Complete Hausa Novels

Rawanin Zalinci Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Rawanin_Zalinci_Part_1_Complete_Hausa_Novel.txt

Chapter 22 of 24

Cigaba da yi mata tafiyar tsutsa a kafar tata ya yi yana mai cigaba da kallonta, ita ma tana shan pina ɗinta tana kallonsa tana ɗan murmushi. A hankali ya gangaro da kafar tasa izuwa dai'dai sai tin tata, sannan ya sanya ƴatsun kafafun nasa ya riƙo nata babbar yatsar kafar yana wasa da shi.

Duk abin da suke yi King yana kallonsu, amma ya cigaba da cin abincinsa tamkar bai ga komai ba, tunanin abin da zai yi kawai yake yi a ransa, tunanin kalar hukuncin da zai yanke masu yake yi.

Matse mata babbar yatsar kafar tata ya yi a cikin tsakiyar nashi yatsun. Har sai da ta ɗan yamutse fuska alamar zafi, ɗan turo mashi baki ta yi tare da ajiye cup ɗin pinan nata, kamar zata sanya mashi kukan shagwaɓa.

Ganin hakan yasa ya É—an sakar mata Æ´atsun nata, yana saki ita ma tasa nata wai zata kamo nashin ta matse ya ji idan da daÉ—i. Amma ina Æ´an yatsunta ba za su iya kama na shi ba, ya yi mata girma. Kamar zata yi kuka take binsa da kallo tare da turo baki.

Wani siririn cool murmushi ya sakar mata wanda ya sanyata sauke ajiyar zuciya, sannan ya kashe mata ido É—aya. Plate É—in abinci da kuyanga Zubaida ta zuba mata ta jawo ta fara ci tana sakin murmushi, tana jin daÉ—in kasancewa da Yah Jawad a yanzu, saboda yana sakar mata fuska kuma yana mata wasa sosai, so tana jin daÉ—in kasancewa a tare da shi sosai da sosai.

Bayan sun kammala cin abincin ne ya janye kafarsa daga kusa da tata, a hankali ya miƙe tsaye. "Jannat ki kawo mun wayata da na baki room ɗina". Yana maganar unexpect again kallonsa ta sauka a kan King, tun ma daddyn nasu bai yi wani yunƙurin ba ya sakar mashi murmushi tare da sa kai da sauri ya wuce.

Sai dai kafin ya fita muryar King É—in ta daki dodon kunnuwansa da cewa. "Ka sameni a room É—ina yanzu Jawad".

Da okey kawai ya amsa sannan ya fice. Da É—aiÉ—ai da É—aiÉ—ai kowa ya watse a room É—in.

Akka tana shigowa cikin room ɗinta wayarta dake saman bed ya fara ruri. A hanzarce ta ƙarisa ta kai mashi agaji.

Picking ta yi tare da hayewa saman gadon mai gabaÉ—aya.

Daga can ɓangaren Rizwan ya fara tsantsara mata sallama tare da ɗaga mata gaisuwa.

Sai da ta zage shi kafin ta amsa, wai yau kuma wani munafurcin yasa ya kirata? Dan rabon shi da kiranta tun last year sallah da ya kirata ya yi mata happy sallah, to yanzu kuma gulmar me yasa ya kirata?.

Hakurin ya fara bata tare da rarrashi yana gaya mata aiki ne ya yi mashi yawa. Tatas ta zage shi daga shi har su Ramish É—in gabaÉ—aya kafin ta saurare shi, Akka akwai dirama tsohuwar nan.

Cikin zumuÉ—i ya sanar da ita dalilin kirata, ya kira ne ya sanar da ita ya samu mata kuma ba kowa bace face Chuchu, dan haka ta taya shi kafin ya zo.

Wani irin matuƙa fari tas ɗin farinciki ne ya mamaye mata cikin zuciya. Haƙiƙa ta ji daɗi kuma ta yi murna, amma sai ta ɓoye murnar tata, ta fara zazzaga mashi masifa a kan ai dama tasan yanzu ma buƙatar kansa ne yasa ya kirata, to dan haka ya sani ba zata bashi Chuchu ba, kuma dai yasan ita ce mai zartar da hukuncin a kan komai.

Lallaɓata ya fara yi yana magiya tare da marairace murya, yasan Akka ita ce nan take da iko da su da iyayensu, yasan idan ta bashi Chuchun to fa babu uban da ya isa ya hana, haka zalika idan ta hana shi, wannan dalilin ma yasa ya biyo ta wajenta kai tsaye bai je wajen daddy ba, dan ko ya je ga daddyn ma zai ce mashi sai abin da Akka ta zartar ne, so shiyasa ya fara bi ta wajenta, kuma Mammaiensu ce ta bashi wannan shawara, ta ce kai tsaye ya tunkari Akka, kuma kada ya wani ɓata lokaci wajen jira, ya yi saurin tunkararta ya gaya mata, hakan yasa ya gaya mata ɗin.........

Lallai da gaske Mammie ta shirya raba Jawad da soyayyar Chuchu karfi da ya ji, domin kuwa hanyar da ta biyo mai karfi ne wanda ya fi na Jawad karfi, tun da Rizwan ya gayawa Akka shikenan kuma, Akkar zata tambayi Chuchun tana son yayan nata ne ko bata sonsa, idan har ta amsa da tana son shi fa shikenan babu wanda ya isa ya sa a fasa wannan aure sai mutuwa sai kuma wani ikon na Allah. Ku ma dai kun san Chuchu dai tana son yayan nata, dan haka da e tana son shi zata amsa. Akwai cakwakiya ba kaÉ—an ba, akwai tashin hankali.

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼

ABU ABDUSSALAM EMPIRE 🤍🔥

Nutsuwa sosai Leesharh ta yi tana sauraron abin da yake faÉ—a. Daga yadda yake fitar da word's É—insa kai kasan nutsatsen mutun ne mai ji da izza haÉ—e da class, ba karya jinin King Zuhair yana gudana a jikinsa.

Magana yake yi a kan lallai a cikin daren nan dole zasu yi wannan meeting ɗin, domin gobe da safe za su wuce ƙasar Tunisia, so ya zama dole a daren nan su haɗu, umarni ya baiwa wanda suke yin wayar da shi a kan lallai karfe takwas ya samesu a wani katafaren luxurious guests house ɗinsa. Ba taro ne da zasu yi a ma'aikatarsu, taro ne na team guda ba na gabaɗaya special weapons and tactics ba, manya manyan zakarun gurayen mazan dake cikin Team na Ramish ɗin su sha biyu ne dai'dai, kowanne daga cikinsu kuma yana da yaran aikinsa a karkashinsa, hakan yasa waɗan da suke a ƙarƙashin Ramish ɗin sun fi mutun 200, waɗan nan maza sha biyun sune jiga jigai masu kula da kannar dake cikin team ɗin, su suke karɓar umarni daga wajen Ramish ɗin su zartar wa da na kasa da su ɗin, so haka suke, team, team, suke, sai dai team na Ramish ya fi na kowa shahara a cikin special weapons and tactics, saboda bashi da wasa, duk kuma wanda za su kasance a cikin team ɗinsa to ba karamar horar wa yake sakawa a basu ba, domin kuwa shi baya ɗaukar faɗuwa, burinsa a kullum cin ma nasara, baya wasa da aikinsa, waɗan nan gurayen maza guda sha biyu na cikin team ɗin nasa ba karamar horar da su ya yi ba kafin su kai matsayin da suke kai a yanzu, ba shi da aboki daga waje sai cikin gida, su ne kuma Bilal, Rizwan and Dr Raj, haka zalika bashi da wani kusanci da wani a wajen aiki, duk da ya kasance cewa ƴan team ɗin nasa horonsa ne, amma baya yarda da kowa, dan yasan farautar rayuwarsa ake yi kamar yadda ake farautar ruwa a sahara mai tsananin zafin rana, yasan komai hakan yasa bashi da wani makusanci biyun Bilal, Rizwan and Dr Raj, a waje baya yarda da kowa, kallo da ido kawai ta raba shi da kai.

A ko da yaushe yana yawan zaman meeting da waɗan nan gurayen mazan ƴan cikin team ɗin nan nasa domin kara karfafa team ɗin nasu ya cigaba da kasancewa shi ne na ɗaya a cikin hukumar special weapons and tactics, yana son ya kasance a sahun gaba kullum....... Yo dama jinin King Zuhair jinin Akka ai dole ya zama haka, su fa basu ɗaukar wasa a lamuransu, wai kun manta me Akka ta ce ne a kan jarumta?..........😅

Sosai Leesharh ta tsumaya da sauraron zazzaƙar muryarsa, tana naɗar duk abin da yake faɗa tana kuma jin daɗin yadda yake yin maganar one by one.

Bata bar wajen ba har sai da ta dai'na jin maganarsa alamar ya bar wajen kenan.

Cikin hanzari ta fito daga in da ta laɓe ɗin ta nufi room nata, jikinta sai kerma yake yi kamar wadda ta aikata wani abin rashin gaskiya....... Ko da yake rashin gaskiyar ai ta aikata tun da ta yi wa wani laɓe ta ji abin da yake faɗa.

Tana shiga ta haye saman gadonta tana sauke nannauyar ajiyar zuciya, kirjinta sai bugawa da sauri sauri yake yi. Zuciyarta sai harbawa pat, pat, pat, yake.

Wani irin razana ta yi jin vibrate na wayar dake ƙarƙashin pillownta, dama can a razane take tsabar rashin gaskiya, da wayar ta fara vuuu kuma sai ta kusa rugawa a guje.

Dafe kirjinta ya yi tana furta Hasbunallahu wani'imal wakil cikin rawar murya. A hankali ta kai kallonta kan pillown, jiki a sanyayye ta janyo pillows tare da É—auko wayar. Da farko kamar ma ba zata É—auki wayar ba, amma tuna cewa number É—aya ce take kirarta a wayar kuma wannan number babban barazanace ga rayuwar mahaifinta yasa ta hakura ta janyo wayar.

Wani irin wahalallen yawu ta haɗiye lokacin da idanunta suka sauka a kan wannan number, ji take yi kamar ta maka wayar da ƙasa ko ta haɗiyi zuciya da mutu kawai huta, ta fara gajiya da fargaba da faɗuwar gabar da suke jefata a ciki, idan ta cigaba a haka wlh faduwar gaba ne zai zama sanadiyar rayuwarta.

Picking ta yi tare da kara wayar a kunnanta jiki kamar wadda aka zarewa laka.

Daga other side É—in aka fara magana cikin sanyin murya. "A'isha na manta ne ban sanar dake wani abin ba, idan kin je wajen walimar nan ki mayar da hankalinki sosai a kan mutane, babu ruwanki da yin magana da kowa, sannan kada ki manta wajen a cike yake tab da camera's sosai".

A tunanin matar yanzu ne Leesharh zata tafi wajen walimar, bata san ita kam har ta je ta dawo ba abinta, zama ya gagareta a wajen walimar saboda rashin gaskiya.

Da kyar ta É—an iya saita nutsuwarta tare da fara gayawa matar duk abin da ya faru tun daga zuwan ta wajen walimar har izuwa yanzu da take zaune a bakin bed dinta.

One thing about Leesharh yarinyar nan bata karya, kome zaka yi mata in dai zata buɗi baki ta yi magana to gaskiya zata faɗa, sai dai idan tasan gaskiyar bashi da amfani a wajen ko kuma tana tsoron faɗarsa kada ya zame mata illa to a nan kuma shiru zata yi sai dai a kashe ta, amma ba zata taɓa yin karya ba!!.

Wani irin sautin dariya ne ya fito daga ta cikin wayar, a hankali sautin yake tashi, da alama sun ji matuƙar daɗin news da Leesharh ɗin ta basu.

Shiru baiwar Allah ta yi tana sauraron dariyar matar har na tsawon minti ɗaya. Ɗan taɓe baki ta yi tana mamakin ko me ya sanya matar yin dariya? Ta tambayi kanta.

Ta shagala da tunane tunane ta tsinkayo muryar matar tana faÉ—in. "A'isha Allah ya yi maki albarka, ashe da rabon kin kusa komawa wajen babanki, yau kin gaya mun labari mai daÉ—i, amma kin tabbatar a guests house É—insa ya ce zasu yi zaman?".

GyaÉ—a mata kai Leesharh ta yi tamkar tana a gabanta kafin ta ce e ta tabbatar.

