Complete Hausa Novels

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Rawanin_Zalinci_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 12 of 24

Cigaba da girgiza mashi kai ta yi, nan take idanunta suka sake ciko da kwallah, kan kace me sun fara bin kumatunta.

"Another case kenan, bana hanaki kuka ba?".

Da sauri ta sanya hannu ta fara goge hawayen nata.

"Okey jeki part É—ina ki yi kneel down ina zuwa".

Okey ta amsa mashi da shi tare da raɓawa jefensa ta wucewa da sauri. Tana wucewa ya juyo da kallonsa a kanta domin ya kara tsareta da idanu. Mugun jin daɗin kallonta yake yi ɗan rainin wayo, amma tsabar walaƙanci da mugunta sai ya rinƙa baƙanta mata rai, ya yi ta takura mata yana sakata kuka.

Yana juyowa suka yi ido huɗu da uncle Abbas da ya saki baki yana ganin ikon Allah, shi dai yasan babu wanda ya taɓa yi wa su Jawad ɗin makamancin haka, amma su sun zo suna cin zalin kannesu.

Ɗan zaro idanu ya yi yana kallon daddyn nasa, yana son ya san yaushe uncle Abbas ɗin ya shigo room ɗin, adduarsa ɗaya Allah yasa bai ji abin da ya ce da Chuchu ba, dan yasan halin uncle Abbas sarai, idan kana son kaga ɓacin ransa to ka taɓa mashi ƴan matan nan nasa, sam baya son yaga an taɓasu, ƴan lelene, shagwaɓasu yake yi over, shiyasa suma suke matuƙar kaunarsa sosai, ba dan ba dan bama sai mu ce sun fi kaunarsa sama da daddynsu King Zuhair.

"Welcome daddy yaushe ka shigo?". Ya faÉ—a yana satar kallon Chuchu da ta fita a yanzu, yana magana yana fargabar kada ace daddyn nasa ya ji maganganunsu da ita.

Shiru uncle Abbas É—in ya yi har sai da Chuchu ta yi nisa da room É—in, sannan ya ce. "Tun lokacin da kake sanya mun Æ´ata kuka na shigo".

Ɗan shafa arab hairnsa ya yi tare da ɗan sunkuyar da kai ƙasa. "Kai daddy ni yaushe na sakata kuka? Kawai sune sun cika yin kuka banza banza, kuma duk kai ka shagwaɓasu ai, ni iya faɗa kawai nake yi mata".

"Jawad wlh ina jiye maka tsoron kar ka tabka kuskure". Uncle Abbas ya faɗa tare da ƙarisowa cikin room ɗin. A saman sofa mai zaman mutun biyu ya zauna tare da ɓalle botir na suit ɗin jikinsa.

"Daddy kuskuren me kuma?". Ya faÉ—a da iya gaskiyarsa, dan shi bai san wani kuskure daddyn nasa yake hango mashi ba.

"Zaka ce mun baka san abin da nake jiye maka tsoro bane?". Ya yi maganar yana wurga mashi wani irin kallo da waÉ—an nan idanun nasa irin na Akka.

"Kai daddy wannan kallon fa?". Ya kai karshen maganar tare da dawowa kusa da daddyn nasa ya zauna a saman sofar.

"Ai dole na kalleka da kyau tukun nan, na tabbatar lafiya kake da zaka ce mun baka san tsoron da nake jiye maka ba".

ÆŠaura wayar Chuchu a saman hannun sofar ya yi tare da cewa. "Daddy da gaske ban san wani irin kuskure kake ji mun tsoron na tabka ba".

"Jawad kenan, to ina jiye maka tsoron ranar da zaka bayyanawa Jannat gaskiya ita kuma ta ce bata so bazata yarda ba saboda kana mata mutunta, a ranar ne zaka gane ka yi kuskure".

ÆŠan zaro idanu ya yi, Æ´ar mamaki ce ta bayyana a saman face É—insa. "Daddy wace gaskiya kuma zan bayyanawa Jannat har da zata ce bata so?".

Hararar wasa uncle Abbas É—in ya wurga mashi kafin ya ce. "Yanzu zaka ce mun ba son Jannat kake yi bane?".

"So kuma daddy? Ni É—in?". Ya faÉ—a cike da mamaki sosai.

"A'a ba kai ba ni, wai Jawad lafiyarka ma kuwa?".

Shiru ya É—an yi yana tunani, sake furta cewa son Jannat ni kuma, ya yi tare da nuna kansa, mamaki abin ya bashi ne.

"Baka yardanwa kanka kana sonta ba ko? To bari na baka wani Assignment ka je ka aiwatar da shi yanzu, idan ka kammala sai ka kirani a waya ka sanar da ni amsa".

