Complete Hausa Novels

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Rawanin_Zalinci_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 11 of 24

Cigaba da hira ita da Mommarta suka yi har izuwa lokacin yin barci, dama already tana shirye cikin kayan barcinta masu bala'in kyau da tsada, riga da wando launin maroon color. Barci ne ya É—auketa kwance a saman laps É—in mommar tata, fuskarta É—auke da annuri tare da murmushi mai kara mata kyau ko da tana barci.

Shiru Momma ta yi tana karewa face É—in nata kallo kamar mai tunanin wani abin. Ta É—auki a kallah tsawon mintuna 10 a haka tana kallon fuskar Æ´ar tata ba tare da kyafta idanu ba. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin nan cikin dabara ta sauketa daga saman laps É—inta tare da sanya mata pillow, sannan ta sauko kasa daga saman bed É—in, dan ta je ta yi wanka ta yi shirin kwanciya.

Bata kai ga shiga toilet ɗin ba sallamar King kasa kasa ya daki dodon kunnuwanta, ya biyo sahun ƴarsa, ya je bedroom ɗinta bata nan, ya leƙa na Chuchu bata can, babu kowa ma a ciki, dan Chuchu ɗin ma tana wajen Akka, hakan yasa ya nufo nan kai tsaye kawai, ba zai iya yin barci ba idan bai yi wa Zunaira addu'a ya shafa mata ya kuma tabbatar tana cikin aminci ba.

Sanye yake da arab jallabiya fara tas a jikinsa, ga arab hairn nan nasa a kwance luf har gaban goshinsa, King ba dai kyau ba, kyakkyawan balarabe ne ajin farko, ga wani bakinkirin ɗin saje mai bala'in laushi da kyau kwance luf a gefe da gefen face ɗinsa, kyakkyawar gemun nan nasa ta sha gyara, sai sheki take yi sosai, ga wani haɗaɗɗen gashi da ya kewayo ɗan red bakinsa, ba ƙaramin kyau ya kara mashi ba, farar fata da bakar gashi ku kunsa dole ya ɗauki ido, ga kuma dara daran idanu masha Allah, gashin gerarsa har kamar zasu haɗu da juna saboda cika, suna kwance luff suma kamar an zana mashi su, sai sheki suke yi........ (Har na ji zan iya yi wa Momma kwace🥱🌝 sai dai ina tsoron commander ZAFAR😥)

Tsare Momma da waɗan nan dara daran idanun nasa ya yi yana kare mata kallo tare da harɗe hannayensa a saman wannan Lion chest ɗin nasa, King fa ansha fama a fagen yaki a lokacin da mahaifinsa King ABDUL MALIK yake raye yake kuma rike da karagar mulki, idan baku manta ba na gaya maku ya taɓa rike commander mayakansu a lokacin, so har yanzu a buɗe yake kamar yana mai cigaba da karɓar horon yakin.

"Barka da shigowa ranka ya daÉ—e". Momma ta faÉ—a cikin girmamawa, sai kallon juna suke yi, ita bata cire idanunta daga kansa ba, shi kuwa dama kunsan ba kawarwa zai yi ba.

(Ni kam na ce mada dai a manta auta tana ɗakin😌🌝)

Shiru suka kurawa juna idanu na a kallah mintoci uku kafin kuma a tare su sakarwa da juna cool murmushi kamar abin haÉ—in baki.

"Ka fara ko?". Momma ta faÉ—a tare da sa kai zata wuce cikin toilet abinta.

"In dai zan shigo ki cigaba da yi mun irin wannan tarba to ba zan canza hali ba".
Ya faÉ—a tare da nufar saman bed É—in nata wajen Zunaira kenan yana cigaba da sakin murmushi kamar ba King sarkin zafin rai da iya tsare gida a fada ba.

"Shi ne baki rufe mun sanyin idaniya ta da duv ba ko? Kika barta sanyin Ac na ratsa mun ita sai ta yi mura ko? Zan rama mata".
Ya kai karshen maganar tare da hayewa saman bed É—in, a kusa da ita ya zauna tare da fara tofa mata addu'a kamar yadda ya saba.

Ita kuma Momma ta shige cikin toilet, dan in ta biye mashi tsab zasu iya kwana a tsaye suna yi, su É—in Æ´aÆ´an kawu da gwaggo ne, Akka gwaggon Momma ce, akwai wasa sosai a tsakaninsu, abokan wasa ne, hakan yasa wani lokaci King É—in yake tsokanarta sosai da sosai kamar wasu yara, tun kafin su yi aure haka suke, har izuwa yanzu kuma basu canza ba, abin gwanin birgewa, ban sha'awa da kuma É—aukar hankali tare da É—aukar darasi.

Ya ɗauki a kallah good 10 mins yana zubawa sanyin idaniyar tasa addu'oi kafin ya shafa mata, sannan ya janyo duv ya lulluɓeta bayan ya manna mata kiss a saman 4 ahead ɗinta, yana ji da ita sosai, ya ce ita ce ke kama da shi a dukka cikin ƴaƴansa, King akwai neman magana, kawai dan yasa Momma yin magana ne yasa yake cewa Zunaira ce mai kama da shi, dan yasan sai ta yi magana, saboda da ita Zunaira take kama ba shi ba, duk da cewa ita da shi ɗin ma suna kama kamar ba mata da miji ba, idan ka gansu sai ka zaci wa da kanwa ne, saboda jini guda ne dama.

Bayan ya kammala tofa mata addu'a saukowa ƙasa ya yi tare da nufar door ɗin fita, dama abin da ya kawosa kenan, kuma ya gama, Momma zata same shi a part ɗinsa, dan yau dama kwananta ne.

A ɓangaren Gimbiya Chuchu kuwa, barci ne mai nauyi ya ɗauketa tun bayan cin abinci da suka yi, ko wankan dare bata samu ta yi ba, da yamma ma da kyar ta iya yin wanka, sai da Gimbiya Fanan ta taimaka mata, tana sanye da doguwar riga mai ɗan nauyi a jikinta da haka barcin ya kwasheta, ita kaɗai ce a bedroom ɗin, idan baku manta ba na gaya maku Akka tana part ɗin uncle Abbas.

Ƙasa ƙasa Yah Jawad ya yi sallama ya shigo cikin bedroom ɗin, hannunsa na rike da waɗan can kwalaben magunguna daya karɓo daga hannun waɗan can nurses ɗin.

Tun ɗazun yake ta jiranta ta zo ya bata ta shafa a kafafun nata amma shiru bata zo ba, shi ne ya biyo sahu, dama idan baku manta ba ya ce ta same shi a part ɗinsa, baiwar Allah barci ɓarawo yasa ta manta gabaɗaya.

A saman bedside drawer ta kusa da ita ya zauna tare da É—aura wayarsa a saman gefen bed É—in ta kusa da ita, da waya guda É—aya ya fito, ya baro É—ayar ta jama'a a É—aki, dama ya fi yawan fita da ta family, dan kada ya yi missing call É—in kowa daga cikin Æ´an uwansa.

Hannu ya sanya ya yaye duv da take lulluɓe da shi, sai sharara barci take yi kamar babu gobe, ta ɗan ƙudundune hannayenta a saman kirjinta. Face ɗinta ya ɗan ƙurawa idanu na ƴan sakani kamar mai nazarin wani abin. Can kuma sai ya gangarar da hannunsa ƙasa ya ɗan ɗage mata dogowar rigar jikin nata izuwa santala santalan cinyoyinta.

Sai da gabansa ya yi wani irin mummunar faɗuwa, na ganin kyakkyawar farar fatan tsala tsalan cinyoyin nata da suke luwai luwai suna sheki, sai ji ya yi kamar Akka zata zo ta same shi, idan kuma ta same shi a haka to ya shiga talatin, sai ta addaba mashi da surutun ko dai yana son Chuchu ne? Ba zata barshi ya zauna lafiya ba, wannan tsohuwa akwai baki, so shi surutun ne baya da buƙata, dan haka sai jikinsa ya fara ɗari ɗari, ya ji kamar kada ya shafa mata ganin ya barshi kawai.

Amma kuma ina ba zai iya ba, ba zai iya barinshi É—in ba, saboda abin da ya fito da shi kenan, ya kasa iya rintsawa ne, har ya yi shirin kwanciya ya kwanta, sai kuma ya kasa iya rintsawa, saboda yana tunanin in dai bai kula da ita ta samu lafiya ba to bai kyauta ba gaskiya, dan koma me shi ne silar jin wannan ciwo tata, so yana da kyau ya kula da ita ta samu lafiya, hakan yasa ya kasa rintsawa har sai da ya fito.

Mayukan ya buɗe tare da fara ɗebowa da nufin ya fara shafa mata, abin mamaki hannayen nasa ne suka fara kerma, ji yake yi kamar ba zai iya shafa mata ɗin ba, da mamaki yake kallon hannun nasa yadda yake kerma kamar wadda akacewa ya taɓa wuta.

Ajiye kwalbar maganin da yake a ɗayan hannunsa ya yi, ya kai hannun ya ɗan shafa lallausan arab hairnsa tare da furta why? A hankali. Nisawa ya ɗan yi kafin ya yi ta maza ya ƙarisa kai hannunsa ya shafa mata. A hanzarce kamar mara gaskiya ya yi sauri ya shasshafa mata sama sama, duk gudun kada Akka ta zo ta kama shi ta janyo mashi jangwangwan ga kuma tsikar jikinsa dake ta faman tashi na taɓata da yake yi.

Ganin Chuchun ta fara ɗan motsawa kamar tana son farkawa ne yasa ya yi saurin miƙewa ya ɗauki wayarsa tare da nufar door ɗin fita ba tare da ya ɗauki ragowar magungunar ba. Har ya kai tsakiyar ɗakin kuma ko me ya tuna ya yi saurin juyowa ya dawo, a hanzarce hannunsa na kerma ya sauke mata rigarta ya mayar mata da shi dai'dai tare da janyo duv ɗin ya rufeta, da sauri ya nufi door ya fice, sai motsawa Chuchun take yi tana son farkawa daga barci.

🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️🕊️

UAE💘

AAJ PRISON💔😥

After two dys. Zaune yau ma Leesharh take a saman bakin bed ɗinta, ta buga uban tagumi kamar dai ranar, ta yi shiru, da alama bata a tare da mutane, ta luluƙa duniyar tunani, kamar ko da yaushe suna cikin uniform na AAJ ɗin, kala biyu ne uniform ɗin nasu, akwai fari kuma akwai blue, yau su canza wannan gobe su canza wannan.

Jasrah ce ta shigo É—akin cikin shigar fararen uniform É—inta ta sameta. A kusa da ita ta zo ta zauna tana mai faÉ—in. "Queen of thinking, yau kuma waye kika tuna a cikin familyn naku?".

Sam sam babu alamar murmushi ko mai ƙanƙantarsa a saman fuskar Leesharh, da alama yarinya ce da since before bata dariya, saboda bata ma yi kama da wadda take ko yaƙe bane, duk abin da za'ayi na dari wlh bata taɓa yi, Jasrah ta taɓa ɗaukar 30 mins tana surutan banza duk dan ta sanyata ko da murmushi ne, amma ina ko yaƙe ta kasa sakata, a tsawon shekara ɗaya na zaman da ta yi a gidan AAJ wlh sai dai suga hakwaranta idan tana magana ko tana yin brush, amma ba dai dariya ba, sam walwala da farinciki baya a saman fuskar yarinyar na, kullum cikin kuncin zuciya take, daga tagumi sai kwanciyar rigingine, abinci ma wani lokaci sau ɗaya take ci a rana, na safe kawai, bata wani damuwa da cin abinci, sai yawan tunani kamar me.

Ita kuwa Jasrah ta ce tun da nan da shekara guda za'a kasheta kamar yadda doka ta yanke mata, gara mata ta ci abincinta ta yi duk abinda tasan zata yi, dan tasan dokar nan ba zai kau daga kanta ba, sai dai wani ikon Allah, amma babu wanda ya isa ya sanya a fasa kasheta, kisa ba fashi, so dan haka gara mata ma ta saki ranta ta samu ta yi bankwana da duniya da kyau da kyau.

Ita kam Leesharh saura mata shekaru uku ta kai munzalin É—aukar hukuncin da aka yanke mata........ Hmmmmm ni ko na ce hmmmmm.

"Ni kam a duniya waye nake da shi da zan yi tunaninsa da ya wuce mamata?". Leesharh ta bata amsa tana mai dawo da kallonta a kanta su fuskanci juna kenan.

"To amma Leesharh where's your father? And you Said you're from Africa, so what brought you here Dubai?". Jasrah ta jefa mata tambaya.

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, tana ƙoƙarin yin magana Aaradiya dake kwance a saman bed ɗinta ta rigata da cewa. "Shima baban naki kashe shi kika yi ko? Dan naga ke horuwa ce, tun da kika zo gidan nan ko hakwaranki ba'a gani a waje, ke anya ma ba mayya ba ce Leesharh? Dan naga duk gidan kin fi kowa manya manyan idanu kamar ball".
Cike da shakiyanci da isgilanci sosai Aaradiya ta yi maganar.

ÆŠayar yarinyar da take kasan bed É—in Aaradiyar ce mai suna Sarah ta ce. "Kuma fa Aaradiya kina da gaskiya, kila mayya ce, ta kashe babanta, yanzu kuma ta kashe mamanta, muma fa kada ta kashe mu".
Ta kai karshen maganar tana zaro idanu.

A ɗan fusace Jasrah ta ce. "Ko ta kashe ku ko bata kashe ku ba nan da lokaci ƙalilan kasheku za'ayi, kuma idan ma ta kashe ku a yanzu ai saukaka maku zata yi".
Jasrah damo sarkin hakuri, bata magana a kan kome za'ayi mata, amma bata son taga irin cin fuskar da suke yi wa Leesharh a gidan, dan ita ce kawai aka kawo wadda ta kashe mahaifiyarta da hannunta, hakan yasa yaran da kansu suke tsangwamanta, yara ma kenan sun san daÉ—in uwa bare kuma manya, shiyasa sam sam Leesharh bata fita waje, dan idan ta fita kowace yarinya da kalar zagin da take yi mata, Æ´an manyan cikinsu ma sai ku ji suna cewa Allah ya tsine maki la'ananniya, la'ananniya ce kawai zata kashe uwar da ta yi silar zuwanta duniya.

Wannan dalilin yasa bata fita, ta gwammaci ta yi ta ƙunsuwa a cikin ɗaki kamar daddawa, yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa kullum take cikin ƙuncin zuciya da ɓacin rai tare da tunani. Ga shi kuma taki buɗe baki ta gayawa kowa ya aka yi ta kashe mahaifiyarta da kanta, ko da jami'ai suka tambayeta ma iya e kawai ta amsa masu da shi, anyi anyi ta yi magana ta bada labarin yadda aka yi, amma ina taki yarda ta buɗe baki.

"Ai munsan zaku iya kashe mu ba sai kin gaya mana ba, ke da kika kashe Ameer bai yi maki komai ba".
Cewar Sarah kenan.

Shiru Jasrah ta yi bata sake bi ta kansu ba, dan in ta biye masu faÉ—a zasu yi sosai, kuma dukkansu zata girme masu da shekara guda, amma saboda su basu da kirki sun rainata, sun mayar da ita kamar wata kanwarsu suna yi mata cin kashi.

"Leesharh amsa me where's your dad?". Cewar Jasrah.

Nisawa Leesharh ta yi tare da ƙoƙarin fara yin magana kenan wata ganduroba mace ta shigo cikin ɗakin nasu bakinta a ɗauke da siririn sallama, tana sanye cikin uniform ɗinsu na aiki.

"Who's Leesharh?".
Shi ne abin da ta faÉ—a tana mai binsu da kallo.

Miƙewa tsaye Leesharh ɗin ta yi tana faɗin gata nan.

Wucewa matar ta yi ta fita tare da cewa. "Follow me".

Da sauri Jasrah ta miƙe tana faɗin. "Ina zaku kaita?".

Abin da kun rigada kun sani ne ba amsa mata zasu yi ba, dan ba sha'aninta bane su ɗin, dan haka sai ta yi wucewarta ba tare da ta sake juyowa ta kallesu bama. Leesharh kuwa bata da zaɓin da ya wuce ta bi bayan matar.

Komawa Jasrah ta yi ta zauna tare da buga uban tagumi tana tunanin to me zasu yi wa Leesharh da suka wani zo suka kirata? Ko dai wani nata ne ya kawo mata ziraya? Ko kuma wani aikin zasu sakata? Ka dai za'a canza mata É—aki a rabasu ne?. Tunani dai kala kala take ta yi a wajen.

Da kallon banza Sahra and Aaradiya suka bita da shi tare da binsu da addu'ar Allah yasa a kashe Leesharh É—in ma a yau kowa ya huta, yadda kuka san a kansu Leesharh É—in nan take zaune, sam basu kaunarta.

Kai tsaye office na shugaban gandurobobi wannan mata ta wuce da Leesharh dake ta faman jan kafa kamar zata faɗi a ƙasa, sam babu kuzari a jikinta, da alama bata ci abincin rana ba yau ma, dik a galabaice take baiwar Allah. Da alama a baya Leesharh tana da ɗan ƙiba kaɗan, saboda yanayin shape ɗin jikinta ya nuna rama ta yi, da ta fi hakan cikar bom bom and hips.

Shugaban gandurobobin tana a zaune a saman kujararta, ta yi crossing na leg's ɗinta, sanyin Ac na dukanta, office ɗin nata ya kawatu iya ƙawatuwa, tana sanye cikin haɗaɗen jallabiyarta launin sky blue a jikinta, yau bata sanya uniform ba, ta sanya wani ɗan ƙaramin please call me hijab da bai wuce kirjinta ba, ƴar siririya da ita, bata da ƙiba ko kaɗan, amma akwai kyau sosai da sosai, balarabiya ce ta usli, ga manya manyan idanu farare tas. Sai uban tulin takardu a gabanta kamar wata mai MD na Company, idanunta sanye suke da wani haɗaɗɗen farin glass mai ɗan girma, sai kamshi take zubawa ita kanta, ga kuma kamshin da office ɗin yake zubawa shi ma.

Wata macece zaune a zaman kujerar zaman baki idan suka zo a cikin office ɗin, daga sama har ƙasa idan ka cire nikaf da yake a fuskarta sanye wannan mata take da fararen kaya, nikaf ɗinta ne kawai baki, amma komai da ta sanya a jikinta fari ne tas, harta luxury hand fashion bag ɗinta ma fari ne, ta yi rolling na veil a kanta, ƴar dai'dai da ita, ba zaka kirata da mai ƙiba ba, haka zalika ba zaka kirata da siririya ba, ta dai ci ta ƙoshi, babu yunwa a tattare da ita, da alama kuma daloli bama nerori ba daloli sun yi mata mugun jiƙo, dan babu alamar gurbin talauci a tattare da ita, diamond ring da yake ɗan ƙaramin yatsan hannunta ma kawai ya haura 10 million, idanunta suna a sanye da black glass kamar wata mara gaskiya, ga nikaf ga kuma glass.

A ƙasa saman carpet Leesharh ta zo ta zauna a gaban ogar tasu, ita kuma wancan gandurobar da ta je ta zo da ita juyawa ta yi ta fita bayan ta isar da saƙon ga Leesharh nan ta kawota.

Cikin girmamawa da muryarta da sam kwata kwata bata fita sosai kamar wata mai koyon magana Leesharh ta ce. "Ganin nan".
Cikin harshen larabci ta yi maganar.

Kallon wannan mata dake zaune a saman kujara ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya shugaban gandurobobin ta yi, da hannu ta nunawa Leesharh wannan mata tana faɗin. "Bani ne nake kiranki ba, ga mai buƙatarki nan".

A hanzarce Leesharh ta juyo da waÉ—an nan dara daran idanun nata a kan matar, tun shigowarta bata kalli matar ba sai yanzu da aka nuna mata ita, hankalinta na'a kan shugaban gandurobobin ne kawai baiwar Allah.

Cikin girmamawa ta sake ce da wannan mata gani nan Aunty.

Kallon shugaban gandurobobin wannan matar ta yi, ɗan guntun numfashi ta ja tare da saukewa a hankali kafin ta ɗan ja ƴan mintoci da a kallah zasu kai biyu ba tare da ta ce komai ba, sannan calmly ta fara magana cikin kwararriyar laraɓcinta da zazzaƙar muryarta mai daɗin sauraro.

"Bismillah Abida kina iya bamu waje a yanzu".
Ta faÉ—a cikin sanyin murya, sai dai da alama akwai isa sosai da ji da kai a tattare da muryar tata.

Miƙewa shugaban gandurobobin ta yi ba tare da ta sake cewa komai ba, ta nufi out door, sai dai da alama ranta bai so fitar ba, kawai an fi karfin ta ne.

Bayan fitarta da kamar minti biyar haka, suna zaune shiru, wannan mata sai karewa Leesharh kallo take yi ta cikin black glass ɗinta, ita kuma Leesharh ta sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da hannunta. Tana son ta ɗago kai ta saci kallon wannan mata, amma kuma tana tsoron su haɗa ido ko kuma ta ganta, hakan yasa ta sunkuyar da kan nata shiru kawai.

"Shin kina son fita daga cikin wannan bakin gida da zuwansa ba alkhari bane Leesharh?".
Ta tambayeta cike da fargabar amsar da zata bata, tana tsoron Leesharh ɗin ta ce bata sha'awar fita daga gidan, hakan zai sa buƙatarta ba zai biya ba......... Ko wani buƙata take da shi a kan Leesharh? Muje dai zuwa.🤔😥

Tamkar saukar aradu haka Leesharh ta ji sautin zazzaƙar voice ɗin wannan mata ya daki dodon kunnuwanta.

A wani irin hanzarce ta fara gyaÉ—a mata kai in doubling. Baiwar Allah da alama bata da wani burin da ya wuce ta fita daga cikin wannan gida na AAJ........ Ba dolema ta so fita ba ko dan yadda sauran yaran suke tsangwamanta suka takura mata.

Wani irin cool ajiyar zuciya wannan mata ta sauke, ta cikin nikaf ɗinta ta saki wani irin shu'umin murmushi wadda fassara shi zai yi matukar wahala, da alama haƙarta zai cinma ruwa.

"Very good Leesharh, na ji matuƙar daɗi da ya kasance kina son fita daga cikin wannan gida".
Ta faɗa muryarta cike da tsantsar farinciki saɓanin ɗazun da magana kawai take yi babu walwala a tattare da ita.

"Aunty ina son na fita daga nan sosai, ko dan saboda tsangwamanta da suke yi suna kyarata, ga zagina da suke yi, kuma bana son a kasheni a nan, ina son na koma kasarmu, ina son na je wajen kabarin mamata na ganta".
Ta yi maganar idanunta suna cikowa tab da kwallah, muryar Leesharh sam baya fita sosai idan zata yi magana, yadda kuka san harshenta a naɗe yake, kamar mai koyan magana, gata kyakkyawa ajin farko, amma sam bata iya yin magana ya fita, a wani daddame maganar tata yake fita, idan ba ka nutsar da hankalinka sosai ba ba zaka taɓa iya gane me take son cewa ba ko me ta ce ba.

Shiru wannan mata ta ɗan yi tana ƙoƙarin iya fahimtar me Leesharh ta faɗa, dan bata wani gane me ta ce ba bayan cewa da ta yi mamanta, iya kalmar maman kawai ta iya ji a cikin maganar nata. Da kyar ta iya fahimtar wasu daga cikin abin da Leesharh ɗin ta ce, ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce.

"Idan kina so yau ba sai gobe ba zan fitar dake daga cikin wannan gidan, kuma zan kai ki asibiti a gyara maki voice ɗinki, zan ƴantaki ki zama mai gata, zaki zama ƴa kamar kowa, zaki samu farinciki da jin daɗi fiye da ƴaƴan shugaban ƙasa, zaki samu rayuwa mai cike da jin daɗi, zaki ci abinci mai rai da lafiya a kullum da ko yaushe kike da buƙata, zaki kwanta a ɗaki mai Ac, zaki kwanta a katafaren bed ɗin da nasan da idanunki ma baki taɓa ganin gado irinsa ba, zaki saka suturuna na alfarma wadda ƴaƴan manya suke sakawa, ke har da gida da mota zan iya saya maki mai kyau da tsada, idan kina son yin karatu ma zaki yi, kome kike so zan yi maki amma da sharaɗi, kin amince?".

A wannan karon a hanzarce Leesharh ta É—ago da kanta, jiki na kerma ta fara gyaÉ—a mata kai alamar ta yarda ta amince tun ma bata ji wani irin sharaÉ—i bane, ita dai burinta ma kawai ta bar wannan gida, ko bara zata yi a bakin titi in dai zata bar wannan gida to zata amince da koma wani irin sharaÉ—i za'a sanya mata, bata damu da sai wannan mata ta bata dukka wannan daula da ta lissafa mata ba, ita dai ta fita daga gidan nan kawai.

"Good girl, wani aiki zaki yi mun, ba aiki bane mai wahala, kuma ba jimawa zaki yi kina yin aikin ba, da zarar kin yi mun shi dai'dai shikenan angama zaki sami duk waÉ—an nan abubuwa dana kirga, kina amincewa ko yanzu ne zaki bar wannan gida ba tare da kin kara one mins ba, amincewarki ne kawai yanzu zai fitar dake a yau É—in nan". With full confidence matar ta yi maganar.