"Good! Kenan Ramish zai fita gida kafin karfe takwas na dare, dan shi baya wasa da lokaci, hakan ma dai'dai ne, yanzu dai abin da nake so da ke shi ne, akwai wata magani da zan sanya a kawo maki, ko in ce ki fita ki je ki nemo wacece zata kai wa Ramish abincin dare? Idan kin dawo zan kiraki karfe 6 dai'dai dan na gaya maki a in da zaki ga wannan maganin, abin da nake so da ke lallai lallai ki shammaci mai kai mashi abincin nan ki zuba mashi wannan maganin a cikin cappuccinonsa, dan na san ko bai ci abinci ba tabbas ba zai fita daga gida ba tare da ya sha cappuccino ba, dan haka zai sha maganin kafin ya halarci wannan taron, idan kika yi komai cikin nuna taka tsantsan da kulawa tabbas gobe zan haɗaki da babanki a waya ku gaisa, idan komai ya tafi yadda muka tsara kam ma a cikin daren nan zaki bar gidan, kina barin gidan kuma sai ƙasarku zaki koma....."

Zubur ta miƙe tsaye tare da zaro idanu tana faɗin. "Aunty da gaske zaki haɗani da babana a waya? Kuma da gaske zan koma ƙasarmu?".

Tabbatar mata da hakan matar ta yi kafin ta katse kiran kit. Wani irin farinciki Leesharh ta ji ya rufeta, nan take ta ji kwarin gwiwa, tabbas in dai zata gaisa da mahaifinta a waya to ba shakka yanzu ba sai anjuma ba zata nemo waye zai kai wa Ramish abincin dare.

Lallai ba shakka matan nan sun san lagon Leesharh, sun san da cewa idan suka ce zasu haɗata da babanta to fa zata yi masu abin da suke so cikin sauri, basu zaɓota a kan wannan aiki haka kawai ba sai da suka tabbatar da lallai tana da jajircewa akan abu idan ta sanya kanta, in dai ta ce zata yi abu fa to wlh sai ta yi shi, haka take, sun san zata iya ne yasa suka fara, da sun san ba zata iya ba ba zasu fara wannan aikin da ita ba.

(Ni kuwa na ce tom Leesharh kada dai ki manta Our twin's Obaid and Omaid na Maman Sultan suna nan😌 ki bi dai a sannu.)

Miƙewa ta yi cikin kwarin gwiwa da azamarta har ta ji karfi ya zo mata ta nufi waje, sai murna take yi zata yi magana da babanta, sam bata san illar da abin da zata aikata zai haifar ba. Kasa ta sauko domin neman wacece zata kai mashi abincin dare kuma da wani lokaci zata kai mashi.

Tsabar rashin tsoron irin na yarinyar nan da muradin cin ma burinta karara a saman fuskarta, ba tare da shakkar komai ba ta tinkari kitchen ɗin dake ƙasa kai tsaye abinta, cikin jajircewa take yin komai tare da burin cinma nasara.......... Akwai kura kuwa ba kaɗan ba, kura mai tashi har sararin samaniya ma kuwa. Leesharh fa tana ganin kamar samun gane mai kaiwa Ramish abinci abu ne mai sauki a gareta! Sannan tana gani aiki mai sauki ne ta iya zuba mashi wani abin a cikin abinci ba tare da an gane ba! Ta manta da cewa a Abu Abdussalam empire take. To wai ma me zata zuba mashi? Me amfanin hakan? Kuma da alama so suke ya ci maganin kafin ya fita! Me suke nufi?.

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

GIDANSU KHADIJAH 💔😥

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 11/9/2024.....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________49🔥

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

GIDANSU KHADIJAH 💔😥

Kai tsaye gida Maman Zainab ta nufo, ranta sai tafasa yake yi, tana tunanin hukuncin da ya dace ta yanke wa kanta.

Tun daga É—an nesa da gate É—in gidan nasu ta fara jiyo hayaniya a cikin gidan kamar gidan biki, kamar kuma gidan dambe ne ko filin yaki za'a ce ne oho.

Ruwan bala'i take ji ake ta zazzagawa wanda sam ta kasa iya tantance muryoyin su wanene?. Sai da ta shigo cikin gidan ne ta fahimci muryoyin masu yin maganar.

Wani irin sanyi ta ji a ranta jin suna hayaniya. A fili ta furta ku kashe kanku ma idan kun ga dama Æ´an iskan kawai. Cikin parlourn ta shigo abinta. Kamar bata gansu ba ta wuce fa nufi saman sofa ta yi zaman, bata son shiga in da su Zainab suke ne, dan tasan ba shakka sai ta samesu suna kuka, Allah sarki bayin Allah, a duk lokacin da suka ji wannan bala'i na familyn baban nasu sai sun shiga cikin É—aki sun sha kukansu son ransu, suna shiga tashin hankali, sam abin baya yi masu daÉ—i, ace kullum da familyn babansu da mahaifiyarsu basu shiri, kullum cikin faÉ—a kamar masu ganin hanjin junansu, abin kam babu daÉ—i kwata kwata.

Zama maman Zainab É—in ta yi tare da zuba masu na mujiya tana kallon faÉ—ar tasu, ta mayar da su Tv abinta.

Maman Haidar ce da maman Hanif sai Hajiyarsu suka zo, sun tasa Hauwa a gaba, Hajiyarsu sai tsinewa Hauwar albarka take yi, ita ma Maman Haidar yanzu da yake taga Hajiyarsu ta zo sai ta samu bakin zazzagawa Hauwar rashin kunya dai'dai gwargwado, domin a tunaninta Hajiyar tasu zata tare mata faÉ—a.

Sai da ina, Hauwa ai ba tayar baya bace, bata da mutunci kuma bata san mutunci ba, ka yi mata halacci ma ta ci amanarka bare kuma ka nuna mata iya shege? Ai wlh tsab zata warware maka zani ta yi maka zigidir a tsakar kasuwa, bata da albarka.

Da farko dai ta yi shiru tana jin Hajiyar tasu tana ta kwashe mata albarka tare da tsine mata bata ce komai ba, ta danne bata tanka ba. Amma da abin ya isheta sai ta fara zazzagawa Hajiyar tasu kwandon bala'in, ta yi wa Maman Haidar zazzajen attarugun masifa, ta haÉ—esu ta cinye masu mutuncin tas!!. Sai da suka yi tsit kamar waÉ—an da ruwa ta cinyesu!.

Baban Zainab dai bawan Allah ko sannu bai iya cewa ba, hakan ba ƙaramin konawa Hajiyarsu rai ya yi ba, har ta kusa yi mashi baki saboda bakinciki, ace wai ɗanka yana zaune wata ƴar gantali titi tana zaginka! Ai abin da ciwo over.

Ita kuwa Hauwa yadda kuka san daga tsatson fir'auna ta fito, tsabar rashin tarbiya har da cewa sai ta tsinke Hajiyar da mari har sai ta ga wuta yana bata taurari a face É—inta.

Maman Zainab dai wannan abin ya sanyaya mata zuciya, duk wani tukukin bakinciki da ta kwaso daga wajen bokan nan sai ta ji ya gudu, ranta ya É—an yi haske, ai dama maganin shege sai É—an banza. Ta saki baki tana kallon film abinta, dan wannan bala'in da ake bugawa a cikin wannan gida film ne mai zaman kansa.

Hajiyarsu ce ta tambayi wacece Hauwa?. Baban Zee da bakinsa ya amsa mata da matarsa ce. Ai kuwa idan ran Hajiya ya kai dubu to sai da ya ɓaci a wannan lokaci, cikin fusata tare da bada umarni ta ce maza yanzun nan ba sai anjuma ba ya saki wannan maras albarka!.

Kai tsaye ya ce mata ba zai yiwu ba, babu saki a tsakaninsu, dan haka ba zai saketa ba, su fice su bar mashi gidansa ma tun ransa bai ɓaci ba, sun zo sun ɓatawa matarsa rai sun sa tana ta faɗa a banza.

Saura kaɗan Hajiyarsu ta yanke jiki ta faɗi ƙasa saboda mamaki game da bakinciki, ta san dai tun da take da baban Zee, tun da ya kai shekaru goma a duniya, ya fara mallakar hankalin kansa ba ta taɓa yin magana ya ce a'a ba, komai ta ce mashi da daɗi da ba daɗi hakura yake yi ya amsa mata da to, kuma ya aikata abin da ta ce ɗin cikin biyayya matuƙar bai saɓawa Allah ba, dan ba'a bin umarnin kowa a aikata saɓon Allah, ko alamar ɓacin ran baya so ma ba zaka gani a face ɗinsa ba, kawai zai aikata umarninta, amma yau rana tsaka shi da bakinsa da girmasa yake mayar mata da martani? Abin da bai taɓa yi tun yana yaro ba!.

Wannan abin ya gigitata kuma ya zame mata izina a rayuwarta, yau ta ga ayar Allah ƙarara. Shiru ta yi tana tunani, gani take yi laifinta ne, sam bata kawo a ranta cewa Hauwa ta asirce shi bane, faɗi take a cikin zuciyarta koma me ya yi a halin yanzu laifinta ne, bawan Allah mai biyayya, ta takurawa rayuwarta shi da familynsa, ta hana shi sakat, ta ɓata mashi farincikinsa bayan kuma shi kullum ƙoƙari yake yi ya ga ya sanya ta farinciki, ta cusa mashi damuwa da tunani, duk wani walwala da yake yi sai da ta toshe mashi wannan kofa ya dai'na samun yinta, yanzu ga shi tura ta kai shi bango har ya juyo yana iya kallonta ido cikin ido ya gaya mata ta ɓatawa matarsa rai dan haka ta fita mashi daga gida? Wato ya gaji da irin cin mutuncin da suka rinƙa yi wa Maman Zainab shiyasa yanzu ba zai bari su yi wa amaryarsa ba, yau ga ayar Allah ido da ido ta gani..... Ita fa take wannan tunanin a cikin zuciyarta.

Wannan ba aya ce ga iya Hajiyarsu ba, ina fatan ya zama izina a garemu mata gabakiɗaya, idan yaro yana yi maki biyayya, yana binki sau da kafa, to fa ki yi ƙoƙari kiga kin kyautata mashi kema, kuma ki yi ƙoƙari taya shi neman farincikinsa kamar yadda yake yi maki, in dai ba abin cutarwa kika ga zai aikata ba kada ki matsa mashi wajen ganin kin hana shi yi, zuciya wani lokaci wawan abu ne, kuma wannan ɗabiarmu ce mata, idan munga mutun yana yi mana biyayya yana kyautata mana sai kawai mu yi ta bashi umarni ba kakkautawa, komai sai mu nuna mashi iko, mu hana shi sakat, tabbas wannan ɗabi'ar kaso tamanin cikin ɗari na mata suna aikatata. Ki sani idan kika takura mashi, yana yi maki biyayya kika matsa mashi ke kuma, kika hana shi sakat da wasu umarninki da ba wahayi ne daga sama ba, wlh a kwana a tashi zuciyarsa zata juya maki baya, musamman idan ya haɗu da abin da yake matuƙar so ke kuma kika hana shi, tabbas zuciya bata da ƙashi, ko bai yi maki rashin kunya ba zai ja baya dake, zai ji baya sha'awar ya rinƙa zuwa in da kike, zai ji kin fita a ransa!. Ga kuma shaiɗan a gefe da zai ƙara ingiza zuciyarsa da ya gujeki!!.

To dan haka ni dai shawarata a gareku iyaye masu ƴaƴa ƴan albarka masu biyayya, da ma mata da basu rigada sun zama iyaye ba, shawarar da zan baku shi ne, duk wanda yake sonku yake kyautata maku, yake yi maku biyayya, yake bin umarninku, ku daure ku so duk abin da yake so matuƙar ba cutarwa ce a gare shi ba, ku daure ku so nashi farincikin shi ma, kada ku yi la'akari da ku kuka haifesa dole ya bi umarninku, Allah da ya halicci mu gabaɗaya ma bai ce dole dole mu bi abin da ya halicci mu dominsa ba, saboda yana da wuta da aljanna! Ki sani idan har zaki daure ki bi farincikin ɗanki mai yi maki biyayya, ki so shi ki so abin da yake so, wlh a kullum sonki karuwa zai rinƙa yi a cikin zuciyarsa, zai ji yana son ganinki a kusa da shi, zai ji shi idan ba gida ɗaya tare da ke bama ba zai iya zama ba, bare ace kina son familynsa, ƴaƴansa ma suna sonki, wlh duk yadda zai yi sai ya dawo dake kusa da shi domin ya cigaba da samun farinciki, ba ƙaramin daɗi yake ji ba idan yaga kina kaunar familynsa, ji yake kamar ya haɗiyeki dan soyayya, zaki ga komai kika ce cikin rawar jiki zai amsa maki, sai kiga ya fi umarnin da kike zama ke Hajiya two seater ki ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya ki zayyana mashi su kamar wadda aka saukowa da wahayinsu, ke sam ba zaki yi tunanin halin da zai shiga ba, bukatarki kawai dai ta biya kamar dai Hajiyarsu baban Zainab....... Abin da yasa na yi maku wannan magana saboda rayuwar gidansu Zainab abu ne wanda yake faruwa a cikin al'umma sosai da sosai, to fisabilillahi mata ku ɗauki hanyar gyara domin farincikin kanku da ƴaƴanku haɗe da jikokinku, Allah ka yafe mana kura kuranmu ka iya mana da iyawarka, ka jikan iyayenmu da suka rigamu gidan gaskiya, waɗan da suke raye kuma Allah ka kara masu lafiya da nisan kwana, Allah kasa mu cika da imani, na so na bawa ƴan'mata ma shawara, amma babu lokaci zaku cinye mun filin page ɗin, sai wani lokaci idan alkalamina ya zago ta makamancin hakan.

