Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Rawanin_Zalinci_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt
Chapter 18 of 24
Cigaba da hira suka rinƙa yi suna neman mafita a tsakaninsu, da haka har barci ya ɗauke Pretty, ya rage Sweetie kawai da ta kasa yin barcin, tunanin mafita ta shiga yi tana ɗan shafa kyakkyawar gashin kan Prettyn wadda yake a saman laps ɗinta, tana matuƙar kaunar ƴar uwar tata, ita ma Prettyn tana matuƙar kaunarta, su biyun nan su ne duniyar juna, ita ce duniyar Pretty, Prettyn ma Sweetien ne duniyarta, komai nata, so suna tsananin kaunar juna.
Kamran kuwa tafiya ya yi wajen wannan teku na jiya dan ya duba ko akwai wata hanya mafi kusa ta gefe gefen tekun.
🕊ï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸ðŸŒ¼ðŸ•Šï¸
GIDANSU KHADIJAH 💔😥
After some days.
A cikin waÉ—an nan kwanaki da suka shuÉ—e dai maman Zainab ta yi nasarar samun sa'a wannan asiri na jikin Zainab dai ya karye, ta tsaya ne tsayin daka wajen ganin ta yi wannan haÉ—in maganin da mamanta ta gaya mata, so Allah da ikonsa Zainab ta dawo normal. Sai dai kuma wani tashin hankali shi ne tun ranar da baban Zainab ya fita gidan a tare da Hauwa bai sake dawowa gidan ba, su maman Haidar sai nemansa suke yi, amma ina basu gansa ba, sosai maman Zainab ta shiga damuwa maras misaltawa, ta yi mummunar rama sosai da sosai, kamar ba ita ba, har duhun wahala da damuwa sai da ta yi, sun dawo yin rayuwa daga ita sai su Zainab da Sadiq, Haidar ma yanzu sai gefi gefi yake shigowa gidan, watarana a gidan kakarsa yake kwana.
Ga wani bala'i da hajiyarsu ta taso masu da shi shi ne wai auren Khadija and Haidar za'a yi shi kafin ta rubuta Exams É—in, sun fasa bari sai ta rubuta, saboda Haidar ya matsa masu sosai, shi fa sam bai damu da rashin sanin in da babanta yake bama, bai wani damu da halin da suke ciki ba, ko a jikinsa, abin da yake gabansa kawai yake yi.
Maman Zainab ji take yi kamar ta kwashi Æ´aÆ´anta su koma wajen mahaifiyarta, Sadiq kuwa ya ce mata a'a ta yi fito na fito da su ta gaya masu Khadija bata son Haidar, dan haka ba za'ayi wannan auren ba, idan sun ki sun ce sai anyi aure to ta shigar da su kara ga hukuma a kwantar ma yarinya hakkinta, tun da yanzu baban Zainab ma ba ta su yake yi ba, dan haka ta tsaya ta kwatarwa Æ´arta yanci.
Ta É—auki kwanaki tana tunani a kan zance Sadiq É—in, daga karshe dai ta kira mamarta a waya ta sanar da ita ga wani lukutar masifa da suke ciki, sannan ga shawarar da Sadiq ya bata.
Da yake mahaifiyar tata dattijuwan arziki ce sai ta ce mata. "A'isha duk abin da zaki yi ki rinƙa kallon Mamarsa tamkar ni ce, ki girmamata kada damuwa ko ɓacin rai or zuciya haɗe da shaiɗan ya ja ki ki yi mata wani abin da ba zaki iya yi mun ba, kada ki manta zamanku da ɗanta a baya, na baki izini ki kwatarwa ƴaƴanki yanci, amma kada ki wuce gona da iri, uwa bata fi uwa ba, mahaifiya dai mahaifiya ce, kada ki riƙi hujjar cewa hankalinsa baya a kanki ki ce zaki walaƙanta mahaifiyarsa, ki sani in shi baya nan Allah yana nan, kada ki yi wannan kuskuren, komai zaki yi ya kasance tsakaninki da Allah zaki yi, baki san me gobe zata haifar ba, Allah ya kyauta ya saita maki al'amuranki, ki cigaba da yin addu'a tare da yin azzumi komai ya kusa warwarewa In Sha Allah".
Sosai Ouumar tata ta yi mata nasiha mai ratsa jiki, daga karshe suka yi sallama. Tana ajiye wayar ta É—aura É—amarar rusa wannan aure ta Haidar da Khadija koma ta yaya ne.
Da misalin karfe uku na yamma, Sadiq ya dawo da su Khadija daga makaranta, ya bawa maman Zainab ɗin kuɗin cefene, ya zama dai kamar shi ne mai gida, ya rikewa baban Zainab komai nasa da amana, yana kula da komai, kowani karshen sati zai zauna su buga lissafi shi da maman Zainab ɗin, ya ware ribar da kasuwa ta bayar ya zuba a cikin account ɗinsa, uwar kuɗi kuma ya koma da ita kasuwa, a cikin kuɗinsa da yake cirewa na sallamar da baban Zainab ya saba basu tun farko yake cirewa ya bawa maman Zainab ɗin kuɗin cefene, sam ba'a kuɗin baban Zainab ɗin yake ciyar da su ba, daga aljihunsa hakkinsa ya riƙesu bawan Allah.
Zai wuce ya nufi kasuwa maman Zainab ta dakatar da shi, ta ce ya zo su yi magana. Ba musu ya shigo cikin parlourn. A saman sofa mai zaman mutun biyu ya zauna, su Khadija kuma suka wuce cikin É—aki domin su cire uniform su yi wanka kamar yadda suka saba.
Cikin rashin kwarin jiki ta gaya mashi yadda suka yi da mamar tasu, sannan ta É—aura mashi da cewa idan sun ki rushe auren nan tabbas kara zasu kai su daga nan har kotu.
Ajiyar zuciya ya sauke, cikin nuna tsantsar kula tare da tausayawa Æ´ar uwar tasa ya buÉ—e baki zai fara magana kenan suka fara jiyo bugun kofar gida.
Haka kawai maman Zainab ta tsinci kanta da fargaba tare da faÉ—uwar gaba, kirjinta ne ya fara bugawa kamar wadda ta jiyo dukan kofar gida da tsakar dare. Hannunta ta kai ta dafe saitin kirjin nata, sannan ta furta Hasbunallahu wani'imal wakil.
"Sadiq duba su wanene?". Ta faÉ—a cike da fargabar su waye zata gani, ita a yanzu buga kofar gidan nasu ma bala'i ce a gareta, dan tasan ba alkhari take gani ba, wani lokaci bala'in su maman Haidar, wani lokaci baban Zainab da Hauwa, dukkansu kuma ganinsu tamkar ganin gagarumin bala'i ne a gareta, da zarar sun zo fa to shikenan É—an sauran walwala da ya saura a tattare da ita ma zai tafi, zata faÉ—a sabon kuncin da sai ta fi kwana uku bata fita ba, so ganinsu ba alkhari bane a wajenta.
Miƙewa Sadiq ɗin ya yi hannunsa na rike da key ɗin mashin din baban Zainab da kuma keys ɗin shago a jiki, haka ya nufi wajen dan ya duba su wanene?.
Shi kansa sai da ya shiga fargabar abin da zai gani idan ya buÉ—e kofar, dan ya gaji da kallon wannan fitina da bala'i shi ma, amma da yake namiji ne shi sai ya É—anne ya zare jam lock É—in kofar.
Yana buÉ—e kofar ta fara zazzaga mashi buhun bala'i kamar dama ta tara bala'i ne tana jiran ta samu wadda zata zazzagewa shi a kansa.
"Wani irin iskanci ne wannan kusan minti uku kun bar mutane a tsaye a waje? Ku baku da tarbiya ko? Baku san darajar É—an adam ba zaku barmu a tsaye!!".
Wani irin ƙululun bakinciki ne ya tokarewa Sadiq maƙoshi, ji ya yi tamkar ya tsinka mata mari sai ta sume a wajen, wata ƴar gajera da ita a gabansa, ba dan ganin baban Zainab da yake a tare da ita ba wlh yau ba abin da zai hana shi dalla mata mari shegiya. Amma haka ya danne ya kawar da kansa, ko sannu bai ce mata ba ya sa kai zai wuce cikin ɗakinsu kawai, ɓacin rai yasa ya mance bai gaishe da baban Zainab ɗin ba ma.
"Kai zo nan". Ta faÉ—a tana wani É—age hanci sama. Da alama rashin mutuncin da take ji da shi yau yafi na kullum, da alama yau rabon babin rashin mutuncin ta buÉ—e.
ÆŠan zaro idanunsa kamar na Zainab É—in nan ya yi tare da juyowa ya kalleta.
"Yeah da kai nake yi, na ce ka zo nan! Ko ba zaka zo bane?". Hauwa duniya, akwai ta da son nuna isa da taƙama! Burinta ta ganta tana fadanci a waje jama'a suna yi mata biyayya, tana da son duniya da sharholiya sosai!. Sai kace Sadiq ɗin ɗanta ne, ta wani kirasa kamar ita ta haifesa, kira ma na walaƙanci.
Kai kallonsa a kan baban Zainab dake tsaye a gafenta ya yi. "Ba zaka zo bane tana kiranka?. Ka tsaya kana ganina?". Cewar baban Zainab É—in.
Ɗan lumshe idanunsa ya yi yana ƙoƙarin danne zuciyarsa, dan wlh in ya biyewa zuciya harda baban Zainab ɗin zai haɗa duk ya ci ubansu, dama a wuya yake da su, suna son kashe mashi ƴar uwa ɗaya tilo, duk time da suka zo gidan idan suka tafi sai ta fi kwana uku tana fama da ciwon kirji, Allah ne kawai yake tsareta wani ciwon bai kamata ba, so a ƙule yake da su, idan ya biyewa zuciyarsa tsab zai sumar da su dukkansu biyu wlh.
Juyowa ya yi ya dawo gabanta. "Gani". Ya faÉ—a yana kawar da kallonsa gefe guda.
"Ba zaka tsugunna ba ka wani tsaya a gabana, so kake wuyana ya yi ciwo wajen É—aga kaina na kalli fuskarka idan zan yi magana ne? Wannan ai rashin tarbiya ne, haka kake tsayawa a gaban mamanka gangan da kai ka sakata É—aga kai sama dan ganin fuskarka kafin ta yi magana........."