Dawo da kallonsa a kan daddyn nasa da kyau ya yi kafin ya ce. "Okey daddy ina jinka wani Assignment?".

Kallon shi da kyau uncle Abbas É—in ya yi kafin ya ce. "Ba ka ce ta je ta yi kneel down a part É—inka yanzu ba?"

GyaÉ—a mashi kai ya yi almar e ya ce.

"Okey in ka je part É—in naka yanzu ka barta ta yi one hour tana kneel down, kuma kada ka hanata yin kuka, ka barta ta yi kukanta, sannan idan ta cika one hour É—in ka ce ta tafi room É—inta da kafafunta, idan ta kasa ka ce dole ta tafi, ko kukan jini zata yi kada ka kulata ta taka da kafafunta dole, idan ka iya aikata hakan ka kirani ka gaya mun.....". Ya kai karshen maganar yana kallon É—an nasa har cikin ido, dan shi dai yasan tun Chuchu bata kai haka ba yasan da cewa Jawad É—in yana sonta, shi ne dai bai gane hakan ba, amma yanzu zai gane ne dolensa, uncle Abbas yasan ko dede da minti É—aya Jawad ba zai iya jure kukanta ba, amma dai koma me yanzu zai gane ai.

"Daddy wai yau da kanka kake cewa na bawa Æ´an gatanka punishment? Kuma kace ko ta yi kuka na barta ta yi ta yi? Anya daddy kai ne kuwa?".

ÆŠan murmushi ya yi tare da faÉ—in. "Ni É—in ne dai, Abbas É—in da kasani ne, ni nace ka je ka yi ai, kawai ka je ka aikata, idan ka iya sai ka kirani ka sanar da ni, dan ni daga nan wucewa zan yi......".

Girgiza kai ya fara yi yana faÉ—in. "No daddy banda kuka kam, ni bana son ganin kukanta, amma zan iya sanyata kneel down sosai, har ma fin one hour, amma ba zan iya jure ganin kukan nata ba".

Harararsa uncle Abbas ya yi kafin ya ce. "Okey tom shikenan na janye wannan Assignment É—in bari na baka wani, idan ka koma part É—in naka yanzu, ka kalleta ido cikin ido na a kallah one mint, duk tunanin da ya zo zuciyarka a wannan lokacin ka kirani ka gaya mun, dan shi ne gaskiyar abin da yake a tsakaninku".

"Daddyyyyyy kai ni wlh wahalar dani kawai kake son yi, Jannat is my sister that's all, bayan haka ni babu wani abin, to daddy Jannat ma nawa take? Yaushe ta girma ma? Me zan yi da ita? Ai ta yi mun ƙanƙanta, ni bani ma da lokacin mata a yanzu".
Ya kai karshen maganar yana turɓune fuska, shi sam bai ma san cewa ya saki layi a maganar tasa ba, ko da yake shi dama bai kai Jaish kunya ba.

"Babu abin da zaka yi da ita, kuma bata girma ba amma a haka kullum kake tsare mun ita da ido, idan kana kallonta ma har mantawa kake da in da kake, jiya ma fa a parlourn Yah Zuhair ina ganinka sai kalle mun ita kake yi kamar ka samu Tv, gaskiya zan gayawa yaya ma duk ku bar family part É—in nan ku koma gidajenku, saboda kun sakawa Æ´aÆ´ana ido, ku barmun su su sakata su wala".

Da yake gidajen nasu dukka a cikin kingdom É—in yake, sai dai yana da É—an nisa da family part gaskiya.

"Kai daddy wai ni yaushe na kalleta ne? Kai da uncle Taheer da dad kun saka mun ido fa, shi ma dad daren jiya har da ce mun wai yanzu aure zai yi mun ni da Jaish ya huta, to mu laifin me muka yi yanzu fisabilillahi da kuke neman É—aura mana wahala?.".
Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya ɗauki wayar Chuchu ɗin da ya ajiye, sannan ya nufi waje. "Allah ya kiyaye hanya daddy".

"Zaka ga mun saka maka idanu ne, sai na yi mata miji cikin É—aya daga cikin Æ´aÆ´an abokaina ba tare da saninka ba za'a É—aura auren, a nan ne zaka san mun saka maka ido, ka jira ka gani".

Shiru ya yi, dan har ya ji ransa ya ɗan ɓaci da last zancen daddyn nasa, da sauri ya wuce ya fita dan kada ma daddyn ya ƙara yi mashi magana mara daɗi irin haka.

Da kallo uncle Abbas ya bishi, sai da ya fice ne ya ce yaro yaro ne, zaka yi bayani ne, ai ita so ba'ayi mata wargi.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.