Sosai Hajiyarsa ta shiga yin danasanin abubuwan da ta yi wa Maman Zainab, dan ita a tubaninta ita ce ta hasasa komai, kuma ba shakka tana da hannu a ciki kam, domin idan da bata biyewa son zuciyarta ba, ta tsaya ta yi mashi addu'a, tana son ganin farincikinsa wlh da wane mutu, wane kaniyar Hauwa ta iya yi cin nasara a kansa, wai kun san karfin addu'ar iyaye kuwa? Musamman ma uwa! Wlh da tana yi mashi addu'a ko shi baya yi sosai babu abin da ya isa ya taɓa shi, amma ta tsaya biyewa son zuciyarta maras amfani, to yanzu ga shi an raba ta da shi, kuma shi ɗin nan dai shi ne mai ciyar da su, shi yake rike da ita da ƴan uwansa su maman Haidar, to yanzu ba dukkansu sun yi rashi ba? A yadda yake ɗin nan ina wani zance kula da su? Ai sai dai kowacce ta ciyar da kanta a yanzu, dan yanzu dai Hauwa ce mai mulki da komai, kuma kunsan Hauwa ƴar tijara kam ba yi masu zata yi ba, sai dai ma ta hana ayi masu! To mata bana son ko wacce readers ɗin litattafaina ta faɗa irin wannan aikin danasanin maras amfani, kun ga aya a fili, da mamarsa tana son abin da yake so, tana zaune cikin kwanciyar hankali da shi tana zuba mashi ruwan addu'oin ai da wane uban Hauwa ta yi nasara a kansa. Dan Allah mata mu gyara.

...........Ni kam anya Hajiyarsu ma bata fi shekaru goma rabon da ta yi mashi addu'a ba kuwa?🤔😅 Mata kullum cikin mashifa da kuntatawa familynsa, bata san idan ta kuntatawa familynsa shi ta kuntatawa ba, ta biyewa su Maman Haidar sun kaita sun baro, kai wato mu mata akwai shegen son girma🤔 kawai ki dake a saman kujera ki ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya kina jerowa yaro umarni babu ruwanki da halin da zai shiga🤔 Allah dai ya shiryamu wlh...............

Jiki a mace Hajiyar tasu ta ce da su Maman Haidar su zo su koma gida. Da mamaki suke kallonta, a tunaninsu ai umarni zata bashi a kan lallai dole ya saki Hauwa, amma sai suka ga akasin haka!.

Juyawa ta yi ta nufi hanyar fita ba tare da ta sake yi wa su maman Haidar É—in magana ba. Har ta kai bakin kofar parlour sai kuma ta juyo da kallonta a kan maman Zainab dake zaune shiru ta mayar da su Tv tana kallo.

Allah sarki maman Zainab sarkin tausayi, gabaÉ—aya sai ta ji mugu mugun tausayin tsohuwar ya kamata, amma ko sannu bata ce masu ba, dan koma me ya faru su suka ja wa kansu!!.

Ƙasa iya yi mata magana Hajiyar tasu ta yi, gabaɗaya kunyar Maman Zee ɗin ma take ji, sai kawai ta juya ta fice daga parlourn zuciya cike tab da danasani maras amfani.

Da sauri su Maman Haidar É—in suka rufa mata baya. Suna barin gidan Hauwa ta dawo da tijararta a kan maman Zainab dake zaune shiru.

Ai tsabar tsanar da maman Zee É—in ta yi masu ma ko tanka mata bata yi ba, dan cewa ta yi magana da Hauwa ma zunubi ne babba, dan haka ita bata sake buÉ—e baki ta kulata.

Sai tijara Hauwar take yi! Ko ci kanki Maman Zainab bata sake ce mata ba, yadda kuka san ta zagi sama ko kuma da mutun mutumi take magana ba Maman Zee ba. Da dai taga ba kulata zata yi ba, sai ta ce da baban Zainab lallai lallai yau sai ya zane Zainab a gidan nan ko kuma ta bar mashi gidansa.

Ta yi hakan ne dan ta ƙuntata zuciyar Mamam Zee, sai dai nan ma dai kamar babu Maman Zee a parlourn, sam bata nuna kamar ma ta ji me suke faɗa ba.

Da ta ga hakan sai ta ce da Baban Zee É—in su je É—aki su tattauna a kan batun auren Khadija da Haidar, dan wannan aure babu fashi wlh.

A wannan karon ne maman Zainab ɗin ta ɗan ɗago idanu ta kalleta amma bata ce komai ba. Wani irin shu'umi kuma munafukin murmushi Hauwar ta sakar mata, dan ta ƙara kona mata rai. A cikin zuciyarta kuma tana faɗin ai wlh tun da baki son Khadijah ta auri Haidar to ba shakka sai anyi auren nan cikin satin nan tun ubanta a hannuna yake, bani da burin da ya wuce in ga ina ƙuntatawa rayuwarki!!............Tashin hankali!! Hauwa fa ƴar iskace bata da mutunci ko kaɗan wlh!! Kowa yasan ko yau ta ce a ɗaura auren nan sai an ɗaura ba fashi, dan uban gayya umarninta yake bi!. Akwai matsala.

Kawar da kallonta Maman Zee É—in ta yi, still dai bata tanka mata ba. Cikin É—aki suka shige da baban Zainab tana gaya mashi yadda za'ayi tsare tsaren bikin, duk dan ta bakantawa baiwar Allah maman Zee rai. Shi kuma baban Zainab komai ta ce sai ya ce yadda kike so haka za'ayi ai Hauwa'u na!.

Suna shiga cikin ɗakinsu ita ma Maman Zee ta miƙe ta nufi ɗakin da su Khadijah suke a ciki.

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

KINGDOM OF POWER 💪🔥💘

Zaune Yah Jawad yake a kusa da King saman bedside drawer, while King ya saman katafaren bed É—insa, suna É—an fuskantar juna, King dai yana aiki ne a laptop É—insa kamar yadda ya saba, dama idan baku manta ba ya ce Jawad É—in ya zo ya same shi.

Shiru Yah Jawad ya yi alamar ya luluƙa duniyar tunani, gabaɗaya yana jinsa babu daɗi, haka kawai yake jin baya son zuwan ƴan uwan nan nasa da za su yi gobe.

Sau uku King yana yi mashi magana bai amsa ba, ya luluƙa duniyar tunani. Sai da ya ɗan taɓa shi ne ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya tare da ɗago idanunsa zuwa saman face ɗin daddyn nasu.

"Daddy ka kammala aikin ne?". Ya tambaya yana tattaro hankalinsa da nutsuwarsa waje guda.

"Jawad menene yake damunka har haka? Tunanin me kake yi haka da har na yi magana baki uku baka ji ba?".

Ɗan zaro idanu ya yi yana mamakin jin daddyn nasu ya yi magana har baki uku yana can yana tunanin da shi kansa bai san me yake tunawa ba..... Tirƙashi.

"Daddy wlh ni ma fa ban san tunanin me nake yi ba, kawai dai ban ji me ka ce ba".

Shiru King ya zuba mashi idanu ba Æ´an sakanni kafin ya ce. "Jawad ka gaya mun me yake damunka? Ina Jaish yake kuma yau bai shigo ba?".

Ɗan shafa arab hairnsa ya yi tare da ƙaƙalo murmushin dole. "Daddy babu abin da yake damuna, Jaish kuma i think ya fita shiyasa bai shigo ba, idan ya dawo da wuri nasan zai zo".

Ajiyar zuciya King ɗin ya sauke kafin ya ce. "Jawad meyasa baka jin tausayin maraicin ka ne? Meyasa kake son ɗaurawa kanka damuwa? Matsalar wajen aiki ce ko ta cikin gida? Ni fa daddynka ne, duk duniya baka da biyuna, ko Abbas bai kai ni kusanci da kai ba, dan shi kansa Abbas da hakwaranka sama da goma ya zo ya sameka tun bayan da ya miƙa mun kai kana cikin tsumma, a tunanina babu wanda ya fini sanin halinka, dan haka kawai ka gaya mun gaskiyar me yake damunka? Ko dai kana da wani mahaifin bayan ni ne?".

Da sauri ya fara girgiza mashi kai bawan Allah. "Daddy tabbas babu wanda ya kaika sanin halina, kuma tabbas bani da wani mahaifin da ya kaika, haka zalika babu wanda nake kauna number one a duniyarnan sai kai, kai ne farincikina daddy, kuma nasan ka sanni in and out, tabbas nasan kaga damuwa a tattare da ni ne yasa ka matsa mun sai na gaya maka menene? Amma daddy ka yarda da ni wlh ni ma ban san me yake damuna ba".

"Kana kewar mummynka ne?". King ya jefa mashi tambaya cike da tsantsar tausayinsa, yana kaunar Jawad over, kuma yana tausaya mashi saboda wasu abubuwa da suka faru a shekarun baya.

Guntun murmushi ya yi kafin ya amsa da. "Daddy ni da ban san ya kalar mum É—in nawa ma yake ba meyasa zan yi kewarta har haka? Ina kewarta amma ba har haka ba, wanda ya rayu da uwa na É—an lokaci ne idan bata nan zai yi kewarta, ni da na tabbata ko rayuwar 30 mins ban yi da ita ba ya za'ayi na ji kewarta har haka? Ban san daÉ—inta ba kuma ban santa ba, kai da Momma kune komai nawa, idan akwai wata uwa da zan yi kwatarta to Momma ce, kuma tana part É—inta, a duk lokacin da na ji kewarta zan je in ganta, dan haka daddy ni bana wani kewar mum".

Haƙiƙa King ya yarda da maganarsa na cewa shi kansa bai san me yake damunsa ba, amma kuma abin ya tsaya mashi a rai sosai.

Ƙoƙarin kawar da zancen King ɗin ya yi ta hanyar sako wani topic dan ya ga ya kore mashi damuwar da take kwance a saman face ɗinsa.

"Aure kake so ko?". Ya jefa mashi tambayar yana kura mashi ido.

Zaro idanu sosai Jawad É—in ya yi, sai kuma ya saki siririn murmushi sakamakon gera guda da King É—in ya É—aga mashi.

"Daddy ni fa ba wani auren da nake so". Ya yi maganar yana ƙoƙarin tuɓune fuska irin shi da gaske yake yin nan.

"Ai duk wanda zaka gansa a cikin damuwa, ka tambaye shi me yake damunsa ya ce maka bai sani ba, to tabbas aure yake so, aure kawai zan yi maka kai da Jaish, shi ne maganin damuwar da ba'a san mecece bace".

"Daddy aure fa? To ina zaka samo matan da zaka aura mana É—in? Ni kam ma dai bana so gaskiya daddy, wata kila dai Jaish, kuma ni daddy Allah ba damuwar aure bace take damuna".

"To me yake damun naka? In dai baka gaya mun me yake damunka ba to ba shakka damuwar rashin aure ce take damunka, kuma zan yi maganin abin, dan ba zan iya cigaba da zuba ido ina ganin my son cikin damuwar da shi kansa bai san na mecece ba".

"Daddyyyyyyyyyy ka fara ko? Ni fa da gaske ba rashin aure bane yake damuna, wai daddy su Yah Ramish da suke manya ma basu yi aure ba sai mu ƴan yara? Kawai salon ka ja mu tsufa da wuri, ni Allah bana so". Yana magana yana kawar da kai, dan kada su haɗa ido da daddyn nasa ya saka shi dariya, saboda ya turɓune fuska ne irin ace da gaske yake yin nan.

"Da gaske baka so?".

Kai ya gyaÉ—a mashi alamar e da gaske yake yi.

"To shikenan, amma gaya mun me a tsakaninka da Jannat?".

Da sauri ya dawo da kallonsa kan daddyn nasu. "Jannat kuma daddy?".

Gera guda kawai King ya É—aga alamar e ita dai.

"Kai daddy kai daddy, ni babu abin da yake a tsakanina da ita, sister mafi soyowa ce a gareni ita da auta, bayan haka babu komai".

"Da gaske?". King ya yi mashi gatse.

"Kai daddy wai ba zaka bar tsokanata ba? Da gaske mana babu komai".