Shiru Leesharh ta É—an yi, kamar zata ce wani abin, sai kuma bata yi wani tunani ba ba kuma ta ji wani irin aiki bane, idanunta ya rufe da son fita daga AAJ, hakan yasa ta gyaÉ—a kai alamar ta amince zata yi wannan aiki da bata san menene bane.

"Kin amince zaki yi mun wannan aiki?". Matar ta tambaya muryarta cike tab da tsantsar farinciki mai nuna alamun ta jima bata shiga farinciki irin haka ba, ga tsantsar ƙaguwa a voice ɗin nata.

Ƙara gyaɗa mata kai Leesharh ta yi alamar yes ta yarda ta amin zata yi wannan aiki da bata ji ko menene ba.

"Kin san wani irin aiki zaki yi mun ne? Bashi da wata wahala fa".
Matar ta sake faÉ—a cike da murna da farinciki.

Girgiza kai Leesharh ta yi alamar bata san wani aiki bane.

"Ba wani aiki mai wahala bane, so nake.............

Ko masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu, amma ku wani aiki kuke ganin wannan mata zata sanya Leesharh da har ta yi mata alƙawarin maƙudan dunbin dukiya har haka?🤔 Anya wannan mata akwai alkhari a tattare da ita kuwa?🤔 Ga shi dai ta rufe ko'ina nata ba'a iya ganin wacece!🤔 To dai shikenan su kuma nasu wasan yanzu zai fara kenan, 🥱 na yi ta nan.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 1/8/2024.....✍️📚🌹

For information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________26🔥

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼

"Ba wani aiki mai wahala bane, so nake kawai ki shiga jikin wani, ina son ki shiga jikinsa ta yadda duk wani abin da yake yi zan samu labari, na sha wahala sosai kafin na samu yarinya irinki wadda take da duk wasu qualities da nake da buƙata wanda kuma nake ganin zai iya jefa Ramish a cikin tarkonmu".

ÆŠan dakatawa da yin magana ta yi cike da fargabar kada Leesharh É—in ta ce ba zata iya yin wannan aiki ba, ta kafeta da idanu ta cikin glass É—inta tana karewa fuskarta kallo tare da karantar yanayin ta, bata san ya zata yi ba idan Leesharh É—in ta ce ba zata iya yin wannan aiki ba.

Cike da kirsa tare da ƙoƙarin yin amfani da ƙarancin shekarun na Leesharh ɗin ta cigaba da yin magana kamar haka.

"Na san da cewa baki jin daÉ—in zaman wannan gida, na san da cewa kina cikin kunci da takura, na san da cewa kina cikin wahala, na san da cewa baki da burin da ya wuce ki fita daga cikin wannan gida, to dukka wannan zai faru ne kawai idan kika amince da tayi na, bafa cutar da kowa zaki yi ba"

Sake dakatawa da yin maganar ta yi tana jan numfashi tare da kara kurawa face É—in Leesharh idanu.

Ni kuwa nace babu rami me ya kawo maganar rami? Me ya kawo zance ba cutar da kowa zata yi ba?......🤔 Anya wannan mata ta kulla gaskiya kuwa? Anya ba so take ta kai Leesharh ta barota ba? To wai waye ma shi Ramish ɗin? Kuma meyasa take son a yi mata leƙen asiri a kansa? Me suke nema daga garesa?.

"Leesharh zaki samu jin daɗin rayuwa sosai da sosai, zaki samu farinciki fiye da tunaninki, zaki sami kuɗi ki taimaki duk wanda kike so, just kawai amsa me with your full confidence that zaki iya, nasan cewa zaki iya shiyasa na zo wajenki, ban zo nan ba sai da na binciki tarihin rayuwarki, and ke ƙaramar yarinya ce, babu wanda zai yi tunanin ga abin da kika je yi a gidan, taimako fa zaki yi, wasu ne suke son cutar da shi mu kuma zamu bashi kariya ta hanyar sanin duk wani motsinsa, ta hakance kawai zamu taimakesa, kinga kema kin taimaka mashi kenan".

Cike da kwarewa a iya juyar da tunanin mutun ta yi maganar, sai dai fa tana magana ne tana fargabar amsar da Leesharh zata bata, domin ta gama saka duk wani hope ɗinta tun kafin ta zo a kan cewa lallai Leesharh zata yi mata abin da take so, amfani zata yi da karantar shekarun Leesharh, dan tasan ƙaramar yarinya kamar Leesharh babu wanda zai yi tunanin leƙen asiri ta je yi, da alama wutar ɗaukar fansa ne yake ruruwa a cikin zuciyarta, shi ne kuma take son ta yi amfani da Leesharh domin cikar burinta. Hmmmm akwai babban yaki da cakwakiya kuwa a gaba, ga shi ko face nata bata bari an sani ba, wato idan ma an kama Leesharh ita kaɗai ayi mata duk hukuncin da za'ayi mata, wannan mata bata kullah gaskiya ba, akwai babban wasa a wannan waje.

"Leesharh say something now, shin kin amince?".

Shiru ta ɗan yi kafin ta ɗago da idanunta da suke cike taf da kwallah, muryarta na rawa, da alamar tsoro sosai a saman face ɗinta, hannayenta dukka kerma suke yi, hakan zai kara tabbatar maka da tana tsorace. Magana ta fara yi cikin rawar murya ga shi dama ba fita sosai voice ɗin nata yake yi ba, sai abin ya kara kwaɓewa.

"Ni Aunty duk wata dukiya bata dameni ba, ni bana da buƙatar komai a duniyar nan da ya wuce na je naga kabarin mamata daga nan na koma ƙasarmu, ƙasarmu nake da burin na koma naje na nemo ƴan uwana da kuma mahaifina, please Aunty ki taimaka mun na koma ƙasarmu zan yi duk abin da kika ce".

Wani irin nannauyar ajiyar zuciya wannan mata ta sauke da jin amsar da Leesharh É—in ta bata, ranta ya yi haske da jin cewa Leesharh zata iya yin komai domin ta bar wannan gida ta koma kasarsu, har wani walwala ne ya bayyana a face nata, da yake tana sanye da nikaf hakan yasa ba za'a gane ba, hankalinta ya kwanta yanzu, ta samu damar da zata cinma burinta da abin da take hari a nata tunanin kenan, ko da yake bata zo wannan gidan yarin wajen Leesharh ba sai da ta shirya ta kuma san labarin Leesharh ta san da cewa zata iya aikata komai idan aka bita ta yadda ya dace, idan aka yi wasa da tunaninta, dan yarinya ce mai jajircewa a kan burinta da aikinta.

"Good Leesharh, haka ake son mutun mai zuciyar jajircewa juriya da hazaƙa, naji matuƙar daɗi da ya kasance zaki yi komai domin mahaifinki, kada ki damu kina gama aiki zan mayar dake ƙasarku ba tare da ɓata lokaci ba, ai uba ya wuce wasa Leesharh, ke ɗin yar baiwa ce Allah ya yi maki albarka".

Ɗan dakatawa da kalaman yaudarar tata ta yi tana kara kallon face ɗin Leesharhr, dan kowa yasan dai waɗan nan kalaman nata na yaudara ne, so take yi ta yi amfani da ƙarantar shekarun Leesharhr haƙanta ya cinma ruwa, daga gani bata ƙullo gaskiya ba.

Da Amin kawai Leesharh ta amsa mata ba tare da ta É—ago da kallonta ba, tunanin a ina zata yi wannan aikin kawai take yi.

"Kina jin yadda aikin zai kasance, zaki je gidan ne a matsayin Æ´ar aikinsu, suna da masu aiki da a kallah zasu kai mutun 50, amma dukka wannan ba damuwa bane, ni nasan ta yadda zan shigar dake gidan a matsayin mai yi masu aiki, zan saya maki sabuwar waya, ba kin iya amfani da ita ba?".

Ta dakata tana jiran amsa.

Girgiza mata kai Leesharh ta yi alamar a'a bata iya amfani da wayar ba.

"Okey wannan dukka ba matsala bane, ni zan sanya a koya maki komai, dama ba'a haka zaki je masu ba, dan su masu yi masu aiki ma sai wanda yake da degree or diploma, ba kananan kai bane suke yi masu aiki, sai na sanya an koya maki abubuwa na a kallah wata guda, kafin nan na shirya ta yadda zaki yi ki shiga gidan, babu ruwanki da kowa a cikin gidan, ko sauran ma'aikatan gidan ban yarda ki rinƙa yi masu magana ba, kada ki yarda ki sake da kowa, muna da ma'aikata a gidan da zasu kula da ke, dukkansu manyan mutane ne da ba zasu iya shiga jikin Ramish ba, shiyasa na zaɓoki, Ramish kawai zaki saka mun ido a kansa, ban ce ki kira kowa da wayar da zan baki ba, haka zalika ban ce ki bawa kowa number wayar ba, nima kuma ba zan kiraki ba, idan ina da buƙatar yin magana dake ni nasan ta in da samu haɗu mu gana, wayar da zan baki zan baki ita ce kawai dan abu biyu, na farko domin akwai abin da zan sanya a cikin wayar dan ya tayaki aikin da zaki yi domin mu kammala da wuri, na biyu kuma wani lokaci ki rinƙa ɗauka mun Ramish ɗin a video idan suna irin tattaunawa mai mahimmancin nan, kuma da zarar kin turo mun video ki goge shi a wayar, ko da yake ma time to time zan rinƙa canza maki wayar, wannan ba abin damuwa bane na san ta yadda zan shirya komai".

ÆŠan dagatawa da maganar ta yi tana jiran ta ji me Leesharh É—in zata ce.

"Aunty to ni da nake matsayin Æ´ar aiki ya za'ayi na iya sanin lokacin da suke tattaunawa mai mahimmancin? Kuma ai idan zasu yi tattaunawa ba'a ko'ina zasu yi ba ko? In dai haka ne ya za'ayi na san in da zasu yi tattaunawar?".

Ɗan ƙaramin tsaki ta ja kafin ta cigaba da cewa. "Aikin da zan samo maki ba kamar sauran ƴan aikin gidan bane, an gaya maki a banza na zaɓeki ne? Akwai dalilan da yasa na zaɓeki wadda ban gaya maki ba, kina da kyau, kina da diri da sai an tara mata 100 ba'a sami goma masu irin dirinki ba, da wannan zamu yi amfani mu sanya shi ya saki jiki da ke ko kuma ku sami kusanci sosai har haƙanmu ya cinma ruwa".

Shiru Leesharh ta ɗanyi, abinku da kananan shekaru, sai bata kawo komai a ranta ba, bata ma san waye zata yi wa wannan shisshigin da leƙen asirin ba, ita dai tun da ance mata taimako zata yi ai shikenan, bata san me za'ayi mashi da ake buƙatar sanin duk wani halin da yake a ciki ba, ita dai burinta na son komawa ƙasarsu ya rufe mata idanu da har take jin cewa tabbas zata iya yin komai a kan hakan.... Babbar magana, in kuwa haka ne akwai kura ba kaɗan ba.

"Tunanin me kike yi Leesharh?".
Ta faÉ—a a É—an tsorace, tana tsoron kada Leesharh ta ce ba zata iya ba ko ta karaya.

Girgiza mata kai ta yi tana faÉ—in. "Bana tunanin komai".

Kada ku mance duk maganar da Leesharh zata yi sai wannan mata ta É—an É—auki lokaci mai É—an tsawo tana jujjuya maganganun a cikin ranta, dan ta fahimci abin da Leesharh É—in ta faÉ—a da kyau da kyau, na gaya maku maganar tata ne baya fita sosai, hakan yasa ba'a gane me take cewa sosai.

"Kada ki yi tunanin komai my sister, ba wani abin da zai faru In Sha Allah, zaki gama wannan aiki lafiya ki kuma koma ƙasarku wajen babanki da ɗinbi dukiya sosai lafiya lou, ba zan bari wani abin ya sameki ba, na yi maki alkawarin, ki yarda da ni taimakon zaki yi".

"Na yarda dake Aunty, na kuma yarda da duk abin da kika faÉ—a, sannan na yarda da zan yi maki wannan aiki".

Wani irin cool ajiyar zuciya ta sauke jin kalaman yarinyar, sai kuma ta ɗan ji wani irin yar a ranta, ba komai bane yasa ta ji hakan face tasan da cewa in dai asirin Leesharh na leken asiri ya tuno to ba makawa kasheta zasu yi har lahira, hakan yasa ta ɗan ji wani iri a cikin ranta, amma da yake abin da suke buƙata kuma yake a gabansu suna ganin cewa yafi ran Leesharh ɗin mahimmanci, sai ta saki wani irin shu'umin murmushi tare da cewa.

"Tom shikenan jeki É—akinku ki shirya ki kuma yi bankwana da kawayenki anjuma zan dawo na É—aukeki mu tafi".
Yadda ta yi maganar with her full confidence sai ka rantse da Allah ba'a gidan yari Leesharh take ba, wai zata dawo ta ɗauketa kamar ba ita aka yankewa hukuncin kisa ba, hakan na nufin koma wacece wannan mata ba kananan mutane bane, dole manyan kai ne suke ƙoƙarin tura Leesharh ga halaka.

Miƙewa Leesharh ta yi jiki ba kwari, dan yunwa take ji sosai, da kyar take iya jan kafafun nata ta nufi kofar da zai mai data izuwa ɗakinsu. Da idanu matar ta bita da shi tana yi mata wani irin kallo mai wuyar fassaruwa.

Har ta kai tsakiyar office É—in, sai kuma ta juyo tare da cewa. "Aunty a gidan waye zan yi aikin?".

Wani shu'umin murmushi ta É—an saki kafin ta ce. "A gidan Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen zaki yi aiki".

Jinjina mata kai kawai ta yi da yake ita ba ƴar ƙasar ba ce, bata san wanenen Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen. Wucewa ta yi ta nufi waje ranta fes zata fita daga wannan gida a yau.

Nannauyar ajiyar zuciya wannan mata ta sauke kafin ta ce. "Lokacin ka ya fara daga yanzu Ramish, time É—imu ya yi".
Ta yi furucin nata a fili, cike da farinciki tare da full confidence sosai ta yi furucin nata.

Ita kuwa Leesharh sai murna take yi ta koma room É—insu. A yadda ta bar Jasrah haka ta dawo ta sameta, ta buga uban takumi tana tunanin ina aka kai Leesharh.

Tana ganinta ta yi maza ta miƙe tsaye, nan take farinciki ya bayyana a samar face ɗin tata, har wani ƴar murmushi ta sakar mata kafin ta ce.
"Alhdulillah nagodewa Allah da yasa ba É—aki suka sauya maki suka rabani dake ba.

A hanzarce Leesharh ta ƙariso ta zo ta rungumeta tana murnar lokacin fitarta daga gidan ya yi.

"Leesharh is there any good news? Naga like you're so happy like ba yadda kika fita ba, ke matsalar ma baki yin dariya bare mutun ya iya fahimtar kina cikin farinciki or not, amma dai a haka nake son kayata, baki dariya ko kina dariya dukka abu É—aya na sani shi ne i really like you".

Wani irin faɗuwar gaba Leesharh ta ji na jin kalaman Jasrah, ba yau ta fara jin kalaman da suka fi haka daɗi da kyau daga gareta ba, amma na yau ɗin sai ta ji sun ɗaga mata hankali kuma sun jefata cikin damuwa, sai yanzu ta tuna cewa zasu rabu da Jasrah kenan? Shikenan ita zata fita ta bar Jasrah? Kuma nan da one year kashe Jasrah kenan za'ayi? Ba zasu sake haɗuwa ba? Sun rabu kenan har abada?. Ya ilahi ya lillilahi, a duniya duka bayan iyayenta babu wanda ya taɓa nuna mata tsantsar kauna tsakani da Allah kamar yadda ƴar tahaliƙan nan Jasrah ta nuna mata, bata taɓa zama da yarinyar kirki biyun Jasrah ba, yarinya so silent, ga hakuri da tawakkali, ilimin addini da yin aiki da shi, nutsatsiya, ta nuna mata kauna kamar ƴar uwarta na jini, wani lokaci har a baki take bata abinci idan ta ki ci, shikenan yau alaƙarsu zata zo karshe na har abada?.

Wani irin sara mata ta ji kanta ya yi, nan take murnarta ya rikiɗe izuwa bakin ciki, damuwar da bata taɓa shiga makancinsa bane ya lulluɓeta, nan take ta ji wani irin karayar zuciya ya dira mata a ranta, idanuwanta ne suka yi wani irin ciwowa da kwallah tab, nan take kuma idanun nata suka yi jajir kamar wuta.

Sai tambayarta Jasrah take yi akwai labari ne suna a rungumi da juna, amma ina Leesharh ta ƙasa yin magana, sai ma wani irin ciwo da nauyi da kanta ya yi mata, ji take yi kamar kan nata zai faɗi ƙasa.

Jin alamar saukar hawaye a saman shoulder É—inta ne yasa Jasrah ta yi saurin raba jikinsu domin taga face É—in Leesharh É—in da kyau.

Su Sarah dai sai binsu da kallon walaƙanci suke yi, sun tsani Leesharh a rayuwarsu yaran nan, babu abin da ta yi masu, kawai bakar zuciya ce irin tasu.

"Subhanallah Leesharh what's happening? This tears is for what?".
A ruɗe ta yi tambayar tata, tana magana tana zaro idanu, alamar tana ɗan tsorace, dan ita ma bata jin zata iya rabuwa da Leesharh a yanzu, duk da cewa tasan lokaci ƙalilan ne ya rage mata a duniyar ma bakiɗaya, amma bata sanya a ranta zata rabu da Leesharh a yanzu ba, ta fi yin tunanin kasheta da za'ayi ne kawai zai rabasu.

Zama a gefen bed ɗinta Leesharh ta yi tare da buga uban tagumi, kan kace me har hawaye sun jike mata fuska, sai simtiri suke yi, sun wanke mata fuska sosai, wani irin kukan zuciya ma da take yi tun da uwarta ta haifeta bata taɓa yin irinsa ba, sai dai kuma duk da haka bata jin akwai wani abin da zai dakatar da ita daga fita wannan gida, tana son ta koma wajen ƴan uwanta, ba zata iya hakuri da mahaifinta tare da ganin kabarin mamarta saboda Jasrah ba, haka zalika bata jin kuma kamar zata iya rabuwa da Jasrah ɗin. Tashin sense, dole kuma a ciki ta ɗauki ɗaya.

A ruÉ—e Jasrah ta zauna a kusa da ita, duk ta rikice tana son ta ji me Æ´ar uwar tata take yi wa kuka? Me yasameta ko me suka ce mata a office É—in da ta je. Shoulders É—inta ta rungumo tana mai cigaba da faÉ—ar subhanallah.

Da taga dai Leesharh ba zata iya gaya mata me suka ce mata ba, dan yarinya ce mai zurfin ciki, sai ta yanke shawarar bari ta yi mata nasiha wata kila idan nasiha ya ratsata zata sami nutsuwa har ta gaya mata abin da yake faruwa, a nutse ta fara magana kamar haka.

"Leesharh duk tsanani yana tare da sauki, duk abin da yake da farko dole yana da karshe, kuma ki sani duk wata second ɗaya da zata wuce a rayuwarmu Ubangiji baya barci yana sane damu, ni bansan me suka ce maki a cikin office ɗin ba, amma dai koma menene nasan ba mai daɗin ji bane, dan abin da yake sanyaki kuka ba ƙaramin abu bane, to koma dai me suka ce maki ina son ki yi hakuri ki fawwalawa Allah al'amuranki, da sannu zai yi mana sakayya, ni har cikin zuciyata ban taɓa yarda da cewa ke kika kashe Oummunki ba, kin kuma ki gaya mun gaskiya yau tsawo shekara guda kenan, amma dai koma me Allah ya fimu sanin dai'dai da ba dai'dai ba da kuma abin da ya dace damu, shiyasa na miƙa mashi ragamar rayuwata, ni bance dole sai kin gaya mun abin da suka gaya maki ba, abin da nake so dake kisani a nan shi ne komai ya yi zafi koda ya fi wuta zafi to maganinsa Allah, duk abin da suka ce maki idan alkhari ne a gareki Allah ya tabbatar maki, idan kuma sharrine to Allah ya wargazar da shi, amma please ki dai'na wannan kuka, mu yi addu'a komai zai koma dai'dai da izinin Allah".
Ta kai karshen maganar ita ma idanunta suna cikowa da kwallah.

Sosai Leesharh ta samu saukin raɗaɗin da take ji a cikin zuciyarta da jin kalaman Jasrah. Haƙiƙa duk abin da Jasrah ta faɗa gaskiya ce, hakan take babu wata tantanma, sai ta ji ta ɗan sami kwarin gwiwar da zata iya gaya mata abin da ya sanyata kuka, dan haka sai ta kai hannu ta goge hawayen da suke a saman fuskarta, cikin voice ɗinta kamar wata yarinya yar shekara huɗu a duniya ta fara korawa Jasrah bayanin abin da yake faruwa daga farko har karshe kamar yadda wannan mata ta gaya mata da yadda suka yi dukka.

Da Aaradiya da Sarah sun mayar da su Tv na kallo, kallonsu kawai suke yi babu kyafta idanun, tunani kawai suke yi da ace sune suka sami wannan damar mana, ai da shikenan komai shar abinsu su bar gidan.

Shiru Jasrah ta yi tana sauraronta, har sai da ta kai aya a maganar tata, tana yi wasu hawaye suna ƙara bin ƙuncinta sosai.

Da yake Jasrah babu mugunta ko É—igo a ranta, ita É—in tana sowa É—an uwanta abin da take sowa kanta ne, sai ta saki cool murmushi ga ragowar hawaye a fuskarta.
"Leesharh ai wannan abin farinciki ne bana kuka ba, ke da zaki fita daga wannan gida, kuma ke da zaki koma wajen iyayenki da ƴan uwanki, to me abin kuka? Ai godewa Allah ma zaki yi sosai, alwala yakamata mu tashi mu yi dan mu nunawa Ubangiji murnarmu, Addu'arki ce ta karɓu wata kila".
Tana magana ne da dukka iya gaskiyarta, tabbas zata sha kukar rabuwa da Leesharh, kuma zata shiga damuwar da bata taɓa shiga ba, domin da ita kawai ta saba a gidan, amma kuma hakan ba shi zai sanya ta tauye gaskiya ko ta hanata cigaba saboda son zuciyarta ba, sam ba haka take ba ita.

Wani irin confidence Leesharh ta kara ji ya dira mata, sai ta ji kaso sittin na damuwar da ta shiga duk ya gudu, ta lura da cewa tabbas Jasrah ta shiga damuwa, amma kuma ta yi ƙoƙarin danne damuwar tata dan kada ta sarewa Leesharh ɗin gwiwa.

Aaradiya da Sarah da yake bakaken zuciya ne da su, kuma basu son Leesharh ta fita gidan ta barsu, sun fi son a kashesu a tare kamar yadda aka yanke masu hukunci tun farko, sai abin ya sosa masu rai over, nan take suka ji koma ta halin ƙaƙa ba zasu bari Leesharh ta fita ta barsu su a kashesu ba, dan haka har suna haɗa baki wajen cewa.

"Ke Leesharh baki da hankali ne da zaki yarda da wannan mata? Wlh kada ki yarda da ita, kila ma kasheki zata je ta yi, gara maki ki zauna a nan wlh yafi maki".

Da yake ita Jasrah ta fisu shekaru kuma ta fisu wayo da ilimi, sai ta fahimci in da suka dosa, ta ganosu hassadace kawai take cinsu, dan haka sai ta ce.
"Da can baya babu wadda ta taɓa bawa Leesharh shawara a cikinku ko? Kuma babu wadda ta taɓa yi mata maganar da zai amfaneta ko? Babu wadda ta taɓa shiga harkarta a cikinku ko? Sai yanzu ne kuke ganin yakamata ku bata shawara kenan?".

Da yake Leesharh har yanzu da sauranta, yarinta yana a kanta sosai, sai taga kamar amsar da Jasrah ta basu bai dace ba, a wawtarta ita gani take yi ai sonta suke yi tun da har suka bata shawara. Wannan shi ne da gaske ne ta yaro kyau take yi bata ƙargo.

Wani kallon uku saura kwata Aaradiya ta wurgawa Jasrah É—in kafin ta ce. "To uwar kanzagi, ai da yake sunan Jasrah muka kira ba Leesharh ba, ina ruwanki da mu? Dole ne mu bata shawara dan munga zata faÉ—a halaka".

(Ni kam na ce su shawara manya, Aaradiya manyan kasa😅🥱)

A takaice Jasrah ta amsa mata da cewa. "Ko kuma dan kunga zata fita ba za'a kasheta ba, zata fita ta barku ba, shi ne hankali duk ya bi ya tashi".

A harzuƙe Aaradiya ɗin ta miƙe zaune, nan take ta hayyako da hayakin masifa kamar wadda dama take wuya tana jiran kiris ta zazzageta.

Jasrah bata sake bi ta kanta, ba kuma ta sake maida hankali ta saurari hayakin masifar da take barbalo masu ba, ta toshe kunne tare da maido da hankalinta a kan Leesharh da take ta faman binsu da idanu.