Aikuwa bata kai karshen maganar ba ya dallah mata wani irin gigitattacen mari. Cikin tsananin ɓacin rai ya ce. "Iskancinki ya tsaya a iya kan maman Zainab, dan itace kuka haɗa wani abin da ita, kuma ko ita ɗin ma idan kika sake kuna wani magana da ita kika saƙo mamarmu a ciki sai kin gane ke karamar maras kunya ce! Mahaifiyarmu ba sa'ar ki bace, idan baki ɗauki taki da daraja ba mu tamu tana da daraja.......".
Shi ma bai kai karshen maganar ba baban Zainab ya dalla mashi mari tas a kumatu.
Wani irin ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗaura hannunsa ɗaya a kumatun nasa, nan take idanunsa suka yi jajir kamar jini, da alama ransa ya ɓaci sosai. A hanzarce ya sanya kai ya fice daga gidan, domin gudun kada abin ya kwaɓe masu sosai, yasan idan ya tsaya zuciya zata ɗebesa ya daki baban Zainab ɗin ma, idan ya yi hakan kuma sam bai kyauta ba, yana da halinki sosai, baya manta alkhari, ba irin Haidar bane shi ɗin, yanzu ma ba dan ya lura Hauwa na ƙoƙarin saka mahaifiyarsu a cikin rai'nin wayonta ba da ba zai sanya mata hannu ba, yasan idan bai dakatar da ita ba tabbas zata cigaba da kiran mahaifiyarsu a cikin maganarta, shiyasa ya yi saurin taka mata birki, ban da haka da zai danne zuciyarsa ya shanye walaƙancinta ko dan saboda baban Zainab ɗin.
Kafin baban Zainab ya yi wani magana tuni ya fice daga gidan da sauri.
Kukan munafurci Hauwar ta saka mashi, cike da makircin tana kukan munafurcin ta fara magana. "Wlh baban Zainab ni ba zan yarda ba, kana gani wani ƙato ya dakeni ina matsayin matarka, dole a bi mun hakkina".
(Matarsa kuma?🤔 Yaushe aka yi hakan?🤔 Dole su yi mana bayani)
Hakuri ya fara bata tare da gaya mata to ba ga shi ya rama mata marin ba. Kafewa ta yi a kan ita fa ba zata yarda ba, wannan marin da ya yi masa ya yi mata kaɗan, idan yana son ta hakura dole ya karɓi komai nasa daga hannun Sadiq ɗin, ya karɓi keys ɗin shagonsa da komai nasa, sannan Sadiq ba zai bisu sabon gidan da ya gina ba, maman Zainab kawai zasu ɗauka, Sadiq ɗin ya koma gidansu. Tirƙashi da alama da biyu ta takali Sadiq ɗin da faɗa, da alama tana da manufa sosai a kan dukiyar baban Zainab ɗin, so ta lura Sadiq ɗin zai kawo mata cikas shiyasa ta takalo faɗar, ga shi kuma da alama burinta zai cika, wanna Hauwar anyi makira wlh.
"Duk yadda kike so haka za'ayi, zan karɓi komai na, shikenan?". Ya yi maganar yana goge mata hawayen munafurcin da take zubarwa.
Kai ta gyaÉ—a mashi alamar e hakan ya yi mata. "Tom shikenan mu je cikin ko?".
To ta amsa mashi da shi tare da wucewa gaba tana mai tambayarsa to yaushe zai karɓi keys ɗin daga hannun Sadiq ɗin. Amsa mata ya yi da duk lokacin da take so. Tana ƙoƙarin shiga cikin parlourn ta yi saurin amsa mashi da yau take so. Babu damuwa ya amsa mata da shi tare da shigewa ciki.
Maman Zainab tana zaune a in da take bata tashi ba, already ta jiyo wannan shegiyar muryar Hauwar mai kama da muryar babanin akuya, jin muryar ma yasa bata motsa daga in da take ba, ta cigaba da zamanta kawai, dan yadda ta tsani mutuwarta haka ta tsani ganin fuskar Hauwa a rayuwarta.
"Ana sallama maman Zainab ba zaki amsa mana ba sai kace ba musulma ba? Ko dai kin manta da muhimmancin sallama ne? Ina karatun islamiyar da kika yi? Ko dai ya zube ne?". Cewar Hauwar, ta yi maganar tana ƙoƙarin zama a saman sofa, cike da iyashege da shakiyanci tare da son ganin ta bakantawa maman Zainab ɗin rai ta yi maganar tata.
"Kada ki kuskura ki zauna mun a saman kujera Hauwa, idan kuma kika zauna wlh zan yi maki ɗanyen aiki, kin san halina!". Maman Zainab ta faɗa tare da miƙewa tsaye.
Kallon baban Zainab Hauwar ta yi ta ce. "Honey waye ya sayi kujerar ne? Kai ne ko kuma daga gida ta zo da su?".
Zama ya yi a saman kujerar mai zaman mutu É—aya. "Ni na saya Hauwa'u na".
Wani irin shu'umin murmushi ta saki kafin ta ce. "To maman Zainab ashe kujerar na mijinmu ne ma ba naki ba, to ki bari sai kin sayi naki sai ki hanani zama, amma wannan ai nima nawa ne tun da mijinmu ya saya!".
Wani irin murmushi wanda ya fi kuka ciwo maman Zainab ta yi, ƙoƙari take yi ta ɓoye ɓacin ranta, saboda ta lura burin Hauwa ne kullum taga ta cusa mata baƙinciki, in kuwa haka ne to bai kamata ta bari Hauwar tana ganin ɓacin ranta ba, hakan yasa ta yanke shawarar fito da nata makircin na mata, ai ba Hauwar ce kawai ta iya makircin ba, kowa ma ta iya.
"Hauwa kenan, to ki zauna a kai ki ga ɗanyen aiki, idan kika zauna ne kuma zaki san ainahin wanene mamallakin kujerar". Ta faɗa tana mai cigaba da ƙaƙalo murmushi dole, daga ta ciki kuma zuciyarta kamar zai fashe, barema da ta ji Hauwar ta ambaci baban Zainab da sunan mijinsu, hakan ya tsaya mata a rai sosai, sai dai taki yarda ta fitar da ɓacin ran a fili bare ma Hauwar ta gani ta ji daɗin ta ɓata mata rai.
Kasancewar Hauwar ta san halin ƙawar tata sarai, sai bata zauna a saman kujerar ba, sai ta fake da jan magana, irin kada ace ta tsorata ta ƙasa zama a saman kujerar, ta fake da kananan maganganu tana ta soki burutsu tana ƙoƙarin ta cusawa maman Zainab ɗin ɓakin ciki ta hanyar nuna mata cewa ai baban Zainab yanzu mijinta ne, har da wani cewa kila ma yanzu sun sami ɗan tayin ciki da bai wuce sati ɗaya ba.
Ba yake maman Zainab ɗin ta gama fahimtar dan ta ƙuntata mata ta zo gidan, sai bata nuna kamar ta damu ba, sai ma murmushi da ta saki tare da cewa. "To ai dama shi namiji mijin mata huɗu ne, me a ciki dan ya aureki? Yanzu ma ai akwai sauran gurbin mata biyu a tattare da shi, so yana iya cike gurbin ya rufe kofa kawai, idan ma bashi da ƴan matan da zai cike gurbin da su ba sai mu samo mashi ba, ki samo mashi ɗaya in samo mashi ɗaya ya kara ya rufe kofa me a ciki?!".
Sam sam Hauwa bata so hakan ba, ta so maman Zainab ɗin ta tada balli dan su ji daɗin yi, ko kuma ta hau kuka burinta ya cika, amma ina maman Zainab ta gwada mata cewa ai ita ma ta iya makircin, ta shanye ɓacin ran tsab ta ɓuye kayanta.
Meyake faruwa a tsakanin Hauwa da kuma baban Zainab ne? Nasan kowa tana son sani, to ku matso ku kasa kunne. Hauwa dai sara ce ta zo mata a kan gaɓa, dama already ta kashe aurenta saboda ta auri baban Zainab ɗin, zaman idda take yi a gidan mijinta da ta mayar da shi wani soloɓiyo, dama tana can tana shirin yadda zata yi ta mallaki baban Zainab ɗin cikin sauki, ta kai sunansa wajen wannan bokan nata na kan dutse, sai bokan ya ce mata aikin ba zai taɓa yiwuwa ba dole dole sai da wani abinsa da ya taɓa amfani da shi, ko dai single ɗinsa ko short ɗinsa, ko wani abin nasa, to tarasa taya zata yi ta sami wannan, tana ta tunani, kwananta uku da gama idda ta sake komawa wajen wannan boka, a nan ma ya sake jaddada mata aiki ba zai yiwu ba dole sai ta kawo abin da ya gaya mata ɗin nan. Hakan ta kwaso jiki kamar wadda kwai ya fashewa a ciki ta dawo, kwananta biyu da dawowa daga wajen bokan maman Zainab ta kirata a kan matsalar da take ciki, ta yi matuƙar farinciki da jin hakan, domin ta samu damar da zata cinwa burinta, hakan yasa bata yi ƙasa a gwiwa ba wajen bawa maman Zainab ɗin shawarar su je wajen wannan boka, ta kuma zagaya ta gayawa bokan nata ga abin da take son ya yi mata zasu zo a tare da maman Zainab ɗin, kada ya nuna kamar ita zai yi wa aiki, ya nuna cewa maman Zainab ɗin zai yi wa aiki, idan ya yi mata hakan komai ya tafi dai'dai zata bashi maƙudan kuɗaɗe.