ÆŠaure fuska sosai King ya yi alamar babu wasan nan, cikin nuna isa ya ce. "Me kaje yi a bedroom É—inta ranar wuraren karfe 11, ka san dai na kamaka a bedroom nata ba sau É—aya ba sau biyu ba ko? Haka zalika na kamaka da ita a room na Akka, kai har room É—in nan nawa baku bari ba, daning room ma baku bari ba, and da kuka fita ranar ina kuka je?". Yana magana yana kara É—aure fuska.

"Daddy ni fa addu'ar barci nake zuwa yi mata a room É—inta, kuma ba ita kaÉ—ai ba har da Auta, wai to daddy laifine dan yaya ya É—auki kannensa sun fita yawata gari? Kuma ai kaga a tare da auta muka je, ni daddy ba zaka barni na huta ba ko?".

Wani irin kallo ya wurga mashi wanda sai da ya saka shi sakin murmushi. "Kai daddy kai daddy ka fara ko? Ni Allah wani lokaci kamar nayi kuka nake ji idan kana yi mana irin wannan abin, gaskiya fa na gaya maka babu komai a tsakaninmu".

"To ka ji nace karya ka gaya mun ne? Ko dai ka tsargu ne? Babu rami me ya kawo maganar rami? Kai da kanka da yake kasan ba gaskiyar ka faÉ—a ba duk ka tsargu, ka ruÉ—e kana ta maimaita kalmar gaskiya ka faÉ—a, to shikenan na ji addu'a kake zuwa yi mata a room É—inta, shi kuma room É—in Akka da nawa room É—in fa? Ko nan ma addu'a kake zuwa yi mata?".

Kamar zai yi kuka ya ce. "Daddyyyyy tom shikenan duk yadda ka É—auki tsakanina da Jannat haka ne, amma dai ni nasan babu abin da yake a tsakaninmu, kuma zaka iya tambayarta ma ka ji, amma please daddy ka bar zancen auren nan ga su Yah Ramish a gaba".

"Tom shikenan tun da baka son zancen, nasan maganinku ai, bari su Ramish É—in su zo, kun kusa dai'na yi mun yawon tsakar dare a cikin gida".

Guntun murmushi ya yi kafin ya ce. "Wai ni daddy daga ina ma kake samun information a kanmu ne? Wai duk yadda muka yi fitar sirri ranar sai da kasan mun fita ko? Kuma wai ya aka yi kasan ina hira da Jannat a É—akin Akka?".

Cikin zolaya ya amsa mashi da. "Ka bari Akka ta kamaka a cikin room nata kana soyayya, a nan ne zaka gane ta in da nake samun information, kasan halinta ai, zaka yi bayani randa ta riƙeka".

"Daddy soyayya kuma? Ni fa kawai hira muke yi da su, dan su É—ebe mun kewa".

"Hirar ce har da yiwa autata wayo ku korata ta tafi ta baku waje ko?".

Shafa kansa ya yi yana murmushi, yanzu dai kam ya rasa abin faÉ—e domin ya kare kansa, shi dai ba zai yarda soyayya suke yi ba, dan ba yanzu ya so bayyana soyayyarta ga kowa ba, ita kanta ma bai bayyana mata bare sauran familyn, ai ba yanzu ba a cewarsa.

"Ka rasa abin faÉ—e don cigaba da kare kanka ne?". Ya yi maganar yana É—aga mashi gera.

"Ni daddy barci ma nake ji, kuma da gaske ni da Jannat babu wani abin da yake a tsakaninmu, wai ni yaushe na kori auta ne ma? Daddy masu baka bayanin nan sun yi mun sharri".

Hararar wasa ya wurga mashi kafin ya ce. "Ko? To ce maka nayi akwai masu bani bayananku ne? A kan me zan buƙaci mai saka mun ido a kanku bayan ina da rai'na da lafiyata? Kawai duk abin da kuke yi ne yana cin karo da a lokacin ina wajen, da idona nake ganin komai, wai shin anya ma amsar da ka bawa Abbas gaskiya ce kuwa? Jawad sanadiyyar Jannat ka fara koyan karya ko?".

"Daddy barci nake ji sosai, in je in kwanta please?". Ya yi maganar ƙasa ƙasa irin a ce da gaske yana jin barcin.

Gefensa King É—in ya nuna mashi tare da cewa. "Zo mana ka kwanta, yau kuka fara yin barci a nan ne? Zo mu kwana tare".

A hanzarce ya girgiza mashi kai yana faÉ—in. "No daddy zan je room É—ina in kwanta......."

Katse shi cikin zolaya ya yi da cewa. "Ba zaka iya yin barci ba sai ka yi wa Jannat addu'a ko? To je kayi mata sai kazo mu kwana tare".

Miƙewa ya yi tare da nufar kofar fita yana faɗin. "Allah daddy kai da daddy idan kuka saka mutun a gaba babu daɗi, ni yanzu fa na gaya maka gaskiya babu komai a tsakaninmu".

Still cikin zolaya King ya ce. "To ai dama ni bance ba gaskiya ka gaya mun ba, sannan kuma ni ban ce akwai komai a tsakaninku ba, kawai dai idan ta yi tsami zanji ai".

Ficewa ya yi yana murmushi, daddy ya gama gane komai, amma ya tsaya sai waske mashi yake yi saboda wata banzar dalilinsa na cewa sai gaba zai bayyanar da soyayyarsa................... Allah sarki rashin sani yafi dare duhu, da yasan bala'in da yake tinkarosa a gabansa da cikin daren ba sai gobe ba zai gayawa King gaskiya ya kuma ɓukaci da a ɗaura masu aure gobe da safe, amma bai sani ba!.

Yana fita part na King kai tsaye nasa part É—in ya nufa, wanka ya je ya yi tare da shiryawa cikin tsadaddun kayan barci riga da dogon wando launin brown, ya yi kyau sosai a cikinsu kasancewar yana da hasken fata, yau sai ya kara fitowa sak uncle Abbas, shi ma gashin gerarsa ta kusa haÉ—ewa irin na Jaish, sai zuba kamshin perfume mai daÉ—i yake yi.

Wayarsa ya É—auka tare da fitowa waje. Bai zame ko'ina ba sai É—akin Chuchun kamar yadda kin ya faÉ—a kuwa.

Yau auta bata cikin É—akin, tana tare da Mommarta tun bayan da suka gama cin abincin daren.

Tura kofar ya yi ya shiga tare da yin sallama ƙasa ƙasa. A lokacin kuma ta kammala shiri cikin kayan barcinta kenan, ta hau gadon hannunta rike da waya tana ƙoƙarin kiran layin Rizwan, dama hira suke yi ta ce mashi bari ta yi wanka kada dare ya yi sosai, shi ne ya ce idan ta kammala ta kira shi.

Ta yi matuƙar kyau sosai cikin riga da wandon barcin nata, ga su launin dark purple, kasancewar jajir yasa kalar ya yi mata kyau, sannan sleeping dress ɗin nata sun zauna a jikinta cif cif, ta ɗaure arab hairnta kashi biyu, a kowani bakin jelar gashin nata ta ɗaure shi da rebbon white color, saboda kada ya warware, gashin nasu yana da tsantsine sosai, hakan yasa dole suke ɗaure bakin jelar gashin da rebbon. Da alama sleeping dress ɗin nata basu da hula, dan bata sanya ba.

Jin sallamarsa haɗe da turo kofar yasa ta kai kallonta bakin kofar tare da dakatawa daga kiran Rizwan da take ƙoƙarin yi.

Cool murmushi ta sakar mashi kafin ta ce. "Yah Jawad baka yi barci ba?".

Cool murmushi shi ma ya maido mata tare da maido mata da tambayar tata. "Kema baki yi barci ba?".

Kai ta gyaÉ—a mashi tare da ajiye wayar tata a gefe ta juyo da kallonta mai gabaÉ—aya a kansa. "Yah Jawad to meyasa baka yi barcin ba?". Ta tambaya tana zuro da kafafunta kasan gadon.

"Kasa yin barcin na yi, barci yaki zuwa, shi ne na ce bari na zo mu yi hira". Ya yi maganar tare da harÉ—e hannayensa a saman kirjinsa, sannan ya jingina da jikin door É—in kofar, hakan yasa kofar ta rufe kirif sosai.

Wani irin daÉ—i ta ji da jin kalamansa na cewa ya kasa yin barci ne ya zo su yi hira, tana son kasancewa a tare da shi yanzu da ya dai'na takura mata.

Vibrate É—in wayarta da ta ji ne yasa ta kai kallonta kan wayar. Yah Rizwan, shi ne sunan da yake yawo a saman screen É—in wayar, ji ta yi ba zata iya É—aga kiran ba, saboda a gaskiya tun da har Yah Jawad ya tako kafarsa ya zo har in da take domin su yi hira dan ya kasa yin barci, to dole ta bashi lokacinta su yi hirar. Dan haka sai bata É—auki kiran ba har ya yanke, yana yankewa kuma ta kashe wayar gabaÉ—aya tare da dawo da waÉ—an nan fararen idanun nata a kansa.

Ya zuba mata idanu yana ta kare mata kallo ya jingina da jikin door. "Yah Jawad meyasa kake ta kallona haka?".

Kamar bakinsa na yi mashi ciwo, a hankali ya motsa lips É—insa ya furta. "Saboda kin yi kyau sosai".

Daga in da yake ya jiyo saukar ajiyar zuciyarta, alamar ta ji daÉ—in maganar.

"To Yah Jawad ka shigo mana". Tana magana tana murmushi mai kara mata kyau.

Girgiza mata kai ya yi alamar a'a, kasa kasa ya ce. "Ba sai na sai na shigo ba, ganinki daga nan ma ya wadatar".

"To ni in zo ne?".
Girgizara mata kai nan ma ya yi. "Ba zaki juri tsayuwa ba ai, dan haka yi zamanki a saman bed É—inki daga nan ma ina iya kallonki da kyau".

"Yah Jawad zan iya tsayuwa mana, bari na zo, dan ni bana ganinka da kyau". Ta kai karshen maganar tare da sauƙowa kasa ta nufo shi.

Tun da ta miƙe ya kara kura mata ido from head to toe yana kallonta, kayan barcin sun yi mata kyau sosai. A kusa da shi ta zo ta tsaya tana faɗin. "Yah Jawad Allah kai ma kayi kyau sosai, kalar sleeping dress ɗin nan naka ya yi maka kyau".

Can kasa kamar mai raÉ—a ya ce. "Da gaske?".

GyaÉ—a mashi kai ta yi alamar e. Ji ya yi duk jikinsa ta yi la'asar, ya kasa motsawa daga jikin door É—in, yana son ya É—an karkato su fuskanci juna da kyau, amma ya kasa, saboda wani irin kasala da ta rufe shi.

"Yah Jawad ya naga kuma kamar kana jin barci?". Ta faÉ—a tana jingina da jikin bangon kusa da door É—in.

Nisawa ya yi kafin ya ce. "Ke ki ka ja mun jin barcin ai".
Zaro idanu ta yi tare da cewa. "Ni kuma?".

Lumshe idanu ya yi dan ba ƙaramin kara tafiya da imaninsa ta yi ba da ta zaro idanu.

"Ganinki yasa har na fara jin barci". Ya bata amsa da É—an buÉ—e murya.

"Tom ka je ka kwanta".

Girgiza mata kai ya yi alamar a'a. "Meyasa?". Ta tambaye shi da mamaki. "Saboda ganinki ya fi barcin daÉ—i".

A wannan karon ta ɗanyi mamakin jin hakan, bata damuwa a duk lokacin da ya ce mata ta yi kyau, dan tana ɗaukar hakan a matsayin yabo na yaya da kanwa ne, amma yanzu da ya ce ganinta ya fi barci daɗi sai ta ji kamar Rizwan ne ya yi maganar, dan shi ma yana gaya mata hakan wani lokaci, idan ta ji yana hamma alamar mai jin barci, idan ta ce ya kwanta ya yi, sai ya ce mata hira da ita ya fi barcin daɗi....... Tirƙashi.

Ta luluƙa duniyar tunani bata ankara ba sai ganin hannunsa ta yi saman fuskarta, shafa face ɗin nata ya yi yana faɗin. "Tunanin me kike yi my sister da har ina magana baki ji ba".

Da yake dai akwai yarinta sosai a tattare da ita sai ta kawar da wancan tunanin tare da sakin cool murmushi. "Babu tunanin da nake yi".

Ƴan hannayenta ya riƙo cikin nasa hannun guda ɗaya, wasa da yatsun hannun nata ya fara yi yana faɗin. "Jannat da gaske yau kin yi mun kyau fiye da kowacce rana".

Zata yi magana suka ji knocking na kofar room É—in. A tare suka zaro ido ita da shi dukka. Abin gwanin ban dariya.