"Leesharh baki gaya mun a gidan waye zaki yi aikin ba? And kuma baki gaya mun wasu irin bayanai na mutumin zaki kwasa ki bawa wannan mata ba, sannan ina son kafin ki tafi ki gaya mun kasar da kike da sunan iyayenki ko da baki bani labarinki ba, zan gayawa kanwata Alveena idan sun kawo mun ziraya watarana ko bana raye ta je ƙasarku ta kai maki ziyara idan ta girma".

Duk wata zuciya mai tausayi sai ta tausayawa Jasrah a wannan gaɓa, sai ta ji wani irin mugun tausayinta, saboda daga jin yadda ta yi maganar kasan kawai ta ƙaƙalo ta ne dan dole, daga jin muryarta kasan e lallai tana cikin matsananciyar tashin hankali da damuwa.

"Aikin da zan yi mata ta ce mun duk wasu motsi nasa tana son ta rinƙa sani, kamar in da zai je da kuma idan ya fita gida, yaushe yake fita? And kafin ya fita tana son sani? Yaushe yake dawowa gida, and idan ya dawo gida ma tana son ta sani da dai sauran dukkan motsinsa, and duk wani muhimmin tattaunawa da zai yi da ma koma waye shi ma tana son ta sani, iya aikin da zan yi mata kenan, batun wajen da zan yi aikin kuma ni ban san a ina bane, ban san wani gida bane, ni dai ta ce mun gidan Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen, so ban san waye shi ba, sai dai ta kaini na gani, batun iyayena da ƴan uwana kuma zan baki..........."

Wani irin jan birki ta yi, ta tsaya cak da maganar tata sakamakon wani irin mimmikewa tsaye da ta ga Jasrah, Aaradiya and Sarah sun yi. ÆŠan zaro idanu ta yi tana kallonsu a cike da mamaki.

Ai a dubu ɗari Aaradiya ta diro ƙasa daga saman bed ɗinta, cikin sarkewar murya ta ce. "A gidan waye zaki yi aiki?".

Da wani irin kallon mamaki ta bita da shi kafin ta maimaita mata kalmar gidan Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen.

Wani irin kara Aaradiya ta fasa kamar wadda aka tsinkawa mari, sai kuma ta sake cewa. "Tab Allah ya bada sa'a, ai Leesharh ki je kawai abinki, ashe banza muƙa ɓata bakinmu wajen baki shawarar karki je ma, ai baikamata mu hanaki tafiya ba, ni yanzu ba zaku sake jin bakina a wannan case ɗin ba, lastly dan girman Allah Leesharh kada ki sake yin tunanin kin sanni a rayuwarki, please koda watara za'a tambayeki wa da wa kika sani a rayuwarki ki ce ke baki sanni ba bama ki taɓa ganin mai kama da ni ba".
Tana kai karshen maganar tana wuce ta haye saman gadonta.

A hanzarce Sarah ta karɓi zance da cewa. "Ki haɗa da ni Leesharh, dan girman Allah ko da sunan wasa kada ki taɓa sake tunanin cewa kin sanni".

Ita dai ta yi kasake tana kallon ikon Allah, daga ambatar sunan Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen duk sun ruÉ—e haka? To waye shi?.

Dafa shoulder É—inta da aka yi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta afka.

"Jasrah wannen Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen É—in?" Ta wurga mata tambayar a É—an ruÉ—e, dan ta tsorata na ganin yadda su Sarah duk suka bi suka ruÉ—e daga jin sunan mutumin.

Wani irin dogon numfashi Jasrah ta ja tare da saukewa a hankali, shiru ta É—an yi na a kallah mintuna uku kafin ta sake nisawa ta fara magana a nutse.

"Tabbas ni ba haifaffiyar nan Dubai bace, amma kuma duk wanda ya kwana ya tashi a cikin Dubai dole zai san familyn Badeen, dole zai san wannen Shaikh Abu Abdussalam bin Badeen, magana ta gaskiya ni yanzu na ji ban ma yarda da cewa wannan mata zata iya shigar dake cikin wannan gida ba farko kenan, gidan da aka ce maki tun daga farkon titin da zai kaika cikin unguwar da gidan yake wasu mahaukatan securitys ne wadda ganinsu tamkar ganin mutuwa haka yake, ban taɓa zuwa gidan ba, amma babana yana bamu labarin gidan, ke in takaice maki ko tsuntsuwa waɗan nan securitys ɗin da da hali ba zasu bari ta gifta ta sararin samaniyar wannan gida ba, babana ya ce duniya ne guda gidan, ma'aikata masu yi masu aiki kawai sun fi mutun 50, a hakan ne zaki shiga cikinsu a matsayin mai aiki? Zaratan mata ne masu lafiya da jini a jika, mata masu kirar maza su suke yin girkin wannan gida, to ina mai tabbatar maki duk wani motsin ma'aikatan wannan gida suna sane da shi, wlh Leesharh gwara maki mutuwa a cikin wannan gidan yarin da ki je ki karɓi aikin leƙen asirin gidan Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen, dan naratse maki da wanda rai'na yake hannunsa idan suka kamaki wani irin kisan walaƙancin da zasu yi maki ko kare ba zai shinshini namarki ba, yafi maki sauki ki tabbata a cikin nan da ki fara tunanin zuwa gidan Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen ziyara ma kawai, wannan mata da ta kawo maki wannan aiki ma sam sam babu ƙwaƙwalwa a cikin kanta, da alama mahaukaciya ce".

Izuwa yanzu cikin Leesharh ya gama É—uran ruwa, ta tsorata sosai da jin maganganun Jasrah, sai zaro idanu take yi, amma sai ta daure ta ce.
"To Jasrah wanenen shi É—in?".

Da sauri Aaradiya ta ce. "Ni ne nan zan baku wannan amsa, dan ko ita Jasrah magana kawai yake yi bata san wa ake kira da Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen ba, ku saurara ku ji wanenen shi ɗin. Shi ɗin ɗane ga the most powerful King of Dubai, babban Yayan Shaikh Abu Abdussalam shi ne president mai ci a yanzu, shi kuma Abu Abdussalam Defence minister ne, shiyasa securitys kala kala suka yawaita a gidansa, domin duk wani security da kuka sani a faɗin Dubai, duk wani mai kaki (uniform ) da kuka sani to dole da umarninsa zai yi aiki, a ƙarƙashinsa suke, dole umarninsa zasu bi kafin aiwatar da wani abin, yana da manyan brothers har guda uku masu rike da manyan muƙamai masu karfin faɗa a ji a duniya bakiɗaya, amma babban yayansu baya kasar nan ma bakiɗaya, King of Dubai ƴaƴansa maza biyar ne mace ɗaya ita ce Gimbiya Rahilarh (Mommar Zunaira) ita ce kuma auta, su Abu Abdussalam bin Badeen duk yayyunta ne, Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen matarsa ɗaya yayansa uku, mata biyu namiji ɗaya, wannan shi ne kaɗan daga cikin labarin gidan da zaki je leƙan asiri, familyn da manyar ƙasar nan suke tsoron haɗa hanya da su, sai dai muce Allah ya bada sa'a yasa ki samu mutuwa mai sauki a hannunsu......"

Tana rufe baki Jasrah ta karɓi zancen da cewa.
"Wlh Leesharh gara maki ki mutu a cikin wannan gidan yarin da ki mutu a hannun ƴan gidan can in suka kamaki, tab akwai ma wanda ya isa ya shiga gidan leƙen asiri ne?! To wlh ki shafawa kanki ruwan sanyi, meyasa ita matar bata je ta yi aikin da kanta ba? Sai ke zata saka bakar muguwa azzaluma! Kuma meyasa ba zata saka maza manya ko kuma mata manya ba? Sai ke ƴar ƙaramar yarinya? Ai naga manya ne ma zasu yi mata abin da take da buƙata daidai, sune suke da girman da sun san ta yadda zasu zulle kada a kamasu".

Sosai Leesharh ta kara tsorata over, muryarta na rawa ta ce. "Ni ai kinga ta ce mun taimakonsa zasu yi, wai wani ne ma yake son cutar da shi su kuma zasu taimaka mashi, kuma ta ce mun wai manyan maza ko mata ba zasu iya samun damar shiga har cikin gidan ba bare su sami kusanci da shi, da alama baya yarda da kowa, amma ni karama ce babu wanda zai yi tunanin leƙen asiri na je yi, zasu yarda na shiga cikin masu aikin da suke aiki a can cikin gida ba tare da wani damuwa ba haka ta ce mun".

"Hmmmmm Leesharh ya tabbata baki da hankali, waye ya ce maki taimakonsa suke son yi? Idan har taimakonsa suke son yi menene na neman information a kan duk wani motsinsa? Su fito mana kai tsaye kawai su sanar da shi cewa ga wani zai cutar da shi in gaskiya ne, wlh babu wani taimakonsa da zasu yi face cutarwa, sannan maganarki gaskiya ce da kika ce ke kamar yarinyar ce ba wanda zai kawo wani bad tunani a kan ki, kuma za'a iya barinki ki shiga cikin ma'aikatan da suke aiki a can cikin gidan, amma ki sani hakan ba mai ɓulle maki bane wlh, dan yadda kika san aljanu haka familynsu suke, kin san takun sakar da ake bugawa da su a duniya kuwa? Kin san adadin makiyan da suke son kaisu kasa kuwa? Ta ko'ina tarin makiya suke da shi sakamakon riko da gaskiya da suke da shi, suna sane da tarin makinyan su, a haka kuma kuke tunanin zasu yi zaman shiru har wani ya iya shiga cikin ya leƙa asirinsu? Lallaima Leesharh na tabbata makiyan familynsu ne suke son yin amfani dake dan cinma burinsu, ki sake yin tunani da kyau, na tabbata sun hango cewa amfani dake zai basu nasara ne yasa suka buƙaceki, wlh idan kika shiga hannunsu ina gaya maki gawarki ma ba za'a gani ba, mahaukatan karnikan gidan ne kawai zasu cinye namarki ɗanya, wata ƴar figaggiya dake a wajen ne zaki ce zaki je leƙar asirin shegun duniya ko?".

Shiru Leesharh ta yi, gabaɗaya ta shiga ruɗani kanta ya ɗaure, duk ta rasa me yake yi mata daɗi, yanzu ya zata yi?..... Masu karatu ku bawa Leesharh shawarar ya zatayi, shin ta yarda ta yi wannan aiki ne ko kuma ta hakura a kasheta a wannan gidan yarin kawai? Ni dai bari na leƙa su Kamran namu na amana mu gani, wata kila kafin mu dawo Leesharh ta samu mafita, amma kam tana ruwa kusa da kada..........🥱

🏞️FOREST🏞️

Kamran ba dan ya so ba ya tashi Sweetie daga barci, dan su koma gida, saboda ya haura lokacin da yake komawa, ya tabbata idan ya ɗan kara ƴan mintoci Mamma zata fito nemansa, dan haka sai ya tashi Sweetie daga barci, ita kuma Pretty sai dai ya ɗauketa cak, dan san kai irin nasa sai bai tasheta daga barcin ba, ko da yake abokiyar rigimarsa ce, ba son kai bane...........😅

Hannun Sweetie ɗin ya riko bayan ya saɓa Pretty a saman shoulder ɗinsa, da haka suka nufi maɓoyar tasu, ya bar Rocky a wajen yana aikin zuba barci, yasan duk lokacin da ya tashi daga barcinsa zai komo gida.

Da kyar ya iya shiga da Prettyn cikin wannan rami, sai barci take zubawa, da alama yau barcin nata ya yi nauyi sosai. A saman gadon nasu ya kwantar da ita, ita kuma Sweetien ya zaunar da ita a bakin bed ɗin, ba tare da ɓata lokaci ba ya yi maza ya kama hanya tare da yi wa Sweetie sallama.

Kai tsaye gida ya nufa, bai sake bi ta kan Rocky ba, sai sauri yake ta zuba wa kada Mamma ta yi faÉ—a.

Yana shigowa cikin ƙogon nasu ya wuce ɓangarensa, tunanin Pretty ce kawai a cikin zuciyar tasa.

"Mamma where are you?". Ya faɗa yana ƙoƙarin cire rigar jikinsa.

Mamma dake wajen madafarta tana ta aikin soka nama a jikin itace tana saƙalewa a saman dutsen, ta amsa mashi da. "Sai yanzu ka dawo ko?".

"Kai Mamma ban fa jima ba".

Wasu duwatsu guda biyu ta ɗauko masu karfi tare da fara ƙoƙarin kunna wuta ta hanyar haɗa duwatsun tana bugawa, suna bada wuta.

"Ba shakka kam baka jima ba, kazo ka ɓare ɓawon masaran nan".
Tana magana tana ƙoƙarin kunna wuta da waɗan nan duwatsun.

"Am coming Mamma, but before na zo let me ask you something, dan na ƙagu na ji amsar, abin yana damuna".
Yana magana yana cire kayan jikinsa.

"Okey ina jinka sarkin tambaya".
Ta faɗa tare da ɗauko wani tukunyar ƙasa ta ɗaura a saman wutar da ta kunna ɗin, sannan ta duba ruwa ɗan dai'dai misali.

"Mamma this two dys am feeling something da ban san ya zan gaya maki ba, ban taɓa jin hakan a jikina ba sai this time around, and hakan yana faruwa ne...............🥱

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 2/8/2024.....✍️📚🌹

For information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________27🔥

"Mamma this two dys am feeling something da ban san ya zan gaya maki ba, ban taɓa jin hakan a jikina ba sai this time around, and hakan yana faruwa ne if i........... " Sai kuma ya ja birki da yin maganar, saboda ya kasa iya ƙarisar da cewa hakan na faruwa ne idan ya taɓa wata mace ba ita ba.

Da yake ita Mamma tasan wani lokaci questions É—in da yake yi mata ba wasu masu amfani bane, kawai ya sanyata magana ne, sai da ta ji ya yi shiru bata sake bi ta kansa ba, ta cigaba da aikin girkinata na dare, ga nama da take gasa masu a gefe, namar gwanin ban sha'awa, kana gani sai ha kaÉ—iyi yawu.

Shi kuwa kammala cire kayansa ya yi tare da nufar in da zai yi wanka zuciyarsa a cike tab da tunanin yadda zai yi da mamma ta gaya mashi menene yake damunsa ba tare da ta san cewa jikin wata ya taɓa ba, a nasa tunanin gani yake yi bashi da lafiya ne, kada kuma ku manta Mamma babbar likitar gargajiya ce, shi ne ma dalilin da yasa yake son ya tambayeta ko akwai wani magana da zata taimaka ta bashi.......... E lallai ni kuwa nace zaka ga magani...😅

Wankarsa ya je ya yi tare da fitowa ya shirya cikin wasu haɗaɗɗun kayansa masu matuƙar kyau, tas tas da su, Mamma ba dai tsabta ba, shi ma Kamran a yadda ta rainesa kenan, baya kaunar datti ko kaɗan, suna da tsabta sosai da sosai.

Itatuwan da take saƙar kayan sakawa irin na mutanen da ya ɗauko tare da audigar da take saƙawa ya nufo waje gabaɗaya, bai je in da take ba, sai tubka da warwara a cikin zuciyarsa yake yi, yana ta saƙa ta yadda zai yi mata ta gaya mashi me yake damunsa?.

Can wata dabara ta faɗo mashi ya gaya mata yanayin da yake shiga kawai ba sai ya ce mata wata ta taɓa shi ba, tuna wannan dabara yasa ya ɗan saki face ɗinsa keɗan.

Kafa itatuwar sakar tata ya yi tare da zama a saman wata dutse da Mammar tasa take zama idan zata yi saka, shi ma izuwa yanzu ya iya sakar sosai, so ya ɗauko ne domin ya saƙawa Pretty sket da riga masu shegen kyau, bai taɓa saƙa kayan mata ba sai nasa, yau ne farau, so ya sanya a ransa idan ya saka ta yi kyau sai ya sakawa Sweetie ma, idan kuma bata yi kyau ba sai ya hakura. Yasan ba yanzu Mammarsa zata fito waje ba, zai iya kammala saƙa sket ma Mamma bata leƙo ba, dan tana girki, idan ta kammala kuma wanka zata yi ta gyara madafa da sauran sassa na cikin ƙogon, so sai can yamma sosai zata fito, yasan cewa yana saurin yin sakar shiyasa bai ji tsoron kada ta fito ta same shi yana saka kayan mata ta tambayesa waye zai sakawa ba, bai wani damu ba, a hanzarce ya fara saka mata sket, dan shi ya fi girma da cin lokacin. Sai dai fa yanayi kuma yana fargabar kada Mamma ta faɗo mashi babu wani excuse.

Sam ya manta Mamma ta ce ya zo ya ɓare mata masara, da dai baya mantawa da maganar Mamma komai ƙanƙantarta, yanzu kuma su Pretty sun shigo cikin tunaninsa da ƙwaƙwalwarsa suna raba mashi hankali gida biyu, har ya fara mancewa da wasu kalaman Mamma, duniya kenan.

Da sauri sauri yake sakar kamar wani mara gaskiya. Sket ya saƙa mata white color, dan Mamma bata rina audigar ba, farace kawai, sket ɗin ya yi masifar kyau, sai dai ɗan guntu ne da ba zai wuce mata gwiwowinta ba, kamar umbrella ya yi yanayin design ɗin sket ɗin, ta yi kyau sosai.

Cikin sauri ya cireta ya sake mayar da audigar ya fara sakar sket ɗin Sweetie ma. Good one hour ya ɗauka yana yi, iri ɗaya dana Pretty ya sakasu kamar yadda yaga Mamma tana yi wa kanta, sai dai nata manya ne har kasa take yi, shi kuma ya yi masu ƙanana, dan yana ganin kamar zata iya kai masu kasan gwiwa kaɗan.

Rigar Pretty ya fara saƙawa kamar yadda ya fara da sket ɗinta, yana yi yana fargabar kada Mamma ta fito ta same shi yana sakar mata, dan ma ya kwashe skets ɗin ya kai cikin ɗakinsa ya ɓoye, idan Mamma ta gani ta tambayesa kayan waye bai san me zai ce mata ba, bashi da amsa, hakan yasa ya kwashe skets ɗin ya kai room ɗinsa.

Yana kammala rigar Pretty ya jiyo motsin Mamma tana shirin fitowa, ta kammala duk wasu ayyukanta da ta saba yi, a hanzarce ya cire rigar daga jikin itatuwar ya cusata a cikin rigarsa ya ɓoyeta a wajen plat tummynsa, sannan ya saka wata audiga ya kama sakar hula ta karya. Wasa wasa Kamran ya fara koyan karya tun bayan haɗuwarsa da su Pretty, ya kuma koyi ɓoyewa Mamma abubuwa saɓanin da can baya kafin ya haɗu da su Pretty, sam baya ɓoye mata komai.

Sarai Mamma ta lura da cewa yana ɓoye mata abubuwa da dama, amma ta zuba mashi idanu ne tana son taga gudun ruwansa, abinku da uwa kuma abin da bai saba ba, bai saɓa ɓoye mata komai ba, rana tsaka ya koya harda karya kunga kuwa dole ta fahimci canzawar ɗan nata, da yake ita macece mai kaifin ƙwaƙwalwa da basira sai bata wani damu ba tana bin komai daki daki taga iya ina abin zai kaita.

Shiru ta tsaya a bakin kofar fitowa daga kogon tana kare mashi kallo, ta zuba mashi idanu tamkar mai nazarin wani abin a face É—insa.

Sarai yasan da tsayuwarta a wajen, amma sai ya yi kamar bai sani ba, tamkar bai ji motsinta ba, saboda kada ta fara zarginsa, yasan halinta sarai.

Ta ɗauki a kallah good 10 mins tana kallonsa babu ko kyaftawa, shi kuma ya zage yana ta saƙa hula ta karya kamar bai san da ita a wajen ba.
Haƙiƙa wannan kallo da take yi mashi kallo ne da ya ƙunshi abubuwa da dama, kallo ne da ya ƙunshi abubuwa da ba zasu fassaru a bakin wani ɗan adam ba face ita, yanayin fuskarta ya nuna cewa da akwai abin da take tunani sosai da ta tsare shi da ido haka.

"Kamran". Ta ambaci sunansa in a low voice sosai.

Sarai ya ji kiran nata, amma sai ya yi kamar bai ji ba, saboda idan ya nuna ya ji zata fahimci cewa lallai akwai wani abin, zata ce kenan yasan da tsayuwarta a wajen. Da yake shi ma ba tayan baya ba wajen basira, ya ganota, wannan shi ne É—an na gada ya fi É—an na koya.

"Kamran".
Ta sake ambatar sunansa da É—an É—aga murya kaÉ—an.

Sai da ya dai'dai ta nutsuwarsa ta yadda ma kada ta gano shi ya yi sakar mata ko ya ɓoye kayan mata a jikinsa, kafin ya juyo da kallonsa a kanta.
"Mamma why are you standing there?".
Ya faÉ—a cikin nutsuwa.

Shiru ta É—an yi kafin kuma ta ce. "What's wrong with you?".
Ta yi maganar ne tana kallon cikin kwayar idanunsa da suke ja a yanzu saɓanin a baya da ta san idanunsa farare ne tas.

Wani littafi da ya taɓa karantawa a cikin takardun da take koya mashi karatu ne ya faɗo mashi a ransa, Kamran ya iya reading sosai kamar ba girman Forest ba, Mamma ta koya mashi, tunawa da wani part na short story of love da ya karanta a cikin littafin ya yi, nan take ya sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da ɗan kwaɓe fuska ya ce.
"Now Mamma kin daina damuwa dani, kina gani na dawo ban ci abinci ba amma ko ki damu, before fa har a baki kike bani abinci idan nace ba zan ci ba".
Wannan magana ba daga zuciyarsa ta fito ba, a cikin wannan littafi ya tuno da ita.

"Yanzu dai tambayarka na yi what's wrong with you ba wai cewa na yi ka gaya mun na damu da kai or not ba".
Ta bashi amsa tare da ƙarisowa in da yake.

"Kanaso ka doje mun ko Kamran? Me kake ɓoyewa?".
Ta yi maganar tare da cire hular da yake a kansa, nan take uban tulin gashin kansa ya watse har bayansa, bashi da mai yi mashi aski bawan Allah, Mammar ce take datse mashi gashin nasa da wuƙa idan ta yi yawa sosai, ga shi kuma da halittar gashi sosai, ya fi mata dayawa gashi, ga gashin nasa a kwance luf yana sheƙi.

Tara mashi kashin nasa ta fara yi tana son ta haɗa ta ɗaure waje guda sai ta ɗauko wuƙa ta rage mashi tsawonsa, dan ta lura ya yi tsawo sosai har izuwa bayansa, hakan yana sanya shi ƴar rama, ita kuma bata son hakan, ta fi son ta gansa ɓul ɓul da shi, wannan dalilin yasa take datse mashi gashin a kai a kai.

"Mamma this two days ina jin canji a jikina sosai, sometimes ina jin kamar sanyin zazzaɓi yana ratsani, and kuma......"
Sai kuma ya yi shiru ya kasa iya gaya mata karshen maganar na cewa gabansa yana tashi ba kamar da ba, bai san me zai ce mata ba.

Sarai ta gane me matsalar tasa tun ma kafin ya sanar da ita, tun ba yau ba ta fahimci yana da karfin sha'awa sosai, sai dai ta zuba mashi idanu ne kawai domin ta ga ko zai iya gane wa ko akasin haka, bata yi zaton zai tunkareta ya tambayeta ba, saboda tasan yana da kunya sosai, ba komai yake iya yin magana a kai ba, yanzu ma idan da yasan menene wlh ba zai yi magana ba bawan Allah.

"Baka barisar da maganar ba ai, and kuma me?".
Ta yi maganar cikin zolaya.

A hanzarce ya ce. "Mammaaaaaaaaa zaki fara ko? Na san kin gane me nake nufi fa, because i know who's my mother, ke É—in special ce, just kawai ki gaya mun ganyen da zan ciro maki ki haÉ—a mun maganin, dan gaskiya abin yana damuna".
Ya kai karshen maganar tare da juyowa suna fuskantar juna.

"Ni babu wani abin da na gane, ni likita ce?". Ta yi maganar tana ƙoƙarin barin wajen ta koma cikin ƙogon, dan ta ɗauko wuƙa ta zo ta datse mashi gashin nan nasa.

Cikin hanzari da zafin nama ya riƙo hannayenta cikin nasa.
"Mamma wai yanzu kin dai'na sona ne? Kwata kwata baki kulani sosai".

"Kai da ka girma ni yanzu wani kula ka zan yi? Yanzu fa ka gama mun bayanin lallai da gaske ka girma, shi ne kake son kulawata kuma? Ai sai dai ka kula da ni yanzu".
Ta bashi amsa tana É—aga mashi gera guda.

Ƴar murmushi ya sakar mata kafin ya miƙe cike da so da kuma kaunarta ya rungumeta a jikinsa, cikin dabara ya zame rigar Pretty da ya ɓoye a wajen plat tummynsa ya mayar ta bayansa, dan kada Mamma ta ji ya ɓoye abu.

"My Mamma you're my world, you're my happiness, you're my everything, ina kaunarki sosai".
Ya faÉ—a yana kwantar da kansa a saman shoulder É—inta.

"Kamran this two days É—in nan kana yin abubuwan da ban saka ka ba sosai".
Ta faɗa tare da raba jikinsu ta nufi cikin ƙogon.