Da yake bokan mutuminta ne sun saba, ba yau ya fara yi mata aiki ba, shi ya yi mata aiki ta mayar da mijinta soloɓiyo sai abin da ta ce zai yi, ya kuma yi mata aiki ta mallake dangin mijin nata basu da bakin magana a kanta, so sun jima a tare da bokan, hakan yasa ya aminta da wannan aiki da ta kawo mashi, cikin sirri suka shirya komai ta munafurci maman Zainab. Bayan sun zo an yi aikin ne sai Hauwar ta kwashe kayanta daga gidan mijinta ta koma gidan iyayenta a garin Kaduna garinsu maman Zainab ɗin kenan, dama already ta gama iddarta da tsawon sati ɗaya ma kenan, burinta ya cika da samu kan baban Zainab, so a Kaduna baban Zainab ya je ya nemi aurenta, dama na gaya maku ƙanin babanta da take a hannunsa mayen son kuɗi ne, sai abin da Hauwar take so yake yi, dan ita take ɗaukar nauyinsu, dan haka bai wani ja ba da Hauwa ta ce ga mijin da zata sake aura, a takaice dai yanzu sati guda kenan da ɗaurin aurensu, shi baban Zainab iyayensa basu sani ba, ita ma maman Zainab bata sani ba, shi kuma kanin baban Hauwa kuɗi kawai yake so ba ruwansa da tambayar daga ina Hauwar ta samo miji ko ya halinsa yake ko kuma ina iyayensa, shi dai kawai ya bi umarnin Hauwar gudun kada ta cire masu tallafi ya shiga uku, zuciya ta mutu ba zai fita ya yi sana'a ba, Allah ka rabamu da matatciyar zuciya. In short wannan shi ne abin da ya faru a tsakanin Hauwa da baban Zainab, yanzu maganar da nake maku sun tare a sabon gidansa, shi ne fa tsabar mugunta irin na Hauwa, dan son ta kuntatawa maman Zainab ne yasa ta cewa baban Zainab ɗin lallai dole dole su zo su ɗauki maman Zainab su koma sabon gida a tare. Da alama so take ta kashe maman Zainab da bakinciki, wato su koma sabon gida a tare dan ta je ta cigaba da cusa mata kayan takaici, wannan Hauwa tamkar green snake under green grass take, shegiya silent killer, ta san ta kan duniya, cikin ruwan sanyi zata dama mutun.
To mata ina fatan wannan yazama darasi a garemu, duk wanda zata ce maki ki je wajen boka wane kaza, ko kije wajen wane ya biya maki bukatunki, hakan yana nufin tasan bokan kenan, sun jima a tare, idan baki ji tsoron Allah kin koma ga Allah mahaliccin kowa da komai ba kika biye mata ta kan iya yi maki irin ta Hauwa, ni labarin gidansu Zainab yi mun yake yi kamar true life story wlh, kamar gaske haka nake jinsa, dan mata dayawa suna tabka irin wannan babban kuskure, yaushe zaki yarda bawa mai kafa biyu! Hannu biyu irin naki, mai yin kashi da fitsari, mai cin abinci kamar yadda kike ci, mai kwanciya ya yi barci ya kuma tashi ya yi tafiya, yaushe zaki yarda mutun kamar ke zai iya biya maki buƙatar da ke ba zaki iya biya ba?! Wannan magana hankali zata ɗauka kuwa?! Mutun ne fa kamar ki! Komai da yake da shi kina da shi! Amma kike yarda da cewa shi ne warakar matsalarki?! To dai ga Hauwa ta nuna maku aya, idan baku kuji bin shawarar kawaye domin Allah ba, zaku guda dan gudun cin amana, bare ma ace kinfi kawar komai, kin fita jin daɗi da morewar rayuwa! Ai abin da kuka ga Hauwa ta aikata wlh kaɗan ne ma a kan wata idan ta tashi tabka maki nata son zuciyar, babu mai sanin mutun sai Allah, Allah shi kaɗai yasan ɗan adam in and out, ko shekara ɗari kika yi a tare da mutun baki isa ki ce kin san shi in and out ba, dan a kowani rana, a kowani lokaci zuciyar ɗan adam tana juyawa tamkar juyin agogo, dan haka mata gareku sai ku kiyaye, kun dai ga aya ƙarara, babu mai yi sai Allah, kuma babu mai hanawa sai Allah, ki miƙa lamuranki ga Allah ki jira ki ga ikon Allah, ba wai ki dogara da wani ƙaton banza mai kashi da fitsari ba!!!. Allah yasa mu fi karfin zuƙatanmu.
Mu koma kan labarinmu tun da kunji menene yake faruwa a tsakanin Hauwa, baban Zainab da kuma maman Zainab da yadda aka yi waÉ—an nan abubuwa suka faru, dan haka mu koma kan cakwakiyar domin ganin ya wasan zata kaya.
Gyara tsayuwa Hauwar ta yi, ta dai kasa iya zama a saman kujerar, dan fa ba karya tana tsoron maman Zainab sosai, tasan halinta sarai, macece mai hakuri da kawaici, amma kuma idan ka kureta, dama ance mai hakuri fa bai iya fushi ba, so a gaskiya maman Zainab tana da zuciya over, faÉ—arta kuma babu daÉ—i idan ta fara shi, hakan yasa Hauwar bata zauna a saman kujerar ba, sai ta ce. "Allah ko maman Zainab, gaskiyarki haka ne, namiji mijin mata huÉ—u ne, to amma fa banda honey, shi daga ke sai ni mun ishe shi".
Sake sakin murmushi wanda ya fi kuka kuna Maman Zainab ta yi kafin ta ce. "A'a ki barshi ya cike huÉ—un kawai zai fi, ko dai kina jin tsoron yin kishi da su ne idan suka shigo? Kada ki damu ai ni zan tsaya maki". Ta yi maganar tana jefa mata wani irin kallo mai wuyar fassaruwa. Yau fa ake yinta a wannan gida, kowacce ashe ba tayar baya bace.
Ajiyar zuciya Hauwa ta sauke. "To ai ni bana kishi, nafi karfin na yi kishi da mace, ke baki gani bane, yanzu duk bama wannan ba, munzo É—aukarki ne ke da yara mu koma sabon gida, mu je mu haÉ—u a can mu zama cikakkun family ai yafi, nasan kuma kina kewar honey sosai, bai kamata ya barki a nan kina É—aukar kwanaki baki sanya shi a idanunki ba, shi ne naga ya dace na zo na É—aukeki mu koma can tare, at least a kowace rana zaki sanya shi a cikin idanunki ko sau É—aya ne kam". Cike da mugunta sosai ta yi maganar, ta kuma yi maganar ita ma tana wurgawa maman Zee É—in wani irin kallo na nuna tsantsar isa da rai'nin wayo. So take dole dole sai ta kuntatawa maman Zainab É—in, burinta kawai taga bacin rai ya bayyana a saman fuskarta.
"Allah ko?". Maman Zee ta faÉ—a tana binta da kallo. Wannan shi ne idan mutun yana son ganin kukanka to kada ka yarda ka bari ya tafi ba tare da ka nuna mashi dariyarka ba, sai dai bakin ciki ta kashe shi!.
Hura chewing gum dake a bakinta Hauwar ta yi kafin ta ce. "Yeah hakan naga ya dace, ai bai kamata mu barki kina zaman kaÉ—aici tare da gauranci ba, dan haka ki shiga ki É—auko mayafinki kawai mu tafi ko honey?". Ta kai karshen maganar tare da juyo da kallonta a kansa. Shi dai ya zubawa wayarsa ido yana aikin latsawa, da alama ma hankalinsa baya a kansu.
A takaice ya ce mata. "Yadda kika ce hakan za'ayi".
Wani irin tauna chewing gum ɗin nata ta yi sai da ya bada sautin kas kas tare da sakin wani shaiɗanin murmushi. "Tom maman Zainab kin ji honey ya ce yadda nace haka za'ayi ba sauran ja, to na ce ki shiga ki ɗauko mayafi mu wuce, waɗan nan tsofaffin kayan ɗakin naki duk ki barsu a nan ko kuma ki turawa mama Kaduna ta yi amfani da su, akwai komai a sabon gida an zuba, so bamu buƙatar tsofaffin kaya".
Haƙiƙa a wannan gaɓar maman Zainab ta kulu da bakinciki, ta zo har wuya, kiris take jira ta fashe, amma sai ta kara daurewa, duk da ta rasa me zata sake cewa da Hauwar, hakan bai hana ta ƙaƙalo murmushin dole tare da sauke ajiyar zuciya ba. Sannan ta sanya kai zata wuce izuwa cikin ɗakinta.
"Kiyi sauri, kada ki bata mana lokaci, dan ba zan iya jimawa a wannan gidan ba, zafi ya yi yawa babu Ac, kuma yanzu lokacin cin abincin honey ya kusa". Cewar Hauwa.
Tamkar maman Zee bata ji ta ba, sam bata juyo gareta ba, ta nufi cikin É—akinta kawai zuciyarta na tafasa tamkar zai fasa kirjinta ya fito waje.
Tana shiga cikin É—akinta Zainab ta fito daga nasu É—akin zata nufi waje.
"Ke Zainabu abu zo nan". Hauwa ta faÉ—a, har lokacin kuma tana tsaye, ta kasa iya zama a saman kujerar, da alama tana mutuwar tsoron maman Zainab, kawai dan taga baban Zainab yana bata goyon baya ne ma yasa ta tsaya har ta iya gayawa maman Zee É—in magana, ban da haka tana tsoronta sosai, alamu sun nuna a lokacin kuruciyarsu Hauwa ta sha kashi a hannunta sosai.
Wani irin matsiyacin kallo Zainab ta wurga mata kafin ta sa kai ta wuce waje, taki zuwa, dama fa ita Zainab kun san ba kamar Khadija take ba, bata da kunya ko kaɗan, kuma idan baku manta ba tun suna yara Zainab ɗin tafi kowa tsanar Hauwar, bata son ganinta ko su haɗa hanya, bare kuma yanzu da ta ji abubuwan da suka faru, mamansu ta gaya masu komai bata ɓoye masu ba, dan gudun kada su aikata irin kuskuren da ita ma ta aikata, hakan yasa ta sanar da su, so sun san komai, shiyasa Zainab ta kara tsanar Hauwar over ta kuma ɗaura ɗamarar yi mata rashin mutunci idan ta shiga gonarta. Kawai cakwakiya kam.
Girgiza kai Hauwar ta yi ba tare da ta sake yin magana ba, da alama akwai abin da zata ƙullawa Zainab ɗin kenan.
In short haka Maman Zainab ba musu ta É—auko mayafinta tare da sanya su Khadija suka É—auko nasu mayafan domin su tafi, abin da yasa zata je sabon gidan kuma domin su gwabza ne, a cewarta yanzu ta dai'na yin shiru, duk uban da ya ce mata kule sai ta ce mashi cas, sannan kuma tasan tun da Hauwar ta zo ta ce su tafi to fa ko ta ce ba zata je ba baban Zainab zai ce lallai dole ta shirya su tafi, ga shi mamanta ta hanata sake yi mashi musu a kan abu, so gara kawai kada ta yi wani ja in ja ta kara zubar da mutuncinta a gaban Hauwar, dan tasan a yanzu idan ta yi ja in ja da baban Zainab ma yana iya saka mata hannu ya kai mata duka, kunga kuma ai mutuncinta ya kara zubewa a idon Hauwar, dan haka gara mata kawai ta bisu, ta nunawa Hauwar ita ma a shirye take da su je sabon gidan ai. E lallai yanzu kam maman Zainab ta shirya gwabza faÉ—ar domin kwatar Æ´ancinta.