Janyota jikinsa ya yi, a kunne ya raɗa mata koma wanene ya zo kada ta yarda ta gaya mashi ita da waye a cikin ɗakin, bari ya ɓuya a cikin toilet ɗinta. Shi a cikin zuciyarsa yana tunanin King ne ko kuma Mummynta, cikin biyun nan, dan yasan auta kam izuwa yanzu ta yi barci, ba zai lamunci wani ya kama shi a ɗakinta almost 11 na dare ba, duk da suke matsayin iyayensa sun san halinsa ciki da waje, su suka renesa, amma dole shaiɗan zai raya masu wani zargin a ransu idan suka gansa a irin wannan lokacin a ɗakinta, so maganin bari kada a fara, kada ya bari su kama shi ma bare shaiɗan ya raya masu wani abin.

Da sauri ya saketa tare da raba jikinsa da jikin door ɗin ya nufi cikin toilet. Sai da ta ga shigarsa sannan ta dai'dai nutsuwarta tare da ɗan ja baya daga wajen kofar, ƙasa ƙasa ta ce. "Wanene?".

MurÉ—a handle É—in door É—in aka yi tare da turo kofar, dama É—azun kofar taki buÉ—uwa ne yasa aka yi knocking, saboda kunga Jawad ya jingina da ita, shiyasa taki buÉ—uwa.

Jin ba'ayi magana ba an turo kofar ne kawai yasa ta É—an zaro idanu..............

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 12/9/2024.....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________50🔥

Jin ba'ayi magana ba an turo kofar ne kawai yasa ta É—an zaro idanu tana jiran kawai taga wanene?.

Tun kafin ya shigo kamshin perfume ɗinsa ya isar mata da saƙon wanene, hakan yasa ta ɗan sauke ajiyar zuciya tare da ɗan sakin fuska.

"Jannat me kike yi har yanzu baki kwanta ba? Almost 11 something fa yanzu, kuma me ya tsayar dake a tsakiyar ɗakin?". Ya jefa mata tambayar tun bai ƙarisa shigowa ciki ba.

Ƴan kame kame ta fara yi, bata iya karya ba, bata son kuma ta karya maganar Yah Jawad, ta rasa me kuma zata ce.

"Jannat ba da ke nayi magana bane? Ko baki da lafiya ne?".

Lokacin guda ta gyaÉ—a mashi ta sake girgizawa, alamar e bata da lafiya kuma a'a lafiyarta lou. Shiru ya É—an tsaya ya zuba mata ido da kyau yana kallon yadda take Æ´an kame kame, zallar rashin gaskiya ne a tattare da ita.

"Ina Jawad?". Ya jefa mata tambayar ne dan yana son fahimtar wani abin!.

A É—an ruÉ—e ta ce. "Daddy ni ma ban gan shi ba". "Keda waye a room É—in da naga kamar alamar ba ke kaÉ—ai bane? Kuma na je room É—in Rahilarh na tatda Auta a can bare nace ke da ita ce".

A hanzarce ta amsa da. "Daddy bani da kowa bane, ni kaÉ—ai ce a ciki, ban jima da fitowa wanka bane, yanzu na gama shirin kwanciya, dama yanzu zan kwanta".

Da hannu ya yi mata nuni da saman bed É—inta. "Jeki kwant to bari na yi maki addu'a, ita ce ta kawoni dama".
A hanzarce ta juya kamar dama jira take yi ya ce ta je ta kwanta.
Binta da kallo ya yi zuciyarsa na ayyana mashi ba ita kaÉ—ai ce a cikin É—akin ba, koma ita kaÉ—ai ce to tabbas Jawad bai jima da barin É—akin nan ba, dan akwai kamshin perfume nasa a É—akin, ga rashin gaskiya dake tattare da ita sosai.

A gefen bedside drawer ya zauna tare da karanto addu'oin kamar yadda ya saba yi masu kullum, ya tofa a hannunsa ya shafeta da shi, sannan da kansa ya janyo mata lallausan katuwar bargonta ya lulluɓeta. Cike da tunani a ransa ya miƙe ya ɗauki wasu remote guda biyu dake cikin bedside drawer. Ya yi amfani da ɗaya wajen kashe wutar ɗakin, ɗayan kuma ya yi amfani da shi wajen rage gudun Ac. Cike da kaunar ƴaƴan nasa ya yi mata good night.

Tana daga cikin bargo ta amsa mashi da daddy Allah ya tashe mu lafiya. Amin ya amsa da shi kafin yasa kai ya fice izuwa É—akin Gimbiya Aneesa Æ´ar Mama. A kowacce dare haka yake binsu É—aya bayan É—aya yana yi masu addu'a tare da dubasu ya tabbatar suna cikin aminci, abin gwanin ban sha'awa, yana sauke hakkinsa a matsayinsa na uba, Æ´aÆ´a mata sai da kula sosai!.

Yana ƙoƙarin janyo mata kofar ɗakin nata ya rufe ne wayar Jawad daga cikin toilet ta fara kara alamar shigowar kira. Ɗan dakatawa ya yi yana son tantance kirar waya ce ko menene? Da yake wayar bata da ƙara kamar android phone. Mamaki ne sosai ya bayyana a kan fuskarsa, shiru ya ƙasa kunne yana sauraro.

Bai kai ga tantance komai ba Jawad ya yi saurin ciro wayar daga aljihun wandon sleeping dress É—in nasa, cikin hanzari ya katse karar yana sauke ajiyar zuciya.

Jin shiru ne yasa King ɗin ya yi tunanin ba ringing na waya ya ji ba, kila gizo abin ya yi mashi, dan haka sai ya ja mata kofar ɗakin nata ya wuce, sai dai har ga Allah zuciyarsa na tunanin kamar Chuchu ba ita kaɗai bace a cikin ɗakin, amma sai ya yi ƙoƙarin kore tunanin tare da shiga wajen Aneesa.

Ɓangaren Jawad ɗin kuwa. Ganin sunan Yah Rizwan ne yake yawo a saman screen ɗin wayar tasa yasa bayan ya ji fitar King ya rufo kofa sai ya yi ƙoƙarin picking. Sai dai bai kai ga ɗauka ba wayar ta katse. Fara ƙoƙarin bin call ɗin ya yi sai ga kiran ya sake shigowa.

Kallon kansa a jikin mirror dake gabansa ya yi, hannu ya kai ya É—an shafi face É—insa kafin ya yi picking.

"Ka fara barci ne my brother?". Rizwan ya jefa mashi tambayar bayan ya yi sallama kenan.

"A'a Yah Rizwan ban yi barci ba, lafiya?"

Daga ta cikin wayar ya jiyo saukar ajiyar zuciyar É—an uwan nasa. "Lafiya lou, amma Jawad ya na ji voice É—inka haka? Baka da lafiya ne?" Cike da kulawa sosai ya yi maganar.

Rizwan da Jawad suna kaunar junansu fiye da tunaninku, yanzu haka King ne ya gayawa Rizwan É—in yana zargin kamar akwai abin da yake damun mashi marayarsa, shi ne yasa Rizwan É—in ya kasa barci ya kira shi domin ya ji menene yake damun É—an uwan nasa, ba zai iya yin barci ba in dai bai san menene yake damun Jawad É—in ba.

One thing da ban gaya maku akan Rizwan and Jawad ba shi ne, Jawad and Rizwan fa uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, dukkansu ba Mammie bace ta haifesu, Mammie matar uncle Abbas ta biyu ce, Sarina ita ce ƴarta ta fari sai Fanan wadda take son Jaish ya aura kenan, ita bata da ɗa namiji. Jawad King Zuhair ne ya renesa, tun ranar da aka haifesa yana cikin tsumma uncle Abbas ya baiwa King shi, shiyasa kuka gansa baya a part ɗin uncle Abbas yake tare da Jaish, tsakaninsa da Jaish kwana uku ne kacal ratar, kusan rana ɗaya aka haifesu kenan, so a tare suka taso, tare suka yi wasa, dan King ya haɗawa Momma sune a Dubai, dan kun san ita a can taken haihuwa, haka kawai King ya zaɓi da ya bata Jawad ɗin ta haɗa da Jaish, ita ma tana ra'ayin rikesa yasa ta roƙa, ko da zata dawo sai ta barosu a can, tare suka yi komai, makaranta da komai har zuwa lokacin da suka dawo ƙasar, wannan dalilin yasa kuka ga suna kaunar junansu shi da Jaish ɗin over.

Sannan Rizwan yana kaunar Jawad fiye da tunaninku, dan shi kaɗai yake da shi, ban san dalilin Mammaien na son haɗasu faɗa a kan mace guda ba, suna matuƙar kaunar junansu, ta zo ta cusawa Rizwan kaunar Chuchu bayan tasan Jawad yana sonta. Shi kuma Rizwan yana yi mata biyayya ne saboda a ganinsa ta riƙe shi tsakani da Allah, bata taɓa nuna mashi wani mugun abu ba tun yana yaro, ta riƙe shi kamar ɗan cikinta, bai san da cewa Allah ne ya taimakesa yake tsalle rijiya da baya daga tarkonta har ya kawo yanzu da Allah yasa ya girma ba, bai taɓa kamata tana ƙoƙarin cutar da su ba ko da sunan wasa, to wannan soyayya da ta nuna masu a zahiri kamar uwarsu yasa suke yi mata biyayya sosai. Baɗininta kuma Allah ne kaɗai masani, Allah ne kaɗai yasan me take shirya masu na mugunta? Kuma menene kudirinta a kan Kingdom namu, Allah masani sai alƙalamina, makirar mata ce sosai, ta iya makirci ta yadda ko baka so sai ka yarda da ita ba muguwa bace ta Allah ce, ta iya takunta sosai.

So a takaice dai yanzu ga shi tasa dukkansu biyu suna matuƙar kaunar Chuchu ba tare da sun san da cewa ɗaya yana sonta ba, ita kanta Chuchun tana kaunarsu dukkansu biyu, sai dai kaunar da take yi wa Jawad na matsayin yaya da kanwa ne, shi kuma Rizwan bayan yaya da kanwa akwai na masoyi a gefe, wlh Mammie ta cucesu over, a yanzu haka duk wanda ya auri Chuchu daga cikinsu zuciyar ɗayansu wanda bai aureta ba sai ya cutu, koma dai ya zama sanadin ajalinsa, kuma su biyun duk randa ɗaya ya gane ɗaya yana sonta to ba shakka ɗayan zai hakura ya barwa ɗan uwansa..... Akwai matsala kam babba ma kuwa. Gaskiya Mammaien ba ƙaramar muguwa bace wlh! Ta cika bakar azzaluma! Dan ba ƴaƴanta bane shi ne ta gwara kansu a kan mace ɗaya! Ko me dalilinta na yin hakan? Wato su mutu idan ma zasu mutu, Allah sarki shi kuma Rizwan yana ganin kaunarsa take yi sosai har yasa ta zaɓa mashi kyakkyawar mata na gani na faɗa, wadda duk namiji mai lafiya dole ya sota! Har da kara kaunar Mammaien ya ji yana yi da ta yi mashi hakan, bai san rami mai zurfi ta tona ta kuma kunna wuta a cikin ramin sannan ta tura shi ciki ba, shi ya ɗauka madarar kauna ce zalla.
(Wai nikam na ce ba ko dai so take duk su haɗiyi zuciya su mutu dan ita bata ɗa namiji ne? 🤔 Ku tayani duba my people's)

STORY🔥

"Babu komai Yah Rizwan".

Daga other side Rizwan ya ce. "A'a Jawad, babu komai kuma? Ni zaka ɓoyewa abin da yake damunka? Idan baka gaya mun ba waye zaka gayawa? Ko kana son ne nima ka hanani yin barci, ka hanani yin komai? Kasan ba zan iya aikata komai ba matuƙar kana cikin damuwa ko?".

"Yah Rizwan please kada ka kwana da damuwa, zan gaya maka, bana son naji wani abin yana damunka". Ya yi maganar tare da nufo kofar fita. Har zai fita kuma sai ya tuna kada Chuchu ta ji abin da zai ce, dan haka sai ya koma ya tsaya a in da yake tsaye É—azun.

"To gaya mun menene yake damun zinariyar zuciyar É—an uwana?". Rizwan ya faÉ—a.

"Yah Rizwan ba komai bane face kewar ɗan uwana Jaish, haka kawai na ƙasa samun nutsuwa a tafiyar da ya yi, kada ka gayawa kowa fa ya yi tafiya, tafiyar sirrice, amma duk na damu sosai, sai nake jin kamar na bishi, mun yi waya da shi ɗazun yake ce mun yana kewata sosai, da tunanina ya yi barci ya tashi, ina jin kamar bani da lafiya ne haka".

Shiru Rizwan É—in ya É—an yi na Æ´an sakani kafin ya ce. "Shikenan my pleasure, ka yi mashi addu'a, kuma ka cire duk wani banzar tunani a ranka, babu komai In Sha Allah, bana son ganinku cikin damuwa, amma idan kaga ka damu sosai to da safe ka bishi kawai, dan ba zan lamunci ganinku cikin damuwa ba"

"In Sha Allah Yah Rizwan zan dai'na damuwa kuma zan yi mashi addu'a". Ya faÉ—a yana sauke ajiyar zuciya.