Da sauri shi ma ya nufi É—akinsa domin ya ajiye rigar na Pretty ya fito, zuciyarsa cike tab da tunanin maganar Mamma na cewa kwana biyun nan yana yin abin da bata sanya shi ba, me hakan yake nufi? Duk sai ya bi ya tsargi kansa, ya afka duniyar tunani.

Kun san ance mutun idan bashi da gaskiya ko yana ɓoye wani abin to fa haka yake, kome zai gani sai ya rinƙa zargin kansa, yanzu dai ita Mamma bada wata manufa ta yi maganar nan ba, hasali ma ta yi mashi harshen damo ne a maganar, abin da take nufi shi ne kwana biyun nan baya yin abin da take saka shi, kunga ɗazun ta ce ya ɓare masara, amma bai yi hakan ba ya zauna saka kayansu Pretty, jiya ta ce ya kawo masu fruits, ya fita ya je wajensu Pretty ya yi zamansa ya manta, kuma da zai dawo ma bai ciro ba, and ya dai'na kawo masu nama a kai a kai, to shi ne harshen domon da ta yi mashi na baya yi mata abin da ta saka shi, amma da yake shi yasan yana ɓoye wani abin, duk sai ya tsargu ya ruɗe yake ganin kamar ta gano shi ne.

"Kamran lafiyarka kawa?".
Voice É—inta ya daki dodan kunnuwarsa.

Ƴar razana ya yi tare da amsa mata da ba komai. Sam bata son ta fara zarginsa a kan komai, amma zuciyarta ta kasa yarda da canzawar da ya yi kwana biyu, sai take jin lallai akwai abin da yake ɓoye mata, shekaru ashirin da biyar suna a tare bata taɓa ganin canji a tattare da shi ba sai wannan karon, kunga kuwa dole ta damu.

Cike da tunani a zuciyarta ta fara datse mashi gashin kan nasa da kakkaifar wukarta. Shi ma duniyar tunani ya luluƙa, amma fa tunanin Pretty yake yi, face nata yadda take barci a saman shoulder ɗinsa ɗazun kawai yake gani tana yi mashi gizo. Sam bai san lokacin da ya furta sarkin rigima a fili ba.

Sai da ya ji voice É—in Mamma a cikin kunnuwansa ne ya gane ashe ma a fili ya yi maganar.
"Wacece kuma sarkin rigima?" Shi ne tambayar da ta yi mashi.

Ƴan kame kame ya fara yi ya rasa waye zai cewa Mamma ita ce ƴar rigimar.

Canza mashi topic na hirar Mammar ta yi, saboda ta sanya a ranta tabbas in zai fita zata bi bayansa domin ta ga menene ya canza mata yaro, ta fara tunanin ko dai ya gano wannan mum twins da yake ta yawan maganarta a baya ne a kan ta ɓata, yanzu kuma ya dai'na yin magana tata, to dole da akwai dalili.

Jansa da hira irin na uwa da É—a ta yi, cike da so da kauna yake amsa mata suna zuba hirar, sai datse mashi gashin take yi tana zubarwa.

Sai da rana ta faɗi suka shiga cikin ƙogonsu, abinci suka ci tare da namar da ta gasa masu, ya kara kyau sosai da Mamma ta datse tsawon gashin nasa ta rage mashi, sai face ɗinsa ta kara wani irin haske.

Bayan sun ci abinci ne suka ɗan taɓa hira kamar yadda suka saba kafin nan kowa ya yi nasa waje ya kwanta.

Mamma tana kwanciya ba jimawa ta yi barci, shi kuwa bai yi barci ba har dare ta tsala sosai, sai juye juye yake yi a saman gadon nasa, shi da kansa ya rasa menene ya hana shi yin barci bawan Allah. Tunaninsa ɗaya kawai shi ne ya tashi ya lallaɓa ya je ya leƙo su Pretty, su kawai yake son gani yasa ya shiga damuwa haka. Sam baya tsoron dare.

Saukar ruwan sama da ya fara gudana a cikin dajin ne yasa ya hakura da tunanin zuwa ganinsu a cikin wannan duhun dare, ya kwanta shiru yana ta tunaninsu har wayewan gari barci ta gagara. Da gari ta fara wayewa ne ya yi maza ya ɗauko abin sakar Mamma ya saƙawa Sweetie rigarta, ya haɗa kayan waje guda ya ɓoye da nufin anjuma in ya fita zai kai masu!.

Da safe kamar yadda suka saba idan suka tashi daga barci haka suka yi, Mamma ta dafa masu abin da zasu ci, ba komai bane face gasasshen nama da kuma ruwan gayyayakin tea masu inganci da ƙara lafiya a jiki. A cikin tea ɗin Kamran sai ta sanya mashi wani ganyen magani green color, kasancewar da zuma suke haɗa tea ɗinsu ba sugar ba, sai yazama ruwan tea ɗin nasu ya yi wani irin orage color mai ɗan duhu, ganyen shayin da suke amfani da shi ya kasance ja ne sosai, so idan suka zuba zuma sai ya ɗan dishashe karfin jan ya ɗan yi kamar orage color, suna da yelwar zuma sosai a cikin dajin, Kamran ne mai ciro masu Mamma kuma ta tace ta zuba a mazubi mai kyau ta ajiye masu suna amfani da shi, zuman da babu mix ko ɗigo a ciki, su ina ma suka san anayi mata mix? Ina suka ga sugar a cikin wannan daji? Ai babu ita.

Kamar yadda suka saba yin breakfast bayan sun yi wanka cike da so da kauna haka suka yi yau É—in ma, suna gamawa Kamran ya ce mata zai je cikin daji yawo, ba tare da jan mashi rai ko ta ce ba zai je ba ta amsa mashi da sai ya dawo ya kula da kansa.

Cike da murna ya nufi ɗakinsa domin ya shirya, ya ɓoye Kayan da ya sakawa su Pretty a jikinsa sannan ya fito ya nufi waje. Da ido Mamma ta bishi har sai da ya fice, sannan ta fara bin bayansa a sese'sese domin taga ina ya nufa.

E TO LALLAI AKWAI CAKWAKIYA, BARI DAI MU JE MU DAWO.

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

KINGDOM OF POWER 💪🔥

Zaune Gimbiya Zunaira take a cikin katafaren lambun da yake a cikin family part.

Zaune take a saman ɗaya daga cikin wasu haɗaɗɗun chairs da suke a wajen da aka tanada dan zama a cikin lambun, an kawata wajen sosai da sosai, ga wani irin iska mai matuƙar daɗi da yake kaɗawa a wajen, iska ne ba mai sanyin cutarwa ba, ɗan dai'dai.

Ta tsantsara kwalliyarta cikin shiga ta alfarma ta Æ´aÆ´an manya manyan sarakuna da ake ji dasu, wata shegiyar Dubai gown ce a cikinta launin pink color, rigar ta sha kyau har ta gaji, yanayin tsarin rigar ya yi kama da masu tula tulan breast ne kamar su Gimbiya Chuchu, dan rigar yana da breast part a jikinsa duk da ba mai girma bane, ita Zunaira yanzu ma ta fara kirgan dangi, amma ta sanya shi a jikinta, hakan kuma ya samo asaline saboda tsawon da take da shi, tsawonta ya fi shekarunta, hakan yasa ake saya masu kaya dai'dai girman na su Chuchu, dan shi ne yake yi mata dai'dai tsawon, da kaÉ—an Chuchu ta fita tsawo, to kun ji in da matsalar take.

Ta yi shiru tana kallon kyawawan tsuntsayen da suke a cikin ɗan kejin dake kusa da ita, irin kananan tsuntsayen nan ne waɗan da suke three colors, akwai brown, akwai blue, sannan yellow, haka kalarsu yake, suna da matuƙar kyau da ɗaukar hankali, ƴan kanana da su.

Cikin takun jarumta Hoorain ya shigo cikin wajen. Tun daga bakin kofar lambun ta tsare shi da waɗan nan kyawawan fararen hazel eyes ɗin nata tana kare mashi kallo yadda yake taka ƙasa cikin zafin nama, yana shirye cikin kayan yakinsa, hannunsa na rike da wani ɗan ganye kamar flower yana ɗan murzawa. Ga wata shegiyar sharɓeɓiyar takobi a ƙugunsa.

A kusa da ita ya zo ya tsaya tare da É—an sirinar da kai ya furta.
"Sannu da hutawa ranki ya daÉ—e". Cikin harshen larabci ya yi maganar.

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ɗan saki ƙayatattcen murmushi mai kara fito da tsantsar kyanta tare da faɗin.
"Waye ya gaya maka ina nan Hoorain?".

Ƙara yin kasa da kansa kaɗan ya yi kafin ya bata amsa da cewa. "Abbie ne ya faɗa mun".

Idan ba ka kasa kunne sosai ba ba zaka taɓa jin me Hoorain yake faɗa ba idan yana magana, in a low voice sosai yake magana ɗan tahaliƙin nan, kamar baya son motsa laɓɓansa.

Da yake ita auta ta saba da shi sosai, dan tun tana karama take tare da shi, sai ta saba da maganar nasa, ko yaya zai yi magana tana iya gane me ya faɗa kuma tana jinsa, ita tama saba da jin magana ƙasa ƙasa sosai ai, ga Yah Jaish da Yah Jawad ma, wannan ba shi bane farau.

"Kai Abbie ya cika sa ido, yaushe wai ya ganni na fito har ya gaya maka".
Ta faÉ—a tana turo baki.

Bai amsa mata ba, dan bai san me zai ce maya ba, shi ba wani iya surutu ya yi ba, idan ka gansa yana magana ma to ka kan yaki ne da sauransu, bayan haka baya wata magana, ko da mahaifinsa commander ZAFAR wato wanda ya kira da Abbie yanzu basa hira, ko dare ne basa wani hira a tsakaninsu, dukkansu sarakan shiru shiru ne, kuma a tare suke kwana, basu taɓa rabuwa, suna manne da juna, amma ba zaki taɓa jin suna wani hira mai tsawo ba, daga tambaya sai amsa kawai ne a tsakaninsu.

"Hoorain kai kullum idan muka haÉ—u sai na ce maka ka zauna ne?".
Ta faɗa tana mayar da kallonta izuwa kan Gimbiya Chuchu da ta shigo cikin lambun a yanzu, kafa ya ɗan sami sauki, sai wani turɓune fuska take yi kamar wadda aka yi wa dole ta zo wajen, tana sanye da kaya irin na jikin Autar, sai dai ita ta ɗaura kyakkyawar alkyabbarta a saman kayan, ita kuma auta bata ɗaura komai ba, sai ɗan ƙaramin lallausan hula da ta sanya a kanta ta rufe arab hairnta.

Ganin bai amsa mata bane yasa ta sake ce mashi. "Hoorain ka zauna mana".

Cikin girmamawa ya karɓi umarnin nata tare da zama a saman ɗaya daga cikin kujerun da suke a wajen in da take zaune ita ma kenan, wasu irin chairs ne masu bala'in kyau a wajen, a baya idan ta ce mashi ya zauna sai dai ya ce zai zauna a ƙasa, ita ta hana shi zama a ƙasan, ta gaya mashi da shi da su duk ɗaya ne a wajen Allah, dukkansu mutane ne halittun Ubangiji, babu wanda ya fi wani a duniya sai wanda ya fika tsoron Allah, dan haka ita idan yana son su shirya kada ya kara zama a ƙasa, ya zauna a in da take zaune ita ma, hakan yasa yanzu idan ta ce ya zauna sai ya zauna a in da ta zauna ita ma, dan kada ya ɓata mata rai.

A kusa da su Gimbiya Chuchu ta ƙariso ta zo ta zauna, sai turo baki take yi kamar wadda aka yi wa wani abin, da ace Sarina ce ta shigo wannan waje kuma ta sami Hoorain zaune a saman irin chair ɗin da auta take zaune, da rashin mutuncin da zata yi mashi kare ma ba zai shinshina ba, sai ta zagesa fes, sannan ta buga mashi warning a kan kada ya sake, kuma ya sani shi ɗin bawansu ne, a karkashinsu yake, dole a kasansu zai zauna ba wai ya jera da su ba. Amma da yake gimbiya Chuchu ce, sai bata wani damu ba, bama ta bi ta kansa ba, zama kawai ita ma ta yi.

"Aunty Chuchu meyafaru naga kina ɓata rai ne?". Cewar auta.

Kara tsuke É—an bakin nan ta yi kafin ta ce. "Ni da Yah Jawad ne mana, na je wajen daddy yanzu dan na roke shi zan je Dubai, shi ne Yah Jawad wai na tafi daga nan babu in da zan je, kamar shi na je tambaya".

"Yauwa kin ma tunaninmun bari na je wajen Yan Jaish ya gaya mun ya gama tunanin da zai yi, nima dai ina son zuwa Dubai É—in ne ai"
Ta kai karshen maganar tare da yunƙurawa ta miƙe.

"Jirani mu fita tare, daga nan na wuce wajen Akka, Allah zan je na gaya mata ta sa daddy ya barni na je".

(Chuchu dai bata daddara ba zata sake kai karan Yah Jawad wajen Akka, da alama ta manta punishment ɗin ne😅 mu dai namu ido)

A tare suka miƙe. "Hoorain zan je wajen Yah Jaish, zaka jirani a nan ne ko zaka tafi?".
Ta faÉ—a tana kallonsa.

Ƙasa ya yi da kansa kafin ya amsa mata da cewa. "Yadda kika ce ranki ya daɗe".

"Auta sunana ba ranki ya daɗe ba, ko kace mun Zunaira". Ta faɗa a ɗan ƙule.

"Ai babu wanda zai kiraki da Zunaira sai mara kunya". Cewar Aunty MieMie da ta shigo cikin lambun a yanzu.

A hanzarce suka kai kallonsu a kanta, tana shirye cikin kayan masu bala'in kyau da tsada, ga wani dankareran alkyabbarta a sama, daga wuya zuwa hannunta dukka gwala-gwalai ne masu tsada ta kawata kanta da su, ga wani haɗaɗɗen ɗan kunnen hancinta na gold shi ma da ta sanya ɗan karami, sai kyalli yake yi, hakan ba ƙaramin kyau ya kara mata ba, cover irin na hamshaƙan matan sarakuna ne a kafafunta launin golden color, haɗuwa iya haɗuwa, jinin larabawa.

Da sauri auta ta taho ta faɗa jikinta tana sakin murmushi, ita ma Chuchu a hanzarce ta ƙarisa wajenta tana faɗin. "Aunty MieMie ina kika je two days?".

Rungume auta ta yi tare da sanya hannu tana shafa kan Gimbiya Chuchu ta basu amsa da. "Na je na halakci taron makarantarsu Omar da aka gudanar ne na kammala secondary school É—insu, yau na dawo".

"Shi ne Aunty MieMie baki tafi da mu ba?". Cewar Chuchu.

"Ban san kuna son zuwa ba ai, nima na wakilci daddy ne, saboda ba zai samu zuwa ba, akwai abubuwa da suka sha mashi kai sosai, uncle Abbas ma bashi da lokaci shi ne na wakilcesu duk da su uncle Rahab sun je".

Gimbiya Zunaira zata yi magana wata kuyanga da ta shigo cikin lambun a yanzu ta katsesu da cewa. "Allah ya kara sawon kwana ranki ya daÉ—e, Momma tana kiranki, wai ki je parlourn mai martaba ki sameta".

Har suna haÉ—a baki wajen tambayar waye ake kira? Dan ranki ya daÉ—e ta ce, kuma dukkansu haka ake ce masu.

"Princess Aunty MieMie ke ake kira".
Kuyangar ta basu amsa.

Shi dai Hoorain yana zaune yana binsu da kallo, sai dai ba kowa zai iya gane cewa yana binsu da kallon ba, baza ma kataɓa yin tunanin yana kallonsu ba.

Raba jikinta dana auta ta yi tare da riƙo hannunta tana faɗin su je su ji me ake kiransu. Ta yi maganar tare da riƙo hannun Chuchu da ɗayan hannunta.

Kai tsaye part É—in King suka nufa, suka bar Hoorain a zaune a wajen bawan Allah.

Sun sha madarar mamaki na ganin gabaÉ—aya family a wajen, harda su Sarina, ga Yah Jaish da Yah Jawad ma nan, dukkansu manyan suna zaune a saman tsala tsalar sofas dake a cikin parlourn, su Sarina kuwa suna zaune a saman Dubai carpet dake a tsakiyar sofas É—in, ga twins Obaid and Omaid a kusa da Gimbiya Fanan.

Cikin mutuntawa Aunty MieMie ta yi sallama tare da wucewa ta zauna a saman sofa mai zaman mutun biyu da yake a kusa da King, tare da zaunar da auta a gafenta kafin ta É—agawa su Momma gaisuwa.

Kowacce tana dake a cikin alkyabbarta, kowacce kuma tana zaune a saman nata sofar na daban, Mama ta wani tsare gida kamar hakan ce zai sa su ji tsoronta, har da Mammie Yah Jawad a wajen, kowa yana cikin shiga ta alfarma.

Gimbiya Chuchu kuma kusa da King ta zo ta zauna a saman carpet É—in, ta kwantar da kanta a saman laps É—in King É—in. Tana turo baki kamar anyi mata wani abin, sai dai rashin sa'arta na yanzu yasa ta zauna a in da suke fuskarta juna ita da Yah Jawad, da zarar ta É—ago kai shi zata fara kallah, shi ma kuma haka, sam bata lura da hakan ba har sai da ta É—an É—ago da kanta da nufin ta kalli su waye da suwaye ne ma a cikin parlourn, tana É—ago kai kawai karaf suka haÉ—a idanu da shi, a dai'dai lokacin shi ma ya É—ago idanu dan ya saci kallonta, dan shigarta ta yi mashi kyau.

Cikin sauri ta yi ƙasa da nata idanun ta fara ƙoƙarin matsawa daga saitinsa ko da kaɗan ne.
Shi ma kawar da nasa kallon ya yi izuwa kan King, ga mamakinsa sai ya ga King ɗin ma shi yake kallon, abin gwanin ban dariya. Duk sai ya ji ya tsargu kuma, sai yake ganin kamar kallon tuhuma King yake yi mashi, alhalin kuma ba haka bane, shi ma King ɗin ya ɗago ido ne kawai sai kallonsa ya sauƙa a kansa, ba wai haka kawai ya kalle shi ba.

Kamar dai wani mara gaskiya sai ya yi saurin kawai da kallonsa daga kan King É—in yana jin gabaÉ—aya a takure yake, izuwa yanzu shi da kansa ya fahimci ba iya burgesa kawai Chuchu take yi ba, sama da hakan ne, akwai dai abin da yake ji dangane da ita.

Shi kam Jaish da tun É—azun yake aikin latsa waya bai ma san me ake ciki ba.

Twins kuwa sai wani ƙus ƙus suke yi ƙasa ƙasa, wani lokaci su yi ƴar kurma kurma kamar wasu munafukai.

Gyaran murya King ya yi tare da fara yin magana a nutse. "Nataraku a nan ne kan abubuwa biyu zuwa uku. Na farko shi ne akan abin da ya faru da Sarina, abin sam bai yi daɗin ji ba, ga shi har ya saka mun ɗan uwana (uncle Abbas) ciwon kai, sam ban ji daɗin hakan ba, shiyasa na taraku domin na ja maku kunne a kan ban yarda wani ya sake zuwa wa wani daga cikinku da zancen yana son ƴaƴana har kuma ku yi mashi jagora zuwa cikin gida na wajen ƴaƴan nawa ba, ban yarda da hakan ba! Ku kyaleni idan sun kai munzalin aure ni zan zaɓa masu maza da kaina, koma ya kuke da mutun bana da buƙatar ku kawo mun shi cikin gidan nan da sunan wai yana son ƴa ta, dukka dukka ma nawa Sarinar take da Abbas zai takura kansa da zai ta yi aure? To ni bana da buƙatar irin hakan ta sake faruwa, ku kyale mun ƴaƴana su huta, sai dai ni ina tunanin wannan yaro Yusuf ba lafiya yake ba, amma dai koma menene Zafar zai yi masu abin da ya dace, wannan shi ne maganata ta farko. Ta biyu kuma Obaid and Omaid zasu koma Dubai gobe, duk da ba'a buɗe makarantarsu ba ko ma nace basu wuci sati ɗaya da yin hutu ba, amma za su koma bisa son hakan da mahaifiyarsu take yi, ta ce tana son su koma yafi mata, so zasu koma. Sai magana ta uku, Omar zai dawo nan da kwana uku, Mommynku ta buƙaci da zata shirya mashi gagarumin walima na murnar dawowarsa, na kuma bata izinin yin hakan, ina gaya maku ne domin na fita hakkin kowa".

ÆŠan dagatawa ya yi da maganar yana sauke numfashi tare da bin fuskokin matan nasa da kallo.

Shi dai Jaish har ga Allah bai ga wani abin da zai sa a kirashi cikin wannan al'amari ba, shi ba aboki yake da shi bama bare ace ko abokinsa zai ce yana son kanne nasa har ya yi mashi jagora zuwa gidan, to shi ko da ace yana da aboki ma ya isa ya yi mashi jagora zuwa neman aure ne? Wlh bai ga wanda ya isa ya sanya shi ya yi mashi jagora zuwa wajen mace ba, a ganinsa ba'a haifi mutun ba.

"Akwai wani mai abin faÉ—a ne?".
King ya katse su da wannan tambayar.

Siririn tsaki Mama ta ja kafin ta ce. "Ranka ya daÉ—e ni ina son a gaya mun menene banbancin su Chuchu da su Obaid da duk wanda Rahilarh zata haifa sai ta ce bata son ya zauna da Æ´an uwansa a nan sai dai a Dubai? Menene a gidan da nata Æ´aÆ´an ba zasu zauna ba sai namu? Ko mu namu Æ´aÆ´an ba mutane bane? Ko dai nata Æ´aÆ´an sun fi namu daraja ne?".
Da iya gaskiyarta ta yi maganar.

Ita kuwa Momma ba wani dalili bane yasa ta buƙaci su Obaid su koma Dubai face wannan matsala dai da take fuskanta a cikin gidan, kwana biyun nan tana yawan mafarkinsu a cikin wani mawuyacin hali ne yasa ta buƙaci da su koma kawai ko hankalinta zai kwanta.

(Ni kuwa na ce bama dole ki gansu a cikin mawuyacin hali ba, yara basu ji, sai dai su yi ta kwasa wa kansu alhakin mutane suna biyewa Sarina suna kwasan hakkin waɗan da basu ji ba basu gani ba, yara kamar an canza maki su lokacin da kika haifesu🤔 ai in a kansu ne ma fin haka zaki gani baiwar Allah😅)

Da yake Momma jinin Modarawa ce ba'a masu su kyale, sai ta ce da Mama ɗin. "To ai naga duk tushe ɗaya ne ko? Kina iya mayar da su Chuchu ɗin Dubai ɗin kema idan kina da buƙata, saboda suma ai kakaninsu ne a can ɗin, babu wanda ya hanaki yin haka, dan haka sai ki cire idanunki a kan rayuwata, haka nake son ƴaƴana su kasance, tun da ba ke kika haifa mun su ba kina iya jan baki ki yi mun shiru".

Akka dake zaune saman nata sofar ta wani dake tare da ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya ne ta karɓi zancen da cewa. "Idan ma baku yi haka ba ai sai na ce Zuhair ba mata ya aura ba".

Karo na farko da Yah Jawad ya ji dariya ta so ta kubce mashi, wannan tsohuwa Akka akwai iya tada bom, a maimakon ta shiga cikin lamarin ta sasanta, amma kun ji wai idan basu yi hakan bama ba mata bane.

Shi dai Jaish haushi har wuya yake ji ta iso mashi, dan shi sam baya son zama a taron mata, yasan fin haka ma zasu aikata, su yi abinsu su bar mutun da ƙuncin zuciya ba abin da ya damesu, ai mata duniya ne, kome za'ayi masu kishin nan dai yana nan, ba zai taɓa tafiya ba, kai ko cire zuciyar mace ka yi ka wanketa fes da ruwan zam zam ka sake dawo mata da shi a kan kishi gobe sai kaga wani bakin halin........😅

"Daddy zamu iya tafiya?". Cewar Yah Jawad, dan ya lura abin na mata ne take shirin motsawa, wato kishi, dan haka gara su kama kansu kada a kashesu da kuncin zuciya.

Shiru King bai basu amsa ba, ya dai zuba masu idanu yana ganin su, dama haka yake yi, sai sun yi sun gaji yaje saka baki.

"Bayan kin asirce shi ya zama ƴaƴanki kawai yake gani da daraja ta ina muke da ƴan cin zaɓarwa ƴaƴanmu in da muke son su yi rayuwa? Ai ke kaɗai ce mai wannan dama, zalunci dai komai daren daɗewa yana da karshe". Cewar Mama.

Omaid ne ya kalli Mama ɗin cikin ɓacin rai ya amsa mata da. "Mama ko Momma ta zaɓa mata in da zamu yi karatu ko bata zaɓa mana ba mu dama bamu da ra'ayin yin rayuwa a cikin kingdom ɗin nan, wajen su mai ran karfe su Uncle Rahab and uncle Abu Abdussalam muke son zama, dan haka ba laifin Momma bane, kuma..........."

Wani irin É—an iskan kallo da Yah Jaish ya wurga mashi ne yasa ba shiri ya haÉ—iye sauran maganar nashi, dan sun san Jaish ba kanwar lasa bane, ba shi bashi da hakurin Yah Jawad, yanzun nan zai sa su ji kamshin ma'aika azarailu, dan haka sai ya yi shiru tsit kamar babu shi a parlourn.