Suna fita daga gidan ba jimawa sai ga su maman Haidar sun zo, dan sun sami labarin yau ya zo gida. Sai dai ko da suka zo kofar gidan a rufe, already su baban Zainab É—in sun tafi, baban Zainab ya sayi sabuwar mota ba tare da sanin Æ´an uwansa ba, Hauwa ce nan ta sanya shi ya sayi motar wai dan ya koya mata, idan ta iya sai ya bar mata kyauta, aikuwa ya saya kuma yana É—an koya mata a hankali hankali, so a yanzu da motar suka zo suka É—auki su maman Zainab, Hauwa an dake a kujerar gaba, sam maman Zainab bata nuna kamar ta wani damu ba, ta shiga gidan baya a tare da Zainab da Khadija.
Su maman Haidar kuwa ganin gidan a rufe yasa suka juya suka nufi kasuwa ita da maman Hanif, a tunaninsu zasu same shi a kasuwa, ba a tare da hajiyarsu suke ba yau, Hajiyar tasu ta ce idan sun gan shi su ce yazo tana son ganinsa, shi ne ma yasa suka zo nemansa.
To bari mu leƙa kasar TUNISIA, wato KINGDOM OF POWER muga me ake ciki.
KINGDOM OF POWER. 💪🔥â¤ï¸
Yau ta kasance ranar jumma'a, kuma a yau su Obaid jirginsu ya ɗaga zuwa Dubai kamar yadda King ya bada umurnin komar tasu, sai dai fa jirgin nasu bai ɗaga da wuri ba, jirgin karfe 6 na safe zasu bi, amma saboda abin da ya faru a cikin kingdom ɗin yasa suka bi jirgin 11 na rana, shi ma dai da kyar suka tafi ɗin, sai da Jaish ya kaisu airport da kansa, domin yau kingdom babu lafiya, ɗaya daga cikin matan king bata da lafiya, hankalin kowa a tashe ban da Jaish da shi ko a jikinsa, ba abin da ya damesa tun da ba mommarsa bace abin ya shafa, shiyasa ma ya iya raka su Obaid airport hankalinsa a kwance, shi ma Yah Jawad bai wani damu sosai ba, ya dai ji babu daɗi, ita kuma Mammaien Yah Jawad ɗin har wani farinciki da rashin lafiyar na mama ta yi............. To me ya sami mama kuma?🤔
King kuwa yana.............
ðŸ¤KADA KU MANTA WANNAN DADDAÆŠAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi ðŸ‘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥ðŸ¤
ðŸ¤ðŸ”¥ð—¥ð—”ð—ªð—”ð—¡ð—œð—¡ 👑 ð—ð—”ð—Ÿð—œð—¡ð—–ð—œðŸ”¥ðŸ¤
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
ð— ð—”ð—Ÿð—Ÿð—”ð—žð—œð—¡
â¤ï¸â€ðŸ”¥FATEEMA ZAHRA MUSA â¤ï¸â€ðŸ”¥
(â¤ï¸A-K-A ð‘·ð‘¹ð‘°ð‘µð‘ªð‘¬ð‘ºð‘º ð‘»ð‘¬ð‘¬ð‘´ð‘¨ðŸ”¥)
🔥ðŸ¤T🔥ðŸ¤T🔥ðŸ¤W🔥ðŸ¤......💻
â¤ï¸ð‘«ð‘¨ð‘»ð‘¬ 3/9/2024.....âœï¸ðŸ“šðŸŒ¹
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
ðŸ¤ð‘ºð‘»ð‘¬ð‘· 1......âœï¸ðŸ“šðŸ”¥
اللَّهÙمَّ صَلّ٠عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌ، اللَّهÙمَّ بَارÙكْ عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا بَارَكْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌâ¤ï¸
E____________44🔥
KINGDOM OF POWER. 💪🔥â¤ï¸
King kuwa yana room ɗin na mamar, saboda ya duba jikin nata, hankalin kowa a cikin kingdom ɗin nan a tashe, kowa sai tunani yake yi a kan me ya sami ɗaya daga cikin matan King ɗin, bayani kuma bai fita a kan me ya sameta ɗin ba, an dai sanar da cewa bata da lafiya. Abin da yasa aka sanar da cewa bata da lafiyar ma shi ne, kingdom of power tana da wata gasa da take gabatarwa na dawakai a kowani jumma'a, kowacce sati suna gabatar da wannan gasa na tseren dawakai wanda jaruman mayaka zasu fito a gabza gasar, wanda ya yi nasar zuwa na ɗaya yana da gagarumin kyauta daga hannun King, daga ɗaya zuwa na goma ake bawa kyauta, ana gabatar da gasar ne domin nishaɗi. A gabaɗaya tarihin kingdom of power ba'a taɓa yin jarumin mayaki biyun HOORAIN ba, shi ne a kullum yake zuwa na ɗaya, kuma kowani sati sai ya shiga wannan gasa, na gaya maku shi ɗin abin alfaharin KINGDOM OF POWER ne, suna ji da shi, haka zali babu yakin da za'a tafi ba tare da shi da commander ne suka ja ragamar rundunar mayakan ba, kuma ko ciwo Hoorain bai taɓa ji a wani yaki da suke zuwa ba, gara commander ya taɓa jin ciwon da sai da ya kwanta jinya, saboda jikin tsufa ya sha wahala sosai, shi kuwa Hoorain sabon jini ne, jininsa a tafashe yake, lafiya lou yake jan ragamar rundunar sadaukan yaki sama da dubu biyar ya jagorancesu su je yaki su dawo, basu taɓa fita yaki basu yi nasara ba, duk girman daula in dai Hoorain da Commander suka jagoranci rundunar mayakan to fa sai sun jijjige wannan daula sun jefar da ita, basu gudu kuma basu ja da baya a fagen yaki komai tsanani kuwa.
Idan ka kalli Hoorain ta wata fuska zaka gansa so silent haka, baya da magana kuma baya son hayaniya, amma fa da zaka same shi cikin abokansa mayaƙa ƴan uwansa, yana hira da su sosai, idan ka kalle shi ta fuskar assistant commander kuwa ba zaka so ka sake yin ido huɗu da shi ba, domin kuwa ganinsa a wannan siffar fa bata da kyau, wasu suka ce tamkar ganin mutuwa ne ganin Hoorain a siffar assistant commander, gara ku haɗu da shi a Hoorain ɗinsa a kan ku haɗu da shi a assistant commander.
So a kullum a tseren gasar dawakai ma shi yake zuwa na ɗaya, kunsan ita fa doki tana gudu ne kusan dai'dai da bugawar zuciyar wanda yake a kanta, iya karfin da ka sanya mata iya gudun da zata yi kenan, iya yadda zuciyarka take harbawa domin muradin cin nasara, iya power da zata baka kenan, so shi Hoorain yana da zafin zuciya sosai, bugu da kari akwai karfin dantse kamar dokin, idan ya hau kanta yana bata wuta sosai da sosai ta yadda idan ya zo na ɗaya ma ratar dake tsakaninsa da wanda zai zo na biyu ba ƙaramar rata bace, yana kere masu sosai, ko kamshinsa basa jiyowa a gasar. Shi fa har wani wasa yake yi da dokinsa a hanya ma idan ya kusa iso wa, har wani irin karkatawa yake yi kamar zai faɗo kasa, amma har ya dawo cikin kingdom ɗin babu mai iya cin masa bare ma ya wucesa.
Sosai Gimbiya Zunaira da kuma Gimbiya Chuchu suke jin daɗin kallon wannan gasa, saboda Zunaira ma yasa King ya kara karfafa wannan gasa ta zama kamar al'ada a masarautar, wajen da ake yin wannan gasa a cikin masarautar take, amma ba ta bangaren fada ba, ta baya ne, an ƙawata wajen sosai, babban fili ne sosai da sosai, tsawon wajen gasar har ta fita daga cikin kingdom ɗin, basa iya ganin karshen filin daga in da suke, kafin a fara gasar dama already za'a ɗaurewa wata lafiyayyar bujumar doki wani jan kyalle mai ɗauke da tambarin kingdom of power wadda kowa yasan tambarinsu shi ne kan zaki, so za'a ɗaurawa wannan lafiyayyar dokin wannan kyalle, sannan a saketa kamar da minti 20 haka, sannan su Hoorain su bi bayanta da nasu dawakan, wanda ya riga kama wannan dokin ya ciro wannan jan kyalle ya kuma ɗaure dokin dan kada ta yi wani wajen, sannan ya dawo da kyallen wajen King shi ne ya yi nasara, abin fa ba sauki ne da shi ba, ba ƙaramin abu bane, har faɗa mayaƙan suke yi a tsakaninsu, su jiwa juna ciwo, amma a haka kullum sati Hoorain ne yake yin nasarar zuwa na ɗaya, duk masu yin wannan gasa fa matasan sadaukan mayaƙa ne masu jini a jika, dukkansu basu wuce sha'anin Hoorain ɗin ba a shekaru, amma shi ya kerewa tsara, renon Commander Zafar ai dama ba za'a haɗa shi da kowa ba, ɗan commander da kansa ai dole dama ya kerewa tsara, horon da ya samu na musamman ne, tun yana ɗan ƙaramin yaro Commander yake koyar da shi dabarun yaki da sauransu.
So a takaice dai saboda wannan gasa yasa labarin rashin lafiyar mama ya fita, King ya tsoke yin wannan gasa a wannan sati saboda rashin lafiyar tata, hakance yasa kowa ya sami labarin bata da lafiya, amma babu wanda ya san me ya sameta sai Æ´an cikin gida.
Nasan kuma kuna son jin me ya sami mama, to ku saurara, daren jiya ne aka samu wasu mayun kwari da babu wanda yasan daga ina suka fito, suka rinƙa ɗana mata harbi kamar zasu kasheta, kafin ta yi ihu a samu a kawo mata agaji duk sun yi mata ruɗu ruɗu da jiki, duk in da suka ɗana mata harbi sai wani kuraje ya bayyana a wajen tulele da shi jajir, abin ku da farar fata, duk jikinta ya yi ruɗu ruɗu, hakan ya saukar mata da mummunar kuma zazzafar zazzaɓi sosai, ga kurajen sai yi mata zogi da raɗaɗi suke yi, ga azaban kaikayi, babu kuma halin ta sosasu, idan ta ce zata sosa sai raɗaɗin azaba ya kasheta, wannan shi ne halin da take a ciki, harta face ɗinta waɗan nan shegun kuraje basu bari ba, har face kwarin suka cijeta, fuskarta ya kunbura kamar cincin puk puk.