"To shikenan ka kula mun da kanka sosai da sosai".

Da okey ya amsa kafin shi ma ya ce yayan nasa ya kula mashi da kansa, suna kaunar juna sosai, da haka suka yi sallama. Suna sallama ya nufo waje.

Kasancewar É—akin da duhu dan King ya kashe wutar yasa sai ya kunna hasken wutar wayarsa, nan take haske ta gauraye wajen, gaban bedside drawerta ya je ya zauna.

Hannu ya kai ya yi ƙasa da bargon da King ya rufeta da shi ita kuma ta kara ja har sama ta rufe kanta gabaɗaya. Ƙasa ya ɗan ja bargon zuwa dai'dai kirjinta, hasketa ya yi da hasken wayarsa, ta lumshe idanu kamar mai barci.

Zubawa kyakkyawar fuskarta idanu sosai ya yi, a nan ne ya fahimci ba barci take yi ba, da gangan ta lumshe mashi idanunta. Siririn murmushi ya saki kafin ya kai hannu ya É—an shafi face É—inta. "Tashi to, na gano baki yi barci ba".

Kin kula shi ta yi, irin ita a dole ta yi barci da gasken nan, ga kuma idanunta yana gani suna rawa duk da suke lumshe. Jin taki kula shi ta dake a zaman dole ta yi barci ne yasa ya kifa wayarsa a saman bed É—in ta wajen hasken, nan take duhu ya karaÉ—e ko'ina. Hannu ya kai ya toshe mata hanci saboda tsokana.

A firgice ta buÉ—e idanun haÉ—e da cewa. "Wayyo Yah Jawad zaka kashe ni, wai me nayi maka?".

Zame hannunsa ya yi ba tare da ya yi magana ba. Ajiyar zuciya ta sauke tare da yunƙurawa ta miƙe zaune. Wayarsa ya ɗauko daga kifata da ya yi, haske mata fuska ya yi tana ta aikin turo baki.

"Awww ashe baki yi barcin ba, amma meyasa kika yi mun barcin karya?".

Tana aikin turo baki ta ce. "Ni fa wasa na yi maka, amma shi ne ka kusa kashe ni?".

"Da gaske wasa aka mun?". Kai ta gyaÉ—a mashi alamar e.

"Jannat ya za'ayi in kashe ki? In na kashe ki ai kai'na na kashe! Dan nima ba zan kai labari ba! Kina mutuwa zan biki! Nima da wasa na toshe maki hanci, baki ga na sakeki da wuri ba? Ai na sake ki da wuri ne dan ma kada wani abin ya samun min ke". Yana magana yana kara kare mata kallo daga sama har ƙasa, dan iya shege sai kalle mata kirji yake yi a cikin sleeping dress ɗin, da yake kayan sun zauna a jikinta dai'dai ita, sai alamar komai ya bayyana.

Cool murmushi ta sakar mashi kafin ta ce. "Amma fa Yah Jawad akwai wahala idan aka toshewa mutun hanci!".

ÆŠan zaro idanu ya yi tare da cewa. "Kunji wahala ne?".
Kai ta gyaÉ—a mashi alamar e.
"KaÉ—an fa na É—an rike maki hancin, amma kin ji wahala?".

Kai ta gyaɗa mashi still tana turo baki. Hannu ya kai ya ɗan shafi kumatun nata. "Sorry my Jannat, ba zan ƙara ba, to yi murmushi".

HaÉ—aÉ—É—en murmushi ta sakar mashi wadda ya sanya shi sakin murmushi shi ma. "To shikenan ni zan wuce bedroom É—ina, sai da safe ko?".

Ƙasa ƙasa ta ambaci sunan. Lafiya ya amsa mata da shi. "Allah Yah Jawad bana son ka tafi, ina jin daɗin yin hira da kai".

Ajiyar zuciya ya sauke tare da duba time a wayarsa. 11:44, "Jannat dare ya yi fa, ki kwanta ki yi barci akwai school gobe".

Ɗan turo mashi baki ta yi kafin ta amsa mashi da to. Miƙewa ya yi zuciyarsa cike tab da tunanin zai yi kewarta, ɗan matsowa ya yi ya bata sumbata a goshinta kafin ya ce ta kwanta bari ya mayar mata da bargonta ya lulluɓeta.

Ba musu ta kwanta, ya lulluɓeta, zuciyoyinsu bai so rabuwa ba, amma haka ya yi mata sallama sai turo baki take yi ya fice zuwa nasa room ɗin. Yana tafiya ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita ba tare da ta kunna wayarta ba, daɗin hira da Yah Jawad yau yasa ta manta da hira da Yah Rizwan.

Shi kuwa a nasa ɓangaren ko da ya kwanta bai iya yin barci ba, tunani ne kala kala cike tab a ransa, har wuraren karfe 2 ya gagara barci, daga karshe ya miƙe ya ɗauro alwala ya zo ya fara gabatar da nafilfilu.

Washegari da safe misalin 6:30. Shirye yake cikin wandon Jeans baka, daga ta sama t-shirt fara ce tas, sai ya É—aura long coat zuwa gwiwarsa a saman kayan, ita ma coat É—in baka ce kalar wandonsa, takalmar kafafunsa ma bakake ne, matsayinsa na farar fata sai bakaken kayan suka yi mashi kyau, ga arab hairnsa bakin kirin da shi ya sha gyara.

Kai tsaye part ɗin Akka ya nufa sai zuba kanshi yake yi, office zai je yau da wuri, amma yana da buƙatar sanya ta a idanunsa kafin ya tafi, yasan kuma a part ɗin Akka kawai zai sameta by this time around.

Dai'dai zai shiga part na Akkar shi kuma uncle Taheer kanin Mama yana fitowa, kusan karo suka yi, da sauri ya ɗan ja da baya yana faɗin good morning uncle. Fuska ba yabo ba fallasa ya amsa mashi tare da tambayarsa ya ya kwana ya kuma ya wayi gari. Da Alhdulillah ya amsa kafin ya wuce ciki, shi kuma uncle Taheer ɗin ya fice ya nufi part na mama dan ya duba jikinta............. Allah sarki mama, su Omaid sun ja mata bala'i, sun barta da jinya, suna can gidan Abu Abdussalam, ko me suke aikatawa yanzu?...🤔

Baki a ɗauke da sallama ya shiga cikin ɗakin. Babu kowa sai Chuchu dake ta ƙoƙarin sanya uniform ɗinta, yanzu Akka ta shiga toilet bayan sun gama gaisawa da uncle Taheer, ita kuma Chuchu uncle Taheer ɗin yana fita ta hau shirin zuwa school, dama ta yi wanka shigowarsa ɗakin yasa ta zauna suka gaisa.

Ta zura rigar a kanta tana kokawar sauke shi ƙasa, da yake rigar dai'dai ita yake hakan yasa sanya shi yake ɗan yi mata wahala.

Cike da tsokana Jawad ɗin ya ƙariso ciki, samar rigar ya rike ya hanata janyo shi ƙasa. Ja da karfi ta yi sai ta ji kamar an rike, ga shi bata iya gani bare taga wanene? Dan ta zura rigar a kanta.

A ƙule ta ce. "Auta bana son walaƙanci fa, zaki sakar mun riga na samu na sauke shi kasa na shaki numfashi ne ko sai kin kashe ni?".

Shiru bai amsa mata ba, sai ma da shaiÉ—an ya É—an ruÉ—esa ya zura hannunsa daga ta bayan nata izuwa saman plat tummynta.

Janyota ya yi ta zo jikinsa. Sai surutu take yi a tunaninta Auta ce, sai da ya ɗan wahalar da ita kafin ya sakar mata rigar tare da jan mata shi ƙasa har lokacin hannunsa yana saman cikinta.

Yana sakar mata rigar bayan ya sauke mata a hanzarce ta fara ƙoƙarin juyowa domin taga wanene? Hanata juyowa ya yi ta hanyar ƙara ƙanƙame mata ciki. A garin ƙanƙame ta ɗin kuwa hannunsa ya ɗan haura sama izuwa kusa da kirjinta, hakan yasa ta kurma ihu mai sauti wadda tasa dan dole ya saketa a ɗari ya shiga dressing na Akka.

Yana shiga Akka kuma ta fito daga cikin toilet cikin zafi tana faÉ—in. "Nashi uku! Jannat lafiya? Ihun me kike yi?".

Ƴar waige waige ta fara kamar mai neman wani abin, kuma fa ta gansa lokacin da ya shiga room ɗin, amma ta rasa ita kanta waige waigen me take yi, ta kuma rasa me zata gayawa Akkar.

Shi kuwa sai addu'a yake yi Allah yasa kada Jannat ta gayawa Akka shi ne ya taɓata ta yi wannan ihun, yasan halinta sarai, idan ba shi ya ce kada ta faɗa ba Akka na tambayarta zata shi ne ya zo ya taɓa mata kusa da kirji, yasan yanzu da wuya idan ba gaskiya zata gayawa Akkar ba, ya shiga talatin yau ba uku ba. Da alama addu'ar King na daren jiya ne ta kama shi, dama King ya gaya mashi one day one time Akka zata kama shi yana yi mata soyayya a ɗaki, kuma idan ta kama shi ya shiga uku, to da alama yau ranar tonon asiri ne.......

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

ABU ABDUSSALAM EMPIRE 🤍🔥

Ko da Leesharh ta shiga cikin kitchen ɗin sai ta rasa ina zata nufa, ma'aikata ne birjik suke maƙare a ciki suna ta aikin dake gabansu, babu wadda ta ɗaga idanu ta kalleta ma bare ta sa ran zata iya tambayarta.

Da farko a tunaninta abin da sauki ne, sai yanzu ta fahimci isn't easy ooooo, damuwa ta shiga sosai, ta rasa wa zata tinkara da zancen?. Ta juya gabas da yamma gudu da arewa a cikin kitchen É—in nan bata ga Æ´ar aikin da fuskarta yake a sake bama bare ta tinkareta, ga shi babu wadda ta kulata, sai ka ce basu ji shigowar mutun ba.

Ita fa Leesharh bata ma san da cewa masu girki daban, masu shirya abinci a parlourn daban, sannan masu serving Æ´an gida abinci suma daban, bugu da kari masu kaiwa zaratan samarin gidan abinci suma daban suke. To a gabaÉ—aya cikin kitchen É—in nan a yanzu dai iya masu yin girke girke ne a ciki, a lokaci guda sai a girka abinci almost kala sha biyu, kunga kuwa dole masu yin girkin su kasance suna da yawa, kowacce da aikin da take kamawa, haka zalika kowacce da kalar girkin da take yi, kun san laraba da iya shirya abinci kala kala a saman table. Idan suka kammala yin girkin ne sai masu kwasa su kai dining room su shirya a saman table kuma su zo su fara aikin jidansu su kai, masu kaiwa su Ramish suma su zo su kwasa nasu, haka tsarin gidan yake,

Ta kai almost 30 mins a tsaye a tsakiyar kitchen É—in babu wadda ta ce mata ko ci kanki. Da dai taga tsayuwa ba zai amfana mata da komai ba sai ta duba a cikinsu ta ga mai É—an dama dama dan ta nufeta.

Can ta hango wata Æ´ar matashiyar yarinya da ba zata wuci 17 year ba a duniya, sai aikin yanka kayan lambu irin su Chinese cabbage, cucumber da dai sauransu take yi. Ita kuma sune aikinta, sai ta wuni tana aiki É—aya, dan duk girkin da za'ayi ana amfani da haÉ—in salad dan cin abincin, da rana haka da daddare haka, ga gidan da girma da kuma yawa, cikin wani katon kwando mai girma take yankawa, da yake ta saba sai sam bata ganin wahalar aikin.

Sannu Leesharh ta yi mata, yauwa ta amsa da shi, ta amsa kuma ba tare da ta É—ago ta kalli Leesharh É—in ba, saboda aikin da yake gabanta, daddatsa su cabbage É—in take yi babu wasa, cikin sauri sauri saboda ta kware, kwararriya ce.

Shiru ta yi tana tunanin ta yadda za'ayi ta tambayi wannan yarinyar abin da take buƙata. Ta ɗan yi nisa cikin tunanin da take yi kawai ta tsinkayo muryar yarinyar a kunnenta tana faɗin. "Kina buƙatar wani abin ne? Da me zan iya taimaka maki?".