Ita kuwa Mama kallon walaƙanci ta wurgawa Momma ɗin kafin ta ce.
"Kina iya yin fin hakan ma ai, kisa yaranki basu daraja kowa".

Shiru gabaɗaya parlourn ya yi, kallon Obaid ta ƙasan ido Omaid ɗin ya yi, burinsu kawai su bar parlourn nan su je su shiryawa Mama ɗin nan wani munafurcin da sai ta yi kuka, dan wlh idan ba haka suka yi mata ba ba zata rabu masu da Mommarsu ba, shi kuma Yah Jaish zai taka masu birki, wlh ka ana ha maza ha mata basu ga dalilin da zai sa su bar wata banza tana yi wa mahaifiyarsu kutse a cikin al'amura ba, a cewarsu sun lura Yah Jaish ɗin nan baya son Momma sam sam, tun da yana zaune Mama ta zageta bai iya cewa komai ba, to su dai ba za su ɗauki wannan iskanci ba, dole kowa ya san matsayinsa a gidan, kafin su koma Dubai sai sun yi maganinta....... Hmmmm lallai akwai kura!.

Shi kuma Jaish ya ja bakinsa ya yi shiru ne saboda King yana wajen, koma dai menene yasan da cewa King zan yanke hukuncin da ta dace, kuma dama a matsayinsa na babba mai ilimi da hankali me ruwansa da faÉ—an kishiyoyi fisabilillahi? Ai wanan ba layinsa bane, amma fa sosai abin ya sosa mashi zuciya, ji ya yi tamkar ya buge Mamar sai ta sume ko ta mutu a wajen, amma ya danne saboda kannensu dake a cikin parlourn ga kuma King and uncle Abbas sannan ga Akka a kwana!.

Miƙewa tsaye ya yi ba tare da ya bi ta kan kowa ba ya nufi hanyar fita, domin idan ya ce zai cigaba da zama a wannan tattaunawa ba makawa tsab zai yi wa Mamma one slap seven death, so gara mashi ya yi gaba tun bai hasala ba.

"Where are you going Jaish?".
Cewar uncle Abbas.

Duk yadda yake kaunar uncle Abbas É—in ya kasa iya bashi amsa, dan zuciyarsa a kusa take, idan ya ce zai buÉ—e baki ya yi magana zai iya haÉ—iyar zuciya ya mutu, so sai ya yi kamar bai ji me uncle Abbas É—in yake cewa ba, a hanzarce ya fice daga cikin parlourn dan ma kada King ya dakatar da shi. Already shi kuma King dama bai yi niyar dakatar da shi É—in ba, saboda yasan halin Æ´aÆ´an nasa da zuciyar bala'i, shi kansa ya ji zafin maganar Mamar bare kuma Æ´aÆ´an Momma, ai dole abin ya sosa masu rai.

"Sarina, Fanan, auta, Jannat, Obaid and Omaid duk ku tashi ku tafi".
Cewar Aunty MieMie.

A hanzarce kusan a tare suka miƙe suka nufi waje.

Mummy kam tana zaune kamar mutun mutumi tana binsu da kallo, ita sam sam ma bata son hayaniya a rayuwarta, ba zaka taɓa jin maganarta a irin wannan abin ba, da girmar kujerarta hajiya uwargidan King Zuhair Abdul Malik ba.

King ya É—auki a kallah 5 mins yana kallonsu tun bayan fitarsu Sarina, kafin ya É—an nisa tare da fara yin magana cike da bada umarni da kuma izza.

"Kada wanda ya sake yin magana a kan hukuncin da Rahilarh ta yankewa ƴaƴanta na girmansu a hannun ƴan uwanta, kowacce a cikinku tana da damar da zata ce mun Zuhair a wajen kakaninsu nake son ƴaƴana su girma, iyayena da yayyuna haɗe da kannena sai kakanina ne fa a Dubai ɗin, me dan ƴaƴana sun girma a hannunsu? Ƴaƴana mata ne na ce bana buƙatar su matsa daga kusa da ni, amma maza ina iya turasu ko'ina su je su yi karatu, ita Zunaira da take mace ba ga shi tana gabana ba? To me wani sabon abu a ciki? Me abin ta da hankali? Bana son wannan hayaniya dukka, ba'a kan haka na taraku ba, abin da na tara ku a kai shi ne, kada ku kuskura ku gayyato mun wani cikin gidan nan da sunan yana son ƴaƴana, sannan Obaid and Omaid zasu koma Dubai gobe, Omar yana dawowa nan da kwana uku, Mummynsa zata shirya mashi walima, idan akwai wadda take buƙatar wani abin ta yi mun magana zan shiga ciki".
Ya kai karshen maganar tasa cikin nuna cewa tsantsar umarnin yake basu.

Mummy baiwar Allah, Omar dai ba ɗan ta bane, ɗan Momma ne yayan Zunaira, amma kun ji har walima ta nemi izinin shirya mashi dan zai dawo, ita dukka ƴaƴan nasu abu guda ta ɗaukesu saɓanin Mama.

"Zan iya tafiya?". Cewar Mama, da alama ranta bai so maganar da king ya yi ba sam.

Akka ce ta ce "Kowa ma zai iya tafiya a yanzu".

A hanzarce Mama ta miƙe ta yi waje, Momma ce ta biyu a fita ta rufa mata baya, sai Mummy ta uku, princess Aunty MieMie ta rufa masu baya. Parlourn ya rage daga Akka, uncle Abbas sai King. Uncle Abbas ma miƙewa ya yi tare da sanar da su zai je ya shirya dan zai koma baƙin aikinsa. Sallama suka yi ya wuce, ya rage saura Akka da King, su kuma suka cigaba da hira na tsakanin uwa da ɗa.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 5/8/2024.....✍️📚🌹

For information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________28🔥

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼

AAJ YARI.💔😥

Shiru Leesharh ta yi, gabaÉ—aya ta shiga ruÉ—ani, kanta ya É—aure, duk ta rasa me yake yi mata daÉ—i, yanzu ya zata yi?.

Dafa shoulder ɗinta da kyau Jasrah ta yi tare da fara magana cikin nutsuwa da ƙoƙarin nuna mata illar da abin da zata aikata zai haifar mata ita da danginta gabakiɗaya, dan wlh idan aka kamata ko mahaifinta da take burin take ikirarin ta koma gida ta je ta gani ba barinsa za'ayi ba, babu wanda zai iya tsira daga cikin familynta, babu wanda zai tsallakewa Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen, duk sai ya ragargazasu, to babban abin tambayar ma a nan shi ne wanenen shi wanna Ramish ɗin kam? Ya yake? Meyasa ake farautar rayuwarsa har haka da ake ƙoƙarin leƙar asirinsa? Kuma kun ji matar ta ce suna da ma'aikata a gidan, hakan na nufin ba ita Leesharh ɗin bace ta farko, kenan an jima ana sanya mashi idanun? Da alama har yanzu haƙarsu bai cinma ruwa bane yasa suka buƙaci Leesharh a wannan aiki, idan kuka yi duba da yadda matar ta ce ma'aikatan nasu a iya harabar gidan suke ba su sami damar shiga ciki ba, hakan yasa basu iya sanin me Ramish ɗin yake ciki, ita kuwa Leesharh karamar yarinya ce da ba za'a barta a harabar gida ta yi aiki ba, dole idan za'a ɗauketa aiki a can cikin gida zata yi aikin, kila ma a ta fannin kitchen ko kuma gyaran ɗaki or wani abu makamancin haka, babu wanda zai kawo wa ransa ita ɗin leƙar asiri ta zo yi, kunga zata sami damar sanin wanenen Ramish da kuma motsinsa a cikin gidan, ina ga tabbas kafin su tunkari Leesharh da wannan magana sai da suka yi gagarumin bincike a kanta, sai kuma da suka shirya sosai.

Amma kuma matsalar a nan shi ne, ita Leesharh idan ta amince ta karɓi wannan aiki da ankamata fa shikenan ita da danginta ne zasu girbi laifukan da basu suka shuka ba! Domin bata san wannan mata ba! Tab akwai cakwakiya na gasken gaske kuwa, yanzu nasu wasan kuma zai fara kenan, zamu ga wanene zai yi nasara a wannan game ɗin da za'a buga kuma!!!.

"Leesharh a wannan magana babu wani tunani da zaki yi, domin kuwa baki da wata mafitar da ya wuce ki ce mata ba zaki je ba, idan kuma kika ki, to wlh karnikan gidan Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen ne zasu cinye gawarki a ɗanyarta, kuma ki sani sun cinyeki sun cinye banza, ke bama wannan ba, wlh duk danginki babu wanda zai iya tsallakewa, babu wanda zai sha a hannun Ramish idan asirinki ya tonu, kuma yadda suke da mahaukatan cameras a gidan kin san kuwa dole asirinki zai tunu, ke ta ina ma zaki fara yin wannan aikin fisabilillahi Leesharh? To ina mai tabbatar maki ganin waɗan nan mugayen fusatattun securitys ɗin da suke gadin kan titin da zata ratsa ta shigar dake unguwar da gidan yake ma ya isa ya sanya ki saki fitsari a wando, duk rashin tsoron nan naki da ƴan gidan nan suke faɗa wlh baki ga abin tsoro bane, bare ace ki ga securitys ɗin da suke gadin ainahin gidan, ina ga daga nan zaki sume, ke ni fa ban ma yarda matar nan zata iya shigar dake wannan gida ba, gidan ɗaya daga cikin ƴaƴan the most powerful King Badeen da duniya take magana a kansa, kowa idanunsa naa kansa, ga karfin iko kamar shi ya bawa kansa, kuma defence minister da duk wani mai kaki yake a ƙarƙashinsa, sai da izininsa kaki zata motsa, lallama kam, ni dai a matsayina na ƴar uwarki ban baki goyon baya ba, ko da bamu da alaƙa ta jini addinin Musulunci ya haɗa mu mun zama ƴan uwan, kuma ba zan zuba maki idanu ina ganin abin da zai cutar dake da familynki na yi shiru ba, dole na gaya maki gaskiya koda zaki gujeni".
Ta kai karshen maganar tana mai cigaba da kallon fuskar Leesharh da tsoro ya gama bayyana a samansa sosai. Bata taɓa shiga irin wannan yanayi ba, ko lokacin da aka kawota gidan da sunan ta kashe mahaifiyarta babu irin makamancin wannan tsoro a face ɗinta, bata taɓa tsorata a cikin wannan gida ba duk da ta san hukuncin kisa ne a kanta, tasan kasheta za'ayi, amma babu tsoron hakan a ranta, yau dai ta tsorata da jin wannan irin bala'i na aikin da zata je.

"Ke fa Jasrah baki da mutunci, yanzu saboda mugunta ne kike son hanata fita daga cikin wannan gida, kina ji Leesharh? Wlh duk abin da Jasrah take faɗa karya ne, kawai bata son ki kuɓuta daga hukuncin kisa da yake a kanki ne, bata son ke kifita ita a kasheta ne, shiyasa take ƙoƙarin sare maki gwiwa, dan haka kada ki yarda, ki je kawai Allah ya bada sa'a, zamu tayaki da addu'a". Cewar Sahra dake makale a saman gado kamar wata mage........ Mugunta dai babu kyau Sahra!!.

Taɓe baki Jasrah ta yi tana mamakin irin wannan kiyayya, kiyayya ido da ido suke nunawa Leesharh babu ko sakayawa! Sai ka ce ba musulmai ba, yaran nan sam sam basu da mutunci, sun tsani Leesharh over, duk wani munafurci ƙoƙari suke yi suga sun kullah mata, su basu ki ba ma a matso da hukuncin kisan da yake a kanta ya dawo yau yau a kasheta su huta, ko me ribarsu idan an kasheta?..............🤔

"Sahra laifin me kika yi ma aka kawo ki gidan nan?".
Cewar Leesharh, daga jin yadda ta yi magana ƙasan zuciyarta ta gama karaya, gwiwowinta duk sun sage, ta tsorata sosai da wanna al'amari, ita tunaninta ma ɗaya shi ne ya zata yi ta cewa wannan mata ba zata yi wannan aiki ba ta, fasa?.

"Dole ki tambaya mana wani irin laifi ta yi aka kawota gidan yarin nan, dan na lura babu Allah a ranta". Cewar Jasrah.

Wani irin matsiyacin kallo Sahra É—in ta watsa masu kafin ta ce. "Baku kai na baku amsa ba, bani ma da lokacinku Æ´an wahala kawai".

Sahra kenan wadda ta turo yaron mai aikin gidansu daga saman bene ya faɗo ƙasa ya mutu, kuma cameras na harabar gidan nasu da wanda yake a balcony duk sun ɗauketa time da take tura yaron ƙasa, yaro ɗan ƙarami wanda bai wuci 5 years ba a duniya, abinku da yarinta, kawai dan ya ɗauki Teddynta yana wasa da shi a wajen balcony shikenan ta wurgoshi ƙasa babu imani bare tausayi, ko da yake ina zata ga imani yarinya mara kunya har haka? Shi ne laifin da ta aikata, gata da uban rashin kunya kamar wadda shaiɗan yake yi wa busar sarewa a kunne, ga shegen rai'na na gaba da ita, iyayi da manyance, ga kauɗi da rawan kai, bata ganin kowa da gashi, bata jima da shigowa cikin gidan ba, yanzu haka iyayenta suna can suna ta faman ta yadda za'ayi su fito da ita, sai faman rokar ƴan aikin suke yi da ta yafewa ƴarsu, dan ita kaɗai suka haifa, suna can suna wahala suna kashe kansu a kanta, ita kuwa tana nan tana tsula tsiyarta son ranta, da yake iyayen nata sun gaya mata ai ba za'a kasheta ba, sun kusa yin nasarar fitar da ita, shi ne nan rashin kunya ya karu sanka sanka, ta zagi uban kowa a cikin gidan babu mai tanka mata, saboda suna tsoron ruwan bala'inta, bata da mutunci, kwata kwata 15 to 16 years ke gareta.

Kawar da kai Jasrah ta yi daga kan Sahrar tare da dawo da kallonta a kan Leesharh da nufin su cigaba da maganarsu dan ganin sun samowa kansu mafitar yadda zasu yi da wannan bala'i da yake shirin tunkarosu. Bata kai ga buɗe baki ta yi maganar ba sai ga wata ganduroba tana ƙoƙarin buɗe kofar ɗakin nasu zata shigo.

Jan baki Jasrah ta yi ta yi shiru tare da bin gandurobar da kallon mamaki tare da kara tsorata sosai, saboda bata san me ya kawo matar ba, abin da ta sani dai shi ne a duk lokacin da kaga wata ganduroba to ba alkhari bane ya kawota, ammafa a nasu ganin kenan.

"Leesharh let's go".
Shi ne abin da gandurobar ta faÉ—a bayan ta gama buÉ—e kofar, ta yi maganar kuma tana wurgawa Jasrah wani irin kallo mai wuyar fassaruwa, kamar dai ba kallon lafiya ba.

Miƙewa Leesharh ta yi jiki ba kwari, ga shi babu halin ta tambaya ina zata je kuma? A tsorace take kada ace matar ce ta dawo ɗaukarta ko kuma makamancin hakan.

Ita ma Jasrah tsoro sosai ya kara bayyana a saman face É—inta, fargabarta É—aya shi ne kada ace matar ce ta zo É—aukar Leesharh É—in, sai addu'a take yi Allah yasa Leesharh ta gayawa matar ba zata je ba idan ma ita É—in ce ta dawo, Allah kuma yasa idan ta gaya mata ba zata je ba ta hakura ta kyaleta, gara masu su kare rayuwarsu a nan har izuwa lokacin da wa'adin hukuncinsu zai cika a kashesu kawai, a kan wannan aikin, dan yafi mutuwa haÉ—ari, fargaba da tsorata tare da faÉ—uwar gaba ne ma kawai zai Kasheka a gidan Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen.

Salun alum Leesharh ta wuce gaba, jikinta sai kerma yake yi, saboda tsoro, ta yi gaba matar ta rufa mata baya.

Dai'dai Leesharh zata wuce office na É—azun in da suka yi magana da matar can, wannan gandurobar ta dakatar da ita ta hanyar cewa. "Ba nan zaki shiga ba ai".

Da mamaki sosai tare da tsoro Leesharh ta juyo da kallonta a kan gandurobar.

ÆŠaure fuska matar ta yi tare da nuna mata wani hanya da yake a tsakanin wasu É—akuna na wasu yaran dake dakon lokacin hukuncinsu ya cika su girbi abin da suka shuka.

Bata da zaɓin da ya wuce dole ta bi wannan hanya, domin ko damar yin magana ma ba'a bata ba. Wucewa kawai ta yi gaba matar ta rufa mata baya, suna tafiya matar tana waige waige kamar wata maras gaskiya, da alama dai ba gaskiyar bane aka kullah. To koma dai menene mu kam namu ido, zamu so ganin wannan cakwakiya, dan da alama zai ƙayatar ya kuma rikitar tare kuma da tarwatsa ƙwaƙwalwale, ya hargitsa tunani gami da ruɗar wa!!.

Sun yi tafiya mai nisa kafin su isko wani É—an siririn hanya da yake a daf karshen wannan hanya, zuciyar Leesharh sai harbawa da karfi karfi yake yi, ji take yi kamar ta ce zata koma wajen Jasrah, amma ina babu bakin yin magana, tana tsoron gandurobobin sosai, saboda basu da sakin fuska ko kaÉ—an, kullum rai a haÉ—e kamar waÉ—an da aka yi wa wahayin mutuwa tare da lokacin da zasu mutu É—in.

Wannan kwana suka bi, suka sake tafiya mai ɗan dogon zango kaɗan kafin su isko wani kofa a ƙarshen hanyar. Wasu irin makullai matar ta ciro daga aljihunta, makullai ne masu tarin yawa sosai da a kallah sun fi guda 70, ga su kala kala.

Wanda ya fi ƙanƙanta a cikin makullan ta sanya a kofar ta buɗeta, nan take haske ya bayyana a wajen. Da mamaki Leesharh take ganin wajen.

Da akwai dogayen bishiyoyi masu tarin yawa a wajen, kowa dai yasan yadda bayan dayawan prisons suke, kamar daji daji wajen haka yake.

Da hannu matar ta nunawa Leesharh hanya a kan ta fita. Kamar zata musa taki fita, sai kuma bata ga fuskar yin hakan a tattare da matar ba, dan haka salun alum ta lallaɓa ta kama kanta ta rufawa kanta asiri ta nufi waje.

Tana fita matar ta mayar da kofar ta rufe tare da murje key É—in, sannan ta juya ta koma cikin prison É—in ta baro Leesharh a waje. To fa babbar magana!!.

Wani irin bugu da kirjinta ya yi ne yasa Leesharh bata san lokacin da ta sanya hannu ta dafe kirjin nata ba, ji take yi kamar zuciyarta zai fasa kirjinta ya fitowa waje, saboda tarin tsoro da kuma danasani na amsawa wannan mata da e zata yi wannan aiki da ta yi, ga kuma tunanin rabuwa da Jasrah! Ko sallama basu yi ba abin gwanin ban tausayi, sannan ga shi yanzu an kawota waje an barta ita kaÉ—ai.

Juyawa ta yi gabas da yamma kudu da arewa bata ga alamar wani halitta mai rai a arear wajen ba, wani sabon tsoron ne ya kara dira mata a cikin ranta. Juyowa ta yi tana kallon wannan prison door É—in, ji take yi kamar ta yi knocking na door É—in da karfi har sai an zo an buÉ—e mata ta koma ciki, dan komawarta ciki shi ne mafi a'ala a gareta. Sai dai kuma tana tsoron yin knocking na door É—in, gudun kada ya haifar mata da wani gagarumin matsala.

To wai me mutanen nan suke nufi da ita ne da suka barta a wajen gidan yarin?. Allah masani sai kuma alkalamin PRINCESS TEEMA taku ta amana.💘

Ta kai almost 10 mins tsaye katsake a wajen, ta kasayin gaba ta kuma kasa yin baya, ta rasa duk wani ƙata ɓus, tunani da tsoro duk ya dabaybayeta baiwar Allah.

"Let's go".

Tamkar saukar aradu ta ji wannan murya ta bayanta an faÉ—i ta zo su tafi. A razane ta juyo mai gabaÉ—aya.

Wata jibgeiyar hajiya ce da daloli suka yi mata mubaya'a, kuɗi suka jiƙata sharkaf ne tsaye a bayanta sanye cikin wata dakakkiyar tsadaddiyar bakar jallabiya tare da nikaf a face ɗinta, kafafunta na a sanye cikin booth mai tsada, ga wani bakin glass a face nata, kusan dai irin shigar matar ɗazun, sai dai matar ɗazun ƴar siririya ce, wannan kuma jibgegiya, tana da tsoka a jiki sosai, ta ci ta ƙoshi, wannan irinsu ake kira da hajiya two seater, masu haɗiye sofa two seater a wajen zama.

Sosai Leesharh ta ƙara razana fiye da tunanin mai tunani, sam bata ma san lokacin da ta fara kallon matar from head to toe ba, saboda ita dai bata taɓa kallon mace mai kibar wannan mata ba, wani irin kerma na tsoro jikinta ya fara yi, ta kasa koda iya ɗaga kafafunta bare ta isa ga wannan matar.

Ganin haka yasa ita matar ta ƙariso gareta tare da riƙo hannunta, ta jata da nufin su bar wajen.

Ƙasa iya tafiya Leesharh ta yi, da alama suman tsaye a wajen ta yi, yau taga tashin hankali, babban damuwarta ma shi ne kada ace shikenan an rabata da Jasrah ba tare da sun yi sallama ba, in kuwa haka ne wlh ancuceta an zalunceta, haka ake yi ne? Zasu rabasu babu ko excuse!.

Ganin Leesharh fa ba iya tafiya da kafafunta zata yi ba dan duk jikinta ya yi wani irin muguwar la'asar kamar wadda aka zarewa laka, hakan yasa wannan mata ta sanya hannu ta É—auketa cancak kamar baby ta wuce da ita!.

Kara razana Leesharh ta yi da wannan mata, duba da yadda ta É—auketa cak abinta.

Cikin wani ɗan ƙurƙuran abin hawa wannan mata ta sauke Leesharh, abin hawan anyisa kamar bayan kunkuru tare da wata ƴar runfa a samansa, ta gaban kuma kamar keƙen hawa yake. Lokacin da wannan mata ta shiga cikin wannan ɗan ƙurƙuran abin hawan sai da ta jijjiga sosai, saboda ƙibar matar nan Masha Allah kawai za'a ce. Cikin harshen larabci ta ce da mai abin hawa ya ja su tafi. Ba ɓata lokaci ya ja suka wuce. Sun yi tafiya mai nisa har sai da suka bar arear AAJ, sannan wannan mata ta buƙaci da mai wannan ƴar ƙurƙuran abin hawan da ya dakata su sauka.

Ba musu ya dakata suka sauka, ga mamankin Leesharh sai taga matar bata biya mai abin hawan kuɗinsa ba kawai ta saɓeta a shoulder ɗinta suka fara takawa da kafa. Shi kuwa mai wannan ƴar ƙurƙura ya gurgura abarsa ya kara gaba, da alama bakinsu ɗaya, duk cikin basaja ne.

Bata sake sauke Leesharh a ko'ina ba sai a gaban wasu irin jiga jigan motoci masu masifar kyau da ɗaukar hankali. Sai dai sun ɗan yi tafiya mai nisa kafin su iso wajen waɗan nan motocin, ba zaka taɓa cewa waɗan nan motoci wata alaƙa ce ta kawo su AAJ ɗin ba, ita kuwa ainahin matar da ta fara yin magana da Leesharh ɗin tana cikin AAJ ɗin tana cike wasu takardu tare da bawa shugaban gandurobobin wasu takardu da ta zo da su ta sanya hannu, da alama yarjejeniya ce a kan sun karɓi Leesharh, ga dukkan alamu takardun da matar ta zo da su daga sama suka fito, ma'ana daga manyan madafun iko suka fito. Gaskiya akwai cakwakiya ta gasken gaske kuwa, ku dai gyara zama sosai!.

Cikin ɗaya daga cikin waɗan nan shirga shirgan dankara danƙaran motocin wannan mata ta sauke Leesharh a gidan baya kenan. Idan ka kalli motocin in the first place ba zaka taɓa yin zaton da akwai mutane a cikinsu ba, saboda bakar glass da suke da shi, sannan babu wani motsi da zai nuna maka cewa akwai mutane a cikinsu.

A tunanin Leesharh dukka babu mutane a cikin waÉ—an nan motoci, sai da aka sauketa a cikin É—aya daga cikinsu ne taga wani shirgegen bodyguard, farin balarabe tas da shi sanye da face mask a fuskarsa, shi ne driver wannan mota da aka sanyata.

Ita kuwa wannan mata hajiya two seater, wata mota na daban ta shiga, tana shiga kuma ko second ɗaya ba'a ƙara ba motocin suka tashi a jere kamar abin haɗin baki. A wani irin haukace suka tashi, da wani irin mahaukacin gudu suka bar arear wajen.

Izuwa yanzu Leesharh ta gama saddakarwa da cewa lokacin mutuwarta ne kawai ya yi ba makawa, jikinta sai ɓari yake yi kamar mai zazzaɓi. Motoci guda goma ne cif dama, haka suka rinƙa sharara uban gudu kamar zasu tashi sama, kai daga gani kasan ba lafiya.