Tun a wannan dare da abin ya faru, family gabaɗaya suka taru a room ɗinta lokacin da take ihun neman taimako, ba wasu masu yawa bane fa kwarin, basu fi su goma ba amma suka yi mata wannan aika aikan, kuma baa iya gane menene ya cijeta ɗin ba, domin kuwa kwarin basu da yawa, gasu ƙanana ido baya ganinsu. Sai dai tun a daren Momman Zunaira ta fahimci tabbas wannan cizon na waɗan nan kwarin na su Obaid ne, sai dai bata nuna kamar ta gane nasu ɗin bane, domin kuwa tasan idan kowa yasan nasu ne ba ƙaramin rikici abin zai zamar masu ba, mama tana da yara ita ma, so suma za su ce ba zasu bari ba sai sun ɗauki fansa, saboda dai suma jinin Modarawa na gudu a jikinsu, akwai jinin Akka, ba sai na sake faɗa ba kun san dai Modarawa basu barin bashi, ko ya ka taɓosu sai sun rama, babu yafiya, idan baka taɓosu ba kusan za'a ce sun fi kowa iya zaman amana da adalci ga mutane, amma ka kuskura ka taɓosu fa sai sun rama, ba ɗaga kafa, idan kowa ya ce zai ramawa mamarsa to fa daga nan gida kuma ya dai'na zaman lafiya, duk da cewa dama yanzu ma ba wani zaman lafiya iyayen suke yi ba, ɗan garama yaran nasu da yake basu ne masu yin kishinba, su kansu a haɗe yake, amma iyayen dai sai a hankali, kun san da hakan.
Wannan dalilin yasa momma ta ɓoye cewa kwarin nan nasu twin's ne suka ciji Mama, amma dai ta ƙuduri niyar sai ta yi masu faɗa sosai, zata tsawatar masu ta yadda ko da sunan wasa ba zasu sake yi wa wani makamancin irin hakan ba, domin wannan irin cizon kwarin ba ƙaramin azaba ne da shi ba.
Amma kash bata samu damar ganawa da su ba har suka wuce Dubai, hakan kuma ya samo asali ne saboda suna a tare da mamar ita da Mummyn Gimbiya Chuchu da Mammiensu Yah Jawad, sai kuyangun da suke yi wa mamar aiki, su ne a tare da ita.
Kwararrun likitoci kala kala har kala wajen biyar ne suke a kan mamar suna kula da lafiyarta, ba'a kaita hospital ba duk da a cikin kingdom É—in asibitin yake, King ya ce likitoci su zo har cikin room É—inta su yi treating É—inta.
Hakan kuwa aka yi, suka zo suna kula da ita, so su Momma suna a tare da ita. King ma yau bai fita fada ba, yana a tare da ita, bata iya gane wanda yake kanta ma saboda zafin zazzaɓi, tasha bakar azaba, har da suma ta yi kafin likitocin su zo, a sume suka zo suka sameta. Da kyar da taimako Allah suka bata taimakon gaggawa ta farfaɗo.
King bai bar wajenta ba sai da lokacin tafiyarsa masallacinsa na jumma'a ya kusa, sannan ya nufi part É—insa domin ya je ya shirya.
Akka ma tana cikin room ɗin, ita ma Akka ta so ta gane cewa waɗan na kwari na su twin's ne suka ciji mama, saboda ita ma Akkar ƴan biyu ce, daga wajenta aka gado twin's ɗin nan, sai dai ita ɗan uwanta namiji ne, amma kuma sai zuciyarta ya raya mata a kan me su twin's zasu yi wa mama wannan aika aikan? Ganin babu wani dalili ne yasa ta kawar da tunanin su suka yi wannan aikin. King bawan Allah yana can yana tunanin ta ina aka samu irin waɗan nan shegun kwarin masu cizon har cikin room ɗinta saman gado? Dan ya gano waɗan nan kuraje da suka feso mata a jiki cizon wasu halittune daga cikin halittun Ubangiji, sai dai bai san ya aka yi aka sami kwarin ba, bai kuma ga kwarin da idanunsa ba, yasa an cire komai na gadonta an kakkaɓe, amma basu ga komai ba! Ya ɗaura tuhumarsa a kan kuyangun da suke gyara mata ɗaki, bai san shakiyan ƴaƴansa suka yi aika aikan ba, sun koma Dubai sun barsu da jidali. Wannan rashin lafiya ta mama ai jidali ne suka ɗaurawa family, dan kowa sai jikinsa ya gaya mashi, zasu sha wahala kafin mamar ta sami lafiya.
Sosai King ya yi shirinsa kamar yadda ya saba zuwa masallacin, ya haɗe a cikin farar alkyabbar wadda kwalliyar jikinta ma duwatsun gold ne, sai kyalli suke yi, haka zali takalmar sarautar da suke a kafafunsa kwalliyar jikinsu da zallar madarar gold aka yi su, ya sha naɗin na wani haɗaɗɗen farar rawanin, ya yi masifar kyau sosai, haka ya fito domin zuwa masallacin. Already an ƙawata mashi dokin da zai hau, ta sha kwalliya da kayan ado na dawakai masu bala'in kyau da tsada, kuɗin kayan kwalliyar dokinsa kawai ya isa ya sayawa mutun katafaren gida a babban birnin tarayya Abuja Nigeria.
Tun ba'a buÉ—e kofar fada ba kilishi da sallama suka fara zuba kirarin sarki zai fito, masu busa suka hau yin busa, tun kafin a buÉ—e kofar fada da take fuskantar harabar kingdom É—in mai sanarwa ya sanar da fitowar sarki ta hanyar amfani da amsakuwa. Hakan yasa kowani bawa mai rai da yake cikin masarautar sai da ya nutsu jin sarki zai fito.
Nan take masu busar dake a wajen fadar suna dakon fitowarsa suka fara buga busar tasu, masu kirari ma suka fara rera kirarinsu, abin gwanin ban sha'awa, komai cikin tsari da bin ka'ida tare da ƙayatarwa, mayaka duk sun nutsu, ga wasu jiga jigan mayaƙa da a kallah zasu kai su 100 da suka jeru tun daga farkon kofar fadar har izuwa karshen stage na haurawa wajen kofar katafaren fadar, duk waɗan nan mayaka suna a ƙarƙashin kulawar Hoorain ne tare da bin umarninsa, already dama sun saba yin hakan, suna tsayawa a wajen ne domin tabbatar da sun bawa King tsaro har ya hau saman dokinsa zuwa masallaci.
Commander kuwa dama shi a cikin Fada yake zama kun sani, da shi ake tattauna duk wata zance da ta shafi fada dama kingdom ɗin gabakiɗaya. Bawan Allah tsufa ta ɗan fara kama shi, yana da ƙoƙari da jajircewa ne sosai, assistant commander yana kula da mayakan sosai, shi kuma yana cikin fada, idan ma zasu je yaki to yana ciki zasu tattauna, idan King ya tsayar da zance sai ya kira Hoorain ya gaya mashi, shi kuma ya hau shirya sadaukai kawai, so haka tsarin yake.
Sai da komai ta kankama sannan aka buɗe katafaren kofar fadar, su Galadima ne a gaba shi da malam liman, sannan su makama suka biyo baya, King yana a tsakiya an rufe shi, wasu jiga jigan mayaƙa biyu suna take mashi baya, Hoorain and commander kuma suna ta gabansa, su ne masu bashi tsaro ta gaba.
A haka suka fito suka nufi wajen dokin da aka shirya mashi dan zuwa katafaren masallacinsa da yake a cikin kingdom É—in, sai dai masallacin yana da nisa da family part.
A haka King ya nufi masallacinsa masu busa suna ta aikin busa tare da zazzaga mashi kirari kala kala. Dakarun kwararrun mayaka ne suka yi gaba domin sharar hanya kada ko tsinke ya taɓa mai girma King.
Ni kuwa na haɗa kayana zuwa DUBAI dan kwaso maku labaran can kuma, mu je muji wace wainar ake toyawa kafin mu sake dawowa mu duba jikin Mama......🥱
DUBAI🔥ðŸ¤
Sosai Leesharh ta sha mamakin ganin irin hidimar da ake yi a gidan yau, ta ga gidan nasu sai baki suke yi, jiniyar motoci ne suke ta dira a cikin gidan duk bayan É—an lokaci, manya manyan baki suke ta yi, ministocine abokan Abu Abdussalam suke ta faman zuwa.
Sai tsantsara girke girke kala kala ake yi, a koda yaushe girki kala kala ake yi a gidan kun sani, to amma yau na musamman ake yi.
Wanka ta tsantsara ita ma tare da shiryawa cikin wani malesian gown mai bala'in kyau launin up pich, ta ɗauki ɗan ƙaramin please call me hijab ɗinta white color mai kwalliyar duwatsu masu haske a jikinsa ta sanya a jikinta, malesian gown ɗin ya zauna a jikinta sosai, ya bi coca cola shape ɗinta kamar dan ita aka yi sa. Sam sam Leesharh bata damu da yin make up ba, bata yin sai jefi jefi, natural beauty gareta, dan haka a yanzu ma bata yi make up ba, natural beautynta ya kata fitowa sosai saboda zama a Ac ga cima mai kyau, sannan ga sabulai masu zafi da suke kara gyara mata skin ɗinta, sai chocolate colornta ya kara fitowa sosai yana wani glowing. Sai dai fa duk da hakan tana ɗan rame, kuma tana firgice, dan a kullum cikin fargaba da zulumi take, kullum tana tsorace asirinta zai tonu, tana cikin tunanin ya zata kasance ranar da akace asirinta ya tonu, ita sam bata taɓa yin tunanin ya za'ayi ta fita daga cikin gidan ma idan ta kammala aikin ba, bata taɓa kawo wannan tunanin bama a ranta, burinta kawai ta kammala aikin ta koma kasarsu. Hmmmm ni kam na ce akwai gagarumin yaki kuwa a gabanki, dan kuwa kin shiga in da babu fita ne, ko dai my people's kun gano mata hanyar fita bayan ta gama aikin da ya kawota ɗin?. Akwai gagarumim cakwakiya, dan kuwa fita daga cikin gidan Abu Abdussalam ba duk kai ba wlh, wane mutun in ji mutuwa! Ba yadda take tunanin abin bane, ya wuci tunanin mai tunani.
Tana shirin nata tana tunanin ta je wajen Sharifat ta tambayeta ko biki za'ayi a gidan ne da yasa ake ta shirye shirye haka, ga motocin ƴan'sanda da sojoji birjin da suka rinƙa rako ministoci gidan.