Tana ƙoƙarin yin magana wani tunani ya faɗo mata a cikin ranta, ba komai bane kuma face tunawa da ta yi da akwai cameras sosai a cikin kitchen ɗin, tambayar mai kaiwa Ramish abinci a wajen babbar barazace a gareta, dan ana ganinsu. Tuna haka yasa ta yi maza ta juya ta fita ba tare da ta sake cewa yarinyar ko sannu ba......... Kai Leesharh fa tana da basira sosai yarinyar.

Kai tsaye room nata ta nufa domin ta je ta sake yin tunani a kan mafitarta. A dai'dai lungun da ta yi wa Ramish laɓe ɗazun suka ci karo da mutun, kasancewar wajen babu wadatatcen haske dan a tsakanin ɗakuna yake, kuma wajen babu Camera.

Rashin haske yasa bata san da waye ta yi karo ba, sai dai koma wacece tabbas macece, dan karon da suka yi kirjin wancan ta buji kafaɗunta, to ta ji tana da breast. Wucewa ta yi da sauri ba tare da buƙaci sanin da waye ta yi karo ba. Ita ma wadda suka yi karon a hanzarce ta wuce kamar maras gaskiya.

Dakatawa da yin tafiya Leesharh ta yi tare da juyowa ta bi yarinyar ne ko matar za'a ce ne da kallo, haka kawai sai ta ji gabanta ya faÉ—i, ji tayi bata yarda da matar ba, duba da yadda ta wuce da sauri kuma bata yi magana ba, ita ce ta bugi Leesharh É—in, amma bata ce mata ko uppan ba ta wuce da uban sauri har haka, hakan yasa Leesharh zarginta sosai.

Da sauri ta juyo domin ta bi bayanta ko idan suka fita haske zata iya ganin wacece?. Sai dai kash! Kafin ta fito wajen haske sam bata ga ko mai kama da alamar matar ba, ta ɓacewa ganinta, da alama wani lungu ta shiga ko kuma wani wajen.

Jiki ba kwari ta juya ta nufi hanyar koma ɗakin nata. Tana barin wajen matar ta fito daga in da ta laɓe ta kusa da hanyar shiga part ɗin su Ramish, ashe tasan Leesharh ɗin ta biyo bayanta, da gaskiyar Leesharh matar bata da gaskiya, kuma ɗaya ce daga cikin masu aikin gidan wadda take a hawa na biyu, ko me ya kawota nan? Ko me ta aikata take wannan uban sauri har da ɓuya haka?.

A bakin gadonta ta zauna tare da buga uban tagumi tana tunanin yadda zata ɓullowa wannan al'amari. Wayarta ta janyo domin ta duba ko matan nan sun turo mata wani saƙo.

Tana kunna hasken screen ɗin wayar sai ga saƙon kuwa ta ci karo da shi sun turo. Buɗewa ta yi ta fara karantawa duk da ba wani kwarewa ta yi a karatun ba. Ba wani saƙo suka tura mata ba face cewa da suka yi ta duba cikin akwatinta sun ajiye mata maganin da suke son ta zubawa Ramish a cappuccino, dan haka ta ɗauko maganin kuma ta kula.

Zaro idanu ta yi tana mamakin ta ya akayi suka iya kawo mata maganin kuma? To ko dai suna tare da ita a cikin gidan ne bata sani ba?. Miƙewa ta yi jiki ba kwari ta nufi wajen akwatin nata. Tana zuwa ta buɗe akwatin da wuri, ga mamakinta sai ga maganin a saman kayanta kamar yadda suka faɗa. Ita dai tasan ɗazun da ta ɗauki kayan sakawarta babu magani a ciki.

Maganin a cikin wani ɗan ƙaramin kwalba yake, kamar kwalbar maganin ciwon idanu, zubawa maganin ido ta yi tana kallonsa, tana son sanin maganain menene? Sai dai ba dama, dan basu gaya mata ba, ita kuma bata isa ta ce zata nunawa Sharifat ta ce zata tanbayeta ko ta san na menene bane, kada ta zo ta ɓata aikinta, amma tabbas tana son sanin maganin menene kafin ta zubawa bawan Allah.

Zuciyarta na ta ayyana mata maganin nan cutar da shi zai yi, zantukan babanta take yawan tunawa a kullum in da yake yawan gaya mata kada ta kuskura ta cutar da wani a duniyar nan, da ta cuci wani gara a cuceta, wannan dalilin yasa duk wani aiki da zasu sakata take yawan shiga zulumin a kan kada ta je ta cutar da wani.

Ta jima sosai a wajen tana tsugunne tana kallon kwalbar maganin kafin daga bisani ta miƙe da maganin riƙe a hannunta, sannan ta rufe akwatin nata, shi kuma maganin ta tura a cikin aljihun wandon jikinta.

Waje ta sake nufa domin kudurinta na neman mai kaiwa Ramish abinci, tana da jajircewa da kuma kafiya a kan abin da ta sanya a gaba, kuma bata taɓa sanyawa ranta sarewa ko karaya.

Sai dai a wannan karon tana yi tana fargaba tare da tsoron kada ta cutar da bayin Allahn da basu ji ba basu gani ba, mutanen da suka karɓeta hannu bibbiyu, suka yi mata gatan da bata taɓa samun makamancinsa ba a rayuwarta, bata taɓa yin tunanin zata taɓa samun irin wannan gata ba, sun bata bedroom haɗaɗɗe, ga cima mai kyau, ga sabulai masu zafi na gyaran jiki, ga haɗaɗɗun kayan sakawa duk bayan wata guda ana sayo masu dayawa, gasu da halacci da kirki sosai. Amma idan ta tuna mata mai nikaf ɗin can ta ce mata ba cutar da shi zasu yi ba, taimakonsa zasu yi, sai ta ji sanyi a ranta, sai ta ji zata iya aikata komai dan ita ma ta taimaka da nata gudunmawar. Amma wani ɓangare na zuciyarta ya ki yarda a kan taimakonsa suke son yi. Tana da ƙwaƙwalwar da basira sosai, amma akwai yarinta sosai a tattare da ita. Masu nikaf kuma da wannan yarinta tata suke amfani dan cika burinsu!!!.

🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘

Share fisabilillahi 👏

ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍

🔥CROWN OF INJUSTICE🔥

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 13/9/2024.....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

E____________51🔥

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼

KINGDOM OF POWER 💪🔥💘

"Jannat lafiyarki kuwa?". Akka ta sake faÉ—a cike da damuwar son sanin me ya sami jikar tata ta zunduma ihu haka.

Dawo da kallonta a kan Akkar ta yi, a hankali ta sake satar kallon dressing room ɗin, da farko kamar zata gaya mata gaskiya, amma sai wani tunani ya faɗo mata a rai, tunawa ta yi cewa to idan har Yah Jawad zai gudu ya ɓuyan wa Akka bai kamata ta gaya mata cewa yana nan ba, yin hakan zai sanya ya ji babu daɗi. Wannan tunani yasa ta dawo da kallonta kachokam kan Akkar.

"Akka babu fa abin da ya sameni, ji nayi ne kamar wani abin ya shiga mun cikin rigata yana tafiya, shiyasa na yi ihu"

Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke daga in da yake tsaye, sanyi sosai ya ji tana ratsa zuciyarsa, ba ƙaramin daɗi ya ji da bata faɗi gaskiya ba, sai albarka yake saka mata a cikin zuciyarsa.

Matsowa kusa da ita a hanzarce Akkar ta yi, riƙota ta yi tana faɗin bari ta duba cikin rigar tata ta gani kada ya zamana akwai wani abin a ciki ya ji mata ciwo, ko ya cutar da ita.

Ƙanƙame rigarta ta yi bata son Akka ta kalle mata tula tulanta, mamaki ne ya kama ƴar tsohuwan. "Jannat lafiya? Ki bari na duba mu gani".

Girgiza kai ta fara yi. "Akka ni ba sai kin duba ba, koma menene ya tafi, kuma ma babu komai a ciki ni ce na ji kamar da akwai wani abin". Ta faÉ—a tana turo baki.

Haba da yake Akka sarauniya ce wajen iya magana, tuni ta fara sababi. "Ah ah ah lallai Jannat, ƴan nonuwar naki ne baki son in gani ko menene?" Nan fa ta fara jero mata kan cewa ai ba ita ba su Aunty MieMie duk taga nasu bare ita, dan haka sai ta duba..........😅

Dariya ne ya so kubcewa Jawad dake laɓe cikin room, yana jiyo duk abin da suke faɗa, yau yaga ikon Allah, yarinya da kayanta Akka ta ce sai ta duba, duk sai ya ji haushi za'a kalle mashi abin da shi ma bai taɓa kalla ba, wai shi ya zai yi da Akkar nan ne? Mata idan ka nuna baka son abu sai ta ce sai ta yi shi, ita fa idan taga kana kin abu ka ce baka so, sai ta ce rashin gaskiya ka kullah a wajen, dan haka sai ta ce sai ta gani!!.

Jawad dai bai ji daɗin hakan ba, dan yasan ran Chuchunsa zai ɓaci sosai, babu wata budurwa da take tasowa wadda zata so a kalle mata abinta, bare ma idan tana da kunya, wannan dabi'a ce ta mata, a jininmu yake.

Ita kam Akka ta kafe sai ta duba cikin rigar, ita kuma Chuchu taki yarda har da kukanta, ran Jawad ya ɓaci sosai, kamar ya kifawa Akkar nan mari yake ji, sai dai ba hali, ya suka iya da ita? Ai dole sai hakuri.

Da Akkar ta ga da gaske kuka Chuchun take yi da hawayenta, sai ta kyaleta ta koma cikin toilet dan dama wanka zata yi, tana shirin farawa kenan ta jiyo ihunta, so sai ta koma kawai tana yi mata sannu haɗe da surutun Chuchu na ɓoye mata ƴan nonuwa.

Tana shiga cikin toilet ɗin ya fito da sauri, ransa a ɓace saboda sanya mashi beb ɗinsa kuka da tsuhuwar nan tasu ta yi. Ya ɗaure fuska kamar hadari.

Yana zuwa in da take ya riƙo hannunta tare da ɗauka mata school back ɗinta dake saman gadon Akkar wadda ta ajiye da kanta. Ya riƙo hannunta tare da nufar kofar fita. Har lokacin ƴan siraran hawaye suna bin saman ƙuncinta.

Kai tsaye part É—insa ya wuce da ita ba tare da ya ce mata ko uppan ba, ya kuma yi sa'a bai ci karo da kowa a hanya ba har ya isa part É—in nasa, kasancewar da safe ne kowa yana can yana ta faman aikin shiryawa, masu zuwa school suna nasu shirin, masu zuwa office suna nasu, masu yin breakfast suna fama, kowa dai yana room nasa yana abin da yake yi.

A bakin bed É—insa ya zaunar da ita tare da ciro handkerchief mai kyau daga aljihunsa, ya zauna saman bedside drawer, a gefenta ya ajiye mata jakarta kafin ya kai hannu a hankali ya fara goge mata hawayen nata.

"Am so so sorry my sister, duk ni na ja maki yin kuka da sassafen nan, kyale Akka hai ki dai'na kuka ba zata gani ɗin ba". Ya faɗa ƙasa ƙasa.

Ƙasa ta yi da kanta, kunyarsa take ji sosai saboda ya ji yadda suka yi da Akka, ga Akka bakinta babu full stop ta rinƙa kiran sunan tula tulan a tsiraransu, abin ku da tsoffi sam bata wani sakaya sunan ba, ta rinƙa ambatarsa ba kakkautawa, wannan dalilin yasa Chuchun ta ji tana bala'in kunyar yayan nata, dan ya ji komai.

Shi ma ya fahimci kunyarsa take ji, sai ya kawar da zancen da cewa. "Yau na kai ki school da kai na ko?". Ya yi maganar yana ƙurawa jikinta ido, gani yake kamar gizo idanunsa suke yi mashi, kamar kuma da gaske ne bata sanya vest a ciki ba, kuma bata sanya bra ita.

Yana son ya tambayeta kuma yana jin fargabar yadda zata É—auki abin, tsoro yake ji kada ta kalli hakan da wata manufa ko kuma ta fara gudunsa ko dai ta fara jin kunyarsa sosai. Idan É—aya daga ciki ya faru ba zai ji daÉ—i ba!.

Wani tunani ne ya faɗo mashi cikin ransa, idan ya tashi daga office ya je ya yi masu shopping na vest dayawa ita da Auta, sai ya bawa Autar ya gaya mata kada su sake saka kaya ba tare da sun saka vest a ciki ba, wannan ce tunanin da ya yi, yanzu haka sam ransa bai so ta tafi school a haka ba, amma ba yadda zai yi, idan ya ce zai yi mata magana a yanzu to tabbas zata haɗa maganar da abin da Akka ta yi mata ta kwaɓesu, daga haka zata fara ja baya da shi.

GyaÉ—a mashi kai ta yi alamar e ya kaita school da kansa. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Kin yi breakfast ne?".