Cikin ikon Allah suka samu damar isa katafaren shinfiɗaɗiyar titin da zata sadasu da unguwar Dubai Hills Estates, a luxurious area kenan, area ce ta manya manyan shegu masu faɗa aji a faɗin ƙasar, area ce da tun farkonta har izuwa karshenta take da matakan tsaro sosai, lafiyayyun securitys masu jini a jika ne suke tsaron arear, dogayen benaye masu matuƙar haɗuwa ne a ko'ina na faɗin yankin, babu karamar gida ko ɗaya a arear, dukka gidan manyan kai ne, tsayawa zayyana maku haɗuwar wannan unguwa ma ba zai yuwu ba, ku dai kawata a ranku ya zai kasance, amma dai ya haɗu iya haɗuwa.

Tun da waÉ—an nan motocin suka danno kai cikin unguwar duk securitys dake arear suke aikin sara masu, da alama motocin gidan wani babban shegene mai faÉ—a a ji!.

Kai tsaye wani tampatsetsan gida na gani na faɗa waɗan nan motoci suka nufa, tun daga kan yanayin tsarin ginin wannan gida kasan ba na ƙananan mutane bane, gini ne da ya amsa sunansa aljarnar duniya, hawa ɗai ɗai har hawa huɗu ne ginin, ga wani irin fitillu masu haske da suka kara fito da ainahin tsantsar kyan wannan gidan.

Da akwai abubuwar kawata idanu sosai a wannan area da kuma wannan gida da waÉ—an nan mutane suka shiga da Leesharh, dan idan ka tsaya kalle kalle ma sai ka kwana ka wuni baka yi abin da ya kawoka ka wuce ba, saboda haÉ—uwa ta ko'ina fa ya haÉ—u.

Kai tsaye tampatsetsan harabar parking space na gidan motocin suka nufa. Izuwa yanzu Leesharh ƙwaƙwalwarta ta dai'na gane mata komai, ta daina ɗaukar komai, sai dai ido kawai take bin ko'ina suka gifta da shi.

Suna kashe motocin wasu mata guda biyu da suke sanye cikin jallabiyas dark blue har ƙasa, da kuma nikaf a face nasu suka ƙariso wajen motocin. Tamkar sun san motar da Leesharh take a ciki, ita kawai suka nufa, suna zuwa ba ɓata lokaci suka ɓalle marfin motar suka buɗe, ɗaya daga cikinsu ne ta roki hannun Leesharh ta fito da ita.

Suna fito da ita kuma waɗan nan motoci suka sake tashi ba ɓata lokaci suka bar wannan gida tare da hajiya two seater a ciki, ita bata fito ba.

Cikin katafaren gidan suka nufa da Leesharh da ta zama kamar mutun mutumi, bayan idanu da kuma numfashinta babu wani abin da yake motsawa a jikinta baiwar Allah, sai jan kafafu take yi ta bisu izuwa cikin, suma sai jan hannayenta kawai suke yi, basu da karfin iya ɗaukarta, dan ƴan sirara ne su ɗin ma, basu da wani ƙiba saɓanin hajiya two seater, hakan yasa suka jata izuwa ciki kawai.

Duk wata mace da zaka gani a cikin wannan gida to tana sanye da nikaf, duk da cewa hakan kusan ɗabi'ar wasu dayawan larabawan ne, amma su waɗan nan nasu akwai ayar tambaya sosai. Mata sosai ne a cikin gidan, sai ayyukan gabansu suke yi, babu mai kula wani!. Lafiyayyun securitys ne masu gadin wannan gida, daga gani kasan gidan wani shegen ƙusa ne a ƙasar.

Kai tsaye wani haÉ—aÉ—É—en elevator suka nufa da Leesharh, hawa na karshe suka haura da ita. A wani katafaren luxury parlour suka dakata, parlourn ya ji komai na more rayuwar É—an adam.

Wata hamshaƙiyar macece take zaune a saman sofa set mai matuƙar kyau da laushi, ita ma sanye take da wani haɗaɗɗen jallabiyarta launin white color, sannan ga nikaf a face ɗinta ita ma, baka iya ganin komai nata face yatsun hannayenta da suke farare kal kal kamar madara, kafafunta ma na sanye cikin safa baka, iya yatsun hannun ne kawai a waje.

A gabanta waÉ—an nan mata suka kawo Leesharh suka zaunar, sannan suka sanya kai suka nufi waje ba tare da sun furta ko uppan ba.

Wani irin kerma da jikin Leesharh yake yi ne yasa hankalin wannan mata gabaÉ—aya ya karkata izuwa kanta. ÆŠan kyafta idanunta ta yi alamar tana son tabbatarwa shin da gaske ne take ganin jikin Leesharh na kerma haka?.

Ganin da gaske ne yasa ta É—an yi gyaran murya, cikin harshen larabci ta fara magana. "Yunwa kike ji ne A'isha? Naga jikinki na kerma".

Jin muryar matar tare da jin yadda ta ambaci ainahin sunanta yasa Leesharh ta kara tsorata sosai, sai kuma a yanzu ta sami dama tare da jin cewa zata iya yin magana, ta É—an ji kwarin gwiwa kaÉ—an, a ruÉ—e take faÉ—in. "Dan girman Allah ku mayar da ni AAJ, wlh ni nafasa yin wannan aiki, ba zan iya ba, ku mayar dani wajen Æ´ar uwata Jasrah". Magana take yi amma bata san me take faÉ—a ba, saboda a tsananin ruÉ—e take, tana magana tana zaro waÉ—an nan dara daran idanuwan nata.

Daga ta bayanta ta ji wata murya mai kamar saukar aradu ya daki dodon kunnuwanta tana cewa. "A'isha Aliyu Haidar, calm down mana, menene abin ruÉ—ewa da tada hankali har haka?".

A matuƙar razane ta juyo da kallonta izuwa wajen da wannan murya ta fito. A hankali matar take saƙo kafarta tana taka haɗaɗɗen tiles na floor ɗin kamar bata son takawa, daga ɗaya daga cikin bedroom da suke a cikin parlourn ta fito, sanye take da wasu kananan kaya da suka kama jikinta sosai, wandon jeans fari tas da ƴar riga mai karamar hannu, ta ɗaura after dress a saman kayan, sai dai bata ja zip ɗin after dress ɗin ba, ta barshi ana ganin kayan da yake a ciki, ga wani munafikin nikaf da yake a face ɗinta.

A ruɗe Leesharh ta miƙe tsaye jiki na kerma ta fara faɗin. "Yauwa Aunty dan girman Allah ku mayar da ni AAJ, wlh ni ba zan iya wannan aiki ba, tsoro nake ji". Tana magana tana zaro idanu kamar an tare ɓera a lungu, dama ga idanun nata dara dara ba'a magana, duk wanda ya ganta a wannan hali da take a ciki sai ya tausaya mata, dan ta ruɗe sosai baiwar Allah, tana tsaka mai wuya. Duk da a AAJ wannan mata da nikaf ta je wa Leesharh, hakan bai hana Leesharh ta iya gane ta ba ta hanyar jin muryarta, sarai ta gane wannan mata da ta yi magana a yanzu ita ce ta je wajenta a AAJ, shi ne ma yasa ta miƙe a ruɗe take sanar da ita cewa ita ta fasa yin wannan aiki.

"Very very sharp brain little girl! Gaskiya Leesharh kina da ƙwaƙwalwa, a cikin nikaf kika kalleni a karon farko, haka zalika yanzu a karo na biyu ma a cikin nikaf muka haɗu, amma kin iya gane ni? Abin da mamaki kuma is so nice, wonderful and interested, hakan ya kara tabbatar mun da zaki iya yin wannan aiki, saboda kaifin brain ɗinki".
Matar ta yi magana cikin wani irin salo da ɗan adam ba zai iya fassara wani irin hasashe ko kuma kudurine a cikin zuciyarta ba, komai kaifin ƙwaƙwalwarka ba zaka gane ina suka dosa ba, saboda yadda suke fitar da magana sai sun taunata sosai da sosai suke sakinta, daki daki one ofter the other.

"Aunty please ki tausaya mun, wlh ba zan iya wannan aiki ba, na fasa yi, ki ji tausayin maraicina". Ta faɗa hawaye zafafa suna bin ƙuncinta, sai a yanzu ta sami damar yin kwallah baiwar Allah.

Sheeeee. Matar ta furta tare da sanya yatsarta ɗaya a saman lips nata dake cikin nikaf, a hankali ta ƙariso gabar Leesharh ɗin.

"Leesharh why are you suffering yourself for what you know you have to do it, tun da kika amsa zaki yi wannan aiki har kuma kika bari muka gaya maki wani irin aiki ne to fa dole sai kin yi shi! Babu wanda ya taɓa jin sirrinmu kuma ya ce ba zai yi aikin ba, kin yi kaɗan". Cewar wannan hajiya da take zaune.

My people's ina da wani tantama, anya idan Leesharh Allah yasa ta kammala masu wannan aiki ba'a kamata ba asirinta bai tunu ba ta tsira daga gidan Sheikh Abu Abdussalam bin Badeen da ranta su zasu barta da ranta kuwa? Ga dukkan alamu sun nuna duk wanda ya ji sirrinsu baya rayuwa, to kenan ita Leesharh me makomarta idan ta yi wannan aiki ta kuma samu nasarar kammalawa lafiya ba'a kamata ba? Kunga kuwa ita dai ta ji sirrinsu, ta ji komai, idan wani abin ya sami Ramish ma ta san sune sila. Shiyasa fa na ce maku wlh akwai cakwakiya da yaki ba kaÉ—an ba a part É—in su Leesharh É—in nan.

Riƙo hannunta wannan mata da ta je wajenta a AAJ ta yi, a saman sofa ta zaunar da ita tare da cewa.
"Mummy ki bari na yi magana da ita mana, kada ki saka baki please, ai zata yi. Leesharh kina ji ko? Ki saki jikinki, anjuma wadda zata koya maki aiki da abubuwan da suka dace dan ki yi basaja da kyau zata zo ta fara koyar dake komai, zaki zauna a gidan nan a kallah one to two weeks kina koya, sai kin goge sosai zamu san ta yadda zaki shiga gidan Sheikh Abu Abdussalam, kada ki damu babu wani abin da zai faru kamar yadda na gaya maki tun farko, ai na gaya maki zan kula dake koda kina a gidan Sheikh Abu Abdussalam É—in ne, kin manta na ce maki muna da ma'aikata a can gidan ne? To kada ki damu babu abin da zai sameki, ki saki jikinki, na yi maki alkawarin lafiya lou zaki koma gida wajen Æ´an uwanki tare da É—imbin dukiya mai tarin yawa da zaku je ku gina rayuwarku ta inganta".
Tana zuba kalaman yaudarar tata zuciyarta na fargabar jin amsar da Leesharh É—in zata bata.

"Aunty ni wlh ba zan iya ba, tsoro nake ji, dan girman Allah ki mayar dani wajen Æ´ar uwata Jasrah".
Tana magana har wa lokacin hawaye na cigaba da bin ƙuncinta, zara zaran gashin idanun nan nata sun jike sharkaf da hawaye, idanun nata sun yi jajir da su gwanin ban tausayi.

A dake wannan hajiya dake zaune saman sofa wadda wannan matashiyar mata ta kira da mummy ta ce. "A'isha kina son Aliyu Haidar ko baki son shi?".

A ruÉ—e kuma a hanzarce Leesharh ta amsa masu da. "Wlh Aunty in son babana sosai kamar yadda shi ma yake sona".

"To in dai kina son Aliyu Haidar dole sai kin yi wannan aiki, idan ba haka ba zaki rasashi rasawa ta har abada".

Ƙara ruɗewa sosai Leesharh ta yi, cikin tsananin tashin hankali ta kai hannu ta dafe saitin zuciyarta da yake harba mata pat, pat kamar zai fasa kirjinta ya fito, ba komai bane ya hassasa mata hakan face tsoro.

"Aliyu Haidar yana hannunmu, ba kuma zamu sake shi ba har sai kin kammala mana aikin mu, abu ɗaya idan kika saɓa mana ki sani a jikin babanki zamu fanshe".
Hajiyar ta sake yin wannan magana cike da iya gaskiyarta.

A ɗan shagwaɓe wannan matashiyar matar ta ce. "Why now mummy? Ai da kin barni da ita ma zata yi aikin ba sai kin saka baki ko kin gaya mata babanta yana a wajen mu ba".

"Ki ɗauketa ku bar parlourn nan, bana son na sake ganinta har sai an gama koya mata komai idan za'a kaita gidan Abu Abdussalam sai mu yi bankwana". Cewar Hajiya, tana kai karshen maganar kuma ta miƙe ta nufi ɗaya daga cikin bedroom da suke a cikin parlourn.

Binta da kallo wannan matashiyar matar ta yi har sai da ta shige ciki, sannan ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da miƙewa tsaye, cikin mutunci ta riƙo hannun Leesharh ɗin a kan ta zo su tafi ta kaita
room É—inta.

Bata da wani zaɓin da ya wuce ta bita, dan tun da ta ji furucin wannan hajiya a kan babanta sai ta ji ta sanyawa ranta dole zata yi wannan aiki, dole ta aikata shi ko dan ta tsiratar da rayuwar mahaifinta da shi kaɗai ya rage mata a duniya.

Ni kuwa na ce to Allah yasa idan kin kammala aikin su cika maki alkawarinsu na sake ku ku koma ƙasarku lafiya ke da baban naki, amma fa akwai cakwakiya, ace irin wannan tampatsetsen gida da dollars ta zauna masu sosai ɗin nan ne suke neman leƙar asirin wani? Daga gani kun san ba dan kuɗi zasu yi hakan ba, dole sai dai ransa ko wani abin makamancin hakan, da alama mummunar gaba ce a tsakaninsu, dole akwai abin da Ramish ɗin nan ya aikata masu da suke neman ɗaukar fansa, to koma dai menene lokaci zai nuna mana...... Mu dai bari mu leƙa FOREST mu dawo, wata kila kafin nan hankalin Leesharh mu ya ɗan kwanta, baiwar Allah marainiyar Allah duk da bamu san asalinta ba.

🏞️FOREST🏞️

Tafiya Kamran yake yi cikin jarumta, amma kuma zuciyarsa na raya mashi kada ya je wajen su Pretty, haka nawai ya tsinci kansa da zargin cewa Mammarsa ta biyo bayansa. Kawar da wannan zargin ya yi daga zuciyarsa, dan yana ganin kamar karya ce kawai, ba dai'dai bane, Mamma ba zata biyo bayansa ba.

Ƙara tsanan ta mashi zargin hakan zuciyarsa ta yi, lokaci guda ya ji jikinsa ya mutu da tunkarar wajen na su Pretty, da yake yana da kaifin ƙwaƙwalwa ya kuma san wacece Mamma, sai ya fara tunanin irin tattaunawar da suka yi da ita jiya da kuma yadda aka yi yau daga ce mata bari ya je cikin daji babu musu ba komai ta amince, ita da wani lokaci sai sun kai ruwa rana take aminta ta barshi ya fita, amma yau kai tsaye ba wata kwana kwana or ƙunbiya ƙunbiya ta ce ya je kawai? Dole akwai abin da take shiryawa.

Tuna hakan ne yasa ya canza hanya daga kan hanyarsa na zuwa wajen su Pretty izuwa wata hanya ta daban. Yana tafiya yana kasa kunne yadda ko zai jiyo motsin Mamma a bayansa. Amma shiru bai jiyo ba, kuma yaki yarda ya juya baya dan kada idan ta biyo shi ma ta gane ya fahimci tana binsa, hakan yasa ya samu waje a ƙarƙashin wata itaciyar ɓaure ya zauna tare da ɗan jinjina da jikin itaciyar.

Laɓewa Mamma ta yi a can nesa da shi in da take iya hangosa daga wajen, ta laɓe tana kallonsa yadda ya jingina da jikin itaciyar tare da lumshe idanu. Shiru ta ɗan yi tana tunanin dama nan wajen yake zama kenan?....... Wannan shi ne ɗan na gada ya fi ɗan na koya, yau Kamran ya yi wa Mamma wayo duk kaifin ƙwaƙwalwar tan nan, tab akwai cakwakiya kuwa duk ranar da ta kama shi tsamo tsamo a wajen su Pretty, ina ga daga ranar rabasu zata yi, kuma da wuya idan bata koresu daga cikin Forest ɗin ba, dan ita fa bata da ɗigon tausayi a ranta.

Almost 20 mins suna a haka, daga karshe dai tsabar basaja da iya waskiya na Kamran harda kwanciya, ya karkata ya gyara ya kwanta a wajen, domin tun zamansa a wajen ya hango Mammar tasa a can bayan itaciyar da ta laɓe, yaga kayan jikinta, amma bai ga face ɗinta ba, shi ne har da kwanciya dan ya tabbatar mata da shi babu in da yake zuwa.

Sanɗo Mammar ta fara yi tana son ta lallaɓa ta koma wajen kogonsu tun da taga babu in da yake zuwa. Tana sanɗo yana kallonta da mamaki, tunani ɗaya kawai yake yi yadda aka yi wannan tunani na tana bin bayansa ya faɗo mashi a cikin ransa, kullun yana zuwa wajen su Pretty, amma bai taɓa jin irin wannan zargin a ransa ba sai yau, ga shi shi bai san Allah ba bare ya ce Alhdulillah, sai dai kawai ya miƙe cikin sanɗo ya fara lallaɓawa zai je ya leƙa ko Mammar ta yi nisa.

A hankali yake tafiya har izuwa bayan wata itaciyar mangoro ya laɓe, yana ganin Mammar tasa har sai da ta kurewa ganinsa, sannan ya sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da juyawa da sauri ya bar wannan yankin.

Kai tsaye wajen su Pretty ya nufa abinsa, sai dai yana tafiya yana fargabar kada ace ita ma Mamma wayo ta yi mashi ta yi kamar ta koma alhalin bata koma ba, ta bari ne taga ko zai je wani waje. Yana tafiya zuciyarsa na harbawa cike da tsoro.

Ko da ya isa wajen su Pretty É—in ma sai da ya jima a tsaye a waje kafin cikin sauri kuma cikin dabara ya buÉ—e ramin nasu ya afka ciki a hanzarce.

Zaune ya isko Pretty a saman dutse ta buga uban tagumi, ita kuma Sweetie tana kwance a saman bed. Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da idanuwansa suka sauka a kansu, Allah ya gani yana kaunar yaran nan sosai da sosai, jinsu yake yi har cikin ransa.

Ya ɗan ji wani irin ba daɗi a ransa na ganin Pretty zaune ta buga uban tagumi saɓanin yadda ya saba samunta a kullum cikin nishaɗi da annasuwa.

Jin motsin mutun yasa Pretty ɗago da waɗan nan idanun nata ta bi hanyar shigowa da kallo, ganin cewa shi ne yasa ta miƙe a hanzarce, kana ganin face nata kasan a matuƙar tsorace take. Da sauri ta nufe shi tun kafin ya ƙariso, tana zuwa kuma ta faɗa jikinsa tare da sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.

Miƙewa zaune ita ma Sweetie ta yi, baiwar Allah da yake bata gani sai ta fara cewa. "Pretty meyasa kike sake yin kuka kuma? Ko dai mutanen ne suka biyoki har cikin nan mun shiga uku?". A ruɗe ta yi maganar, daga jin muryarta kasan ta sha kuka ta ƙoshi.

Sosai Kamran ya ruɗe tare da shiga tashin hankali na ganin Pretty tana kuka ita kuma Sweetie daga jin voice ɗinta kasan ta sha kukan ne har ta ƙoshi.

"Pretty what happened? Why are you crying? Please stop this crying and tell me what happened". Ya yi maganar cikin tsananin damuwa, dan a yanzu ya fi shiga damuwa idan aka taɓasu sama da idan aka taɓa shi, ya fi shiga ɓacin rai idan su suna cikin ɓacin rai sama da ace idan shi ne ransa ya ɓaci.

Jin zazzaƙar voice ɗinsa yasa Sweetie sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da lumshe idanuta kamar wadda aka jefa a cikin ruwan sanyi a sahara mai tsananin zafi.

"Pretty talk to me now?". Ya yi maganar a hankali sosai.

Cikin kuka ta amsa mashi da cewa. "Ba waɗan nan mutanen da ka yi faɗa da su ranar bane na je ɗebo mana ruwa a ƙoramar nan suka kamani".

Zaro idanu waje ya yi, a hanzarce ya ce mata. "To da suka kamaki sai me ya faru? Ya aka yi kika kuɓuta daga hannunsu har kika dawo nan?". A ruɗe ya yi maganar.

"Wannan mutumi mai rufe fuskar ne wanda ya taimakemimu ranar ne ya zo ya kashesu dukka, sai ya ce mun na gudu na tafi, na gudu shi kuma ya fara faÉ—a da su".

"Ina mutu min yake?". Ya tambayeta cikin ƙaguwa.

"Nima ban kara ganinsa ba ai, daga ya ce in gudu shikenan na gudu na dawo, ban san ya suka kare ba".

Sarkin tsoro ta tsorata ne sosai, dan a wannan karon kamata suka yi zasu tafi da ita, ta je ɗebo masu ruwa, su kuma mayakan sun je wajen domin dawakansu su sha ruwa suma, shi ne suka ganta, sai suka kamata, wannan mutu da ya taimaka masu ranar ne yau ma ya zo ya taimaketa ya kuma ce ta gudu, shi ne ta gudo ta dawo. Toh fah! Ko waye wannan mutumi? Wannan sai alƙalamina ne kawai zai warware maku wannan cakwakiya, kedai kada ki bari a baki labari, yanzu labari zai fara ɗaukar zafi.

Rarrashinta Kamran É—in ya fara yi yana É—an bubbuga bayanta a hankali a kan ta yi shiru to tun da ta samu ta tsira. Sarkin son jiki, kara kwanciya mashi a jikinsa ta yi tana tunanin yadda waÉ—an nan mayakan suka damko gashin kanta, da yake tana nan Æ´ar piritu ba nauyi sai suka É—agata da gashin kai saboda rashin imani, yau ta ga bone ai Æ´ar kaniya, shi ne yasa ta tsorata sosai.

Da kyar Kamran ya samu ta yi shiru, sai dai bata tashi daga jikin nasa ba, ta cigaba da kwanciyarta a saman kirjinsa tana mai da numfashi. Daga Kamran har su Prettyn dukkansu fa babu wanda yake tunanin yana da uba a cikinsu, dan dukkansu uwa kawai suka buɗe idanu suka kallah, basu san da ma cewa sai mutun biyu bane suke haifan ƴaƴa, su dai kawai iyayensu mata suka sani, basu san me aure ba, kuma basu ma san a cikin ciki mahaifiya yaro yake rayuwa har izuwa wata tara a haifesa ba, duk basu san wannan ba, saboda idan kuka yi duba da yanayin yadda suke dukkansu basu da kanne bare ace sun san lokacin da mahaifiyarsu take da cikin kannen nasu, duk basu san wannan ba, gara ma shi Kamran ya yi karatu wajen Mamma, amma fa ba ta wannan fannin ya karanta ba, ya dai san abin da ya sani, kuma ya taɓa kallon wani maharbi yana wucewa rike da ƙaramin yaro a hannunsa, a nan ne ma ya fara sanin ashe akwai kananan yara a duniya, shi da duk a tunaninsa kowa da girmansa kamar yadda ya yi wayo ya gansa da girmansa a tunaninsa kowa a haka yake zuwa duniya......... Da kuwa an shiga uku😅

Su Pretty sune mutane na uku da ya taɓa gani suna kanana a rayuwarsa, su kuwa su Prettyn basu taɓa ganin kananan yara ba, shi kawai suka sani sai mum ɗinsu, sai kuma yanzu da suke ganin waɗan nan warriors ɗin time to time, shiyasa kuka ga dukkansu suke a haka, basu taɓa yin tunani ina iyayensu maza ba? Ba su taɓa yin wani tunani makamancin hakan ba........ E lallai akwai cakwakiya kuwa, ko waye zai koyar dasu sanin hakan?.....🤔

Sweetie da take a saman gado ne ta ce. "Kamran sannu da zuwa".

Sai a lokacin ya kai kallonsa a kanta, amsa mata da yauwa ya yi kafin ya ɗaura da cewa. "Pretty sakeni bari na je na duba wannan mutumi a wajen ƙoramar ko? Ko zaki rakani?".

A hanzarce ta fara girgiza mashi kai alamar ita ba zata je ba. Hannu ya kai ya É—an shafa lallausan gashin kanta da yake bakin kirin ta É—aure shi kashi biyu gwanin birgewa kafin ya ce. "To bari na je na dawo, na kawo maki wani kyauta, ki jirani ko?".

GyaÉ—a mashi kai kawai ta yi ba tare da ta amsa ba.

Raba jikinsu ya yi tare da juyawa a hanzarce ya nufi waje, ita kuma ta yi maza ta koma saman gado tare da kwanciya ta tada kai da cinyar Sweetie tana goge hawayen nata.

Kai tsaye wajen ƙoramar Kamran ɗin ya nufa ba tare da tsoro ko shakkar komai ba, cike da jarumta tare da fata da kuma yakinin son ganin wannan mutumi ya nufi wajen. Yana ƙarisawa wajen ya wani ja uban birki babu shiri, a razane ya zaro fararen idanuwan nan nasa waje kamar zasu faɗi ƙasa........