Ta yi kyau sosai, waje ta nufo. A parlourn ta isko su Fadila suna aikin gyaran parlourn nasu. Sannu ta yi masu tare da sanya kai zata fice daga part É—in nasu.
"Leesharh ki shirya da misalin karfe huÉ—u zamu yi serving na baki drinks da sauran kayan cima a cikin hall É—in Abbie na yin walima". Cewar Fadila.
Kamar zata tambayeta biki za'ayi a gidan ne? Sai kuma ta fasa ta amsa mata dawo okey kawai, a cewarta gara ta je ta tambayi Sharifat zai fi mata kuma zata fi samun cikakken bayani a matsayinta na yar masu gida. Tana amsawa ta wuce izuwa waje. Da kallo su Fadila suka bita har sai da ta fice, sannan ne Radia ta ce. "Gaskiya Leesharh kyakkyawa ce ajin farko, gata kuma black beauty".
"Faɗe ma ai ɓatawa ne". Cewar Fadila, ta yi maganar tana shirya pillows dake a saman sofas ɗin nasu.
Ita kuwa Leesharh kai tsaye bedroom na Sharifat ta nufa, dan tasan tabbas a nan zata sameta. Sharifat yarinya ce da bata cika son hayaniya ba, dayawan lokuta idan bata a tare da Ummienta to zaka sameta a cikin room ɗinta ta haye saman katafaren king bed ɗinta tana aikin karance karance, ita ɗin macece mai ra'ayin karance karance da bincike bincike kamar yayanta Jaish, wato kamar ƴar jarida, sai iya kaƙale kaƙale.
Baki a ɗauke da sallama ta tura kofar room ɗin ta shigo, yau ba ita ta gyara babbar parlourn ba, saboda yau gyara na musamman aka yi mashi, manya manyan masu aikin da suke aiki a hawa na ƙasa ne suka zo suka gyara, ya kuwa sha gyara, kusan komai na parlourn sai da aka canza, aka zuba sabbi, sai tashin fitinannen kamshi parlourn yake yi, kun san larabawa da shegen son turarukan wuta, ƙamshi mai kwantar da hankalin duk wani mai shaƙa ne yake tashi.
Kwance ta isko Sharifat a saman gadonta, ta ci kwalliya kamar ba ita ba, arab dressing ta yi kamar yadda ta saba, ta yi rolling veil a kanta, kasancewarta farar fata hakan yasa bakaken kayan suka yi mata kyau sosai. Ta nutsu cikin karanta wani ɗan littafi da yake riƙe a hannunta, littafin larabci ne. Guyson na zaune a saman sofa a cikin room ɗin nata, yana latsa wayarsa, bai jima da gama magana da su Obaid ba, sun gaya mashi jirginsu ya sauka, suna gidan King Badeen, ya ce yaushe zasu zo, suka ce mashi ai ba za su zo ba sai an yi hutun school, saboda ba lokaci, za su je wajen uncle Rahab kafin su koma school, so ba zasu zo gidan Abu Abdussalam ba. Sarai Guyson yasan da cewa gudun haɗuwa da su Yah Ramish suke yi, hakan yasa basu son zuwa, amma bai wani damu ba ya ce masu shi yana nan zuwa gobe su ga juna kafin su wuce school ɗin, on Monday zasu koma school, daga haka suka yi sallama a kan shi zai je gidan King Badeen ya same su.
Gaisuwa ta ɗagawa Guyson cikin girmamawa. Fuska ba yabo ba fallasa ya amsa mata gaisuwar tata cikin mutunci. A yanzu shi ma ya fara sabawa da ita saboda ganinta a tare da Sharifat da yake yawan yi, so ya fara sakin jiki da ita, ita kuma Sharifat already dama kunsan ita ta fara neman sabo da Leesharh ɗin ma, so a yanzu sun saba sosai, sun zama kamar wasu ƙawaye. Leesharh kuma har yau har gobe tana aiki ne bisa umarnin masu nikaf, duk abin da kuka ga ta aikata sune nan suka bata umarni, a yanzu suna yawan waiwayarta, suna turo mata saƙonni ba kamar da can baya da suka zuba mata idanu ba, da alama a yanzu sun ɗa gano wani haske dan gane da aikin da suka sanyata ɗin ne yasa suke waiwayar tata.
A saman bedside drawer ta zauna tana É—agawa Sharifat É—in ma gaisuwa bayan Guyson ya amsa mata gaisuwar tata kenan.
Rufe littafin hannunta Sharifat ɗin ta yi tare da miƙewa zaune a tsakiyar bed ɗin, fuska a ɗauke da ƙayatattcen murmushi ta ce. "Leesharh kin yi kyau sosai, kamar kin san yau Yah Bilal zai dawo, shi da Yah Ramish za su je ƙasar Tunisia duba jikin Queen Mama, kowa na gidan nan ya yi kwalliya sosai, kinga Yah Guyson ma ya yi kwalliya". Ta kai karshen maganar tana nuna Omar ɗin da hannu.
Haƙiƙa kuwa ya sha kwalliya fiye da kullum, duk da cewa shi dama tun ainahinsa ɗan kwalliya ne, babban yaro ne ɗan kwalisa, shegen son gayunsa ma yasa suke ce mashi Guyson, amma fa gayun da ya ci yau na musamman ne, ƙananan kaya ne a jikinsa, wandon jeans and polo shirts masu bala'in kyau launin white color up and down ɗin dukka, ya gyara kyakkyawar dark black arab hairn nan nasa, abin ba'a magana, kamshi kuwa duk yadda ka kai ga sonta ina ga Guyson ya fika sonta, yana bala'in son kamshi sosai.
Wani irin faÉ—uwar gaba Leesharh ta ji da jin sunan Yah Ramish a bakin Sharifat.
"Kai Masha Allah, Allah ya dawo da shi lafiya, shiyasa naga anata hidima a gidan". Cewar Leesharh.
"E ai dole kiga ana hidima, da Yah Ramish, Yah Rizwan, Yah Bilal, Yah Raj su ɗin na musamman ne a wajen Abbie, yana ji da su fiye da tunaninki, kamar shi ya haifesu, shekaru dayawa fa suna nan ya ki yarda ya bari su je ƙasar Tunisia, saboda ba ya son su yi nisa da shi, yanzu ma ba dan Queen mama bata da lafiya ba da ba zai iya barinsu su yi nisa da shi har haka ba, ko tafiyar da kika ga Yah Bilal ya yin nan dan saboda aiki ne, badan haka ba suna nan a tare da Abbie". Ta kai karshen maganar tare da zuro kyawawan kafafunta kasan bed ɗin.
Miƙewa Guyson ya yi yana faɗin. "Is time, Shareefat lokacin zuwa airport ya yi". Ya kai karshen maganar tare da nufar hanyar fita.
Da sauri ta miƙe ita ma tana faɗin. "Wait for me mana Yah Guyson, Leesharh zan bisu airport, sai na dawo, idan kuma zaki bini ki zo muje, a jerin tawagar motacin Yah Ramish zamu tafi".
Da sauri ta girgiza kai tare da faÉ—in. "A'a ina tsoron binki, sai dai kun dawon kawai".
"Me kike tsoro?". Cewar Guyson. Ya yi maganar tare da tsayawa daga tafiyar da yake yi, ya É—an juyo gareta.
"Ina tsoron waÉ—an nan securitys masu face mask É—in, da kuma waÉ—an can masu manya manyan bindigun, fuskokinsu tsoro yake bani".
Murmushi ya yi har sai da haÉ—aÉ—É—iyar dimple É—insa ta lotsa. "Kada ki ji tsoronsu, babu abin da za su yi maki, kawai face É—insu ne kullum a fusace, amma ai ba zasu yi wa mutun komai ba ba tare da ya yi masu laifi ba, dan haka ki dai'na jin tsoronsu".
Da okey kawai ta amsa mashi, amma fa tsoro kam dole ta ji, waÉ—an nan fusatattun mutane masu kama da dodannin, ita idan aka ce mata waÉ—an nan securitys É—in suna cin namar jikin mutun É—anya ma ba zata musa ba, domin kuwa fuskokinsu babu É—igon annuri ko sauki a kansa, waÉ—an nan idan suka kama mutun ya yi masu laifi Allah sarki, sai dai wani ba shi ba, sun iya ganawa bawa azaba.
Wucewa Guyson ɗin ya yi ya nufi waje, da sauri Sharifat ta riƙo hannunsa tana murmushi, a haka suka fice daga ɗakin suka bar Leesharh. Ta ɗan jima a zaune tana tunanin saƙon da aka turo mata yau da safe, saƙo ne da masu nikaf suka turo mata a kan lallai ta nemi wanene or wacece take kaiwa Ramish abinci a cikin ma'aikatan dake gidan, idan ta gano wanene to lallai ta san ta yadda zata yi su ƙullah alaƙa, su sami kusanci sosai, idan suka saba shikenan akwai wani aikin da zasu bata, wannan shi ne saƙon, yanzu ya za'ayi ta nemo mai kaiwa su Ramish abinci a cikin ma'aikatan gidan nan fisabilillahi? Ma'aikata ba ɗaya ba biyu ba, kowani hawa da nasa ma'aikatan, ita da kwata kwata ma bata san a wani hawa su Ramish ɗin suke ba, ba ta taɓa ganinsu ba, yanzu ya zata yi kenan? Wannan shi ne abin da ya tsaya mata a ranta take ta aikin tunani a kansa tun safe.
Daga karshe dai ta miƙe ta nufi waje domin ta koma cikin room ɗinta, sai tunanin take yi ko dai ta tambayi Sharifat wacece take yi wa su Ramish aiki ne? Ko kuma ta tambayi su Radia? Tana tsoron tambayarsu kuma kada hakan ya zamar mata matsala, kada wani abin ya zo ya faru ace ai ita ce ta taɓa neman masu yi mashi aiki ta shiga uku.
Babbar parlourn ta fito tana tafiya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki. Wani irin razana ta yi tare da zaro idanu tana kallon Ummie dake a zaune a saman sofa mai zaman mutun uku tare da wata jibgegiyar hajiya ita ma tana zaune a saman sofa mai zaman mutun uku. Sosai Leesharh ta zaro waÉ—an nan manya manyan idanun nata tana ganin wannan mata.
"Wlh ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba wannan ita Hajiya two seater da ta É—auko ni daga AAJ House". Ta faÉ—i wannan magana a cikin zuciyarta tana mai cigaba da kallon matar.