Kai ta girgiza mashi alamar a'a. Waya ya É—auko ya kira kuyanga Zubaida a kan ta kawo mashi kayan breakfast yanzu. Yana ajiye wayar ya hau janta da hira dan ta saki jiki ta mance da abin da Akka ta yi mata ta koma walwalarta.

Ba'afi minti biyu da kiran da ya yi wa kuyanga Zubaida sai gata ta iso baki É—auke da sallama. Izinin shigowa ya bata ba tare da ya kawar da kallonsa daga kan Chuchu dake ta faman murmushi ba, har ya mantar da ita kuncin da take ciki, ya sanyata farinciki.

Saman carpet ya yi mata umarnin ta ajiye mashi abincin, a hanzarce ta karɓi umarninsa tare da aiwatarwa.

Bayan ta fita ne ya ce da Chuchun ta zo su je su yi breakfast a tare. To ta amsa mashi da shi, hannunta ya riƙo suka nufi wajen kayan abincin.

Zama ya yi tare da zaunar da ita a kusa da shi. Cup mai shake da coffee mai zafi ya ɗauko ya kai mata bakinta. Ba musu ta buɗe baki ta fara karɓa. Wayarsa ce ta fara kara daga cikin aljihun coat ɗin jikinsa. Hannu yasa ya ciro wayar tasa.

Yah Rizwan, shi ne sunan da ya bayyana a saman screen É—in wayar. Cigaba da bata coffee É—in ya yi yana haÉ—a mata da pepper soup na kaza mai bala'in daÉ—i. Cike da kaunar yayan nasa ya É—auki wayar yana kuma mamakin kiran da yayan nasa ya yi mashi da sassafe haka.

"Assalamu alaikum Yah Rizwan barka da safiya". Ya faÉ—a cikin nutsuwa, yana magana yana yanko tsokar kazar yana cusa mata a baki. Ta saki jiki sai ci take yi abinta.

"Jawad ka tashi lafiya?". Rizwan ya tambaya, daga jin muryarsa kasa yana kaunar ɗan uwan nan nasa sosai, sannan muryarsa da alama damuwa matuƙa a tattare da ita.

Da lafiya lou Alhdulillah ya amsa mashi da shi, sannan ya É—aura da cewa. "Yaya ya naga ka kirani da sassafe haka? Ko dai akwai wata matsala ne?".
Sai a lokacin Chuchu ta É—ago idanu tana kallonsa jin ya ambaci matsala.

Daga ɗayan ɓangaren ya amsa mashi da. "E akwai matsalar babba ma kuwa, amma ba ita ce tasa na kiraka ba, na kiraka ne dan naji ya ka kwana? Ya kuma ka tashi? Jiya ban samu ishasshen barcin kirki ba, saboda tunaninka".

Miƙawa Chuchun cup ɗin coffee ɗin ya yi tare da miƙewa tsaye ya nufi hanyar fita yana faɗin. "Matsala kuma Yah Rizwan? To matsalar me? Meyake faruwa?"

Bin shi da kallo ta yi har ya ficewa ganinta. Cigaba da cin abin nata ta yi tana tunanin to matsalar me aka samu kenan?.

After some minutes ya dawo cikin É—akin fuskarsa babu annuri ko kaÉ—an, da alama Rizwan É—in ya gaya mashi wani abin da ya É—aga mashi hankali sosai, jikinsa duk ya yi sanyi sosai kamar ba shi ba. Kusa da ita ya koma ya zauna yana faÉ—in. "Jannat ci abinci da wuri na kai ki school akwai in da zanje".

Cikin sanyin murya ta ce. "Yah Jawad kai fa? Ba zaka yi breakfast É—in ba ne?".

Kai ya gyaÉ—a mata alamar e ba zai ci ba, sannan ya É—aura da cewa. "Sauri nake yi, ki ci da wuri in kaiki school ke dai, idan na dawo daga in da zan je zan yi breakfast É—in".

"Yah Jawad meyasameka naga fuskarka ta sauya haka". Ta faÉ—a tana kallon face É—in nasa.

Babu komai ya amsa mata da shi, sannan ya fara ƙoƙarin kiran number Jaish domin su gaisa su kuma yi magana, dan basu yi wayaba, ya so ya kira shi tun farkawarsa daga barci, amma bai samu dama ba, ya sha'afa.

Ringing wayar ta yi har ta katse ba'a ɗaga ba, duba time ya yi a danƙareriyar watch dake hannunsa. 7:05 am, yakamata ace Jaish ya tashi barci yanzu ai. Ya faɗa a bayyane tare da sake gwada kiran number.

A karo na biyu ma ba'a ɗaga ba. Knocking na kofar ɗakin da aka yi ne ya ja hankulansu shi da ita izuwa bakin kofar. Kasa ƙasa ya furta wanene?.

Daga wajen kuyangarsa ta amsa mashi da ita ce, tazo tana son fara yin aikinta ne na gyaran É—aki. "Ki je sai anjuma ki dawo". Ya faÉ—a yana dawo da kallonsa a kan wayarsa da call ya shigo ciki yanzu.

Mammie, shi ne sunan da ya bayyana a saman screen É—in wayar. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya É—auki call É—in, yana sonta, ya É—auketa kamar uwa, saboda yana ganin cewa tana son su kuma ta rike su kamar Æ´aÆ´an cikinta.

"Good morning Mammie". Ya faÉ—a cikin sanyin murya.

Tana daga zaune saman sofa a fatafaren parlournta, ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, kamar kullum tana cikin haɗaɗɗen kwalliyar nan nata na alfarma, ga ruwan madaran gwala gwalai da ta zuba wuya da hannu, ta fito a hamshakiyarta, ta ko'ina dai bata da makusa sai bakar zuciyarta, kyakkyawar macece ga iya ɗaukar wanka, sai dai kash, kyan ɗan macijine. Daga gefenta wata hamshaƙiyar budurwace take zaune mai tsananin kama da ita, daga gani ba tambaya kasan kanwarta ce, dan sun yi kama sosai, yarinyar ba zata wuci 25 to 27 years a duniya ba, ita ma kyakkyawace, ga shi ta iya ɗaukar wanka kamar Mammie ɗin, yanzu haka ta sha wanka, duk wanda ya kalleta sai ya sake waigowa ya kalleta, da alama abin ya samo asali ne, duk yadda aka yi ainahinsu ƴan son gayu ne sosai.

"Morning Jawad how was your night?". Ta faÉ—a tana kallon kanwar tata.

Bayan ya amsa mata sai ta ce. "Kafin ka tafi office ka sameni a parlour mu É—an yi magana".

Da okey kawai ya amsa mata, katse kiran ta yi tana bin kanwar tata da kallo. "Aliyah lafiya kike cunkushe rai haka?".

Kara tunɓune fuska kanwar tata ta yi kafin ta ce. "Aunty ba dole na turɓune fuska, ni ban san ya zan yi ba, saboda King nake zuwa gida nan, amma har in je fadarsa in gaishesa in fito baya ɗaga idanu ya kalleni, kuma ni ina matuƙar sonsa Aunty"............. Tashin hankali kenan, yau ake yinta, ita King ɗin da kansa ma take so ba ƴaƴansa ba, lallai wannan ta ɗebo da zafi, kai bama da zafi ba ta ɗebo mai tafasa!!.

Wani irin zaro idanun Mammaien ta yi, tamkar idanunta zasu faɗo ƙasa. "Amma dai Aliyah baki da hankali! Ko dai kin sha wani abin ne yau kafin ki zo gidan nan! King Zuhair ma kike magana ko wani King ɗin da ban sani ba?!". Cikin tashin hankali ta yi maganar.

Kara turɓune fuska sosai ta yi. "Aunty idan ba King Zubair ba wani King muke da shi mai power a ƙasar Tunisia? King Zuhair nake magana a kai mana, kuma shi nake so, shi nake burin aura, In Sha Allah kuma ni ce cikon matarsa ta huɗu! Da ni zai rufe kofa, ko ana ha maza ha mata wlh sai King ya aureni!!". Babbar magana!.

"Aliyah lallai mutuwa kike nema, wlh idan baki yi hankali ba a ɗanya ƴaƴansa zasu cinye namarki, wai ke Aliyah ni da nake nan ina ta faman yadda zan yi in ga King auri Jahiz ɗan autan su King ɗin, shi ne bashi da aure, bai taɓa yin aure, matashi saurayi ne mai jini a jika, ga shi shararren mai kuɗi, duk duniya ta san shi, ya fi Abbas fa kuɗi nesa ba kusa ba, ke in takaice maki ma wlh zai iya fin King Zuhair ɗin ma kuɗi, ga shi sabon jini, shararrene da duniya dukka suna san shi, shi ba iya ƙasar Tunisia ne kawai aka san shi ba, duniya gabaɗaya ta san shi, shararren ɗan kwallo ne da yake bugawa Real Madrid, ke kanki kin san da haka, kin san Jahiz ganinsa da ido ma ba abu bane mai sauki, ko a cikin family na kusa kusa ba kowa yake samun damar ganinsa ba, ni kai'na da nake matsayin matar yayansa ma idan ya zo gidan nan ba samun ganinsa nake yi ba, idan kinga na gansa to yayansa yana nan, nan ne zai shigo wajen yayan nasa, a nan nake samun damar ganinsa, kuɗi iya kuɗi yana da shi, ga shi sabon jini matashi, me kuma zaki buƙata....."

Katseta Aliyah ta yi da cewa. "Sarauta! Yana da sarauta ne? Duk kuɗinsa a banza idan ba shi da mulki, burin mulkar ƙasar Tunisia nake da shi ni ba kuɗi ne a gabana ba, burina in yi mulki, in zama mai faɗa aji, dan haka yasa nake son zama mace ta huɗu da zata rufe kofa a zuciyar King Zuhair....." Tashin sense!!.

"To idan mulki kike so ai magajin masarautar zaki ci burin ki aura, magajin wannan powerful seat ɗin zaki kwaɗaitu da son aura, ga Ramish! Ga Bilal! Ga Suraj! Ga Jaish! Sannan ga Aryan! Ɗaya daga cikinsu yakamata ki zaɓa ai, dan sune zasu gaji wannan kujera mai matuƙar power da karfin ikon, in dai burinki ki zama mai faɗa a ji a faɗin ƙasar Tunisia ne to ɗaya daga cikinsu zaki buƙata........"

Kara kwaɓe fuska ta yi tare da wurgawa Aunty tata wani irin kallo mai kama da zargi. "Gaskiya Aunty kanki baya kawo wuta sam sam, ni fa ba ce maki na yi ina son in auri wanda zai yi mulki a nan gaba ba, so nake na haifi wanda zai yi mulki a nan gaba, kina tunanin ko na auri ɗaya daga cikin ƴaƴan King zan samu yadda nake so ne? Gaskiya Aunty sam baki tunani mai kyau, ai ko na auri magajin kakkarfar kujerar izza buƙatata bata biya ba, dan dai ke da kanki kin san ƴaƴansa ba masu juyuwa bane, baki isa ki juyasu yadda ranki yake so ba! Amma idan kika auri uban kika haifi naki ƴaƴan, ko ba yanzu ba nan da shakaru 20 zuwa da 25 zaki zama yadda kike burin ki zama, zaki zama mai karfin iko, a duk lokacin da aka ce ɗanki ne a saman wannan the most powerful seat ɗin, sannan ya sanya powerful Crown a kansa, ai kinga daga nan zaki murza kambunki son ranki a faɗin ƙasar, amma idan kika biyewa ƴaƴan nan nasa sai su ce maki basu son sarauta kamar dai Yah Abbas, kin ga shi ma ya ce maki baya sha'awar sarauta, to nasan ƴaƴansa ma yadda suke shararrun ƴan bokon nan ba wani mulki da za su yi, shiyasa bana son na auri magajin mulki, nafi son na haifi magaji wadda ko ya ce baya son ya yi mulki zan tursasa shi dole ya yi, sannan shi Jahiz da kike magana kada ki manta bashi da gadon mulkin nan a yanzu, dan King yana da yara, da bashi da yara ne sai kaninsa ya hau kujera........"

Kallon tsab Mammie ta yi mata. "Lallai Aliyah kin girma, waye ya ce maki Jahiz bashi da gadon mulki? Yana da shi mana, idan su Ramish suka kekashe ƙasa suka ce basu da ra'ayin mulkar ƙasar Tunisia ai dole idan King ya tsufa Jahiz ya karɓesa tun da Abbas baya ra'ayi".

Cike da rashin respect a maganar tata ta furta. "Aunty koma dai menene ni magajin nake son haifa, magajin da ko baya son mulki zan tursasa shi yi dan cinmma burina, dan haka ni King Zuhair ne burina, shi nake son aura!".

"Aliyah King Zuhair ya fi karfinki, Jahiz shi ne zaɓin da na yi maki, dan haka ki dai'na maganar King!!".

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.