce ko King, su biyun nan yake yi wa magana har voice nasa ta ɗan fita, saboda baya son ya zamana ya yi masu magana basu ji ba sai sun sake wahalar da kansu wajen sake tambayarsa me ya ce? Baya son haka shiyasa yake ɗan buɗe murya idan zai yi masu magana, bai ɗauki iyayen nasa abin wasa ba, sune komai nasa, yana bala'in kaunarsu fiye da komai, da da hali ma ina ga har abinci zai rinƙa tauna masu dan kada su sha wahala.
"Yah Jaish baka yi magana ba". Cewar auta, ta yi maganar a shagwaɓe sosai.
"Baby I will think about it, ki bari zuwa gobe".
Ya bata amsa yana sakin hannun Mommar tasu.
"Allah ya yi maka albarka my son". Cewar Momma.
Da Amin ya amsa mata kafin ya sake cewa. "Momma zan iya tafiya ko kina buƙatar wani abin?".
Girgiza mashi kai ta yi alamar bata buƙatar komai zai iya tafiya.
Miƙewa tsaye ya yi tare da kai hannunsa ya shafi lallausan kumatun auta da ta tsare shi da idanu.
"Sarkin kallon mutane ayi addu'ar barci kafin a kwanta".
Ya faÉ—a haÉ—e da É—an jan karan dogon hancinta.
Wani irin cool murmushi ta sakar mashi har sai da dimples É—inta suka lotsa, wani irin sihirtacen kyau ne ya kara bayyana a saman face É—in nata, dama ita fa ba baya ba wajen kyau, wlh ta fi su Jaish É—in dukka kyau, yadda kuka san duk an haÉ—e mata kyansu ne aka cure waje guda aka bata, idan ka gansu dai dukka zaka san cewa Æ´aÆ´an Momma ce saboda jini ba wasa ba, amma dai ta fisu kyau har twins Obaid and Omaid, Yah Omar dukka, ita ce tauraruwarsu.
ÆŠan yatsarsa karami ya É—an saka mata a ramin da dimples É—in nata suka lotsa, ya É—an danna wajen kafin ya ce. "Naki ya fi na kowa kyau a gidan, kin yi mana wayo".
Ya yi maganar kasa kasa tare da ɗauke hannunsa daga saman face ɗin tata. Sai binsu da kallo Momma take yi, gwanin ban sha'awa abin, akwai soyayya da kauna mai karfi a tsakaninsu. Daga King har Momma dukka suna da dimples, hakan yasa gabaɗaya ƴaƴan Momma suke da shi, ita ma Gimbiya Chuchu tana da shi, amma Gimbiya Aneesa ƴar Mama bata da shi, uncle Abbas yana da shi, amma su Sarina duk basu da shi, Akka ce tushen dimple ɗin nasu, duk da ta tsufa idan tana magana zaka gansa a face nata ɓaro ɓaro.
Hannunsa auta ta kama ta ɗan sumbata kafin ta ce. "Take care Yah Jaish, kaima kada ka manta ka yi addu'a, nima kuma zan yi, Momma zata kara yi mun kona yi barci, kuma nasan daddy ma sai ya zo ya yi mun, dan baya taɓa yin barci ba tare da ya zo ya yi mun addu'a ba, ina fa samun addu'oi sosai".
Nufar kofar fita ya yi yana tafiya a nutse, sai da ya kai tsakiyar É—akin ya kusa bakin door É—in ya ce. "Ni ma baki san ina dawowa na yi maki addu'a bako? Ai ke Æ´ar gata ce, bana jin a gidan nan akwai wanda baya yi maki addu'a".
Ya kai karshen maganar dai'dai lokacin da ya fice daga ɗakin, bai jira amsarta ba, dan baya buƙatar ji, idan ya biye mata zasu iya kwana a wajen, auta bata gajiya da magana.
"Mommana dama Yah Jaish yana dawowa ya yi mun addu'a idan na yi barci?".
GyaÉ—a mata kai ta yi alamar e tare da faÉ—in. "Harda Yah Jawad duk suna zuwa bedroom naki su yi maki addu'a, amma idan a nan kika kwana basu zuwa, dan basu son takura mun suka ce".
Shiru ta ɗan yi kafin kuma ta ɗan shagwaɓe fuska tare da faɗin. "Allah sarki suna sona sosai".
Yadda ta yi maganar sai da ta sanya Momma sakin murmushi, wai Allah sarki suna sonta sosai, ashe ma ita bata san cewa ita ɗin kamar bugun zuciyarsu take ba, bata san cewa sun fi sonta fiye da kansu ba, saboda kyawawan halayenta irin na King yasa take da mugun shiga rai, harta Mama da take bata shiri da Momma tana kaunar Zunaira, wannan suna na Zunaira ma Mamar ce ta zaɓa mata a lokacin da aka haifeta, yarinyar ce dole ta shiga ran mutun, saboda yadda take bata ɗauki duniya a bakin komai ba, bata ɗauki abubuwa da zafi ba, komai nata very calmly and softly conduct.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.