Matar bata lura da ita ba, haka zalika ita ma Ummie bata lura da ita ba, da yake parlourn yana da matuƙar girma, daga in da suke zaune da in da take akwai rata sosai da sosai, so basu san da ita a cikin parlourn ba, su suna a saman sofas da suke ta kusa da dining room ne, ita kuma kunga tana ta ɓangaren ɗakinsu Sharifat, akwai rata a tsakaninsu.
Hannu ta kai ta sake goge idanuta sosai domin ta tabbatar da abin da take gani. Tabbas dai wannan mata ce a cewarta, duk da tasa nikaf lokacin zuwanta AAJ House ta ɗauketa, hakan bai sa yau da tazo gidan nan babu nikaf ta ganeta ba, LEESHARH akwai ƙwaƙwalwa sosai, da idon wannan mata ta iya ganeta babu nikaf, idan baku manta ba dama tana iya banbantasu da yanayin idanunsu, to fa hakance yasa take tunanin wannan jibgegiyar hajiya ita ce hajiya two seater.
Lallai akwai cakwakiya, kenan makashin Ramish suna a tare da shi? Meya kawo wannan hajiyar gidan? Wacce iriyar alaƙa yake a tsakaninta da familyn Abu Abdussalam? Ya abin yake? Anya tana da alaƙa ta jini da su kuwa? Wacece ita?. Alƙalamin na ne kawai zai warware maku wannan cakwakiya, ku dai mu cigaba da tafiya, mun kusa cinwa ainahin in da RAWANIN ZALINCI yake........🥱
Salallaɓawa Leesharh ta yi ta nufi hanyar fita daga parlourn ba tare da sun ganta ba, tunani take yi kenan haka kamannin masu nikaf ɗin nan yake? Haka kamanin hajiya two seater yake?!
Kanta ya É—aure sosai, ta kuma shiga ruÉ—ani, ji ta yi ta dai'na gane komai, a haka ta fice daga parlourn cikin dabara ba tare da sun ganta ba. Sai hira suke zubawa a tare da Ummie, da alama suna cikin farinciki tare da annashuwa.
Leesharh tana shiga cikin room ɗinta ta nufi wajen windownta dake fuskantar harabar gidan, ta zuge windown tare da janye labule ta tsaya tana kallon cikin gari, tunani ya taru ya yi mata yawa a cikin ƙwaƙwalwata, har ji take yi kanta yana yi mata ciwo, wannan wace iriyar bala'i ce? Ta tambayi kanta da kanta.
Tana tsaye a wajen jerin gwanon danƙara danƙarar motocin masu zafa suka fara fitowa daga cikin parking space na gidan, sun kasance a jere cikin tsari, hakan ba ƙaramin burjewa ya yi ba, motocin ƴan'sanda uku ne suka yi gaba, sannan waɗan nan jerin motoci suka rufa masu baya, sai motocin sojoji uku suka take masu baya. A kallah motocin zasu kai 15, da alama airport suka nufa, da kallo kawai ta bisu har suka fice.
Da fitarsu bai fi da minti biyu ba wasu jeren danƙara danƙarar motocin ma suka sake danno kai daga parking space ɗin, taɓe baki ta yi tana mamaki tare da kara jijjinawa girman gidan Abu Abdussalam, bata san daga ina parking space na gidan ma yake ba, ita dai tana ganin motocin kawai suna ketowa ta harabar gidan wadda kuma take da yakinin daga parking space suke fitowa, dan duk motocin gidan ne, duk suna ɗauke da tambarin gidan. Motocin da suka fita na farko na su Ramish, Dr Raj and Rizwan ne, na biyun nan kuma na sauran ƴan uwa, duk airport suka nufa dan tarbo Bilal, ga motocin dukkansu suna da tinted, ba zaka iya ganin waɗan da suke a ciki ba.
Cikin kwanciyar hankali suka hau saman wannan haÉ—aÉ—É—iyar shinfiÉ—aÉ—iyar titin da ta fita zuwa babban gate na fita unguwar tasu, yadda motocin suke tafiya kai É—aya sai sun burgeka.
Ba normal airport suka nufa ba, kai tsaye AL MINHAD AIR BASE suka nufa, wato airport na AIR FORCE kenan, kada ku manta shi Bilal AIR FORCE ne.
Ko da suka isa airport ɗin jirgin su Bilal ɗin bai sauƙa ba, saura five mins ya dira. Hakan yasa suka yi parking a katafaren parking space na airport ɗin, sai dai babu wanda ya fito daga cikin motar tasu, duk suna ciki. Babban airport ne sosai, kalar fentin bangon airport ɗin ma kalar uniform na air force ɗin ne, dan airport ɗinsu ne, ga jiragen yakinsu bitjik ta ko'ina.
Ta ko'ina idan ka juya dakakkun jami'ai masu sanye da kakin air force ne cike a cikin airport ɗin, sai kai komo suke yi, kowannensu ka ɗaga ido ka gani ba zaka so ka sake ganinsa ba, saboda yadda kyawawan fuskokinsu suke a turɓune a kuma fusace, dakon jiran jirgin ƴan uwansu jami'an kawai suke yi, kowannensu ka gani a shirye yake da a mutu ko ayi rai, sun riga da sun sayar da rayukansu, yanzu fa idan suna yaki da zarar an yi bombing na jirginsu an jefe shi daga sama fa shikenan, kashesu bai da wuya, shiyasa ba kowa yake yarda da aikin ba, gara sojoji sau dubu, su sojoji suna iya ɓuya a sunkuru idan ana yaki, su kuwa air force da suke sararin samaniya kowa yana gani, ana jefa nakiya zata yi bombing na jirgin yakin nasu, ko gawarsu kuma ba'a samun gani, dan tarwatsewa suke yi, wasunsu kuma jirgin mai ɗauke da ƙananan nakiya ake tasa ta bi tasu ta yi bombing su tarwatse, musamman idan ƴan ta'addan da suka je yaƙan shegun kai ne, abin baya masu ta daɗi, sai mai taurin rai yake yarda ya yi wannan aiki. Ko shi Bilal Mummynsa ta so ta hanashi yin wannan aiki, King ne ya ce a'a namiji da jarumta aka san shi, shi bai haifi rago ba, jarumai ya haifa, dan haka Bilal zai yi wannan aiki tun da ita ya zaɓa, kun san halin King ai, akwai tafasasshen jini, ita ma Akka ta zage har da karawa abin armashi, wai idan Mummy ba zata iya ganinsa a gabanta yana wannan aiki ba to ya haɗa kayansa ya koma Dubai, wannan shi ne dalilin da yasa tun farko suka dawo Dubai da zama abinsu, Akka ce nan ta hurawa abin wuta, kun santa ita ma akwai son sabgar jarumta, bata da wasa, bata son ragwaye, wannan da namiji ne ita ban san a iya ina zata tsaya ba, duk ta reni su King sun taso da Barden zuƙata, babu tsoro sai ma ban tsoro da suke da shi.
Jiga jigan Fighter Jets ne suka dinfaro airport É—in. Jiragen A400M Atlas da C-130J Hercules, sune a gaba da suka fara saukowa a filin saukar jirgi na airport É—in. Da saukarsu kamar da two mins haka sai ga wasu Typhoon FGR4 da F-35B Lightning suma suka yi landing, dukka jirage ne na AIR FORCE. Jirgin F-15 Eagle ce a tsakiya, wadda kuma ta kasance ita ce na Bilal É—in, a cikinta yake, sannan jiragen Typhoon FGR4 da F-35B Lightning suka rufa mashi baya wajen sauka, su ne suke takewa F-15 Eagle na Bilal É—in baya, so nasa tana dira da kamar minti biyu suma suka dira.
Nan take jami'an Air force ɗin da suke cike a wajen suka fara cincirindon ƙarisawa wajen jiragen.
Jaruman Jami'an Special weapons and tactics guda biyar ne suka fito daga cikin jerin gwanon motocin su Ramish. Gabaɗaya fuskokinsu a matuƙarn turɓune, kamar waɗan da aka aikowa da saƙon cewa wutar jahannama zasu shiga, kun ga kuwa ai ba zaman lafiya mutun ya ji zai shiga wuta.........😅
Duk suna sanye cikin bakaken kaya ne, harta takalmar dake a kafafunsu bakake ne, ga su dai fararen arab guy's kyawawa, amma kada ku so kuga yadda suka haÉ—e rai kamar ba lafiya ba. BubbuÉ—e kofofin motocin nasu Ramish su ka yi, hannayensu na sanye cikin black hands gloves, from up to down dai shagar bakake ne, ba uniform É—insu suka sanya ba.
Omar da Sharifat ne suka fara fitowa kafin su Dr Raj su rufa masu baya. Ramish shi ne a karshen fitowa, sai da ya kalli kofar F-15 Eagle na Bilal ta buÉ—e sannan shi ma ya zuro kafafunsa dake a sanye cikin wasu tsadaddun shoes masu matukar kyau waje. Da alama yana son su fito a tare da Bilal É—in ne, Dr Raj da Rizwan sun yi gaba abinsu, shi kuwa ko da ya sako kafar tasa waje ma sai da ya nuna wannan, izza da fadanci tasu ta jinin sarautar kafin kuma a cikin nutsuwa ya fito waje..............
ðŸ¤KADA KU MANTA WANNAN DADDAÆŠAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘
Share fisabilillahi ðŸ‘
ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥ðŸ¤
ðŸ¤ðŸ”¥ð—¥ð—”ð—ªð—”ð—¡ð—œð—¡ 👑 ð—ð—”ð—Ÿð—œð—¡ð—–ð—œðŸ”¥ðŸ¤
🔥CROWN OF INJUSTICE🔥
ð— ð—”ð—Ÿð—Ÿð—”ð—žð—œð—¡
â¤ï¸â€ðŸ”¥FATEEMA ZAHRA MUSA â¤ï¸â€ðŸ”¥
(â¤ï¸A-K-A ð‘·ð‘¹ð‘°ð‘µð‘ªð‘¬ð‘ºð‘º ð‘»ð‘¬ð‘¬ð‘´ð‘¨ðŸ”¥)
🔥ðŸ¤T🔥ðŸ¤T🔥ðŸ¤W🔥ðŸ¤......💻
â¤ï¸ð‘«ð‘¨ð‘»ð‘¬ 4/9/2024.....âœï¸ðŸ“šðŸŒ¹
For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.