Bamu fara komai ba, dan har yanzu ba mu kai ga nemo RAWANIN ZALINCI ba tukun nan, yanzu labarinmu zai fara, ga Leesharh ta baro gidan AAJ babu shiri, ya Jasrah zata ji a ranta idan ta ji shiru Leesharh bata dawo ba? Shikenan sun rabu kenan? Wani irin rabuwa ne wannan mai tsananin ciwo haka? Leesharh dai zata yi aikin dole domin ta ceci rayuwar mahaifinta, ya kuke tunanin zata gudanar da wannan aiki? Shin asirinta zai tonu a kamata ne ko zata yi nasarar kammala aikin? Idan ta kammala waɗan nan unknown mutanen zasu cika mata alkawarin da suka ɗauka mata na sakar mata babanta da kuma maƙudan dukiyar su kuma mai da ita ƙasarsu?.

WAJEN SU KAMRAN. Ya kenan idan Mamma fifikon wayo ta nunawa Kamran ta yi kamar ta koma alhalin bata koma ba? Ya makomar su Pretty, su waye su? Ina ne usulinsu? Ina mum É—insu? Suna da uba ko babu? Meyasa ake farautar rayuwarsu kamar yadda ake kafautar ruwan sanyi a sahara mai tsananin zafi?.

KINGDOM OF POWER meyasa Momma take fuskantar barazana a cikin masarautar?. Meyasa Mammien Yah Jawad bata son shi a tare da Gimbiya Chuchu? Meyasa da Mamma da Mammie ɗin dukka suke kamar ƴan leƙen asiri a cikin kingdom ɗin? Ya makomar su Yusuf? Me su twin's Obaid and Omaid zasu ƙullawa Mama?.

GIDAN SU KHADIJA. ya makomar rayuwarsu a yanzu? Maman Zainab ya tabbata ta je wajen boka? Shin idan ma ta je zai sa a fasa auren baban Zainab da kuma Haidar and Khadijah? Zai sa su maman Haidar É—in su fara sonta ne?. Kai akwai tarin tambayoyi amma bari na barku da iya waÉ—an nan ku farata caza brain naku zuwa gobe idan Allah ya kai mu mu ji me ake ciki.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 6/8/2024.....✍️📚🌹

For information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________29🔥

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

🏞️FOREST🏞️

Kai tsaye wajen ƙoramar Kamran ɗin ya nufa ba tare da tsoro ko shakkar komai ba, cike da jarumta tare da fata da kuma yakinin son ganin wannan mutumi ya nufi wajen. Yana ƙarisawa wajen ya wani ja uban birki babu shiri, a razane ya zaro fararen idanuwan nan nasa waje kamar zasu faɗi ƙasa.

Fara bin gawarwakin warriors ɗin da idanunsa ya yi, mamaki ne sosai ya kama shi na yadda ya ga gawarwakin nasu, babu wata gawa da zaka iya kallah da mutuncinta, kisan walaƙancin wannan mutumi ya yi masu, da alama fa wannan mutumi an sha fama da shi a fagen yaki, da alama ya sha gwagwarmayar rayuwa, domin daga ganin yadda yake farautar mayaƙannan yake kashesu kisa mafi muni ba makawa shahararren jarumi ne na kin karawa.

A hanzarce Kamran ya fara juyawa gabas da yamma kugu da arewa yana dube dube ko Allah zai sanya ya ga wannan mutumi.

Amma ina babu shi babu alamarsa. Mutum kamar aljani, nan take yake iya yaƙan mayaƙa komai yawansu, zai tarwatsasu kuma ya yi tafiyarsa abinsa, sai ka rasa ina ya shiga? Ko alamarsa baka sake gani. Abin akwai ɗaure kai, anyama mutun ne ma kuwa? Na fara tantanma!.

Kamran ya jima tsaye a wajen yana ta jimamin abin, kafin daga bisani kuma ya hango robar da Pretty ta zo ɗeban ruwa da shi ɗazun. Ɗauko robar ya yi tare da ƙarisawa wajen da ruwan ƙoramar yake zubowa daga saman dutsen, a nan ya ɗeba masu ruwa mai haske, sannan ya juya ya nufi cikin ramin nasu, zuciyarsa a cike tab da tunanin wanenen wannan Jarumin sadaukin? Su waye waɗan nan warriors ɗin? Meyasa ake ta kashesu kuma basu gajiya da sake shigowa dajin? Wanda yake turosu kuwa anya yana da imani? Duk wanda ka turo cikin dajin basa komawa, amma a haka kullum yake cikin turo wasu dan su nemo mashi kananan yaran da su kansu basu san kansu ba? Abin da ɗaure kai sosai gaskiya.

Cikin ramin ya koma gabaɗaya jikinsa a mace, tunanin canzawa su Pretty maɓoya kawai yake yi, sai dai shi kaɗai ba zai iya ba, ba zai iya irin wannan gini da Mammarsa ta yi a cikin ƙogonsu ba, suma su Pretty wannan gini da yake ramin nasu dakakkun jaruman maza suka yi shi, ba mum ɗinsu bace ta yi shi, dan wane ita, bata isa ta yi shi ba, dole maza madaka katti ne suka yi shi, dan ba ƙaramin aiki bane, ba aikin yara bane ba. Shi ma zai iya yi, amma za'a ɗauki tsawon lokaci yana yin wannan aiki, kuma ba lallai aikin ya kai ko rabin na mammarsa da ta yi ƙargo ba.

Sai tunanin mafita na ya zai yi yake yi har ya ƙarisa wajensu, a gefe ya ajiye masu ruwan tare da zama a saman dutsen da ya saba zaba.

Tun da ya shigo Pretty ta tsare shi da waɗan nan idanun nata masu rikitar da shi. Da yake shi ma hankalinsa baya a jikinsa sai ya tsareta a ido a zahiri, amma a baɗini ba ita yake kallah ba, hasalima bai san in da yake kallah ba, ya luluƙa duniyar tunani.

"Kamran ka kalli wani abin maras kyau ne a wajen?". Cewar Pretty sarkin ba'a gani ayi shiru. Ta kalli face É—insa ya sauya daga yadda ya bar cikin ramin ne, ya fita da annuri a saman fuskarsa, ya dawo cikin tunani da jimamin al'amarin, hakan yasa yanayin face É—insa ta sauya gabaÉ—aya.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, jin muryarta yasa ya dawo daga duniyar tunanin da ya afka. "No I didn't see anything, kawai am thinking ta yadda zan yi na sauya maku waje ne".

A hanzarce Prettyn ta miƙe daga kwanciyar da take tare da cewa. "Do you see the man?".

Girgiza mata kai ya yi alamar a'a bai gansa ba.

Shiru ta ɗan yi kafin ta miƙe ta diro ƙasa daga saman gadon, wajen wani ma'ajiya da aka gina da taɓo ta nufa. Da kallo Kamran ya bita kawai.

Ita kuwa Sweetie ta jingina da jikin bangon dutsen baiwar Allah, bata iya ganin komai, sai dai shiru kawai take yi tana sauraron maganganunsu a kullum, abin gwanin ban tausayi, rashin idanu babban cuta ce. Allah Alhdulillah da ka bamu ji da kuma gani haÉ—e da lafiya, kafafu da kuma hannaye.

Ƴan dube dube ta fara yi a wajen kamar mai neman wani abin. "What are you looking for?". Kamran ya jefa mata wannan tambayar.

Ba tare da ta kalli in da yake ba ta amsa mashi da. "Am looking for my mum pen and book, I want to draw something, ina ganin zan iya zana face É—in mutumin nan, with his eyes like mine".

Shiru ya É—an yi kafin ya ce. "Waye ya koya maki rubutu ma bare kuma zane Pretty?".

Sai a lokacin ta juyo da kallonta a kansa, dan bama ta ga abin da take nema ba. "Mum É—in mu mana, ai da tana koya mana abubuwa sosai har da su karatun Alqur'ani mai girma".

Maimaita sunan Alqur'ani mai girma ya yi tare da tambayarta wani littafi ne kuma Alqur'ani mai girma?. Ɗauko wani ƙaramin Alqur'ani na mum ɗin nasu mai English translation ta yi tare da dawowa kusa da shi ta miƙa mashi tana faɗin ga Alqur'ani nan.

Da yake yarinya ce babu ruwanta da yana da tsarki ko bashi da shi, kawai ta miƙo mashi full Alqur'ani izu sittin abinta. Shi kuwa da yake bai ma san menene bane sai ya sanya hannu kawai ya karɓa tare da fara dubawa.

"Kamran you said that you have some surprise for me, kuma baka bani ba". Ta kai karshen maganar tana zama a kusa da shi.

Yana kan duba farko farkon Alqur'ani ya amsa mata da close your eyes na baki. Ba musu ta kai Æ´an kyawawan fararen tafukan hannunta ta rufe fuskarta tana É—an murmushin da yasa dimples É—inta suke lotsawa sosai.

Juyo da kallonsa a kanta da kyau da kyau ya yi tare da rufe Alqur'ani ya rike da hannunsa na dama. Ganin yadda take É—an murmushin dimple É—inta yana lotsawa ne yasa ya sanya karamar yatsarsa a ramin dimple É—in nata yana faÉ—in. "Irin na Mammana". Idan baku manta ba Mamma tana da dimples.

Kara faÉ—aÉ—a murmushinta ta yi idanu a rufe. "Ka kaini in ga mammarka É—in". Ta faÉ—a ba tare da ta buÉ—e idanu ba.

Ɗauke hannunsa daga saman face ɗin nata ya yi tare da fito masu da kayansu da ya ɓoye a ƙugunsa wajen da yake ɗaure wuƙarsa.

"Mamma ba zata zama abu mai daÉ—i da zamu iya gani ba, haÉ—uwarku ba zata yi kyau ba, dan haka ki bar batun yanzu, maybe wani lokaci zan gwada".

Daga jin yadda ya yi maganar zaka san ya yi ta ne kawai, amma ba cikin daÉ—in rai ba, Pretty tasa ya ji wani irin a ransa, sabuwar tunani a kan meyasa mamma bata son yin taimako ne ya dawo mashi a cikin kwakwalwarsa, ya yi iya tunanin da zai yi domin ya gano dalilinta na kin taimakawa mutane, amma ya kasa iya ganowa, kuma babban abin ban mamakin a nan shi ne, ita tana bala'in kaunar Kamran É—in kamar ta yi mashi numfashi, amma bata son kowa, bata tunanin cewa kamar yadda take son É—an nata kowa ma haka yake son nasa? Ita dai a'a nata É—an ne kawai mutun, saura duk a banza suke, wannan abin da É—aure kai sosai wlh.

"Meyasa ka ce haka?". Cool voice É—in Sweetie ne ya katse mashi tunanin da yake yi.

Nisawa ya yi kafin ya ce. "Wani lokaci zan gaya maku, now Pretty open your eyes?".

A hanzarce ta janye tafukan hannayenta da ta rufe fuskar nata tare da waro idanun nata waje. Miƙa mata kayan dukka ya yi tare da bin face ɗinta da kallo, yana fargabar ta ce kayan basu yi mata ba, dan ita fa na gaya maku bata suturta abu, in dai bai yi mata ba ƙaramin aikinta ne ta dubi idanunsa ta ce bata so basu yi kyau ba, da dai Sweetie ne zata hakura ko da basu yi mata ba ta yaba su, amma Pretty wlh ba zata yabi abin da bata so ba, tab ai ko a gaban abin zata ce bai yi mata ba, sai dai dik abin da zai faru ya faru.

Wani irin cool murmushi ta saki wanda ya kara bayyanar mata da kyanta sosai. "Kamran kamar kasan irin kayan nan naka yana yi mun kyau sosai idan na gansa a jikinka". Ta faÉ—a tana warware kayan ta gani.

Ɗan yatsarsa ya kai saman wannan ɗan ƙaramin lips ɗin nata na kasa, a hankali ya ɗan shafi lips ɗin nata tare da faɗin. "Me ya ji maki ciwo a nan Pretty?".

ÆŠan turo bakin ta yi kafin ta amsa mashi da. "WaÆ´an can mugayen dodannin ne mana, da suka É—aga ni sama da gashin kai'na zasu É—aurani a saman dokinsu, sai wannan mutumi ya harbesu da wani abin irin naka da zaka koya mun harbin nan, da ya harbesu shi ne suka sake ni na faÉ—i kasa bakina ya É—an fashe, da mutumin ya zo ne sai ya É—aga ni ya ce na gudu".

Shoulder ɗinta ya ɗan rungumo tare da ɗan jawota jikinsa kaɗan, sannan ya sanya yatsunsa guda biyu na hannun da ya rike da Alqur'ani nan ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna, sam yaki yarda ya kalli cikin idanunta, hannunsa kawai ya sanya ya ɗan buɗe ɗan bakin nata domin ya ga ciwon da ta jin da kyau.

Hakorinta ne suka ji mata ciwo a lips ɗin tata, amma ta ciki ne, kaɗan ne ya fito ta waje, sai ka lura sosai ma zaka iya gane cewa ta ji ciwo a wajen, da yake shi Kamran ɗin tana a cikin ransa shiyasa ya yi saurin gane cewa an ji mata ciwo, kuma sau da dama ya fi yawan kallon ɗan bakin surutun nan nata, idan ya kallah yana tuna ranar da aka haifeta ta rinƙa ihu, hakan yana sanya shi shiga cikin nishaɗi........😅

Kamran dai ya kasa mantawa da ranar da aka haifi Pretty ta rinƙa ihu, wato har nishaɗi yake ji idan ya tuno da ranar, lallai kuwa Pretty zata sha gori idan ta girma ta zama ƴan mata ta fara yi mashi yanga, zai ce ke dallah mai kuka kawai yi mun shiru......😅

Kallonsa sosai take yi har cikin idanu, shi kuma ya zubawa ciwon nata idanu yana kallon yadda hakwaranta guda biyu suka haɗu suka datse namar wajen har ya yi jini, ga wajen ya yi jajir ya kuma ɗan kumbura, tunanin ciro mata magani ya fara yi, dan ba ya jin zai iya jure komai ƙanƙantar ciwo a jikinta ba tare da ya nema mata magani ba.

Slowly ya dawo da kallonsa a saman face nata gabaÉ—aya, ta wani tsare shi da idanu tana jiran ta ji me zai ce, har da wani kara kwanciya mashi a jiki, dama yaya lafiyar kura bare kuma ta yi zawo? Dama bai janyota jikinsa bama ta iya kwanciya bare kuma ya janyota da kansa, ai shikenan kuma ta samu gado da katifa har ma da pillow.

Ganin yadda take kallon cikin kwayar idanunsa sosai ne yasa ya hura mata iskar bakinsa a ido, a tunaninsa hakan zai sanya ta rufe idanun nata. Ga mamakin sa kuma sai yaga ko kyafta idanun ma bata yi ba bare asa ran zata rufe su, yadda kuka san ta sume ido a buÉ—e, kawai kallonsa take yi...... Dole ya ce idanuta suna rikita shi, wanna yarinyar akwai abubuwan mamaki sosai a tattare da ita, koya aka hurawa mutun iska a cikin idanu sai ya É—an ji wani iri, wani ma harda kwallah yake yi saboda iskar, wani kuma a take zai datse idanun, amma ita kunga ko kyaftawa ma bata yi ba bare asa ran zata rufesu.

Ba ƙaramin mamaki ta bawa Kamran ɗin ba, sake hura mata iskar ya yi a karo na biyu yana mai cigaba da kallon idanun nata. Ko gezau bata kyafta ba. Tsoro ne ya ɗan kamashi kada ace sume mashi a jiki ta yi, da sauri ya ɗan girgizara tare da ambatar sunanta.

Nisawa ta yi tare da amsawa tana sakin wani irin cool murmushi. Nannauyar ajiyar zuciya shi kuma ya sauke tare da cewa. "Kekam ba mai iya maki, yanzu me kika tsareni da ido haka?".

Hannunta É—aya ta kai ta dafa shoulder É—insa ta gaba tare da gyara kwanciyarta a jikin nasa ta ce. "Yanzu me na yi?".

Yadda ta gyara kwanciyar tata sai gurun wuyarta ya fito sosai. Yatsunsa biyu na hannun da yake rike da Alqur'ani mai girma ya kai saman wuyar tata yana faÉ—in. "Pretty wannan tsokar da take a wuyar nan taki tana yi mun kyau over, tana kara maku kyau sosai har Sweetie, amma kuma kamar mum É—inku bata da shi ita".

Girgiza kai Pretty ta yi, cikin sauri ta ce. "Kasan mum É—in mu ne?".

Sai a lokacin ya san ya yi suɓutar baki, ƴan kame kame ya fara yi yana son waske mata kada ta gane shi ne wanda mum ɗin nasu ta ce su nemo.

Tsare shi da ido ta yi, sai gabaɗaya ya tsargu ya rasa me zai ce. Ƴan hannunta ta kai saman karan dogon hancinsa ta ja da ɗan karfi har sai da ya ce wash. "Amsa me, kasan mum ce?".

Girgiza mata kai ya yi alamar a'a bai san ta ba, kawai tunani yake yi kamar ita bata da gurun wuyar. Da yake dukkansu yara ne sai ya yi wasa da ƙwaƙwalwarsu ya waskar da zancen, sai dai fa ita Sweetie ta fahimci akwai abin da baya son su sani, tabbas ko dai shi ne wanda mum ta ce su nemo, ko kuma dole da biyu yake zuwa wajen nasu, ko dai yama san in da mum ɗinsu take kawai baya son gaya masu ne, shi ne tunanin da Sweetie take yi.

"Kamran bari na ɗauko maka wani rubutu da Mum ɗinmu ta yi, ta ce mu bawa wannan mutumi idan muka gansa, sai kuma wani littafi karami da ta ce shi ma mu bashi, yanzu bari na ɗauko maka takardan tun da ka iya karatu sai ka karanta mana mu ji me mum ta rubuta". Cewar Pretty sarkin kauɗi, ta yi maganar tare da yunƙurawa ta bar jikinsa.

Da kallo kawai ya bita, har cikin ransa yake jin duk wani magana da zata yi, zazzaƙar voice ɗinta yana ratsa shi sosai da sosai.

Wannan envelope É—in da ya É—auka ranar shi ta É—auko mashi, a saman gado ta zauna tana faÉ—in. "Sweetie in nunawa Kamran ya karanta mana mu ji me mum ta ce?".

Sam Sweetie bata so hakan ba, bata so ace Pretty ta ɗauko wannan ajiya ba, saboda mum dai ta ce sai wannan mutumi kawai zasu bamawa, amma ta je ta ɗauko shi, ga shi ba halin ta ce mata ta mayar da shi kada ta nuna mashi, zai ji babu daɗi tun da yana wajen, da baya nan ne, amma a gabansa ba zata iya cewa kada a nuna mashi ba, dan haka bata da wani zaɓin da ya wuce ta ce. "Ki nuna mashi iya takardan kawai, sauran abubuwan kuma duk ki barsu a cikin envelope ɗin".

To ta amsa mata da shi, cikin hanzarce ta fara fito da abubuwan da suke a ciki, ba iya takardan da aka yi rubutu bane kawai a ciki, har da wasu ring guda biyu iri ɗaya sak, da wasu chain suma gida biyu irin ɗaga, irin siraran chain ɗin nan ne, kansu akwai tambarin ɓauna kamar tambarin gidan sarauta, haka shi ma ring ɗin da yake a cikin, shi ma yana ɗauke da wannan tambari, akwai dai karikitai a ciki, sai wani littafi mai kama da diary, da alama tarihin rayuwarta ta rubuta a ciki ko makamancin haka.

Wata farar takarda dake nannaÉ—e ta fito da shi, sannan ta kwashi duk sauran abubuwan ta mayar ciki tare da rufe envelope É—in ta ajiye a gefe guda.

Warware takardan ta yi tare da cewa Kamran zo ka gani. Ba musu ya taso hannunsa rike da Alqur'ani ya dawo kusa da su ya zauna. Ita dai Sweetie shiru abinta baiwar Allah.

ShinfiÉ—e takardan a gabansu ta yi tare da cewa ya karanta masu su ji.

Fara karanta rubutun da aka rubuta cikin harshen turanci ya yi, amma kafin ya fara karantawa sai da ya tsaya ya tsare rubutun da idanu sosai, yadda kuka san ba hanu bane ya rubuta shi, kamar computer ce ta rubuta, rubutun ya tsaru sosai da sosai, komai daki daki.

"Gaisuwa da fatan alkhari a gare ka Kamran, nasan da izinin Allah saƙona zai iso gareka, ban yarda da kowa ba a rayuwata sai kai, ga amanar ƴaƴana na baka, na san zaka kula mun da su sosai, a yanzu basu da kowa a duniyar nan sai Allah sai kuma kai, zan so kasan tarihin rayuwarsu ko in ce rayuwata, akwai wata littafi da na ajiye maka a tare da wannan saƙo da kuma wasu abubuwa, a nan zaka sami dukkan wata amsa a kan rayuwata, daga karshe ina mai yi maku fatan alheri tare da yi maka albishir da idan Pretty ta girma na baka aurenta duniya da lahira, ita kuma Sweetie ka rike mun ita tamkar kanwarka na jini, na gode sosai godiya mara iyaka". Shi ne abin da yake rubuce a jikin wannan takarda.

Slowly ya ɗago da idanunsa bayan ya kammala karanta saƙon, saman face ɗin Pretty ya sauke fararen idanun nasa, while ita ma shi take kallo har cikin idanu. Cikin nutsuwa da sanyin muryar ya ce mata. "Pretty menene kuma aure? Na ji mum ɗinku ta ce ta bani aurenki".

Ya kai karshen maganar yana cigaba da kallonta.

"Kamran ɗan sake karanta mun layin farko na sakon bari na kara ji". Cewar Pretty, ta yi maganar kamar wata mai cike da ɓacin rai.

Bai kawo komai a ransa ba, sam bai fahimci ya yi suɓul da baka ba, kawai ya sake fara karanta mata. "Gaisuwa da fatan alkhari a gareka Kamran........"

Dakatar da shi ta yi a wajen tare da sake tambayarsa wani suna ya karanta a wajen?. Sai a lokacin ya fahimci ya saki layi wajen karanta sunansa da yake rubuce a wajen, abin gwanin ban dariya, shi gabaɗaya ma ya mance da cewa ya ɓoye masu shi ne wanda suke nema, to yau dai fa Pretty ta kamo shi tsamo tsamo, ba sauran waskiya kuma.

Ƙasa ya sunkuyar da kansa tare da ɗan fara shafa hular da yake a kansa, ƙasa ƙasa ya ce. "Kila wani Kamran ɗin ne mai irin sunana, amma bani bane".

A ƙule Pretty ta yi kansa tare da kai hannunta dukka biyu ta riƙo kunnuwarsa, da karfi ta fara ja tana faɗin. "Ashe ma wani Kamran ɗin ne ko? Har yanzu baka tuba ba kenan? Ba zaka dai'na yi mana wasa da hankali ba?".

Da yake da karfin take jan mashi kunnuwan nasa hakan yasa ya ji zafi ya ziyarcesa, da sauri ya janyota ta faÉ—a jikinsa tare da cire Æ´an hannayen nata daga kunnuwar nasa yana faÉ—in. "Haba mana, ki bari kada ki cire mun kunnuwa, da zafi fa".

Kuka ta saka mashi har da hawaye, ita a dole ta ji haushi ya yi masu karya. Ita kuwa Sweetie cikin nutsuwa ta ce. "Kamran da gaske kai ne ko ba kai bane? Please kada ka yi wasa da zuciyoyinmu ka ji? Kai mutumin kirki ne sosai, na tabbata ba zaka so ka ganmu cikin ƙunci ba, so please ka gaya mana gaskiya".

Yana ƙoƙarin ƙanƙame Pretty dake son tashi daga jikinsa ta nufi waje, sai kuka take yi hawaye wani na bin wani ya amsa mata da cewa. "Da gaske ne Sweetie, ni ne, na ɓoye maku hakan ne ba dan komai ba sai dan naga zaku iya ganeni da kanku ne ko ba zaku gane ba, amma kuyi hakuri kin ji?". Ya kai karshen maganar dai'dai lokacin da Pretty ta kwace kanta tare da barin jikin nasa, ta diro kasa daga saman bed ɗin ta nufi waje tana kuka sosai.

"Pretty sarkin rigima, to me abin kuka kuma? Ai daÉ—i ma yakamata ta ji tun da mun ganoka yau, shiyasa mana kake kula damu sosai, dama mum ta gaya mana zaka kula damu sosai" Cewar Sweetie.

"Haka ne Sweetie, amma ku yi hakuri da ce maku bani bane da na yi". Yana magana hankalinsa na a kan Pretty da ta bar cikin ramin, burinsa kawai ya bi bayanta ya je ya rarrasheta.

"Ba komai Kamran, ai kai yakamata ma mu bawa hakuri". Cewar Sweetie baiwar Allah.

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya miƙe tsaye tare da ɗaukar kayan da ya kawo masu wadda Pretty ta zubar da su a kasa ta nufi waje, ya ɗaura kayan a saman gadon tare da ajiye Alqur'ani hannunsa a kan gadon yana faɗin. "Bari na bi bayan Pretty ina zuwa yanzu". Yana kai karshen maganar bai tsaya jiran me zata ce ba ya nufi wajen shi ma.

Yana fitowa ya fara waige waige ta ina zai hangota, a hankali ya fara takawa yana naman ta ina take wannan yarinyar.

Can saman dutse wajen ƙorama ha hangota, ta takure jikinta waje guda, da alama a tsorace take da zamanta a wajen, kawai dai karfin hali ne yasa ta zauna, irin ita ta yi zuciyar nan, ta yi fushi. Dariya ma ta bashi, gata da tsoro kuma ga ban tsoro.

A hankali ya lallaɓa ya nufi wajen nata, har lokacin kuma gawarwakin warriors ɗin yana wajen, sai dai ba ta gefen da Prettyn ta zauna ba, ta can gefe ita Pretty ta je ta zauna, da yake wajen yana da matuƙar girma sosai.

Ta yi shiru ta zubawa ruwa idanu tana kallon yadda yake zuba gwanin ban sha'awa, ga hawaye a saman fuskarta. Ruwan wannan ƙoramar yana da matuƙar haske sosai, tankar yake.

Sam bata ji motsin mutun ba sai ji ta yi an rufe mata idanu ta baya. A tunaninta warriors É—in ne suka dawo, dama a tsorace take da zama a wajen, kawai dan tasan Kamran yana nan, kuma zai biyo bayanta ne ma yasa ta daure ta cije ta zauna a wajen, ba dan haka ba ina ba ita ba fitowa yau.

Wani irin ihu ta kurma har sai da arear wajen ya amsa, a dubu ɗari ta fara ƙoƙarin tashi ta gudu, dan kwata kwata bata kawowa ranta cewa Kamran ne ya rufe mata idanu ba.

Ganin a garin gudunta tana ƙoƙarin faɗawa cikin ruwan yasa Kamran ɗin ya yi saurin zame hannun nasa daga idanun nata ya yi maza ya riƙo kugunta ta baya. Jikinsa ya janyota dan kada ta faɗa ruwan. Sai ƙoƙarin kwace kanta take yi, dan bata san waye bane, ga shi yana ta bayanta babu halin taga fuskarsa.

"Sarkin tsoro ai sai ki nutsu ni ne to". Ya faÉ—a yana É—agata sama zai sauko da ita kasa daga saman dutsen, dan ma kada ta yi ta afka cikin ruwan nan ta sanya shi faÉ—awa ba shiri, bai shirya shiga ruwa da safiyar nan ba.

Yana sauƙo da ita kasa ta juyo tare da fara kai mashi duka a kirji na tsoratata da ya yi, ya wani zo ba excuse ya tsoratata a banza, ya sa ta kusa sumewa. Ƴan hannayen nata da take dukan nasa ya riƙo tare da cewa. "Sorry our rigimammiya, wai ma da kika fito wajen nan idan warriors ɗin nan wasu sun zo fa? Idan suka kamana mana ke ya kike son mu yi ni da Sweetie? Kin san fa za mu iya mutuwa idan suka kamaki suka cutar dake".

"Ni kada ka yi mun magana mun ɓata". Ta faɗa a shagwaɓe tana ƙoƙarin raɓawa gefensa ta wuce.

A hanzarce ya riƙo hannunta yana faɗin. "To ai ni bance mun ɓata ba, ki bari sai nima na faɗa sai ki tafi". "Ni bawani jiranka da zan yi kawai mun ɓata".

"To shikenan am so sorry, zo ki gaya mun menene aure? Dan na ji mum ta ce ta bani ke na aure! Sannan ki gaya mun menene mum take nufi da ta ce da izinin Allah, menene Allah?" Ya yi maganar cike da ƙaguwar son jin amsa, dan duk abin da zai fito daga bakin mum twins yana ɗaukar hakan da mahimmanci kamar maganar Mammarsa yake ji.

"Nima ban san menene aure ba, amma dai nasan Allah, Allah shi ne wanda ya haliccemu dukkanmu, shi ne wanda ya halicci wannan daji da komai da komai, shi ne abin bauta da gaskiya shi kaɗai, bashi da abokin tarayya, ba'a haɗa shi da wani, shi ne mai riƙe da rayukanmu da komai dai da kasani".

Hannunta ya riƙo suka zauna a saman dutse domin ta cigaba da yi mashi bayanin wanenen Allah, shi kuma batun aure ya barwa ransa cewa zai tambayi Mammarsa idan ya koma gida, ni kuwa PRINCESS TEEMA na ce lallai akwai case idan ya tambayi Mamma, jiya ya gaya mata yana jin feeling a jikinsa, yau kuma ya tambayeta menene aure? Me kuke tunanin zai faru? Me kuke tunanin zata ɗauke shi ko zata yi tunani a kansa? Ai dole ta zargesa sosai ma. To bari dai mu leƙa KINGDOM OF POWER, daga baya zamu dawo mu saurari hirarsa da Pretty mu ji ya zasu kaya.

KINGDOM OF POWER 💪🔥💘

Kwance twin's Obaid and Omaid suke a saman katafaren bed É—in Obaid, dama kullun a gado É—aya suke kwana, basu rabuwa duk da kowa da gadonsa.

Omaid dai yana aikin latsa waya, chatting suke yi da sistersa Jannat Æ´ar uncle Rahab dake a Dubai, dama itace kawarsa, suna mugun shiri sosai, idan suka koma Dubai kullum tana tare da su a gidan King Badeen, wato kakansu, sun fi yawan zama a gidan, basu cika zuwa gidansu Abu Abdussalam bin Badeen ba, a cewarsu su Yah Ramish suna takura masu, ko gidan uncle Rahab É—in ma basu zuwa, sun fi son zama da mai ran karfe, wato kakarsu mace kenan, ita kuwa ba kamar Akka take ba, sam bata da tsauri, goya masu baya take yi suna tsula tsiyarsu, ita ce nan ta koya masu kada su yafe laifi idan aka yi masu, ita ma tsohuwar Æ´ar yi ce.

Obaid ya buga uban tagumi kamar mai tunanin wani abin, ya yi kwanciyar ruf da ciki, ga wani haɗaɗɗen pillow da ya sanya a dai'dai chest ɗinsa ya kwanta a kai. Kullun dai cikin tashin daddaɗar kamshi suke, haka zalika bedroom ɗin nasu ma, kullum cikin ƙamshi yake zubawa, kuyangunsu sun iya gyara sosai.

Ganin alamar Obaid fa ya luluƙa duniyar tunani ne yasa Omaid ya yi wa Jannat voice na karshe a in da yake ce mata cikin harshen larabci yana zuwa two mins. Yana tura mata ya ajiye wayar tare da fara bin Obaid da kallo, dukkansu daga short sai single ne a jikinsu.

"What are you thinking blood?". Omaid ya faÉ—a yana zare pillow da yake a tsakanin chest na Obaid É—in da kuma bed.

Mirginawa Obaid ya yi ya sake mirginowa kafin ya ce. "Am thinking about Mama, kasan me zan yi mata kuwa?".

Tsare shi da waÉ—an nan shegun eyes É—insa masu shegen rikita mutun idan suna kallonkan nan Omaid É—in ya yi ba tare da ya yi magana ba. Jira kawai yake yi ya ji me Obaid É—in ya shirya.

Wan nan munafukin dariyar tasa ya saki, har da kara kwanciya a saman pillow, da alama mugun abu sosai yake shriyawa.

"Please Obaid stop this laughing mana, ka fara ko? Please i ƙage nake da na ji me kake tunani a kanta".
Ya yi maganar yana ɗaure fuska kuma cikin ƙaguwa da son jin me blood ɗin nasa yake shiryawa, nan take kamanninsa da Jaish ta kara bayyana sosai, twin's ɗin nan idan suka ɗaure fuska sai ka kalli kamar Yah Jaish ne a wajen.

"Wait mana pleasure, i will tell you dolena ka sani ai, but please ka barni kaÉ—an, let me laugh more so that na samu damar iya É—aure fuska idan abin ya faru, kasan we can't laugh a wajen da abin zai faru, kada a gane mu, dan haka ka barni na yi dariyar tun daga nan".

"You're a bad boy Obaid like Akka". Omaid ya faÉ—a

(Hasbunallahu lallai yaran nan sun tsani Akka 😅 wato ita mutuniyar banza ce a gabansu 😅 kash wayyo ciki, idan kunji ance dariya ya kasheni to su twin's ne sila.)

Tsabar dariyar mugunta har da hawaye ne yake fita mashi a cikin idanunsa izuwa saman lallausan kumatunsa, ya dafe ciki, kamar wani zararre, da kyar ya iya cewa Omaid É—in. "I think I'm even better than Akka ma ai".

Dukan wasa Omaid É—in ya kai mashi a shoulder É—insa yana faÉ—in. "To is okey, now gaya mun me ka shirya?".

Da kyar ya iya dakatar da dariyar tasa tare da haÉ—e nutsuwarsa waje guda, sannan ya fara magana. "Snake mana zamu sakar mata ko kuma scorpion, kuma sai cikin dare zamu yi hakan, ya cijeta ko sau É—aya ne".

"Obaid you're not serious fa, so kake ka kasheta ko? Idan snake ko scorpion suka cijeta ai kafin a kaita hospital ma ta mutu, kuma tsabar kai you're a very very bad boy sai cikin dare za mu yi mata hakan ko? Wlh Yah Jaish yana nan, idan ya rikemu ina ga ko daddy ba zai iya kwatarmu a hannunsa ba, kuma kowa ya sani a cikin gidan nan mune kawai muke da su scorpion, muna sakar mata su za'a san aikin mu ne, ina ga kafin wayewan gari ni kam ina hanyar Dubai da kafafuna, ba zan jira jirgi ba, dan da punishment É—in Yah Jaish gwara na je Dubai da kafa".

Dariya sosai Obaid ya sake kwashewa da shi kafin ya ɗan tsagaita kuma, ko me ya tuna sai kuma ya sake cewa. "Yakamata sai mun shirya zamu bar ƙasar nan mu sakarwa Yah Jaish ma scorpion guda ɗaya".

A wannan karon Omaid bai san time É—in da ya fashe da dariya ba. WaÉ—an nan yara wlh anyi Æ´an albarka, ba'a faÉ—in É—ayan, sai dai shirin Allah kawai zamu yi masu fata.

"Amma ni ban taɓa sanin cewa blood kai mugu bane sai yau, wato sai mun shirya barin ƙasar zamu sakarwa Yah Jaish ɗin ma nasa scorpion ko? Ai wlh ina ga ko cikin momma muka koma sai Yah Jaish ya bi mu". Cewar Omaid. Yana magana yana ɗan dariya, da yake shi na gaya maku bai cika yawan dariya sosai ba, Obaid ya fishi yawan dariya.

"Ai Yah Jaish É—in ne ya cika takurawa mutane, yakamata mu É—an É—an É—ana mashi azaba kaÉ—an, shiyasa fa ni bana son zuwa gidan uncle Abu Abdussalam, saboda muguntar su Yah Ramish". Obaid ya faÉ—a yana janyo wata pillow ya rungume.

"Kai mu yi magana serious me yakamata mu yi wa mama kafin mu koma? I really hate this woman, da idonta kamar na Akka".

(Wai kowani kayan tsiya yaran nan suka ɗebo sai su ce irin na Akka?🤔😅 Ita dai Akka tana shan zagi a hannunsu ba tare da saninta ba.)

"I think this night mu je mu san ta yadda zamu yi mu saka mata diaza a cikin drink nata or water ta sha". Cewar Obaid.

Wani irin zaro idanu waje Omaid ya yi, dama ga idanun dara dara a waje, yadda ya zarosu a yanzu idan ka gansu sai ka ruga a guje dan tsorata. A hanzarce ya ce. "Real bad boy without a mix, kai Obaid wani irin bakin mugu ne wai? Yanzu Mamar zamu bawa diaza ko? So kake yi ka zubarwa da daddy mutunci kawai. Tab wayaga mama ta sha diaza? Wai da kuwa KINGDOM OF POWER ya É—auki jan launi". Ya kai karshen maganar tare da kwashewa da wani É—an iskan dariya.

Cikin dariya yake faÉ—in. "Har na hango Mama tana bin jikin bangon kingdom É—innan dukka tana wankewa, kai amma kuma da ta taimaka fa". Cike da shakiyanci da iyashege ya yi maganar.

A hanzarce Obaid ya karɓi zancen da cewa. "Ba iya jikin bango ba, ai wlh idan ta sha diaza ina ga harta motoci da dawakan gidan nan ba zata bari ba sai ta wanke, har mu ba barinmu zata yi ba sai ta wanke mu, komai na gidan nan babu abin da zata bari, caf zata wanke komai, 24 hours tana aiki". Shi ma cike da shakiyanci ya yi maganar. Sun zauna sai tsiya suke zubawa Mama ƴan albarka.

Kara fashewa da dariya Omaid ya yi tare da É—aukar pillow yana kaiwa Obaid duka, da kyar yake iya faÉ—in. "Please blood ka barni haka kada kasa dariya ta kasheni, dan ka tuna mun da uncle Muslim da muka bawa diaza a school, bawan Allah har bangon jikin class namu sai da ya wanke, gobe ya kara yi mana faÉ—a har ma ya raba mana wajen zama uban diaza a aiki zamu bashi ".

Wani irin bushewa da dariyar iskanci Obaid ya yi, kamar wasu zararru suna ɓaɓɓaka dariya mai sauti ba tare ma da sun san sautin yana fita ba, sun kulla mugunta kala kala yaran nan, uncle Muslim uncle nasu ne a school wanda kullum yake yi masu faɗa a kan su dai'na ana yi masu magana suna yin banza da mutane. A gaskiya su idan kaga suna magana to a gida ne da su Sarina, amma wlh a waje ko uncles ɗinsu a school basa yi masu magana su amsa, kamar wasu masu aljanu haka suke, sai ayi ta magana su yi banza da mutane, idan kaga twin's ɗin nan suna dariya to sai sun haɗu su biyu irin haka, su biyu suke hira, su yi dariya, to shi ne fa uncle ɗin ya yi masu faɗa sosai dan ya ji haushin yana yi masu magana sun ki amsa mashi kuma suna ta hira a tsakaninsu a cikin class ɗin, izzar bala'i ke garesu suma, jinin sarauta na gudu a jikinsu.

Har uncle ɗin ya so ya zanesu ma kuma sai ya hakura ya kyalesu, daga nan sai ya raba masu wajen zama a class ɗin, dan idan suna a tare wlh ko malami yana class suka so yin magana sai sun yi, basu jin magana ne na wuce misali, ga shariya da mannin hauka game da izza. To su wannan raba masu wajen zama da ya yi ne ya baƙanta masu rai, ba zasu iya rabuwa da juna ba ko dede da minti ɗaya, hakan yasa suka shammaci bawan Allah suka sanya mashi diaza a cikin ruwan shansa, yana sha ya haukace a school ɗin, 24 hours yana aiki kamar computer, ko barci bai iya yi ba, bawan Allah ya wahala a lokacin, abin gwanin ban tausayi kuma gwanin ban dariya idan kuka kalli yadda yake tiƙar aikin. Diaza wata shegiyar kwaya ce mai haukatar da mutun, yasa ka yi ta aiki kamar jaki babu gajiya. Ko a ina suke samo abubuwan kulla muguntar tasu? Ƴan yara da su, abin da mamaki, dole akwai mai basu wasu abubuwa, dan dai su idan ba shopping ba basu zuwa ko'ina bayan school, ko gidan uncles nasu kaisu ake yi a kuma dawo dasu, basu driving da kansu ma bare ace sun ɗauki mota sun fita sun je sun sayi wani abin, idan zasu fita sai da driver and bodyguards masu rai da lafiya da zasu yi tsaron lafiyarsu, su kaisu su kuma dawo da su gida lafiya, to a ina suke samo kwayoyi masu haɗari haka? Akwai matsala kam babba ma kuwa..........🤔

Za dai mu gani, lokacin zai nuna mana komai, amma dai twins Obaid and Omaid kamar ba Æ´aÆ´an Momma ba wlh, basu ji sam.

Yah Jawad ya zo wucewa ta saitin bedroom ɗin nasu zai je wajen Akka ya jiyo sautin dariya kamar wasu zararru. Ƴar mamaki ce ta kama shi, dan shi dai yasan twin's basa dariya, kuma basu da yawan magana, bai san a waje ne suke haka kamar malaman islamiya ba, idan suna ɗaki su biyu kamar ƴaƴan shaiɗan haka suke, su yi ta tuna muguntar da suka yi a baya wa mutane suna ɓaɓɓaka dariya kamar waɗan da aljanu suka shafa.

Room É—in nasu ya nufo, handle É—in door É—in ya rike tare da murÉ—awa a hankali ya sanyo kai. Suna jin an buÉ—e kofar suka wani irin nutsu sit. Wani irin kallo ya wurga masu.

Nan take suka sha jinin jikinsu, tsuru tsuru suka yi da idanu. "Me yake damunku haka?". Shi ne tambayar da ya jefa masu yana É—aure fuska.

Omaid ne ya ce. "Nothing Yah Jawad, kawai we're watching some comedys in my phone ne yake bamu dariya".

"Shi ne kuke dariya haka like you're out of your sense?".

Obaid ne ya ce. "Sorry Yah Jawad ba zamu sake ba".

Juyawa ya yi ba tare da ya sake yi masu magana ba ya fice daga ɗakin. Kallon juna suka yi tare da sake kwashewa da dariya ƙasa ƙasa suna toshe baki kada sauti ya fita Yah Jawad ya dawo ya karairayasu.

Shi kuwa Yah Jawad yana fita part ɗin Akka ya nufa. Gimbiya Chuchu ta tsantsara kwalliyarta cikin wani abaya pink color mai shegen kyau, ta yi kyau sosai, arab hair ɗin nan nata ta ɗaure shi part biyu, Kuyanga mama Haulat ta kitse mata jelar gashin nata gwanin birgewa, sai sheki yake yi ita kuma tana ta tashin kamshin daddaɗar perfume mai sanyaya zuciyar mai shaƙa wadda Momma ta basu ita da auta Zunaira.

Sam ta manta da yarjejeniyar da suka yi da Yah Jawad, ta tsaya sai É—aukar kanta hoto da videos take yi a wayarta abinta, dan ba karya ta yi kyau over......... Dama ai mai hali baya fasawa, da wuya ta dai'na É—aukar hoton nan lokaci guda haka, abin da ta saba yabi jininta ai ko zata dai'na ba lokaci guda haka ba, sai a hankali.

Yana shigowa É—akin ya harÉ—e hannayensa a saman kirjinsa yana binta da kallo tare da jingina jikinsa da jikin door É—in shigowa room É—in, tunani yake yi yadda zai yi da yarinyar nan a duniya..............

Nima tunani nake yi lokacin da zan dasa aya ya yi, sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kaimu da rai da lafiya, zamu ji ya Yah Jawad zai yi da Gimbiya Chuchu? Wani hukunci zai yanke mata?....🤔

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 7/8/2024.....✍️📚🌹

For information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________30🔥

Yana shigowa É—akin ya harÉ—e hannayensa a saman kirjinsa yana binta da kallo tare da jingina jikinsa da jikin door É—in shigowa room É—in, tunani yake yi yadda zai yi da yarinyar nan a duniya.

Sam bata ji motsinsa ba, videonta kawai take ɗauka, ta turo bakin nan ta sake ɗaga jera ɗaya, sai style kala kala take yi. Kamar a mafarki ta gansa ta cikin camerar wayar tata. Ai a dubu ɗari ta juyo har wayar tata sai da ya faɗi ƙasa.

Tana juyowa suka haÉ—a idanu, ko kyafta idanu daga kallonta bai yi ba. Tana juyowa sai da ya ji gabansa ya faÉ—i, saboda kyan da ta yi, kun santa da shegen iya make up, dama kuma ga kyau kamar su suka yi wa kansu.

Ƙasa da kai ta yi kamar wata mumina sahabiya. Tun bai yi mata magana ba ta fara ƴan kame kame tana in'ina ta ce. "Am.... Im so sorry Yah Jawad...... Na mance na ce ba zan sake bane". Tana magana kirjinta na dukan uku uku.

Kamar mutun mutumi ne a wajen ba shi ba, ko motsawa bai yi ba bare tasa ran zai amsa mata, in fact ko kallonsa daga kanta bai kawar ba, ya tsareta da ido kamar wadda aka yi wa guduma a tsakar kai ya yi tsumar tsaye.

Duk baiwar Allah ta tsargu, tana son ta É—ago kai ta saci kallonsa, amma tana tsoron su haÉ—a idanun, ga shi ta ji ya yi shiru bai yi magana ba, tana son ta ga action da ya É—auka, shin yana harararta ne ko kuma dai yaya? Face É—insa a É—aure take ne ko kuma dai a É—an sake? Duk tana son sani, amma ba halin ta É—ago kai, saboda tsoronsa. Sai addu'a take yi Allah ya kawo Akka, idan Akka ta shigo shikenan ta tsira. Har kerma Æ´an hannayenta suka fara yi, ba abin da take tunawa irin punishment na ranar, narai narai ta yi da idanun tana shirin fara yin kuka kawai.

Almost 10 mins yana tsaye a haka, sai da ya ga hawaye ya fara bin kyakkyawar kumatunta yana ɓata mata make up nata ne, a nan ne ya ɗan sauke ajiyar zuciya tare da lumshe idanunsa ya sake buɗesu. A hankali ya fara takowa izuwa cikin ɗakin.

Datse idanunta gam ta yi tana jiran kawai ta ji saukar mari. Gabanta ya ƙariso yadda ta tsaya kamar wadda aka sassaka.

Ɗan sunkuyawa ya yi ya ɗauko wayarta da ta yasar a kasar, pause ɗin video da take ɗauka ya yi, sannan ya yi saving video, yana ƙoƙarin buɗe baki ya yi mata magana ta raɓa gefensa da gudu da nufin ta yi waje.

Cikin sauri ya riƙo hannunta tare da ɗaure fuska sosai. "Where are you going?". Ya faɗa cikin sanyin murya.

Bai san cewa uncle Abbas ta gani a bayansa yasa zata gudu ta je wajensa ba, yanzu ya shigo room É—in, sallama ya zo yi da Akka zai wuce, shi ne da ta ga ya tsaya a bakin kofa yana kallonsu zata gudu ta je wajensa, hankalinta ya É—an kwanta uncle nata ya zo shikenan ta tsira, shi kuwa Yah Jawad bai san da uncle Abbas É—in ya shigo ba.

Janyota ya yi ta dawo ta gabansa, kara É—aure fuska sosai ya yi irin ba wasan nan. GabaÉ—aya hankalinta na'a kan uncle Abbas É—in, shi ma ya harÉ—e hannu a saman kirjinsa yana kallonsu. Ganin hankalinta na'a kansa yasa ya yi mata alama da ta yi shiru bari ya ga gudun ruwan Jawad É—in.

Ganin uncle Abbas ɗin ya yi mata alamar ta nutsu ne yasa ta nutsu tare da yin ƙasa da kanta.

"Am i not talking to you?". Yah Jawad ya yi maganar yana sakin hannun nata da ya riƙe.

"Am so sorry babu in da zanje". Ta bashi amsa tana É—an satar kallon uncle Abbas.

"Wai Jannat anya babu wata matsala a tattare da ke kuwa? Ban hanaki É—aukar hoto ba?".

"Mantawa na yi, amma ka yi hakuri ba zan sake ba".

Nisawa ya É—an yi kamar wani wadda ya yi wani aikin ya gaji. "Yanzu wani hukunci kike son na yi maki?".

Sai a lokacin ta ɗan ɗago da kanta, a hankali ta kai kallonta izuwa saman face ɗinsa, while shi ma face ɗin tata yake kallo, hakan yasa suka kalli juna a cikin idanu. "Dan Allah Yah Jawad kada ka yi mun komai, Allah ba zan sake ba, na tuba, wlh bana son kneel down ɗin nan, please Yah Jawad, gwara mun ka kwace wayata na har abada akan ka ka bani punishment ka ji?". Kamar zata yi kuka ta kai karshen maganar, a shagwaɓe kuma ta yi maganar, ga ragowar guntun hawayen ɗazun a saman fuskarta.

Lumshe idanunsa ya yi, har cikin ransa ya ji voice É—in nan nata. "Last time bana ce ki sameni a part É—ina ba? Meyasa baki zo ba? Kin rai'na ni ko?".

A hanzarce ta girgiza mashi kai alamar a'a tana mai cigaba da maimaita mashi kalmar sorryn nan dai da ta saba faÉ—a kullum.

"Ina Akka?". A hanzarce ta amsa mashi da. "Bata nan ta fita, ina ga ko tana wajen daddy ko kuma wajensu mummy".

"Meyasa kika ce mata ni na hanaki zuwa Dubai?".

Zaro idanu waje ta yi, ita kwata kwata ma ta mance da cewa ta kai karansa wajen Akka É—in, wannan shi ne laifi a kan laifi, dan kuwa Akka ta je har part É—insa wai sai ya gaya mata dalilin da yasa ya hana Chuchu zuwa Dubai?. Da kyar ya shawo kanta ta rabu da shi, wannan dalilin yasa ya biyo Chuchun, yasan confirm zai sameta a nan É—in, shi ne ya zo.

"Ba zaki bani amsa ba kenan ko? Wai ni Jannat yaushe na zama abokin wasanki ne?".

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.