ðŸ¤ð‘ºð‘»ð‘¬ð‘· 1......âœï¸ðŸ“šðŸ”¥
اللَّهÙمَّ صَلّ٠عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌ، اللَّهÙمَّ بَارÙكْ عَلَى Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯Ù ÙˆÙŽØ¹ÙŽÙ„ÙŽÙ‰ Ø¢Ù„Ù Ù…ÙØÙŽÙ…Ù‘ÙŽØ¯ÙØŒ كَمَا بَارَكْتَ عَلَى Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ وَعَلَى Ø¢Ù„Ù Ø¥ÙØ¨Ù’رَاهÙيمَ، Ø¥Ùنَّكَ ØÙŽÙ…Ùيدٌ مَجÙيدٌâ¤ï¸
E____________45🔥
Masha Allah. Sanye yake da tsadaddun suit masu zafa, idanunsa a sanye da white glass kamar medicated, dogo ne sosai kamar King Zuhair, kyakkyawar gaske ne ajin farko, da gani kasan jikan Akka ne, ya fi kama da King sosai, sai dai fa ya fi King Zuhair hasken fata gaskiya, shi fari ne tas har ya ɗan yi yellow yellow, King Zuhair kuwa ya ɗan yi ja, yana da kirar jaruman maza sosai, kamar renon Commander Zafar, arab hairnsa ba'a magana, ta sha gyara sai kyalli take yi, tana kwance luf ka tsantsi, kun dai san yadda gashin larabawa yake, to haka suma dai ƴaƴan King dukkansu gashin kan nasu yake, daga matansu har mazan dukka akwai gashi mai matuƙar kyau kam.
Taku yake yi cikin natsuwa, sai dai da kallo ɗaya zaka yi mashi kasan e lallai jarumin namiji ne sosai mai jini a jika, duba da yadda yake a buɗe kuma yana tafiya ne da jikinsa sosai, ba shi da kiɓa sosai, yana dai murmure, Rizwan ya ɗan fisu kiba a cikinsu.
Kai tsaye wajen F-15 Eagle ya ɗin ya nufa, a daidai lokacin shi ma Bilal yake ƙoƙarin saukowa, shi yana sanye da kakinsu na air force, sai dai kakin yaki ne a jikinsa ba normal ba.
Special weapons and tactics uku ne suka takewa Ramish ɗin baya izuwa wajen F-15 Eagle jet ɗin. A lokacin da ya isa wajen Bilal ɗin ya fito sun rungumi juna da Rizwan har ya sake shi ya rungumi Dr Raj suna ƙoƙarin raba jikinsu.
Yana ƙarisawa wajen, shi kuma Bilal ɗin ya yi saurin sakin Dr Raj suka yi hugged ɗin juna shi da Ramish ɗin, da ka gansu ba tambaya kasa lallai waɗan nan jinin King Zuhair ne, da shi da Bilal banbancinsu kaɗan ne, ya fi Bilal tsawo, haka zalika ya fishi da shekaru, sannan ya ɗan fi Bilal hasken fata da kyau, amma aka ce jini ba wasa ba, akwai kamar jini sosai a tsakaninsu.
Da yanayinsu zaka fahimci suna cikin farinciki, sai dai dukkansu babu alamar murmushi a saman fuskokinsu.
"Yah Bilal nafa riga Yah Ramish ƙarisowa wajenka, amma shi ne ka rungumesa kaki kulani ko?". Cewar Guyson dake tsaye kusa da Sharifat yana ƙoƙarin tura wayarsa a cikin aljihunsa.
"Our Guyson ai naga waya kake yi tun da ka ƙariso nan, da waye kake magana?". Bilal ɗin ya bashi amsa, voice nasa sak na King Zuhair, da alama jinin King ya fi na su Mummy karfi sosai, hakan yasa dukka ƴaƴa suke kamanceceniya da shi.
"Waya na yi da daddy, shi ya kirani, shiyasa na ɗauka, ai kasan idan ba daddy ko su Momma ba ba zan ɗauki call ɗin kowa ina murnar ganinka ba". Ya faɗa yana ɗan tuɓune fuska, irin shi gaskiya ba'a kyauta mashin nan ba.
Raba jikinsu suka yi, sannan Bilal ya rungumi Guyson ɗin haɗe da riƙo hannun Sharifat dake tsaye ta yi shiru kamar wata mai sauraran kira'ar Alqur'ani mai girma, sai binsu da kallo take yi.
"Shikenan our Guyson". Cewar Bilal É—in.
"Yah Bilal sannu da dawowa". Cewar Sharifat É—in.
Yana riƙe da hannunta ya amsa da. "Yauwa lil sis, fatan kuna lafiya?"
Sai sakin ƙayatattcen murmushin take yi ta amsa da. "Lafiya lou Yah Bilal".
Sakin hannun nata ya yi yana ƙoƙarin raba jikinsa da Guyson. "Wato Yah Bilal lil kawai ka gani ko? Ita ce kawai ka tambaya ya take? Ni baka damu da kasan ya nake ba ko?". Cewar Guyson ɗan rigima. Ya yi maganar kamar zai yi kuka.
Idan da sabo sun daba da mitarsa, shi dai kada a nuna wani ya fishi a gabansa, sai shegen kishi tun yana ƙarami, yanzu wai dan me za'a tambayi Sharifat ya take shi ba a tambayeshi ba, kenan anfi damuwa da Sharifat a kan shi, shi ne yake yi wa raki.
Kallonsa da ido kawai Bilal É—in ya yi ba tare da ya yi magana ba, domin idan ya biyewa Guyson sai su kwana a nan. Tsayawa Guyson É—in ya yi a kan shi ba zai tafi ba tun da dai sun nuna sun fi damuwa da Sharifat a kan shi har suna tambayarta ya take shi ba wanda ya tambayi ya yake?.
Ramish ne yasa hannu ya ɗauke shi cak kamar ɗan baby ya saɓa a shoulder ɗinsa suka nufi wajen motocinsu, domin ba biye mashi zasu yi ba, idan ya fara raki kamar wata kaza mai kwanci yake.
Jiga jigan jaruman jami'an air force guda shidda ne suka ƙariso wajen Bilal ɗin, dai'dai lokacin da shi kuma y ƙarisa wajen jerin gwanon motocin su Ramish domin su koma gida. Cikin girmamawa suka ɗaga hannu suka sara mashi, sannan ɗaya daga cikinsu ya ce "Sir office zamu wuce ne?".
Yana riƙe da hannun Sharifat da ya kama tun lokacin da Ramish ya ɗauki Guyson suka nufo wajen motocin, shi kuma sai ya riƙo hannun Sharifat ɗin ya rufa masu baya. Yana riƙe da hannunta ya amsa masu da. "No gida zan wuce, ni da office sai next week kila". Cikin harshen larabci suke maganar.
A cikin mota gidan baya Ramish ya sauke Guyson yana jefa mashi wani irin kallo mai kama da harara. Murmushi Guyson É—in ya sakar mashi domin yasan ma'anar wannan kallo. Wucewa Ramish É—in ya yi ya zaka ta É—ayan side É—in ba tare da ya yi magana ko ya sake bi ta kan Guyson É—in ba.
BuÉ—e mashi kofar motar jami'in Special weapons ya yi, ya shiga kusa da Guyson É—in ya zauna, shi ma Bilal wannan motar ya shiga suka sanya Guyson a tsakiyarsu, ita kuma Sharifat ta shiga wata motar na daban.
Kamar yadda motocin suka shigo a jere haka suka tashi a jere bayan su Rizwan dukka sun koma cikin nasu motocin. Da haka suka nufi gida. Jami'an air force mota guda suka yi masu rakiya zuwa gida, dan Bilal ya ce ba zai je office nasu ba, gida zai wuce, shi ne zasu yi mashi rakiya su tabbatar da ya isa gida lafiya, sannan su koma headquarter É—insu.
A wannan karon gudu sosai motocin suke shararawa a saman shinfiɗaɗiyar titin. Hakan yasa cikin ƙanƙanin lokaci suka isa gida.
Leesharh dake kwance a saman gadonta ne ta ji diran motoci a cikin gidan, jiniya ya karaÉ—e ko'ina, motocin Æ´an'sanda da sojojin dukka sun saki jiniya kamar zasu tafi filin daga, hakan yasa jiniyar take tashin kai, ta yawaita sosai.
A hanzarce ta diro kasa daga saman bed ɗin nata, da sauri ta nufi wajen window domin ta leƙa taga su waye ne?.
Sai dai kash, bata samu damar ganin motocin ba, dan already sun wuce izuwa parking space na gidan, shi kuma parking space É—in yana ta can gefe ne, bata iya ganinsa daga wannan window tata, dan haka bata sami damar ganinsu ba.
Mai da windown ta yi ta rufe tare da sakin labulen, sannan ta nufi waje. Babu kowa a parlournsu, kai tsaye ta nufi barin part ɗin nasu mai gabaɗaya, yau ƙasa ma take son sauƙa. Elevator ta je ta haye ta nufi ƙasa kamar wadda zata ɗauki wani abin. A hawa na biyu ta tsaya, ma'aikata sai hidima suke yi, sai kai komo suke yi, ta sha madarar mamakin ganin ma'aikatan wannan hawa suna da yawa, sai dai bata wani damu ba ta nufi cikin hawar da kyau dan ta sha kallo, ta gaji da kwanciya a ɗaki ne babu abokin hira, ga shi ba da kowa aka yarje mata ta yi hirar ba.
Su Ramish kuwa kai tsaye part ɗinsu suka nufa, shi da Bilal sun jero kamar wasu tagwaye, sai dai Ramish ya ɗan fi tsawo na gaya maku, Dr Raj and Rizwan ma sun jero kansu ɗaya. Ramish yana rike da hannun Guyson dake ta faman kunbure kunbure na anfi damuwa da Sharifat a kansa. Ita kuma Sharifat Bilal ne ya riƙe hannunta suka nufi elevator.
Sam basu leƙa Ummie ba, ita ma bata leƙasu ba sai can yamma da misalin karfe huɗu, a lokacin dakkansu sun yi wanka sun shirya cikin wasu tsadaddun suit masu bala'in kyau, zasu halarci waliman da Abbie nasu ya haɗa ne domin dawowar Bilal ɗin, sai a wannan lokacin ne Ummie ta leƙasu, ita ma ta tsantsar kwalliya cikin wani Turkey gown, kun san yawancin dogayen rigunar mutanen Turkey suna nan da kauri sosai kamar cuit, yadikansu kusan kamar yadikan suit ne, so haka rigar da ta sanya ɗin ma yake, ga rigar ta fita shape ɗinta sosai, ta sha ado kam ba'a magana, ta yi rolling gyalen a kanta.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.